You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"A school fa wata class mate ɗita ta bani wannan labarin, ta ce in taimaka mata
da shawara, hakan yasa kema na baki dan ki kawo naki shawarar".

Ajiyar zuciya Sharifat ta sauke, dan kuwa hankalinta ya ɗan kwanta jin abin da
Leesharh ta ce, da a tinaninta a kanta abin yake faruwa, amma tin da ta ce labari
aka bata sai ita ma ta ɗauko handkichief dan goge hawayenta.

"Yanzu wani shawara zaki bada ke ma?". Leesharh ta sake jefa mata tambayar cike
da matsuwa na san jin amsar da zata bata, a ƙagare take.

Goge hawayenta tas Sharifat ta yi, sannan ta gyara zama, cikin sanyin murya ta
ce. "Kuskure ne dan wasu sun cutar da kai kai ma ka ce zaka cutar da wasu!".

Ɗan zaro mata idanu Leesharh ta yi. Ganin hakan yasa ta ce.

"Bari na baki missali yadda zaki fi fahimta, waɗan da suka rike mata baba ta sani
in suka cutar da shi to tabbas Allah ne zai yi mashi sakayya tin da babu abin da ya
yi masu, haka zalika ita ma idan ta ce hujjanta shi ne babanta ta cutar da waɗan da
basu ji ba basu gani ba to fa ta sani suma Allah zai yi masu sakayya, bata da
ƴancin cutar wani idan ba shi ya cutar da ita ba, in dai shi ya cutar da ita wannan
tana iya rama dai'dai da abin da ya yi mata".

"Misalin cikin suratun Nahl, aya ta 126 Allah ya ce

‫َّٰصِّلل‬
‫ْيٌرَّٰص ِبِريَن‬ ‫ۖ َوَلِئن َصَبْرُتْم َلُهَو َخ‬
ۖ ‫َوِإْن َعاَقْبُتْم َفَعاِقُبوا ِبِمْثِل َما ُعوِقْبُتْم ِبِهۦ‬

"Allah ya ce Idan an cutar da ku, yazamana kuna san ramawa, to ku yi ramako daidai
da abin da aka azabta ku da shi. Amma idan kun yi hakuri, to haƙiƙa hakuri shi ne
mafi alheri ga masu yin ta".

"Wannan aya na nuni da cewa idan wani ya zalunci mutum, yana da damar ramawa daidai
da abin da aka yi masa, dai'dai fa kada ya ƙara ko ɗiko, amma idan ya yi hakuri ya
bar wa Allah, to Allah zai yi mashi sakayya da abin da bai taɓa zata ba".

"Haka ma a cikin suratul shura, aya ta 40 Allah ya ce
‫ٌۭة ِّمْثُلَهاَفَمْن َعَفا َوَأْصَلَح َفَأْجُرُه َعَلى لَّلِهۚ ۚ َّنُه اَل ُيِح َّٰظ‬
‫ُّبلَّٰظِلِميَن‬ ‫َّٰظَٰٓز‬
‫َج۟اَسِّيَئٍۢة َسِّيَئٌۭة‬
‫َوُؤ‬
‫ٍۢة‬‫َج‬ ‫َّٰظ‬
‫"ٍۢةٌۭةَو‬
‫۟ا‬
‫َٰٓز۟ا‬
ۚ‫َٰٓز‬
‫ِإ‬

"Sakamakon mugunta ita ce mugunta irin ta, amma wanda ya yi afuwa kuma ya daidaita
komai cikin ruwan sanyi da yafiya, to ladansa yana wajen Allah, lallai Allah ba ya
son azzalumai da zalinci"

"Dan haka a shawarata ni dai shi ne ta barsu da Allah, kada ta damu idan sun cutar
da babanta, ta sani wanda ya halicci baban nata ya fita sonsa, kuma yana ganin
komai, sannan ki sani Allah bai yi alkawarin agazawa azzalumai ba, dik abin da suka
yi wa babanta Allah zai yi mashi sakamakon. Cikin suratul Hajj, aya ta 10 inda
Allah (SWT) yake cewa

