You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miƙe
cike da jarumta, da gudun gaske damusan ya yi kansa dan ma kada ya bashi wata damar
kara karfafa kansa kenan. Juyawa ya yi da gudu damisan ya rufa mashi baya. Tsalle
ya yi ya taka wata bishiyar ɓaure dake kusa da su sannan ya juyo da karfi haɗe da
haɗa hannayensa dikka biyu da karfi sosai ya dakawa damisan duka a tsakiyar kai,
nan take damisan ya durkushen kafafunsa a kasa yana sakin wani irin kurnani mai ban
tsoro da kuma ban tausayi, alamar Hoorain ya ji mashi ciwo a kai.

Ko kaɗan Hoorain bai yi niyar kashe shi ba, ganin ya yi ƙasa ya yi mubaya'a yasa ya
rabu da shi, a hanzarce ya wuce ya nufi in da take yana sauke numfashi a hankali
hankali.

Da hannu ɗaya ya ɗagota bayan ta duƙa. Kai tsaye wajen koramar ya nufa da ita.
Cikin nitsuwa ya kwnatar da ita a saman dutse, ƙarisawa gaban koramar ya yi haɗe da
tarar ruwa ya fara wanke jininsa da damusan ya fidda mashi, har lokacin sai jan
numfashi kamar haki yake yi alamar wanda ya gaji.

Sai da ya wanke jikinsa tsab kafin ya dawo kusa da ita, cak ya sake ɗaukarta suka
ƙarisa gaban koramar. Gabaɗayanta ya sanyata cikin ruwan.
Da ihu ta farka tana sambatun damusa zai cinyeta. Shi ma ruwan na jiƙasa, dan
kusan a tare suka shiga cikin koramar, sai dai shi ta ɗan baki baki ne, da kyar ya
iya ambatar sunanta da ranki ya daɗe.

Ina ai bata ma san yana yi ba, ihu ta cigaba da yi tana ƙoƙarin kwatar kanta, da
alama bata cikin hayyacinta. Ƙanƙameta sosai ya yi, cike da tausayinta ya matsar da
face ɗinsa ɗan dab da ita, sannan ya ce ta nitsuwa damusan ya gudu.
Jin hakan yasa ta yi saurin waro idanunta, ganinta a hannunsa kuma cikin indoron
ruwan dake kwaranya yasa ta yi saurin juyar da kanta izuwa gefe da gefe tana neman
ina damusan yake.

"Ki kwantar da hankalinki baya nan, ya tafi". Cike da so da kauna ya faɗa.

A tsorace sosai ta ce. "Ina ya tafi Hoorain?". Ta yi maganar tana kai hannunta
saman face ɗinsa.
"Bai yi maka komai ba ko?" Ta sake tambaya tana shafa kumatunsa".

Jinjina mata kai ya yi haɗe da cewa. "Babu wata barazana ranki ya daɗe". Ɗan daure
fuska ta yi haɗe da turo baki, a shagwaɓe ta ce. "Hoorain wai kai baka iya soyayya
bane sai wani ranki ya daɗe kamar wani bosawa? Babu ko irin sunan love ɗin nan?".

Shiru ya ɗan yi tare da matsawa baya kaɗan ya fitar da ita daga cikin ruwan
kenan, sannan ya rabata da jikinsa ya sauketa ƙasa a kan kafafunta.

"Hoorain baka bani amsa ba". Wannan karan murya a ɗan kasashe ta yi maganar.

"Na iya soyayya, sai dai ina tinanin abin da zai je ya dawo shiyasa nike ja da
baya, bana san dik abin da zai iya jawo mana matsala da ni da ke".
"Ban gane nufinka ba". Cike da mamaki ta yi tambayar.

Gyara tsayuwansa da kyau ya yi, cikin nitsuwa ya fara warware mata komai dan gane
da abin da yake jiwa tsoron yasa baya san zurfafawa a soyayyarsu, baya san sakin
jiki sosai.

