You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da ita.

Cike da mamaki Aunty MieMie ta fara binsu da kallo, taga yan kauye jiki dik datti,
zaro idanu ta yi lokacin da ta ga momma ta ɗago Mahreen ta rungume tana
rarrashinta, kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Momma waɗan nan fa daga ina?".

Fanan ma mamaki ne ya kamata, sai dai bawai kyamarsu take ji ba, kawai dai mamakin
ganinsu take yi.

"Fanan ɗaukesu ku je ɗakin Zunaira da su, ki taimaka masu su yi wanka ina zuwa
da kaina na basu kaya da kuma abinci". Cewar momma da ta dawo da kallonta a kan
Fanan.

Fanan yarinya mai biyayya, bata yi wani magana ba ta ce su zo su tafi, sai dai taki
matsawa kusa da su dan tana ganin datti a jikinsu. Mannewa da juna suka yi,
dikkansu sai kuka suke yi, sun ki motsawa bare a sa ran zasu bi Fanan.

"Mahnoor ku yi hakuri ku je tare da Fanan kun ji?". Cewar Momma.

Kin motsawa suka yi, Mahnoor ce ma ta yi ta mazan cewa. "Mu kam a mayar da mu
wajen bappanmu, ba masan nan". Tana magana tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Take momma ta ji tausayinsu ya kamata, Allah sarki dole su yi kuka basu taɓa zuwa
irin wannan waje ba.

Matsawa kusa da su Aunty MieMie ta yi, dan kun santa da fahimta, ta fahimci koma su
wanene su ba shakka momma ta ɗaukesu da mahimmanci, sannan kuma da kallo ɗaya ta yi
masu ta ji yaran sun burgeta, sai ma taga kamar kannenta, saboda suma fafaren fata
ne.

Rarrashinsu ta taya momma yi, sannan ta ce Fanan ta zo ta kama hannunsu su je. Sam
Fanan bata san taɓasu, dan kada su saka mata datti a jiki, ita ma yanzu ta ji
kyamarsu yakamata saɓanin ganin farko da ta yi masu, har da ɗan kawar da kanta wai
suna wari, amma da yake Aunty MieMie ce ta ce ta zo ta kamasu su tafi sai bata musa
ba, ta matso ta rike hannun Mahnoor kamar wadda ta rike kashi, haka ta wuce gaba
suna rungume da juna suka rufa mata baya.

Da kallo momma da Aunty MieMie suka bisu da shi har suka fice. Suna fita Fanan ta
yi saurin sake hannun Mahnoor tana wani kwaɓe fuska game da toshe hanci, a fili ta
furta.
"Tab dik gidan nan ba ɗakin wanda ya kai ko kwatan ɗakin Auta a kyau da
tsaruwa haɗe da kayan alatu na more rayuwa masu bala'in tsada da babu su a kasar
nan, sannan ace waɗan nan ƴan datti kazaman za a kai can, gaskiya an cuci Auta".

Sarai Mahnoor ta ji abin da ta faɗa, saboda ita tana jin larabci, ita kuma Mahreen
ta ji wasu bata iya jin wasu ba, to kun dai san Mahreen bata gani ta kyale, ta ji
ance masu ƴan datti sai ta ce.

"Wlh mu ba yan datti bane, mun yi wanka, sai dai idan kece ƴar datti, da
wani shegen idonki kamar na Hamma a wajen, wlh kin yi sa'a saboda Hamma zan ɗaga
maki kafa, da sai kin ci dukan zaginmu ƴan datti da kika yi!". Cikin harshen
fillanci ta yi maganar, hakan yasa Fanan bata gane me ta ce ba.

Tab da Fanan ta gane me kuke tinanin zai faru? Hajiya Mahreen manyan ƙasa, bata
gani ta kyale, ni yanzu tsorona ɗaya Mahreen ta iya larabci ta kuma haɗu da Sarina!
Kam bala'i wato akwai bidiri ba kaɗan ba, dan dai dik da a gidansu take wlh Mahreeh
ba zata ɗauki cin fuska da walaƙanci ba.

Mahnoor dai bata ce komai ba, sai ƙoƙarin goge hawayenta da suka zubo take yi,
dikkansu suna tafiya ne kankame da jikinsu, saboda suna ganin kamar zasu faɗi ƙasa,
dan in baku manta ba a hawa na sama suke, ta elvator suka biyo, su suna ganin kamar
zasu faɗi kasa yasa suka kame jikinsu waje guda.

