You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Sororo ta yi tana kallon sa, sam ba ta fuskanci in da ya dosa ba, abun da ta iya ganewa kawai shine ?waila, wato wadda ba ta da nono.

"Am talking to you kin tsaya kina kallona"
Cikin tsuke fuska ta ?arasa gaban booth Win, manyan ledoji ne a ciki.
Ya dubeta ya ce "Gasu nan, iman ta ce yadin wanda zaki rabawa ?awayenki, sauran bayanin ban ri?e ba, idan kun yi waya ta yi miki.
Akwai invitations da wurin da za ayi events, sai kayan sawarki".

Maimakon ta ce Ta gode, sai cewa ta yi "Ni ta yaya zan iya Waukar wannan kayan masu nauyi, kuma fa an sai mini kaya a gida, nifa kar ka zo daga baya ka din ga yi mini gori, idan ka san ba da zuciya Waya ka bani ba, ka ri?e abunka, ?awayena za su saka abun da suke da shi" Wagowa yayi ya kalli rumaisa, sai dai maimakon ya ji haushin abun da ta faWa, sai ma ya yaba da yadda take taka tsan-tsan, ita dai kar ayi mata gori, tana da gudun abun wani.

Amma a zahiri, sauke mata kayan ya yi a ?asa, ya rufe booth Win motarsa, ya saka hannu ya Wauko wata babbar ledar a motarsa, Wora mata a kan kayanta ya ce "Idan da wani abun ki saka Aliyu ya kirani" daga haka ya shiga mota ya ja ya tafi.

Gida ta shige ta ce wa su Huzaifa su je waje su kwaso kaya, idan ba haka ba a sace. Sun zata da wasa take yi, ashe da gaske take.
Gwaggo tuni ta zo kano, ita da lawisa, da zaliha, aka baje kayan da takawa ya kawo wa rumaisa.

Iya leshin da zata saka na dinner, ka san ba ?arami bane ba, an Winka shi da jakarsa da takalmi da komai, an haWo mata kayan fitar biki, ga kuma invitations, rumaisa ta yi ta kallon invitation Win tana mamakin wai sunanta ne a jiki.

Ledar nan da ya bata kuwa, babbar envelope ce a ciki wata dubu Wari biyar Win ce a ciki.

Mama ta kalleta ta ce "Rumaisa tambayarsa ki ka yi?"

"Haba mama, to ni ce masa ma na yi, idan ya san zai yi mini gori wataran, ya Wauki kayansa, ni za a sai mini a gida".
Gwaggo ta yi salati ta ce "Shi mijin naki ki ka gayawa hakan?"

Rumaisa ta ce "Mijina kuma taS".

Usman ya ce "Ke fa banza ce, yanzu ya kawo miki wannan uban kayan ki kasa yi masa godiya, saboda ke dai baki da al?ibla?"

Ta yi shiru tana muzurai. "Bari Aliyu ya dawo, ya kira shi a waya, ki yi masa godiya tun da ba ke ki ka nema masa kuWin ba"

HaWe rai ta yi, saboda zuwa yanzu yaya usy yana takura mata a kan mutumin fiye da kima.

Can kuma ta hau murna, tana lissafin ?awayenta da zata bawa ankon da zasu Winka, ga uban kuWi kuma tana gani.

Mama dai shiru tayi tana bin kayan da kuWin da kallo, ita ba tarin kayan alatun ba, fatan ta Allah ya sa rumaisa ta shiga a sa'a ya sanya mata albarka.

***
Bin invitations Win yake da kallo, yana tuna lokacin da yayi auren fari, tun saura wata guda biki ya fara Woki, yana murna yana rabon invitation card, a wannan karon da shi da amaryar bai san wanda ya fi wani anti serious ba.
Rumaisa Mahmud, ya din ga kallon sunan nata, da kuma nasa Adam Sharif Galadima.

Bashir ne yayi sallama a falon, Adam ya amsa masa, ya ?arasa suka gaisa sannan ya zauna ya kalli Adam ya ce "An kammala komai na gidan, zasu iya kai kaya a kowane lokaci".

Adam ya ce "Masha Allah, that's good ina godiya sosai, ina sidi?"

