You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki tsaya ki faɗa mun, in ba haka ba in na kamaki i will give you
a hot punishment"...... Tana ƙoƙarin buɗe kofa ta amsa mashi da. "Fara kama ni ɗin
tukunnan before you think about the hot punishment da zaka yi mun ɗin"........ "Kin
rai'nani ko? Yau Allah ba zan barki ba". Ya kai karshen maganar tare da bin bayanta
da gudu. Tini ta buɗe kofar ta yi waje tana dariya tana kara faɗin maza ya zo idan
ya isa.

A gaggauce Black Tiger ya matsar da su daga gaban mirrornsa, dama su yake
kallo, wani irin farinciki yake ji idan yana kallansu, amma kuma baya san su kama
shi yana kallonsu, in dai yasan za su zo bedroom ɗinsa sai kuga ya fiske kamar bai
san da su a empeir ɗin ba, alhalin munahiki ɗan air daɗin ganinsu yake ji, har da
wani pretending ya yi gaggawar barin gaban mirror ya dawo tsakiyar bedroom ɗin
nasa, sanye yake da bathrobe, linƙaya fa zai je yi a cikin karamar pool ɗinsa dake
sama, amma da yaga suna dirama sai ya tsaya kallansu.

Da gudu Sweetie ta faɗo cikin bedroom ɗin nasa tana dariya tana kara faɗin Ronnie
ya zo in ya isa. Da gudu shi ma Ronnie ya faɗo ɗakin yana faɗin Allah sai ya kamata
yau, dan dole ya gwada mata akwai banbanci tsakanin mata da maza, ta ce idan bai
kamata ba shi rago ne, dan haka shi ba rago bane dole ya kamata. Bayan Black Tiger
ta zo ta tsaya tana haki tana faɗin. "Yi sauri ka zo, gani a bayan big bro kuma our
shield".

Wani irin Black Tiger ya ji a ransa, kenan Sweetie tana yi mashi kallan shi
garkuwansu ne, bango majinginansu? To in dai haka ne meyasa zai rinƙa cutar da ita?
Meyasa ba zai ɗauketa kamar Ronnie ba tun da ita ma ta ɗaukesa yaya tamkar yadda
Ronnie ya ɗaukesa?......... Da gudu Ronnie ya nufota, a guje ta fara kewaye Black
Tiger yana binta tana tikar dariya tana kara tunzura shi a kan ya zo ya kamata.
Sosai hakan ya yi wa Black Tiger daɗi, sai yake jin kamar dikka kannensa ne na
jini, farincikin da suke ciki suna nishaɗi ya nishaɗantar da shi shi ma matuƙa.

Sosai ta yi gudu har ta fara gajiya, kun san kewaye take yi hakan ya haifar
mata da ganin wani irin jiri mai karfi yana ƙoƙarin ɗibanta. Ronnie ya lura da haka
sai ya ce. "Now is my time, zan kamaki in kuma hukuntaki".... Tana haki sama sama
ta ce. "Ba zaka taɓa kamani ba saboda big bro ba zai bari ka hukuntani ba". Tana
kai karshen maganar ta tafi zata kifa dai'dai lokacin ta zago ta gabansa. Cikin
zafa yasa hannu ɗaya ya riko wuyar rigar jikinta, tafiya ta yi gabaɗaya ta faɗa
jikinsa tana numfashi sama sama, ta sanya hannunta ɗaya a saman shoulder ɗinsa ta
wajen damatsan hannunsa tana cigaba da yin haki.

