You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

your time, her number isn't going now, before i called her more
than 30 times she didn't pick the call, yanzu kuma the number was not going, switch
off".

Momma bata daka ta tashi ba sai da ta gwada kiran number, a kashe suka sanar da
ita, hankalinta ne ya kara tashi sosai.

A hanzarce ta nufi kofar fita, kamar ta mance da guyson a tsaye a wajen. Ganin haka
yasa ya yi saurin rufa mata baya.

Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King. A lokacin har barci ta fara ɗaukarsa, jin
motsin taɓa kofa yasa ya farka.

Ganin sune yasa ya yi saurin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin. Wajen switch momma ta
nufa, dama iya lamp ne kunne a ɗakin, so sai ya kunna wutar gabaɗaya.

King he was very shocked na ganinsu a tare da kuma ganin yadda suka shigo momma a
hargitse, da Momma ita kaɗai ce ba zai ji komai ba, amma a tare da guyson sai ya
zaci ba lafiya ba, dik tinaninsa ta ta'allaka a kan ciwon guyson ɗin ne ya hanasu
rintsawa.

A ƙage da son jin cikakken bayanin meyake faruwa yake binsu da kallo. Ita ma Momma
kallonsa take yi ta rasa ta ina zata fara, dik yadda take ji a ranta take kuma
tsananin tsorace a kan me ya sami yarta, hankalinta yake tashe ganin face ɗin King
yasa ta ji nata tashin hankalin wasa ne a kan wanda shi zai shiga idan ya ji me ya
kawosu.

Guyson ne ya katse masu kallon juna da suke yi ta hanyar ƙarisawa gaban bed ɗin,
tamkar zai rushe da kuka ya ce. "Daddy Auta bata nan, mun duba ko'ina amma bamu
gan.........."

Wani irin birki ya ci tare da haɗiye sauran maganganun a cikinsa, ba komai ya ja
hakan ba kuma face idanu da King ya zaro mashi tare da zabura ya yaye bargon dake
jikinsa. Ai bai san time da ya sauko ƙasa daga saman bed ɗin ba.

Idanunsa a kan momma ya ce. "Da gaske ne abin da Omar ya faɗa?".

Kai kawai ta iya jinjina mashi ta kasa yin magana.

"To ina ta je? Kun duba dik part's na cikin gidan nan?".

Guyson ne ya tabbatar mashi da tabbas ya duba ko'ina bata ciki.

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne abin da King ya furta kafin ya nufi waje
da sauri.
Bayansa suka bi, a parlour ya tsaya tare da harɗe hannayensa saman kirjinsa, tunani
ya fara yi a kan ina Auta ta tafi? In dai bata cikin kingdom ɗin nan to tabbas
hanune ya ɗauketa, saboda ba ta yadda za'ayi wata halitta ta iya ketare gates ɗin
nan gabaɗaya ta fita ba tare da saninsa ba! To ina take kenan?. Ya jefawa kansa
tambayar da bai san amsarta ba. Zuciyarsa ta cika tab da tunani haɗe da ruɗani mai
tarin yawa.

A nan momma ta isko shi, cike da tashin hankali ta ce. "Yanzu me abin yi?".

Guyson dake tsaye a kusa da momma idanunsa sun ciko da kwallah King ya ɗaura
idanunsa a kansa. "Ɗauko mun wayata Omar"........... Ya faɗa tamkar wanda yake
koyan yin magana, a hankali.

Cikin zafa guyson ya juya ya koma cikin master room ɗin. Kallon juna King da momma
kawai suke yi babu wanda ya iya furtawa ɗan uwansa word.

A haka guyson ya dawo ya samesu, wayar ya miƙawa King, da sauri ya karɓa ya shiga
latsawa.

Karata ya yi a kunnensa tare da matsawa gaba kaɗan.
Binsa da kallo kawai suke yi momma kamar zata ɗaura hannu bisa kai ta
zunduma ihu, wannan bala'i dame ta yi kama? Abin ya yi mata yawa, Jaish ya ɓace
shiru shiru tsawon watanni babu shi babu labarinsa, ta danne sai dai ta yi kuka a
ɓoye, a fili tana nuna kamar bata damu ba, ta jajirce wajen shanye madarar
bakincikin, yanzu kuma ace Auta ta sake ɓacewa basu san ina take ba? Ai gara mata
Jaish namiji ne kuma babba ne, Auta fa? Mace kuma yarinyar da ko 14 years bata cika
ba, dole hankula su ɗugunzuma su tashi.

