ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace ba dole ta zama farincikin Ronnie ba tun da ta bashi kalmar shahada,
ta janyo shi cikin haske, dole ya yi farinciki idan yana tare da ita.

"Please mana our big bro, nasan baya cikin yarjejeniyarmu, amma kuma ai akwai
batun kada ka bari wani abin cutarwa ya zo kusa da mu ko?". Ta faɗa tana ƙoƙarin
kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata. "Wannan ai ba abin cutarwa bane, da na
cutarwa ne Ronnie ba zai ɗaura maki ba". Ya yi maganar tare da sakinta. Yana saketa
tamkar wadda aka turo haka ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa again......
"Allah abin cutarwa ne shi ma". Cikin muryar kuka ta yi maganar.

Banza da ita ya yi, bai da niyar kwance mata, ɗan rainin wayo dan bai gaji da
kallan madarar kyan da Allah ya yi mata ba, sai ya fake da cewa ai ba shi ya ɗaura
mata ba, dan haka ta nemo Ronnie ya kwance mata, har da dagewarsa irin da gaske
yake yi shi fa. Kamar zata yi kuka ta bar jikinsa ta fara laluɓar hanyar fita.
Allah ya bata nasara ta samu ta fito, idanunsa a kanta bai hanata ba, haka ta fara
laluɓe har ta isa wajen stair case, ga ruwan dake zuba a jikinta, bata san ta isa
wajen ba, tana ɗaga kafa ta sauke sai ta tafi gabaɗaya ta yi ƙasa, tin daga kan
step na farko ta yo kasa har karshe, dik kuma yana ganinta bai taimaka mata ba, bai
kuma yi amfani da magic wajen tsayar da ita ba, ya barta ta isa ƙasa dik ta bubbuge
jikinta, har ta dan ji ciwo a hannu. Azaban da ta ji ne yasa ta saki ihu mai sautin
da ya ja hankalin Ronnie dake zaune saman sofa yana shan tea mai zafi sosai.

Da gudu ya ajiye cup ɗin a saman table dake gabansa ya nufota yana tambayarta
lafiya kuwa. Kuka ta saka mashi kawai ba tare da ta yi magana ba, duƙawa ya yi ya
ɗauketa cak ya yi waje da ita, har ya canza kayansa izuwa na sport, sarkin san
wasanni ba. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma da ita, a nan ya kwance hanki ɗin ya yi
ta rarrashinta har ta yi shiru, sannan ya ce ta je ta yi wanka ta canza kaya, ba
musu ta bi umarninsa. Yau da ta yi wanka irin shigar mutanen birnin ta yi, wato
umbrella gown mai maɗauri a tsakiya, ta yi kyau sosai, gashin kanta saboda samun
kwanciyar hankali ya kara tsawo sosai, har ya kusa zarce mazaunanta, ya kuma kara
tura kala sosai. Kwace saman bed ta iskosa yana kallan chandelier ɗin ɗakin nasa, a
gefensa ta zauna, cike da nuna kauna ta ce. "Lovely bro ina san zuwa church ɗinku".

Zaro idanu ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. "Mezaki je ki yi?". Ya yi
maganar tare da miƙewa zaune suna fuskantar juna. "Babu kawai ina san zuwa ne in
gani". Shiru ya ɗanyi kafin ya ce. "To gobe idan kika dawo daga school zamu je a
tare by 4:00 ko 4:30 haka". Sosai ta ji daɗin amincewarsa, cike da murna ta matsa
ta sumbacesa a kumatunsa, siririn murmushi ya saki kafin ya ce. "Kin san wani abu
sister?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata sani ba. Tana ta sakin ƙayataccen
murmushi.
Kashe murya sosai ya yi kafin ya ce. "Ina san ganinki a tare da big bro, kuna
kyau sosai, dan Allah ki rinƙa kasancewa a tare da shi, kinga yanzu kin fara canza
mana shi ko?". Shiru ta ɗan yi alamar kamar bata ji daɗin maganar ba, sai kuma ta
saki siririn murmushi kafin ta bashi amsa da. "Ina fatan ya sauya, ya canza ya zama
musulmi, ina yi mashi kwaɗayin rahamar Allah sosai". Ɗan zaro idanu Ronnie ya yi.
"Kina nufin ba kya san yayana? Dik abin da kike yi mashi kawai kina yi ne dan ya
musulunta?". Jinjina mashi kai ta yi alamar ba shakka haka ne, sannan ta ɗaura da
cewa. "Ko kaɗan babu soyayyarsa a rai'na, soyayar Kamran ce kawai a raina, and na
fi jin sonka a rai'na ma sama da yayanka, ina jin yayanka tamkar ɗan uwana ne na
jini wanda ina ga hakan ce tasa bana jin sonsa na soyayya a rai'na, kasan wani
abu?".

