You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waga ta ce "Ya aka yi?".

Cikin kuka baba uwani ta ce "Ina cikin bala'i ranki ya daWe, yarinyar nan wai ashe tana sane ta ce kina yi wa takawa asiri, dan ta gane idan ina kai miki maganar giwa, wallahi a sashinki ma akwai munafukinta, wallahi yarinyar nan ba yarinya ba ce aljana ce ranki ya daWe, dan Allah kiyi wani abu a kai".

A fusace Mummy ta ce 'Kuma ki ka samu ?warin gwiwar kirana ki gaya mini wannan shirmen? Yayi miki kyau, ki mayar da hankali ki yi mini aikin da na saka ki, na san matakin da zan Wauka a kanki"

"Na shiga uku, hajiya wani irin mataki?" Katse wayar Mummy ta yi, ta jefar a kan gado ta ce "Aikin banza"

**
Kamar kullum takawa ya je gaida ammi, ya tarar da kaya a Wakinta, har da ?aramin keke na yara.

Ya ce "Ammi, wannan kayan fa?"

"Mahmud ne ya saya wa takwaransa"

Har zai yi magana, da ya kalli fuskar ammi sai ya fasa.

Ammi ta ce "Yauwwa, ban gaya maka wani abun arziki ba".

"Wane abun arzikin?".

"Ina ranar da jabir ya zo, muka fita ka ke tambayata fara'ar me nake yi?"

Ya jinjina kai alamar ya tuna.

"Wata magana ya zo mini da ita, da ta faranta mini rai"

"Maganar me kenan?"

"Cewa yayi ya na son Iman, kuma aurenta zai yi"

Adam ya yi Jimmmm sannan ya ce "Yaushe kuma ya fara sonta?"

Ammi ta ce "Ban sani ba, ya ce mini dai zai je ya lallaSa hajiya Lubabatu, ba ka ji daWin da na ji ba, idan ta amince ai na ji daWi, tun da Wan gida ne, kuma na yaba da shi, jabir Wa ne a wurina"

Adam jinjina kai kawai yayi, ya tashi ya ce "Bari na je wurin aiki, ina da idan na taso zan biyo, sai na dawo"

Ammi ta ce "Allah ya tsare".

Abun ya din ga damun Adam, baya son tonawa Jabir asiri, amma sam bai dace da auren Iman ba, salihar yarinya kamar wannan, duk da kashedi da gargaWin da yayi masa, bai ji ba, bai kuma janye maganar son auren Iman ba.

Ga wanccan batu da rumaisa ta Waukko masa a kan Jamil, gaba Waya sai abubuwan suka ?ara rikice masa. Sosai yake son saka pressure a kan Jamil, dan har yayi maganar da Bashir ma, sai dai gefe Waya yana tunanin anya haka zai yiwu kuwa? Kar ya Sata zumuncinsu, tayaya Jamil zai saka hannu a Satan aisha, bayan babu wanda ya san ma ta zo ?asar sai shi, kar ya biyewa shirirtar rumaisa ta rufta shi, amma duk da haka akwai ?amshin gaskiya a maganganunta.

?arfe sha biyu ya kira sidi a waya, ya ce ya je ya Wauki rumaisa, ya mayar da ita gida.

?arfe biyu ya tashi, daga wurin aiki, ya tafi wurin aikin su Jabir.

Fuskar Jabir babu yabo babu fallasa, suka gaisa.

"Jabir, zuwa na yi na ji dalilin da ya sanya ka je ka samu ammi, ka ce mata kana son iman, baya ka san yadda muka yi da kai?".

