You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*



Mama ta ce "Ai kin san masu sarauta ba sa son wauta, ita kuma ?ar taki sai fatan shiriya"

Ammi ta yi dariya ta ce "Rabu da su, namu addu'a da ido, ai rumaisan ce dai-dai shi".

"To, Allah ya iya mana ya jikin iman kuwa?"

Ammi ta ce "Jiki yayi kyau mun gode Allah, har tana iya barci yanzu, in da nake ta yi wa Allah godiya, an ce zuciyarta lafiya ?alau wannan karon, ciwon kai ne dai da razana take yi".

Mama ta ce "Allah sarki, sai a dage da addu'a, a haWa da na islamic, kin san kana da ido ba na ganin gari ba, mussaman ita da take tubarkallah Masha Allah, kyau kamar ita ta yi kanta, sai ana dagewa da addu'a"

"Wallahi maman rumaisa ana yi dai-dai gwargwado, kin san sabgar iyali ce, sai dai ka yi iya yin ka ka bar wa Allah sauran, idan wannan ya ce wash anjima wannan ya ce wayyo, kuma duk kai kaWai ranka, sai fatan Waukin Ubangiji"

"Haka ne wallahi, dama shi ne mai tafiyar rayuwar gaba Waya, ba dan haka ba idan an kira ka, ba zaka amsa ba, ko yaya ace kula da ragamar gida a kan mace itakaWai, akwai ?alubale, Allah ya raya mana su yayi musu albarka".

Ammi ta ce "Amin ya Allah, dan Allah maman rumaisa idan da abun da take bu?ata kar a saka ta yi ?wauron baki, duk ta gaya masa, tun da rayuwa za su yi inuwa Waya, a ?yaleta ta faWi abun da take so".

Mama ta yi murmushi ta ce "Na lura son kan ku yayi yawa, kin fiye son ?ar nan taki, babu mai takurawa Wana nima ehe".

Ammi ta yi dariya, cikin jin daWin hirar ta su, suka shiga tattauna yadda yakamata abubuwa su tafi game da auren.

Kamar an jefota rumaisa ta faWo Wakin mama, mama ta Waga kai ta kalleta ta ce "To madiga, yau babu sallama?".

"Na yi fa, baki ji bane ba, yunwa nake ji"

"Kai rumaisa ni wannan ci naki yana bani mamaki, gidan miji zaki tafi, maza ba sa son mace mai shegen cin tsiya, kuma ba ma cin kirki ba, kina ci kina wasa ba zaki zauna ki mayar da hankali ki ci lokaci guda ki tashi ba".

"TaS, aikuwa mama sai in din ga dawowa gida ina cin abincin, Allah ya halicci bawa da ciki, wani ya ce wai baya son mace mai ci"

"Ke tafi can ki bani wuri, yauwwa sirikarki ta ce, in an jima mijinki zai zo"

Rumaisa ta yatsune baki ta ce "Waye mijina kuma?"

"Ban sani ba" Mama ta bata amsa.

"Mama to ni kawai sai ki wani ce masa mijina"

Mama ta ce "Ke, nutsu ki saurareni, bana son wannan shirmen da wautar taki, dole ki shiga hankalinki, aure ba abu ne na wasa ba, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki ka yi wani abu na shirme ba dai-dai ba, wallahi ni da ke ne.

Namiji duk in da yake, ko ba mijinki ba abun girmamawa ne, balle shi da zai aureki, ki ka sake ki ka yi masa wata wautar ko fitsarar, sai kin ga yadda zan yi da ke".

Rumaisa ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tana tunanin shi meyasa ba ayi masa faWan ya daina yi mata abun da yake yi mata, ko dan tun farko ba a san ita me yayi mata ba?.

"Yanzu me ki ke ganin za ayi masa wanda za'a tarbe shi da shi?"

Kai tsaye ta ce"Ruwa"

Abdallah da yake jiyo maganar ta su daga tsakar gida ya shigo, ya ce "Mama, ita fa wannan yarinyar taki, kamar namji take ba ta san komai na rayuwa ba, sai an karanta mata yadda yakamata".