"Na ajiye shi, shima ya sha aiki ya gaji"

"Na gode sosai bashir, zan shiga na je na gani, daga nan sai na Wauki ko mutum biyu a yayyenta, mu je su ga gidan".

Bashir ya ce "Hakan yayi, Allah ya sanya albarka, amma haryanzu fa ba ka fara rabon invitation ba, ko a social media ba a saka ba".

Adam ya Wan yi jimm sannan ya ce "Wallahi Bashir sam bana Wokin auren nan, bana son duniya ma ta san zan yi shi, ni da za a shafa fatiha ma ba wannan events Win da na so hakan, rainon yarinya kawai za a kawo mini"

Bashir ya yi murmushi ya ce "Ka yi ha?uri, ammi ba zata zaSa maka abun da zai cutar da kai ba. Sannan ba zai yiwu ka Soyewa duniya zaka yi aure ba, idan ta fasu aka sani, za a iya yi maka wani sharrin"

"Haka ne, haka zalika idan aka ga Yarinyar da zan aura, shi ma ba zan tsira ba, mussaman idan aka san ita ta zo da Wa na daga hannun ?an bindiga".

Bashir ya ce "Mafita Waya ce, duk yadda zaka yi ka Soye wa duniya cewar ba son auren ka ke yi ba, dole a ga farinciki da Woki a fuskarka".

Adam ya yi murmushi ya ce "Yadda za a ji daWin cewa, saboda na auri yarinya ?arama na kashe matata ko?"

"Ai dama dole sai an faWi wani abu, amma yafi ace ka yi amfani da ?aramar yarinya ka Soye wa duniya laifinka, na kai kashe matarka, ka turasasata ta aureka, dan kar a cigaba da surutu da zargin ya za ayi yarinya ?arama kamarta ta kuSuta da jariri a hannun 'yan bindiga"

Adam ya yi ajiyar zuciya, ya Wan murza goshinsa ya ce "Duniya gidan rikici, Allah ya iya mana".

"Amin ya Allah"

Wayar takawa ce ta fara ringing, ya Wauka ya duba ya ga sunan Aliyu.

Ya Waga ya saka a kunnensa tare da yin sallama, Aliyu ya amsa ya ce "Barka da wannan lokaci, ya hidima?".

"Alhamdilillah, ya taku hidimar?"

"Mun gode Allah, dama rumaisa ce za ta yi magana da kai"

Adam ya ce "Ok, ba ta".

Rumaisa ta karSi wayar, Usman ya sakata a gaba ya tsareta da ido.

Ta karSi wayar ta saka a kunneta, amma ta tsaya tana kallon Usman, ta kasa magana.

Ya daki ?afarta ya ce "Ba zaki gaishe shi ba?"

"Ina wuni?"

Maimakon ya amsa ya ce "Ya aka yi?"

"Gaisheka fa na yi" ta yi maganar a ?ule.

"Ba a yi wa basarake irin wannan gaisuwar, babu ladabi a gaisuwarki, dan haka ko sau nawa zaki yi ba zan amsa ba, ri?e kayarki, ina jin ki"

Rumaisa ji ta yi kamar ta yi zagi, meye aibun gaisuwar ta, idan ba neman bala'i ba.

"Idan kin shirya yin magana, sai ki sake kirana".

"Su yaya ne suka ce dole sai na kiraka na yi maka godiya, na gode, kuma wai kuWin da ka bani sun yi yawa, sannan......"

"Lokacin da ki ka san abu yakamata, ba sai wani ya saka ki ba, sai ki neme ni, yayyenki na ?o?ari wurin baki tarbiyya, Allah ya biya su, kuWi kuma ki zubar" ya kashe wayarsa.

Dungurar da wayar ta yi a ?ufule, ta ce "Yaya usy kalli abun da ka janyo mini"

Dungure mata kai yayi ya ce "Ki ka jawa kanki dai, ke a rayuwar duniya baki iya siyasa ba? Ji yadda ki ke gantsara masa magana, kamar kashi ba tausasa lafazi, ba Wan karya murya, wai ke ma namiji ce irinmu ne? to ko mu muna kashe murya, ranar da na kama malam habu yana waya, kamar ma nutse dan kunya, amma ke kina ta wani shirme.
Ke, tashi mu je Waki, na yi miki bayanin me auren ya ?unsa, in fayyace miki komai in gaya miki, na ga mama ba ta da niyyar gaya miki, daga ita har su gwaggon.