Kasa bata amsa ya yi ko ya motsa daga in da yake, ya kafeta da ido mamaki kamar ta
kashe shi, shi dik tinaninsa tana san yayansa shiyasa yake tayata yakin neman
soyayyarsa, bai san ita wanda take so ma daban ba ne...............Dik da bai amsa
mata ba hakan bai hanata cigaba da yin maganar da take da niyya ba. "Yayanka ya
haɗa dik abin da kowacce mace zata so a duniya, nasan kasan da cewa komai isar mace
idan ta gansa sai ta faɗa mashi, amma ni kaunarsa nike a matsayin ɗan uwa na jini
haka, soyayyar Kamran ne kawai a rai'na".

Shiru ya yi na almost 3 mins kafin ya nisa, sannan ya saki ƙayatattcen murmushi.
"Sister a labarin da kika bani kin ce mun Kamran ma ba musulmi bane
ko?"............. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "To meyasa baki taɓa tsayawa ki
jajirce a kansa lallai sai ya musulunta ba? Ko shi baki yi mashi kwaɗayin rahamar
Allah ne?"....... Shiru ta yi kamar mai tinanin abin faɗe, da alama ya ɗaureta da
magana.
"Baki da amsa ko? Dama ai ba zaki iya bani amsa ba, amma ni zan baki amsa, dalilin
da yasa kika tsayawa big bro kika zage kina san ganinsa a cikin ni'ima ta Ubangiji
ba komai bane face so, shi ne wanda kike yi wa so na gaskiya, dik wanda zaki so to
a bayansa ne........." A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "No Ronnie, ko ɗaya
ban taɓa san yayanka ba, in dai kaunarsa". Jinjina kai ya ɗan yi. "Kin san soyayya
ne ma da zaki iya banbanta wanda kike kauna da wanda kike so?". Ya tambaya kamar
shi ma ya san me so ɗin, da dalilin ɓacewar Floris daga garesa ne fa ya fara
fahimtar me soyayya, amma har ya fara zaƙewa zai nuna shi ya sani.

Da sauri ta jinjina kai kafin ta amsa da. "Niko na san soyayya, soyayya ai ayoyi
gareta a cikin Alqur'ani mai girma, idan ka ɗauki suratul Ali Imran sura ta uku aya
ya 31 da ɗaya, wanna aya tana magana ne a kan ainahin soyayya ma, wato soyayyar
Allah ga bayinsa, sai kuma cikin suratul Ar rum, sura ta 30 aya ta 21, wannan tana
magana ne a kan soyayyar ma'aurata wato mace da namiji, kazalika cikin suratul
ma'ida, sura ta biyar aya ta 42, nan ma magana ce kan kauna, cikin suratul Maryam,
sura ta 19 aya ta 96, Allah yana magana a kan soyayyar da yake sakawa a tsakanin
mumunai maza da mata kenan, soyayyar da ta fi kowannen wato soyayyar Allah, Allah
ya ambaceta a cikin suratul Ali Imran, sura ta uku aya ta 159, kaga kuwa ni ce na
san soyayya ciki da wajenta".

To dik wanda ya ce soyayya karya ce ya yi karya, dan soyayya ayoyi gareta a cikin
Alqur'ani, so ba karya bace wlh, ni ba dan bani da isasshen fili ba ai da na baku
tarihinsa amma ba komai ku tara a littafina na gaba idan Allah ya kaimu da rai da
lafiya!.

