You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, kar kuma ya sake nemana"

"To meyasa?"

"Fauza yayanki ne fa, kuma kin san abin da yake zuciyata game da takawa"

Fauziyya ta jinjina kai ta ce "Na san yayana ne, amma ke yanzu haryanzu ki na nan a kan bakanki kina son sa, ana barin halak dan kunya fa"

"Ke ki ka san ta, ita halak Win, bari na shiga wanka" ta yi maganar tana mi?ewa.

?an shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci 'wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani' da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga Wakin.

***
Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata daWi. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.
Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.
Gabanta ne ya faWi da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.
Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.
Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.
Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ?asa tana sunkuyar da kai.

"?ago ki kalleni" ya faWa a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta ?asa.

"Aure ki ke so ko?" Nan ma ba magana sai girgiza kai.

"Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura Win, ranar juma'a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta"

Da sauri ta Wago ta kalleshi, "Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba"

"?arya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so"

"Wallahi a'a, ban san batsa nake tambaya ba"

"Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma'a za a Waura miki aure"

"Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba"

"A ina saurayin naki yake?"

"A cikin tv nake ganinsa, Wan wrestling ne, amma ban san a ina yake ba"

Mai sunan Baba ya kalleta ya ce "To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to sa?onki ya isa za ayi abin da ki ke so"

"Wallahi yaya ba haka nake nufi ba"

"To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu'a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ban sani ba"

Ya sake tsuke fuska ya ce "?arya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan"

"Wallahi ban sani ba, 'yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa"

"Wace irin soyayya?"

"Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da daWi, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba".

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma'a Waurin aure"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah ka yi ha?uri, manya ake yiwa aure ban da yara"

Cikin zafin rai ya ce "Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri" jiki na rawa ta tafi Waki, tare da fashewa da kuka.
Gaban mama ta je tana kuka ta ce "Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini"

"To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya zaSa miki shikenan"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi"

Mama ta ce "Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya"

Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ?arshe a nan wurin bacci ya kwasheta.
Da safe kuwa wasan Suya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, ta?i yadda su haWu, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

Ruma fa gaba Waya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.
Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta Suya sai kuka, duk ta rasa sukuni.
Mama ta shiga banWaki ta lallaSa ta Wau wayarta, ta kira Abubakar.
Yana Wagawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya faWi "Ruma, menene? Meyafaru?"

"Yaya, mai sunan baba ne"

"Me ya same shi, me ya yi miki?"

"Wai aure zai yi mini, dan Allah ka yi masa magana, mama ta?i hana shi, dan Allah ka ce masa ni yarinya ce, dan Allah kar ayi mini auren nan bana so"

Cikin rashin fahimta ya ce "Wani irin aure kuma?"

"Haka ya ce wai ranar friday zai mini aure da wani, dan Allah ka hana shi"

"Kwantar da hankalin ki 'yar gudaliyar, zan kirashi in sha Allah, ki daina damuwa"

"A'a ba zan iya dainawa ba, ka kirashi yanzu kawai"

"To an gama, kiyi ha?uri babu mai yi miki wani aure yanzu".

Ya yi ta kwantar mata da hankali, har ta samu ta Wan nutsu.

***
Yana zaune a falo, yana duba labarai a wayarsa, Mummy na gefe tana shan fruit, ta kalli yadda ya sha fararen kaya, da shuWiyar alkyabba hannunsa ya sha zobbunan azurfa, sai kaWa ?afa yake a hankali.

Ta yi murmushi ta ce "Ka ga kyan da ka yi kuwa? Sai ka fito a basaraken ka na asali jinin galadima, Allah ya kawo gingimemiyar kujera"

Bai kalleta ba ya ce "wace irin kujera ce gingimemiyar?"

