You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kalli Mama, ba tare da ta ce komai ba.

"Saboda tsabar rashin hankali, ki kwanta ki yi fitsari a kwance, ke ba jaririya ba ba 'yar yaye ba" jin abin da Mama ta faWa ne ya sanya ta mi?e zumbur, ta ganta luntsum a cikin fitsari.

Waro ido ta yi ta ce "Na shiga uku, wallahi na zata a mafarki ne, dan Allah kiyi ha?uri"

Mama cikin Sacin rai ta girgiza kai ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, zaki tashi ki fita kije ki gyara jikinki ko kuwa?"

Sannu a hankali ta sauka daga kan katifar, saboda yadda jikinta ko ina yake yi mata ciwo, saboda punishment Win da Yaya Umar ya sanya ta.
Da ta fita tsakar gida da rarrafe ta ?arasa banWaki, ta wanke jikinta ta dawo ta canza kaya, ta jingine katifar tayi kwanciyarta a ?asa.

Har ga Allah, tana jin yadda fitsarin ya matseta, amma ta ji gandar tashi, saboda bacci take ji sosai, ga kuma ciwo da jikinta yake yi, dan haka ta cigaba da baccinta, da ta ganta a banWaki ta zaci a gaskene ta saki fitsarinta.
Tana jin yadda Mama ke ta mita, amma ita ko a jikinta, wani nannauyan baccin ne ma yayi awon gaba da ita.

Da Asuba ma an kai ruwa rana kan Mama ta samu Rumaisa ta tashi ta yi salla, dan sai da ta yi i?irarin haWata da Yaya Umar sannan ta tashi ta yi sallar.
Ta idar da salla Mama tayi mata maganar shirin makaranta, amma ta tura baki ta ce "Ai kina gani jiya mai sunan Baba yana azabtar da ni baki hana shi, ni bani da lafiya, ba zani ba cinyata kamar an mini Worin karaya haka nake ji na"

Mama ta yi mata shiru ta cigaba da laziminta, Huzaifa ne ya fara shigowa Wakin Mama ya gaisheta, suka gaisa ya tambayi Mama mai za'a Wora na karin kumallo?.

Mama ta ce "Bari gari yayi haske, sai a sayo gasara, ka cewa Yasir ya feraye maka dankali, sai a soya"

Huzaifa ya jinjina kai ya mi?e, har zai fita idonsa ya sauka a kan katifar Rumaisa, ya Wan yi turus ya dubi Mama ya ce "Mama ba dai fitsarin kwance yarinyar nan tayi ba?"

"Gashi kuwa kana gani, ai Yarinyar nan sai addu'a kawai".

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, su Balama an yi asarar kunnuwa, ba sai ki saka ta fitar miki da ita daga Waki ba, sai Wakin ya fara wari tukuna, abinka da fitsarin gardiya bana jariri ba, tashi shashasha" ya ?arasa maganar yana zuba wa Rumaisa duka a ?afa.
A gigice ta tashi zaune ta raba ido, tayi zaton Mama ce ta daketa, amma taga Huzaifa a kanta.

"Me nayi maka zaka dakeni?" Tayi maganar a ?ule.

"An dake ki Win, tashi ki fitar mata da wannan katifar daga Waki, mai abin kunya ?atuwa da ke kina fitsarin kwance"

"Ba zan fita da ita Win ba, uban shishshigi ko ina ruwanka, tun da ba a kan ka nayi ba, kuma ruwa ne ya zube ba fitsari nayi ba".

"Au Mama ?arya take yi miki kenan, ba zaki tashi ba?"

Cikin tsiwa ta ce "Ba zan tashi ba"

mi?a hannu yayi, ya janyota ya Wagata, ya ce "Wallahi sai kin fita da katifar nan kin wanke kayan da kika yi tsiyar a kan su". Idan da sabo Mama ta saba da wannan halin nasu na faWace-faWace, gashi Huzaifa ya bawa Rumaisa kusan shekaru shida, amma faWa kamar suna ganin hanjin junansu.

