You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hango kafar mutum a bayan labule wanda ko ba'a faɗa mata
ba tasan kafar dattijuwa ce!.

Mamaki ne ya kamata na ganin dattijuwa a cikin bedroom ɗin, wato knowking da ta yi
a farko ne yasa ta farga ta ɓuye kenan, to me ya kawota ɗakin? Me take yi mashi a
ciki? Shiru ta natsa cikin thinking ɗinta, can kome ta tina sai ta saki ƙayataccen
murmushi tare da juyawa ta nufi waje. Bedroom ɗin ta murzawa key ta baya sannan ta
nufi bedroom na dattijuwar. Bincike ta hau yi mata babu kakkautawa kamar an aikota,
ta kuwa yi nasarar samun wasu hotuna na mutane daban daban. Sannan ta yi nasarar
gano cewa wannan matashiyar budurwa ta jima tana son Ramish, hakan ba karamun daɗi
ya yi mata ba ta samu hanyar tunzura tsohuwar nan har sai ta tona asirin kanta da
kanta!!.

Bata ɗauki komai a cikin ɗakin ba, sai dai ta yi snaping na wasu pic a wayarta,
sannan ta mayar da komai yadda ta samu kafin ta dawo ta nufi bedroom ɗinsa, murza
key ɗin ta yi ta buɗe, ba tare da tsoro ba ta shiga ciki, har lokacin dattijuwa na
laɓe a bayan labule.

Ciki ta shige tare da zama a gefen bed tamkar tana jiransa, da alama akwai abin da
ta shirya a ranta wanda bata bawa kowa damar ya sani ba. Da zamanta a gefen bed ɗin
da shigowarsa room ɗin dik bai wuce ratar mintuna biyar ba, tana jin motsin zai
shigo ta yi gaggawar kwanciya tamkar wadda barci ya ɗauka, irin kwaciyar da ta yi
kamar unexpected barci ya ɗauketa haka, ta dunkule waje guda.

Sosai ya yi mamakin ganinta a room ɗinsa, har lumshe idanunsa ya ɗan yi ya sake
warosu a kanta dan ya babbatar ba gizo mane ba!. Samun tabbacin hakan yasa ya sauke
ajiyar zuciya tare da ƙarisowa ciki, ko kaɗan bai game dattijuwa tana cikin room
ɗin ba!. Gaban bed ɗin ya iso, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da sanya hannunsa ya
gyara mata kwanciya da kyau, wlh har ya rame saboda damuwa a kan masu nikaf. A fili
ya furta. "Ɗaukarki fa nazo yi Aesh". Ya yi maganar tare da zama a kusa da ita.

A hankali ta ɗan motsa wai irin mai barci yana son farkawa ɗin nan! "Aesh". Ya
ambaci sunanta a hankali. Sake motsawa ta yi haɗe da cewa ummm irin mutum a cikin
barci ya ji an kirasa ɗin nan. "Zaki iya tashi yanzu ne ko dai in kyaleki sai zuwa
gobe mu je?". Jin ya kira batun fita ta yi saurin sake cewa ummm, an ji yawo ba,
har da juyawa wai irin ta farkan nan, ita ma fa Leesharh A ce wlh. Cikin dabara ta
ɗan buɗe idanunta, a lokacin yana bin surar jikinta da kallo, yadda ta kwanta mashi
a saman bed ɗin nan yau da ita mallakinsa ne da ta sha mamakinsa, ya kwaɗaitu da
ita sosai yanzun nan, idanunsa a kan kirjinta da suka fito sosai saboda yanayin
yadda ta kwanta.
Ita kuwa ganin ba face ɗinta yake kallah ba yasa ta yi gaggawar satar kallon bayan
labule, aikuwa nan ta ga dattijuwa tana leƙosu, ta ji daɗin hakan sosai, zata shaƙa
mata bakinciki, a cewarta tin da ta gano yarinyar tana son Ramish soyayya na
gaskiya to ba shakka da kishi zata amfani wajen sanyata ta tonawa kanta asiri.

