You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wato ta rufewa ƴan gidan baki kada su nemi in da suke. A gefe
guda kuwa ana can ana ta rabon kayan masarufi saboda azumin da za'a tashi da shi
gobe, sarkin hatsi King ya bawa ragamar kula da wannan, talakawa sun wadatu da
kayan abinci kam babu karya, ga tarin dukiya da aka raba masu dan sayan kayan
abinci!!.

YANZU NE CROWN OF POWER WATO (KINGDOM OF POWER) ZATA KAMA DA WUTA, YANZU WASAN ZAI
FARA. ƘAƘA KARA ƘAƘA, GA HOORAIN GA KAMAR, SANNAN GA KING AND COMMANDER A TSAKIYA,
UHM MAI WARWARE WANNAN CAKWAKIYA INA GA SAI MAMMAN KAMRAN KAWAI!!.

🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥
A hankali take salallaɓowa kamar wata ɓarauniya, misalin karfe 6 ne na safe, sanye
take da uniform ɗinta, yau sport wears na school ɗin ta sanya, ta yi kyau a cikin
kayan sosai, tin da take a cikin empeir ɗin bata taɓa shiga cikin kitchen ba sai a
wannan karan, dan haka sai ta nufi kitchen ɗin cikin sanɗa.

Sai dai fa a lokacin da ta isa cikin dry kitchen ɗin nasu sai da ta waro idanu
waje, duniya guda ta gani, gabaɗaya ta zama ƴar kallo, ta ko'ina Robbot ne suke ta
aikin kai komo, aikin dake gabansu kawai suke yi! Ajiyar zuciya ta sauke, almost 10
mins tana tsaye tana karewa kitchen ɗin kallo kafin ta karisa ciki. Babu wanda ya
kulata, nan ta fara ƴan waige waige tana neman ta ina ne wajen girki da wajen
shirya abinci suke!.

Ta ɗauki a kallah good 10 mins kafin ta iya gano wajen girki a ciki. Can ta hango
katafaren trys mai shake da kayan girke girke da ake kaiwa Black Tiger, sun kammala
shirya mashi breakfast yadda yakamata, lokaci kawai suke jira ya cika su kai mashi,
kun san shi ba'a haura lokacinsa kamar yadda ba'a nufara idan lokaci bai cika ba!
Dole sai lokacin ya cika sannan ake zuwa kai mashi kome ya buƙata

Can ta nufa kirjinta na dukan uku uku, tana zuwa tana satar kallon robot ɗin, dan
tana ga kamar zasu ganota. Sai karanta Hasbunallahu wani'imal wakil da kuma lailla
haillah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, ta haɗa da ayar kariya. A cikin
suratul yasin, aya ta 9.
‫َأ‬ ‫ْل‬ ‫َأ‬
‫َنٰـُهْم َفُهْم اَل ُيْبِصُروَن‬
‫ْمَسًّۭد ٰـَف ْغَشْيا‬
‫ًّۭد‬ ‫َوَجَعْلَنا ِم ۢن‬
‫ۢن ًّۭد َبْيِن ْيِديِهْم‬
‫َسًّۭدا َوِمْن َخ ِفِه‬


Ta karanta wannan aya, tana karantawa tana nufar wajen abincin. Kuma wannan addu'a
ya taimaka mata Allah ya datse ganinsu basu ganta ba har ta isa wajen, cikin
gaggawa tasa hannunta ta ciro wani robar ruwa da ta ɓoyesa a wajen cikinta, a
gaggauce ta ɗauke ruwan dake a saman tray ɗin da suka sanyawa Black Tiger ta sanya
mashi wanda ta zo da shi, a miliyan ta bar wajen ta gudu ta koma parlourn.

