You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba surutan nata.

Silent talk ya yi wajen cewa. "


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Silent talk ya yi wajen cewa. "My Hoonaira dama zaki sake yin tinanina har kizo in
da nike?".
Kuka mai narka zuƙatan masoya ta saka mashi, a hankali take ɗan bubbuga
hannunsa a saman lion chest ɗinsa, da kyar muryarta ya samu damar fita ta fara
faɗin.

"Kamanta dama na faɗa maka ko zan mutu babu gudu ba ja da baya ne? Ba zan
taɓa iya rabuwa da kai ba, kai ɗin jinin jikina ne, please my Hero kada wani wuya
yasa ka juya mun baya, In Sha Allah zamu yi nasara, nasan daddy yana kan fushi ne,
idan ya sauko zai saurareni, please ka t............".

Wani irin tari ne ya kubce mata wanda ya sanyata dan dole ta haɗiye sauran
maganganunta, hannunta tasa da sauri ta toshe bakinta gudun kada tarinta ya fita ya
sanya masu gadin su fahimci akwai mutum a ciki.
Su fa Modarawa haka suke da zuciyar bala'i, kada ku ga laifin King, zuciya a
jininsu take, basu isa su cirewa kansu ba, shiyasa kuka ga King a haka, wai baku ga
dikka jikokin Akka idan sun fusata haka suke rikiɗewa su zama basa ji kuma basa
gani bane? To gado ne shi ma wannan tin zamanin jahiliyyah.

Allah sarki yana san rungumarta ya rarrasheta amma babu dama, saboda dikka
hannayensa a ɗaure suke. Yana jin raɗaɗin kukan da take yi har cikin ransa tana
ratsa shi, amma babu halin taɓuka komai, muryarsa bata fita sosai yake ta faman ce
mata ta yi shiru ta daure, sam bata jin me yake faɗe, sai da ta yi kuka sosai har
tasa zuciyarsa ta fara yi mashi ciwo, sannan ne ta komar da kanta saman kirjinsa ta
kwantar tana shessheka mai taɓa zuciya.

A hankali ta zame hnnunta daga ɗan bakinsa, sannan ta ɗago kafafunta tare da sanya
hannayenta ta saƙalo wuyarsa da shi, ta haɗe fuskokinsu waje guda, murya a sarkafe
ta ce. "My Hero, promise that ko wani hali zamu shiga tabbas zaka tsaya a kan
soyayyarmu babu gudu ba ja da baya".

A yadda take maganar lausasan lips ɗinta suna taɓa nashi yasa gabaɗaya ya jisa a
wani sabon babin na yanayi, gabaɗaya sai ya kara jin kasala sosai, dama ba wani
kwari ne da jikin nasa ba. Da kyar ya iya cewa. "Ba zan taɓa juya maki baya ba my
princess, dik wahalar da za'a bani matsawar ina numfashi to tabbas zuciyata zata yi
kowacce bugawarta ne da sunanki, ba zan janye ba sai dai a kasheni ko kuma ke ki
juya mun baya!!".

Kai ta fara girgizawa kafin ta ce. "Ba zan taɓa juya maka baya ba ka ji?". Kai
kawai ya jinjina mata yana cigaba da sauke numfashi mai ban tausayi.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Khadijah and Zee ne zaune a saman sofa a part ɗin mama bedroom na Aneesa. Su biyu
ne kawai a cikin ɗakin, sai hira suke yi Zee tana jin daɗi Khadijah ta samu lafiya.

Khadijah dai ciwo bai rage mata komai ba, sai kiba ma da ta kara, kumatunta ɓulɓul
gwanin sha'awa, momma ta ce ta fara bawa babynta nono tin da ta samu lafiya, dan
nonon uwa ba ƙaramin abu bane, idan yaro ya rasa shi ma sai kuga ya girma ga shi ga
shi nan ne kawai.

So tana rike da babyn a hannunta, dikkansu kayan Aneesa suka sanya, sun yi kyau
matiƙa, sai dai dik in ka kalli face ɗin Khadija zaka kalli tana cikin bakinciki,
dan damuwa na cunkushe a ranta, wai a hakan ma dan likitoci sun ce ta cire damuwar
dake ranta in ba haka ba zata iya kamuwa da ciwon zuciya, shi ne fa ta ɗan rage.