Da gudu Ronnie ya zago da nufin ya kamata, tin bai ƙariso ba ya ce. "Nakamaki
ai yanzu". Ya kai karshen maganar haɗe da sa hannu zai capko shoulders ɗinta. A
miliyan Black Tiger ya ɗagata da hannu ɗaya ya juya da ita alamar ba zai bari
Ronnie ya kamata ɗin ba kenan........... Sosai Ronnien ya yi muguwar mamakin ganin
hakan, bai taɓa tinanin hakan ba ko a mafarki, kenan Black Tiger ya shigar mata
faɗa? Ya jefawa kansa tambaya, lokaci guda kuma ya ji wani irin sanyi a ransa, dan
hakan ma wata nasara ce a garesu, tabbas ko a iya haka big bro ya fara canzawa,
Allah mai iko.
Amma saboda su cigaba da samun nasara sai bai nuna mamakinsa a fili ba, sai ma
ya haɗe fuska tare da cewa. "Kenan haɗe mun kai zaku yi? Yanzu big bro kenan ka
shigar mata? Wannan ojoro ne, kuma ban da ojoro, ka bari kawai in kamata". Ya kai
karshen maganar tare da sake kai mata capka zai kamata, sake juyawa da ita Black
Tiger ya yi, saboda sun tafi da imaninsa har bai san time da ya ce. "Ba zan bari ka
kamata ɗin ba". Wlh bai ma san ya yi wannan magana ba.

Daga ita har Ronnien sai da mamaki ya daskarar da su na ƴan dakiku, kai abin
al'ajabi wai ba zai bari Ronnie yakamata ba, like wow abin ya ƙayatar ba shakka, da
alama yau Allah ya amsa addu'ar Sweetie yasa zuciyar big bro ta fara sauyawa, dama
ta jima tana yi mashi addu'a, kullum tsakar dare sai ta tashi ta yi nafilfili ta yi
mashi addu'a, har ta fara cire ran addu'arta zai amsu, ashe kuwa yana hanya. A
cikin zuƙatansu gabaɗaya suka shiga faɗin alhamdulillah, alhamdulillah sun nuna
godiyarsu ga Ubangiji matuƙa, yau big bro nasu ya shiga maganarsu, kai ba zasu taɓa
manta wannan rana ba.

Cigaba da binta Ronnie ya yi yana san kamata mamaki kamar zai kasheta, shi kuwa
Black Tiger ya cigaba da kaucar da ita yana faɗin Ronnie ba zai kamata ba, tin da
ta kasance mai rauni tana da shi wanda shi kuma ba mai rauni bane. A takaice dai
sai da Ronnie ya gaji lilis ba tare da ya iya kamata ba, shi kuwa Black Tiger yana
tsaye waje guda ya yi nasarar wahalar da Ronnie har ya gaji ya durkushe a wajen
yana haki yana faɗin. "Wannan ojoro ne, ba dan kai ba big bro Allah da na kamata,
kuma ni ban yarda da wannan ojoron ba, amma ba komai zamu haɗe anjuma ne ai". Ya
kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Bari in duba
parents na Floris, zan je in apologies, zan ɗaukota in dawo da ita, i really missed
her to much".

Lokaci guda face ɗin Black Tiger ya sauya jin kalaman kanin nasa, dan yasan me
zai biyo baya idan Ronnie ya je can, ga shi bashi da hanyar dakatar da shi. Shiru
ya yi bai iya dakatar da shi ba har ya fita daga bedroom ɗin har lokacin yana haki
kaɗan kaɗan. Yana fita Black Tiger ya sauke Sweetie, cikin gaggawa ya wuce ya nufi
wani siririn stair case dake cikin bedroom ɗin ya haura sama in da pool ɗinsa take.
Da kallo Sweetie ta bi bayansa tana jin wani irin fargaba, gabanta na faɗuwa sosai.

Almost 5 mins tana tsaye a wajen, daga karshe ta yanke shawarar bin bayansa,
domin tana san yin magana da shi. Ba tare da tsoro ko tinanin menene a saman ba ta
yi maza ta haura ita ma...... Like wow, wani irin yanayi ta tsinci kanta a lokacin
da ta haura saman nan, domin kuwa wani haɗaɗɗen waje ne wanda sai ka yi zatan ba a
duniya kake ba, blue light ne a wajen, tamkar ɗaki haka aka yi shi, kazalika blue
light ne a cikin kwayayen bulb dake cikin pool ɗin, hakan yasa suka sanya ruwan ya
koma blue sosai, ga wani kamshin dake tashi a wajen, abin dai ba'a magana.