"Ka gaji Galadima mana, ko ma kujerar garin gaba Waya"

Mahmud ya ce "Mummy you are funny, ni fa sabgar sarautar nan ba ta dameni ba, ki bar ni da karatuna, na kammala na samu aikina period, shi dai da yake ta zazzare ido, na san bai wuce a kan sarautar ba, sai ya je yayi ta yi"

Cikin mamaki ta kalli Mahmud ta ce "Mahmud, wai kai meyasa ba ka da kishin zuci ne, sarautar nan fa taku ce, ta mahaifinku ce gaba Waya a ka Wauka aka kai wani gidan, kuma muna saka ran za ta dawo mana, tun da galadiman yanzu shi ma yana can babu lafiya, kuma da zarar ya mutu babu batun wani ya gaje shi, tun da duk 'ya'yansa mata ne, Jabir kuma bai isa ya saka rai ba, dole gidan nan za ta dawo. Dan haka ba zan zuba ido a bawa Adam sarauta bayan ga ka ba, kai ma Wan galadima ne, dan haka kai ma ka cancanci ka gaji sarauta".

Mahmud ya Wan yi shiru ya na tunani, amma bai ce komai ba.

"Mahmud, kar ka watsa mini ?asa a ido, idan ba haka ba, haka fa zamu cigaba da zama Giwar Galadima ta mamaye komai, ta cigaba da juyamu yadda take so, yaka ke gani idan sarauta ta dawo Adam ya samu, kai menene naka, a wani babin ka tashi?"

Ajiyar zuciya Mahmud ya yi, ya fesar da iska daga bakinsa, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta ya ce "Mummy, zan je salla daga nan zan Wan shiga gari, sai na dawo" yana gama maganar ya mi?e a hankali ya bar falon.

Fauziyya da ke laSe take jin su ta fito, ta nufi wurin Mummy ta zauna tana murmushi ta ce "Hajiya Mummy, mai abubuwan ban mamaki, irin wannan famfo haka?"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Ai ba ayi komai ba ma tukuna, dole sai na sakawa Mahmud ?awazucin kujerar nan, yaron nan akwai ba?in taurin kai, Wan uwan Wayan ne a taurin kai, tun da ?uruciya nake kwaWaita masa daWin mulki, amma ya?i ganewa, amma zan cigaba da gwada masa fa'idar ace mulki yana hannunsa, in sake rura wutar ?iyayya a tsakaninsa da Adam, kuma in toshe kafar da sarautar za ta dawo gidan nan, dan ita ma Hajiya Lubabatu kwaWayi take na ta Wan ya gaji sarautar idan mahaifinsa ya mutu"
Fauziyya ta jinjina kai ta ce "Mummy kenan, akwai lissafi, na zo miki da wani labari ne mai daWi"

"Wani labarin kenan?"

"Khalifa Usman wakili, kin san case Win su da takawa, kusan shi ne yake trending a media yanzu"

Mummy ta jinjina mata kai.

"To dai in gaya miki shi ne ya gayyaci Samha, wai yana son su haWa kai, su kawo ?arshen yaya Adam, ita kuma ta ce bata yadda ba, kin san son shi take yi"

"Eh, na sani, ai itama Samha wata makami ce da nake amfani da shi ta ?ar?ashin ?asa, amma labarin nan yayi mini daWi sosai, ke dai ku cigaba da baza kunnuwa, duk abin da ku ka ji, ko kuka gani kawai ku sanar da ni"

"In sha Allah Mummy, Allah ya ida nufi"

Suka yi murmushi gaba Waya.

Takawa ne zaune a wani ?aton falo, mai Wauke da kayan ado na gidan sarauta, gefe gud kuma tarin litattafai ne a jere a cikin wata drower.
Ya sanya system a gaba, yana dannawa yana Wan juyi a jan kujerar da yake kai.
Jabir na zaune a kan kujera yana facing Win sa. Jabir ya tattara nutsuwartsa a kan Adam ya ce "Takawa, kana bibiyar shafukan sada zumunta kuwa?"

"Meyafaru?"

"To ai gani na yi ka yi burus, kamar baka bibiyar meke faruwa"

"Shi ya sanya na tamabayeka, meyafaru?"