‫َظَّٰلٍم ِّلْلَعِبيِد‬‫َّٰلِب‬
‫ْيَس‬ ‫َٰذَٰذِلَك ِبَما َقَّدَمْت َيَداَك َوَأَّن ٱلَّلَه َل‬

"Wannan azaba sakamakon abin da hannayenka suka aikata ne, dan Allah ba mai
zaluntar bayinsa ba ne, dik wani hukunci da kuka ga ya hau kanku to ku sani tabbas
kun aikata ba dai'dai bane aka hukuntaku. Wannan aya na nuni da cewa dik wanda ya
aikata zalunci ko wani nau’in cin zarafin mutane, zai fuskanci sakamakon abin da ya
aikata, Allah ba mai zalunci ba ne, kuma kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa,
ko na alheri ko na sharri".

"Haka zalika a cikin Suratul zumar, aya ta 24 Allah ya ce.
‫َأ‬
‫َلَّٰظِلِميَن ُذوُق ۟ا‬
‫و۟ا َما ُكنُتْم َتْكِسُبوَن‬ ‫َّٰظِلل‬
‫َٰيَمِۚة َوِقي‬
‫َم‬ ‫ْلِق‬
‫ِۚة‬‫َفَمن َيَّتِقى ِبَوْجِهۦٱٱِه َٰي ُسٓوَء ْلَعَذاِب َيْو‬

Dik wanda ya kare kansa daga mummunar azaba, wato ya guji aikata ba dai'dai ba, to
a ranar ƙiyama zai zama wanda ya tsira! Su kuma azzalumai za'a ce masu za ku
ɗanɗana abin da kuka kasance kuna aikatawa. Wannan aya ta kara jaddada cewa
azzalumai ba za su tsira ba, kuma Allah zai saka wa kowa daidai da abin da ya
aikata".

"Dan haka dik wanda aka zalunta ya barwa Allah, kada ta yarda ta bari Allah ya
kamata tana zaluntar waɗan da basu ji ba basu gani ba, ta koma ga Allah ta kai
kukanta a kan babanta, ba wai dan Allah bai san halin da take ciki ba, yana sane da
komai, amma ta koma garesa ta kai karansu a kan abin da suka yi wa babanta, kada ta
yarda ta cuci kowa".

Tin da Sharifat ta fara magana ta ƙasa kunne take sauraranta cikin nitsuwa, kuma
tabbas ta gamsu da kalaman Sharifat, tabbas Allah da ya halicci babanta ya fita
kaunarsa, dan haka ta bar masu nikaf da Allahn baban nata kawai, shi zai yi mata
maganinsu.

Tana tsaka da wannan tinanin ne wani sako ya kara shigowa wayarta. Sai da ta ɗan
saci kallan Sharifat ta wutsiyar idanu kafin ta buɗe saƙon. Taga Sharrifat
hankalinta ya koma kan wayarta da guyson yake kiranta, ya tura mata saƙo a
what'sapp ya jita shiru bata amsa ba, shi ne ya kira ya ji lafiya tana online bata
bashi amsa ba.

"Sharifat ina zuwa, zan je gidan wata class mate ɗina". Cewar Leesharh kenan.
Dan yanzu saukin da ta samu har ta koma school.

Cikin halin ko in kula ta amsa da. "In zo in rakaki ne?". Da sauri ta girgiza kai
tare da cewa. "A'a ba sai na wahalar dake ba, yanzu zan je in dawo, wasu handouts
zan karɓa".

Jinjina kai Sharifat ta yi, sannan ta sake cewa. "Waye zai kai ki to?". Kai tsaye
ta amsa da. "Yah Bilal ne zai kai yi, dama tin da safe mun yi magana da shi".