Mama ta sharesu ta ?i ko kallon in da suke, Rumaisa ta dinga turjewa tana kwarara ihu.
Basu yi aune ba suka ga Yaya Umar a tsakiyar Wakin, take suka yi cirko-cirko suna kallonsa.

Cikin kaushin murya ya ce "Meye haka karnuka ne ku?"

Suka girgiza kai a tare.

"Me kai mata take wannan ihun, da idon Mama bai sanya kun daina ba?".

"Fitsari ta yi a kwance, shi ne nace ta fita da kayan"

Cikin mamaki Umar ya kalleta ya ce "Fitsarin kwance kuma? Kina me kika yi fitsari?"

Cikin rauni ta ce "Wallahi Yaya tsautsayi ne, kasa tashi nayi"

"Tsautsayin uban wa? Kwashe kayan ki fita ki wanke ?azamar banza kawai".

Haka ta ja katifar ta fita da ita tsakar gida, ta kwaso kayan da ta yi wa fitsari ta hau wanki.

Huzaifa ya faki idon Yaya Umar ya dinga yi mata dariya.
Duk wanda ya fito tsakar gida ya ga katifar Rumaisa sai ya ce me ya fito da katifar, Huzaifa sai yayi farat ya gaya musu ai fitsarin kwance ta yi.

Tausayinta ne ya kama Usman, ganin yadda take kuka, kuma ba ta saba yin fitsarin kwance ba, ya je ya karSi kayan ya tayata.
Kowa da abin da yake faWa a kan Ruma, wasu na mata Addu'a shiriya wasu kuma na yi mata faWa har da zagi.
Tamkar gidan 'yan mata, haka zaratan samarin nan suka kama aikin gida, wasu na wanke-wanke, wasu shara da Abin karyawa, kan gari ya ?arasa haske, hatta ruwan da Rumaisa zata yi wanka, an dafa ta haWa ta yi wanka.

Haka suka jeru a tsakar gida, tare da Mama suna karyawa, Rumaisa kuwa sai shan kunun take da ?yar tana yamutsa fuska.
Can ta kalli Mama ta ce "Mama Kununa bai ji suga ba, yayi tsami da yawa".

Haushi ya kama Mama ta ce "Amma a gabanki aka zazzage sugan kowa ya Wiba ko? Kuma kin san ya ?are"

Ta ture kofin kunun ta ce "Nifa dama kunun nan gudawa yake sani, gashi bai ji suga ba, ni cikina ma har ya fara ciwo"

Umar kawai ya girgiza kai, Rumaisa ba zata taSa zaman mintuna goma lafiya ba, ba tare da tayi abin da za a yi mata magana ba.
Haidar ya kalleta, ya zura hannu a Aljihunsa ya Wauko Wari biyu ya bata ya ce "Jeki wurin Mamuda ya baki buredi da suga, akwai ruwan zafi sai ki haWa shayi ki sha"

Washe baki tayi, ta ce "Allah dai ya biya da aljanna, gadanga na Mama" ta Wau kofin kununta ta turawa Mama kunun ta ce "Mama ki shanye kunun na bar miki" tayi waje.

***
Da ?yar ta ?arasa makaranta yau, saboda ciwon cinyoyi da take yi, sakamakon horon da Yaya Umar ya bata a daren jiya.

"Ruma hatsari kika yi ne?" Cewar wata matashiyar yarinya sa'ar Ruman, gannin yadda take tafiya da ?yar.

Ta haWe rai ta ce "Me kika gani?"

"Gani nayi kina tafiya da ?yar, kamar wadda ta warke daga karaya"

Cikin gatse Ruma ta ce "Eh, tirela ce tabi ta kaina, da ta wuce na taso na taho"

"A'a Allah ya baki ha?uri"

Duk da yadda jikinta babu daWi, hakan bai hanata faWace-faWace da neman rigima ba, dan idan ba tayi hakan ba ace lafiyarta ?alau ba.

Bayan an tashi ba ta tsaya ko ina ba ta tafi gida, tana zuwa ta tarar da katifarta a tsakar gida kamar yadda ta barta.

"Mama yanzu dan Allah a nan aka bar mini katifata, sai anyi ba?i sun tambayi ba'asi ace fitsarin kwance nayi?"