Jinina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Dik na yarda kin karanta waɗan nan,
amma baki iya banbanta so da kauna ba, ki yarda kawai". Hararar ta dalla mashi
kafin ta ce. "A'a ba zan yarda ba, ni Kamran nike so, babu mai canza hakan". Ya
fahimci yarintar ce ta motsa, sannan kuma a gaskiya bata san so da kauna ba abu
guda bane, sai ya ce bari ya yi mata dabarar fifikon shekaru. "Na yarda Kamran kike
so, kuma zan tayaki yakin nemansa, yanzu abu ɗaya zaki yi mun sai nima na zage mu
nemo Kamran". Yana magana yana lumshe idanu alamar barci yake ji. Cike da zumuɗi ta
ce. "Faɗi abin da kake san in yi, matsawar bai saɓawa shari'a ba zan yi".

"So nike ki ƙara kusanci da big bro, ki rinƙa matsa mashi a kan wasu abubuwa
har zuwa mu yi nasara, da zarar mun yi nasara big bro ya musulunta, to zamu shiga
neman Kamran, da taimakon Allah nasan ba zamu sha wahalar nemansa ba zamu gansa".
Ya kai karshen maganar yana komawa ya kwanta, dan har gyangyaɗi yana ɗaukarsa. Cike
da matsuwar san ganin Kamran ɗinta ta amsa da ta amince, kuma zata yi iya ka yinta
ko da kuwa zata wahaltu, amma tabbas zata zage. Sosai ya ji daɗin hakan, bai sake
furta word ba ya lumshe idanunsa, kan kace me barci ta yi awon gaba da shi. Ita
kuma miƙewa ta yi ta sauko ƙasa daga saman bed ɗin, ta nufi wajen books set ɗinsa,
wani katan Markus Bible ta ciro tare da wani notebook and pen, saman dining table
ta koma ta zauna tare da fara dube duben abin da take da buƙata.


AFTER ONE DAY.

Zaune Ronnie yake a saman dining dake cikin parlournsa, ya tasa haɗaɗɗun kayan
abinci a gaba yana yin breakfast, yana ɗan motsa baki da small chop yana latsa
wayarsa, baya san cin abinci ba tare da ita ba, jiranta yake yi ta zo su ci,
shiyasa hankalinsa gabaɗaya yake a kan wayar yana ɗan motsa baki. Ya yi bala'in
kyau cikin tsantsararren shigarsa na army green shirt and black trouser, ya sanya
p-cap a kansa, while kafafunsa suna cikin Crocs launin army green, kyakkyawan white
hairn nan nasa ya sha gyara sai kamshi yake tashi yana wani sheki, yau dai babu su
earing sosai a kunnensa, dan ya fara rage sanyasu, ya ma cire pil na wajen lips
ɗinsa, kazalika ya cire na gaban goshinsa wajen gerarsa, kuma yanzu ya dai'na raba
gerarsa gida biyu ta hanyar aske dogon layi a tsakaninsu da yake yi, dik wasu
abubuwa da basu dace ba ya bar yi, saura sanya ɗankunnen ne kawai, shi ma yanzu
guda ɗaya yake sakawa, ita ma yana fatan dai'nawa, kun san sabo, idan ka saba da
abu yana da wuyar bari, shiyasa

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Ya yi nisa cikin abin da yake yi sai ji ya yi an rufe mashi idanunsa ta baya. Ɗan
turo baki ya yi kafin ya ce. "Lovely sis zafa ki yi latti, kinga dai almost 7
yanzu"........ Kausasa murya ta yi, ta kwaikwaiyi muryar gardawa wai dan ta nuna
mashi ba ita bace, ko iya abin ma bata yi ba, ga murya irin na yara, ta zage ta
faɗaɗa makogoro wajen cewa. "Wannan ba lovely sis ɗinka bace, aljana ce". .......
Siririn tsaki ya ja tare da sakin cool murmushi kafin ya ce. "Ai bama ki iya abin
ba, da wani muryarki kamar na mage, zo nan ki ci abinci kada ki ɓata mun lokaci
hai". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya ɓanɓare hannunta daga face
ɗinsa, sannan ya fisgota ta dawo ta gabansa.