Suna shiga parlon Auta Mahreen ta ƙanƙame Mahnoor tana ƙoƙarin sake yin kuka,
dan ita bata taɓa ganin irin waɗan nan abubuwa ba, ga tsoron mutuwa ga rashin kunya
kwando kwando cike da kai tab.

Ƙanƙameta Mahnoor ma ta yi suna jan kafaru, da kyar suka yarda suka karisa shiga
bedroom. Ai suna shiga ihu Mahreen ta saki, sai ma da idanunta suka sauka a kan
manya manyan teddys dake shirye saman bed da wasu a saman sofas dake cikin room
ɗin. Ihu Mahreen ta rinƙa yi wai ɗakin aljanu aka kawota zasu kasheta. Ita ma
Mahnoor tana san yin ihun amma tana jin kunya, sai ta danne tana ƙoƙarin rarrashin
Mahreen.

Fanan da sun gana kulata har wuya, ranta ya bakanta sosai ne ta dakawa Mahreen
tsawa a kan ta yi mata shiru ko kuma ta dalla mata mari yanzun nan. Ai banza
Mahreen ta bawa ajiyarta ta cigaba da ihunta tana faɗin a mayar da ita wajen
bappanta.

Fanan tana shirin kai wa bakinta bugu momma da Aunty MieMie suka faɗo cikin ɗakin,
hakan yasa Fanan ta janye kudurinta haɗe da ɗaure fuska ranta bai so shigowar su
momma ba, taso ne ta dallawa Mahreen mari ko guda ɗaya ne, dan ta ji bata sansu ko
kaɗa.

Wai nace ba, a haka fa Fanan bata san Mahnoor matar abin kaunarta Jaish bace, bata
san kishiyarta bace, da ta sani me kuke tinanin zai faru? Muje zuwa, akwai show fa.

Da gudu Mahreen ta saki Mahnoor ta yi wajen momma tana ihun a mayar da ita
wajen bappanta, ita bata san wannan gidan na aljanu ne.
Aunty MieMie da tin fitarsu momma ta sanar da ita su wayesu ne ta hau rarrashin
Mahreen haɗe da faɗa mata ba gidan aljanu bane.

Ai ina Mahreen ta ce bata san wannan magana ba, ita dai Jimeta kawai za'a mayar da
ita.

"Momma ki je ki yi wanka ki ci abinci ki huta bari zan rarrashesu". Cewar Aunty
MieMie da Mahreen ta ƙanƙame mata hannu.
Da yake momma a gajiye take sai ta amsa da to, sannan ta juya ta fita ta barsu da
Aunty MieMie ta cigaba da rarrashinsu.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangaren Jaish kuwa. Yana shiga bedroom ɗinsa cikin toilet ya wuce, hakan yasa ko
da Jawad ya shigo bai samesa a ciki ba.

A gefen bed ɗinsa Jawad ya zauna dan ya jirasa, saboda ya fahimci toilet ya shiga,
yana zama wayarsa ta fara ruri alamar shigowar kira. Cirosa ya yi daga aljihun
wandan kayan barcin jikinsa.

Jannawad shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin wayar, wato Jawad and Jannat su
ya haɗe cikin soyayya suka bashi sunan Jannawad.

Miƙewa tsaye ya yi, ya so yin magana da Jaish, amma kuma dole ya tafi wajen Jannat,
dan dama da kyar ya iya fitowa izuwa wajen Jaish, baya san yin nisa da ita saboda
halin da take ciki. Bedroom ɗinsa ya nufa kai tsaye, a hanya ya ci karo da Sarina
sanye da wasu shegun kaya na barci wanda kusan da su da babu dik ɗaya ne.

Riga ce doguwa wanda ta kai mata har ƙasa, ta kuma matseta sosai, sannan shara
shara ce, daga gwiwonta izuwa kasa ta gaban ribar a buɗe take, akwai wata tsaga a
wajen, dik wasu albarkatu na jikinta a waje, babban abin takaicin ma shi ne yadda
rigar ya matseta ya fito da murarar surar jikinta.