"Au ba ke kika yi ba, ni nayi kenan?"

Ta ?arasa ta zauna a kusa da Mama ta ce "Haba Mama, kema fa kin san tsautsayi ne, rabona da fitsarin kwance tun ina jairiya, tun ban fi wata huWu ba na daina fitsarin kwance" wani irin kallo Mama tayi mata, jin uwar ?aryar da ta saki.

Mama ta ce "Tashi ki cire Uniform, kiyi wanka ki zo kiyi salla, ki tsefe wannan kan naki, ?azamar banza da yake ban yi magana ba, baki ga dama kin mayar da kai kin tsefe ba, kuma wallahi ya kai gobe in Allah ya kaimu baki gama tsifar nan ba, sai na zaneki".
Hannu ta saka ta shafa kanta, ?anann kitso ne a kanta, a ?alla guda arba'in da Woriya, Mama ta bata kuWi ta je ayi mata kitson hannu guda biyar, saboda ba ta son tsifa, amma ta karSi kuWi a wurin Yaya Usman ta je aka yi mata ?anana.
Ta san yau ko Mama zata kwaWanta ta ta cinye ba zata iya gama wannan tsifar ba, haka nan ta tashi ta je ta yi wanka, ta yi alwala ta saka wasu kayan. Ganin Mama ta tada salla, ta le?a Window ta ga Usman da sallaya a hannu zai tafi masallacin juma'a, ta Wau hijjabinta ta bi bayansa.
Sai da ta fito ?ofar gida sannan ya kalleta ya ce "Ina zaki?"

"Masallaci mana" ta bashi amsa.

"Kin tambayi Mama?"

Ta gyaWa masa kai alamar eh.

Ya ce "Shikenan muje" ya sanyata a gaba suka tafi masallaci.

Mama ta daWe tana yiwa Rumaisa Addu'a bayan ta idar da salla, kullum cikin Addu'a take yi mata, amma tana girma tamkar ana sake turata, ko alamar hankali babu a tare da Rumaisa.

Da suka dawo daga masallaci tana kallon Rumaisa, ba ta ce mata uffan ba, Rumaisa sai raragefe take yi, tana sauraron ko Mama zata yi mata magana amma taga ta shareta.

Ba tare da ta yi tsifar ba, ta ci Abincin ranarta tare da Yaya Aliyu, ya siyo kifi Wauri biyu, ya bawa Mama Waya ya ce gashi nan duka gidan, Wauri Waya kuma suka ci shi da Rumaisa.

Bayan sallar la'asar, ta Wau allonta ta tafi makarantar allo.
Tana zuwa Habiba ta tare ta da harara, tare da sheda mata cewar Sani ya ce sai ya yi mata dukan tsiya, idan ba ta biya shi tayarsa ba.
Tsaki Rumaisa tayi ta ce "To, ya kasheni ya huta mana, tayar banza da ta wofi, shi bai san tsautsayi ba"

A ?ufule Habiba ta ce "Au hakama zaki ce? Ki zo girma da arziki na ara miki tayar, amma ki je ki Satar ko a jikinki?"

"To tayar da kuWi ya saya? Idan da kuWi ya saya ya faWi kuWinta, yayyena su biya shi"

Habiba da ta gama fusata ta ce "Dalla can, uwar meye a gidan naku, banda gayyar maza da tsiya, sai ka ce wata uwar kuka ajiye, har kike a faWi kuWin tayar a biya"

"Ku kun ajiye wata uwar Win ne, da kuna da wani abun ai babarku ba zata sayar da fanke da safe ba" Tayi maganar tana murguWa baki.

