You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
a zuwan idan suka harbeta sai su gudu kawai,
Allah yasa Ramish ɗin ya fita shi da yaronsa suka tinkaresu, a nan suka yi wannan
faɗa har suka jijji mashi ciwo, suna tsaka da faɗar ne ɗaya ya zari gun zai harbi
Ramish kenan babban yaronsa ya tare suka fasa mashi ƙwaƙwalwa, haƙiƙa Ramish ya ji
zafin mutuwan yaron nasa, saboda sun haura sama da shekaru 7 suna a tare, sun saba
kaman ƴan uwa.
Waiwaye adon tafiya🔥
Ina ranar da suka je wajen cin abinci a tare da shi har aka yi ta yi masu hotuna?
Waɗan nan hotuna su suka baza media har masu nikaf suka san in da suke, a take suka
tura mutane suka biyo bayansu, a nan ne suka rinƙa bibiyarsu har suka ga arear da
suke, shi ne suka cigaba da gadin fitowar Leesharh ita kaɗai, sai a wannan lokaci
Allah ya basu dama, to kun ji a ta yadda suka yi suka san in da suke har suka bi
bayanta.
Ta shiga tsananin tashin hankalin da yasa gabaɗaya ilahirin jikinta ya fara
kerma..... "Yah Ramish ka yi hakuri, kwata kwata ban kawowa rai'na akwai abin da
zai iya faruwa dani dan na fita ba, ina mai baka hakuri kuma ina mai jajanta maka a
kan rashin da ka yi". Tana magana idanunta suna ciccikowa da kwallah, haƙiƙa ta ji
babu daɗi matuka a kan abin da ya faru, hannunta na kerma tana san taɓa ciwon nasa
ta kara bashi hakuri, dik ta bi ta ruɗe kamar wata zararriya. Kan kace me hawaye
sun fara zarya a saman face ɗinta, jikinta dik ya yi la'asariyar jemage. Yana tsaye
tamkar wanda aka sassaƙa, bai sake ce mata komai ba. Hannunta na rawa sosai kamar
wadda aka sanyawa lantarki, cikin tsananin damuwa ta ɗaura a saman wide chest
ɗinsa, hawayen face ɗinta suna tsananta gudu matuƙa.
Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa jin yadda ta taɓa shi. Slowly ta ɗago da
kallanta a kansa, while shi ma ita yake kallo. "Sannu ka ji? Ni na tsani kaina, ban
san meyasa a koda yaushe nike aikata irin waɗan nan abubuwa ba, kwata kwata bana
amfani da ƙwaƙwalwarta da tinanina, kullum sai na aikata abin da zan zo ina
danasani, na shiga uku na, wai menene yake bibiyar rayuwata haka ne? Shin na yi wa
wani laifi ne? Wani zunubi na aikata?". In out of control take surutan nata, tana
magana tana kara tsananta kukanta...... Lokacin guda tsananin tausayinta ya mamaye
zuciyarsa, hannu yasa ya riko hannunta dake saman kirjinsa, muryarsa a ɗan sarke ya
ce. "Ya isa haka, komai da ya faru ya rigada ya wuce, je ki yi dinner ki sha magani
sai ki kwanta ko?".
Kai ta fara girgiza mashi tana wani irin kuka irin wanda zuciyar mutum yake a kusa
ɗin nan.. "i can't eat anything Yah Ramish, na tabka babban kuskure, ni ban san
menene ma ya shiga kai'na ba, ni mahaukaciya ce kawai wanda bata da tinanin kanta,
kullum cikin jefaka a cikin masifa nike, na tsani kai'na". ..... "Aesh! Stop saying
all this, ke yarinyar kirkice mai zuciyar zinari, dik abin da kike aikatawa rashin
samun ishasshen ilimi ne da kuma ƙarancin shekaru ga rashin natsuwa da kwanciyar
hankali, amma tabbas ke yarinyar kirkice, ke ɗin jaruma ce, ba kowace mace zata iya
kwatanta abubuwan da kika yi ba, cikin mata dubu da wuya a samu goma da zasu iya
abin da kika yi, mahaifinki fa suka kama, amma dik da haka kin jure kin ce ba zaki
yi masu aiki ba, Allah zai kula da babanki, In Sha Allah babu abin da zai same shi,
zai dawo gareki cikin aminci". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar.......... "A'a
Yah Ramish, ni mahaukaciya ce kawai, kuma zan tabbata a haka tin da bana tinani da
ƙwaƙwalwata". Tana magana tana girgiza kai, tamkar wadda ta zauce, ta fita a
hayyacinta sosai!.