Wannan aya ta cikin suratul yasin, aya ta 9.
‫َأ‬ ‫ْل‬ ‫َأ‬
‫َنٰـُهْم َفُهْم اَل ُيْبِصُروَن‬
‫ْمَسًّۭد ٰـَف ْغَشْيا‬
‫ًّۭد‬ ‫َوَجَعْلَنا ِم ۢن‬
‫ۢن ًّۭد َبْيِن ْيِديِهْم‬
‫َسًّۭدا َوِمْن َخ ِفِه‬


Aya ce dake makantar da idanun abokan gaba dan cinma mutum, wannan aya Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallama yake karantawa a dik lokacin da mushrikai suka nufosa,
a lokacin da ya bar garin Makka ya yi hijira zuwa Madinah, lokacin da suka shiga
kogo da sayyidina Abubakar wannan aya Manzon Allah (SAW) ya karanta hakan yasa
Allah ya datse idanun mushrikan da suka biyo bayansu, basu samu damar ganinsu ba, a
lokacin da Manzon Allah ya yi tafiya da Nana A'isha ma ayar nan ya karanta suka kau
daga idanun makiya, so wannan aya tana da matuƙar muhimmanci ga Musulmi ya riketa,
musamman a rayuwar yanzu da tsaro ya zama abin da ya zama, so na baku shi sadaka ku
mun addu'a ta alkhari da bakunanku masu albarka!.

Suratul Fatiha da Ayatul Kursiyyu ma suna daga cikin abin da Annabi (SAW) ke
karantawa don neman kariya daga wajen Allah!.

-----------------------------------🔥🔥

A miliyan ta nufi waje rike da robar ruwansa da ta ɗauko a cikin tray ɗin, tsabar
murna sai murmushi take saki. A parlour ta isko Ronnie yana tsaye, yana shirye
cikin hoodie mai bala'in kyau, yau garin nasu akwai sanyi sosai, ga iskar dake
kaɗawa kamar za'ayi ruwan sama, damuna ta kusa dawowa, a wasu yankuna ma ta dawo!.

"Good morning lovely bro". Ta faɗa tana tsananta murmushinta, ji take yi yau
tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha...... A tinaninku me ta saka a cikin ruwan da ta
bawa Black Tiger?.

Hararar ya ɗan dalla mata kafin ya ce. "Ina kika je kuma bayan kin san ina
jiranki". "Sorry my bro, na je wani wajen ne, mu tafi yanzu". "Ba za'a faɗa mun in
da aka je ɗin ba?". Hannu tasa ta rufe fuskarta tana ɗan murmushi mai
ƙayatarwa....... "Me zaki yi da robar ruwa ke da kike azumi yau?". Ya jefa mata
tambayar yana kallan robar ruwan dake hannunta.

"Mantawa na yi da ina azumi na ɗauko har zan sha sai na tina, yanzu dai please
let's go". Ta kai karshen maganar tare da wucewa ta ɗauki jacket ɗinta and school
bag ɗinta, ta miƙa mashi school bag ɗin kafin ta sanya jacket ɗin, tana ƙoƙarin
zuge zip sama ta wuce gaba tana faɗin su je. Bayanta ta bi yana yaba irin kyan da
ta yi yau, ya ce ta fi kyau a cikin sport wear ɗin nan, godiya kawai ta yi mashi
suka wuce izuwa wajen motocin.

Ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce school. Kamar kullum yana sauketa ya dawo gida.
Yana dawowa bedroom ɗinsa ya nufa ya kwanta, dan dama barci bai ishe shi ba, daren
jiya bai samu ishasshen barci ba, dan tin da ta farkar da shi da ihunta da ya koma
bai rintsa ba.

A ɓangaren Black Tiger kuwa, dik karfin tsafinsa Allah ya datse idanunsa sakamakon
addu'ar da Sweetie ta yi, so bai ga lokacin da ta canza ruwan shansa ba, saboda
haka ana kawo mashi abinci kamar yadda ya saba ya ci ya ƙoshi, sannan ya zuba ruwan
nata a cikin cup ya sha ba tare da tinanin wani abin ba.

Sai dai kuma yana shan wannan ruwa sai me? Take a wajen ya fara kwarara amai tamkar
zai amayar da kayan cikinsa, wani irin amai bakinkirin kamar bakar leda mai bala'in
yauki ya fara kwararawa tamkar ba daga cikinsa ya fito ba, gabaɗaya ilahirin
jikinsa ya hau kakkarwa tamkar wanda ake jonawa kantarki, lokaci guda gabaɗaya
empeir ɗin ta yi wani irin azabbabben duhu na ƴan ɗakiku kafin daga bisani ta sake
yin haske, wani irin juyi yaga gabaɗaya room ɗin nasa tana yi mashi, kansa dake
barazanar tarwatse mashi ya dage, lokaci guda idanunsa suka rikiɗe zuwa Jade eye
mai duhu kafin su koma normal.