Ɗaure fuska ta yi tana turo baki, ita a dole ya ɓata mata rai tun da bai bari ta
razana shi ba. Tana shirye cikin uniform ɗinta, yau ta sanya lips balm mai ɗan
launi mai kuma kyalli, wanda hakan yasa kyallin ya kara kawata dark purple lips
ɗinta, sai wani sheki yake yi yana ɗaukar idanu, shi kansa Ronnie sai da zuciyarsa
ta amsa ganin laɓɓanta. Sake hannunta ya yi tare da nuna mata saman nata chair ɗin
yana faɗin ta zauna ta yi breakfast sauri sauri ya je ya kaita school.

Zama ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba, wai ta yi fushi da shi. Cikin fushi ta
ɗauki chopping stick tare da matsar da plate mai shake da Chinese spaghetti mai ɗan
faɗi faɗi haka, an zuba girki a wannan waje, ga wasu dakwalan cinyoyin ƙosassun
kaji, sai tashin kamshi yake yi. Yana ta fitar da tiriri kaɗan kaɗan ta sanya
chopping stick ɗin ta fara ɗebowa, kaɗan kaɗan ta fara kaiwa ɗan bakinta, amma da
yake spagh ne har ya ɓata mata gefe gefen bakinta zuwa kumatunta.

Shi ma janyo nasa plate ɗin ya yi tare da ɗauko chopping stick ɗinsa, a hankali ya
nannaɗo spagh ɗin tare da kaiwa ɗan bakinsa yana ɗaura phone ɗinsa a saman table
ɗin. "Lovely sis today food was so delicious". Ya faɗa ba tare da yasan fushi take
yi da shi ba........ Shiru bata amsa mashi ba, sai ma cigaba da danna spagh a baki
take yi babu kakkautawa, wai tana turawa dayawa ne dan ya san tana jin haushi, shi
kuma bai gane ba. Jin bata amsa ba yasa ya sake maimaita maganarsa tare da dawo da
kallonsa a kanta. Tamkar bata a wajen ta yi banza da shi. Cike da mamaki ya ce.
"Lovely sis are you okey kuwa? Am talking you refuse to answer me, why?". Cikin
sanyin murya ya yi maganar haɗe da alamar damuwa, dan bai ji daɗin hakan ba.

Banza ta yi da shi tana danna spagh dole dole, tin na bakinta bai kare ba
zata danna wani dan ya fahimci cin takaici take yi.... Shiru ya ɗan zuba mata idanu
na ƴan sakanni kafin ya iya fahimtar fushi take yi da shi. Ɗan siririn murmushi ya
saki, ya cigaba da kallonta har sai da ta danna spagh a bakinta tana ƙoƙarin
nannaɗo shi ta tura gabaɗaya cikin bakinta sai ya yi saurin sanya hannu ya riko
bayan wuyanta tare da juyo da face ɗinta ya zamana suna kallon juna, bai bari ta
nannaɗe spagh ɗin ba yasa ɗan bakinsa ya fara nannaɗe mata yana ci, ƙoƙarin cinye
kayanta ta yi da saurin shi ma ya yi zafin namar ci sosai, sun shagala da rije
rijen cinyewa basu ankara ba sai ji suka yi bakinsu ya haɗe da juna, dan sun cinye
spagh ɗin gabaɗaya har sun iso junansu ba tare da sun sani ba.