Mai da idanunta ta yi ta datse gam tare da juyawa ta ɗaura kanta a saman laps
ɗinsa, irin wai tana gigin barcin nan. Har cikin zuciyarsa ya ji ta amsa, wani irin
dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. Hannunsa ya kai saman lallausan
kumatunta, cikin sanyin murya ya ce. "Aesh zaki iya tashi kuwa?". Ya yi maganar
idanunsa a kan shape na HP ɗinta, tin da ya shigo bai kalli idanunta bane da zai
gane barcin karya take yi, gabaɗaya hankalinsa a kan surarta. Marairace murya ta yi
irin muryar barci, cike da shagwaɓa ta ce. "Yah Ramish barci nike ji sosai amma ka
tashe ni"............... 🤔🥱

"Sorry to cigaba da yin barcinki kin ji?". Kai ta ɗan girgiza tare da juyawa ta
yi kwanciya ruf da ciki, dan ta ga ya kurewa kirjinta da HP ɗinta idanu, sai abin
ya bata kunya sosai, kun san mu fa Nigerians da kunya aka sanmu, mu ɗin ma arewaci
ne masu kunyar, so Leesharh dai da sauran kunyarta...... "Yah Ramish ai ka rigada
ka kori barcin tin da ka tasheni". Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa game da waro
idanunta. Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, dai'dai lokacin ta miƙe zaune
tana kallon kasa. Kallo ɗaya ya yi wa idanunta yasan ba barci ta yi ba, ya ɗan yi
mamaki, a ransa ya ce ko dai kewata Aesh take yi ne yasa ta zo bedroom ɗina ta
kwanta da ta ganni kuma dan kada in ce me ya kawota shi ne ta yi acting kamar barci
ne ya ɗauketa a wajen? Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya yi wannan tinani, sai
ya ji daɗi, ko ba komai yau ta damu da shi.

"Yah Ramish yaushe ka dawo?". Ta yi maganar tana bin ɗakin da kallo, wai irin
ta nuna kamar bama ta san nan ta shigo ta kwanta ba. "Kai me yakawoni bedroom ɗinka
kuma? Kai innalilahi barcin nan bai mun dai'dai ba!". Ya faɗa tana ƙoƙarin sauka
bed ɗin, wai tana son nuna mashi barci ne ya yi mata yawa bata san nan ta shigo ta
kwanta ba , dama bedroom ɗinta zata wuce sai gigin barcin ya kwasheta. Bata san ya
gama gane komai ba, ya ganota. Binta da kallo ya tsaya yana yi, wai irin zata yi
basajan nan, ta manta a gaban babban jami'i take!.

Ganin ya yi shiru yana kallonta yasa ta yi gaggawar yunƙurawa zata sauka ta bar
gadan tana ƙoƙarin danne murmushin dake san kubce mata. ANKAMA WATA TA YI KARYA..😅

Hannunta ya capko tare da janyota ta faɗa saman kirjinsa. Sai da dattijuwar nan ta
ji kirjinta ya amsa, wani irin zafi ta ji a ranta, abin ya komata sosai. Kai
kallanta a kan kafar dattijuwar dake leƙowa ta gefen labule Leesharh ta yi, nan ta
ga matar ta matse yatsun kafafun nata a kasa, nan Leesharh ta gane abin ya ciza
mata zuciya, bata so ba!.

Cikin wani irin kasalallen murya ya ce. "Me kika zo yi bedroom ɗina?". Ya yi
maganar tare da sanya hannun ya zame pil da ta kama veil da ta yi rolling a
kanta......... "Ni fa Yah Ramish ban san cewa bedroom ɗinka na shigo ba, na fito
daga wajensu Auta ne barci kamar zan yi hauka, shi ne na afko nan ban sani ba". Ta
kai karshen maganar tare da dafa kirjinsa zata miƙe. Mayar da ita ya yi ta kwanta,
veil ɗin nata ya cire ya ajiye a gefe, haɓarta ya ɗago ya zama suna fuskantar juna.
Ɗan zuba mata idanu kamar na ƴan sakanni kafin ya ce. "Meyasa kike wahalar da ni ne
Aesh? Meyasa ba zaki yarda mu yi aure ba?".