Ya lura da ta ruɗe dayawa, dan haka sai ya jata a jikinsa tare da ɗaukarta suka
koma bakin bed ɗin, cikin sigar rarrashi ya rinƙa lallaɓata har ya samu ya shawo
kanta ta natsu, da kansa ya janyo mata dinner ɗin ya ce ta ci, bata musa mashi ba
ta fara ci kamar yadda ya buƙata. Binta da kallo ya yi yana jin wani irin yanayi a
tattare da shi har ta kammala cin abincin, ta ci sosai saboda tana jin yunwa
matuƙa, and tin da ta fara cin abincin kanta a ƙasa, taki yarda su sake haɗa idanu.
Bayan ta kammala ya bata magani ta sha, sannan ya umarceta da ta kwanta sai da
safe. Ba musu ta kwanta, ya rufa mata bargo kafin ya miƙe ya nufi waje. Har ya kai
tsakiyar bedroom ɗin ya tsinkayo voice ɗinta tana faɗin. "Yah Ramish forgive me
please, i made a big mistake that word can't explain, na tuba ba zan sake ba".
Ba tare da ya juyo in da take ba ya jinjina mata kai da to, sannan ya ce. "Have a
wonderful sleep and sweet dreams". Yana gama faɗa ya yi waje da sauri. Shiru ta
kwanta tana tinanin irin balai'n da ta rinƙa jefasa a ciki, yakamata a yanzu ta
tsaya mashi ne, ta taimaka mashi dan ya kama waɗan da suke farautar rayuwarsa. Da
wannan tinani a ranta barci ɓarawo ya saceta sai sauke ajiyar zuciya take yi.
In short a cikin kwanaki biyu sun samu fahimtar juna da jituwa, sai dai
dikkansu sun ɗan ja baya da juna, shi saboda abubuwa ne da suka yi mashi yawa, ita
kuma saboda kare amanar Sharifat, dan ta ji a ranta kamar ta fara jinsa a cikin
zuciyarta, shi ne sai ta ja baya da shi, tana gudun abin da zai rinƙa haɗasu waje
guda, wannan tsohuwa dake kawo mata abinci ita ta cigaba da kula da ita, ko parlour
bata fita, kullun tana ƙunshe a cikin bedroom tana kallo, wani lokaci ta yi karatun
Alkur'ani mai girma. Wannan kenan a Dubai, bari mu leƙa KINGDOM OF POWER kuma mu ga
me yake wakana.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
ِإَّنَك َحِميٌد، َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم،الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد
ِإَّنَك، َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم، الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد،َمِجيٌد
️❤َحِميٌد َمِجيٌد
🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥
52
Zama mai matuƙar muhimmanci yau King yake gabatarwa tare da dikka wakilan fada ta
dattawa a cikin zauren majalisar tattaunawar cikin fada, yau magana ce ta musamman
wanda hakan yasa suka haɗu a zauren Majalisar tattaunawa dake cikin wajen. Sannan
yana da manyan baki daga kasar Iceland, ya saukesu a masaukin baki na cikin fada,
suna cikin meeting sai sun kammala zai saurari bakin nasa.