Yana tsundume a cikin ruwan, ya lume gabaɗaya jikinsa, iya kansa ne kawai a waje,
ya ɗaga kan nasa sama haɗe da lumshe kyawawan shape eyes ɗin nasa tamkar mai
tinanin wani abin. Tabbas ya ji motsinta, amma bai ji kamar zai buɗe idanunsa ba.
Cikin natsuwa ta tako ta nufo in da yake, a gabansa ta tsugunna tare da kurawa
kyakkyawan face ɗinsa idanu. Lokaci guda ta ji wani irin shock a jikinta, ko
idanunsa a rufe wlh kwarjini ne da shi sosai........ "Please ka faɗa mun menene ya
samu Floris?". Ta jefa mashi tambayar cike da fargabar amsar da zai bata, kirjinta
har wani dukan uku uku yake yi, Allah Allah take yi kada ya ce mata wani abin
mummuna sosai ne ya sameta, har yanzu dai basu bata mutuwa ba.

Shiru bai amsa ba, kuma bai motsa daga in da yake bama, saboda kwata kwata baya
san tina zancen.......... "Tabbas akwai abin da kake ɓoye mana, tabbas akwai abin
da ya samu ƴar uwarmu, tabbas naga hakan a cikin idanunka a lokacin da Ronnie ya ce
maka zai je dubata, please ka sanar damu menene ya sameta ko zamu ji sanyi a
ranmu". Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa da kwallah, saboda tabbas taga
rashin jin daɗi a kwayar idanunsa a lokacin da Ronnie ya ce zai je ya duba iyayen
Floris ya basu hakuri.

Nan ma dai shiru bai yi magana ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa.
"Shirunka ya fi komai kona mun rai, shirunka dai'dai yake da amsar cewa Floris is
not alive, shin haka ne?"...... Ai bai san lokacin da ya tsinci kansa da girgiza
mata kai alamar a'a ba haka bane, kuma ya yi hakan ne gudun balain da zasu tayar
mashi ita da Ronnie, yau ita ce ranarsa ta farko da ya fara yin karya a kan wani
abin dan gudun samun matsala da su.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta canza murya zuwa na nuna kauna da soyayya ta ce.
"Har ƙasa na ji sanyi a rai'na, to faɗa mana in take?". Ta kai karshen maganar tana
kallan zara zaran eyelashes ɗinsa da suka kara tsawo sosai suka kara bayyana saboda
rufe idanun nasa da ya yi. Ɗan zuba masu idanu ta yi na ƴan sakanni kafin ta mayar
da kallonta izuwa saman kyakkyawan wuyansa, a hankali ta mai da kallonta izuwa kan
lallausan gashin kansa da yake bakin kirin yana wani curlyn, kaɗan ya kwanto mashi
ta gaban goshinsa ya manne saboda ruwan da ya jiƙasa, hakan ya kara fito da
tsantsar kyansa. Kan kyawawan romance pink lips ɗinsa ta dawo da kallonta, shiru ta
zuba masu idanu tana jin tamkar tasa hannu ta taɓa su saboda sun haɗu matuƙa, sun
kuma tafi da ita.

........ A hankali ya waro idanunsa wajen domin ya kalli meyasa ta yi shiru a
wajen. Yana buɗe idanu ta yi saurin dawo da kallanta kan idanun nasa, zubawa juna
idanu suka yi babu ko kyaftawa, kamar waɗan da suka afka duniyar tinani. Cikin
dabara ta kai hannunta cikin ruwan ta ɗan ɗebo, saboda tsabar shegen tsokana ya yi
mata over yarinyar nan, cike da tsoron abin da zai iya aikara mata a face ɗinsa ta
watsa mashi ruwan. Wani irin lumshe idanu ya yi, har cikin ransa ya ji saukar
wannan ruwa, sai ya ji tamkar ba ɗaya yake da ruwan da yake ciki ba, ji ya yi
wanda ta watsa mashi ɗin tamkar na daban ne. Slowly ya sake waro idanun nasa a
kanta haɗe da ɗan zarosu kaɗan.

