You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ammi ba ta gudun abun da zai Sata mata rai sam"

Ruma ta ce "Dan Allah zuciyar mutum ce a jikinka? Ka san me ake nufi da uwa da Wa kuwa? Kai banda dalilin sihiri da nake da tabbacin shi ya raba ammi da daddy, kai kana zaton akwai dalilin da zai sanya ta zuba ido ta barwa wata mata Wan ta.
To ai ko ni da abun da ke cikina bai zo duniya ba, da shi da Sabir, ban ga wanda ya isa rabani da su ba, kai idan aka ce za ayi asirin ma, sai na haWa asirin da bokan na ci ubansu wallahi.
Dan Allah papa kaima ka sassauta wannan ?iyayyar, yanzu bari in saka kaya in bika".

Ya ce "No, ki zauna a gida, zan je kawai"

Ruma ta ce "Hankalina ba zai kwanta ba, ka tafi da ni dan Allah, idan ba haka ba zan biyoka idan ka fita".

"Mimi kina da matsala, cikin nan ne bana son a gani".

Ta kalleshi ta ce "Saboda me?"

"Kin fi kowa sani ai, ba na son wani abu ya samu cikin nan naki, kullum cikin Addu'a nake yi Allah ya sa ki haihu lafiya, kin san komai ai"

"Babu abun da zai faru sai ikon Allah, ka tafi da ni saboda zatin Allah, hijjabi zan saka, ba wanda zai gan shi ai" kasancewar rumaisa ta ?ware a iya magiya, tamkar ?ar maro?a, haka ya sanyata a gaba suka tafi.

Da shi da Nusaiba, da Ammi, haka suka rankaya asibitin da aka ce Mahmud yana can.

Gaba Waya Ammi ba ta cikin nutsuwarta, takawa ya ce "Ammi dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin San ki na da high bp".

A rikicen dai Ammi ta ce "Kai ka san sani high bp, ka tambayar mini Wakin da yake dan Allah "

Ruma ta din ga kallon ammi cikin tausayawa, haka ta shafe shekaru da soyayyar nan da tausayi suna nu?ur?usa zuciyarta, ruma ta jinjinawa mugunta irin ta mummy.

Ba ?aramin razana ammi tayi ba, ganin Mahmud a kwance ba ya motsi, ga ruwa an saka masa, ga kuma oxygen da take taimaka masa yana numfashi, gefensa kuma mummy ce a zaune.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Mahmud meya sameka haka?" Ammi ta yi maganar cikin rawar baki.

Jin muryarta ya sanya shi ya motsa, ya fara yi wa ammi nuni da hannunsa ta zo.

Cikin hanzari ammi ta ?arasa, idonta na ta zubar da hawaye.

Ya mi?a hannunsa ya ri?e nata, sai dai ba baki, sai hawaye da yake zuba ta gefen idonsa.

Ammi ta ri?e hannunsa tana jejjera masa sannu.

Ya Wora hannun a kan cikinsa.

Ruma ma ta ?arasa gaban sa cikin kuka ta ce "Daddy meyafaru? Meya sameka?"

Wata irin mi?a yayi bakin sa yana zubar da kumfa, cikin sar?ewar numfashi ya ce "Daughter mutuwa zan yi. Ammi. Amm....Ammi na faWa yau rumaisa, Ammi ki yi mini Addu'a cikina" yayi maganar tamkar numfashin sa zai bar gangar jikinsa.

Daga rumaisa har Ammi kuka kawai suke, Nusaiba ma kuka take.

Cikin kiWimewa Mummy ta tashi cikin azama, ta ce "Mahmud ciwo ba mutuwa bane ba, kar ka sake cewa zaka mutu, haba Mahmud kar ka yi mini haka dan Allah " tayi maganar tana fashewa da kuka.