"Tambayar da ka zo ka yi mini kenan Adam? Ka watsa komai kana neman ka Sata zumunci, saboda kana auren wannan ?ar yarinyar, gaba Waya kanka ya juye, abun da ta ce kawai shi kake yi babu bincike? Ka je ka cewa Jamil yana da saka hannu a Satan matarka, ta yaya ?ar uwassa ce fa, ta yaya zai yi hakan? Ta ce Mummy tana yi maka asiri, magana ta koma kunnenta, ka je ka yi wa ?annenka wula?anci dan su je gidanka duba ka, dan rashin ta ido, a gaban Mummy, yanzu kuma ka zo kana maganganu dan na ce zan auri Iman, kai ka san aurena da iman shine rufin asirinta, kuma ka sani Mummy sun kai ?ararka wurin mai girma wambai, dan yau da safe ya kira Ammi a waya, lallai yana nemanka, kuma zama za ayi na mussaman a kanka da matarka, dan da yiwuwar har gaban mai martaba, ba zai yiwu dan ka yi aure, ka hargitsa mana family ba.

Duk da gaban takawa ya faWi, amma cikin jarumta ya ce "Jabir, gaban mai martaba ba gaban Ubangiji bane ba, daga nan a kaini duk in da aka ga dama, shi ciki da gaskiya, wu?a ba ta taSa huda shi" ya fita ya bar office Win.

Yanayin yadda ya zo ya wuceta a falo, ya sanya ta gane, akwai damuwa, har zata basar da shi, sai ta ji ba zata iya ba, ta bi bayansa.

"Papa, yau ba cin abinci, ba magana, iya sanina ban yi wani laifi ba"

Ya Wan lumshe ido ya ce "Bakomai, ki je bacci zan yi".

"Ba bacci ka ke ji ba, wani abu ne yake damunka",? ta yi maganar tana murza zoben hannunsa. A hankali ya buWe idonsa ya kalleta.

Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Bari na yi maka ta Yaya usy, ya ce gist me masoyiya ya ake ciki, to gist me aboki ya ake ciki?"

Ita duk tsananin situation, ba ka rabata da wasa.

Sai ya samu kansa da gaya mata halin da ake ciki.

Ta kwashe da dariya ta ce "Ohh, ni ?a su, yaro bai san wuta ba sai ya taka, to kar a fasa kaini wurin mai martaban mana, idan ban warware kowa a gabansa ba me nake, ni fa bana tsoron kowa sai Allah, kuma wallahi duk abun da na faWa gaskiya na faWa. Sai in faWi komai a gaban mai martaban".

Cikin rashin fahimta ya ce "Me zaki faWa?"

"Ba zan gaya maka ba, daga gaya maka abu a kan Jamil ka je ka gaya masa, dama na san zuciyarka ba zata bari ka danne ba, shiyasa bana gaya maka wasu abubuwan, sai ka Sata mini aiki, ni bana ?waina sai da zakara, ka san wanda ya gaya wa Mummy na ce tana yi maka asiri?"

Ya ce "A'a"

"To baba uwani ce, kuma ina sane na faWa, dan daga ita sai ammi da iman a wurin na faWa, baba uwani na kwasar sirrin ammi, ta je ta gaya wa Mummy. Saura kuma ka faWa so muke mu kama ta red handed, Daddy ya tabbatar mini da ya ganta sau biyu a sashin Mummy cikin dare".

A sukwane ya tashi zaune, yana kallon rumaisa kamar ya ga abun tsoro, ya fara tsorata da lamarin rumaisa, kamar wata mai rauhanai.

Ta tura baki ta ce "Meye kuma? Saura ka gayawa wani, idan ka faWa ba zan sake gaya maka abu ba, yanzu in anjima mu je gida, ina son in ga Mummy, na tabattar maka da babu wanda zai wani kira ka ya tuhume ka".

"Kin fara bani tsoro ne, don't make things complicated, tayaya za ki ce baba uwani tana cin amanar mu?"

Rumaisa ta ce "Ai ban ce ka yarda ba dama, amma zan tabattar maka da hakan, yanzu dai zo mu ci abinci, mu yi wasan gudu a backyard, in anjima in je wurin Mummy".

Ya ce "Am not in mood, je ki yi wasanki"

"To buWe mini wayarka na yi game" shiru yayi mata, ya tsunduma kogin tunani.

Ta Wau wayar, ta kama yatsansa ta buWe, ta jingina da jikinsa tana dannawa.