••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Aunty Khadijah tin da kin samu lafiya yakamata mu koma Nigeria ko?". Cewar Zee.
Yadda ta yi maganar tasa Khadijah ta zargi wani abin. Cike da mamaki Khadijah ta
ce. "Kina da matsala da nan ɗin ne?".

Kai ta jinjina da sauri tana amsawa da e tana da matsala. Nisawa Khadijah ta ɗan yi
kafin ta amsa da.
"Meyasa Zee dik in da muka je sai kin yi wa wajen mummunar zato ne? A nan ɗin
ma nasan cewa zaki yi kina zargin wani abin ko?".
Kai Zee ta gyaɗa. "To Aunty Khadijah ki faɗa mun wani waje ne da na yi wa mummunar
zato bai zama sharri a garemu ba? Kina dai gani mai napep da ya ɗaukemu daga kawo
Kaduna da nace ban yarda da shi ba, kin dai ga sace mu ya yi izuwa Abuja, Allah ya
kuɓutar damu, muka sake faɗawa gidan matar can, ita ma na ce maki ban yarda da ita
ba, haka kika matsa mu zauna da yanzu babu junior ta sacesa, nan ma Allah ya karemu
da kariyarsa, muka tsallaka rijiya da baya, kinga kuwa ai ba kya tuhumeni a kan dan
nace nan ma ban yarda da su ba, basu kwanta mun a rai ba".

Tun da ta fara magana Khadijah take binta da kallo tana sauraronta har ta kai aya,
sannan ta ce mata. "To ke yanzu meyasa kike zargin wannan gida?".

Ajiyar zuciya Zee ta sauke, juya harshe ta yi izuwa turanci, sannan ta ce. "Saboda
wannan ɗan kwallon, ina zargin yana shigo mana ɗaki da daddare, sannan kuma yana
yawan sakawa dik wani motsina idanu..........."

A hanzarce Khadijah ta katseta da cewa. "Wani ɗan kwallon kenan?". "Jahiz mana". Ta
bata amsa tana kara ɗaure fuska.

Zaro idanu sosai Khadijah ta yi zata yi magana daga bakin kofa suka jiyo muryar
Aneesa cikin harshen turanci ita ma tana faɗin.
"My second dad ba yadda kika ɗaukesa yake ba, ke ba abin alfahari bane ma a
wajenki ki ce kin taɓa ganin shi a zahiri? Na tabbata dik wanda zaki ce wa kin taɓa
ganin uncle na a zahiri ma ba yarda zai yi ba, domin baki yi kalar wadda ta taƙa
matsayin da zata samu damar ganinsa a zahiri ba".

Ɗan siririn tsaki Zee ta ja, a kule ta ce. "Then so what? Kuma da kike wannan
magana ce maki aka yi wata tsiya ce shi? Ko an faɗa maki Nigeria irin nan ne da
zamu yi alfahari da ganinsa?".
Zee ta samu Khadijah ta samu lafiya yanzu kuma su Aneesa sai sun sarara mata,
dama saboda lafiyar Khadijah ta koma baya ta yi zaune, yanzu kuwa kowa zai sha
mamakinta, ba ɗaga kafa.

Wani irin matsiyacin kallo Aneesa ta wurga mata kafin ta ce. "Ni ba mate naki
bane okey? Ki rike words ɗinki da kyau kada ki bari su kubce maki a kai'na, dan
zaki yi danasani, rubbish useless people kawai". Ta yi maganar tana dalla masu
harara.

Da sauri Zee ta buɗe baki zata mayar mata da martani, a hanzarce Khadijah ta
tareta da faɗin ta rufe bakinta a wajen. Ranta ne ya ɓaci sosai, ba zata iya yi wa
Khadijah musu ba, dan haka sai ta miƙe da sauri ta nufi waje, Khadijah na kiranta
amma bata tsaya ba, ta ce ita ta bar wannan ɗaki ma ba zata sake dawowa ba, gara ta
kwana a waje da ta sake kwana a ɗakin, kun san mutuniyar da shegen zuciya.