Tana wani taunar chewing gum hannunta rike da hotuna guda biyu, daga ɓangaransu
maman Yah Ramish ta fito, sai wani sakin murmushi take yi, kasancewar bata da
fara'a hakan yasa ake zargin murmushinta a dik lokacin da ta yi shi, sai ta shirya
mugunta take murmushi.

Wani irin ɗan iskan kallo da ya wurga mata ne yasa sai da ta yi tuntuɓe kafarta ya
turguɗe ta faɗi ƙasa, babu komai a wajen da zai iya sanyata yin tuntuɓe, amma sai
gata ta yi har ta kai ƙasa. Dik iskancinta da rashin kunyarta yau da kyar ta jawo
yawu ta haɗiye a wahalce tana ɗan datse idanu. Dik kuma saboda wannan kallo daya
dalla mata.

Shi kuwa ya rasa yadda zai yi da shegiyar yarinyar nan, idan ya ce zai daketa wlh
tsab zai iya kasheta ko ya sumar da ita, kunnenta ya fi na ƙashi tauri, yarinya ana
ga annabi tana rintse idanu, in suka biyeta wlh ba zata yi saura a wannan gida ba.

Tsabar tabbatar rashin kunya wai sai ta yi kasa da kai tana ɗaga mashi gaisuwa na
rashin kunya, irin ita bata ga kamar ta yi wani laifi ba. Yadda kuka san ya dallawa
jajir ɗin kumatun nan nata mari, takaici kamar ya take hegiya a kasar, a fusace ya
bar wajen gudan kada zuciya ta ɗebesa ya yi mata one blow seven die.

Tana ganin ya wuce ta bishi da matsiyacin harara tare da miƙewa tsaye, ta tsaya a
kan kafafunta, hannunta dikka biyu tasa ta rike waist ɗinta da shi, kasa ƙasa ta
furta.

"Ko uban me yasa ma ka warke daga ciwon son Jannat baka mutu ba bakin azzalumi?
In dai Mammie tana shakar numfashi ta fetsar dik abin da kake so ba zaka taɓa samu
ba, Jannat dai ta haramta a gareka, shi ma kuma Yah Rizwan ɗin da ya aureta ba zata
taɓa zame mashi alkhairi ba, sai ya gwammaci mutuwarsa a kan aurenta, dan sai ta
ɗanɗana mashi madarar azaba fiye da tunanin mutum, dan yanzu dab take da shiga
sarrafawar Mammie na, dik sai kun gane baku da wayo, dik a tafin hannunmu kuke
kanann marasa kunya!".

Cike da confidence take maganar, ta yi maganar ne bisa rashin sanin cewa Jannat
Jawad ta aura ba Rizwan ba, kun san ita da Mammiensu basu da labarin abin da yake
faruwa, Mammie na can part ɗinsu a kwance, ta yi karyar ciwo dan bata san ta zo
cikin family ayi hidimar biki da ita, shi ne wai bata da lafiya, suna can suna
shirya muguntarsu ita da ƴarta.............. Amma my people's me kuke tinanin
Sarina take nufi da cewarta saura kaɗan Chuchu ta shiga karkashin sarrafawar
Mammiensu? Anya ba wani abin a kasa kuwa?.

Hannunta ɗaya ta ɗaga izuwa dai'dai saitin face ɗinta, sannan ta naɗe yatsunta
dikka ta bar iya na tsakiyar a tsaya, cike da iskanci da iyashege ta ce. "Fuck you,
nonsense guy, zaka zo hannu ne yaro, soon kowa zai ɗanɗani kuɗarsa a cikin gidan
nan, sai ma na auri Yah Omerish, a nan ne zaku gane baku da wayo, dan wlh har dad
ma ba zan ɗaga mashi kafa ba, na godewa Allah da yasa Yah Omerish bashi da sauki
dik ubanku zai ci, ni kuma in juya shi yadda rai'na yake so banzaye kawai, ni yanzu
na wuce ajinku". Ta kai karshen maganar tare da fashewa da dariya kamar wata
zararriya.