Aliyu ya ce "Kai fa wasu lokutan baka da kamun kai, uban me zaka gaya mata?".

"Komai ma gaya mata zan yi, yo haka za ta je ta zauna masa a gida kamar gardi, idan ka ga tana tausa murya to wani abun take nema, tashi mu je na fayyace biri har wutsiya".

Aliyu da dariya ta ?wace masa ya ce "Mama, wallahi usman ya zama abun da ya zama, zai juyawa yarinya tunani, saboda bashi da kamun kai".

Usman ya ce "Eh, bani da kamun kan, ni ina ma ni za ayi wa auren nan, wai muna zaune ?ar da aka haifa a gabanmu za ta rigamu girma Allahu Akbar wata shekarar sai ta fara ?a ?a kuma".

Aliyu ya ce "Wani irin ta fara ?a?a wata shekarar, kamar wata bishiyar lemo, wannan yarinyar ko nan da shekara biyar albarka"

Wani irin kallo Usman ya yi masa ya ce "Haba, a banza za ku kaita ya din ga bata abinci, yana biya mata kuWin makaranta ko? You don't get sense. Ko kaza dan a cinyeta ake killace ta a? sai mata dusa, kar ka yaudari kan ka".

Aliyu ya ce "kai haba, she's too young for it, and the man is very decent and calm, bana tunanin haka".

Usman ya yi dariya ya ce "Uban calm da decent Win, that thing don't get sense, don't fool yourself, if not ku fasa aurar da ita, hauka ake mutum zai kashe kuWi ya auri ?a ya sakata a gaba yana kallonta, Allah ya sa jaririya ce"

Aliyu ya yi tsaki ya ce "Zaka Sata mini rai "
Rumaisa da ba gane kan hirar take ba, ta din ga bin su da kallo, Usman ya ce? "To Algume, sai kallon bakinmu ki ke, ?ila kin san komai, ki ka yi wani kasa?e da kai".

Aliyu ya ce "A hakan ta san komai? Tana wannan gidadancin".

Usman ya ce "Kuma fa haka ne, to jeki na fasa gaya miki komai, duniya zata gaya miki, Allah ya shiryeki".

"Nuraini, Allah ya baka abun yi na aurara da kai, ina ga daga rumaisa kuma sai kai, tun baka wuce in da nake tunani ba" a guje Usman ya faWa Wakinsu, dan sam bai san mama ta ji hirarsu ba.

***
Jabir ya din ga juya invitation Win, sannan ya kalli Adam ya ce " da gaske Adam saura kwanaki a Waura maka aure, amma ban sani ba?"

"Am sorry, abun ne ya zo cikin gahgawar gaske fiye da yadda na yi zato, sai ha?uri".

Jabir ya sake kallon invitation Win, sannan ya ce "To ita kuma wacece, a ina take? Kamar na san sunan nan".

Adam ya ce "Zaka ganta very soon".

"Da jamil ya gaya mini maganar auren nan, na zaci da wasa yake yi, ashe da gaske ne, Allah sarki samha ina tausayin yarinyar nan sosai".

Adam ya ce "Please, don't raise that issue here, ku daina ganin laifina, ?addara ce ta zo a haka".

Jabir ya ce "Na yadda, ban ce wani abu ba, kawai dai ina jin tausayinta ne, sai dai na yi mamakin yadda har ka nemi aure, har ka samu ban sani ba, yaushe muka fara haka da kai".

"Jabir, this is an arranged marriage, ku yi mini uzuri".

Jabir ya ce "Arranged marriage, to Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu".

"Amin, addu'arku nake bu?ata dama, yanzu ka tashi mu je gidan mai girma turaki, zan kai masa nasa katin, da zai bawa mutanensa, da na jamil da gidan gaba Waya".

Jabir ya ce "Ok, ba damuwa bari mu yi salla tukuna"

Bayan sun idar da salla, suka tafi gidan turaki, kai tsaye sashinsa suka shiga, bayan sun tarar da babu kowa a falon.