Ya buWe ido a galabaice ya kalli Mummy, ya zare hannunsa daga na ammi, ya ri?o nata "Mummy na gode, na gode Mummy"

Ya sake zare hannunsa daga na Mummy, ya mi?awa adam, sannan ya cewa ruma "Ki ce masa ko sau Waya ya ri?e hannuna Daughter" ya yi maganar yana sake mimmi?e wa.

Cikin matsanancin kuka da tashin hankali rumaisa ta kalli Adam ta ce "Papa dan Allah"

Adam da tuni ya karaya, kuma ya tsorata da lamarin, A? hankali? ya tako, ya zauna a kusa da rumaisa, ya saka hannunsa a na Mahmud ya rungume shi.

"Ina son ka Wan uwana, ?addara ce"

Mummy ta rasa in da zata sanya kanta, dan lafiya ?alau Mahmud ya kwanta, idan har ta ce ba ta ?aunar Mahmud ?arya take yi. Saboda yayi mata biyayya fiye da yaran da ta haifa, kuma ta saka an ?wace shi an bata shi, dan mugunta, amma kuma sai ta fara son sa daga baya.

Likita ne ya shigo, ya din ga yi wa Mahmud wasu allurai.

Bayan fitar likita, duk sun yi shiru sun zuba masa ido, Adam yana rungume da shi, rumaisa ta mi?e zumbur, dan tamkar ana mata raWa ta ji komai.

"Me ya haWa shi da jabir ne?"

Takawa ya ce "A ina?" Duk suka tsaya suna kallonta.

"Meyasa ya daki Jabir ya kulle shi?"

Duk suka zubo mata ido.

ganin da Mahmud yayi Mummy, tana cikin damuwa, ya sanya ya sakata a gaba, a kan ta gaya masa meke damunta, ta kasa Soye masa ta gaya masa komai. Ba ?aramin girgiza yayi ba da jin abun da Jabir Win ya yi ba shi da ru?ayya, tun da ya fita a fusace, sai wayar Hajiya Lubabatu ta gani, ta tabattar mata da zata ga abun da za ta yi wa Mahmud muddin bai saka an sakar mata Wa ba domin kuwa ta san muddin asirin jabir ya tonu ba zai yi sarauta ba, kuma ta fuskanci kamar yanzu Mummy ?o?ari take taga Mahmud ne ya samu sarauta.

Sai a yanzu Mummy ta tuna da furucin hajiya Lubabatu.

Tashi rumaisa ta yi ta fara tashin Mahmud.

Takawa ya ce "Ya samu bacci fa"

"Tashe shi kawai, daddy"

Ya buWe ido a matu?ar wahale ya kalleta.

"Meya haWaka da jabir?"

"Bakomai" ya furta yana numfarfashi.

Ta ce "To koma me ka yi masa, babarsa ta ce zaka gani"

Takawa ya ce "Mimi bana son rigima fa, ke a ina ki ka ganta?"

Ruma ta ce "?azu da asuba ina bacci, na gansu su na faWa, ban san a kan menene ba, amma ita ta ce zai gani, jabir yana police station ko?"

Ammi ta tashi ta kamo ruma ta zaunar da ita, ta ce "yi shiru da bakinki" shi dai takawa a iya sanin sa, suna tare da ruma, kuma ba wani wurin suka je ba, balle ace ta ji.

Mummy ta hau bala'in cewar mahmud sun yi faWa da Jabir, amma ba wani abu da Hajiya Lubabatu ta yi masa.
Tayi maganar tana karewa saboda kar a gane sun samu saSani da Hajiya Lubabatu, kuma muddin asirin lubabatu ya tonu, na ta ne ya tonu.

Takawa ya ce "Mimi ba ta ?arya a cases irin wannan, zan yi bincike a kai, duk wanda na gano da saka hannunsa wani abu ya same shi, wallahi sai ya fuskanci hukunci ko waye shi".

"Matarka ba ta ?arya ni nake yi kenan?"

Ammi da sauri ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri, ku yi ha?uri Takawa kar in sake jin bakin ka, rumaisa ku yi shiru mu yi masa addu'a".