"Abbas ka bincika mun Zunaira tana ɓangarenka ne!"........... Cewar King da ya
kara waya a kunne.

Da sauri su momma suka kara nitsuwa haɗe da kara tsaresa da idanu da kyau.

Uncle Abbas da yake zaune saman dadduma yana gabatar da nafilfilin dare ne ya yi
saurin miƙewa tsaye, dama ya idar yana addu'oi ne.

Mammie tana kwance saman bed tana barcin asara, kun san ita fa yanzu ba sallah take
yi ba, sai shirka.

Uncle Abbas tin ba'a gaya mashi ta ɓata ba ya shiga tashin hankali, yanzu ai suna
nemanta ne, a tinanin kowannensu tana cikin gidan, sai da King ya kira kowannensu
har uncle Taheer ya ce su dubata, sai a sannan ne idanunsu ya fara rena fata, dan
dik in da suke tinanin tana wajen babu ita, a yanzu kwata kwata basu sa a ransu
kasheta ma aka yi ba, tun da ba'a ga gawarta ba, sun fi sawa a ransu saceta aka yi.

Shi King kam ma kai tsaye King Al-Mustapah ya ɗaurawa zargin yin hakan, dan in baku
manta ba ya kawo masu jiyara yau da rana, kuma shi abokin gaba ne, so dole a
zargesa.

King yana zargin shi ya saceta dan su cinwa wani buri nasu a kan kingdom of power.

Shi kuma uncle Abbas yana zargin Queen Zarina ce ta turo mutanenta suka saje da ƴan
biki suka shigo suka ɗauke Auta, kowa da abin da yake zargi yake kuma hasashe, sai
dai babu wanda ya yi hasashen ta mutu mai gabaɗaya ta bar duniya.

Dik tsananin taurin zuciya da jarumta haɗe da dakiya irin na King sai da ya shiga
tsananin tashin hankalin da yake ƙoƙarin fita hayyacinsa a lokacin da suka tabbatar
da bata a cikin Kingdom ɗin, dan dik wasu sassasa da mutum zai iya zuwa a cikin
kingdom ɗin nan sai da suka je suka duba.
Kowa ya tashi daga barci har da su Mummy, King ya tashi kowa, commander Zafar kam
shi ne mutum na uku da King ya fara tasa daga barci bayan uncle Abbas da uncle
Taheer.

In short Akka ce kawai ba'a sanar da ita abin da yake faruwa ba, ita ma saboda bata
da lafiya ne kada ciwon ya kara tsananta suna iya rasata a kan hakan, shi ne yasa
suka ki sanar da ita.

Jigum jigum suka zauna cikin parlourn King, su commander Zafar kuwa sun gama kewaye
kota ina da warrios a cikin kingdom ɗin anata kai komo wajen nemanta.

Lokacin da commander ya zo sanar da Hoorain ga halin da suke ciki gimbiya Zunaira
ta ɓata, sai ya tarar da shi da zazzaɓi mai tsananin zafi, jikinsa ta yi zafi jaw
kamar wuta, hakan yasa ya fasa gaya mashi halin da ake ciki, ya ɓoye mashi, ya ce
ya zo duba shi ne kawai.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Gabaɗaya family hankulansu in ya kai miliyan ta ya tashi, harta maman Yah Ramish ta
shiga damuwa matuƙa, mummyn Chuchu har kusan kwallah ta yi, Momma kam ba'a magana,
tana tsaye taki zama, kamar wanda aka sassaƙa.

Kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare zaune a cikin parlon King, lokacin da
aka yi kiran sallar asuba ta farko King ya fito waje hararbar kingdom ɗin, dan yana
zargin warriors da commander zafar ya wakilta wajen nemanta a dik wasu lungu da
saƙo na kingdom ɗin basu duba da kyau ba, so sai ya fito da kansa dan ya duba.