Satar kallon kafar dattijuwar ta yi kafin ta ɗan kalli sama, nan taga tana lekansu
bata dai'na ba, dawo da kallonta a kansa ta yi, sillent talk ta yi mashi ta hanyar
motsa lips ɗinta, babu wanda zai iya fahimtar me ta ce mashi sai shi ɗin, a fili ya
sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce. "In kuwa haka ne zan kasance cikin
dakon wannan rana, sannan kuma a ranar zan baki kyakkyawar kyauta da na tabbata
zaki ji daɗinsa sosai". Ya kai karshen maganar tare da matsar da ɗan bakinsa dap
kunnenta, ya cigaba da cewa. "A wannan rana babu shakka ba zan kyaleki ba sai na yi
round two, dan kin bani wahala sosai".

Ɗago da kanta ta yi, a hankali ta kai ɗan bakinta saitin kumatunsa, zazzafar
sumbata ta bashi wanda sai da ta sanya dattijuwar nan sakin labulen da ta rike ta
ɗan yaye tana leƙansu, idanunta sun yi jajir sun cika da kwallah, wlh Leesharh ta
iya tsiya. "Nima ina da kyakkyawar kyauta yau a gareka, amma idan na baka me zaka
bani?". ME KUKE TINANIN ZATA BASHI?.

Ai bai iya bata amsa ba saboda wani irin tayar mashi da hankali wannan sumbata
tata da ta yi, ji ya yi tamkar wanda aka jonawa lantarki.
Jin ya yi shiru yasa ta sake maimaita abin da ta faɗa tare da ɗan ɗago kanta da
kallonta a kansa, tana ɗagowa bakinsu ya haɗe dan in baku manta ba ya kai bakinsa
ya yi mata raɗa a kunne.

Tana ƙoƙarin yin gaggawar zame kanta ya ce ina baki isa ba, ai rikota ya yi ya fara
rage zafin da ta haɗa mashi, hot kiss ya shiga bata tare da cusa hannunsa a cikin
kyakkyawar gashin kanta da ya sha gyara. Ai tsabar takaici dattijuwa bata san time
ɗin da ta furta no ba, sai dai Ramish ya yi nisan da bai jita ba, amma ita Leesharh
ta ji time da ta faɗa, hakan yasa ta kyalesa yana kissing ɗinta bata hana shi ba,
sai ma hannu da ta kai ta rungumesa da kyau. Haba ai kara haɗa mashi zafi ta yi, ya
matseta sosai a jikinsa, yana ƙoƙarin tura hannunsa cikin rigarta cikin fitar
hankali sai aka yi knowking na door ɗin wanda hakan ya ja ta yi gaggawar kwace
bakinta daga nasa.

Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kaman ɗan maye, murya kamar na ɗan maye ya ce mata.
"Aesh please bayan kiss ba zan yi maki komai ba, please ki barni in kara kaɗan".
Out of control yake maganar, idanunsa a limshe. "Yah Ramish knowking ake yi
shiyasa". Ta faɗa tare da janyo vail tana ƙoƙarin maidawa kanta. Ɗan ciza lips
ɗinsa gam ya yi, sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa, sam bai so hakan
ba. Miƙewa ta yi ta nufi door ɗin tana jin wani irin farinciki na musamman a ranta.

Tana buɗewa suka yi four eyes da guyson. "Aunty Aesh ke fa muke jira ki zo mu yi
lunch amma shiru tun ɗazun". Yana magana kallansa a kan Ramish da ya waro eyes
ɗinsa da suka rikiɗa izuwa red sosai. A natse ta ce. "Muje to". Guyson yana zargin
wani abin, dan ya ganta gabaɗaya a hargitse, amma bai ce komai ba ya juya da nufin
su tafi.

"Omar kuje ku yi lunch ɗin, fita zamu yi da ita". Muryar Ramish ya daki dodan
kunnensu, ya yi maganar tare da miƙewa ya nufosu. Wucesu ya yi cikin sauri yana
faɗin. "Aesh ki sameni a mota". Kallon juna suka yi ita da guyson kafin ta saci
kallon dattijuwa, a ranta ta ce ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, yanzu masu
nikaf zasu samu labarin hakarsu bai cin ma ruwa ba, sun so tagayyara rayuwarta,
idan ta kammala aikinta su kasheta, idan kuma asirinta ya tonu su Ramish su
kasheta, sai ga shi da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, su samu labarin
soyayya ma take da Ramish ɗin, su san sonta yake yi kamar ransa, sai su mutu da
haushi, rayuwarta bai tagayyara da suka yi fata ba!!.