Zaro idanunta waje ta yi tana kallonsa, shi kuwa cikin salo ya kashe mata ido guda
kafin ya ɗan janye laɓɓansa baya kaɗan yana sauke ajiyar zuciya. Sorry ya furta
tare da yunƙurawa zai miƙe ya bar wajen. Cikin sauri ta riƙo hannunsa, a hankali ya
juyo da kallonsa a kanta, marairace fuska ta yi kafin ta ce. "Ni ce na yi maka
laifi, for give me please". Jinjina mata kai ya yi haɗe da cewa. "Babu komai, ci
abinci da wuri mu tafi". Ba musu ta saki hannunsa ta ɗauko chopping stick ɗin ta
cigaba da nannaɗo spagh ɗin. Komawa shi ma ya yi ya zauna haɗe da ɗauko nasa stick
ɗin suka cigaba da ci a tare.
"Lovely bro rufe idanunka in baka wata bazata". Ba musu ya rufe, ɗauko katan
cheeseburger da ta fi karfin bakinsa ta yi. "Open your mouth". Ta faɗa tana
kallansa. Bai yi tinanin komai ba ya buɗe bakin nasa, dakarkarewa ta yi ta danna
mashi burger a bakinsa tare da watsawa da gudu ta yi sama tana faɗin. "Gobe ma ka
sake idan na tsorataka kada ka tsorata"..... Ai sai da ya ji numfashinsa ta ɗauke
na wucin gadin, da kyar ya iya ciro burger daga bakinsa, dogon numfashi ya ja tare
da saukewa a hankali, da gudu ya miƙe ya bi bayanta dan ya kamata ya rama. Kamar
wasu ƴaƴan mage haka suke, basa zama waje guda basu tsokani juna ba, musamman ma
ita, kullum sai ya tsokanesa!.

Bedroom ɗinsa ya fara leƙawa, bata a ciki, da sauri ya wuce bedroom na yayansa,
yana ɗaure fuska a kan yau ba zai kyaleta ba. Sai dai ko da ya shiga bedroom na
yayan nasa ma bata a ciki, babu ma kowa, ya ɗan yi mamakin ganin ba kowa. Har
toilet ya leƙa bai ga kowa ba, da sauri ya fita ya haura sama izuwa gym area nasu
ko ta maƙale a can. Sai dai bata a can ma, yawon nemanta ya hauyi, ton yana nemanta
cike da burin ya ganta ya ɗauki fansa, har ya fara nemanta cike da damuwar ina ta
shiga?. Wasa wasa har tsawon good 20 mins yana nemanta bai ganta ba. Da sauri ya
sauko ƙasa dan ya duba harabar empeir ɗin, hankalinsa ya tashi sosai a yanzu kam,
dan yasan empeir ɗin yana da wajaje daban daban, akwai wurare masu haɗari, akwai
kuma wuraren da idan ta shiga tabbas ba zata iya fita ba, zama ta iya rasa ranta
idan ta shiga, hankali tashe ya bazama nemanta.

A dai'dai wannan lokacin ita kuwa tana wata duniya ta daban, dan a lokacin da ta
gudu ta haura sama, bedroom na Black Tiger ta nufa, saboda ta haɗa da sallama dik
ta yi mashi na zata wuce school. Sai dai da ta shiga bata samu kowa a cikin bedroom
ɗin ba, sai ta gudu balconynsa dan ta ɓuya a can, nan dai ta ga kamar a nan ma zai
iya ganinta, hakan yasa ta dawo ta shiga dressing room, kun san nan akwai drawers
da sauransu, so zata samu wajen laɓewa ba zai ganta ba. Sai dai kash, tana shiga
suka ci karo da Black Tiger yana sanya kaya, yana tsaye a ta kusa da kofa wajen
shoe set ɗinsa dake shirye cikin wasu mahaukatan glasses masu tsadar gaske, wani
irin white light ne a cikin glases ɗin nan masu masifar haske da suka haskaka
zafafan shoes ɗin nasa, yana san ya yi selecting na wanda zai sa ne, daga shi sai
B- short wanda ko haɗaɗɗun cinyoyinsa bai gama kaiwa ba a jikinsa, tamkar dan iya
penis ɗinsa aka yi short ɗin, Lion check ɗin nan nasa a buɗe, ya ɗaura wani small
white towel a kansa, da alamar yana tsane ruwan dake gashin sa ne.

Aikuwa tana shigowa ta sauke kallanta a kansa, while shi ma ya juyo da kallonsa a
kanta slowly, ya ji motsi ne yasa ya ɗago. Ai sumar tsaye ta yi, a zahiri kamar shi
take kallo, amma kuma ina hankalinta ya yi nisa, kamar wadda aka daskarar!. Shi
kuwa kallonta ya fara yi tin daga kan santala santalan cinyoyinta da suke tamkar
madara har izuwa saman kirjinta da yanzu suka fara cika pam sosai, yanzu girma ya
fara zuwa, matasan tula tulanta sun fara ciccikowa sosai. Ga yanayin uniform ɗin
nasu sai dai shiru, kun san ba addini ne da birnin ba, mini skirt ɗin nata ko gwiwa
bai rufe ba, a dai'dai tsakiyar tsala tsakan laps ɗinta ya tsaya, daga sama rigar
ma dai sai shiru, dan ya kamata sosai, har kana iya ganin shatin tula tulan, sai
dai ita tana sanya jacket na school ɗin dan suturta kayanta, amma yanzu dai bata
sanya ba, saboda basu kai ga tafiya ba, dama idan zasu tafi ne take sakawa. Jacket
ɗin yana parlor tare da school bag ɗinta!.