Shi muma ya bita da ido, kamar mai kallon abun al'ajabi.

Ta gama danne-danne wayarta, ya ajiye masa ta tafi nata shagali.

Sai dai da ta sauka ?asa, ta tarar baba uwani bata nan, ta tambayi su Asiya, suka ce mata tun safe ta fita ba ta dawo ba.

Ta tafi backyard, ta samu ball ta yi tayi, kamar ba matar ba sarake ba, ta window takawa yake hangota, yadda take sarrafa ball Win a ?afarta ka san ?anwar maza ce.

Da la'asar bisa kasada, takawa ya Wau ruma suka tafi gida, suna tafe yana sake tambayar ta, me za ta cewa Mummy, ita kuma ta?i faWa masa.

Ko da suka je, ya ce sai dai su shiga tare, ita kuma ta ce idan tare suka shiga, abun ba zai yiwu ba.

A falo ta tarar da ru?ayya tana danna remote.

Rumaisa cikin fara'a ta ce "Mummy tana nan ne?".

Ru?ayya tayi tsaki ta ce "Wace Mummy?".

"Jamila babarku"

"Sunan Mummyn ki ke faWa haka?"

"Kin ji abun da na ji, ranar da ki ka faWi sunan Ammi gatsal".

Mummyn ce ta fito tana waya, tana ganin rumaisa ta yi turus.

Ruma ta gaisheta, cike da duniyanci, ta yi murmushi ta ce "Amarya ba kya laifi, yau ke ce a sashina?"

Ruma ta ce "Eh Mummy wurinki na zo".

"To gani"

Ruma ta ce "Sirri zamu yi"

"Ba damuwa Bismillah" suka shiga wani Wakin na daban.

Ruma ta ce "Mummy, na ji kin kai ?arar papa ne, shi ne na zo na baki ha?uri, dan Allah ki janye, kar ki saka ayi taron nan, ni nayi laifin ba shi ba".

Mummy ta yi murmushi ta ce "Turo ki aka yi kenan? Gara na kai ?ararku ai, dan ban san laifin da na yi muku ba, kuma taro babu fashi, dole ku je ku wanke ni".

"Mummy, tayaya zan san kina yi wa papa asiri, sharri aka yi mini, baba uwani ce fa ta gaya mini, kina yi wa papa asiri"

A firgice ta ce "Baba uwani kuma?".

"Ita, kuma ba ?arya take yi ba, tun da na kamata da wannan Wazu da safe" rumaisa ta yi maganar tana Wagawa Mummy, wasu layoyi, da wasu irin abu a cikin leda.

"Yanzu ko dai ki janye maganganun ki, ko kuma idan aka je gaban mai martabar, zan gaya masa komai, kuma mu ma muna da CID a sashinki, wadda take kawo mana rahoto. Abun da baku sani ba shi ne, na sanku tun kan na shigo cikinku, ina kuma sake maimaita muku, tunanin maza bakwai ne a cikin kaina, da kuma nawa na takwas.
Mummy ina ro?onki, da ki jingine makaman nan, ki sassautawa mijina haka, wallahi a dalilinsa nima bani da kwanciyar hankali, muraran nake ganin abun da mutane ba sa gani a kansa, dan Allah ki bari ya huta haka.

Ayshercool.

Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?





Mummy ji tayi, tamkar an sanya mata dabaibayin ?arfe an Waure mata ?afafuwanta, ta kasa motsi, jikinta kuma yayi wani irin mugun sanyi, ta kasa motsa ko ina. Har rumaisa ta gama yi mata maganar, ba ta iya cewa uffan ba, mussaman ganin wannan layoyin a hannun rumaisa, kuma rumaisan ta Sare fatar tsaf.

A tsakiyar garden Win gidan, ta bawa baba uwani ta binne mata, shi ne cigaban aikin da ake yi mata a kan Adam, akwai irin layoyin a gidansu, akwai a gidan da ya zauna da aisha, wannan karon ma an yi ta saka a gidansa, saboda ana son ya din ga shige da fice a kai a kai, a in da layoyin suke.
Kuma wannan laya ta bawa baba uwani jinin mage, da za ta din ga zubawa a ?asar wurin sa'ai da lokaci.