Sai kuma ta yi saurin toshe bakinta saboda tana kusa da part ɗin Akka ce, kada
sautin dariyarta ya fita ya ja mata wata masifar, a hanzarce ta wuce izuwa part ɗin
uncle Abbas, ko tsoron Allah babu bare kunya haka ta tsaga tsakanin waɗan nan part
guda biyu, ta keta cikin warriors dake gadi ta nufi part ɗinsu da wannan ɗan iskar
shigar nata, dik wani mayaki ya ganta sai ya haɗiyi yawu, sai dai takasance guba a
garesu, dan sun san ko mutuwa suke yi ba samunta zasu yi ba, kallanta ma a sace
suke yi, dan kamasu suna kallanta ma ba ƙaramin laifi bane, kuma sai sun karɓi
tsastsauran hukunci.

Shi kuwa Jawad ransa a tsannin ɓace ya karisa part ɗinsa, sam baya san halin
Mammie, dik ita take goyawa Sarina baya har ta lalace haka, ya rasa yadda zai yi da
su, a yanzu yana takaicin a ce kannensa ne su ɗin.

Kwance ya isko Chuchu saman bed, tana kudundune a cikin bargo, jikinta ya samu
sauki fa aka sallamosu daga asibiti suka dawo gida, amma yanzu jikinta da ɗumin
zazzaɓi, ta kasa iya jurar rashin Auta, idan ta tinata sai kanta ya sara mata.

A gefen bed kusa da ita ya zauna, cikin sanyin murya ya tambayeta meyafaru ya ganta
a cikin bargo bayan ya barta lafiya lou zata shiga wanka? Ya yi maganar yana kai
hannun zai yaye bargon.

Kuka ta saka mashi haɗe da yunkurawa ta miƙe zaune. Jikinsa ta faɗo tana
faɗin................. "Yah Jawad yanzu da gaske sun ɗauke mun Autata? Ni dan Allah
kace su dawo da Auta su ɗaukeni ka ji?".

Cikin salon rarrashi ya ce...... "Ki yi hakuri, dad ya tura rungunar mayaka guda
sun tafi ɗaukota, nan da kwana biyu war haka Auta tana tare da mu In Sha Allah,
yanzu dai sauko ƙasa in baki abinci ki ci kin ji?".

Kankame rigar sleeping dress na jikinsa ta yi, kanta ta fara dirzawa a saman
kirjinsa, kamar zata haɗiye ranta ta fara faɗin. "Yah Jawad ba zan iya cin komai
ba".

"Why?". Ya jefa mata tambayar yana riko hannayenta cikin nasa............. "Ban
sani ba Auta ta ci abinci ko bata ci ba! A wani hali take ciki dikka ban sani ba,
Yah Jawad wlh ina ji a jikina Auta tana buƙatar taimakona, tabbas tana cikin
damuwa, domin idan bata cikin damuwa kirjina ba zai rinƙa bugawa da karfi a dik
lokacin da zuciyata ta ambaci sunanta ba, wayyo daddyna na shiga uku nikam, nasan
idan basu dawo mana da ita ba mutuwa zan yi".

Kuka take yi sosai, ya fahimci ta fara fita a hayyacinta, dan haka sai ya zage
wajen ganin ya rarraheta sosai, jikinta ya kara ɗaukar zafi sosai, Allah sarki bata
san shima cikin wannan tashin hankalin yake ba, damuwarsa ma shi ne Jaish ya samu
labarin ɓatar tata, ya twins bro ɗin nasa zai ji a ransa? Wanna yafi ɗaga mashi
hankali fiye da komai.

Ƙasa ƙasa ya yi da murya sosai, cikin salo mai jan hankali ya ce. "Jannat kina san
zuciyata ta buga in mutu ne?".

Kai ta girgiza mashi alamar aa bata so....... "To meyasa ba zaki barni in ji da
zafi biyu ba? Meyasa ke ba zaki saukaka mun ta ɓangarenki ba? Kina dai gani har yau
number Yah Rizwan bata shiga, sannan kuma su Yah Ramish sun ki haɗani da shi a
waya, kowa sai ya ce mun baya kusa ko ya yi barci, a jikina ina jin akwai abin da
suke ɓoye mun dange da shi da basa san in sani, saboda rashin lafiyarki na daure
ban ɗaga jirgi na je na same shi ba, sannan ga ɓatar Auta da ya fi komai ɗaga mana
hankali, ki daure ki yi hakuri Auta zata dawo kin ji?".