Tana fitowa ta nufi elvator, ƙasa mai gabaɗaya ta yi domin ta fita waje. Ita da
bata san ko'ina ba amma saboda zuciya sai gata a tsakar kingdom ɗin, ta ko'ina
warriors ne suke shawagi dan tabbatar da tsaro. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan
yadda hasken bulb suka haska harabar kingdom ɗin tamkar rana, ko allura ka jefar
zaka iya tsinta.

Wani ɓangare na zuciyarta ne ya zugata wajen ce mata ta ɗan yawata cikin kingdom
ɗin mana ko zata huce kafin ta koma ciki ta je su kwana a tare da Pretty, dan ba
zata sake komawa part ɗin mama ba, kun san zuciya da sake sake, sai ya rinƙa saƙa
mata tabbas Aneesa ta ci mutumcinta.

A hankali ta fara taka kafarta tana tunane tunane ta fara kewaye cikin harabar
family part. Wasu warriors guda biyu ne suka nufota cikin takun jarumta. Ta ɗan ji
tsoro da ta gansu, amma haka ta daure ta cigaba da tafiya suna tinkarar juna.

A gabanta suka tsaya, cikin girmamawa suka ce ko tana buƙatar wani abin ne ta fito?
Kai ta girgiza masu kafin ta amsa masu da bata buƙatar komai, shan iska kawai ta
fito yi. Ɗaya daga cikin warriors ɗin ne ya nuna mata hanyar babban garden na
family part, sannan ya ce mata ga wajen shan iska a can ai idan tana da buƙata.

Ta ji daɗi sosai, sannan ta nufi wajen tana yi masu godiya. Juyawa warriors ɗin
suka yi suka koma bakin aikinsu........ Sosai Zee ta baza idanu tana kallan
ƙawatuwar garden ɗin nan, ga wasu irin flowers masu kamshin daɗi, a hankali iska ke
kaɗawa yana ratsa jiki, sai ta ji wlh zata iya kwana a nan wajen, haɗuwar wajen ya
tafi da imaninta.

A hankali ta nufi karisawa wajen da luntsuma luntsuman sofas dake wajen wani
ƙayataccen rumfa dan ta zauna a can, tana tafiya tana waige waige dan ta kurewa
ko'ina kallo a cikin garden ɗin. Unexpect suka ci karo da mutum, a razane ta juyo
da kallanta a kansa domin ta ga wanenen?.

Tana juyowa dai'dai lokacin ya ɗaga hannu zai dallah mata mari sakamakon cappuccino
dake hannunsa ta buge mashi ya zube a white sleeping dress dake jikinsa,.hakan ya
kona mashi rai sosai, ga wayarsa da ta buge ya faɗi ƙasa, ya ji zafin hakan natuƙa.

A fusace ya cire hannu zai dallah mata mari, da sauri tasa hannunta dikka biyu a
face ɗinta domin ta kare lafiyar fatarta daga marinsa. Ta datse idanunta gam tana
jiran ta ji saukar mari sai kuma ta ji shiru bai mareta ba. A hankali ta ɗan waro
idanunta domin taga meya hana shi sauke mata wannan mari.

Tsaye yake ya mace da kallan face ɗinta, dalilin da ya dakatar da hannunsa ga isa
fatar kumatunta kenan, da alama a kallan farko ya fola, idanunsa a kan dogon
wuyarta mai kyau da ƙawa. Ganin ta waro kallanta a kansa ya sa ya dawo da kallonsa
a saman face ɗinta.

Kara waro idanunsa waje ya yi yana kallan haɗuwarta, lokaci guda ya wani ja
numfashi tare da mai da kallansa a saman kirjinta. Ita kuwa ganin face ɗinsa ba
ƙaramin girgizata ya yi ba, ta ga kyau na jinin Akka tamu ta amana, sai taga kamar
ya fi kowa kyau a gidan. Yo dama yana kanin Ramish ba dole ya yi kyau ba.
Slowly ta kai kallanta kasa saman kyawawan fararen kafafunsa dake cikin wasu
kyawawan takalma na yawo a tsakar gida, a hankali ta fara binsa da kallo har izuwa
sama dai'dai wuyarsa, sai ta ji nauyin karisa kai kallanta saman face ɗinsa dan
kada su haɗa idanu.