Yayi murna sosai yayi addu'a da fatan alkhairi, sannan ya yi wa adam nasiha sosai mai shiga jiki. Sai dai kamar haWin baki suka tarar da mama da Samha, har ma da zainab a falo.
Samha jikinta har tsuma yake da ta ga Adam, ga soyayya ga kuma kishi, ya gaida mama ta amsa masa sama-sama, ta saki jiki ta amsa gaisuwar Jabir.

Su Samha suka gaishe shi ya amsa, ya ajiye wa mama katuna, ya ce "Gashi nan, ammi ce ta ce in kawo miki, na taron wunin da za ta yi, na bawa mai girma turaki nasa".

Da ?arfi Samha ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam wai dama da gaske ne, ta tabatta aure zaka yi?" Ya Waga kai ya kalli Samha da tsoro da kishi ya bayyana a fuskarta, ya jinjina mata kai a hankali cikin tausayawa.

"Shikenan, bakomai na gode " ta tashi ta bar falon. Jikin Adam ya yi sanyi, mama kawa jan tsaki ta yi ita ma, Zainab kuwa cewa ta yi Allah ya sanya alkhairi.

?angaren ammi ma, da ta bawa mummy katin gayyata, masifa mummyn ta din ga yi, wai har ace adam zai yi aure, amma a kasa sakata a cikin lamarin bikin, sai dai ta zo a ?an gayya, saboda ba a mayar da ita a bakin komai ba.

A gidansu rumaisa ma, shirye shirye sun yi nisa. Mai sunan baba ya buga wani invitation Win na Waurin aure, aka rubuta sunan Adam sharif, ba tare da sanya cikakken sunan Adam ba. Ba ?aramin mamaki ?an unguwar su rumaisa suka yi ba, jin za ayi mata aure, wasu suka din ga surutu suna cewa sai ka ce a ?auye, wasu kuma suka ce ta tabbata rumaisa ta yi cikin shege ne, ake son a li?awa wani, kuma aka kasa gane wanene mijin, sai dai hatta wurin da aka rubuta za ayi bukukuwan a wurin ba ?ananan wuri ba ne, nan ma aka yi ta surutun ina suka samu kuWin kama wannan wurare.

Zaman Gwaggo a gidan, ta din ga yi wa rumaisa faWa, tare da nasiha a kan aure, da yadda za ta kula da miji, sai dai sam rumaisan ba ganewa take yi ba, yadda aka sakata a gaba ana sake koya mata girki ya fi komai ci mata rai, a ganinta ana hanata hutawa, girkin nan da karambani ta iya shi, dan tun shekara tara take gwadawa, tun mama tana hanata har ta ha?ura ta rabu da ita.

Samha ta yi kuka kamar zata yi hauka, gaba Waya ji take komai ya fita daga ranta, ko abincin kirki ba ta iya ci, sabuwar soyayyar adam ta dawo mata sabuwa fil, sai dai ta yi alwashin yadda ta zubar da hawayenta a kan sa karo na biyu, daga shi har matar ta sa sai sun WanWana kuWarsu.
Fauziyya ta din ga zigata a kan ta san duk yadda za ta yi, ta cuzgunawa matar da adam zai aura, har da ba ta tabbacin cewa, ta ji an ce auren haWi? ne ba son ta yake yi ba.

Ana gobe za a yi wa rumaisa jeren kaya, Adam ya Wauki Aliyu da Abdallah, zuwa gidan rumaisa, dan su gani daga nan ya basu mukulli.
Sai dai da suka je, Aliyu ya raina kayan da suka saya, da suna ta murna sun yi wa rumaisa kaya masu kyau da yawa, sai dai gidan babba ne sosai.
Sama da ?asa ne, ?asan akwai babban falo, da Wakuna biyu, da kitchen da store, saman bene kuma falo biyu, bedroom uku, da kitchen da dining, kowane Waki da toilet.
Gidan ya tsaru yayi kyau, dan an kashe kuWi wurin yin sa sosai.