A cikin zaman da suka yi ɗin sun tattauna batutuwa masu muhimmanci sosai da abin da
zai kara ciyar da mulkinsu gaba, abin da zai kawar da dik wani abin da zai kawo
masu tangarɗa or tseko, sannan suka tattauna batu a kan zalincin da Queen Zarina
take yi wa jama'arta, nan ma suka tsayar da matsayan yakarta su kasheta kawai a
halin yanzu kowa ya huta, sai a canza tsarin mulkin masarautar tata izuwa ta
addinin musulunci. Batu kan Spender ma ya ratso ta cikin tattaunawar nasu, sannan
batu a kan cin amana ma ya ratso, saboda harta manyan wakilan fada ɗin ma yanzu
King ya fara zarga, bcos yana mamakin yadda za'ayi su yi magana a tsakaninsu kuma
ace Zarina ta samu labari, abin yana bashi mamaki, yanzu ya fara yarda da zancen
Ramish na ce wa kada ya yarda da kowa har su uncle Abbas ɗin ma, dan haka ba komai
ya tattauna da wakilan fada ɗin ba, ya bar wasu batutuwa a ransa da nufin zai yi
shawara da Smart and Ramish.
A cikin wannan zama dai Aunty MieMie tana ciki, sannan Akka ma ta halacci zaman a
matsayinta na Queen mother, yana da kyau Momma ta halatta ita ma, saboda ita ce
ainahin sarauniya, matar da sarki ya fi so ya fi ji da ita ita ce babbar Queen ba
wai uwargida ko ta tsakiya or amarya ba, babbar Queen yana ta'allaka ne a kan yadda
sarki yake santa, ya kuma aminta da ita. So a matsayin momma na babbar Queen ya ci
ace anyi wannan zaman da ita, amma King ya ce a'a baya da buƙatar hakan, saboda
bala'in kishi irin nasa, yana daga cikin dokikin da ya zartar a kan kingdom ɗin,
wato hana matansa fita, hana su zuwa fada, hanasu zuwa dik wani taron meeting.
A wannan zama dai King ya sakowa su commander Zafar zancen auren Auta, har da
commander a taran, dan ya warware sosai, shi kansa Hoorain ya warware har an
sallamesu, yana room ɗinsa yana karasa jinya manne da waya a kunne yana bayin ruwa
wa flowernsa.
Wani irin faɗuwar gaba commander ya ji a lokacin da ya ji batun auren, amma sai ya
danne, domin ya nunawa King ne Hoorain ya rabu da auta, a zahiri kuma ni da ku mun
san ya kasa iya tinkarar Hoorain da batun su rabu ɗin, so ya barsu suna cigaba da
soyayyarsu, ya shararawa King karyar sun rabu, to yanzu ga shi King ya zo da babban
al'amari mai girma, wato auren auta. Shiru ya yi yana tina lion ɗinsa, Allah sarki
maraya bawan Allah.
Shi kuwa King cigaba ya yi da cewa. "Jibi za'a ɗaura auren, abin ya zo ne ba shiri
cikin gaggawa, dan haka a tsananta tsaro sosai a cikin masarautar da kewaye, sannan
a shirya gagarumin bikin da ba'a taɓa yin irinsa ba, muna tashi wannan taro a
turawa manya manya sarakunan nan gabaɗaya gayyata, wannan nauyi ya ta'allaka ne a
wuyarka aminta". Ya kai karshen maganar yana bin amintan da kallo. Cikin girmamawa
ya risinar da kai haɗe da cewa ya karɓi umarni. Dawo da kallonsa a kan commander
King ya yi. "A tsananta tsaro sosai, sannan ka shirya dakaru yadda yakamaya domin
ana gama bikin nan da kwana biyu zaku shafe Zarina daga doran duniya, zalincinta ya
kai matakin da babu gargaɗi ko ɗaga kafa, mun daka mata warning har ya fi sau uku,
dan haka mun cike ƙaida, a rufe babinta kawai!!".
Jinjina kai commander ya yi, cikin girmamawa ya karɓi umarni, sai dai fa kowa a
cikin wajen yasan commander ya canza, ya shiga cikin yanayi lokaci guda. Sarai King
ma ya lura da canzawar, amma sai ya yi tamkar bai gani ba, ya cigaba da jawabinsa
da irin tsare tsaren da yake da ɓuƙata a gidan, gagarumin biki za'a gudanar, bikin
ƴar Auta guda! Dole sai an shirya, za'ayi taran da ba'a taɓa yi ba.