Cike da murna Sharifat ta ɗago da kallanta daga kan wayarta izuwa kan Leesharh ɗin,
fuska ɗauke da murmushi kamar ba yanzu ta gama sharar kwallah ba, har farinciki ya
baibaye zuciyarta baiwar Allah. "Allah yasa idan kun je kafin ku dawo a hanya ku
ƙullah soyayya da Yah Bilal, ai bama zan biku ba dan kada na shiga hakkin masoya,
Allah ya mallaka maki zuciyar Yah Bilal sai a haɗa aurenmu".

Sharifat da karfin hali take, ita da bata samu nata soyayyar ba take faman nemawa
wata, har da wani za'a haɗa aurensu, ko yaushe ta mallaki zuciyar Ramish har zasu
yi aute?.

Girgiza kai kawai Leesharh ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, dan ita tasan
abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa ba ta samu soyayyar ɗaya daga cikin King Badeen or
King Zuhair familys, bata kai ba, amma Sharifat sai wani hakikancewa take yi tana
haɗata aure da Bilal karfi da ya ji, ita a suwa wai?.

Mayafin kayan jikinta ta ɗauka tare da matsawa ta mannawa Sharifat sumbata haɗe da
yi mata sallama, sosai Sharifat ta zage tana addu'ar Allah yasa kafin su dawo
soyayya ta kullu, banda girgiza kai babu abin da Leesharh take yi. Haka ta wuce ta
fita abinta.
Ita kuma Sharifat ta cigaba da hira da guyson ba tare da ta kawo wani mummunar
tinani a ranta ba.

After some times.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Tuki yake yi a hankali cikin nitsuwa, dare ta yi, a kallah lokacin karfe 10 zata
yi, zaune take a kujerar gaban motar hannunta rike da bakar laida mai ɗan girma.

Dik da tana sanye da nikaf hakan ba zai hana mu iya gane cewa Leesharh bace, saboda
idanunta da yanayin jikinta, kai komai sak Leesharh ce.
Yana tuki yana waigowa dik bayan second ya kalleta, har sai da ta gaji ta
ce. "Yah Bilal kada fa mu je mu samu accident".

Maganar da ta yi ne ma ya kara tabbatar mun da Leesharh ce, dan babu banbanci a
voice ɗinsu.

"Ai ke ɗin ce, ba zan iya kawar da kallona daga kanki ba, dole ina juyowa in
ganki in ba haka ba sai a samu matsala". Ya faɗa yana sauka daga titin sama izuwa
na kasa.

"Kai Yah Bilal ka fara ko?". "To ya kike san in yi? Dole ce tasa ai".

Shiru ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Samu waje ka tsayar da motar sai mu yi magana
ko?"...... Ba musu ya gangara gefen titi ya yi parking, sannan ya juyo ya kura mata
ido.

"Menene next my lovely wife?". Ya faɗa. Dai'dai lokacin call ɗin Ramish ya shigo
wayarsa, bai kai ga kawar da kallonsa a kanta izuwa kan wayar ba tasa hannu ta ɗage
nikaf dake face ɗinta.

Ƙasa kawar da kallonsa ya yi, da ɗan karfi ya furta wow. Leesharh ta sha make up
yau sosai, ta yi kyau matuƙa kamar ba ita ba, sai glowing take yi.

Har call ɗin Ramish ya katse yana nan yana kallanta bai yi magana ba.

Me kuke tinanin ya haɗasu a wannan dare da har yake ce mata my wife? Dama suna
soyayya ne? Ko dai yau suka fara?.

"Yah Bilal mu je ka saya mun ice cream sai mu koma gida dare ya yi". A ɗan shagwaɓe
ta faɗa.

Nisawa ya yi, maza anga kyau iya kyau har ya ji kamar ba'a duniya yake ba.
"Wife kin yi kyau matuƙa sosai".

Siririn murmushi ta saki kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa. Hannunsa yasa ya ɗago
haɓarta.
"A'a barni in kalli face ɗin matata da kyau". Ya faɗa yana zame hannunsa
daga haɓar tata.