Kasa Dr Raj ya yi da hannunsa ya fasa marin nata, sannan ya ɗan kawar da
kallonsa a kanta yana maidawa kan wayarsa dake ƙasa, sai faman sauke ajiyar zuciya
yake yi. Ganin yana kallan ƙasa yasa ta kai kallanta wajen ita ma. Wayarsa yake
kallah, ɗan satar kallansa ta ɗan yi kafin ta duka zata ɗauka mashi wayar.

Dai'dai lokacin shi ma ya duƙa zai ɗauki kayansa ya wuce, ba tare da sun ankaraba
suka kai hannunsu kan wayar a tare, ta rigasa ɗauka, amma da hannunsu ya goge juna
wani shock da ta ji ne yasa ta saki wayar, shi ma sai ya ja hannunsa baya kaɗan. A
hankali ya ɗago da kallansa a kan face ɗinta, while ita ma dai'dai lokacin ta ɗago
da nata kallan a kan face ɗinsa, wato wannan fa shi ake cewa soyayya a kallan
farko, the most luckys persons.

So idan ta tashi shiga mutum fa wlh bata excuse, wani lokaci ma zaka haɗu da
yarinya da rana, sai da daddare idan ka koma ka kwanta santa ya shigeka im ka
tinata, so, so, so, a karshe dai ao ita ce silar kowa a duniyar nan, bari dai mu
cigaba.

Sarkafe juna da kallo suka yi, Dr Raj ya ga jinin Nigerians ya rasa natsuwa da
control of his heart. Ita ma Zee taga ɗan balarabe jinin modarawa jinin Akka tamu
ta amana ta rasa natsa natsuwar. Sun ɗauki a kallah 2 mins a haka suka kallan juna
ido cikin ido kafin ta yi ta mazan zare idanunta daga kansa, sannan ta miƙa hannu
ta ɗauka mashi wayarsa.

Wai ni kam ba Zee bace ta ce babu ita babu maza? Har da wani cewa ta tsani maza! Ko
dai ba ita bace nikam?! Kaina ya ɗaure, ina ƴan special grp kuzo ku warware mun
kullin dake kai'na,...........🥱

Cikin sanyin murya ta ce. "Am so so sorry, this is ur phone". Ta yi maganar tana
miƙa mashi wayar.
Miƙewa tsaye shi ma ya yi, a maimakon ya karɓi wayar sai ya harɗe hannayensa
a kirjinsa yana binta da kallo. Ɗan ƙasa kaɗan ta yi da kanta, kamar zata saki
murmushi saboda wani irin bargon farinciki da ta ji ya lulluɓe zuciyarta ba tare da
tasan dalilin farincikin ba.

Ya ɗauki a kallah 2 mins again yana ta kallanta kafin ya miƙa hannu ya karɓi
wayarsa, cikin natsuwa ya juya ya nufi hanyar fita, yana tafiya yana waigota, wai a
haka ma dan King ne ya yi mashi waya da ya same shi a main parlour, da ba zai tafi
ya barta ba, sao ya tsaya jin wacece ita, amma King na jiransa, dan haka ya wuce
yana kara waigota.

Ita ma wucewa gaba ta yi, tana tafiya tana waigosa, da alama ta ya burgeta. Saman
ɗaya daga cikin sofas na wajen ta zauna tana dawo da kallonta a wajen, ta fara
rarraba idanu tana kara jinjina irin dukiyar da aka narka a wajen.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥

Mammie and Fanan, zaune suke suna shawarin yadda zasu ɓullowa lamarin Fanan da
Jaish, mammie ta ci alwashi kuma ta yi rantsuwa da Allah sai Fanan ta auri Jaish,
idan ba haka ba Jaish ɗin ya mutu kowa ya rasa, sai tsara yadda zasu wahalar da
Mahnoor suke yi, yanzu Mammie ta gama tsara yadda za'ayi Fanan ta koma part ɗin
Jaish da zama tare da mama Haulat kenan, ta kuma tsarawa Fanan ɗin irin abin da
yakamata ta yi wa Mahnoor idan ta koma can da zama.