Momma ta so binsa, sai dai kunsan a doka irin tasu ba zata fita waje ba,
killacesu ake yi, matan sarki bayi da warrios basu da damar ganinsu, suna da
ƙaidoji da dokoki masu karfi.

So Mummyn Chuchu ta riketa ta hanata fita.

Dik yadda King yake tinani abin ya wuci nan, dan babu in da basu duba ba babu ita
babu labarinta, da kyar uncle Abbas ya rarrashesa suka koma ɗakunansu dan su shirya
zuwa masallaci.

Yau gabaɗaya zargin Momma a kan maman Yah Ramish yake, dama ta jima tana zarginta,
kawai tana dannewa ne saboda bata san tashin hankali, amma yau a kan ɓatar Zunaira
wlh ba zata ragawa kowa ba, dole ta fito da zarginta ta ɗaura a kan wanda zuciyarta
take raya mata!!.

Lokacin da su King suka dawo daga masallacin sallar asuba, babu ɓoye ɓoye suka
sanar da matan cewa Auta fa bata cikin kingdom ɗin nan, ta ɓata, dan haka kowa ya
zage da yin addu'ar Allah ya bayyanata.

King yana sanar da su gabaɗaya parlourn ya dauki shiru mai tsananin girma fiye da
kowanne kuka. Momma zube gwiwowinta a kasa ta yi, nan take hawaye suka fara gudu
ba kakkautawa kamar ruwan kogin da ya ketare iyaka a saman face ɗinta.

"Ba zan iya yarda ba! Ba zan yarda cewa Zunaira bata cikin kingdom ɗin nan ba!
Ba zan iya yarda ta ɓata ba!"....... Haka ta fara sambatu, muryarta na kara
tsananta kuka.

King da aka san shi da jarumta, yana tsaye a gefe kamar wanda ya rasa hanyar
tunani. Idanunsa cike da hawaye da ba ya so su zubo, amma ba zai iya hana su ba. Ya
harɗe hannunsa a saman kirjinsa, yana kallon momma ya kasa yin magana.
Guyson ne ya ce. " Dad Momma wai me na yi wa duniya har za'a kashe ni da irin
wannan bakin azaban ciwo mai tsananin zafin? Da a ɗauke Zunaira ai gara ni a
kasheni!"............ Ya tambaya da muryar da ta nuna karayar zuciyarsa. Guyson mai
saurin kuka yau dai hawaye taki fitowa, sabdoa azabar dake cikin ransa ba zata iya
baiwa hawaye gurbin fita ba!.

Yah Jawad wanda idanunsa yake yi mashi gizon Auta tana tsaye kusa da guyson tana
murmushi ne ya kasa iya furta word. Kamar ma baya cikin hayyacinsa sosai.

Su uncle Taheer sun kasa yin magana, sai kawai kukan zuci da suke yi. Fanan da ta
manne da Chuchu ce a cikin ranta ta ce. "Auta ta kasance mai kawo dariya da
farinciki a kan fuskar kowa dake gidan nan, ta sanya zuƙatan kowa a nitsuwa, sanyi
idaniyar kowa, yanzu ace babu ita? Kai anya zasu iya ɗauka kuwa? Gurbin ta tamkar
rami ne mai zurfi wanda babu abin da zai iya cikawa a zuƙatansu".

Kowanne daga cikin su yana tuna abubuwan da ta yi na alkhairi, irin murya mai daɗin
da ke jansu cikin farinciki, yadda take cika gida da rayuwa da ƙauna.

Chuchu dai ganin abin kamar mafariki take yi, hakan yasa bata iya furta word ba,
tana dai binsu da ido, gata nan gata nan kamar wadda aka sassaka ta kasa motsawa.

Momma kuwa kara fashewa da kuka mai sauti ta yi, hakan ya ja hankalin mummyn Chuchu
a kanta, da sun afka duniyar tunanin ina Auta take? Jin kukan Momma yasa suka yi
saurin karisowa in da take.

A tare Mummyn Chuchu da Maman Yah Ramish suka tsugunna a gabanta, a tare suka kai
hannu suka rungumota.