"Ke da kanki kin san ƴan uwanki ba zasu taɓa yarda da ni a matsayin masoyinki
ba, ba zasu taɓa karɓata ba, sannan kin san matsayina da naki daban daban, ke kanki
ina jiyewa zuciyata tsoron ki juya mata baya, na san daddynki ba zai taɓa yarda ya
bani ke ba, kema kuma kin san da hakan, idan muka cigaba da soyayya na tabbata
wahala zamu sha, and nasan ke ba zaki iya jura ba, idan kin ji wahala kaɗan zaki
guji zuciyata ki barni a wahale, wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da nike guje
mana".

Tabbas ta fahimci dalilansa, sannan kuma ta gamsu dalilai ne masu karfi da dole
zasu iya sanya shi ja da baya, tasan King ba zai taɓa yarda ba, bama azo ga King
ba, ko guyson ba zai yarda ba, ranar iya ganinta kawai ya yi ta kusa da part na
mayaka ji yadda ya tashi hankalinsa bare kuma ace ya ji tana san assistant
commander? Tab ai babu wanda zai goya mata baya, ko Chuchu ba zata bi bayanta ba a
wannan gaɓar.

Amma dik da haka sai ta kallesa ido cikin ido, cike da tsantsar makauniyar
soyayyarsa ta fara magana masu zafa kamar haka.

"Tabbas dik abin da ka faɗa haka ne, kuma ka fini gaskiya, amma akwai kalma ɗaya da
ka faɗa wanda ba hakan bane kuma ba zan lamunta ba!!".

Tattara mata hankalinsa a kanta ya yi yana sauraronta, cike da sa ran zata kawo
masu mafita.

"Abin da ka faɗa ba daidai ba kuma shi ne cewa da ka yi idan na ji wuya zan
juyawa zuciyarka baya, ka yi kuskure! Ban ga wata wahala da zata sa in juya maka
baya ba a duniya, soyayyar gaskiya nike yi maka ba ta yaudara ba! Kada ka manta
nasoka ne tin ban taɓa ganin kamanninka ba, tun da na taso a rayuwata bani da abin
san kalla sama da kai, ka yarda dani, mu haɗa hannu zamu yi nasara! Na yi maka
alkawarin a kai'na kuma dalilina dik ƴan uwana zasu canza su karɓeka a matsayin
zaɓina hannu bibbiyu, ka mun alkawarin dik halin da zamu shiga ba zaka taɓa ja da
baya a kan soyayyarmu ba?".

Ta kai karshen maganar tare da buɗe tafin hannunta ta miƙo mashi. Da yake
jajirtacce ne babu tsoro a tatare da shi sai bai yi wani tinani ko ya damu ba, shi
ma ya buɗe tafin hannunsa ya ɗaura a saman nata.

"Na yi maki alkawarin babu gudu babu ja da baya kome zai faru ina kan bakata na
ina sanki!".

Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Tabbas ba zan baka kunya ba,
kuma na yi maka alkawarin sai dai a zare raina da soyayyarka a kirjina, ba zan taɓa
san wani ba kuma ba zan taɓa yarda a haɗani da wani ba".

Wani irin bargon farinciki ne ya lulluɓe zuciyarsa, ya ma rasa abin faɗe, sai dai
kawai ya yi shiru yana jin wani sanyi tana ratsa zuciyarsa.

"Yanzu meyakamata mu yi?". Cewarta kenan. "Gida zamu tafi yanzu, hanya zamu
ɗauka, gobe zamu iya isa".

"Har na ji bana san mu koma yanzu, kamar mu kara kwana biyu a nan, wajen akwai
daɗi sosai". Cike da yaranta a word ɗinta ta yi magana.

Kai ya girgiza tare da riko hannunta da kyau a cikin nasa, ƙasa ƙasa ya ce mu je.
Bata yi musu ba ta bi bayansa suka tafi wajen Pretty, har lokacin sai barci take
zubawa.

Kamar zai tambayi Auta su tafi da Pretty ko su barta a wannan dajin tun da ta faɗa
mashi a nan suka sameta. Sai kuma ya ji ba zai iya tafiya ya barta ba, tin da suka
ganta haka bata da kowa kenan, dan haka su tafi da ita kawai.

"Jirani ina zuwa, ki tashi Pretty kafin na ɗauko dokina". Yana kai karshen maganar
ya sake hannunta, bai jira amsarta ba ya wuce da sauri izuwa ɗan baya da su kaɗan.