Ruma ta ce "To ammi, amma wallahi ba ?arya nake yi ba"

Mai sunan baba ne yayi sallama ya shigo, hankalinsa a tashe, "Subhanallah" yake ta maimaitawa saboda halin da ya ga Mahmud a ciki, dan kuwa sun yi waya jiya da safe, yake ce masa zasu haWu yau.

Bai iya yi wa kowa magana ba, ya ?arasa gaban gadon yana ambaton sunansa.

Gashi da an kira sunansa yake amsawa, ya buWe idonsa ya kalli mai sunan baba.

"Mahmud, meyafaru haka ne? Wayarka na kira wata yarinya ta Wauka ta ce mini wai kana Asibiti" ya cewa mai sunan baba "?ago ni"

Mai sunan baba ya sanya hannu biyu, ya Wago shi, ya jingina da jikinsa.

Ammi ta din ga ajiyar zuciya ganin Mahmud a zaune.

"Ku yi ha?uri duk na tayar muku da hankali"

Mai sunan baba ya ce "Kar ka damu sannu ya jikin naka?"

"Da sau?i, zan sha ruwa"

Mai sunan baba ya kalli Adam, Adam ya Waukko roba ya tsiyaya ruwa ya bawa umar, ya karSa ya bawa Mahmud, ya karSa ya sha sosai.

Ya ce "Alhamdilillah, ina ?anwata tana lafiya?"

"Lafiya ?alau, bata san me ke faruwa ba, na riga na fito sannan na kira wayarka, sannu Mahmud"

"Yauwwa yaya" kasancewar haka yake kiran umar.

Ammi ce ta ce "Mai sunan baba ya gida?"

Ya ce "Afuwan ammi, hankalina ne a tashe wallahi, ya gida ya mai jiki kuma?"

Ammi ta ce "Jiki da sau?i Alhamdilillah"

Mummy kuwa sai cika take tana batsewa, Fauziyya ba ta taSa ?arewa mai sunan baba kallo ba sai yau, lallai Iman ta auri mai kyau, da cikar zati.

"Me zaka gaya mini ne ka ke nema na?"

Mai sunan baba ya ce "Ka ji da jikinka ka samu lafiya, kana tambayata me zan gaya maka" yayi maganar yana murmushi.

"Am curious about it" yayi maganar yana lumshe idanunsa, saboda allurar baccin ba ta sake shi ba.

"Zan gaya wa yayanka ya gaya maka"

"Wai Takawa? Ba zai gaya mini ba"

Mai sunan baba ya ce "Zai gaya maka mana, zaka ci abinci ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Bari sai na gama farfaWowa, idan kuma na mutu....

"Shhhh, zaka farfaWo in sha Allah, har aurar da kai sai na yi"

Ammi bakinta ya ?i rufuwa dan murna, ita ba ta san ya aka yi ma ta sa ta zo Waya da Mahmud ba, saboda Mahmud akwai taurin kai da rashin mutunci, mai sunan baba kuma akwai izza da son girma, amma yadda yake yi masa zaka gane akwai mutuntawa da girmama juna a tsakaninsu.

Ya kwantar da Mahmud, ya ce "Ka yi bacci, zan je gida ?anwarka ta yi maka girki, mu zo ta duba ka"

"Kar ka wahalar da ita, ga Mummy ga Ammi ga daughter duk na wanda na samu zan ci".

"Ba wata Mummy, na ammi zai ci" Rumaisa ta faWa tana harare-harare.

Fauziyya ta buWe baki za ta yi magana, amma kwarjinin mai sunan baba ya cika mata ido, dan ta san ?arya take, ta zagi rumaisa a gabansa ya ?yale ta.

Ya kalli Adam ya ce "Ina son yin magana da kai"

Mamaki ne ya kama Adam, amma ya tashi ya bi bayan mai sunan baba suka fita.

Fauziyya ce ta Wora da rashin mutunci.