Cikin rawar murya Habiba ta ce "Kar ki sake ki zagar mana uwa"

"Ni ban zagi babarku ba, ni dai na san fanke take sayarwa, fanken naku ma mai Shegiyar tsada, ?anana kamar ?uli-?uli, dan ranar Yasir ya ce har kiyashi ya gani a cikin fanken" kan Rumaisa ta rufe bakinta, tuni Habiba ta sha?o hijjabinta, zata rufeta da duka.
Abinka dai mai nema a duhu, balle ya samu a sarari, nan Rumaisa ta zage ?wanji ta tabattarwa da Habiba ita Win ?ANWAR MAZA ce.
Abin takaici da malami a gefe yana biyawa wasu allo suka har?e da dambe.
A fusace ya mi?e ya saka bulala ya zane musu jiki, musamman Rumaisa, tsabar masifarta ya sanya baya son ta a ajinsa, kullum cikin rigima take, ga allonta sai yayi wata ba tayi wani rubutun ba, ga da?i?anci da surutu.

Idan da abin da Rumaisa ta tsana bai wuce duka ba, ta ji zafin dukan bulalar da Malam Ashiru yayi mata? ba kaWan ba, dan haka ta koma gefe tayi shiru tana kuka. Ta rasa meya sanya ya tsaneta haka.

Habiba kuwa da ?awayenta, suka ?udiri aniyar idan aka tashi sai sun naWawa Rumaisa duka saboda suna jin haushinta suma, a kan damben da aka yi a ?ofar gidan mai markaWe ranar Alhamis, gashi ta zagi fanken babar ?awarsu.

Ana tashi cike da takaicin dukan da Malam yayi musu, Rumaisa ta Wau allonta ta nufi gida, sai share hawaye take. Sai dai yau babu tsokana a hanya, babu neman magana?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? saboda bayanta sai raWaWi yake na dukan da malam yayi mata, gashi ba ta warke daga ciwon jikin punishment Win Yaya Umar ba.
Babu tsammani ta tarar da su Habiba a wani lungu suna jiran isowarta.
Turus tayi tana binsu da kallo kamar ba ta sansu ba.

Babu ko War ta cigaba da tafiya tana yin?urin ratse su ta wuce.

Shan gabanta Habiba ta yi ta ce "Ke kin isa ki tafi, ba dai ni kika zaga ba, kika kuma zagi babarmu ba, wallahi yau sai kin gane kuskurenki, kuma wallahi Sani ma ya ce sai kin biya shi tayarsa.
?aya daga cikin yaran ta ce "Ai wallahi yau sai kin daku, haka nima ranar kika zubar mini da markaWe, zaki gane baki da wayo".

Bin su Rumaisa take da ido, sai kurari suke amma an rasa wadda zata kaiwa Rumaisa duka.
Sake yin?urin wucewa tayi, amma Habiba ta janyo Rumaisa ta baya, yaran suka fara kai mata duka.
Tayi kukan kura, ta Waga allonta saukewa Habiba allonta a fuska, wani uban ihu Habiba ta kurma, jin danshi a hancinta.
Tamkar namiji a filin dambe, haka Rumaisa ta zage ita kaWai ta dinga dukan yaran nan, yadda ta dun?ule hannu tana kai naushi, kai ba ka ce 'ya mace bace.

Da ?yar da siWin goshi wani mutum ya rabasu, saboda Rumaisa akwai taurin kai, zuciyarta a bushe ana rabasu tana cigaba da kai duka.
Ta Wau allonta ta nufi gida, tana ta huci, duk da dukan da tayi musu sai dai jikinta duk yayi tsami ita ma. Dama ga jikin nata babu daWi ji

Sai dai kash, tuni wasu daga cikin yayyen yaran maza suka samu labari, suka yi gaba zasu datse Rumaisa a hanya, su zaneta.


Ayshercool
08081012143

[16/06, 9:00 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ?ANWAR MAZA

? ? ? BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Ku yi subscribing YouTube channel Win mu, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Page3

'yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ?arfin namiji da na mace ba Waya bane ba.
Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da wa ake.

tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta dur?usa ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ?wale masa kai da dutse.

Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.

Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ?afarsa ta faWi ?asa, wani dan?o ya Wauko a aljihunsa, ya fara dukanta da shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ?yar a kan ?afafuwanta.

Ta yi kukan kura ta kafa masa ha?ora a kafaWarsa, tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ?ashinsa ya ji ha?oram Ruma, sai ka ce mayya.

Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama da raWaWin jifan da suka sha, ya sanya ta dur?usa ta Wauki takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.
Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar wal?iya haka take she?a da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball Win su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ?artin mazan nan take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a tsakiyar filin ?wallon ta rirri?e shi.

Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.

Ri?eta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma ta?i magana sai ajiyar zuciya take yi.

Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a tsanake ya ce 'Menene?" Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi take.

Haushi ne ya fara kama shi ya ce "Dan ubanki menene, me aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?" Yayi mata maganar a hasale.

Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ?wace mata.
?an shiru yayi sannan ya ce "Amma ina fatan baki yi kukan a gaban yaran ba?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai na ?ara miki".

Cikin sheshe?a ta ce "Ban yi ba"

Aliyu ya ce "Bari na canza kayana muje, Waya bayan Waya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke zancen"

Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball Win su, shi zai tafi.

Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta Sace musu, suka ha?ura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da zasu naWa mata duka, dan tayi musu Sarna sosai.

Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce "Ke amma ba a banza zan je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball Wina da takalmina".

Cikin hanzari ta ce "Eh na yadda, zan wanke maka"
ya ce "To shikenan"

Ya sakata a gaba har ?ofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro yace a kira masa Sani.
Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta fama da kafaWarsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi da manjagara a wurin ba ha?orin Wan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka take, leSe yayi suntum ya kusa haWewa da hancinta, bakin ya?i rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da tukunyar ?arfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.

Sani ne ya fito yana waige-waige, yana neman wanda ya aiko a kirashi, Aliyu yayi caraf ya dan?e shi.
Zazzare ido Sani ya hau yi, Aliyu ya ce "Kai, kaine ka tattaro abokan ka ka daki Ruma ko?"

Cikin fitsara Sani ya ce "Nima ?anwata ta daka, kuma ta Satar mini da tayata".

"Kuma saboda kai mahaukaci ne, sai ka tattaro abokan ka maza su daketa, saboda baka da tarbiyya ko? Meyasa ba ka bari ?anwarta ka ta rama da kanta ba?".

Fizge-fizge Sani ya fara, yana yiwa Aliyu rashin kunya, aikuwa Aliyu ya dinga kifa masa mari, har sai da bakin Sani ya mutu, fuskarsa duk tayi ja. Ya saka shi a gaba zuwa gidan abokansa da suka yi yin?urin dukan Rumaisa.
Duk da irin Sarnar da Ruman ta musu da duwatsu, hakan bai hana Aliyu kama yaran Waya bayan Waya ya zane musu jikinsu ba, sannan ya saka Ruma a gaba yana rarrashinta suka tafi gida.
Ko da suka je gida, yanayin Ruman Mama ta kalla ta ga kamar ba ta da gaskiya, amma ta share ba ta kula ta ba, dan idan ta biye wa halin Rumaisa kullum sai ta daketa.

Da daddare bayan sallar isha'i duk suna zaune a tsakar gida, Rumaisa na ta tunanin me zata ci yau, dan yau ma ma?iyin na ta Mama tayi, wato tuwo, Allah ya sani yau ba ta jin za ta iya cin wannan tuwon, gashi haryanzu ranta a Sace yake a kan abin da ya faru, dan marin da Yaya Aliyu ya yiwa Sani bai gamsar da ita ba, ji take ba zata huce ba sai ta fasa masa kai, ko ta hankaWa shi kwata, ga? kuma tuwon nan da Mama tayi ya sake ?ara mata Sacin rai.

Yasir ne yayi sallama, hannunsa ri?e da leda, duk suka amsa masa, banda Rumaisa da ta yi zurfi a tunani.
In da Rumaisa take ya ?arasa, ya jijjiga kanta ya ce "Ke tunanin me kike?"
HaWe rai ta yi ta ce "Meye kuma na dakar mini kai?"

Yasir ya ce "To kwalba uwar sharri, ni ban dakar miki kai ba"

Tsaki ta yi ta ce "Ai na saba in dai ?arya ce"

Dire mata ba?ar ledar yayi a cinyarta, ya wuce Wakinsu.
BuWe ledar tayi ta kwance, gurasa ce fal ta masu tsire a ciki.