Wasu irin zaratan jijiyoyi ne suka bayyana sosai a gaban goshinsa, dafe cikinsa
dake tsananin murɗa mashi da hannu guda ya yi, a take a wajen ya zube ƙasa a saman
gwiwowinsa ya hau murkusoso a wajen. Robot dake serving ɗinsa abinci ne ya yi
gaggawar ɗaukarsa cak daga wajen, sai dai kafin ya motsa da shi daga wajen Black
Tiger ya daina numfashi gabaɗaya. Dik wannan abin dake faruwa Ronnie yana can yana
barcinsa, ba shi ya tashi ba sai karfe 1:30 dai'dai, kai tsaye bedroom na yayan
nasa ya nufa, sai dai a lokacin ya iskosa yana barci, bai san ba barci yake yi ba,
tin wannan suma da ya yi Robot ya dawo da shi saman bed ɗinsa shi ne har yanzu bai
farfaɗo ba!

Ronnie ya ɗauka barci ne, so sai ya wuce cikin luxury toile ɗinsa ya watsa ruwa,
sannan ya ɗauro alawala ya fito. Shiryawa ya je ya yi cikin pj's dress ya zo ya
tada sallah domin yin azahar sai ya je ya ɗauki Sweetie a school. First time ɗinsa
da yin azumi kenan yau, amma bai ji wani wahala ba, saboda iska da sanyin da suka
tashi da shi.

Ko da ya idar da sallah bai bi ta kan yayan nasa ba ya fito ya nufi wajen parking
lot ɗinsu. Cikin motarsa ya shiga tare da escort ɗinsu suka wuce ɗaukota. Yau dai
ita kaɗai take zauna abinta tana jiransa, dik ƴan kawayen nata ma sun janye jiki da
ita, saboda sun gano daga BLACK TIGER EMPIRE take, suna bala'in tsoro sai suka ja
baya, ta yi ƙoƙarin nuna masu babu komai, amma sun ki yarda da ita, sun ce ina ta
wuce class ɗinsu!.

Ko da ta dawo daga school bata zame ko'ina ba sai part ɗin Big Bro, dan tasan me
ta yi mashi, so burinta kawai ta zo ta gansa, ta ga abin ya yi aiki ne ko bai yi
ba! Da ta zo taga yana barci sai ta ji babu daɗi, dan sai ta yi tinanin bai sha
ruwan ba, dan haka jiki babu kwari ta juya ta koma bedroom ɗinta. Ronnie ya so
zargan wani abin, amma kuma sai ya kawar da hakan ta hanyar korar shaiɗan.

Wanka ta yi ta shirya cikin malesian gown wanda ya kai mata har ƙasa, ya bi coca
cola shape ɗinta ya zauna ɗas, hp ɗin nan nata ya fito sosai, gata ta ko'ina ta
cika ɓul-ɓul. Kasancewar yau suna azumi babu batun yin dinner, sai suka zauna yin
karatu kawai har zuwa bayan la'asar. Bayan sun yi sallah sai ta ce su wuce church,
har lokacin Black Tiger yana nan yadda yake tin safe, bai farfaɗo ba!.

Church suka wuce ita da Ronnie, amma sai da ya ja mata kunne sosai a kan kada ya
ji bakinta ta yi magana, da okey kawai ta amsa mashi. Ta so su gana da Black Tiger
kafin su tafi, amma ina, bata samu wannan dama ba, dan a tinaninsu barci yake yi.
Addu'a sosai ta yi a lokacin fitarta empeir ɗin, shi ma Ronnie ta ce ya yi addu'a,
ba musu ya yi, dan yasan dik abin da zata ce ya yi to mai kyau ne.

Tin da suka doshi katafaren ginin church ɗin ta ji gabanta yana wani irin faɗuwa,
yana bada bugu dum dum, amma ta cigaba da ambato sunan Allah har suka ƙarisa ciki.
A tare suka sauko ita da Ronnie, yau sai ta saje da kiristocin ma, dan kan babu
ɗankwali, kun san a irin wannan birni dama yaushe zasu samu ɗankwali? Ai babu, so
haka ta fito dan sonta da zuwa church ɗin.