"An yi magana wani ammi ce za ta bashi abinci, sai ka ce ammin wahalar sa ta sani, uwarmu ce dai ta yi masa duk wata wahala ta rayuwa".

"Da tayi mata fashin Wan? Kallon biri ku ke masa yake yi muku na ayaba fa. Uwar me ta tsinana wa rayuwar ta sa ban da masifa, uwar ri?on arziki ce za ta raba uwa da Wan ta, ta raba jini da jininsa, ta raba shi da Wan uwan sa, yanzu dai shi ma ya san gaskiya, gurbin ido ba ido ba ne, kuma wallahi ko bayan shekara dubu, tuwo sunan sa tuwo"

Ammi sai ?o?arin hana magana take yi, amma rumaisa tayi mursisi ta din ga gasawa Mummy da Fauziyya magana, ita kaWai su biyu ba tare da kunya ko tsoro ba.

Duk abun nan da ake yi Mahmud yana jin su, amma yayi shiru kamsr mai bacci.

Mai sunan baba ya kwashe komai ya gaya wa takawa, game da Alhaji Aminu, jikin takawa har tsuma yake yi ya ce "To yanzu Lagos Win zamu je, ko yaya za a yi? Mu ga shi Alhaji Aminun, idan ta kama tambayarsa zamu yi, ko ma a tafi da ammi sai ayi "

Mai sunan baba ya ce "A'a ina ga gara mu mu je mu tabbatar, tun da yanzu tana cikin damuwar rashin lafiyar Mahmud, dama da shi na so mu je, to gashi ba shi da lafiya"

"Bakomai, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu, in dai ya ?ara warwarewa, sai mu je kawai, ina fatan Allah ya tabbatar ya sanya ?an uwan iman ne "

Mai sunan baba ya amsa da Amin, har takawa ya juya zai tafi mai sunan baba ya ce "Na ce ba" ya juyo ya tsaya yana sauraren sa.

"Akwai bu?atar duk abun da ya faru a baya ya wuce, a fuskanci gaba.

A zamana da Mahmud babu abun da yake marari da so da ya wuce ka, you have to play your role as his senior brother, babu abun da yafi Wan uwa daWi. Ba zaka gane hakan ba sai ranar da babu shi a duniya"

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai" mai sunan baba ya jinjina masa kai ya tafi.

Samha sun je duba Mahmud a asibiti, dan tuni labari ya zaga masarautar, Mahmud ba shi da lafiya, ?an dubiya sun fara kaiwa suna komowa.

Sai dai fa cacar baki ta?i tsayawa a tsakanin Fauziyya Mummy da rumaisa.

Muraran yau ruma take nuna musu asalin tantirancinta.

Samha za ta saka baki ruma ta ce "Yi mini shiru, ba dake nake ja gayyar mushirikai ma?iya Allah, ai wallahi a doron duniya ban ga bokan da zai yi asirin da zai kamani ba, sai dai ku yi wa wasu".

"Su waye mushirikan?"

"Gaku nan gaba Wayanku, ban da yawon asiri da ?o?arin rusa rayuwar mutane me ku ka saka a gaba, azzalumai ma?iya Allah"

A rikice ammi ta fita neman Adam, suka yi kiciSis a hanya, ta ce masa maza ya je ya Wau rumaisa ya mayar da ita gida.

Sai dai suna shiga Wakin, suka tarar Samha da Fauziyya tamkar za su rufe ruma da duka, ita ma ta tsaya ta ri?e ?ugu tana bala'i, Nusaiba sai ba su ha?uri take.

Babu abun da ya gigita Samha sama da ganin tirtsetsen ciki a jikin rumaisa bayan ta mi?e, ta ri?e ?ugunta.

Ruma ta ce "Mamaki ki ke yi ko Samha, kin ga ciki a jikina? Baba uwani ba ta gaya miki na cire layar da aka saka a cikin katifar Wakunan mu ba?.
Ai tunda Allah ya sa na ritsuta, duk wani lungu da sa?o, sai da ta tone komai, na zauna na warware abun da ki ka ?ulla mini na tsiya, masifarku sai dai ta ?are muku".