Ita kuma ta wuce ta tashi Pretty daga barci, yana dawowa suka hau saman dokin da
dik wani abin da zasu buƙata, wajen da suka yi faɗa da damusan nan ya koma ya ɗauki
takobinsa, sannan suka kama hanya, Auta a gaba Pretty a tsakiyansu shi a baya, ba
komai yasa yaki saka Auta a tsakiyansu wato kusa da shi ba face kaucewa sharrin
shaiɗan.

Auta ta manta da tana jin yunwa, haka suka kama hanyar nufar Kingdom of power.....
To sai dai mu ce Allah ya kaiku lafiya.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

2:30am.

Dare ta tsala sosai, ko'ina ya yi tsit, dik wani na kirki yana cikin gidansa, banda
kukan karnikan Ramish su bisho dake tashi babu wani abin da zaka ji.

A hankali karan Acn ɗakinta yake tashi. Kasancewar bata da nauyin barci ko kaɗan
hakan yasa in abu ya motsa a kusa da ita tana ji kuma yana farkar da ita, dama dik
wanda ya yi zaman gidan yari da wuya ya iya nauyin barci.

Ta yi nisa cikin barcin da take yi cikin kwanciyar hankali, yau tana farincikin ta
amayarwa masu nikaf kunan da ya daɗe yana babbaka ranta, yau ta samu sai'da da
salama, har ta ji bata taɓa yin barci mai daɗin wannan ba.
Can a tsakar kanta ta ji kamar an taɓa mata kofar ɗaki, dik da tasan ba ita
kaɗai take kwana a ɗakin ba, amm tasan yau Sharifat bata nan, kuma da wuya ta dawo
cikin wannan daren.

A karo na biyu ta sake jiyo an mai da kofar nata an rufe tamkar wani ne ya shigo ya
rufe, kamar a mafarki ta ji ana datse keys na kofar wanda tun da suke daga ita har
Sharifat babu wanda ya taɓa datse wannan kofar da keys ɗinsa.

Hakan yasa ta zabura ta miƙe zaune, ɗakin duhu bakin kirin, dan yau ko lamp dama
bata kunna ba. Wani irin ɗan motsi ta ji kamar alamar tafiyar jami'i a yakin
sunkuru, ko kaɗan bata tsorata ba, dan ba ƙaramin abu yake tsoratata ba ita.

Cikin dabara ta laluɓa ta sauko kasa daga saman gadon, tamkar wata hawainiya ta
fara taka kafafunta ta nufi switch. Unexpect ta isa wajen ta kunna wutar ɗakin, nan
take haske ya gauraye ko'ina.

Ya ilahi ya lilliahi, wani irin mahaukacin razana ta yi. Idanuwanta ne suka yi mata
tozali da wani tsayayyen namiji cikin shigar ban tsoro, baka iya ganin komai daga
jikinsa, from up to down gabaɗaya bakaken kaya ne a jikinsa, fuskarsa rufe yake da
tactical mask, ba zaka taɓa iya gane wanene bane, kafafunsa na sanye da combat
boots masu karfin gaske. Ga shi a tsaye a tsakar ɗakinta, ya rufe kofar ɗakin kuma
da key babu halin gudu ta fita.

Sosai ta razana, da karfi ta waje baki zata zunduma ihu kamar walkiya haka ya wurga
mata wani abu mai kamar da karfen star a baki.

Wani irin baya baya ta yi kamar zata faɗi, dan dolenta ta haɗiye ihun da take
yunkurin kurmawa, jinine ya fara bulbula daga bakinta, alamar abin ya fasa mata
baki. Ganin hakan yasa ta fahimci komai, wato kasheta aka zo yi dan ta yi barazana
wa masu nikaf.

Amm waye kuke tinani mai kwarin gwiwar da zai iya keta camarorin da suke kan titin
hanyar ratsowa gidan Abu Abdussalam har ya iso, sannan ya keta dikka waɗan nan jiga
jigan securitys ɗin ya shigo cikin gida, ya keta cameras dake cikin gida har da
babban parlourn ya iso ɗakinta dik kuma babu wanda ya gansa? Anya wannan makashi ba
daga cikin gida kuwa yake ba?.