Kai kawai ta gyaɗa mashi amma ba wai dan zata iya daurewa ɗin ba. Da ya fahimci in
dai tana nan a cikin kingdom ɗin nan bafa zata iya daure rashin Auta ba, dan haka
sai ya yi wa P.A ɗinsa sms a kan ya yi mashi booking flight zuwa Dubai gobe da
sassafe, gara ya ɗauketa su je duba Yah Rizwan meyafaru tin da ya bar kingdom ɗin
wayarsa bata shiga? Daga nan su ɗan huta a can har a gane Auta ko kuma raɗaɗin ya
ragun masu sannan su dawo bayan kura ta lafa.

Yana turawa P.A ɗin nasa sakon ya ajiye wayar a gefen bed, sannan ya cigaba da
rarrashinta, shi dai bai more aurensa ba, matsaloli sai faruwa suke yi tin kafin
auren har kuma yanzu, amma dik da haka bai wani damu ba, saboda shi ma yana cikin
damuwar da ba zai iya gudanar da wani soyayya ba a yanzu.

Da kyar ya samu ta hakura ya buƙaci da ta zo ya bata abinci a baki, bata yi wani
musu ba ta yarda, dan balai'n yunwa take ji, rashin nitsuwa da kwanciyar hankali
yasa ta kasa cin abinci. Amma da ya zauna yana bata ta ci sosai, hakan kuma yasa da
ta gama ci da ƴan mintuna ta samu barci mai nauyi da daɗi ya ɗauketa wanda tin da
aka fara batun aurenta rabonta da ta yi irinsa.

Ganin ta yi barci yasa ya ja bargo ya rufeta tare da matsar mata da pillow kusa da
ita dan ta ji kamar shi ne a wajen, ya sauko kasa ya shiga toilet.

After some minutes ya fito ya shiga dressing room, cikin ƙanƙanin lokaci ya fito
shirye cikin brawn and milk arabs jallabiya, dadduma ya shinfiɗa ya tada sallah dan
neman saukin abin dake damunsa daga wajen Allah.

Sai karfe uku dare ta tsala, sannan ya sallame sallar tare da tsawaita addu'oi,
bayan ya kammala ya miƙe ya hau shirya masu kayansu da zasu yi tafiya Dubai gobe.
4:00 dai'dai ya kammala, sannan ya ɗan kwanta kafin asuba ya ɗan rintsa.

A ɓangaren su Mahnoor kuwa, kwata kwata sun ki cin abincin da momma ta saka aka
kawo masu, saboda basu taɓa ganin irin abincin ba, ga uban yawa, shake da tabkeken
tray, nau'ika daban daban abincin sai wanda ka zaɓa.

Amma dik sun ki ci, sun takure waje guda sunki sakin jiki, wanka ma Aunty MieMie ta
yi wa Mahreen da kyar da suɗin goshi, Mahnoor kuma ta nuna mata yadda zata yi ta
yi. Sun ki rabuwa da juna, sunki hawa gado, sun zauna a ƙasa, ba yadda momma bata
yi da su ba sun ki yarda, sun tsorata sosai ne. Mahnoor kayan Chuchu momma ta bata
ta saka, ita kuma Mahreen kayan Auta, amma kayan Autar sun ɗan yi mata yawa.

Da momma taga sun ki cin abinci sai ta ce Aunty MieMie tasa kuyanga Zubaida ta
dama masu fura da nono, shi kam ai zasu sha, kun san gidan sarauta ba'a rabasu da
tsabtataccen fresh nono da fura ai, dan haka sai Aunty MieMie tasa aka haɗo masu
mai rai da lafiya. Nan ne fa suka ɗan sha, Mahreen ta sha mai yawa, Mahnoor kuma
saboda kunyarsa momma da take ji kamar ta nitse kasa yasa ta ɗan sha kaɗan ba dan
ya isheta ba ta bari.
Da kyar suka yarda suka hau gadan Auta suka kwanta, momma tana zaune kusa da su har
sai da suka yi barci sannan ta fita, ba komai ya hanata fita ba kuma face kada su
yi ta ihu in ta fita, saboda sun ki yarda su hau gadan sai da ta hau a tare da su,
sannan ne suka kwanta, da Allah ya yi barci ɓarawo ya sacesu sai ta fita.

Bedroom ɗin mama Haulat ta shiga dan ta duba babyh Khadija da yanzu yaro ya sha
wanka, kyansa ta kara bayyana matuƙa, kamar ka sace shi ka gudu.