Cikin matsanancin tashin hankali Samha ta ce "Me ki ka nufi? Nima sharrin zaki yi mini?".

"Wallahi na fi ?arfin in yi miki ?arya, rufa miki asiri kawai na yi, amma tarkacen layoyi da kayan tsubbun duk da ku ka binne mana a cikin gida an tone su, na kuma tara su wuri Waya saboda sheda, duk bala'inki ke da Adam sai dai ido Samha"

Ba tare da sanin Adam ya shigo ba, ta yi ?o?arin hankaWa Rumaisa.

Amma cikin zafin nama, ya hana faruwar hakan, ya Wauketa da mari.

Tsit suka yi suna kallon Adam.

"Wallahi ko da makamancin wasa, ki ka sake ki ka yi wa rumaisa wani abu, sai na taka ki, sai dai zumuncin ya watse uban kowa ya kama gabansa wallahi. Kuma na gode da abun da ki ka yi mini, na mayar da ni mara amfani a gidana, sai dai Allah ba a azzalumin sarki bane ba, kanki ki ka yi wa samha"

Mahaifiyar Samha ta fara bala'i "Wane irin mutum ne kai? Duk abun da yarinya ta faWa sai ka yarda da shi, kai ba ta laifi kenan. Saboda rashin ta ido, a gabana ka mari ?a ta"

"Saura Jamil ma, wallahi sai na warware kowane munafuki, babban algungumi mara tsoron Allah"

Nurses ne suka shigo, suka ce su fa asibitinsu ba wurin hayaniya ba ne ba, dan haka a tafi a bawa mara lafiya damar hutawa.

Adam ya maze ya ce kowa ya tafi Shi da Ammi za su zauna, ruma kuma anjima zai mayar da ita gida. Mummy ta ce bai isa ba.

Likita ya zo da kansa, ya ce wace mahaifiyar Mahmuda ta zauna da shi, ita da mutum Waya, ruma ta nuna Ammi ta ce "Ga mahaifiyar sa nan" Mummy na ji tana gani aka sallame su, ya rage sai ruma Ammi Nusaiba da takawa.

Mahmud ya kalli ruma ya ce "Daughter kina ganin bai yi wuri ba?"

"Bai yi ba daddy, yakamata komai ya zo ?arshe, enough is enough"

Adam ya ce "Ban gane me ku ke nufi ba"

"Zaka gane very soon, amma kar ka matsa Please"

Ammi ta ce "Mahmud, a kawo abincin? Ya ka ke ji yanzu?"

"Alhamdilillah da sau?i, Yaya zai kawo abincin"

Da azahar takawa ya tafi sallar juma'a, bayan ya dawo ne Iman suka zo tare da mai sunan baba.

A lokacin Mahmud yana zaune, har yayi salla jikin da sau?i.

Iman ta din ga jera masa sannu, mai sunan baba ya ce "Deeja zuba mana abincin tare da shi, ko zai samu ya ci da yawa".

"Cikina dai babu daWi, kar a Wura mini abinci da yawa".

Mai sunan baba ya yi murmushi, ya ajiye abincin a kan gadon, ya ce "Ko a baki zan din ga baka ne? Na iya Wura ka tambayi deeja ka ji"
Iman ta sunkuyar kai, saboda ammi na wurin a zaune da nusaiba.

Takawa kuwa ya cewa ruma ta tashi ya mayar da ita idan sun gama cin abincin.

Iman sai tsokanar ruma take yi, wai yau abun Soye ya fito fili, sabir zai yi ?ani.

Ta din ga tura baki, tana harar su.

Ko da suka je gida gaba Waya takawa ya hau yi wa rumaisa faWa.

"Why are you making things complicated rumaisa?"

Cikin rashin fahimta ta ce "As how?"