Tsorata ta yi, a tinaninta hukuntata zai yi, dan haka sai ta yunkura ta miƙe da
gudu zata bar wajen. Cikin zafa ya sanya hannunsa ya capki dogon gashin kanta ba
tare da yasan ya yi hakan ba, ai tafiya ta yi gabaɗaya ta afka cikin ruwan ta faɗi
saman lion chest ɗinsa. Lokaci guda ya ji wani iri a jikinsa, while ita kuma
tsorata ta yi sosai, da kyar ta iya janyo numfashinta ta cigaba da tafiya daidai,
murya na kerma ta fara faɗin. "Wayyo na shiga uku, am so so sorry big bro, na tuba
ba zan sake ba". Tana magana tana zazzare idanu haɗe da ƴan kame kame, take ta yi
kasa da hannunta izuwa cikin ruwan ta ɗaura saman flat tummynsa.

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, slowly ya ɗan yi blinking eyes
ɗinsa ya sake tsaidasu a kanta, while ita ma shi take kallah, a yanzu ma sake tsare
juna da kallo suka yi, take ya fara hasko wasu sirrika na musamman dake tattare da
kwayar idanunta, kamar dai akwai wani buri da take san cinmawa a rayuwarta. Ita ma
kuma karanta kwayar idanun nasa take yi, saboda taga alamar akwai abin da yake
hidden masu.

Tsit wajen ya yi, sun mace da kallan juna, cikin salo ya ɗan motsa romance lips
ɗinsa da nufin ya yi mata magana ba tare da ya kawar da kallansa daga kanta ba, sai
ta rigasa da cewa. "Please our big bro ka faɗa mun ina Floris take?". Ta yi maganar
tana ɗan hauro da hannunsa izuwa saman lion chest ɗinsa ta cikin ruwan kenan. Babu
riga a jikinsa fa, daga shi sai Swimming short, ya cire bathrobe ɗin.

Tamkar wanda bakinsa yake yi mashi ciwo, baya san motsasu haka ya ɗan motsasu wajen
cewa. "She died". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar....... A razane ta wani irin
zaro mashi eyesball ɗinta tamkar kwayar zasu firfito su faɗi ƙasa, tana ƙoƙarin yin
magana cike da tashin hankali ya yi saurin sanya hannunsa ya rufe mata baki, a
hankali ya girgiza mata kai alamar a'a ta yi shiru. With his lion voice ya fara yi
mata bayani wanda bai bawa kowa damar sauraron abin da yake faɗa ba, sai da ya kai
karshe daga nan ga rufe maganar nasa da cewa ta san yadda zata yi da Ronnie kada ta
bari ya birkice sosai, ta taya shi ɓoye mutuwar Floris har zuwa wani ɗan lokaci,
kada su sanar da Ronnie.

Ai yadda kuka san ruwa ya cinye Sweetie, ta kasa motsawa daga in da take, tamkar
wadda ta sume, idanunta a kansa kuma babu ko kyaftawa.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




51




🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Kurawa face ɗinta idanu ya yi, sai yau ya tabbatarwa da kansa cewa Sweetie
kyakkyawar gaske ce, ta sume mashi amma idanunta a buɗe, ɗan lumshe idanunsa kaɗan
ya yi tare da sake buɗesu a kanta, hannunsa ya ɗago, tafukan hannun nasa ya ware
tare da shafa face ɗinta da shi, take ta ja doguwar numfashi, da alama magic ya yi
mata ta farfaɗo. Kamar mai raɗa haka ya fara raɗa mata cewa kada ta bar Ronnie ya
fahimci abin da ya faru, ta yi mashi dabara, daurewa ta yi ta yi ta mazan cewa sai
dai idan shi ma zai yi mata wani alkawari, in ya yi mata hakan ita kuma ta yi mashi
alkawarin Ronnie ba zai taɓa shiga wata damuwa ba izinin Allah.

Jama'a ku tafawa addu'a, lallai ne addu'a bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, sai dai
jinkirin amsawa, da izinin Allah addu'ar Sweetie a kansa ta karɓu, black heart ɗin
ta fara sassautawa!.