Cikin ɗaga murya momma ta ce da mama kada ta sake taɓata!. Tashin hankali.

Nan fa kallo ya koma kansu a cikin parlourn, yadda Momma ta yi maganar ya girgiza
kowa. King da yake tsaye kaman wanda aka sassaƙa ma sai da ya ji gabansa ta faɗi ya
dawo cikin hankalinsa.

Mama da bata gane me Momma take nufi ba, a tunaninta saboda raɗaɗin rashin ƴar tata
ce yasa take sambatu, sai bata saketa ba, sai ma ta yi ƙoƙarin goge mata hawaye dan
ta rarrasheta.

A tsananin fusace momma ta kwace kanta daga riƙon mama, take ta fara huci kamar
zakanya tana jin yunwa, cikin zafa ta ce. "Idan kika sake taɓani dik abin da na yi
maki ke kika nema!!". Babbar magana!.

Ganin hakan yasa su Jawad gabaɗaya suka matso kusa da su, so suke yi su kwantarwa
da Momma hankali da kalamansu, amma dikkansu babu wanda yake da kalmar da zai iya
tinkarar momma da shi.

Dan haka sai dai suka matso suka tsaya jugum jugum kaman wasu gumaka.

Allah sarki Chuchu da ta ɗauki abin matsayin mafarki ba gaskiya ba, dik da haka
hawaye ne yake gudu a saman face ɗinta kamar ruwan pampo, tana tsaye kamar wadda
aka sassaƙa, da alama bata a cikin hanyacinta.

Wai a haka sun ɗauka sace Auta aka yi, to idan suka san ta bar duniya mai gabaɗaya
me kuke tinanin zai faru? Akwai bala'i gaskiya.

Da kyar King ya iya motsa laɓɓansa da suka yi mashi masifar nauyi ya furta kowa
dake cikin parlourn nan ya je su kyale shi daga shi sai Momma bari su yi magana.

Babu musu kowa ya nufi waje, Mummyn Chuchu ta saki momma ta miƙe, a babban
parlour suka haɗu suka zauna jugum jugum.

Chuchu ta kasa motsawa har sai da Yah Jawad ya tallaɓota ya ja suka fita.

King da Momma kawai aka bari a cikin parlon King, harta Guyson mummyn Chuchu ta ja
shi sun fita wajen, kamar ba mutum ta rike ba, dik ya sake mata jiki kaman wanda ya
sume, Allah sarki bawan Allah, da alama ya fita hayyacinsa ne.

King da momma sun ɗauki a kallah 30 mins suna tattaunawa ta sirri, kafin daga
bisani King ya rarrasheta tare da gaya mata wanda yake zargi da sace Auta wato king
Al-Mustapah kenan, kuma ta kwnatar da hankalinta cikin ƙanƙanin lokaci za'a dawo
mata da Auta lafiya lou In Sha Allah, yanzu za'a shirya dakarun yaki domin tinkarar
Daular Qahtaniyawa, tun da sun tsokalo yaki dole a yakesu.

Aunty MieMie dai bata da labarin dik abin da yake faruwa, tana can ɓangarenta tare
da mijinta. Tsabar tashin hankali yasa suka manta da ita ba'a sanar da ita ba!.

Momma da kyar ta hakura ta yi shiru, hakan ma dan King ya yi mata alkawarin
dawo da Auta cikin kwana ɗaya ne.

Cikin bedroom ɗinsa ta shiga ta kwanta, shi kuma ya wuce toilet, wanka ya yi tare
da shirin tafiya fada, nan ya buƙaci Commander Zafar da ya kira mashi Hoorain ya
kuma haɗa kan mayaƙa tawagar farko.

Me zai yi wa Hoorain kuma?.

===========================🔥

Karfe 9 daidai gabaɗaya manya manyan jiga jigan masu faɗa a ji a cikin fada suka
haɗu, hankalin kowa in ya kai miliyan a tashe yake, dik sun nitsuwa tsit suna cikin
alhini, dik wanda ya ɗaga idanu ya kalli fuskar King ba zai so ya sake ɗaga idanu
ya kallesa ba, saboda fuskar a ɗaure take, uban kwarjininsa ta kara bayyana, zarra
ga marasa adalci da san gaskiya kenan.