Nan ta isko shi da mama Haulat kwance saman gado suna barci, sosai momma ta ji
kamar ta ɗaukesa su koma bedroom ɗinta, amma kuma wajen King zata je, Aunty MieMie
dake biye da ita ce ta tambayi ɗan waye shi ɗin? Bata faɗa masu ba ta sanya hannu
ta ɗaukesa.

Tana ɗaukarsa mama Haulat ta farka daga barcin da take yi a razane, Allah sarki
mace mai amana, a tinaninta sace shi aka zo yi yasa ta yi irin wanna farkawa.

Ganin momma ce yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da risinar da kai ta fara
kwasan gaisuwa. A takaice momma ta amsa mata kafin ta sanar da ita zata je wajen
King da babyn amma zata dawo da shi. Cikin girmamawa ta amsa da to a dawo lafiya.

Juyawa suka yi ita da Aunty MieMie suka fita, daga nan Fanan ta wuce part ɗin Akka
cike da al'ajabin ɗan waye momma ta kawo? A ina ta same shi?.
Suna fitowa parlon Aunty MieMie ta miƙa hannu a kan a bata babyn, tana san
yara sosai. Miƙa mata babyn momma ta yi. Karɓa ta yi tare da buɗe fuskarsa cikin
haske dan ta gansa da kyau.

Subhanallah, saura kaɗan ta saki yaron nan ya faɗi ƙasa, sai ta yi saurin rikesa da
kyau tana zaro ido.

Cike da mamaki Momma ta ce. "Lafiyarki Raeesa?".

"Momma ina fa lafiya, naga yaron ne tamkar hoton uncle Jahiz yana jariri,
hotonsa da take manne a jikin bangon bedroom ɗin Akka". Cike da mamaki sosai ta yi
maganar.

"Jahiz kuma?". Momma ta jefa mata tambayar ba tare da nuna damuwa ba.

"E momma! Uncle Jahiz wlh, Allah sun yi kama ni dai na gani".

"Wannan yaron fa da Koreans yake kama, tayaya zaki haɗa shi da Jahiz?! Ko kuna da
ƴan uwa koreans ne ban sani ba? Ko kuma Jahiz ya taɓa aure ne?". Cewar Momma, ta yi
maganar tare da wucewa gaba dan ta je wajen love ɗinta wato King.

"Wlh momma ni dai dik da yake kama da Koreans ya yi mun kama da uncle Jahiz,
bamu da ƴan uwa koreans, amma kuma shi ma uncle Jahiz ya so ya yi kama da Koreans
time da yake ƙarami, baki ga hotonsa a ɗakin Akka bane?".

Momma da ko a jikinta ta juyo ta karɓi babyn haɗe da cewa. "Yanzu dai jeki wajen
mijinki dare ya yi, da safe kyazo ki ga babyn da kyau sai ki tabbatar mana da waye
yake kama? Nasan dare yasa kike ganin kamar Jahiz a tattare da shi". Tana magana
tana cigaba da tafiya ta rungume baby da kyau da kyau.

My people's me kuke tinanin zai faru? Babyn Khadija kuma da uncle Jahiz? Muje dai
zuwa, is time for surprised.🤍💘🔥

Aunty MieMie taso ta sake yin magana, dan ita wlh wannan babyn da uncle Jahiz ya yi
mata kama, amma ganin momma taba saurin isa ga King yasa ta hakura suka yi sallama
ta nufi part ɗinta, amma a ranta ta gudurta zata daka sammakon ganin wannan babyn,
dan ba zata bari kanta ya kulle ba.
Sallama suka yi, Momma ta wuce izuwa wajen love ɗinta, Aunty MieMie ta wuce wajen
nata flowern. My people's akwai cakwakiya fa, ni dai komai ta ɗauki zafi ina da
Maltina mai sanyi, dan haka kowa ya samo Maltinars mai sanyi ta yadda idan kansa ta
ɗauki zafi ƙwaƙwalwa ta ɗauki caji sai ya ɗan korata ko ya kuka ce?.

===========================🔥
••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••🔥

9:30 pm.