Jinjina mata kai ya yi alamar ya yarda da batunta tin ma bai ji wani irin alkawari
bane, Ronnie amanarsa ne, kun san da cewa amana mahaifinsa ya bar mashi Ronnie? Kun
san da cewa sai da ya rokesa da kada ya bar hawayen Ronnie ya zuba a banza?. Kun
san da cewa kafin mahaifinsu ya rasu ya yi wa baban nasu alkawarin in dai yana
numfashi to ba zai taɓa barin hawayen kanin nasa ya zuba ba? Shiyasa kuke ga zai
iya aikata komai a kan kanin nasa, kuma yana bala'in sansa na haƙiƙa shi ma, ba wai
dan iya alkawarin da ya ɗauka bane yasa yake kula da shi, yana kaunarsa sosai.

Ɗaga ƴan kafafunta ta yi tana san kai tsawonsa dan ta yi mashi raɗa a kunne, sai
dai ina, bata iya kaiwa tsawonsa ba, ya fita nesa ba kusa ba, yana da tsawo sosai.
Ganin hakan yasa ya rage tsanwonsa ya ɗan rankwafo kanta, hannu tasa ta saƙalo
wuyansa kafin ta gwada sake ɗaga kafa ko zata kai. Sai dai kash bata kai ba, hakan
yasa ya ɗagata cak sai saman lion chest ɗinsa, hakan ya bata damar kwanto kanta a
saman shoulder ɗinsa, ta kai ɗan bakinta saitin kunnnesa, nan ta fara yi mashi
raɗan yarjejeniyar da zasu yi kafin ta yi mashi aikin kula da Ronnie, idan ya
aminta tabbas zata kula da Ronnie sosai wajen sanya shi farinciki.

Hakika maganganunta sun zo da tsauri, sai dai kuma farincikin Ronnie ya fi mashi
komai, kuma babu in da Ronnie ɗin yake samun farinciki na wuce misali face a
wajenta, dan haka yazamar mashi dole ya aminta da wannan yarjejeniya in ba haka ba
akwai matsala. Shiru ya yi yana tinanin ya amince ko kuwa ya daure ya juri tashin
hankalin da Ronnie zai shiga?. A wannan hali Ronnie ya shigo wajen ya samesu,
fuskarsa ɗauke da damuwa matuƙa ya ƙariso in da suke.

Ai yana sauke kallansa a kan yayan nasa da Sweetie bai san time da ya saki cool
murmushi ba, sun yi matuƙar burgesa, da sauri ya tsugunna a gaban pool ɗin, cikin
sanyin murya ya ce. "Wow you guy's looks so very cute and amazing"....... Maganarsa
ya fargar da Black Tiger har ya yi saurin zare kallansa daga kanta, kamar wani
maras gaskiya ya yi saurin saketa ya kuma ɗan yi ƙasa kaɗan ya kara lumewa a cikin
ruwan kaman mai san ɓoye wani abin. Ita kuwa, da tsantsar tashin hankalin da take
ciki yaki ɓoyuwa a kan face ɗinta ne ta juyo da kallanta ga Ronnie, tamkar zata yi
kuka, ta ƙasa yin magana, dan yanzu ganinsa yasa wani irin tausayinsa ya kamata.
Take yanayin face ɗin Ronnie ya canza, dan ganinta cikin damuwa bai yi
mashi ba, kamar mai tsoronta ya ce. "Lovely sis big bro ya yi maki wani abin ne?".
Ya yi maganar yana satar kallan Black Tiger ta wutsiyar ido.

Kai kawai ta iya girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba. "Big bro me
ka yi wa lovely sis ɗita?". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar. Banza da shi Black Tiger
ya yi, sai ma ya kara lumewa cikin ruwan, tamkar bai san da su a wajen ba, da alama
kuma akwai abin da baya san su gani a jikinsa shiyasa ya yi ƙasa a cikin
ruwan........ Ronnie fa ya zo da kokensa ne a kan bai ga iyayen Floris ba, ya
tambayi mutanen birnin kuma kowa ya ce mashi bai gansu ba, shi ne ya dawo wajen
yayansa da kokensa dan ya nemo mashi su, amma yana tarar da su cikin wannan yanayi
ya tsinci kansa a cikin farinciki maras misaltawa.