Da safe rumaisa na ta sauri, ta kammala abun da za ta yi kar ta makara, dan haka ana idar da sallar asuba ta hau ayyukanta, sai dai kanta ya din ga sara mata, ta din ga kamar wani sauti, daga bayan Wakinta, kawai ta sauka ta zagaya, wanda a nan ta iske baba uwani, ta gama binnewa, ta jira ta bar wurin, ita kuma ta tone ba ta sani ba.

"Ina sake ro?onki Mummy, mu rabu cikin mutunci da kwanciyar hankali, abun da aka yi a baya, Ubangiji Allah ya yafe, amma idan aka cigaba a haka zaku ji babu daWi, na san ni yarinya ce a kan ku, da ku ke yi mini kallon mara hankali, amma zan iya abun da tunaninku bai taSa kaiwa kai ba, kamar. Na kama baba uwani, kuma ta yi mini bayanin komai, wanda kafin in dawo daga makaranta ta bar gidanmu, amma kar ki damu, ban gayawa kowa ba, daga ni sai ita muka sani, idan kin so, sirrin zai zauna daga ni sai ke, idan kuma aka matsa mini, ki tambayi takawa yadda nake" ta mayar da ledar cikin hijjabinta, ta fita.

Sai da ta fita sannan Mummy ta ji ta dawo hayyacinta.

Jikin Mummy ya fara tsuma, tana zazzare ido, gaba Waya ta kasa tunani ma, neman wuri ta yi ta zauna daSas a kan gado, wani irin gumi ya din ga tsatstsafo mata, har ta tsakanin cinyoyinta.
"Lallai wannan uwani an yi ?ar........, ni zata tonawa asiri, mutuniyar banza da ta wofi?"

Jiki na rawa ta janyo wayarta, ta kira baba uwani.

Baba uwani ta fara koWata, ta ce "Ke dalla saurara mini, ashe baki da hankali? Shi ne ki ka bari yarinyar nan ta kama ki, kina binne-binne a gidan?".

"Ni kuma? Ai ba ta kamani ba, wallahi ba ta gani ba"

"?arya ki ke uwani, yanzu ta bar shashina, da ?ullin layoyin a hannunta, ni zaki munafunta? Ashe baki da mutunci? Tun yaushe na baki aikin, ki ka ajiye baki yi ba, har ta gani, kenan ma ke ki ka gaya mata ina yi wa Adam asiri".

Kamar baba uwani ta saka kuka, ya ce "Wallahi, wallahi hajiya ba haka aka yi ba, ina iya ?o?arina dan Allah kiyi ha?uri".

Kashe wayar mummy ta yi, tana fifita da hannunta, gaba Waya ta gigice.

Ru?ayya ta shigo Wakin, tana duban Mummy ta ce "Mummy ya aka yi ne, wai me ta ce miki?"

"Bakomai, jeki hutawa zan yi" Ru?ayya ta Wage kafaWa ta fice.

Rumaisa ba ta tarar da takawa a in da ta bar shi ba, dan haka ta wuce sashin Ammi.

Ta tarar da shi a zaune a gaban ammi suna hira, sabir sai hawa yake wuyan takawa yana saukowa.

"Ammi sannu da gida"
Ammi ta ce "Yauwwa ?ar auta ta, ina ya baro mini ke ya shigo shikaWai? Ai ban san tare ku ka zo ba"

Ta zauna ta ja yatsan takawa da ?arfi ta ce "Tafiya yayi ya barni".

"Ke baki san da zafi bane" ruma ta harare shi ta ce "To waye ya ce ka tafi ka bar ni?" Ta mayar da idonta kan Ammi ta ce "Ammi ina Anty Iman ne?".

Ammi ta ce "Kin san ta sarkin Waki, tana can ko tana bacci ko tana karatu".