"Tone-tonen da ka ke ?o?arin yiwa Senator usman wakili, akwai ?ura fa sosai da sosai"

Ya Wan Wago ya kalli Jabir ya ce "Ai ni ?urar nake son ta tashi, ta hana kowa nutsuwa, saboda haka nake wannan aikin"

"Duk da haka, ko dan tsaron kannka da lafiyarka, yakamata ka san yadda zaka din ga gudanar da ayyukan ka, taSa manyan nan ba abu bane ba sau?i ba fa"

Adam ya yi murmushi ya ce "Na fahimce ka mutumina, kar ka wani damu, ka tayani da addu'a kawai, amma dole mu yi wa ?asarmu hidima"

Jabir ya jinjina kai ya ce "Haka ne".

***

Bil ha??i mai sunan Baba ya nunawa ruma aure zai yi mata, ya je ya a sayo sabuwar katifa ta 'yan makaranta, ya ce wa mama gata nan a ajiye ta ruma ce, ya sayo kwano da kofin silba mai murfi da sabuwar buta, shi ma ya ce na ta ne.
Hakan ya ?ara dugunzuma hankalinta, cikin dare mama ta na bacci ta ga ruma tana shimfiWa sallaya tana kuka.

Mama ta ce "Ke lafiyarki kuwa?"

"Sallar dare zan yi, na ro?i Allah a kan mai sunan Baba, tun da kin ?i ki hana shi, an rasa wanda zai hana shi yi mini aure".

Mama ta yi murmushi ta ce "Ke fa ki ka ce kin ji kin gani, ki yi addu'a kawai Allah ya baki zaman lafiya da ke da wanda zai aura mikin"

Zaman dirshan ruma tayi, ta Wora hannu a ka tana kuka, mama ta rufe fuska tana yi mata dariya ba tare da ta sani ba.

Ruma ta daWe a sujjada tana addu'a, sannan ta koma ta kwanta.

A islamiyya kuwa, malamin ajin da take ne, ya lura yana ?ari tana kuka, dan yanzu a Wan samu cigaba, ta daina guje-gujen aji, a babban aji da ajin su Yasir take zama, kuma yanzu tana iya karatu ba kamar da ba.

Sai da ya kammala ?arin Alqur'ani, sannan ya kira ruma yana tambayarta me ya sa take kuka?
Ba ta gaya masa ba, ta ce mai babu komai, ?arshe sai ?yaleta yayi.

Ranar juma'a kuwa da farar safiya da kuka ta tashi, dan yau ne kwanakin da mai sunan baba ya Wibar mata suka cika, ba tare da ta samu wanda za ta kawo ba, a matsayin wanda take so, to ita wa ma take da shi.

Mama sai fama take da ita ta shirya ta tafi makaranta, amma ta rungume uniform Win tana kuka.
Umar ya fito fuska a haWe ya daka mata tsawa, cikin tsuma ta hau saka kayan ba tare da ta yi ko wanka ba.

"Ki fice ki tafi makaranta, idan kin je can sai ki yi musu kukan, shi ne ki ka gayawa Wan uwa wai zan yi miki aure ko? To shi ma bai isa ya hanani abin da na yi niyya ba, ai ke ki ka nuna ki na son auren, wuce ki bawa mutane wuri"

Kamar korarriya, ta Wau jakarta ta tafi makaranta.

Bayan fitarta, mama ta kalleshi ta ce "Babana, a sassauta mata ta horu haka, kwanaki uku kenan ba ta ko cin abinci, ayi mata afuwa babana"

"?yaleni da ita, horata kawai nake, amma yau zan ?yaleta in sha Allah"

?in shiga makarantar ta yi, ta tsaya a waje tana kuka, mai gadi ne ya ganta, ya ja ta ya kaita ofishin Headmaster, ya sanar masa da a waje ya ganota ta tsaya ta na kuka.