Hannunta Ronnie ya kama suka ƙarisa ciki. Wani irin mamaki ne ya kamata ganin yadda
aka ƙawata ginin church ɗin, an zuba kayan alatu na more rayuwa, ga wasu irin
luntsuma luntsuman kujerun zama mai sa mutum ya mance in da yake, ga wani sanyin Ac
mai ni'ima dake dukan kowa. Can saman stage father church ne zaune saman haɗaɗɗen
kujerarsa mai kama da King seat, yana sanye cikin suit while face ɗinsa da white
glass, daga bayansa wani katan bookshelf mai girman gaske wanda yake shake da tulin
Bibles da littafan tarihi, ga wasu kyawawan flowers decorations a kusa da bookshelf
ɗin, sannan a gaban father church akwai wani katafaren table mai shake da wasu
littattafai da kuma bell na bugawa dan samun attention na mutane!. Gaskiya Church
ɗin ya haɗu babu karya.

A saman waɗan nan haɗaɗɗun kujerun suka zauna, mutanen birnin suna cike sosai, da
alama wannan Church na manyan kai ne, dan dik waɗan da suke ciki jikinsu ya nuna
alamar jin daɗi da hutu!.

Kowa ya natsu tsit sun mayar da hankali a kan Father church wanda shi ma a yanzu ya
shigo, gyaran murya Father ya yi kafin ya fara jawabinsa game da buɗewa da addu'a
tasu ta kiristoci, a cikin addu'ar ne ya ce sun fara da sunan UBANGIJI Jesus.......
Pastor na faɗin haka ta yi gaggawar miƙewa tsaye, with harsh voice ta ce.

"Karya ne, Annabi Isa ba Allah bane, kuma shi bai taɓa ce maku shi Allah bane,
infact shi ce maku ma ya yi ku bi Allah ku yarda da shi manzan Allah ne sai ku
tsira, amma babu in da ya ce maku shi Allah ne, idan kuma akwai shi ka bani hujja,
in dai ka kawo mun in da ya ce maku ku bini nine Allah to na yarda daga yau zan
ajiye addinin musulunci na bi kristanci!!". Babbar magana, tashin hankali kenan!!!
Zaro idanu Ronnie ya yi yana kallanta, dama a ransa yasan dik jan kunnen da ya yi
mata a kan kada ta yi magana in suka zo dik na banza ne, saboda ya san ba'a ɓarna a
gabanta ta yi shiru, sai dai bai taɓa zatan ta haka zata yi fito na fito da su a
bainar nasi ba, tana neman jefasu cikin cakwakiya tasa shi ma a gano ya musulunta,
shi wai ya zai yi da Sweetie ta ɗan rage zafa a kan addini ne? Ya jefawa kansa
tambaya. A hankali ya ɗago ido dan ya saci kallonta.

Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Dik matsoraci baya da'awa, ni bana tsoron dik
wani hukuncinsu, abin da na sani shi ne dole ko a bakin zaki nike zan faɗa cewa
Allah shi ne Allah shi kaɗai, ba zan taɓa yarda da akasin hakan ba, koda ina
tsakanin mutuwa da rayuwa!! Ka dai'na tsoron bayin Allah, ka ji tsoron mahaliccin
bayin ne kawai!!".

Da farko ya yi niyar dallah mata harara, zafafan kalamanta yasa ya fasa, saboda
ta fishi gaskiya.

Kallan tsab pastor ya yi mata kafin ya tambayi who's she?. Ronnie yana ƙoƙarin basa
amsa ta rigasa da cewa. "Mai gaskiya wadda bata goyan bayan karya kuma bata shakkar
faɗar gaskiya a koma ina!! Sannan kuma wadda take rike da fitillah mai haske ta zo
haskaku a cikin duhun da kuke, ta fitar da ku daga cikin duhun kai zuwa hasken
musulunci".

Tin da ta fara magana Black Tiger yake kallanta yake mamakin karfin hali irin na
yarinyar nan, kai ka ji wai mai gaskiya, Sweetie akwai abin dariya wani lokaci,
bilhakki da gaskiyarta ta zage zata yi masu wa'azi, ta ɗaure fuska tamau wai irin
su san ba wasa take yi ba.