Yana dake saman kujerarsa, yau babu wargi bare wasa, su commander Zafar dik sun
shiga taitayinsu, kowa yana nan bisa ƙaida, dik sun tattaro hankulansu a kan King
Zuhair, shi kawai ake jira da ya yi magana.

Dai'dai lokacin da Hoorain ya dimfaro babbar kofar fada da nufin ya shigo ciki
dan amsa kiran da King ya aika ayi mashi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan baya a
cikin hayyacinsa sosai, dik ya firgice, tamkar wanda aka zarewa laka, yana yafiya
yana jan kafafu tamkar ba sadauki Hoorain assistant commander ba, jarumi mai tafiya
cike da zarra da kwarjini mai razanar da zuƙatan dik wasu warriors dake cikin
kingdom ɗin, amma yau ya taho tamkar mace yana wani jan kafa.

Masu gadin kofar fada har sun bashi hanya, ya matsa gada da su kaɗan har ya kusa
shiga fada, kunsan dai'dai in da suke tsaye domin gadin kofar akwai ɗan tazara
tsakaninta da kofar, a kasar stage na hawa suke tsayawa, kofa kuma tana sama.

So sun bashi hanya zai wuce, ya haura saman step ɗai ɗai har uku zai taka na huɗu
kenan ya tsinkayo muryar King ya fara magana cikin kakkausar murya da zafa, dama ga
voice ɗinsa da kaifin bala'i, hakan ya yi gaggarumin ɗaga hankulan su commander.

"Kaiconku! Kun bani kunya kuma na raina kwarewarku! Commander kana da shekaru
sama da talatin kana matsayin mai jan ragamar warriors da suke cikin kingdom ɗin
nan, amma yau har a samu wani mai karan kwana da zai iya keta tsaronka ya shigo har
cikin kingdom ɗin nan ya ɗauki Zunaira ya fita da ita! A gaskiya ka gaza dayawa
Zafar!"............ Shi ne abin da King ya faɗa a kan kunnen Hoorain da ya dakata
da yunƙurin shiga fadar ya kasa kunne yana sauraronsu.
Kasa da kai commander ya yi, bashi da bakin yin magana tun da ba'a bashi izini ba,
sai kawai ya yi ƙasa da kai yana sauraron faɗar King.

Cigaba da faɗa cikin zafa King ya yi.

"Dole hukunci zata hau kan Hoorain! Saboda shi na ɗaurawa alhakin kula da
Zunaira! Shi na ɗaurawa alhakin kada ya bari ko guda ya taɓa mun ita, dan haka idan
wani abin ya samu Zunaira dole in hukunta shi!!"..........

A dai'dai wannan gaɓa sai da commander Zafar ya yi hanzarin ɗago kansa da kallonsa
izuwa kan King, ya ji zazzafar magana da baya jin zai iya jure hakan, wato hukunta
Hoorain, yasan hukuncin King bata da sauki, bare kuma a kan Auta, ai ina abin ba
zata yi kyau ba.

Sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi, gaban maza sai da ta bada dukan uku uku,
Hoorain shi ne farincikinsa, sannan ace za'a hukunta shi da laifin da bai sani ba?
Gaskiya a wannan gaɓar baya jin zai iya ɗaukar wannan hukunci na King, to amma ya
zai yi? Ya jefawa kansa tambaya. Sai sake sake yake yi a cikin zuciyarsa ya daina
sauraron abin da King yake faɗa.

Kamar daga sama ya ji warriors dake tsaye a kusa da shi ya kai hannu ya taɓa shi
yana faɗin. "Master King yana magana".

A ɗan zabure ya miƙe tsaye, bawan Allah ya afka duniyar tunani ne bai ji King yana
tambayarsa ina Hoorain ɗin yake ba?.

Ran King ne ya kara ɓaci na ya yi magana commander bai jisa ba, kun san idan
mutum yana cikin ɓacin rai da zarar an mashi abu kaɗan zai tashi ya hau bala'i, to
haka abin take.