Headmaster ya ce "Ai ni rigimar yarinyar nan nake tsoro, ke me aka yi miki?"

"Yayana ne ya ce zai yi mini aure yau"

Waro ido ya yi ya ce "Aure kuma? Waye zai kwasa? Ke bana son wasa"

"Wallahi haka ya ce"

Headmaster ya kalli ruma, sai ya kawo ko rashin hanklin ruman ne ya motsa, dan haka ya ce "To shikenan, ki yi ha?uri ki tafi aji, zan kira gidan na ku mu yi magana da su" yayi ta lallaSa ruma ya kaita aji.

Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba, sai da ta dawo gida ta tarar mama tayi tuwon shinkafa da miyar taushe, da wainar masa wai azo a kai ma?wabta ace na auren ruma ne, mai sunan Baba ya ci farar shadda ya fito tsakar gida ya ce "Mama, idan an idar da sallar juma'a za a Waura mata aure, sai ayi mata addu'a"

"Na shiga uku, mama wai da gaske ne? Mama ku yi mini rai ban isa aure ba wallahi"

Wani mugun kallo ya yi mata, ta shige Waki da gudu tana kuka, ya fice ya bar gidan.
Dariya Huzaifa ya din ga yi mata yana "Ruma, Allah ya sanya alkhairi zan kawo miki goron Waurin aurenki har gida ki tauna, dan mijin naki ma tsoho ne, malam labaran ladan ne"

Ruma sam ba ta shiri da malam labaran ladan, saboda ya taSa tsula mata carbi, wataran yana kiran salla, ta taSa tsayawa a ?ofar masallaci tana? kiransa da ?arfi, wai saboda muryarta ta fito a sufika, ya idar ya kamata ya zane ta da carbi, gashi tsoho sosai.

Mama ta shiga Waki ta tarar da ruma sai rizgar kuka take.

"Haba amarya, ya da kuka kuma kamar ba amarya ba?"

"Dan Allah mama ki bani kuWin mota na gudu"

Mama ta kwashe dariya ta ce "Dama ruma akwai abin da zai baki tsoro haka?"
Rungume mama tayi cikin kuka ta ke faWin "Dan Allah mama kar ayi mini aure, wallahi na daina rashin ji, ina sonki sosai, bana son na rabu da ku, mama zaki yadda a aura mini wanda ya dakeni dan Allah mama ki hana shi aurar da ni"

Rungumeta mama ta yi tana murmushi, tausayin ruma ne ya kamata, dan har ramar dole ta yi, saboda damuwa.
Mama ta zubo mata abinci, ta zaunar da ita ta bata, amma ruma ta?i ci.

Mai sunan Baba suka yi sallama, duk suka shigo a tare daga sallar juma'a, duk sun sha kwalliya.

Aliyu ya ce "Amarya kin sha kuka, to Allah ya sanya alkhairi" ta rirri?e mama tana girgiza kai tana zubar da hawaye.

Mama ta kalli mai sunan Baba ta ce "Tuba muke babana, Allah ya bada ha?uri duk ta rame, ayi ha?uri"

Yasir ya ce "Haba mama, ya zaki yi mana haka?"

Mama ta yi masa da?uwa tana harararsa.

Umar ya ?arasa gaban ruma da ta takure a jikin mama, tana share hawaye.

"Kalleni" yayi maganar yana tsareta da ido.

Ta Wago a hankali ta kalleshi, idanunta sun yi jawur.

"Daga rana mai kamar irin ta yau, idan na sake jin ki aikata wani abu na rashin mutunci, ko wannan shegen surutun naki, to ki tabattar aure babu fashi, kin ji na gaya miki?" Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana sake rungume mama.

Mama ta ce "To madalla godiya muke, Allah ya rayaki, ya kaimu auren ki na gaske, da miji na gari ko?"

"Ni ba zan aure ba, bana so da ma da wasa nake, kuma ba zan auren ba"

Mama ta ce "Tashi ki yi godiya, tun da dai ya janye maganarsa"

"Na gode" tayi maganar tana Soye fuskarta.