Hannu ya sanya a wajen combat boots ɗinsa ya zaro wata karamar wuƙa mai bala'in
kaifin gaske, ga shi har kwayar idanunsa baka iya gani, dan tactical mask idan ka
sanya mutum ba zai iya ganin komai na face ɗinka ba sai dai kai ka gansa. So yau ko
idanun bata samu damar gani na bare ta iya hasashen wanenen ko ta sa ran zata iya
ganesa.

Ganin ya zaro wannan wukar yasa ta ƙara tsorata, da gudun gaske ta yunkura zata
shiga toilet ta rufo kofar. Sai dai ina, bai bari ba, taku biyu ya yi ya damko
gashin kanta. Da karfi ya fisgota da gashin nata ya yi wurgi da ita a saman bed
ɗinta.

Sosai ta ji azaban jan gashinta da ya yi, amma haka ya daure ta shanye, da gudu ta
yunƙura ta miƙe. Sai dai bata kai ga sauka gadan ba ya sanya combat boots ɗinsa ya
take kirjinta da karfi har sai da ta bugu da jikin headboard na gadon.

A wannan gaɓar azaban da ya ziyarceta ya ja ta saki wani marayar kuka, ga shi
bakinta sai bulbular da jini yake yi. Ta maza ta sake yi ta yi yunƙurin tashi zata
gudu again tana dafe kirjinta, dan ya taketa a tula tulanta, kuka kunsan dole ta ji
azaba over.

Kafafunta ya take da combat ɗin nan nasa, har cikin ranta azaban hakan ya ratsata,
ta gagara yin kuka, ta ko'ina zogi da raɗaɗi take yi.
Matsawa ya yi kusa da ita, ya damko gashin kanta cikin hular kayan barcinta, sai
da ya jijjiga kanta da karfi sannan ya bugata da jinin headboard na gadan, nan take
goshinta ya fashe. Ko kaɗan babu alamar zai tausaya mata, babu imani a ransa,
wuyarta ya sake shaƙowa da karfi, hannunsa na cikin Black gloves. Ya matse mata
wuya da iya karfinsa.

Tuni ta fara jiyo kamshin mutuwa, tuni idanunta suka fara rufewa ta fara ganin duhu
mai yana yana lulluɓe ko'ina, ta dafe kirjinta saitin tula tulanta, ko da zogin da
suke yi mata kawai ya kyaleta ai ya isheta ba sai ya kara mata wani ba.

Hannunsa ɗayan ya kai saman kumatunta, yana rike da ƴar wukar, sai ya sanya
wukar a tsakiyar yatsunsa, hakan ya bashi damar matse mata kumatu sosai har sai da
ta ja wani irin azabbabben numfashi.

Bata iya ganin idanunsa, amma shi idanunsa kar a kan kirjinta, hakan yasa ya saki
kumatunta ya mayar da hannunsa saman kirjin nata, da karfi ya matse mata tuka
tulanta dan bakar mugunta, azaba yasa ta ji wani karfi ya zo mata ta fara ƙoƙarin
kwatar kanta. Ganin hakan yasa ya ji a ransa yana da kyau ya keta mutumcinta kafin
ya kasheta.

Wannan tinani nasa yasa ya zame hannunsa daga fatar wuyarta ya mayar wuyar rigarta.
Da karfi ya ja rigar ya yaketa. Ko kusa ko alama ba zata iya kwatar kanta daga
hannunsa ba, ga shi babu ko vest a ciki, haka ya yage mata riga, ya kuma yage mata
wando, ya rage pant a ciki kawai.

Kafarsa da ya take nata da shi ya cire. Da hannu ɗaya ya damki kafafun nata ya jata
a in da ta dawo tsakiyar bed ɗin, gabaɗayansa ya tafi kanta da nufin aiwatar da
abin da yakeso. Dik jikinta ya yi wanka da jinin dake bulbula daga goshinta and
bakinta, ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi, hankalinta ya fara gushewa, tana ji ya
haye kanta haɗe da rabata da komai nata.

