You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girgiza mashi. "Ni ko akwai ladan tin da akwai
yunwa bana so, ni ba zan yi ba". "Ɗago kanki ki kalleni". Ya faɗa yana tattare dark
black curly hairnta da ya zubo ta gaba ya tufe mata fuska, tattare mata ya yi ya
tara a baya, sannan ya riko haɓarta da hannunsa ɗaya yana kallan face ɗinta, dik ta
yi jaga jaga da hawaye!.

"Idan kika yi azumi zuwa dare zan saya maki su chocolate dayawa". Sarkin son zaki,
kowa ya san halinta sha zuma ce......... "Ni dai kawai idan zaka saya mun saboda
Allah haka ka bani to, idan kuma sai na yi azumi ne na hakura ka riƙe kayanka". Ta
faɗa tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka. .......... "To ya isa haka, yanzu mu je mu
ci abinci kafin mu yi batu a kan azumi........." Bai iya ƙarisa maganar ba ya
dakata sakamakon wani irin shock da ya ji na saukar hannunta a saman mararsa, a
fujaje ya waro idanunsa sosai a kanta, turo mashi baki ta yi, ita a tinaninta jiran
amsarta yake yi, bata ɗauki taɓa mashi cibiya da take yi a wani abu ba, sai ta ce.
"Ni fa koma me za'ayi ba zan yi azumin nan ba, dan ba zan zauna da yunwa ba". Tana
magana tana sake turo baki.

Nisawa ya ɗan yi tare da rakwafo da kansa kaɗan a kanta, kamar mai san raɗa mata
magana a kunne, cikin dabara ya haɗe fuskokinsu tare da capke lips ɗinta na ƙasa ya
fara tsotsa. Zaro mashi idanu ta yi wanda sai da tasa ya kara jin tsikar jikinsa
yana tashi, hannu bibbiyu tasa tana ƙoƙarin tureshi ya sakar mata baki, shi kuwa ya
kara riketa da kyau, tirgewa ta fara yi tana mutsu mutsu zata kwace kanta, ina ai
yaki bata dama sai da ya yi kissing ɗinta da kyau, sannan ya saketa tare da jingina
kansa da jikin headboards na bed ɗin. Ita kuwa kuka ta saka tare da barin jikinsa,
hannayenta bibbiyu tasa ta fara goge bakinta wai yasa mata datti kuma yawunsa babu
daɗi dan babu zaƙi ita ga sha zuma, zaki kawai take martabawa.

Bilhakki da gaskiyarta take kuka tana ta dirza ɗan bakinta wai tana goge in da nasa
ya taɓa mata, sai tufar da yawu take yi, waje ta nufa da gudu, sam bai ji fitarta
ba. Kai tsaye ta wuce wajen momma, tana zuwa ta faɗa jikinta tare da sanya mata
kuka mai sauti, har lokacin mom tana wajen suna a tare. Da yake momma tasan hali,
sakalcin Pretty ya wuci tinani, sai ta ce mata. "Ke da waye kuma babyn Yah Omerish?
Yau ba'a kai mashi kara ba sai aka kawo mun?". Momma bata san yau shi ya yi laifi
ba, yau kararsa aka kawo ba na mutane da aka saba kawowa or kai mashi ba.
Ita dai momma ba ruwanta, ta fita daban, dama a ko'ina akwai na kirki dana banza,
ita dai bata nuna kabilanci da kyamar wasu da ba nasu ba, kowa nata ne da hannun
bibbiyu take rungumesa!!.

Cikin kuka ta ce. "Momma Yah Omerish ne ya sa bakinsa a cikin nawa, kuma
yasa mun yawunsa da babu zaki babu daɗi a cikin nawa, ya kuma sha mun nan". Ta kai
karshen maganar tana nuna lips ɗinta da hannu!. Ajiyar zuciya momma ta sauke, dama
tasan za'a yi hakan one day one time, saboda su jaraba gadonta suka yi, ita kuma
Pretty ga ɗan banzan kyau kamar ita ta yi kanta, ai keɓewarsu waje guda abu ne mai
haɗari sosai, shiyasa take ta lallaɓa Smart ɗin ya aureta kawai sai ayi dik wacce
za'ayi, wlh ita Momma ta san cewa Smart yana bala'i kaunar Pretty, dan kuwa ita ce
mace ta farko bayan ita da mom ɗinsa and Auta da taɓa shiga rayuwarsa har ta zauna
kusa da shi, abin gaskiya yakamata ta ɗauki mataki.