Har aka tashi wannan zama commander bai sake cewa uppan ba, ya risinar da kansa
ƙasa yana sauke numfashi a hankali hankali, a ransa yake faɗin ba zai iya sanar da
Hoorain ga abin da yake wakana ba, dan za'ayi babban tashin hankali sosai.
Ko da ya koma ɗaki ya samu Hoorain bayan an tashi zaman, mannne da waya ya iskosa,
hakan yasa jikinsa ta kara mutuwa, cikin gaggawa ya juya zai fice daga ɗakin.
Hoorain ɗin ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Abbo Gimbiya tana gaidaka".
Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, cikin sauri ya nufi kofar fita.
"Abbo Gimbiya zata yi magana da kai". Hoorain ya sake dakatar da shi.
Zuciyarsa tamkar zata fashe, hankalisa a tsananin tashi, ba dan ya so ba ya
juyo ya dawo, wayar ya karɓa tare da mannata a kunnensa. Tsaresa da kallo Hoorain
ya yi yana nazarin fuskar mahaifin nasa, take ya fahimci akwai wani abin dake damun
baban nasa.
"Abbo barka da safiya". Daga can Auta ta faɗa, sai sakin murmushi take yi, tana
zaune daga ita sai wani simple gown mara nauyi da ya tsaya mata a iya gwiwa, hannun
rigar ɗan siriri kamar na vest, ta ɗaure throw pillows guda biyu a saman laps
ɗinta, tana zaune bakin ruwan da dolphins ɗinta suke ciki, sai janta da wasanni
suke yi, amma taki kulasu. Ita kuwa Pretty sarkin sakalci da shiririta tana sama
tare da Smart, taki yarda ta rabu da shi, dan tsoro, dik in da zai je kafarta
ƙafarsa, yanzu haka yana sama gabaɗaya yana gym, ita kuwa tana zaune saman chair
tana kallansa, dan dole Smart ya fara yin sabo da ita, yanzu har yana jinta a cikin
ransa, kun san idan mutum yana yawan zama a tare da kai, dole yau da gobe ka fara
jinsa a cikin ranka.
"Barkanki dai Gimbiya, fatan kina lafiya ya shirye shiryen azumi?". Commander ya
tambaya yana ɗan juyawa, dan baya san kallan da Hoorain yake yi mashi, yana tsoron
ya fahimci wani abin, bai san tini ya harbo jirginsa ba. "Abbo ina nan lafiya, na
yi kewarku sosai, ina san dawowa ko dan na ganku". Ta faɗa cike da zumuɗi. Rasa
abin faɗe commander ya yi, dan gabaɗaya hankalinsa baya jikinsa, to kawai ya iya ce
mata, nan ma sai da ta kara maimaita maganarta a zuwan bai ji me ta ce da farko ba.
Tin bata yi sallama da shi ba ya miƙewa Hoorain wayar ya yi gaggawar ficewa daga
ɗakin.
Manna wayar a kunne Hoorain ya yi kallansa a kan Abbon nasa, a hanzarce ya ce. "My
princess zan sake kiranki anjuma, yanzu bari in ɗan yi wani abin". Cike da muradin
san bin bayan Abbonsa ya ji meke damunsa ya yi maganar....... Kai ta fara girgiza
mashi tamkar tana a gabansa. "No my Hero, ni ban yarda ba, kwata kwata fa ko two
hours muna waya bamu yi ba, ni dai Allah a'a, ka bar dik abin da zaka yi ɗin sai
anjuma, now is my time". Nisawa ya ɗan yi. "Ai ko iya wannan shagwaɓar ta isa tasa
dole na in ƙasa iya katse kiran, Hoonairata kina narkar mun da zuciyata da
shagwaɓarki".
"Uhm uhm ba na ce kai ma ka mun kaki ba, naku sa yin fushi da kai, haka jiya na
ce ka mun murmushi ka ce baka iya ba ko?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Komawa
ya yi ya kwanta, salanta yasa ya manta da yana san bin bayan Abbonsa, ɗan mirginawa
ya yi ya kwanta ruf da ciki, cike da tsantsar madarar kaunarta ya ce. "Ban iya bane
ne, amma kema kin san da na iya dole zan yi maki, but ki koya mun yadda ake yi zan
yi maki". In a low voice sosai ya yi maganar, kamar wani yana yi mashi laɓe.....