Ita kuma Sarina ta gama tsara mata yadda zata buga barikanci wajen samun soyayyar
Jaish ko yaki ko y so, har da faɗa mata wai idan dare ya yi ta rinƙa saka sleeping
dress tana zama a parlour da sunan zata yi kallo, hakan zai rinƙa jan hankalinsa a
gareta, Sarina dai ta bata shawarin zama karuwar cikin gida sosai,......... My
people's me kuke tinani a kan wannan shawari na Sarina? Anya kuna ganin hanya ce
mai ɓillewa Fanan kuwa?.

A gefe guda kuwa, Sarina and abokanan rashin mutumcinta ne suke zaune a rest
parlourn uncle Abbas suna shirya wani makircin, Omaid dai sai chatting yake yi a
Whatsapp da sabuwar budurwarsa, shi kuwa Obaid sai tsarawa Sarina yadda komai zai
gudana yake yi, shiri suke yi a kan yadda zasu ganawa Mahnoor azaba, tana neman da
su tayata tun da kunga su suna da kunama da kwari, shi ne ta nemesu a kan wannan
harka, dama kun san mutanenta ne. Obaid sai tsara mata yadda za'ayi yake yi, shi
kuma Omaid yana chatting.

Sosai Sarina ta so yi wa su Obaid wayo wajen tambayarsu wanenen Omerish? Sai dai
bata fito ta tambayesu wanenen shi kai tsaye ba, gudun kada su zargeta, ta fake da
ce masu.

"Obaid na yi mafarki wani kyakkyawan saurayi mai cikar mazantaka da jarumta, dogo
mai kama da daddy, ga shi da fuskar kwarjini da haiba, fari tas kamar momma, yana
da saje irin na daddy, sai dai kwayar idanunsa irin na Auta ce wato hazel, sannan
sunansa Omerish".

Lokacin da ta ambaci sunansa sai da dikkansu suka ɗago da kallonsu a kanta, lokaci
guda kuma ko me suka tuna suka yi gaggawar kawar da kallonsu daga kanta suka cigaba
da abin da suke yi. Ta fahimci sun yi shock da jin sunan da ta ambata, hakan yasa
ta kara tsananta zarginta a kan abin da suke zargi ita da Mammiensu.

Cigaba ta yi da yi masu zabara dan su faɗa mata wanene Omerish kuma me hotonsa yake
yi a wajen momma da har ta iya ɓoyewa a kasan bed ɗinta bata san kowa ya gani (kun
tuna envelope da ta ɗauka a kasan bed ɗin momma? Hotunan dake ciki kenan, a jikin
hoton matashin ne aka rubuta Omerish, a nan tasan sunansa). Sai dai da yake suma A
ne wajen dabara da kaifin ƙwaƙwalwa sai suka shashantar da ita, suka tsara mata
labarin karya wanda dole in mutum ya ji ya yarda da su. Suma da wayansu ashe.

A ɓangaren guda kuwa, Chuchu and Yah Jawad sai kashe junansu da love suke yi, yanzu
hankalin Chuchu ya kwanta dan Auta ta dawo, sai kashe Yah Jawad da salan soyayyarta
take yi tana rikita mashi ƙwaƙwalwa, dik abin da ta iya dange da soyayya tana iya
kokarinta wajen koyar da Mahnoor, amma ita Mahnoor wai kunyar kwatantawa Jaish take
ji, ga tsaronsa dake ranta, yanzu sun dawo wasan ɓuya ne ma, in yana nan bata
fitowa parlour, sai ta tabbatar ya fita, kuma bata zuwa bedroom ɗinsa, saboda ta
samawa kanta lafiya.

Suna tsaka da zuba soyayyarsu King ya yi wa Jawad massages a kan ya zo main parlour
ya samesa yanzun nan. Dan dole ba dan ya so ba ya fita zuwa parlourn a tare da
Chuchu ɗin.