Tsaye Sweetie take a gaban mirror na room ɗin Ronnie, ta fito daga wanka, wasu irin
kyawawan kayan barci mai nitsar da tinani ne a jikinta, shi ya saya mata su ɗazun
da ya je fada ya ga yayansa sai ya wuce super market ya yi mata sayayyan abubuwan
da zata rinƙa tsantsara kwalliya.

My people's fitowar Black Tiger fada ya yi bala'in tada tarzoma, ya jijjiga
zuƙatan mata da mazan Black world.

Ba matan ba ba mazan ba dik wanda ya gansa sai da ya haɗiyi yawu, jama'a dayawa sun
mutu a kansa, sai a yanzu ƴan'matan Black world suka fahimci ashe haukar banza suke
yi da suke mutuwa a kan kyan Ronnie, ashe ga uban Ronnie a kyau, sai dai kowacce ta
gani a banza, infact tsoronsa ma ya hana dik mutanen birnin kallansa sau biyu.

Dik wadda ta kalli face ɗinsa na farko bata sake ɗagawa ta kalli na biyu, dan ba
zasu iya ba, tamkar mutuwarsu haka suke jinsa, yana razana zuƙata, tun basu gansa
ba ya kasance tashin hankalinsu, yanzu kuwa ganinsa ya fi jinsa ashe. Ga shegen
kyau amma ba halin ganin kyan a ji daɗi......😥

Jama'an birnin nan babu wanda bai ziyarci cikin empeir ɗinsa ba a yau, dik dan
ganinsa, sai dai fa akwai dayawan mutane da suka suma a kallonsa na farko, dama in
baku manta ba babansa ya faɗa mashi babu wanda zai iya kallan face ɗinsa kawai ya
sake ɗaga idanu ya kalla, iya face ɗinsa kawai ba kwayar idanunsa ba.

Wanda zasu kallesa a kallon farko basu suma bama sai masu karfin zuciya, masu
raunin zuciya nan take zasu sume, kuma haka ne, jama'a dayawa sun suma saboda
raunin zuciya, masu juriya kaɗan ne. Gaskiya a gabaɗaya faɗin birnin Black world ko
rabin mai karfin halin Sweetie ba za'a iya samu ba, domin kuwa ita kaɗai ce ta iya
kallan kwayar idanunsa kuma ta zauna lafiya. Ni kam anya baban Black Tiger bai
tsafe face ɗin ɗan nan nasa ba kuwa? Kowa baya iya kallansa saboda bala'in tsoronsa
da suke ji!.

Master Devil dik wannan tauri da bakar zuciyar nan tasa ya ƙasa iya kallan face ɗin
Black Tiger sai biyu, tin da ya kallah sau ɗaya ya yi ƙasa da kai bai sake ɗagowa
ba, haka ma fa wai dan namijin gaske shi ɗin.

Abin haushin kuma dik wanda ya ɗaura idanunsa a kan face ɗinsa to fa da wannan
kallo ɗayan face ɗin take zama mashi a ransa babu mantuwa, dik birnin fuskarsa ya
kama zuƙatansu, tinanin kyansa ne kawai a cikin ransu. Ga shi da bala'in kwarjini
da farinjini, idanunsa kamar na riƙaƙƙen ɗan love, ga su kaifafan gaske, akwai
sirrika masu tarin yawa a kwayar idanunsa wanda ba zai iya bari a haɗa ido da shi
ba.

In short shigarsa fada ya wuci tinanin mai tinani, abin ya yi matukar tashin kan
jama'ar birnin Black world, sai da hasken fatar Ronnie ta ɗan dishashe lokacin da
ya zo kusa da yayan nasa, hasken wata mai dishashe hasken taurari..

Kuɗi ta ci ubanta a wajen bayyanarsa a fadarsa, anyi tsare tsare da zuba sabbin
abubuwa, motocin da aka zubo kawai sun kai kuɗin budget na wata ƙasar, dukiya dai
ta zube ƙasa ta yi mubaya'a matuƙa.

Kunsan yanzu arzikin Black Tiger ya ci uban na da, yanzu suna da arzikin red gold a
karkashin kasarsu, kunga kuwa ai abin sai wanda ya gani.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Floris tana zaune saman bed ɗin Ronnie, Allah sarki, Ronnie ya je ya rarraso
kayarsa, sun shirya yanzu. Sweetie tana ƙoƙarin gyara

Please Login or Register in order to submit comment