"My Hero ni nasan ba zaka taɓa iya yi ba, ɗan garama shagwaɓar kila zaka iya
kwatantawa"......... Murya kamar yana cikin mayen madarar kauna ya ce. "To mu yi
video call sai ki koya mun shagwaɓar, zan yi maki, kece fa, ai dolena in yi". Bin
kayan jikinta da kallo ta ɗan yi kafin ta ɗan turo baki kaɗan. "My Hero ka bari
zuwa dare ko anjuma sai mu yi video call ɗin, yanzu babu k........". Ƙasa ƙarisa
maganar ta yi, saboda ta ji nauyin ce mashi babu kayan arziki a jikinta, kuma tasan
idan ta faɗi hakan ma kishinsa ne zai motsa ya yi fushi, dan shekaran jiya da suna
waya ya jita tana magana da Robbot mai kawo abinci a take a wajen ya ce mata
wanene, da buɗar bakinta sai ta ce mai girki ne, aikuwa taga kishi, dan cikin ɓacin
rai har mantawa ya yi ya daka mata tsawar a kan me zata yi magana da mai girki
namiji? And babu masu girki mata ne sai maza? Take ya hau ya fara masifar da bai
san ya iya ba, ya kuma ya manta cewa princess ɗinsa ce, kishi ta rufe mashi idanu.
Da kyar ta shawo kansa, da kyar ta samu ya ɗan sassauto har ta sanar da shi Robbot
ne ba mutum ba, dik da haka ya ce baya san ta rinƙa magana da shi, ai namiji ne
koma Robbot ɗin ne, dole ta yi alkawarin ba zata sake ba, ta kuma bishi da love
word masu zafi, a takaice dai a wannan lokaci bai iya yin soyayyar ba, dik da
kalaman da ta zuba mashi, ransa ya rigada ya ɓaci sai kawai ya ce mata sai anjuma,
ya katse kira ya zauna yana huci shi kaɗa.
Wannan dalilin yasa bata ce mashi babu kayan arziki a jikinta ba, dan kishin zata
motsa, zai ce akwai maza a gidan, tasan rigimarsa bata karewa a kan kishi, har yau
idan ya kirata sai ya ce ina wannan Robbot ɗin, kuma yana tambaye fa kawai dan ya
ji shin tana kusa da shi ne ko dai ta yi nesa da shi kamar yadda ya ce mata, kai
Hoorain ba dai kishi ba, ko da yake jinin Modarawa haka suke dikkansu! Balai'n
kishin tsiya daga mazan har matan!.
Kamar zai tambayeta meyasa bata san su yi video call a yanzu, sai kuma ya basar da
cewa. "To shikenan Allah ya kaimu, ki gaida mun da Pretty and Yah Omerish". Da okey
ta amsa mashi kafin ta ce. "To ka bani na barci". Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke
har sai da ta jiyo shi kafin ya manna wayar da ɗan bakinsa ya bata sumbata. Ɗan
lumshe idanunta ta yi tamkar da gaske ya yi wa kumatunta, a hankali ita ma ta bawa
wayarta sumbatar, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har a
ransa ya ji kamar da gaske ta yi mashi, ya ji daɗi sosai. Da kyar ya iya katse
kiran, ya jima a kwance kafin ya tashi da kyar ya bi bayan Abbonsa.
A ɓangaren King kuwa, shirye shirye suka fara yi babu kama hannun yaro, suna gama
zama yasa Momma ta kira Smart ta bashi umarnin a kan ya dawo da Auta, nan da gobe
su dira a kingdom of power, sai dai King ya ce kada su kuskura su sanar da Smart
ɗin auren Auta za'ayi, a ɓoye mashi sai ranar ɗaurin aure ya ji a masallaci, ita ma
Auta a ɓoye mata sai an ɗaura auren sannan a bayyana mata, a dawo da ita ta shiga
dilka da halawa game da kunshi da sauran gyare-gyare.... Kam bala'i, lallai King ya
shirya da zafansa, wato sai an ɗaura aure zasu sani, tab akwai cakwakiya.