A wani ɓangare kuwa Pretty and Mahreen da mama Haulat ne suke zaune suna hira, mama
Haulat na koya masu abubuwa dan kara wayar masu da kai. Daga gefen su mama kuwa,
mama tana can kishi kamar zai kasheta, ita kuma mummyn Chuchu tana fama da takaicin
abin da yake faruwa tsakanin Auta da commander Zafar, ita a ganinta ai ba laifi
bane dan Hoorain ya so Auta, saboda Auta fa tana da kyan da dik wani namiji ya
ganta sai ya kyasa, kuma kada ku manta mummy ƴar talakawa ce, so bata ga dalilin da
zai sa a wulaƙanta talaka kaman ita kuma ta goyi baya ba.

Waɗan nan sune kaɗan daga cikin abin da yake faruwa a cikin kingdom of power ta
kowani ɓangare kenan. Mu koma kan labari in da muka dosa kenan.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Cigaba kuka Auta ta yi tana kara faɗa mashi zasu yi nasara, ya jure saura kaɗan ne,
dama dik abin da bawa yake so sai Allah ya jarrabcesa a kansa, to suma su ɗauki
wannan a matsayin jarrabawarsu. Suna tsaka da karfafawa junansu gwiwa unexpect suka
ga haske ya gauraye cikin ɗakin. Kafin ta yunkura domin ganin wanene sai ji ta yi
an damki hannunta. Da karfi aka figeta, ta kofa aka fita da ita.

Dikkansu biyu idan hankalinsu ya kai miliyan to ya tashi, bana kaman Hoorain da ya
shiga tashin hankali kamar zuciyarsa zata buga, damuwarsa ɗaya shi ne za'a hukunta
mashi ita, hakan yasa shi a damuwa.

Ita ma bata kanta take yi ba, hankalinta a kansa, ta kara ja mashi wani musifar,
sai ta ji ta yi danasanin zuwanta wajensa, yanzu za'a kara mashi azaba kan azaba.

Ba kowa bane ya ja hannunta face King, idan baku manta ba na faɗa maku yasa
idanu a kanta, dik wani motsinta yana sane da shi, so tin da suka fita ita da
guyson suke a kan idanunsa, ya gansu sarai, yanzu haka ya kama guyson ɗin ma yana
main parlour, shiyasa ya yi wa su Jawad dikka massages a kan su same shi a
parlourn, dan zai ɗauki tsastsauran mataki a kan Auta da guyson, bawan Allah guyson
dik ya sha jinin jikinsa.

King bai zame da ita ko'ina ba sai main parlour, sai kuka take yi tana yi
mashi magiya a kan ya yi hakuri ta tuba ba zata kara ba.

Sam bai saurareta ba, yana zuwa ya tsayar da ita a tsakiyar parlourn, da karfi ya
ɗauke fuskarta da mari sai da ta tafi ta kifa ƙasa. Da gudu Chuchu ta yunkura zata
tashi ta nufi Autar. A miliyan Jawad yasa hannu ya riketa, tana ƙoƙarin kwace
hannunta King ya daka masu wani irin tsawa wanda ya sanyata komawa jikin Jawad a
miliyan ta lafe, tin da suke basu taɓa ganin King cikin ɓacin rai irin na yau ba.

Kowa yana cikin parlourn banda su Zee da suke ba ƴaƴan familyn ba, sannan Jaish ma
baya nan, amma tin daga kan su uncle Jahiz da suke cikin kingdom of power har kansu
Omaid dik suna parlourn, su Mammie, uncle Abbas dik kowa ya hallara. Dan ran King
ya ɓaci.

Akka tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ita kanta bata goyan bayan
wannan alaƙa ta Auta and Hoorain.

Sai huci King yake yi, Auta and guyson dik suna zube a ƙasa suna kuka, shi guyson
King bai dakesa ba, taya Auta kuka kawai yake yi, ita kuwa nan take shatin yatsun
king ruɗu ruɗu suka fito a face ɗinta, ta masu ne matiƙa.

Mummyn Chuchu ce ta yi ta mazan buɗe baki, cikin girmamawa ta ce. "Allah ya huci
zuciyarka, dan Allah ka yi hakuri, ka kyale Zunaira haka, kada ka hukuntata a bisa
laifin da ba yin kanta bane".