"Ni da ke idan kin gaya mini abu ina yarda da ke, sauran mutanen fa? maganganu sun fara yawo, mahmud ya daki Jabir ya rufe shi ba wanda ya san dalili, mahaifiyarsa ta je an ?i sakin sa an ce sai mahmud ya je. Kin ce Samha na asiri, a dalilinki na daketa, komai ya hargitse na ma rasa ya zan yi, wambai ya ce lallai in zo da ni da ke, kun hargitsa al'amura, babu wanda ya san me ku ke ciki, kina Soye mini wasu abubuwan"

"Wait" tayi maganar tana Waga masa hannu.

"Duk cikin wannan maganganun naka, marin Samhan da ka yi ne ya fi baka haushi kenan? To sai ka koma ka bata ha?uri ai. Ka san dai ba zan yi mata ?arya ba, tun da lokacin da na zo gidanka ba uwar abun da na sani, balle in san an yi maka wani asiri baka da lafiya, ko in yi wa Samha ?arya. Kuma ba wambai ba ko gaban waye idan na je ina da gaskiya kuma zan faWeta.

Ta ?arasa ta saka mukulli, ta buWe wata wardrobe, ta Waukko wata Viva bag, cike da takaici ta watsa masa.

Ta ce "Ga kaWan daga binne-binnen da aka yi a hanani zama, daga ni har kai, da yake Allah ba azzalumin sarki bane, duk in da nake rayuwa in dai da sihiri, sai na sani. Ka duba a ciki har da abun da Samha ta yi, ta saka aka sanya a cikin katifarka da tawa, banda abun da aka binne"

Jikin takwa yayi sanyi, tsigar jikinsa ta tashi, saboda uban tarkacen da suka zubo daga cikin ledar, sai uban wari suke, ?o?arin rumaisa ya gani, da ta iya ajiye wannan tarkacen a Wakinta.

"Kuma ka sani ban Sallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faWa a gaban wamban nan da yawa, dan sai dai ka sake ni ko a kashe ni, dan Jamil shi ne mutumin da anty aisha ta gaya mini ta gayawa cewar ta zo kano, za ta je dubiya. Kuma lambar ?an bindiga suka kira, suka sanar da cewa ta rasu, na haddace ta, Yasir yayi tracking Win ta, Jamil ne, kuma shi ne yake haWa kai da wakili yake ko waliyyi oho muku dai. Kuma duk abun da na faWa ina da cikakkiyar hujjata, kuma ba wanda ya isa ya hana ni magana"

A gigice cikin tsawa ya ce "Me ki ke nufi rumaisa? Me ki ke faWa ne? Jamil fa ki ka ce"

"Malam sake ni, ba gaya maka nayi dan ka yarda ba, amma ko ka so ko ka ?i, Jamil ne ya bayar da bayanan da aka sace anty aisha, kuma har da shi aka je aka Wauki gawarta, duk da a cikin kaya yake ya rufe fuskarsa, amma na gane shi"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un " ya din ga maimaitawa jikinsa yana rawa.

Banza ruma tayi masa, ta fice daga Wakin ta bar shi.

Wata irin rawa jikin Adam yake yi, yana fatan Allah ya sa abun da ruma ta faWa ba gaskiya bane ba.

Jikinsa yana rawa, ya Waukko wayarsa da take vibrating, Sunan Bashir ya gani, ya Waga amma ya kasa magana.

"Adam, maganar madam fa ta zama gaskiya, Wakili su ne Smoke, kuma ba su kaWai ba ne ba, manyan ?usoshin ?asar nan SMOKE! Sai dai magana mara daWi, DSS fa na Kano sun je Abuja sun kama Jamil, an kama shi da laifin fitar da sirrin hukumar ga marasa gaskiya, yanzu haka yana tsare"

Ba tare da ya katse wayar ba, ya ajiyeta yana jin yadda kansa yake wata irin bugawa, zuciyarsa sai harbawa take yi da saurin gaske.

Ruma ta dawo Wakin ta tarar da shi ya haWa gumi, sai tsuma yake yi.