Momma ta ji zafin hakan, amma yazamar mata dole ta bi umarnin King, dole su
hakura.
-------------------------------------------------🔥
Rasa mafita yasa shi nufar kofar da nufin ya buɗe kawai. Sai addu'a yake yi Allah
yasa ba shigowa ciki Omaid zai yi ba, ga shi ya cire kayan jikinsa, ga mace kwance
a saman bed ɗinsa, me za'a zarga kenan? Ya gefawa kansa tambayar. Tamkar wanda kwai
ya fashewa a ciki haka yasa hannu ya buɗe door ɗin. Suna haɗa ido Omaid ya ce. "Yah
Omar barci zaka yi ne?". Ai bai san time da ya gyaɗa mashi kai ba, alamar e barci
zai yi. "Dama na zo mu yi hira ne fa, yau na ɓata da Obaid, amma tin da barci kake
ji no need, bari in je wajen Momma kawai". Kara langwaɓar da kai guyson ya yi, ya
ƙara shagwaɓe fuska alamar da gaske barcin yake ji. A hankali ya jinjina kai yana
ƙaƙalo hammar dole. Juyawa Omaid ya yi yana yiashi good night. Ai yana barin wajen
ya mai da kofa ya garƙame tare da juyawa da gudu ya koma cikin ɗakin, saman gadan
ya haye ya zauna tare da buga uban tagumi tana tinanin meyakamata ya yi ne?. Nan fa
ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsar ya bari sai dare ya yi sosai, kowa ya yi barci sai ya
mayar da ita bedroom ɗinta. Na'am ya yi da wannan shawara, sannan ya fara binta da
kallo, gabaɗaya ta tafi da tinaninsa, bare ma ɗan bakin tsiwar nan tata, ga shi ɗan
ƙaramin amma sai iya fito da magana. Hannu ya kai saman ɗan bakin nata ya ɗan ja da
ɗan karfi kafin ya ce. "Masifaffa kawai!". Ya yi maganar idanunsa a kan yatsun
hannunta dake zara zara ƴan sirara. Haka ya yi ta bi yana karewa surar jikinta
kallo har dare ta tsala, sannan ya miƙe ya zura jallabi a jikinsa. Ya nufo waje,
sai da ya gama leƙe leƙensa ya tabbatar babu kowa, sannan ya zo ya ɗauketa ya mayar
da ita bedroom ɗinta. Wani irin ajiyar zuciya ya rinƙa saukewa time da ya dawo
bedroom ɗinsa, saman bed ya haye da nufin ya yi barci, yau ko sleeping dress ba
za'a saka ba, sai dai kuma barcin sam sam taki zuwa, tinaninta ne kawai fal a cikin
ransa har kusan asuba, yarasa dalilin dayasa yake tinaninta sosai haka. Daga karshe
dai ya miƙe ya ɗauro alwala tare da hayewa saman dadduma ya fara nafilfili tin da
kyan Mahreen ya azalzali zuciyarsa ya hanasa rintsawa.
-----------------------------------------------🔥🔥🔥
Ko daga ina ya koyi yiwa mata wanka? To dai yau ya yi wa Mahnoor wanka, kuma da
kansa ya bata kayan da yake so ta saka, sannan ya rungumeta suka kwanta a tare.
Zuciyarsa fara tas yau, ya yi barci mai shegen daɗi, ita ma ta yi barci mai shegen
daɗi, yau gata ga Hammanta. Washegari da safe, bayan sun yi sallar asuba dama sun
koma barci, karfe 7 ta farka, cikin sanɗo ta kwaci kanta daga garesa, a hankali ta
sauko kasan bed ɗin, kai tsaye ta nufi waje, bedroom ɗinta ta koma, alkyabbarta ta
ɗauko ta ɗaura a saman kayan jikinta, cikin sauri ta fita ta nufi bedroom na momma,
wai dan ma kada momma ta gane a tare da mijinta ta kwana, irin ta nuna a part ɗin
momma ta kwana, dan sun yi da momma ɗin a kan ba zata koma wajen Jaish ba sai ya zo
ya bada hakuri, shi ne wai zata yi wayau.