"Yah Omar bari in je". Hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce. "Ina da meeting dake
Aunty Aesh, sannan kada ki wahalar mun da yaya, ki yi mashi dik abin da yake so dan
faranta mashi, na baki amanarsa". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya tafi.
Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, siririn murmushi ta saki a ranta ta
ce ta yi sa'ar ƴan uwansa masu saukin kai ne kuma suna kaunarta...... Ni kuwa ya ce
tab lallai kuwa mafarki kike yi, dan kuwa a yaran King Auta da guyson ɗin ne kawai
masu sanyin halin, uhm kada ki yi fatan shiga kingdom of power da sunan zaman aure
kina matsayin bare, inai maki fatan idan Allah ya yi aure tsakaninki da Ramish ku
yi zamanku a Dubai, idan ba haka ba mama kawai ta isheku bala'i, baku zasu karɓeki
matsayin sirika ba!!.

Bayansa ta bi tana cigaba da godewa Allah. A cikin mota ta iskosa zaune yana
jiranta, gidan gaba ta buɗe ta shiga, kanta a kasa saboda kunyar sumbatar da ta yi
mashi ɗazun, kunna motar ya yi ba tare da ya kalleta ba, kai tsaye suka nufi office
ɗinsa. Suna tafiya tsohuwar nan ta yi gaggawar fitowa ta nufi bedroom ɗinta,
idanunta sun yi jajir kamar wuta, har da guntun kwallah a face ɗinta, ranta ya ɓaci
Leesharh ta yi mata taboooooooooooooo.

TO! Ina mai farincikin sanar da ku cewa book ɗina mai suna MACE MAI DARAJACE, zai
saukan maku da zafizafinsa very soon, wannan book ɗin na yisa ne kawai dan matan
aure da kuma waɗan da suke gab da yin aure, ko zawarawa wanda ba aure zasu yi ba
ban yarda su karanta mun littafi ba, ba novel bane, littafi ne da dan ma'aurata na
yi shi, na jima ina tsara shi ina kuma tattara dik wasu muhimman abubuwa a cikinsa,
book ne da ya haɗa komai da komai na rayuwar aure da sauransu, kada wata budurwa ta
buɗe mun book tam!!! 2k yake, akwai sirrika kala daban daban a cikinsa, akwai kayan
gyare gyaren abubuwa daban daban, kai baki ba zai iya faɗar abin dake cikin book
ɗin nan ba, in kina buƙata kai tsaye ki mun magana, amma ba yanzu zan sake shi ba,
saura kaɗan, idan na tashi sakansa zan sanar da ku!!. Amma dik mai so tin yanzu ta
mun magana in san da ita, an zuba abubuwa a ciki, akwai salo kala kala sai wanda ya
karanta zai gane, bana san buɗe me a ciki saboda kada na baku satar amsa, amma fa
akwai abubuwa a ciki ba karya!!. IN SHA ALLAH RAYUWARKI ZATA CANZA KAMAR HAKA IDAN
KIKA SAMU DAMAR MALLAKAR WANNAN LITTAFI KUMA KIKA YI AMFANI DA ABIN DAKE A CIKI!.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬


60




Auta da guyson kuwa a tare suka yi lunch ɗinsu, Auta taki ci da farko, sai da
guyson ya yi ta lallaɓata sannan ne ta ci.

Shi kuwa Ramish yana yin parking motarsa a parking lot na h-c ɗinsu kan kace me
wasu jiga jigan jami'ai sun kewaye motar, sosai Leesharh ta tsorata daga ciki, dan
a tinaninta tin da taki tayasa aiki shi ne ya kawota su lallasata irin na wancan
karan!. Zuba mashi idanu ta yi tana kallan yadda ya ɗaure fuska tamau tamkar
hadari, abin sai ya yi mugun bata tsoro.