Tana can tana tinani sai ji ta yi Pretty ta miƙe zata bar jikinta tana faɗin. "Bari
in je in faɗawa Zunaira abin da Yah Omerish ya yi mun"..... Ita fa Pretty bata ma
san dik gurmin da ake yi a kan Auta ta mutu ba, dan tana waya da ita idan ta je
wajen Smart, so dik bala'in da ake yi a kingdom ɗin ko a slippers ɗinta, hankalinta
a kwance..

A hanzarce momma ta rikota tare da cewa. "Ba sai kin faɗawa kowa ba kin ji my baby?
Kada ki faɗawa ko Zunaira ɗin ce ma, ki bari iya ke da ni zan rama maki abin da ya
yi maki!". Girgiza kai ta yi. "Ni Momma ki bari in faɗawa Zunaira, ai ita ma ta
faɗa mun da Hoorain ɗinta ya sha bakinta"....... Ai momma bata san lokacin da ta
zaro idanu waje ba, bala'in can, yaushe Zunaira ta iya dikka wannan abin? Yaushe
aka yi hakan? Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Gaskiya King ya yi kuskure da ya
hanasu mallakar juna, abin har ya kai haka?.

Tana can tana tinani Pretty zata gudu, kuma fa wajen Smart ɗin zata koma dan
yarinta, shi ne kawai zai kira mata Auta a waya ta kuma faɗa mata ya sha mata baki,
kai kuruci dangin hauka.
"Zo mana my baby, baki san shi Yah Omerish ɗin mijinki bane? Shi zai aureki
ai! Kada ki faɗawa kowa abin da ya yi maki, ki rufe sirrinku". Momma ta faɗa mata
hakan ne dan ta samu ta yi mata wayo kada ta faɗawa kowa, sai dai ina, taki fir, ta
ce babu wannan magana, ita wlh sai ta sanarwa da Zunaira abin da yake faruwa.

Cigaba da lallaɓata momma ta yi, dan ta samu ta yi shiru, tasan idan ta ce zata yi
abu to wlh sai ta yi ne, idan kuma ta ce ba zata yi abu ba ko me zaka yi mata ba fa
zata yi ba, ai abin da kunya ta faɗawa Auta ga babban yayansu ya yi mata kiss, haba
zata zubawar da Smart mutunci................😅

To shi ɗan air me ya kai shi dama, ko da yake ba laifinsa bane, laifin Prettyn ce,
ƴar rainin wayo sai ta rinƙa yi mashi abubuwa, ta godewa Allah ma da abin ya tsaya
a iya kiss, badan yana da dauriya ba yadda suke da gadan abar ai wani canza ake ba
wannan ba, in ba iskanci irin nata ba ina ruwanta da cibiyarsa? Dan ta saba yi wa
Kamran haka, shi Kamran a lokacin da take yi mashi ai kunga bai ma san me feeling
ba, time da ya fara jin feeling ya sanar da mammarsa kuma ai kunga kashe mashi
sha'awar ta yi da magunguna, ko kun manta lokacin? Saboda ma kada ya shiga haɗari
ya yi ciwo tasan babu mata a forest ɗin shiyasa take bashi magungunar kashe
sha'awa, wannan yasa dik abin da Pretty take yi mashi baya jin komai bawan Allah,
amma Smart fa? Ai kunga da banbanci, dole idan ta yi mashi ya yi mata...........😅

Da kyar momma ta shawo kanta ta hanyar yi mata alkawarin cartoon na kayan zaƙi,
sannan ne ita ma ta yi alkawarin ba zata faɗawa kowa ba, ajiyar zuciya momma ta
sauke kafin ta miƙe haɗe da riko hannun Pretty ɗin ta ce da mom tana zuwa bari ta
duba Smart. Da okey mom ta amsa, bata jin larabci bata ji me suka tattauna da
Pretty ba.
Bedroom na Smart momma ta nufa da ita, a parlourn ta ce mata ta zauna bari ta zo,
da okey ta amsa tare da zama saman sofa tana turo baki ita kaɗai kamar wadda aka yi
wa wani abin. Ciki momma ta wuce, yadda Pretty ta bar shi haka momma ta shigo ta
samesa, idanunsa a lumshe, da alama tashi jarabar ta fi ta kowa, har sallama momma
ta yi mashi amma bai jita ba, hankalinsa ya yi nisa sosai.