Tashi yayi ya bar Wakin ba tare da ya ce mata komai ba, ta din ga sauke ajiyar zuciya ta ce "Amma an shiga hakkina, Allah zai sakawa marainiya"

Yana tsaye a bakin ?ofa, karaf maganarta a kunnensa.

(BOOK 1 FREE NE, BOOK 2 PAID, BOOK1 YA KUSA KAMMALA IN SHA ALLAH, GODIYA TA MUSAMMAN GA MASU BIBIYAR LITTAFIN ?ANWAR MAZA)

Ayshercool
08081012143
[29/07, 7:26 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ?ANWAR MAZA

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


P 18


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR? DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHE?I TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*




https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haWa 1k subscribers a channel Wina ba, anya akwai amana kuwa=??*

Ku yi subscribing YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.


Sarai ya ji abin da ruma ta ce, amma ya share kawai ya tafi, dan idan ka biye mata babu abin da zai hana ta saka maka hawan jini.

Sai a lokacin ta samu zarafin dirarwa wainar da mama ta yi, ta fara ci ta na ajiyar zuciya, dan a kwanaki ukun nan Allah kaWai ya san tsananin damuwar da ta shiga.

Yasir ya ce "Na so auren nan aka yi miki, mu ga ta tsiya, kowa ma ya huta da halinki"

"Ta Allah ba taka ba, bakinka ya sari Wanyen kashi, na asuba mai tururi"

Mama ta ce "Meye haka, ki na cin abinci kina zancen ?azanta"

"To mama ba sune suke tsokanata ba"

"Ina ruwanki da su, wato har kin samu kanki za ki Wora daga in da ki ka tsaya ko?".

Ta girgiza kai ta ce "A'a, ai na shiryu ba zan ?ara ba"

"Kima cigaba, wallahi kin san idan ya zuciya da halinki, zai aikata abun? da ya ce"

Sallamar Abubakar da suka ji ne, ya sanya ruma yin wani zillo, ta daka tsalle ta yi waje, ma?al?ale shi tayi tana murmushi tana faWin "Oyoyo yaya"

"Amarya ba kya laifi, kar dai har an Waura auren ban samu Waurin auren ba?"

Ta Sata fuska ta ce "Yaya har da kai ko?"

"A'a, nima fa kirana aka yi a waya, aka ce mini yau Waurin aure"

Waiwaya ta yi, ta kalli mai sunan Baba da ya shimfiWa tabarma ya baje litattafai yana dubawa, ta kalli Abubakar, ta kai bakinta kunnensa ta ce "Wallahi hussaininka ya Wau hakkina, ba dan yayana bane ba ko? Hmmm"

Ya kalli mai sunan Baba ya yi murmushi ya ce "Kai, a wani dalilin ya sa ka Waga mana hankali haka fisabilillahi?" Ko Wagowa bai yi ba, balle ya kallesu. Ruma ta kama hannunsa suka shiga Wakin mama.

Mama ta ce "Ta barka ka ?araso in ganka kenan? Na ga ta je ta tsareka da zance, kamar ba yanzu ta gama kuka da neman taimako ba"

Abubakar ya yi murmushi, ya zauna ya ce "Sannu da gida Hajiya mama, uwar 'yan maza da 'yar budurwa, na sameku lafiya?"

Mama ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, amma ba ka da lafiya ne?"

Ya Wan kalli jikinsa sannan ya ce "Me ki ka gani?"

"To ai ganinka nayi wuri-wuri duk ka rame Saddi?u"

Ya shafi sumar kansa da taru sosai ya ce "Mama wannan karatun namu, ai ba sau?i ne da shi ba, pressure ce kawai, ruma zubo mini abinci" mi?ewa ruma ta yi, ta fita ta kawo masa kulolin abincin ta dire masa, ta zauna ta saka shi a gaba, tana ta zuba masa surutu, mama kuwa kallon yadda yake zira abincin nan yake babu ji babu gani, kai da ganin yadda yake cin abincin ka san akwai yunwa a tare da shi, ba dai ta ce komai ba suka cigaba da hira.