Rarrashin Sweetie ya hau yi yana ce mata ta yi hakuri zai rama mata idan ma yayansa
ne ya yi mata wani abin, ita dai da okey kawai ta amsa mashi, amma na ciki kam yana
ciki. Sai da ya tabbatar ya sanyata ta yi murmushi, sannan ya juya ya ce da Black
Tiger. "Big bro ina iyayen Floris?". Ai Sweetie bata san lokacin da ta ce mashi.
"Sun gudu sun bar birnin nan wai saboda big bro ya kona masu ƴan uwa".

Ɗan zaro idanu Black Tiger ya yi jin ta fitar masu da hanyar da bai zata ba, dama
yana tinanin abin faɗawa Ronnie, gaskiya Sweetie she was very smart, ya jinjinawa
ƙwaƙwalwarta wajen iya fito da mafita cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ransa ta
sanyaya matuƙa da samun mafitarsu. Shi kuwa Ronnie ido ya zaro, kamar zai ɗaga
murya, sai kuma yasa kukan shagwaɓa tare da cewa shi lallai bai yarda ba! Dole big
bro ya nemo mashi in da suke, dan shi yana kaunar Floris, yana san ta dawo su
cigaba da rayuwa kamar da. Nan ne fa Black Tiger ya samu damar ce mashi zai nemo
mashi su soon ya kwantar da hankalinsa, yana magana yana satar kallan Sweetie da ta
tsare lip's ɗinsa da kallo.

Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke, ya ji sanyi a ransa za'a nemo mashi su. Sweetie ce
ta riko hannunsa ɗaya cikin nata, kamar mai raɗa ta ce matso ka ji wani abu lovely
bro. Matsar mata da face ɗinsa ya yi yana ɗan murmusawa. Matsowa ta yi dab
kunnensa, raɗa ta fara yi mashi tana sakin murmushi,. A hankali hankali murmushin
dake saman face ɗinsa ta fara faɗaɗa alamar kalamanta akwai sugar, suna shigarsa
yadda yakamata. Satar kallansu Black Tiger ya fara yi yana mamakin irin shakuwar
dake a tsakaninsu, a yanzu fa Ronnie ya fi farinciki idan yana tare da ita sama da
idan yana tare da shi, abin akwai mamaki. Tsabar daɗi da murnar jin kalamanta bai
san lokacin da ya afka cikin ruwan ba shi ma, a jikinta ya faɗa hakan yasa suka yi
kasan ruwan, dan bata da karfin ɗaukarsa. Shi dai Black Tiger abin ya birgesa
matuƙa, suna kashe shi idan suna tare!.

Juyawa Ronnie ya yi cikin sauri ta dawo saman jikinsa, sannan suka ɗago saman ruwa,
take ta fara jan numfashi da karfi karfi, saboda ta dannu kam. Riketa Ronnie ya yi
yana faɗin ta tsaya ya hura mata numfashinsa dan nata ya daidaitu. Sai dai bai kai
ga yin hakan ba take ta dawo daidai tamkar wadda aka yi wa magic, runguneta Ronnie
ya yi yana faɗin sorry a gareta. Ɗan rungunesa ita ma ta yi kafin ta amsa mashi da
ba komai. Cikin wasa ya ce. "Let play a game". Ɗan zaro idanu ta yi, game kuma a
cikin ruwa, ta jefawa kanta tambaya a cikin zuciya.
Tana can tana tinani Ronnie ya zaro hanki (handkerchief) daga
aljahinsu, dik ta jiƙe da ruwa, ɗaure mata idanu ya yi kafin ya saketa, ya sumbaci
lallausan kumatunta sannan ya ce to ta kama shi a cikin ruwan idan ya kirga one to
ten. A cikin ranta ta ji da biyu Ronnie ya ce su yi wannan wasa, amma ba zata ki yi
ba ko dan alkawarin da ta ɗaukawa yayansa na sanya shi farinciki na musamman, so
zata yi dik abin da yake so matsawar bai saɓawa shari'a ba.