My people's waye kuke tinanin zai yi wannan aika aikan? Shin ina mazan gidan Abu
Abdussalam da har wannan abin zai faru basu sai ba? Ko da yake part ɗinsu yana da
nisa da nasu Ummie, amma koma wanenen wannan anyi mai karfin zuciya da kwarin
gwiwa, tab wannan masifa haka. Mekuke tinanin zai faru? Allah sarki Leesharh, ko
tsoro baya ji zai kasheta cikin gidan ministan tsaro na ƙasa gabaɗaya? Lallai akwai
cakwakiya.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Ko tausayinta babu alamar zai ji, da karfin tsiya ya fara ƙoƙarin haike mata,
kasancewar wandan jikinsa irin Armored leggings ɗin nan ne sai ta yi mashi wuyar
ciruwa lokaci guda, ga shi ba zata yagu ba bare ya yageta.

Hakan yasa ya ɗan ɗaga jikinsa daga nata kaɗan, da zafa ya fara ƙoƙarin kwance belt
dake jikin wandan dan ya yi abin da zai yi da sauri.
__________________🔥

Lokacin guda ya ga wani irin warkiya kamar shocking na wutar lantarki, ya
kuma ga wani irin jiri mai karfi ya ɗebesa, daga haka bai sake gane komai ba, sai
jin kansa ya yi ya faɗi a saman mattress ɗin rigijib kaman kayan wanki. Ba komai ya
ja hakan ba kuma face, lokacin da yake ƙoƙarin cire belt ɗin wandasa ita kuma ta
lura da ya bar kanta, hankalinta ne ya dawo jikinta, cike da kunan ran abin da ya
yi mata, ga azaban da take ji, cikin dabara da jajircewa irin nata ta sanya hannu
ta laluɓi lamp dake saman bedside drawer, da iya karfinta na karshe ta jawosa.

Shi kuma hankalinsa dik yana a kan yadda zai zare belt ɗinsa, Allah ya bata dama,
da yake bata da hakkinsa sai ta shammacesa ta dakarkare ta maka mashi a kai. Wannan
shi ne abin da ya faru.

Da kyar ta iya motsa jikinta ta miƙe zaune, shesshekar kuka take yi sosai, hannunta
tasa tana tattaro rigar barcin jikinta dan ta ɗan sitirta kanta. Kamar gizo haka
idanunta suka hango mata shi yana motsawa a saman mattress ɗin yana san tashi
kenan, alamar ba suma ya yi ba dama, zafin buguwa ce nawai ya ji yasa ya faɗi kamar
ya suma.

Ai bata san lokacin da wani irin karfi ya zo mata ba, a maliyan ɗari kamar wata
walkiya sai gata ta diro kasan bed ɗin, kai tsaye kofar room ɗin ta nufa, a
gaggauce ta fara ƙoƙarin ɓalle key ɗin ta fita, hannunta sai kerya yake yi, yaki
tsayawa waje guda bare har ta iya buɗe kofar.

Hankalinta dik a kansa, kun san idan mutum yana tsorace haka abin yake, sai ji ta
yi key ɗin ma yaki murzuwa ta buɗe.

Shi kuwa a lokacin ya farfaɗo, a zabure ya zaro idanunsa da suka yi jajir waje, ya
ji bugu hege. Wani irin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin ya yi yana zaro idanun
kamar ma tare ɓera a tarko. Wayam bai ganta a saman bed ba, hakan yasa ya fara
jujjuya jajayen idanunsa yana neman ta ina zai ganta.

Ita kuwa kerman da hannunta yake yi yasa kofar taki buɗewa, sai zaro idanu a kansa
take yi karjinta tamkar zai fashe saboda bugawa, iya tsorata yau ta yi shi, cikinta
ya gama ɗuran ruwa, har gudawa ta ji, kamar fitsari zai zuba mata take ji.

Ganinta a wajen kofa yasa a miliyan ya diro ƙasa daga saman bed ɗin, sai ƙoƙarin
murza key take yi tana ihu ƙasa ƙasa dan voice ɗinta baya fita. Cikin zafa ya
nufeta yana wani uban ɗaure fuska, sai huci yake yi alamar ransa a tsananin ɓace.