Fitarsu ke da wuya Black Tiger ya farfaɗo daga sumar da ya yi, shi ne ya zauna yana
kallansu.

"A cikin injila ta yahaya chapter 1 verses 1 a nan ne Yesu ya ce shi ne Allah!".
Cewar pastor kenan. Da gadara da full confidence ɗinsa ya faɗa, shi nan irin
shegen nan, wai ya kawo hujja...... A karo na biyu Ronnie ya yi mamakin biyewa
Sweetie da pastor ya yi, bai yi tinanin zai biye mata ba, abin da bai sani ba shi
ne, shi maras gaskiya a dik in da yake in dai ka yi magana sai ya biye maka, saboda
yana san wanke kansa ya nuna shi mai gaskiya ne, mai gaskiya na ainahi baya damuwa
da sai jama'a sun yarda da shi, burinsa kawai Allah ya yarda da shi, idan Allah ya
yarda da shi to da izininsa zai sanya jama'a su yarda da shi!!.

Wani irin sanyi Sweetie ta ji ya ratsa zuciyarta, abin nema ya samu, dama so take
pastor ya biye mata ta kaisa ƙasa, har ita zai kawowa wani hujja, muje zuwa. Gyaran
murya ta yi kafin ta fara da cewa.

"A'a, cikin Bible gabaɗaya babu in da aka ce Annabi Isa (A.S) shi ne Allah!!.
Akwai wurare da ake nuni da cewa shi yana da matsayi na musamman, amma a cikin
littafin Injil (Bible) dayawa daga cikin maganganun Annabi Isa (A.S) suna nuna cewa
shi bawan Allah ne kuma manzon Allah. Dik kuma zan kawo maka hujjoji masu karfin da
zaka gamsu idan ka buƙata".

Binta da kallo gabaɗaya jama'ar cikin church ɗin suka yi, shi kansa pastor kaman ya
ɗan tsorata ne ko yaya ne, sai ya ce. Ta fitan mashi a church yanzun nan. Gyarawa
ta yi ta zauna kafin ta amsa da babu in da zata je har sai ta gama amayar da abin
da ya kawota, babbar magana kenan. Rai a matuƙar ɓace pastor ya bada umarni ga
securitys su zo su fitar da ita. Kan kace me wasu shirga shirgan securitys sun
shigo cikin zafa da nufin sun zo su ɗauketa su yi waje da ita.

Aikuwa suna zuwa Ronnie ya miƙe tsaye, da wani irin mugun kallo ya bisu wanda yasa
suka ci wata uwar birki ba tare da sun shirya ba, kun san gabaɗaya birnin tsoron
Ronnie suke ji, shi ne zakarar da ya buge kowa, dan haka suka kasa motsawa daga in
da suke tsaye, saboda tsoronsa. Hararar ya bisu da shi kafin ya nuna masu hanyar
fita da hannunsa ɗaya, ba tare da ya yi magana ba, ai a miliyan suka juya suka
fita. Ta witsiyar ido ya bi pastor da kallo kafin ya tsayar da kallansa a kan
Sweetie, cikin natsuwa ya ce. "Kina da hujoji a kan maganarki ne?". Ya yi mata
wannan tambaya ne ba dan bai san tana da hujjijo ba, sai dai ya kare kansa, irin ya
nuna shi bai san komai ɗin nan ba, kuma yana yiwa su pastor kwaɗayin Rahmar Allah,
so zai so ta cetosu daga duhun kai izuwa haske.

Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas tana da hujjijo kafin ta ce. "Ina da hujjijo
kwarara sosai Ronnie". "To kawo mana su". Ya faɗi hakan tare da komawa ya zauna.
Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, hankali ya kwanta, buƙatarta ta biya,
rai ya yi sanyi, abin nema ya samu, dan haka cikin natsuwa ta cigaba da cewa.

"A cikin Injila ta yahaya chapter 17 verses 3 yana rubuce cewa. Kuma wannan ita ce
rai madawwami (Allah kenan), su san kai Allah wanda kai kaɗai ne na gaskiya, da
kuma wanda ka aiko Yesu Almasihu wato Annabi Isa kenan"
"Wannan yana nuna cewa Allah shi ne kaɗai na gaskiya, kuma Yesu (Annabi Isa)
manzonsa ne. In bai yarda ba ya duba cikin Bible ɗin yanzu zai ga hakan, dan haka
Annabi Isa dai bai ce ayi bautarsa ba, kuma dik mai kaunarsa na gaskiya ma ba zai
bauta mashi ba!!".