Da la'asar shi da mai sunan Baba suka tafi masallaci, bayan sun dawo kuma suka zauna a tsakar gida suna hira.
Ruma so take ta zauna da Yaya Abubakar, ta yi masa hira sosai dan ya fi kowa tsayawa ya saurareta, amma ta ga hankalinsa yana kan Wan uwansa.
Ganin ta zauna daga nesa tana ta kallonsu, ya sanya yaya Abubakar cewa "Ruma, Wauko comb ki zo mu yi tsifa, na ga kitson kanki ya tsufa" ta jinjina masa kai, ta shiga Waki ta Wauko comb da kibiya ta kawo masa, ta zauna a kusa da shi, tana yi tana kallon fuskar Umar, dan kar ya hantareta ko ya koreta.
Yaya Abubakar ya karSi kayan tsifar, ya kwantar da kanta a kan cinyarsa, ya fara tsfefe mata kai.
Rai a haWe mai sunan Baba ya ce "Amma dai ka san bana son ?azanta ko?"

"?azantar me kuma?"

"Dan me zaka zo kusa da ni kana aikin gashi, ko ?yan?yami ba ka ji"

Abubakar ya yi murmushi ya ce "Kayi karatunka ka ?yalemu mu yi tsifar mu" a hankali ruma ta fara lumshe ido, bacci yana Wibarta, cikin gyangyaWinta ta ji Abubakar yana cewa mai sunan Baba "Ka ga ?oshin nan da na yi cikina har wani ciwo yake yi"

Mai sunan Baba ya kalle shi ya ce "Kamar yaya, da ba ka ?oshi ne?"

"Wallahi Akhi rabona da Abinci kusan kwana biyu yau, a ?afa fa na taho tasha, na samu mota na taho gida shi ma daga tasha na ninko, Allah ya haWani da wani Wan unguwar nan ya goyoni a babur"

Cikin mamaki Umar ya ce "Garin yaya?"

"Wallahi kamfanin 'yan chinan da muke yiwa aiki ne suka koremu, suka kawo mutanensu. Ni kuma na ga ban aiko da komai gidan nan ba, ta yaya zan bugo na faWi matsala, na sayar da wayata na sai ?arama ina ta fama, gashi mun kusa exam, shiyasa ban zo gida ba, shekaranjiya garrin kwaki na ci ko ji?awa ban yi ba, na wahala a semester nan wallahi"

Umar yayi tsaki ya ce "Akhi kana da matsala, amma ko baka gaya wa mama ba, ni mai ya hana ka gaya mini, sai ka je ka kashe kan ka da yunwa, idan ba abinci ta yaya karatu zai yiwu?"

"Kai ba fa ban gaya maka ne dan ka yi mini masifa ba, ko nima ?aninka ne?. Na tafi na barku kuma kuna ta fama da yadda zaku yi, ni ban muku ba, kuma na Woro muku matsala, gashi na yiwa yarinyar nan al?awarin sabuwar jakar makaranta ban samu saya mata ba, har kunyarta nake ji wallahi".

Mai sunan Baba ya numfasa ya ce "Dole mu din ga gaya wa juna matsalolinmu, watarana sai labari, ni kaina abubuwan sai a hankali, na saya wa yarinyar nan sabuwar katifa kusan dubu talatin,? ta ta ta lalace, da so nake na sauya mata makaranta, makarantar gwamnatin nan ba ta iya komai, an ce mini registration dubu Arba'in, duk term kuma dubu Ashirin da biyar, gashi muma an yi mana ?arin kuWin makaranta, ga komai ya yi tsada, rayuwar ?asar nan sai dai Allah ya sassauta mana, ina jin su Huzaifa ma suna zancen zasu yi sauka, suma kusan

Please Login or Register in order to submit comment