Ya kalleta ya ce "Ke, ki nutsu malama, aure zaku yi, so muke idan ki ka tafi kin tafi kenan, ba zaki dawo mana gida ba, dole ki din ga yi wa mutane abun da ya dace, har zancen ma zan koya miki. Yanzu mama ki kawo kuWi, mu sayo kayan meat pie, in taya ta mu yi, sai a haWa masa da lemon roba da abinci"

"Duk shikaWai? Gaskiya ni ba zan iya aikin wani meat pie ba, bacci zan yi, ni idan ya zo ma ban san me zance masa ba? Sai dai Huzaifa ya rakani, ko Yasir"

Abdallah ya ce "Ka ga shashasha, tashi ki je ki yo cefanen meat pie Win nan"

Gaba Waya rumaisa ga rasa gane dalilin da ya sanya, kowa laifinta yake gani a kan Adam, kowa so yake lallai sai ta kyautata masa, haka mama ta saka baki, aka aiketa sayen kayan meat pie da za a karSi Adam.

Abdallah da Huzaifa suka sakata a gaba, a kan aikin, amma ta ?i mayar da hankali, ?arshe su suka yi aikin suka Wai.

Yaya Usman ne ya dawo, ya tarar da su Abdallah suna ta kai kawo, an yi girki, kamar dai wani abu mai muhimmanci na shirin faruwa.

"Wai lafiya na ga ana ta wani shiri, ko bikin aka fara tun Yanzu babu labari, abu na masu hannu da shuni"

Huzaifa ya yi dariya ya ce "Yaya Usman, sirikin ne zai zo, yau zai fara zuwa zance, shi ne ake shirya masa abinci, kar azo a ji kunya. Gara mu? kankaro kanmu, sai dai ita yarinyar ce ba ta da hali, ana saita ta a hanya tana fizgewa".

Usman ya nufi Wakin mama yana faWin, "ubanta kuwa za ta ci wallahi, dole a saita ta. ke kina ina?" Yayi maganar yana shiga Wakin mama, rums ta yi Wai-Wai tana kallon Tv, tana cin kantu mai gishiri.

"Ba zaki tashi ki fara shiri ba, yaushe ya ce miki zai zo?"

Rumaisa ta Waga kai ta kalli Usman ta ce "Oho masa"

"Ke ina yi miki magana, kina amsa mini a haka, tashi zaune"

Rumaisa ta tashi zaune tana Sata rai. Mama da ke gefe ta ce "Ai gara ku shiga cikin lamarin, tun da ni ba zan gaya mata ta ji ba".

Usman ya ce "Aikuwa da ni take zancen, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki yi masa rashin mutunci, ko wannan cin maganin, sai na yi miki bugun sakwara, ko ki zauna kina wannan Sata ran, ki na kumbura baki zaki ga yadda zan yi da ke"

"To ni yaya usy ya zan yi? ku fa ku ka ce mini ba ruwana da maza, ni ban taSa zance ba ban san me ake cewa ba, sai dai Huzaifa ya rakani, ni tsoro ma nake ji".

Usman ya ce "Au idan aka yi miki auren ma, huzaifa ne zai biki gidan mijin, ya tayaki zama da kula da mijin?".

"Ni ba zani gidan kowa ba, sai dai shi ya dawo nan gidan ya zauna, kuma bada Sabir kawai zan kula ba, shi ?ato da shi me zan masa?"

Huzaifa ya ce "Ki ce auren Bollywood za ayi, ayi aure miji ya tare a gidan su mata, yarinya sai dai kar ki yi zancen, idan ni zan rakaki".

Usman ya ce "Ni bari na koya miki abun da zaki ce, ya za ayi wani huzaifa ya raka ki, ya ji kalaman soyayya ya dawo yana tsokanar ki".

Ta kwaSe baki ta ce "Soyayya kuma?"

Usman ya ce "Eh mana, au da ?iyayya?" Ta yi shiru, tana kallon Usman.