Rumaisa ta tashi ta nufi Wakin Iman, Sabir ya biyota, ta tsaya ta Wauke shi suka tafi tare.

Ammi ta ce "Yaya ake ciki, ai yanzu rigimar ta ta da sau?i ko? Kuna sabawa a hankali na ga ta rage daru sosai".

Yayi murmushi ya ce "Ba zata sauya hali ba, kawai na koyi zama da ita ne kawai. She's simple at times wasu lokutan kuma ba a gane kanta"

Ammi ta yi dariya ta ce "Tun da ka iya zama da ita ai Alhamdilillah, Allah ya ?ara haWa kanku"

Ya ce "Amin, sai dai Ammi akwai wani abu".

"To, Allah ya sa ba matsala ba ce"

"Ba matsala ba ce ba, ta ce zata gaya wa mummy abun da zai saka a fasa kirana wurin mai martaba, ban san me ta ce mata ba"

Ammi ta ce "Wai yanzu daga can take?"

Ya ce "Eh".

"Takawa meyasa ka barta? Idan kuma ta je sake hargitsa lamuran fa?".

"Ammi, am testing her thinking capacity, tama Sharp brain fiye da tunani, kuma na fara yadda da abun da ta gaya mini a kan Jamil, idan har tayi nasarar sanya Mummy, ta janye ?arata data kai wurin su mai girma wambai, duk abubuwan da rumaisa take faWa gaskiya ne".

Ammi ta numfasa ta ce "Takawa, kaifin basirar yarinyar da tarbiyyarta, su ne suka saka na zaSa maka ita, ni na san tana da kaifin tunani tun kan ku yi aure, tana da basira. Dan haka a ?ara ha?uri, ka bi komai a hankali, ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa kafin ka yi tafiyar nan, abun da hali zai yi"

"To shikenan Ammi, in sha Allah".

Ammi ta ce "Amma zan so sanin me za ta gaya wa Jamila, da har zai sanya ta janye abun da ta je ta faWa".

Takawa ya ce "Nima na so sani ta?i faWa, kuma mun yi da ita ba zan gayawa kowa ba. Idan na cigaba da matsa mata ba zata faWa ba".

"To Ubangiji Allah ya iya mana, ya sanya ita ce sanadiyyar warwarewar matsalolin nan"

"Amin Ammi".

Ruma kuwa a kwance a ?asa ta tarar da iman, a Wan razane ta ?arasa ta taSa jikinta, ta ji yayi Wumi.

"Anty iman, lafiya ko baki da lafiya ne? Ciwon kan ne ya dawo?x ta jero mata tambayoyin.

Iman ta tashi zaune, tare da yin ya?e ta ce "Maman sabir, saukar yaushe?"

"Ba wani saukar yaushe, baki da lafiya ne?".

"A'a lafiyata ?alau, kawai dai kwanciya nayi".

Rumaisa ta zaune sosai ta ce "Ke da papa wasu lokutan halinku Waya ma, idan ba rashin lafiya ba, akwai damuwa fuskarki ta nuna, dan Allah anty iman menene, bana son in ga damuwa a fuskarki, gaba Waya raina Saci yake yi. Ko wani ne yayi miki wani abun? zan iya rama miki".

Cikin dauriya, Iman ta ce "Maman sabir, bana son Sacin ranki nima, kasancewarki a tare da ni, yana bani ?warin gwiwa.
Zan gaya miki menene, amma dan Allah kar ki bari ammi ta sani, kin san bana son damuwarta".

"Anty iman, duk surutun nan nawa, ina Soye sirri, gaya mini ko bani da maganin zan tayaki da addu'a".

"Ammi ce ta ce mini, wai uncle J yayi mata maganar yana so na, wai zai je ya sanar da mai girma turaki, a zo a nema masa aurena, naga ammi tana murna, amma....." Sai kuma tayi shiru.

Rumaisa ta ce "Amma ke ba kya son sa ko?"

Iman ta zubawa rumaisa ido.