A saman bedside drawer ta zauna tare da kai hannu ta ɗan shafi lallusan gashin
kansa. Nisawa ya ɗan yi ba tare da ya yi magana ba, sai dai ya waro idanunsa da
suka kaɗa suka yi jajir kamar wuta. "Omerish". Momma ta ambaci sunansa cikin sanyin
murya, bai iya amsa mata ba, sai dai ya ɗan juyo da kallonsa a kanta, sai a lokacin
ya farga da Pretty bata a cikin ɗakin, a hanzarce ya yunkura ya gyara zamansa yana
ɗan wawwaigawa nemanta!.

"Bata nan ta fita". Momma ta bashi amsa, dawo da kallonsa a kan mommar ya yi, da
yake shi ba kunya ne da shi ba, renon masu jajyen kunnuwa sai ya ce. "Momma ta je
ta faɗa maki na yi kissed ɗinta ko?"....... Jinjina mashi kai momma ta yi alamar e,
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To ina take ta zo muci abinci". Ya faɗa yana
kawar da kallonsa daga kanta.

"Tana parlour, amma yanzu dai ba wannan ba, idan kun kammala cin abincin sai ka
ɗauketa ku je ka siya mata cartoon na kayan zakin da na yi alkawari, sannan ina da
magana da kai". Juyowa gareta ya yi. "Kayan zaki kuma a daren nan?". Kai ta jinjina
mashi alamar e kafin ta ɗaura da cewa. "Sai da na yi mata alkawarin kayan zaki
sannan ta yarda ba zata sanar da kowa abin da ka yi mata ba".

Da mamaki ya ja ɗan siririn tsaki haɗe da cewa. "To me a ciki momma dan ta sanar da
na yi kissing ɗinta?"......... Momma bata yi mamakin jin hakan ba, dan tasa daga
ina ya fito, ba ruwansa da wani kunya. Kawar da zance ta yi da cewa. "To ni dai ina
san kuje ka saya mata kayan zaki". Ita dai momma tasan kunya, kuma tasan wannan ba
magana ce da za'a fitar da shi ba, yana matsayin Prince ace Pretty ta fitar da
wannan magana ai sam bai yi ba!
"Momma zakin nan fa cuta ce a gareta, baikamata take sha ba". Yana ɗan ɗaure
fuska ya yi maganar. "For today dai ka saya mata". Shiru ya yi yana tinanin yadda
zai yi ya rabata da zakin nan ya huta. "Omerish ". Ta ambaci sunansa tana kallansa.

Dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Na'am Momma".
Tattara natsuwarta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Omerish kana son Pretty,
meyasa ba zaka yarda ka aureta ba kawai tin da ire-iren waɗan nan abubuwa sun fara
shiga tsakaninku?".......... "Momma saboda na yi kissed ɗinta ba shi ne zai nuna
ina santa ba, kiss daban soyayya daban that's all!".

Shiru momma ta ɗan yi, yana neman goge mata hadda, wato kiss ba wani abin bane, e
lallai ma Smart, wato zai gaji babansa kenan!!.

"Na yarda kiss daban soyayya daban, amma kuma ai kasan haramun ne ka yi mata
hakan ko?". Shiru ya yi bai bada amsa ba, babu kuma alamar zai yarda da zancen
momma ɗin ma.

"Please ka yarda ka aureta ga ji my son? Ina san yarinyar sosai, na tabbata zaka
ji daɗin zama da ita, kuma nasan kana sonta kai ma......." Saurin katseta ya yi da
cewa. "Ni bana sonta momma, ki dai'na faɗa mun haka".... Murmushi irin nasu na
manya ta saki kafin ta ɗan girgiza kai, a ranta ta ce ta yaro kyau take bata ƙargo,
a fili kuma sai ta ce. "Na yarda baka sonta, amma nikuma ai ina sonta ko?".

Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, can kuma sai ya ce. "Momma please ki bari in yi
dinner, am feeling hungry, ta ya za'ayi ki fara cewa in auri wannan ƴar yarinyar da
na kai in haifeta". (Ku ji iskanci, wai ya kai ya haifeta amma a haka ya sha mata
baki.🤔)
"Amma kuma ai dik da ka kai ka haifeta ɗin zaka iya kissing ɗinta ko?"........
Wani irin kallo ya wurga mata haɗe da cewa. "Mommaaaaaaa, zaki fara ko? Shiyasa
jiya naki zuwa wajenki, saboda kada ki cigaba da kawo mun zancenta, ga mom ta
dameni da zancen Heleena, so kuke yi in daina zuwa wajenku ko?.........." "Mom
ɗinka ai bata san ka rabu da ita ne shiyasa take son ka auri Heleena, kaga zaku
kasance a tare, nima bana son ka rabu da ni shiyasa nike son ka da Pretty, please
ka duba mu mana my son". Cikin tausasawa ta faɗa.

"Momma mata mayaudara ne, please ku kyaleni haka, ni bana da sha'awar wata mace
ta shiga rayuwata a yanzu, Please kada ku katsa mun farincikina". Ya kai karshen
maganar yana saukowa kasan bed ɗin. Riko hannunsa ta yi da sauri, hakan yasa ya
dakata a bakin bed ɗin ba tare da ya karisa sauka ba. "My son meyasa yanzu baka son
farincikina sosai ne?".
"Mommaaaaaaa, zaki fara ko?". "Gaskiya na faɗa ai". Kai ya girgiza. "Kenan
kin san ina sanki kuma ina san farincikinki, kawai so kuke ku wahalar dani".......
"Haba my aboy".... "Mommaaaaaaa wai ba zaki manta da wannan suna ba?". Ya faɗa yana
binta da kallon kauna.

"Sai ranar da matarka ta haifa mun jika zan daina ce maka sunan in mayar kansa,
idan kana son na dai'na faɗa to ka yi aure ka haifa mun jika". Ta kai karshen
maganar tana shafa kansa. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik abin da kike so kin san
shi nike yi mommata, kuma farincikina, this time ki ɗan bani lokaci zan yi tinani,
zan yanke hukunci"........... Jinjina kai ta yi tare da cewa. "Okey tom amma ka
yanke hukunci mai kyau, sannan ka rinƙa kulawa a zamantakewar da Pretty, kada ka
zurfafa abubuwa"...... Ya gane nufinta, wato kada ya rinƙa taɓa Pretty har a kai ga
kiss, ya gane in da ta dosa, sai ya miƙe kawai ba tare da ya sake yin magana ba ya
nufi wajen abincin nasa. Miƙewa momma ta yi ta nufi waje tana sanya mashi albarka.

Tana fita ta turo mashi Pretty, babu ko sallama ta afka mashi cikin ɗaki, alamarta
ya gani ta wutsiyar idanunsa, bai ce mata ko uppan ba, a kusa da shi ta zauna tana
kallan abincin. Tana zama ya kai hannu ya capki shoulder ɗinta haɗe da cewa.
"Saboda na yi kissed ɗinki shi ne zaki kai karata wajen momma?". Harara ta dallah
mashi kafin ta ce. "Saboda me zaka saka mun yawunka da babu zaƙi kuma babu daɗi?
Kuma na goge bakinka da ya taɓa nawa tas, na tufar da yawun naka ma".

"Da gaske?". Ya tambaya. Kai ta gyaɗa mashi alamar e tana yamutse fuska. Ɗan ciza
laɓɓansa ya yi, alamar ya ji haushin abin da ta yi wai ta tofar da yawunsa kuma ta
goge bakinta in da nasa ya taɓa. Hannunsa ɗayan yasa ya janyota jikinsa, da karfi
ya matseta tare da kai ɗayan hannunsa ya matse mata ɗan bakinta, lips ɗinsa ya kai
saman tata, sai da ya tsotsa son rana, sannan ya cika mata yawunsa sosai a bakinta,
ya kuma matse hancinta yasa dole sai da ta haɗiye kafin ya saketa tare da ɗaukar
spoon da nufin ya fara cin abincinsa, yawa wani irin sauke ajiyar zuciya, shi kaɗai
yasan me yake cikin zuciyarsa!!.