"Kazalika cikin injila ta Matiyu chapter 26 verses 39 tana nan a rubuce lokacin da
Annabi Isa (A.S) ke addu'a yana cewa. Ya UBANGIJINA ka ɗauke mun wannan kofin, amma
kada nufina ta cika, sai da sanka".

"Wannan yana nuni da cewa Annabi Isa yana da UBANGIJI da yake roƙonsa dik abin da
yake da buƙata, ba shi ba ne ALLAH. Sannan a cikin injila ta Markus chapter 12
verses 29 Annabi Isa (A.S) ya ce. Ku Isra'ilawa ku ji UBANGIJI ALLAHNMU UBANGIJI
ɗaya ne tak da bashi da abokin tarayya. Wannan ya bayyana cewa ALLAH ɗaya ne, ba
Annabi Isa ba, dan da bakinsa ya ce ALLAH ɗaya ne kuma ba shi bane!!".

"To amma me yasa wasu Kiristoci ke cewa Annabi Isa ALLAH ne?". Ta jefawa kanta
tambayar da tasan babu mai bata amsa, dan haka sai ta bawa kanta amsa da cewa.
"Akwai wasu wurare da aka fassara su da cewa Annabi Isa yana da wata alaƙa ta
musamman da ALLAH, kamar Yahaya chapter 1 verses 1 da ka ambata a baya". Ta yi
maganar idanunta a kan pastor, dan shi ya ambaci cewa a shafin farko na Injila ta
yahaya Annabi Isa ya ce shi ne ALLAH, dan haka sai ta ce. "A farkon shafin layin
farko tana nan a rubuce cewa. Abu kalma ce, kuma Kalmar tana tare da ALLAH, Kalmar
ita ce ALLAH...........Waɗanda suke da ra'ayin Trinity, wato masu ra'ayin cewa
UBANGIJI uku ne, Uba, ɗa, da ruhu mai tsarki, to su sukan yi amfani da irin
waɗannan ayoyi su kafa hujja kan cewa annabi Isa ne ALLAH. Amma a cikin Bible
gabaɗaya, babu inda Annabi Isa ya ce shi ne ALLAH, ko ya umarci mutane su bauta
masa, sannan kai kanka ka sani har yanzu akwai saɓani tsakanin masu tafsirin Bible
kan wannan batu, kuma da yawa daga cikin Kiristoci da kansu sun yarda cewa an canza
Bible tun asali, kawai san zuciyarsu suke bi kamar dai kai ma, ina da tabbacin
kasan an canza Bible. Wannan yasa musulmai suke da aqidar cewa Annabi Isa (A.S)
bawan ALLAH ne kuma manzonsa, ba ALLAH ba, saboda ku kuna da Bible sun fi kala
goma, mu kuma Alqur'ani guda ɗaya ce, tin ranar da aka saukar da ita har yau babu
ko wasali ɗaya da aka canza, bama wanda ya isa ya canzata!! Saboda kalamul lah ce
ita!!". Ta kai karshen maganar tare da dakatawa tana mayar da numfashi.

Ronnie ya ji daɗin wannan batu, abin ya yi mashi sugar sosai, ya sanyaya ransa, har
wani ajiyar zuciya ya sauke, ya ji kwarin gwiwar zai tsayawa Sweetie tin da ta faro
wannan batu ta dire aya, ta yi mashi kaca kaca da pastor yau.

Sai dai basu ankara ba sai gani suka yi pastor ya harbo bell dake gabansa sai kan
gaban goshin Sweetie ya sauƙa, take ya fasa mata goshi sai jini, cikin tsawa da
kakkausar murya ya ce. "Yarinyar banza, ni zaki zo kina kalubalanta? Yaushe aka
haifeki da har zaki ƙaryata littafanmu? Wacece ke a duniya? Littafan da suke tun
tsawon shekaru aru-aru? Ke har kin isa in

Please Login or Register in order to submit comment