Buɗe mashi door ɗin aka yi, ba tare da ya sake kallan in da take ba ya fito waje
abinsa. Shiru ta yi a ranta tana tinanin ya zata yi? Sai gani ta yi an buɗe mata
door na side ɗinta, kallon jami'in da ya buɗe mata ɗin ta yi, wani shirgegen
balarabe ne mai tsawo da cikar halitta. Fitowa ta yi jiki ba kwari, tinanin irin
azaban da jami'an nan suka bata a farkon karonta da su ne kawai ya faɗo mata a rai,
tin da ta zo duniya bata taɓa shan azaba irin wanda suka gana mata ba, a lokacin
har ji ta yi da sun bata wata dama kaɗan tsab zata kashe kanta ta huta!.

Ta yi nisa a cikin tinaninta sai ji ta yi anja hannunta, almost 3 times yanayi mata
magana bata ji shi ba, shi ne yasa ya kama hannunta kawai. Zaro idanu ta yi tana
kallonsa tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, da ta san nan zai zo ba zata rakosa ba.
Binsa kawai take yi tana karanta lailahaillah anta subhanaka inni kuntu minaz-
zalimin, gabaɗaya jikinta kerma yake yi. Ya lura da ta tsorata sosai, hakan yasa ya
yi ƙasa da murya sosai wajen cewa. "Aesh babu abin da za su yi maki fa, a yanzu
wannan zuwan na daban ne, ba irin wanda kika yi a baya bane!".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa mashi da to, manya-manyan jami'ai guda shidda
ne suke take masu baya har izuwa cikin office ɗinsa. Already mai zane yana zaune
yana jiransu. Saman wani lallausan seat ya ce mata ta zauna. Ba musu ta zauna tana
kallon office ɗin, ɗauko mashi wata chair dake kusa da table ɗinsa yasa aka yi aka
kawo mashi kusa da ita, zama ya yi suna fuskantar juna, sannan ne ya ce. "Ki faɗa
mashi fuskokin waɗan da kika sani daga cikinsu, dan gabaɗaya waɗan da kika ambata
na bincikasu a gidan Abbie babu su".

In baku manta ba dattijuwa tasa sun ɓoye shaidar da za'a iya kamasu da shi, so
ya bincika bai iya kamasu ba, dan haka dole su kasance suna da zanensu. Ganaɗaya
jami'ansa tsayuwa suka yi a bayansa suka binta da kallo suna jiran ta fara zayyano
bayanai. Lokaci guda ya ji hakan ya kona mashi rai, a ɗan dakile ya ce da jami'an
dik su fice mashi daga office, dan bai ga amfanin su tsaya suna kalle mashi ita ba,
shi kaɗai zai ganta kuma ya ga zanen da za'a zana.

Abin har murmushi yaso ya sakata, sai ta danne tare da cewa. "Yah Ramish ina tsoro
sosai". ......... Hannunsa ya miƙa ya riƙo nata, cikin natsuwa ya ce. "Babu abin da
zai faru kin ji? Please ki daure". Jinjina mashi kai ta yi tare da juyo da kallonta
a kan mai zanen, cikin natsuwa ta fara bashi bayanan yadda suke a zahirance. Zanasu
ya fara yi har da face mask na fuskokinsu, tana cigaba da yi mashi bayani yadda
yakamata har suka kammala, bata yi kuskure ba sam sam, zanen ya fita sosai.

Ana kammalawa kallo ɗaya Ramish ya yi wa zanen ya gano su wanenen daga cikin
securitys ɗinsu, ya girgiza sosai da ganinsu, zubawa hoton zanen idanu ya yi yana
kara tambayarta ta tabbata sune babu kuskure, kai ta gyaɗa mashi alamar ta tabbata.
Nisawa ya yi kafin ya karɓi zanen, sannan ya cewa mai zanen ya haɗa kayansa ya je,
already dama ya biyasa hakkinsa.