"Kai Yah Bilal ni fa kunya nike ji". Ta faɗa tana kallansa ƙasa ƙasa. Matsar da
bakinsa dab da kunnenta ya yi, ƙasa ƙasa kamar mai raɗa ya furta. "Kin girma fa,
komai ya ciko dai'dai yadda nike so, yakamata......."

Katse shi ta yi ta hanyar jiyowa garesa da sauri. Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da
matsar da bakinsa saitin kumatunta, sumbata ya bata a lallausan kumatunta.
Lunshe idanunta ta yi tare da sauke ajiyar zuciya. Ƙara matsa dab da ita ya yi,
kamar zai haɗe bakinsu waje guda, kamar mai raɗa ya ce. "Yau kam za'a bani dama ne
ko dai za'a cigaba da hanani kamar a baya?".

(What?😳 Kenan ya saba kawo mata harin kiss? Tab akwai matsala, a warware mana
wannan cakwakiya ko zan samu damar shan maltina mai sanyi.)

Tana kallan cikin idanunsa ta ce. "Yah Bilal ko da can baya ban taɓa hanaka na ai,
kai ne dai kake ganin kamar ina hanaka".

Gera ɗaya ya ɗaga mata tare da kara matsawa dab da ita sosai, a hankali yasa
hannunsa zai ɗan rungumota.

A karo na biyu call ɗin Ramish ya sake shigowa wayarsa. Ɗan ciza laɓɓansa kaɗan ya
ɗan yi haɗe da janye jikinsa daga kusa da ita, ya koma ya mannu da jikin kujerarsa
yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗauko wayar, kamar ba zai yi picking ba, dan
yasan wanenen Ramish, tsaɓ zai iya cankar a wani irin yanayi yake ciki da jin voice
ɗinsa kawai.

Amma sai kuma ya tina in har bai ɗauki wannan call ɗin ba to Ramish zai fita
nemansa ne, saboda sun san dik abin da ya sha kansu basa wuce miss calls biyu ma
junasu ba tare da sun yi picking ba, shirunsu basu yi picking ba hakan na nuna suna
cikin matsala kenan, kunga dole ya fita nemansa.

Hakan yasa ya ɗauki call ɗin tare da kara wayar a kunnensa yana seseta nitsuwarsa.
Daga ɗayar ɓangaren Ramish ya yi cikakken sallama. Amsawa ya yi idanunsa a kanta,
ita ma shi take bi da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa.

"Ina kake Bilal?". Ramish ya jefa mashi tambaya.

Shiru ya ɗan yi yana tinanin abin faɗe, basu saba yin karya ba, hakan ya ja ya
rasa abin faɗe.
"Ina zuwa gida yanzu". Ya faɗa yana san katse kiran.

Katse shi Ramish ya yi da cewa. "Ka faɗa mun in da kake in zo in sameka yanzu". A
hanzarce ya ce. "A'a ba sai ka zo ba, ina hanyar gida yanzu".

Shiru Ramish ya ɗan yi, can kuma sai ya ce. "Ka dai san bana magana biyu ko?".
Jinjina kai Bilal ya yi alamar e tamkar yana gabansa haɗe da cewa e haka ne.

"To ina kake zanzo yanzu".

Zaro idanu Bilal ya yi, sai ya ji kamar an kwaɗa mashi guduma a kansa, hankalinsa
ne ya tashi, Ramish ya zo ya samesa a nan ai ya shiga uku, me zai ce mashi ya rabu
da shi kenan?.

Zare wayar daga kunnensa ya yi, ba tare da ya sake yi wa Ramish magana ba ya yi
saurin katse kiran, a hanzarce ya tashi motar.

"Yah Bilal lafiya?". Ta jefa mashi tambayar tana kallan wayar dake hannunsa.