Ya ce "Idan ya zo, ba ?ifi-?ifi zaki yi da ido, kina kallonsa kamar fusatacciyar kyanwa ba, ya ga alamar girmamawa a idonki, idan ya zo sai ku gaisa, ki tambaye shi ya mamansa, da ?annensa da Sabir. Cikin mutuntawa ba da zazzare ido ko harare-harare ba, ki na yi kina sunkuyar da kai, ban da tsyawa ki ?ure shi da ido, na sa cikin naki, duk abun da ya tambayeki ki bashi amsa, ba cikin tashin hankali da masifa ba, sai dai idan kin ga yayi miki wani abu da ya saSa shari'a da tarbiyyar da aka baki, sai ki zo gida ki gaya mana".

A ranta ta ce "SaSa shari'a da tarbiyya na nawa kuma, dan dai kawai kar na zubar masa da mutunci ne, amma da sai na gaya wa kowa abun da ya yi mini".

Muryar Usman ce ta dawo da ita hayyacinta, da ya ce "Kin ji abun da na ce ko kuwa?".

"Na ji" ta amsa da ?yar.

"To tashi ki je ki yi wanka, zan din ga yi ina zagawa in ga yadda ki ke zancen, idan ki ka kuskura, ki ka aikata abun da na hanaki, a gabansa zan tuburbuWaki".

"To yaya usy, ni fa na yi wanka da safe"

Huzaifa ya ce "Sokuwa, wannan wankan tarbar masoyi ne, wankan ganin baby".

"Allah ya kiyaye na ce masa wani baby, kamar wata ?ar iska, sunansa Adamu"

Usman ya saka hannu, ya talle mata ?eya, sai da ta kusa kifawa. "Shashasha, ana koya miki abu kina iskanci, ki je ki yi shirme a auren, zaki gane baki da wayo, tashi ki je ki yi wanka" tashi tayi ta dafe ?eya, ta fice daga Wakin.

Mama ji take kamar ta yi dariya, yayyen sun zauna suna koyawa ?anwarsu, yadda ake yin zancen???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?.

Mama ta ce "Malam usman wannan lakcar, anya ba a zagaya zauruka da magariba? Ba a taSa bani labarin sirikar tawa ba"

Usman ya sosa kai ya ce "Mama a wurin abokaina nake ji".

Mama ta yi murmushi ta ce "Ba zan hanaka ba, ni dai fatana aji tsoron Allah, kar a din ga zuwa rage dare wurin yaran mutane, alhalin ba aurensu za ayi ba".

"Mama kar ki kawo komai a ranki ma, ba wurin da nake zuwa"

"Idan ma ana zuwan dai, ai dole na yi kashedi" Usman ya din ga murmushi yana sinne kai.

****
Iman tana zaune a kan gadonta, ta sunkuyar da kai, gefe Nusaiba na zaune, sai kuma jabir da ya saka Iman Win a gaba da kallo, kamar zai haWiyeta.

"Talk mana iman ko na ji daWi, saboda an ce baki da lafiya ban gama abun da nake yi ba, na baro Germany, na zo na dubaki kuma kin ?i magana, talk please"

Nusaiba ta ce "Please iman, stop treating our uncle J this way, ki yi magana mana".

Cikin sanyinta ta ce "Anty Nusaiba, maganar ce bana so in general, bana jin daWi sam"

"Amma duk da haka bai kamata ya yi ta magana ki yi masa shiru ba"

Ta Wan kalleshi ta ce "Am sorry".

"To ya zan yi da ke jarumata, bana son yadda ki ke yi mini wula?anci, idan wani abun na yi miki am so sorry for it"

Ta girgiza kai ta ce "A'a babu komai"

"Shikenan, na ga kamar ina takura miki, bari na je gida, Nusaiba take a good care of her please"

Nusaiba ta ce "To uncle J, but you have pay for the service"

Yayi murmushi ya ce "Biyoni mu yi ciniki, za a biyaki ko nawa ne" ta yi murmushi ta tashi ta bi bayansa suka fita.