Zaune ta isko momma a saman King sofas set masu bala'in kyau na cikin bedroom
ɗinta, hannunta rike cup na cappuccinon tana sha. Binta da kallo ta yi, sosai
Mahnoor ta shiga shakku da kame kame ganin irin kallon da momma take binta da shi.
Daurewa ta yi ta kariso gabanta ta tsugunna dan ta kwashi gaisuwa. Still binta da
kallon mamaki Momma take ta yi. "Ina kwana Momma?".
Shiru momma bata amsa gaisuwar ba, wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji, addu'a ta
shiga yi Allah yasa ba fushi Momma take yi da ita ba. A dai'dai wannan lokacin
Omaid ya shigo, a kusa da Momma ya ƙariso ya zauna. Yana sauke kallansa a kan
Mahnoor ɗin ya ce. "Momma wannan mahaukaciyar fa?". Shiru dai Momma bata tankasu
ba, kallanta a kan Mahnoor babu ko kyaftawa, kuma ba kallan tuhuma take binta da
shi ba face kallan mamaki, abin abin dubawa ne!.
Zama Mahnoor ta yi a kan kafafunta, ta rasa abin yi, sai kawai ta yi ƙasa da kai
tana jiran hukuncin da za'a yanke mata....... Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo,
yana sanye da white arabs jallabiya, a kusa da momma shi ma ya je ya zauna, ya wani
ɗaure fuska kamar ba Jaish da ya gama holewarsa daren jiya ba, har mamakinsa
Mahnoor ta yi, ya wani basar kamar bai ganta a wajen ba, cikin ladabi da biyayya ya
ɗagawa Momma gaisuwa.
Nisawa ta yi tare da maido da kallanta a kansa, a hanzarce ya yi ƙasa da kai yana
ɗan shafa kansa. Amsa mashi gaisuwar Momma ta yi tana kare mashi kallo tamkar mai
san gane wani abin. "Momma dama zan je office ne na ce bari mu gaisa first". Ya
faɗa yana satar kallan Mahnoor dake kallan ƙasa. Tini Omaid ya natsu tsit kamar
babu shi a wajen, da zai yi wa Mahnoor walaƙanci, da ganin Jaish yasa ya janye
kalamansa ya bita da ido kawai........ "To shikenan, idan ka je office ɗin ka gyara
shirin dake office ɗin naka, dan jeren da ka yi a wajen bai yi ba sam sam". Cewar
Momma. A hanzarce ya ɗago ya kalleta jin abin da ta faɗa. Hararar wasa ta wurga
mashi kafin ta yi mashi alama da Mahnoor da ido. Da sauri ya yi ƙasa da kai, kunyar
rashin kunyar tasa ta motsa!..
Sallamar guyson ne tasasu kai kallansu a bakin kofa dikka har da Mahnoor ɗin. Ai
yana sauke idanu a kanta bai san time ɗin da ya kwashe da dariya ba, har da rike
ciki yana duƙawa ƙasa. Kallan mamaki ta bisa da shi, ta rasa gane me yake yi wa
dariya. Ai Momma ma bata san time da murmushi irin nasu na manya ya kubce mata ba
ganin yadda guyson yake dariya, dama tun ɗazun dariya kamar zai haukatata, da kyar
ta iya dannewa ta ɓoye, sai ga shi guyson ya zo ya sanyata murmusawa.
Ɗan tsuke fuska Mahnoor ta yi tana bin guyson da kallo. Cikin dariya ya ce. "Aunty
Mahnoor wace mahaukaciyar ce ta yi maki wannan make up ɗin? Kin ganki kuwa? Ko
aljana Bilkisu sarkin kwalliya bata gwada maki hauka ba yau". Ya kai karshen
maganar tare da kara kwashewa da dariya mai sautin gaske.
A hanzarce Mahnoor ta kai hannu ta shafi face ɗinta, jin alamar kwalliya yasa ta yi
gaggawar ɗago ido ta kalli Jaish. A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta kamar
ba shi ba.
"Yah Omar kana nufin kwalliya aka mun?". Ta faɗa tamkar zata
Book Chapters
Chapter 77
Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500