Wlh yau dai sai da ƙwaƙwalwarsa ta amsa, barema yadda yana skin ɗinta wajen
cinyarta, tamkar ka latsa jini ya fita, tin ainahi dama babu abin da yake mugu
mugun tafiya da shi sama da golden white hair ɗinta da idan ya sha gyara yake wani
irin kyalli na musamman, sai ga shi yau ta sake shi ma bata ɗaure ba, dan bata
kammala shirin tafiya ba, sai zata tafi school zata ɗauresa.

Me kuke tinanin zai faru da dikkansu suka bushe da kallan juna? Waye zai fara
dawowa cikin hayyacinsa?.
🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥


Kiran farko na asuba ta farkar da shi daga ɗaddaɗar barcin da yake yi. A hankali ya
waro fox-s eyes ɗinsa da suke jajir alamar barci bai ishe shi ba. Yunƙurawa ya yi
ya miƙe zaune, jikinsa dik ciwo yake yi mashi tamkar ba lafiya ba, slowly ya waigo
da kallansa ta side da take kwance. Ga mamakinsa sai ya ga babu kowa a wajen,
wayam, ina ta yi to? Ya gefawa kansa tambaya, sai ya ji tamkar a mafarki ne dama ya
kawota bedroom ɗinsa ba a zahiri ba. Miƙewa ya yi jiki ba kwari ya nufi toilet.

Jim kaɗan ya fito ɗaure da white towel a kugunsa. D-room ya wuce domin shiri. Sanye
da white arabs jallabiya mai bala'in kyau ya fito, sai ya kara fita a ainahin arabs
guy ɗin nasa, ya yi kyau sosai, sai tashin kamshi yake yi, yau dai kamar yana ji da
mutumci, dan da ya gabatar da sallar rakatainil fajir sai ya ɗauko alkyabba mai
shige da na sarauta ya sanya a saman jallabiyar tasa, alkyabba ce ta manyan malamai
ba ta sarauta ba, yau kuma ya koma gefensu Abu Abdussalam, wato ya yi shigar manyan
malamai, har da rawani ya yi a kansa, ga dikkan alamu daga masallaci zai wuce wani
wajen.

Bai je ya dubata ba, ya wuce ya fita bayan ya ɗauki wayarsa da car key. Ita kuwa,
tsakiyar dare ta farka sai ta ganta a gado guda da shi, shi ne ta lallaɓa ta gudu
bedroom nata zuciyarta cike da zargin ko ya yi mata wani abin ne, har da kara duba
jikinta da kyau dan ta tabbatar, dik da bata ga wata alama ba, amma tabbas tana
zargi dole ya yi mata wani abin, hakan yasa ta ji ta kara jin haushinsa sosai, ta
tsanesa, dan tana ganin kamar halinsa ne neman mata kenan, amma fa ba har kasar
zuciyarta ta yarda da cewa yana neman matan ba, kawai dai kokari take yi ta tirsasa
zuciyar tata wajen ganin ta ɗaura mashi tuhuma dole dole.

Ko da ta koma bedroom ɗinta bata iya rintsawa ba, ta kwana cikin tinani da
zilimin abin da yake faruwa, zuciyarta ya rinƙa ingizata a kan meyasa zata yarda ta
zauna a gidan da daga ita sai namijin da ba muharraminta ba? Kuma ga abin da ya
taɓa shiga tsakaninsu! Ai wannan ita da kanta ta kawo kanta, dan haka koma me yake
yi mata ita ma da nata laifin, dan haka kawai ta gudu ta bar gidan nan shi ne
mafita a gareta, idan ba haka ba za'a samu matsala, zata tabka danasani fiye da a
baya, dan ita wlh babu batun yarda da aurensa a ranta, ba zata taɓa yarda ta auresa
ba, Sharifat take yi wa kwaɗayin samunsa!.