Aliyu suka yi ta santin gida, suna yi wa Adam godiya. Sai dai tun da suka koma gida suka sanar da mama, gidan yafi ?arfin abun da za a kai, jikinta yayi sanyi, dan ba dan kar ta nuna halin ?aranta ba, cewa za ta yi idan da ?arami a saka rumaisa a ciki.

Kaf ?an unguwa ba wanda mama ta ce su je yi wa rumaisa jere, ?an uwanta da ?an uwan mahaifinsu rumaisa, sai yayyenta ne suke je suka jera mata abun da ya samu a saman benen.
Gado biyu aka yi mata, dangin babansa suka yi mata ?an waje guda Waya, yayyenta suka yi mata ?an gida, masu matu?ar kyau.

Kitchen Win ta ma babu laifi, a dai ?ar talaka, iyayen rumaisa sun taka rawar gani sosai da sosai, ga kujerunta da labulaye, ga dininga komai dai-dai gwargwado.

?an uwa suka dawo, suka din ga santin gida, suna yi wa mama barka da arziki, rumaisa ta je gidan hutu.

Da daddare Adam ya je gida da shi da su ammi, suka ga jeren da aka yi, ammi ta jinjinawa ?o?arin iyayen rumaisa, ba ita ba shi kansa adam, abun ya bashi mamaki, aka jere mata akwatunanta goma sha biyar a bedroom.
Washegari Adam ya saka aka kawo abubuwan da babu, wanda basu ?arasa ba.

Rumaisa ba ta yadda aurenta za ayi ba sai da satin biki ya kama, dama Aliyu sun shirya football match, a nan cikin unguwa.
Tun da rumaisa ta tabattar da idan aka yi auren barin gidan za ta yi, ta fara koke-koke tana fasa.

Ranar da za ayi bridal shower, daga gidan su adam, aka aiko da mota, aka Wauki rumaisa zuwa gidan kwalliya, ita da ?awayenta, babu ko sisinsu, aka yi musu kwalliya aka wuce da ita wurin biki.

Su Iman tuni suna can, sun sha kwalliya iman kamar balarabiya, da ita da wasu daga cikin famylinsu, da su ?awayenta.

Rumaisa gaba Waya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan ?ar yarinyar takawa zai aura?.

Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ?awayen amarya.

Babu zato babu tsammani, sai ga ?an mazan mama sun dira a wurin, da shigar ?ananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon.

Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata.
Yasir ya ce "TaS, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?"

Ta Wan kwaSe fuska ta ce "Na sani nima, fuskata sai ?ai?ayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan Sata kwalliyar"

Abdallah ya ce "Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau"

Mamaki ne ya kama ?an wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?.

Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin 'yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ?ara gyara cake Win da yake kan table.

Rumaisa ba ta taSa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo.

Gaban table Win ya ?arasa, kusa da iman ya Wauki ?ar ?aramar wu?ar yanka cake Win, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buWe bakinta, ta buWe kaWan ya saka mata a baki sannan ya ce "Happy marriage life ?anwar maza, Allah ya sanya albarka" tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake Win idonta ya cika da ?walla.

Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce "Smile, amarya ba ta haWe rai ranar aurenta"

Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ?o?arin yin abun da zai kwantar mata da hankali.

Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba Waya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a Sangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haWa ido, gabanta ya faWi.

?arshe dai da su aka gama partyn, suka Wauki ?anwarsu suka yi gida.

Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa.

Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira.

Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba.

"Me ki ke jira baki tafi gida ba?"

A tsorace ta ce "Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho".

"Wuce mu tafi" yayi maganar cikin command.

Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi.

Ayshercool
08081012143
What's app only please

*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*


Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce.

Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a Waki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu.
?an uwa sai bawa rumaisa ha?uri suke yi.

"Meye haka?" Ya faWa a kausashe.

Gwaggo ta ce "Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daWi za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi"

"Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya"
Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar Wakan mama.

Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba Waya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake.

***
Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne.
Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta Waga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba.

"Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?"

"Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?"

"Babu Waya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?"

A hasale Samha ta ce 'Look wakili, i don't have time, for all this now allow to rest"

Khalifa ya ce "Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ?ure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ?afarsa ba zaki hango ba, let's join hands together"

Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faWin "Shashasha kawai".

Iman ita kaWai a Wakinta, ta yi

Please Login or Register in order to submit comment