Ɗan risinar da kai ƙasa commander ya yi alamar girmamawa.
"Kayi hakuri ranka ya dade, tun ɗazun da kace in kira Hoorain ɗin na
faɗa mashi kana kiransa, ban yi tsammanin zai kai har iyanzu bai iso ba!".

Sosai ran King ya kara bakanta, a ɗan fusace ya umarci ɗaya daga cikin warriors
dake cikin wajen a kan su kira mashi Hoorain yanzun nan, sannan kuma dole ya
fuskanci wani hukuncin a kan jinkirin da ya yi bai amsa kira ba.

Dik maganganun da suke faɗa a kan kunnunsa suka yi ta, ya ji komai! A maimakon ya
shiga cikin fadar ko hakurine ya bawa King ko zai samu sassaucin hukunta shi da
za'ayi, sai ya juya ya fasa shiga, cikin sassarfa ya bar wajen. Masu gadi kuwa basu
ce da shi ko uppan ba!.

Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma. After 5 mins da shigansa cikin ɗakin ya fito ya
nufi katafaren wajen dawakansu, dik da yana sanye cikin kayan yaki ya ɗaura jacket
mai girma a jikinsa, ya kuma sanya hular jacket ɗin a kansa, hakan ba zai hana ka
gane yana cikin tashin hankali na kin karawa ba!.

Saman wannan ƙosasshen jibgegen dokin nasa ya hau. Da karfi ya bawa dokin
wuta, kai tsaye babbar gate na Kingdom ɗin ya nufa.

Tun daga kan gate na farko har izuwa babba na karshe babu wani warriors da ya
dakatar da shi ko ya ce zai hana shi fita ko dai ya tsaya a bincikesa, saboda dik
wanda ya kwana ya tashi a cikin kingdom ɗin yasan wanenen Hoorain kuma me
matsayinsa, dan haka basu yi gigin dakatar da shi ba, sai ma hanya da suka bashi
cikin girmamawa ya danna waje a miliyan.

Ina kuke tunanin zai je? Meyasa yaki amsa kiran King? Meyake shirin faruwa ne?
Guduwa ya yi ne ko menene?....................

=======================🔥

Dai'dai lokacin da wannan warriors da King ya aika da ya kira Hoorain ya dawo cikin
fada dan ya isar da sakon Hoorain baya nan bai gansa ba, a dai'dai wannan lokacin
uncle Jahiz ya danno kai cikin fada, ta kofar da zata sadaka da cikin gida kenan.

Sun jero a tare shi da Jaish, tin ɗazun suka shigo cikin kingdom of power, yanzu
haka basu fara isa ga kowa ba sai da suka iso ga King.

A karo na farko a tarihin kingdom of power yau King bai san lokacin da ya miƙe
tsaye daga kan kujerar mulkinsa a zabure ba lokacin da ya ɗaura idanunsa a kan
Jaish.

Tun da King yake bai taɓa jin wani abin na tashi hankali ko na farinciki or
al'ajabi da zai sanya shi ya zabura ya miƙe tsaye daga saman kujerarsa ba sai
dawowar Jaish unexpext, Ramish ya iya bazata kam gaskiya.

Sun jima suna dakon wannan rana shi da Momma, kullun addu'arsu Allah ya bayyana
masu ɗansu farincikinsu, sai ga shi Allah ya bayyana shi a lokacin da basu tsammata
ba, lokacin da suka fidda rai suka yanke kauna, suna cikin wani tashin hankalin
kawai ya dawo garesu unexpext, kai Allah abin godiyane matuka, ya baka wani lokaci,
wani lokaci kuma ya hanaka, dik cikin ikonsa da kyautatawansa ne!!.

Dik da commander yana cikin tashin hankali da damuwar furucin King a kan Hoorain
zai karɓi hukunci hakan bai hana shi ya zaro idanu yana kallan Jaish ba.

Gabaɗaya su salama sun zuba mashi idanu, suna san yi mashi sannu da dawowa, amma
babu hali, dan King bai bada damar ayi magana ba.

King ɗin kuwa, ya tsaya ne tamkar wanda aka dasa. Idanunsa sun zaro waje sosai,
kallonsa a kan fuskar jaish ɗinsa da ya ke kallan abin tamkar a mafarki ko kuma
zuciyarsa ce take yi mashi gizo.