Da wannan tinani da zulumi ta kwana har asuba, da kyar ta iya tashi ta yi sallah,
sannan ta koma ta kwanta, tsawon kwanaki biyu tana ƙoƙarin shirya yadda za'ayi ta
samawa kanta mafita ba tare da saninsa ba, dik iya binciken da take yi ta rasa
samun mafita, idan ya fita baya nan har bedroom nashi take shiga ta yi ta yi mashi
bincike, amma dik ta rasa samun mafita. A ɓangarensa kuwa, yana mamakin wanenne
yake yi mashi bincike a ɗaki, dan bai taɓa kawowa ransa zata shiga bedroom ɗinsa
bama bare har ta yi mashi bincike, ga shi kuma su biyu ne kawai a gidan, abin da
ɗaure kai sosai, bai kawo komai a ransa ba, kuma bai tuhumeta ba, sannan kwana
biyun nan yana ɗan busyn da baya samun wuni a gida, kazalika baya samun haɗuwa da
ita sosai, wani lokaci kafin ya dawo ta yi barci, kuma yanzu garƙame door ɗinta
with key take yi abinta, kun san zuciya da iya sake sake, tini ta saka mata wai
idan ta yi barci yana zuwa ya yi amfani da ita, shiyasa ta dai'na yarda ta ci
abincin idan ya sayo mata, sai dai ta girka a gidan, dan zuciya ya raya mata ai
kila yana sanya mata maganin barci ta sha ya yi amfani da ita, ta dai kasa yarda da
shi gabaɗaya!.

Yau garin an tashi da hadari sosai, iska mai daɗin gaske ne yake kaɗawa, hadarin ya
yi bakinkirin, zaune take a bakin bed ɗinta ta kurawa tvn dake fuskantar balconynta
idanu, wata kyakkyawar balarabiya yar jarida ce take ta magana a cikin tvn, da
alama akwai abin da yake faruwa, dan news dake fita daga bakinta gabaɗaya maganace
a kan rashin zaman lafiya da suka tashi da shi a yau, ta natsu tsit tana sauraron
matar. Sanye take da riga da wando arabs dress wanda zaku ga rigar ya kai mata har
gwiwa, while wando kuma dogo ne wanda kasansa yake da faɗi. Ta ɗaura silky headband
milk color kalar kayan nata kenan a kanta. Ta yi masifar kyau sosai da sosai,
fuskarta fayaw, kamar bata da lafiya, mood na face ɗinta looks some how haka.

Lokaci guda ta ji kamar a takure take, tamkar dai akwai wanda yake kallanta, hakan
yasa dik ta ji babu daɗi, ta jita a tsarge, cike da fargaba gabanta na faɗuwa ta
juyo da kallanta a kan kofar shiwowa cikin bedroom ɗin. Tsaye yake ya harɗe
hannayensa a saman wide chest ɗinsa tare da ɗan ɗaure angry face ɗinsa, kamar dai
shi ma his mood for today isn't good.

Bin sexy sleeping dress ɗin jikinsa da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi,
gudun kada ya ganota yasa ta yi saurin kawar da kallonta daga kansa, tasan
kwararrun jami'ai suna amfani ne da motsi da kuma idanun mutum wajen gano mai laifi
ko mai gaskiya, dan haka sai ta yi juriyar zare kallanta a kansa, ba wai dan bata
sha'awar ta yi ta kallansa ba, saboda kowa ya gansa sai ya sake kallah. Dan kawai
ta kare kanta kuma ta tabbatar da shirinta. TO ME TAKE SHIRYAWA KENAN? HAR DA WANI
TA TABBATAR DA SHIRINTA!.

Shi kuwa binta da kallon tuhuma ya yi, yadda ya ga idanun nan nata bai yarda da ita
ba, dole akwai abin da take shiryawa wanda bai sani ba, dan haka

Please Login or Register in order to submit comment