Cauting from one to ten ya yi kafin ya lallaɓa ya gudu bayan Black Tiger ya ɓuya,
sannan ya ce mata let's go. Lalluɓarsa ta fara yi tana tafiya a hankali. Shi ma a
hankali hankali ya baro bayan Black Tiger ya matsa ya dawo ta bayanta, ya zamana
tana tafiya yana biye da ita a baya, sam bata jisa ba, gabaɗaya hankalinsa a kan
Black Tiger, ya tsare yayan nasa da kallo kamar mai nazarin wani abin. Sai nemansa
Sweetie take yi tana zagaye cikin ruwan, ga shi ruwan ya fi karfinta, dan har wuya
ya kai mata, dan dai ba ruwan gudu bane, da ba zata tsira ba. Ta sha kewaye a wajen
bata ji alamarsa ba, dab kusa da Black Tiger ta tsaya, suna fuskantar juna ba tare
da ta sani ba, Ronnie na bayansu, a shagwaɓe sosai ta saka kuka tana faɗin. "Ni
lovely bro ka zo ka kwance mun wannan abin, ka ɓuya nakasa ganinka..........." Bata
kai karshen maganar ba Ronnie ya tureta da karfi ta tafi sai saman lion chest na
Black Tiger.

Murmushi ya saki kafin ya ce. "Dama a manne da juna na sameku, ni na rabaku, yanzu
kuma da zan tafi shi ne na mayar daku yadda na ganku". Yana kai karshen maganar ya
yi zafan fita daga cikin ruwan wai dan ma kada Black Tiger ya kama shi, abin gwanin
ban dariya kuma gwanin birgewa. Yana fita bai dakata ba ya yi gaggawar barin wajen
ya koma cikin bedroom ɗin Black Tiger. Ita kuwa Sweetie ƙoƙari kwace abin dake
idanunta ta yi dan ta samu gani, sai dai ta ƙasa, saboda yadda kuka san padlock aka
sanya aka datse hanki ɗin, yaki kwancuwa ko kaɗan.

(Anya ba Black Tiger ya rike shi ya hana shi kuncuwa ba kuwa? Ɗan duniya ba! Ka
gansa kaman wani salihi, ɗan rainin wayo.😅)

"Big bro please remove this thing for me". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Kamar
babu Black Tiger a wajen, ya yi banza da ita idanunsa a kan face ɗinta, kaman mai
nazarin wani abin. Laluɓe ta fara yi tana ɗan tattaɓa jikinsa dan ta tabbatar da
yana wajen ne ko dai baya nan, ta yi magana without reply, shi ne take zaton ko dai
baya wajen ne.

Lokaci guda ya yi wani danko hannunta ɗaya cikin zafa, ba komai yasa hakan ba kuma
face a garin laluɓenta take ƙoƙarin sake capke mashi hero kamar dai ta ranar.....
Ajiyar zuciya ta sauke jin ya damki hannunta, hakan yasa ta fahimci yana wajen
kenan. Can ƙasa ta tsinkayo lion voice ɗinsa yana faɗin. "Na yarjewa
yarjejeniyarki, amma kada ki wuce gona da iri".

Yarjejeniyar me kuke tinanin ta ce su yi? Sweetie akwai wayo sosai wlh, da alam
tarko ta ɗana mashi. "To shikenan na yarda, amma yanzu dai kwance mun wannan abin".
Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

"Hakan baya cikin yarjejeniyarmu, and ai bani na ɗaura maki ba". Ya faɗa a sanyayye
sosai................ Ɗan rainin wayo, so yake ya yi ta kalle mata fuska kada ta
san ya kalla, shiyasa ya ce ba zai kwance mata ba, saboda ba kara mun kyau ta yi ba
a yadda ruwa ya jiƙata, gashin kanta ya kwanto har face ɗinta, lip's ɗinta sun kara
kyau matuƙa saboda ruwa da ya taɓasu, gashin gaban goshinta sun kara kwanciya luff,
ko makiyinta ya ganta yasan ta yi kyau over, kuma sai ya shagala da kallonta bare
kuma shi Black Tiger da ba kiyayya suke yi ba, bashi da wata matsala da ita,
hasalima yanzu yana san ta kasance da su dan ya lura kaso 60 cikin ɗari na
farincikin Ronnie yana tattare da ita, so bashi da wata matsala da ita yanzu......
Ni kuwa

Please Login or Register in order to submit comment