A hankali iman ta furta "Ohh Allah, ka iya mini, Allah ka yi mini zaSi na alkhairi, Allah kar ka saka Jabir ya gayawa wani yana sona, he has no space in my heart. Ni ba kowan kowa ba ce, duk zaSin da ka yi mini ina so Allah, Allah ka iya mini" ta ?arasa maganar tana kwanciya a kan pillowanta.
Sai dai tana kwanciyar, ta ji tamkar an sanys igiyar ?arfe, an WaWWaure mata jijiyoyin kanta, ta sanya hannu ta dafe kan ta fashe da wani marayan kuka, ta rasa me ma za ta yi, lamarin nan ya fara bata tsoro, dan kuwa ji take tamkar zata haukace.

Jabir ya kalli Nusaiba ya ce "Nussy, see how your sister is behaving towards me, just because i have feelings on jer, me yasa ba ta so na, meye aibu na?"

"Uncle J, yakamata ka yi mata uzuri, this girl suffer alot in this family, kalli yadda take samun manema, suna tafiya saboda abun da mutane basu da tabbas a kan sa, kalli saboda yarima ya ce yana son ta, kalli wula?ncin da fulanin yola ta yi mata da cin mutunci, har a gidan nan ma ba ta tsira ba, na waje ma idan sun biyota suna so, sai a samu mai zigasu su daina zuwa. A yanzu ta riga ta ce ba ta son kowa ya raSeta da sunan soyaya, ba ta son kowa, ka san abu na ?arshe da ya faru a gidan nan ai, ba wanda bai ji ba, shi ma aka din ga surutu a kai. Dan haka ta ce idan har mijin aurenta ya zo ko ba soyayya, ta ce za ta yi, amma for now, tana bu?atar hutu ne".

"Nusaiba, babu Wan adam Win da baya faWi tashi da gwagwarmaya da ?addara, amma hakan ba ya sanya wa a sare, this is not an excuse da za ta yi denying kowa ya ce yana son ta, ni da gaske ina son iman, amma wace shawara zaki bani a kan ta?"

Nusaiba ta numfasa ta ce "Uncle J, ga ka da takawa, ga ka da Ammi, ai a duniya babu abun da za su ce ta yi, ta ?i yi muddin bai saSawa shari'a ba, ka bi ta wurinsu kawai, ina fatan idan komai yayi daidai, zaka kula mini da iman, ka kuma ji tsoron Allah a kan ri?on ta".

"Nusaiba da zan cutar da iman, ba zan aureta ba, ina son ta so na gaskiya ne, abu na gaba ina ga ammi zan samu kawai, takawa zai iya yi mini wasa da hankali, kin san halinsa, bari na je kawai na gode, ki yi mata sannu"

"Za ta ji, ka gaida gida" suka yi sallama ya tafi, ita kuma ta koma.

***
Aiki ya samu ?an maza fa, domin kuwa su Usman ne suka zaSowa rumaisa kayan da za ta saka, sai cika take tana batsewa, wannan ya dungure mata ya ce "Ki yi dariya dan ubanki".

Wannan ya ce "Ki ka yi mana shirme dakuwa zaki yi".

Suka shiryata cikin doguwar rigar atamfa, ta sanya dogon hijjabi, Abdallah ya ce "Ina hoda a shafa miki?"

"Ni bani da hoda" ta amsa masa tana Wan hararsa.

Usman ya ce "Jambaki fa?"

Ta Sata fuska ta ce "Ni fa kun san mai kawai nake shafawa, shi ma ba kullum ba, bani da komai ni".

Usman ya ce "Ikon Allah, lallai kin cika deluwa, kina mace amma ba hoda ba Jambaki, kamar gardi, wallahi ki ka je gidan miji ba kya kwalliya, wahala zaki sha, to yaushe mutum zai ajiye mace, amma shi da ita ba maraba? Ai na ga mama tana da kwalli, shi zaki saka"

Rumaisa ta ce "Yaya usman, idona fa yaji yake idan na saka kwalli".

"Ai ko tsiyayowa zai yi sai kin saka, Abdallah ya ri?eta, Usman ya saka mata kwalli, tana kuka sai ka ce dole"

Mama ta ri?e haSa tana "Yau nake ganin ikon Allah"

Abdallah har da lakato Vaseline, ya shafa mata a leSenta.