Mai zanen yana fita Leesharh ta matsa kusa da shi. "Yah Ramish akwai abin da nike
san faɗa maka fa, ko in ce akwai abin da nike san baka, amma dan Allah idan na baka
kada ka tambayeni daga ina na samu ka ji?". Dawo da kallonsa tsam a kanta ya yi.
"In Sha ALLAH ba zan tambaya ba". Ya faɗa yana sake riko hannunta cikin nasa.

Wayarta ta fitar daga aljihun rigarta da ɗayar hannunta, kai tsaye ta shiga picks,
hotunan da ta ɗauka a ɗazun bedroom na dattijuwa ta fitar, miƙa mashi wayar ta yi
tana faɗin. "Dik waɗan nan suna da sa hannun a abubuwan da suke faru, and ka nemosu
zaka samu dik abin da kake so daga bakunansu".

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a ransa ya furta alhamdulillah almost 3 times,
kai amma ya ji matuƙar daɗi, koba komai yanzu ya sami wasu da face ɗinsu yake a
buɗe, a gaskiya Leesharh ta taimaka mashi, ya kuma ji daɗi, dole su nemo waɗan nan
fuskokin.

Cigaba ya yi da duba hotunan a tinaninsa zai ga wasu, sai kawai ya fara ganin
hotunansa kala daban daban a cikin wayar, dik kuma bai sani ba ta yi ta ɗaukarsa,
sun yi fitina hotunan ba kaɗan ba, saboda yadda ta ɗaukesu bai sani ba, kun san
hoto idan baka sani ba aka ɗauketa wlh ya fi kyau, ba karamun daɗi ya ji ba, ɗago
idanu ya yi ya kallenta, while ita ma shi take kallo. Suna haɗa ido ta yi gaggawar
sunkuyar da kanta ƙasa. Matsar da kujerarsa dab da ita sosai ya yi tare da ɗaura
hannunsa a saman shoulder ɗinta, ya kashe masu selfish mai bala'in kyau, murmushi
ne ya subce mata tasa tafukan hannayenta ta rufe face ɗinta tana yin ƙasa da kai!.

"Waye ya ce a saci mun hotunana ba tare da izinina ba?!". Ya faɗa yana janyota
jikinsa. "Kai Yah Ramish ni da hotunan yayana kuma ka ce meyasa na sata? Yayana ne
fa!". Ta faɗa tana cigaba da rufe fuska. Haɓarta ya ɗago. "Ni ban yarda da wannan
wayan ba, kawai a bani amsar me ake yi da hotona". Ya kai karshen maganar tare da
matsar da bakinsa saitin kunnuwanta. "Ko dan kinga kyakkyawan guy yaron mamarsa shi
ne kika kyatsa kika kware mun e ƴan'mata?".

Ɗan turo baki ta yi. "Ni ba wani kyatsawar da na yi". "Da gaske?". Kai ta gyaɗa
mashi alamar e. "To me kike yi da hotunana? Faɗa mun in ji!". "Ni babu abin da nike
yi da su". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Masu sunanki suna mai daraja basa karya
fa, faɗa mun gaskiyar me kike yi da su?!". Kara rufe face ɗinta da kyau sosai ta yi
kafin ta ce. "Zuwa dare zan faɗa maka, amma yanzu please ka barci". Ɗan lumshe
idanu ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Mu je gida ko mu je yawo?".

Shiru ta ɗan yi, can sai ta ce. "Yah Ramish yaushe zaka kai ni gidan Abbie in ga
ƴar uwata?". Take mood ɗinsa ta ɗan canza, alamar bai ji daɗin maganar bama, amma
sai ya ce. "Ba yanzu ba, sai mun kammala binciken da muke yi, zuwanki gidan a yanzu
babban haɗari ne sosai". Da zata ce ya kaita a yanzu, amma ganin ya nuna alamar
rashin jin daɗi yasa ta hakura, sai ta ce su wuce gida kawai dan tana san kasancewa
da guyson and Auta. Bai musa mata ba ya ɗauketa suka wuce wajen cin abinci mai kyau
da tsada game da tsaro, daga haka suka wuce gida ya mayar da ita ya sake dawowa h-c
ɗinsu dan su cigaba da bincike a kan wannan zane da ta basu game da hotunan waɗan
can fuskokin!.