"To wa ki ke so, dan ni ma bana son wannan jabir Win, babarsa ba ta da mutunci, wahalar da ke zata din ga yi"

"Ba na son kowa maman sabir, bana son sake yin Soyayya, na barwa Allah lamarina, amma wallahi bana son jabir".

"Kin tabattar babu wanda ki ke so, tuna dai" ruma ta yi maganar tana basarwa.

Sai da gaban iman ya faWi, tayi fatan, Allah ya sa ba ganota rumaisa ta yi ba.

"Na tabattar bana son kowa ni yanzu"

"Amma ya san ba kya son sa ya nace, kar ki damu ki yi ta addu'a, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, ba bari za ta yi ba. Ko kina son wani a yayyena, amma su talakawa ne?"

Iman kallon rumaisa take yi, tana son gano gaskiya, ko dai ruma ta gano ta ne. Ganin sun gaza haWa ido, ya sanya ta ce "Kin manta nima talaka ce, ?ar fulanin tashi da aka tsinta a dokar daji, ai mutane masu asali kamar yayyenk......"

"Iman bana son wannan maganar wallahi, raina Saci yake idan kina gayawa kanki haka"

"Shikenan na daina".

Ruma ta ce "Da dai yafi, yauwwa da muka je gida ranar, mai sunan baba ya tamabayeni kina ina? Na ce masa kina nan ?alau"

Murmushi ne ya bayyana a fuskar iman ta ce "Allah sarki yaya umar" ruma murmushi kawai tayi, dan tuni ta harbo jirginsu.

"Kar ki damu anty iman, ba zan gayawa ammi ba kya son sa ba, amma in sha Allah ba za ki aure shi ba, dan nima haushin sa nake ji. Bari na je wurin papa" ta tashi ta koma falo, ta tarar ammi ta tashi.

Ta je ta zauna a kusa da adam, ta yi ?asa da murya ta ce "Done, na gama aiki, ka zuba ido ka gani".

Adam ya ce "Amma baki gaya mini me ki ka ce mata ba".

"Zan gaya maka, amma sai ta fasa Win tukuna"

Ya ce "Shikenan, mu tafi ne, kin gama?"

Ta ce "A'a sai da daddare"

"Aliyu ya kirani, ya ce mini mama ta za ta yo miki aike, wannan yayan naki mara fara'a zai zo"

Ruma ta ce "Da mai sunan baba ka ke ko?"

"To waye mara fara'a idan ba shi ba"

"Hmmm, ai kusan halinku Waya, ina kallonku fa ko magana ba kwa yi, kowa yana ji da kansa ko, zan gani dai "

"Ke waye ya ce miki bama ma magana"

Ta kai bakinta kunnensa, ta kare da hannunta ta ce "Ina kallon duk abun da ku ke yi fa, idan ku ga juna ku wani din ga basarwa, shiyasa duk na iya zama da ku, amma gara kai ka fi sau?in kai wataran, kai baka sakani punishment kamar mai sunan baba, tsakar dare zai sani kneeldown idan na yi laifi fa".

Dariya Adam yake, hannu Waya yana danna wayarsa.

"Banbancinku, shi bai fiye magana ba, kai kuma idan ka ga dama, kana magana, wasu lokutan kana da wasa kamar yaya usy, jin kai kamar da son girma kamar yaya Aliyu, wataran sau?in kai kamar yaya Abubakar, idan nayi wani laifin sai na zata zaka dakeni ne, amma sai na ga ka mini banza. Shiyasa wataran nake jin kunyar yi maka rashin kunya".

"Ashe kina sane ki ke duk abun da ki ke mini".

"Mama ta ce hali zanen dutse, ai ka ga bana tsokanarka sosai, kuma zuwa yanzu ba shiryu ba dan Allah, a makaranta fa ko ?awaye bani da su, saboda kar a Sata mini rai, a kawo maka ?arata, bana son ka din ga Sacin rai sosai, tausayinka nake ji" jiki a sanyaye ya Wago ya kalli rumaisa, har cikin zuciyarta, take maganar.