Huzaifa ya ce "Ai dole idan ya tafi, a yau ba sai gobe ba, a sayo kayan kwalliya ta din ga yaSawa"

Usman ya ce "Dolenta ma kuwaa"

Aka Wauko turare aka fesa mata, Usman ya ce "Ranar kamu ni zan kamaki, an ce da turare ake yi ko? Idan na din ga fesa miki, sai kin fara haya?i"

"Sai ka ce wata ita ce"

"Koma dai menene, ina sake jaddada miki, ki ka yi mini kwaSa, da takalmi zan ladabtar da ke".

Ta kalli kanta a mudubi, ta ce "Kalli yadda ku ka mayar mini da ido, kamar wata sheWaniya"

Yasir da yake zaune yana kallonsu yayi dariya ya ce "Koma dai wacece, idan ya zo, baby ka zo, you are welcome ya aiki? Ya family, kamar dai yadda ki ke gani a film, mussaman bollywood".

Ta buWe baki ta ce "TaS, Allah ya tsareni, Bollywood ba taSa mata suke yi da maza ba, wallahi ya taSa ni, sai na gantsara masa cizo, babu namijin da zai taSa jikina in tsaya ina kallonsa, ko a wurin ?an bindiga, bana yadda, wallahi faWa ake da ni" ga mamakinta sai ta ga gaba Waya sun tuntsure da dariya, Usman ya ce "Wannan bawan Allah yana ruwa, mama akwai bu?atar ilimantar da yarinyar nan kan aure"

Mama ta yi masa shiru, kamar ba ta ji ba, wanda a ranta tunani take yi, ta yaya za ta yi wa rumaisa bayanin wannan al'amari mai girma, yarinyar da ta tashi a kan iya abun da aka nuna mata shine dai-dai a gida, kome za ayi ba zata yadda ta canza ba, yanzu da an ce mata wani abu, tsaf za ta ce kenan da ?arya ake yi mata.

Wata zuciyar ta ce "Ko da yake, ai ina ga zai Wan ?yaleta ta ?ara wayo, tun da saboda karatunta ma mamansa ta ce ayi auren'

'Namiji ne fa' wata zuciyar ta tunatar da ita.

Ta Wan dafe kai ta ce "Yarinya ce, lokacin da aka yi mini aure, shekara sha biyar, na fi rumaisa girma sosai da sosai, amma lamarin aure abu ne mai faWi"

Yasir ya ce "Mama magana ki ke yi ne?"

Ta ce "A'a kallonku nake yi dai".

Mai sunan baba ya shigo, hakan ya sanya duk suka yi shiru suka nutsu.

"Ke ki zo, ga mutumin can yazo, ki Wau abun zama ki saka muku a soro, kar ki sake ki tsaya a waje, balle wannan iyayen saka idon su ganki".

Cikin rawar murya ta ce "Mama ni fa tsoro nake ji, gabana faWuwa yake yi"

Mama ta buWe baki tana kallonta, har idonta ya ciko da hawaye.

"To cinyeki zai yi?" Mai sunan baba yayi maganar yana tsareta da ido. Ta girgiza kai alamar a'a.

"To kukan uban me zaki yi? Wuce dalla, sai kin tayar mata da hankali haka kurum".

Huzaifa ya Wau turare da darduma, ya ce "Bari na yi maza, na je shimfiWa dardumar na fesa turare a soron, sai taho kina taku kamar gimbiya, dan gidan sarauta ba sa son hauma-hauma" ya ruga yayi soron da gudu.

Ya shimfiWa, ya feffesa turare, ya dawo da sauri ya ce "To fito, ki ce masa ya shigo".

Ta fito tsakar gida zari silifas, za ta yi waje, Usman ya ri?eta "Wai ke rumaisa wace irin ?ar ba?in ciki ce? Yasin gidan sarautar nan sai kin je shi, ba zaki mana bu?ulun zuwa gida mai kyau ba, canza wannan Wan iskan takalmin, ko na cire shi, na tsinke ki da mari da shi, kuma idan ya shigo mintuna biyar, ki zo ki Wauki kayan abincin nan ki kai masa, dole mu koya miki soyayya, dan ba zaki yi aure ayi miki kishiya ba"

Tana cusa baki, ta sauya wani ta fita, bagazan-bagazan ta le?a wajen, ta ganshi a tsaye a jikin motarsa yana amsa waya.