Aunty MieMie ce ta capki zancen da cewa. "Daddy ni kaina baka taɓa sanya hannu ka
dakeni ba, ba ni ba, na tabbatar gabaɗaya tun daga kai'na har kan Obaid baka taɓa
ɗaura hannunka a jikinmu da sunan duka ba, kuma dik mun san cewa kafi san Auta fiye
da kowa, dan Allah daddy ka dubi irin san da kake yi mata, ka yi mata afuwa ka dubi
irin san da take yi wa Hoorain..........".

Kasa ƙarisa maganar Aunty MieMie ta yi sakamakon wani irin kallo da King ya wurgo
mata, cikin kakkausar murya ya ce. "Wlh na yi rantsuwa da girman Allah, ba zan taɓa
bawa Hoorain Zunaira ba, idan zata mutu ta mutu, ba zan yi kaffara ba, wlh billahi
na yi mata iyaka da shi, babu ita babu shi, idan taki kuma to tabbas zan sa a
kashesa".

Ai Auta tana jin karshen maganar King bata san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye
ba, kisa kuma? Ta maimaita a ranta, ba komai ya ɗaga mata hankali ba face tasan
mahaifinta baya magana biyu, tsab zai aikata abin da ya yi niyya, tabbas zai iya
sawa a kashe Hoorain.

Cigaba da magana cikin bada umarni King ya yi yana mai kara kausasa murya. "Daga
rana irinta yau ko parlourn nan na haramtawa Zunaira fita, zata kasance ne a cikin
ɗakin mahaifiyarta, dakin takalma ban yafe ta yi domin fitowa waje ba, sannan na
taraku a nan ne dan ku shaida na bawa Abdussalam aurenta, (Abdussalam ɗin Abu
Abdussalam kenan) ko taki ko ta so shi ne mijinta, kuma ba zan jira wai sai ta
girma ba, dan girma ya kare tin da har tasan ta je wajen Hoorain, har tasan tana
san Hoorain, cikin ƙanƙanin lokaci za'ayi auren ya wuce da ita Dubai!!!!".

Da alama ran King ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dik cikin parlourn babu wanda bai
tausayawa Auta ba, har momma ta ji tamkar tasa kuka, amma ta daure tana jin zafin
hukuncin King a ranta, amma fa Mammie ta ji daɗin hakan, dan ita burinta ta gansu
cikin kunci a kullum.

Ƙasa ɗaukarta kafafunta suka yi, durkushewa ƙasa ta yi a saman gwiwowinta a
gaban King, tana kuka tamkar ranta zai fita, ta kasa yin magana sai kerma da
jikinta yake yi, lokaci guda jikin nata ya ɗauki zafi raw kamar wuta, alamar
zazzaɓi, kanta na sara mata da karfi karfi, tana san rokon King da ya yi hakuri ya
yi mata afuwa amma ta kasa iya buɗan baki ta yi magana.

Lokacin guda wani irin lallausan kamshi ya daki hancin kowa dake cikin parlourn,
gabaɗayansu sai da suka shaki wannan kamshi suka lumashe idanu. A miliyan Auta ta
kai kallanta a kan kofar shigowa cikin parlourn.
Da karfi ta furta. "Yah Omerish". Ta yi maganar ne ba tare da taga kowa a wajen ba,
da alama kamshin perfume ɗinsa da ta ji ne ta furta sunansa. Lokaci guda gabaɗaya
parlourn suka kai kallansu a kan kofar shigowa ganin taga wajen ta kuma furta sunan
da basu taɓa jinsa ba.

A miliyan Sarina ta miƙe tsaye tana cigaba da kallan kofar shigowa tana shaƙar
wannan daddaɗar kamshi da yake buga mata hanci.

Ruɗewa Auta ta yi ta fara ƙoƙarin nufar kofar fita. Tsawan da King ya daka mata ne
yasa ta dakata cak kallanta a kan kofar shigowa.

A hankali aka turo kofar parlourn, Jaish ne ya

Please Login or Register in order to submit comment