Yana isa dab da ita Allah ya bata sa'a ta ɓalle key ɗin kofar, yana ƙoƙarin
damko gashin kanta ta danna waje a miliyan. A haukace ta fito main parlour na sama,
har lokacin jikinta dik jini, bata san ina ta nufa ba ga duhun dare, dik kwayayen
fitillu a kashe. A tinaninta ya biyo bayanta hakan yasa ta kara gudu sosai.

Dai'dai zata fita parlourn suka ci wani uban karo da shi yana shigowa. Baya baya ta
yi ta faɗi ƙasa, da yake akwai duhu a parlourn hakan yasa baka iya gane wanenen,
amma ita dik da tana cikin tashin hankali bai hana ta fahimci da Ramish ta yi karo
ba, saboda kamshin perfume ɗinsa ya banbanta da na kowa a cikin gidan.

Shi kuwa ko a jikinsa bai nemi sanin da waye ya yi karo ba, sarkin yawon tsakar
dare a cikin gida kenan, ba shi da aiki sai ya yi ta yawo har garden ɗin dake
harabar gida yake zuwa da tsakar dare, ya zauna ya yi ta latse latsen waya, to ya
fito yawon nasa ne yanzu ma suka ci karo. Bai bi ta kan wanda ya buge ba yasa kai
ya tsallaketa ta wuce ciki.

Ita kuma da karfi ta tashi ta fice wajen. Bata zame ko'ina ba sai part ɗin Abbie
cikin rashin sani, Allah sarki bata san ina ta dosa ba, gudun cetan ranta kawai
take yi. A lokacin karfe 4:00 daidai ta buga, asuba ta kawo kai kenan.

Takuwa yi sa'a idanun Abbie biyu yana saman dadduma yana sallah. A haukace ta
afka cikin ɗakin, har taso ta ɗan bashi tsoro, amma da yake yana gaban Ubangijinsa
sai bai wani damu da sanin wanenen ya afko mashi ɗaki a haukace haka ba. Cigaba ya
yi da sallarsa cikin nitsuwa, ita kuwa cikin rashin sani ga duhu yasa ta fara bin
jikin bango tana neman gane ina ta shigo ne?.

Tabbas lamps na ɗakin a kunne suke, amma bata iya hango Abbie, saboda ɗakin yana da
girma sosai, hasken lamp basa kaiwa in da yake.

Cigaba da laluɓe ta yi tana haki haɗe da sauke numfashi da karfi karfi. Har ta isa
in da Abbie yake ba tare da ta sani ba, tana layi kamar wadda take a make. Tana isa
dab da shi a lokacin ya sallame sallah ya miƙe dan ya je ya kunna wutar ɗakin yaga
wanene ya shigo mashi ɗaki a irin wannan yanayi haka.

Yana miƙewa suka ci karo, a lokacin dik wani karfinta ya kare, tafiya ta yi zata
faɗi ƙasa ya yi saurin rikota. Sai da gabansa ya faɗin jin cewa yarinya ce mace
kuma kamar babu kaya a jikinta. Amma dik da haka ya yi ta maza ya rungumota a
jikinsa gudun kada ta faɗi.

Da kyar ya iya riketa suka karisa gaban bed ɗinsa. Sosai ya zaro idanunsa a lokacin
da wutar lamp ta haska mashi face ɗinta, a fili ta furta Leesharh da ɗan ɗaga
murya.

Lokacin ta fara fita a hayyacinta, sam bata gane a hannun wa take ba, hankalinsa ne
ya tashi bawan Allah, jiki na kerman mamaki ya kwantar da ita a saman gadansa. Ga
bedsheets ɗinsa white color ne sosai, haka ya yi dama dama da jininta. Ɗan kawar da
kallansa daga kanta ya yi duba da cewa babu sitira a jikinta, ya janyo white duv
ɗinsa ya lulluɓeta da shi har saman kirjinta. Jikinsa dik ya ɓaci da jininta, dama
white jallabiya ce a jikinsa.