Ta cigaba da yi masa raWa ta ce "Amma duk da haka fa, ban manta abun da ka yi mini ba, kuma zan rama". Jabir ne yayi sallama a falon, sai zuba ?amshi yake. Ya Wan tsaya yana kallon yadda rumaisa ta daddane kafaWar Adam, ta dafa kafaWarsa take yi masa raWa, a tsakiyar falo ma'aikata na kaiwa suna komawa.

Ya ?araso ba tare da rumaisa ta tashi ba, dan ba ta da niyya ma.

"Takawa barka da yamma"

Adam ya kalli Jabir ya ce "Barkanmu dai"

Rumaisa ta yi saurin cewa "Papa zan ?arasa maka idan mun je gida, bari na kira anty iman mu tafi, da daddare sai mu rako su gida ko papa?" Ta yi maganar kamar ?aramar yarinya tana kallon fuskar sa.

Ya Wan ja hancinta ya ce "To mimi" ta tashi ta nufi Wakin iman.

Tana shiga ta ga iman na Soye wayarta, kasancewar hoton mai sunan baba take kallo.

"Anty iman ta so mu je gidanmu, da daddare sai ku dawo"

"Maman sabir kiyi ha?uri, gobe in Allah ya kaimu sai mu zo".

"Mai sunan baba ne zai zo, yana son zai ga sabir idan ya zo, shiyasa na ce mu tafi tare, sai papa ya dawo da ku, kuma ga wancan jabir Win ya zo, idan kuma zaki zauna ne shikenan"

Ba shiri iman ta tashi, ta shiga toilet, ta wanke fuskarta ta shirya a gurguje, suka fito tare har da Sabir.

Jabir ya ?are ta da ido.
Ammi ta ce "Iman sai ina?"

Adam ya ce "Da ita zamu tafi, anjima zamu dawo"

Suka fita, Jabir ya biyo bayansu yana ?walawa iman kira.

Adam ya waiwaya ya ce masa "Ya aka yi?"

"Adam meyasa ka ke yi mini haka ne? Ka san wurinta fa na zo"

"Ai ka san yadda muka yi da kai Jabir, tun da ku ka nuna mini iyakata da kai da Jamil, nima dole na tauna tsakuwa, aya ta ji tsoro. Ka fara nemo yardar mahaifiyarka tukuna, dan ba zaka auri iman ka ta wula?anta ba"

Rumaisa kuwa tuni sun yi gaba, Adam ya biyo bayansu, suka tafi.

Shiru Jabir ya yi ya tsaya yabi bayansu da kallo, ya jinjina kai tare da yin ?wafa.

***
Iman har ta Wan wartsake, suka cigaba da sabgoginsu tare da ruma.

Ta ce "Maman sabir, amma yaya umar zai ci abinci idan ya zo ko? Me za a dafa?"

Ruma ta ce "To, nima dai ban sani ba, sai dai idan ki ka saka shi wata?ila ya ci"

Gumm iman ta yi da bakinta, tare da gudun kar ta sake wata maganar da rumaisa za ta fahimci wani abu.

Mai sunan baba bai tashi zuwa ba, sai bayan sallar magariba.

Duk da ba sakin jiki zai yi ba, amma rumaisa ta yi murnar ganin sa sosai.

Babban abun da ya saka shi farinciki, bai wuce ganin iman ba, sai dai kallo Waya yayi mata ya san tana cikin damuwa.

Cikin sanyin halinta ta ce "Yaya Umar sannu da zuwa, ya mama?".

"Alhamdilillah" ya bata amsa, a ganinsa yayi ?o?ari ya amsa mata a sake, ba tare da sanin amsar ta sa ta ta?aice da yawa ba.

Ya kalli rumaisa ya ce "Ga sa?onki nan, na je katsina shekaranjiya, gwaggo ta bani kaya na kawo miki iya ma haka, zaku yi waya da mama".

Ruma ta kalli kayan a manyan ledar viva, ta ce "Amma na gode sosai da

Please Login or Register in order to submit comment