"Sauke nikaf naki, sorry ba zamu iya tsayawa sayen ice cream ba, gida kai tsaye
zamu wuce, gobe muna da taro, idan mun taso daga taron zan saya maki ice cream ɗin
in kawo maki". Ya kai karshen maganar tare da kunne mota.

Da gudun gaske ya figi motar tamkar zai tashi sama, har sai da ya bata tsoro.

A can gida kuwa. Ramish yana tsaye a parlournsu, daga shi sai sexy short, babu riga
a jikinsa sai white singlet mai kyan gaske, yana tsaye a jikin windownsu dake
fuskantar harabar gidan, hannunsa rike da cup and his phone.

Shi ma Ramish yana da zanen letter R a damtse hannunsa da ya zana kamar yadda Bilal
ya yi zanen B a wuyarsa, yanayinsa ta nuna yana cikin damuwa sosai, saboda abubuwa
sun sha kansa matuƙa, ga shi gobe zasu yi wannan taro da yake sa ran kafin taro ya
kama masu nikaf kenan, sai dai har yanzu bai samu wata makama da zai iya kamasu da
ita ba, babu ma wanu abin zargi da suka bar mashi, abin dai ya sha gaban tinani,
dik yadda aka yi su ma shegu ne.

Ya yi shiru yana kallan harabar gidansu kamar mai tinanin wani abin, bawan
Allah damuwa ta yi mashi yawa, bai san ya taron gobe zata kasance ba.

Ba tare da ya juyo ba, cikin nitsuwa ya ce. "Daga ina kake a cikin wannan dare
bayan kasan halin da muke ciki?"............ Kamar wani aljani, ko yaushe ya ji yo
takun sahun Bilal?.

Bilal da ya shigo yanzu ne ya ɗan fara kame kame kamar wani maras gaskiya, dama
kamar yasan zai sami Ramish a wajen yasa ya shiga parking space ɗinsu ta kofar baya
ba tare da kowa ya gansa ba, dik dan gujewa ƴan gidan kada su gansa.

"Meyasa kaki yarda in zo in sameka a in da kake? And meyasa ka katse kirana ba
tare da mun gama magana ba?". Ramish ya sake jefa mashi tambaya a karo na biyu ba
tare da ya jira ya amsa ta farko ba.

Shiru ya kasa amsawa, dan bai san me zai ce mashi ba, ga shi dik in da suke zuwa
dama a tare suke tafiya bare ya yi mashi wani karya.

A hankali Ramish ya juyo garesa, wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke kafin ya
ce.
"Me kake ɓoye mun my love". Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallan
tuhuma, dan yanzu zuciyarsa ta rigata da kai point ɗin da ba zai iya ɓoye zargin da
ya jima yake yi ba, ya daɗe sosai zuciyarsa tana ɗarsa mashi zargi a kan Bilal na
ɓoye mashi wani abin, amma a koda yaushe ƙoƙarin kawar da wannan zargi yake yi
domin yaga ya kori shaiɗan dake san rabashi da ɗan uwansa ya haɗasu faɗa.

"What do you think that I'm hiding for you?". A ɗan razane ya yi maganar, alamar
kamar dai da gaske akwai wata a ƙasa.
"Ka fini sani Bilal, ka fini sanin abin da kake ɓoyewa". "Wai
Yah Ramish lafiyarka yau kuwa? Shin na taɓa ɓoye maka wani abin ne? Tin tasowata
har zuwa yau ba a tare muke yin komai ba?..........."

Cikin zafa da kunan rai ya ce. "Banda wannan lokacin
Bilal, tin da muka taso tare muke yin komai amma banda yanzu!". Yadda ya yi maganar
da alama ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa ta fara raunata sosai, dan da alamar
zarginsa tana san tabbata, idan kuma abin da yake zargi ta tabbata da gaske, magana
ta domin Allah zai iya rasa ransa, saboda kowa yasan bayan iyayensa babu wanda yake
kauna biyun Bilal, yana sansa

Please Login or Register in order to submit comment