Karisowa gabansa Jaish da uncle Jahiz suka yi, shi Jaish mamakin irin kallansa da
King yake yi mashi ya yi, saboda in baku manta ba a baya ya yi loosing memorunsa
ne, yanzu ne ya dawo dai'dai, so shi bai san da cewa ya jima baya gida ba, ya mance
da rayuwarsa ta baya wato na gidan bappa kaf.

Har sai da Jaish ya tsugunna a gabansa domin kwasan gaisuwar ban girma wanda kun
san yin hakan dole ce a sarauta matuƙar masu gudanar da mulkin irin King Zuhair ne
masu ƙarfin izza.

Jin bugun numfashin ɗan nasa a kurkusa da shi ne yasa ya gasgata abin da idanun
nasa suke gane mashi, amma dik da haka sai da ya ce.
"My Jaish kai ne? Hakika kai ne ɗana, tabbas kai ne!"............. Ya yi maganar
cikin murya mai sanyi, amma cike da rawar jiki.

Bai jira amsar Jaish ba, ya yi sauri duƙawa ya ɗagosa ya jawo shi jikinsa ya
rungume.

Rungumar tasa tana da ƙarfi, cike da kewar watanni da suka wuce. Ya rike jaish gam
kamar kar ya sake barinsa ya motsa ko nan da can, kamar kada ya raba jikinsu
tsantsar so da kauna.

"Na jima ina jiran wannan rana, mun jima muna neman ka........... ba zan sake
rabuwa da kai ba!".
Ya furta cikin farinciki wanda ke haɗe da murmushi mai bayyana farincikin
sosai.

Jaish da bai gane me King yake magana a kai ba sai ya ce. "Dad ba zamu rabu ba ai
dama".

Kara kankamesa sosai King ya yi tamkar zai mayar da shi cikin cikinsa. Sai murmushi
uncle Jahiz yake yi. Gabaɗaya fada sai da suka ɗan murmusa ban da commander wanda
dama shi baya yin murmushi, sannan kuma ya kara haɗuwa da yana cikin damuwa King
zai hukunta mashi ɗan gold ɗinsa.

Dawowar Jaish ya sanya su farinciki ya kuma sanyaya masu zuƙatansu akan raɗaɗin da
suke ciki na rashin gimbiya Zunaira.

Yanayin ya cika da farinciki mara misaltuwa, kamar duniya ta tsaya domin
wannan lokaci na musamman. Kowannensu yana jin tamkar zuciyarsa tana kara kaunar
juna. Wannan haɗuwa ta koma alamar soyayya da ƙarfin alaƙar uba da ɗa, wanda baki
ba zai iya misiltawa ba.

Uncle Jahiz ne da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya matso ya ɓanɓanre
Jaish daga jikin King yana faɗin.
"Is okey yaya, Jaish lest go to ur mom room, I want to see her reaction a
lokacin da zata ɗaura idanunta a kanka".

Ɗan ɗaure fuska kaɗan Jaish ya yi. "Uncle sai ka ce wanda ya ɓata tsawon lokaci
sai yanzu aka ganesa? Tafiya fa nayi na je na dawo, kaga dad ma sai wani ƙanƙameni
yake yi".

Tun da ya fara magana idanun King a kansa, sai yanzu suka fahimci Jaish fa bai
san komai dangane da ɓacewansa na tsawon watanni ba, dan haka sai King ya ce Jaish
ya je wajen mommarsa da wuri, ya ce mashi hakan ne kuma dan yana da yakinin zata
rage damuwar da take ciki a halin yanzu idan ta gansa.

Aikuwa hakan ce ta faru. Lokacin da suka haɗu da momma a bedroom na King, hawaye
masu ɗumin gaske ne suka fara kwaranya daga idanunta, tamkar ruwan sama mai ɗauke
da albarka. A hanzarce ta sauko kasa daga saman bed ɗin King, da sauri ta kariso ta
rungume shi da karfi, numfashinta yana cike da farinciki mara misaltuwa.

Ganin abin take yi tamkar a mafarki, shi kuma mamakin hakan yake yi, dik da yasan
cewa

Please Login or Register in order to submit comment