"In ka gama wayar, ka shigo" ta faWa tana ri?e ?ugu. Kamar bai san ta yi maganar ba, ya cigaba da wayar, ita kuwa ta koma soron, ta zauna ta mimmi?e ?afafuwanta.

Ya kai mintuna goma, kan ?amshin turaren sa ya mamaye ilahirin soron, brown Win yadi ne a jikinsa, kansa babu hula, sai zuba ?amshi yake, ta Waga kai ta kalleshi, kamarsa da Sabir ta sake fitowa sosai da sosai.

Ya nemi wuri ya zauna a kusa da ita, ta matsa can ?arshen sallayar, tana kaWa ?afa.

Jin shirun yayi yawa, ba shi da niyyar magana, ya sanya ta ce "Ina wuni?" Ya kalleta ya yi shiru bai amsa ba.

"Ai dama na san ba amsawa zaka yi ba, dan a gida an ce in gaisheka ne, amma idan na gaishe ka, ba amsawa kake yi ba, ai ni na riga na gama sanin halinka kaf, daga A har Z"

Nan ma shiru bai amsa mata ba.

"TaS kana da aiki wallahi" ta juya masa baya, ta kalli wani wurin. Ya kalli bayanta, yana jinjinawa tsiwa da rashin jin ta, wai ta san halin sa daga A har Z. Can aka kwashi wasu mintuna, sai ta tuna abun da Usman ya ce mata ta tashi da sauri ta Wauko kayan abinci nan.

Gaba Waya suka taso suna tambayarta yaya aka yi?

Ta ce "ba komai"

Usman ya ce "To, wallahi ki ka dawo da kayan Abincin nan, bai ci komai ba, to tabbss rashin mutunci ki ka yi masa, kuma zaki daku" ta gyaWa kai, ta tafi soron ta tarar da shi, ta ajiye masa kayan a gabansa ta zauna ta ce "Ga abinci nan" ya Wago ya kalleta ya cigaba da taSa wayarsa.

"To, ni dai zan juya maka baya, ka ci, dan ba zan yi wahalar banza ba, tun safe ake azabtar da ni a gidan nan saboda zaka zo, zan juya maka baya, ka ci idan ba zaka iya ci a gabana ba"

Ta juya masa baya, ta Wauko goruba tana ci.

A ransa ya ce "Na ga ta kaina ni Adamu, wai wannan ce matar da zan aura?"

Ta waiwayo ta ce "Wai ba zaka ci ba? To wallahi ba zaka ja mini duka ba.

Ta Wauki coca-cola, ta tsiyaya a kofi, ta shiga hijjabinta ta sha, ta buWe meat pie, ta Wauki Waya, ta? shiga hijjabinta ta ci, ta gutsuri wani ta ajiye ta ce "Yauwwa, dan ba zaka ja mini duka ba, an ce idan har na koma da shi ba ka ci ba, yaya usy zane ni zai yi"

Adam ya zubawa sarautar Allah ido, ita a rayuwarta ba ta san kara ba, idan ana neman mutum kai tsaye da ba ya rufi, to kowa ya bi bayanta.

Kamar wadda ta ci wani abun maye, ta takure abun ta, ta haWa kai da gwiwa ta hau bacci, shi dai ikon Allah kawai yake kallo, wannan zance ya zo, ko kallon drama.

Ya mayar da hankali kan wayarsa, yana dannawa.

Usman da yake kaiwa yana komowa ya ce "Kai shirun nan yayi yawa, bari na duba"

Wata irin razana rumaisa ta yi "Iman!" Ta faWa da ?arfi, tare da faWawa jikin Adam gaba Waya jikinta yana rawa, hakan yayi dai-dai da shigowar su Usman cikin rige-rige, domin ganin abun da yake faruwa, saboda ihunta da suka ji.

Ayshercool.
08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA

Please Login or Register in order to submit comment