Wajen phone set dake kusa da bedside drawer ya nufa, fili ne da aka yi sa domin
ajiye waya, hannunsa har yana ɗan kerma wajen ɗauko wayarsa. Number zaratan samarin
gidan nasa yake san kira ya ji menene yake faruwa a cikin gidan haka? Su zo su duba
mashi me ya samu Leesharh? Waye ya yage mata kayan jikinta haka?.

Sai dai bai kai ga kunna wutar screen ɗin wayar bama bare aje ga call sai ganin
ɗakin nasa ya yi ta gauraye da haske an kunna bulbs. A ɗan razane ya juyo ga switch
na ɗakin.

Sanye take da sleeping gown tana tsaye a kan kafafunta, tsaresa da ido ta yi taba
binsa da wani irin kallo wanda za'a iya fassara shi da kallan tuhuma. Ummie kenan.

Me kuke tinani ya kawo Ummie a dai'dai wannan lokacin? Abu kamar tasan da Leesharh
a cikin ɗakin, ko da yake ɗakin mijinta ne, zata iya shiga a dik time da taga dama,
ga shi kuma asuba ya kawo kai, dama za'ayi expect ɗin dik wata mace ta gari a irin
wannan lokaci tana ga mijinta zata tashe shi sallar asuba ko?......🥱

From head to toe ta fara bin Abbie da kallo, abin ya yi matuƙar bata mamaki
sosai, cike da zargi a idanunta ta mayar da kallanta a kan Leesharh dake kwnace a
saman bed ɗinsa tana wani irin numfashi sama sama kamar zata sume.

"Omar, me zan gani kenan?". Ta faɗa tana zaro idanun, yau babu batun Abu
Abdussalam, da ainahin sunansa Omar ta kirasa, mata duniya ne wlh.

Tabbas ya ji mamakin wannan suna da ta kirasa, yau sama da shekaru 30 suna a tare
bata taɓa ambatar wannan suna ba sai yau, abin ya ɗan girgiza shi, nan ma wai
hankalinsa bai kai ga kan abin da take zargi a ranta ba kenan, ya zaci ta tsorata
ne na ganin Leesharh a cikin mawuyacin hali har ya ɗaga mata hankalinta, shiyasa
har ta kirasa da Omar ba tare da ta sani ba, bai san babban bala'in dake tinkarisa
ba.

"Lafiya kuwa?". Ya jefa mata tambayar cike da matsuwar san jin dalilin kiransa
da ta yi da Omar ɗinsa. Amma fa bai yi mamakin ganinta a ɗakinsa a wannan lokacin
ba, saboda ta saba zuwa, wani lokaci a nan take kwana, yau ta ce da Sharifat zata
kwana shiyasa ta tafi ta bashi waje.

"Ni kake tambaya lafiya ma ko? Dama abin da kake aikatawa kenan? No wonder wani
lokaci kake nuna cewa kafi san wannan shegiya tsintacciyar yarinyar a kan ƴar
cikinka, ashe da biyu!!".

Ai Abbie bai san time da ya wani irin miƙe da kyau ya tsaya a kan kafafunsa ba,
zaro mata idanu ya yi, ji ya yi tamkar an kwala mashi guduma a tsakiyar kai, da
tsufarsa da mitumcinsa ne zata zargesa da abin da ko ɗansa ya kama yana yi sai ya
ɗauki mummunar mataki a kansa, abin kyama, ya tsufa yana neman cikawa da imani ne
zata nemi lalata mashi karshensa da banzan tinaninsu ma mata? Anya akwai hankali a
kwakwalwata kuwa? Ya jefawa kansa tambaya.

A fili kuwa sai ya ce. "Ban gane me kike nufi ba?". Cikin kakkausar murya ya yi
maganar.

"Taya zaka gane abin da nike nufi, dama ai shi tabarmar kunya da hauka ake naɗesa,
yanzu kai babu kunya babu tsoron Allah zaka hakewa ƴar yarinyar da ko Sharifat ta
fita shekaru? Ko tsoron Allah baka ji! Dubi jikinka fa, dik jini, ko tausayin
yarinya baka ji ba? Wlh ba zan yarda ba, wannan ƴar iskar karuwar sai ta fita gidan
nan

Please Login or Register in order to submit comment