🔥🔥🔥🔥JIMETA🔥🔥🔥🔥

Ai tijara Nenne ta tsayar masu a kan ko sama zata haɗe da kasa yau sai bappa ya
fitar mata da Mahreen, idan kuma ba haka ba zai ga jajjagen bala'i, banza da ita ya
yi tare da wucewa ya shiga cikin gida abinsa, ransa fes tin da Mahnoor dai ta koma
ga mijinta, yanzu damuwarsa a nan shi ne kewarsu da ya addaba mashi.

Ɗakin Diddi Mairo ya wuce ya je ya kwanta a zuwan anjuma zai koma wajen kiwonsa.
Yana cikin kwanciyar ne ya ji mutum a kansa, ɗago kai da zai yi sai ganin Nenne a
tsaye da zabgegen wuƙa tana kaɗa ƙugu kamar sandar snooker a kan lallai ya fitar
mata da Mahreen, cikin sauri ya miƙe zaune yana kallonta, kamar ba zai yi magana ba
sai kuma ya ce. "Amma baki da hankali ko? Ko dai wani abin ne kika sha a yau?".

Wata uwar harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Gaka babban mahaukaci kuma azzalumi!
Ka sayar da ƴarka ga masu kuɗi, wlh sai ka fitar mun da Mahreen ko kuma in kasheka
a cikin ɗakin nan, bakin shaiɗani kawai"....... Ransa ne ya yi mummunar ɓaci jin
kalaman da take dangantasa da su, wai baƙin shaiɗani, cikin fushi ya miƙe tsaye
suna fuskantar juna. Yau ya koma ainahin kalarsa, wani irin gigitaccen mari ya
ɗauketa da shi wanda sai da yasa ta yi baya baya kamar zata faɗi ƙasa.

Ranta ne ya yi mummunar ɓaci da yasa ta ɗaga wukar da gaske zata buga mashi a ciki,
sai dai ina, kafa yasa ya taketa ta yi baya ta bugu da jikin bango ta faɗi kasa
wukar ma ya faɗi ƙasa, sandar kiwonsa ya ɗauka ya hau jibgarta tamkar an saukar
mashi da wahayi. Jin ihunta yasa Diddi Mairo shigowa ciki da gudu, hankalinta ne ya
yi mummunar tashi ganin abin da yake faruwa, dama ita tasan shi da iya duka tun da
ya yi ta jibgar mahaifiyar Mahnoor, so ta ɗauka ya dai'na ne, ganin hakan yasa ta
kara shiga taitayinta, tsoron zuwa bashi hakuri ma ta yi, sai ta ja baya tana ruwan
hawaye.

Shi kuwa sai da ya tabbatar ya jiwa Nenne ciwo, sannan cikin fushi ya ce. "Ki tashi
ki tafi gidan Arɗo na sakeki, kada in kara ganin kafarki a gidan nan!!". Ya kai
karshen maganar tare da jefar da sandar ya nufi waje cikin fushin da tun bayan
mutuwar maman Mahnoor bai sake shiga fushi irin wannan ba!.

Rushewa Diddi Mairo ta yi da wani irin kuka mai tsuma zuciya, bata taɓa tinanin
zai iya sakin Nenne ba, saboda auren gida ce, sannan kuma kanwa ce ga mahaifiyar
Mahnoor, ai ko ba komai sirirkinsa Arɗo ya yi mashi halaccin da ba kowa zai iya yi
ba.

Amma kuma idan aka dubi tsawon shekarun da Nenne ta kwashe tana gana mashi azaba
kowa yasan ya yi hakuri, kwata kwata bashi da kwanciyar hankali da ita, masifar yau
daban na gobe daban, ga rashin zaman gida, bini bini tana yawon makota, ko girki
bata zama ta yi mashi bare sauran abubuwan da yazamana hakki a kan mata ta yi wa
miji, kai ya yi namijin ƙoƙari sosai da halinta dik da cewa shi kansa yasan alhakin
maman Mahnoor ce yake bibiyarsa shiyasa ya haɗu da ukubar second wife, amma dai ya
yi

Please Login or Register in order to submit comment