Murmushi ta yi ta Waga murya ta ce "Na gode rabin ran"

Daga Waki ya ce "Ko ba rabin rai ba, tun da na baki abin duniya ba, uwar son zuciya"

Rumaisa ta ce "kai dai Allah yayi maka albarka, kamar ka san ba son wannan tuwon nake ba, tunani kawai nake me zan ci? Wannan tuwon ne yake toshe mini kai bana gane karatu sosai, Allah dai ya biyaka rabin raina "

Murmushi Yasir yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.

Ya gama abin da yake ya fito tsakar gida, zamansa yayi dai-dai da shigowar dodonsu, wato Yaya Umar.
Cikin muryarsa ta ?asaita yayi sallama.
Duk suka amsa masa, ba tare da ya kula kowa ba, ya ajiyewa Rumaisa leda da indomie ya ce "Tashi ki dafa mini" tabbas ba dan Mai sunan Baba ne ba ba zata yi ba, ita a rayuwarta tana son ko aiki zaka sanyata, ka lallaSata shi kuwa mai sunan Baba bai san wannan ba, ya bada umarni a bi kawai ya sani mutum ya ?i kuma jikinsa ya gaya masa.

Haka ta tashi ta je ta kunna wuta ta Wora masa.

Rumaisa na tsaka da aiki, suka ji sallama, kai da jin yadda aka yi sallamar, ka san babu alheri a tare da mai sallamar.
Mama ta amsa tana faWin maraba.

Jin yanayin yadda aka yi sallamar ne ya sanya Rumaisa faWuwar gaba, ta tsaya cak tana sauraron abin da zai biyo baya, dan ta san babu wanda zai aikata abin da za a zo ana musu wannan sallamar a daren nan idan ba ita ba.
Mama tayi wa matar nuni da tabarma dan ta zauna, amma matar ta ce "A'a ba ma sai ma zauna ba, ai abin bana zama bane na"

?an zuro kai Ruma tayi daga Kitchen, domin taga wacece, tozali tayi da Habiba da ?aninta Sani.
Ita ba zuwansu ne ya Waga mata hankali ba, babu tantama ta san ?ararta aka kawo, amma tashin hankalin ta, Mai sunan Baba yana nan.

"Ban sani ba ko ke ce ki ka sanya 'yar ki ta dinga abin da ta ga dama a cikin unguwar nan, saboda tsabar rashin mutunci da rashin ta ido, ta kama mini 'ya ta daka, kalli fuskar Habiba, kuma duk da haka bai isheta ba, ta Wauko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.
Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki ya haye, ya fashe ta ri?e kai sai kuka take, shima Sani kalli fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?" Ta ?arasa maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya yi, leSen sama ya Wage ya kusa danganawa da hancinta, duk dadashi a waje.
Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta ?unshe baki tayi dariya ?asa-?asa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma kamar an naushi fura.

Jiki a sanyaye Mama ta ce "Dan Allah dan annabi kiyi ha?uri, yaran yanzu ne sai addu'a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan nata ba, amma kiyi ha?uri".

Haidar yayi gyaran murya ya ce "Mama nine, su meyasa yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai zasu daka.....

"Rufe mini baki ban tambayeka ba" Mama ta dakatar da haidar cikin tsawa.

Mama tayi ta bawa Babar su Habiba ha?uri, amma ba kunya babarsu Habiba ta ce "An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da suka ga dama, saboda tana ta?amar ita ?anwar maza ce, sai tayi ta isakancin da ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana ma?ota da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini 'ya, shi kuma ya zo ya zage ?wanji a kan Wana".

Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta ya ce "Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban mace kina cewa 'ya'yanta basu da tarbiyya, tana baki ha?uri kina cigaba da ?anan maganganu, kar Allah ya sanya ki ha?ura Win, ki kai duk in da zaki kai ki je ki faWa, kuma ko yau wani ya kuma yin?urin taSa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa duniya ?anwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri"
Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haWe rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.

Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ?an?antar mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.

Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ?ofar Kitchen Win ya ce "Ke kuma fito nan munafuka" aikuwa kamar munafukar ta fito tana sunkuyar da kai

Please Login or Register in order to submit comment