"Ka tashi ka bar mini Wakina, Wakin ma?aryaciya mai haddasa muku husuma a dangi, ka je ka bawa wadda ka ke so ha?uri, kuma ka kwashe wannan kayan tsubbun da aka binne mini, duk saboda kai".

Kallonta yake yana sake jinjina yadda abubuwa suke gudana, tashi yayi ya bar mata wayarsa da kayan tsubbun, ya fice ya bar Wakin.

Ta kwashe kayan ta Soye, ta Wauki wayar sa, ta buWe pin Win, ta kira Iman.

Iman na Wagawa ta ce "Kun tafi ne?"

"Eh, amma yanzu su mama suka shiga"

Ta ce "Ok".

Ta kira wayar mama, mama ta Waga "Mama ya jikin daddy, ya tashi kuwa?".

"Eh, a zaune muka tarar da shi, jikinsa da sau?i sosai".

"Mama dan Allah ba shi wayar"

Mama ta mi?awa Mahmud, da yake zaune yana hira da su mama da Ammi.

"Hello daughter"

"Jikin ka da sau?i daddy?"

Ya ce "Sosai Alhamdilillah"

"Get ready, an ce gobe in Allah ya kaimu za a kawo ?arshen wannan lamarin, zamu haWu a gaban wambai, kuma ba zamu yi magana ba sai a gaban ?an sanda"

Ya ce "Am ready in sha Allah, ku yi magana da su Yasir, dama komai na sa ya zama ready, zai tafi Canada, next week"

"Shikenan daddy, na gode sosai".

Hankali kwance ruma ta sha baccinta yau, sai ?arfe uku da rabi ta tashi, ta na sallar dare, tana ro?on Allah ya basu sa'a.

Shiru tayi tana tunani, lokacin da take mamakin yadda mama ke katse bacci tana sallar dare, yau sai ga abun ya zo kanta.

Takawa kuwa bacci ya gagari idonsa, yana sake nanata Kasancewar Jamil a cikin mummunan aikin nan, to idan rumaisa ?arya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?.

Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ?arfe biyu suna hira.
Ta yi iya ?o?arin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haWawa da abubuwan alkhairin Mummy.

Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya Wuri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faWa a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala'i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse.
Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ?arar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station Win aka kai shi ba.

Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba.

Suna tsaka da wannan bala'in, maman ta lura da wuni guda, yau Jamil bai kira su ba, sun kira shi amma ba ta shiga, hakan ya ?ara dugunzuma hankalinsu.

Dan haka marasa gaskiya, bacci sai rabi da rabi.

***
Da safe ruma ko ta kan takawa ba ta bi ba, ta shiga sabgoginta, Asiya ta tayata gyara Waki, saboda yadda cikinta ya fara tsufa, duk da ba a gani, sai ta saka kaya ?anana.

"Rumaisa" ta ji ya kira sunanta.

"Ba zamu Asibiti ba?"

"Sai ka dawo, kar na je na kuma Sata muku zumunci"

"Kiyi ha?uri, na rasa yadda zan yi ne"

Ta ce "Ni ba zani ba"

"Dan Allah "

Ruma ta ce "Ba fa zani ba, idan an shirya zama a gaban Wamban, na je kuma ba zan yi magana ba, sai da ?an sanda a wurin".

Juyin duniya ruma ta ce ba in da za ta je.

Ya ?yaleta ya fita tafi.

Ya tarar da ammi, tana bawa Mahmud abinci a baki.

Takawa ya samu wuri ya zauna, yayi shiru bai ce komai ba.

Ammi ta ce "Takawa, ya dai?"

"Bakomai" zata sake magana Mummy ta shigo, Mahmud ya ce "Mummy sai yanzu ko?"

"Eh ai jiya korata aka yi, aka nuna bani na haifeka ba, ba dan kai ne ba ba abun da zai dawo da ni".

Ya ce

Please Login or Register in order to submit comment