Kuka ta saka mashi mai sauti yana faɗin Allah ya isanta, ta yi maganar tana kai
hannunta saman lips ɗinta ta hau gogesu dana dirzasu da karfi karfi. Shi kuwa
abincinsa ya cigaba da ci ko a jikinsa, yana ganinta ta wutsiyar ido tana ƙoƙarin
goge bakinta. Sosai ya ji daɗin hakan, koba komai ya haɗiye yawunsa sosai, har zata
ce yawunsa babu daɗi ta tufar, to ai ga shi yanzu ta haɗiye. Miƙewa ta yi da gudu
zata fita daga ɗakin, da sauri ya kai hannu ya rikota tare da mayar da ita ya
zaunar.

"Ina kika fita daga ɗakin nan yau ba sai gobe ba tare da tiger zaku kwana a ɗaki
guda, in kuma kin ce ba haka ba fita ki gani". Ya kai karshen maganar tare da sake
mata hannu. Kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwantawa a saman carpet
ɗin ta juya mashi baya. Banza da ita ya yi ya cigaba da cin abincinsa kamar bai san
tana yi ba!.

A can gefe kuma, uncle Abbas yana sanar da Mammien ya yi wa Sareena miji wato
Smart, haƙiƙa Mammie ta ji daɗin wannan haɗi, dama burinsu kenan, yau zata zuba
ruwa bisa ƙasa ta sha, har ta kira Sareena a waya a kan ta zo ta ji daddaɗar
labari!!.. Shi kuma King yana nan damuwa sai kara ninkuwa a ransa take yi, ya yi
zaton ya rufe sirrin da bawan da zai iya sani, ya aka yi Smart ya sani to?. Shi fa
King a tinaninsa idan ya yi wa Smart aure shikenan zai koyi sanin darajan mutane da
girmamasu, shiyasa ya nema mashi auren Sareena!. Kun san aure yana canza abubuwa
sosai.

A ɗayan ɓangare kuwa uncle Jahiz sai ƙoƙari shiga zuciyar Zee yake yi, while ita
kuma ta rigada ta kamu da soyayyar Dr Raj, shi kaɗai take gani, dik in da uncle
Jahiz zai je suna a tare da baby Ahmad, wato yaron Khadijah, yaro ya yi wayo yanzu,
har rarrafe yake yi, Allah sarki mai keken napep ɗinsu dai ya samu sauki ya koma
Nigeria, sun karɓu numbersa a zuwan idan sun dawo zasu nemesa su gana, uncle Jahiz
ya yi mashi kyautar makudan kuɗaɗe.

While shi ma uncle Abbas yana can yana fama da tinanin Khadijah a cikin
kwakwalwarsa, yarinyar tana burgesa sosai. Ita kuwa Akka tana can tana fama da
tashin hankali, dan King ya sanar da ita batun da ake ciki, dik yadda aka yi ita ma
ta san wasu sirrikan da suke ɓuye.

Mammie kuwa ta sako Mahnoor a gaba yanzu, burinta ta rabata da Jaish wanda banda
wahalar da ita babu abin da yake yi dama, yana sonta, amma sai ja maga rai yake yi,
yasata ta yi ta abubuwan wahala dik saboda iskanci irin nasa. Chuchu na can tana
fama da jinya, dan har yanzu bata warware daga ciwon rashin Auta ba, Aneesa ma
jinya take yi. Mama kuwa tana nan tana raba jaraba na wanna hali nata, ta ki yarda
Smart ɗan King ne har yanzu, ta matsawa Ramish sai ya yi mata bincike, ya dai ce
mata to kawai, dan shi ma yanzu abin da yake kansa kawai ya ishesa.

A gefe guda kuwa, guyson da yake Dubai kullum sai ya kira Jaish video call ya ce ya
haɗa shi da Mahnoor, idan ya haɗasu sai ya roketa ta haɗa shi da Mahreen, sai dai
Mahreen ɗin bata karɓar wayar, sai Mahnoor ta rike mata suna hira, masifa take
zazzaga mashi amma shi daɗi yake ji, Mahnoor tana yi mata faɗa sosai a kan masifar
da take yi mashi, amma taki dai'na wa, ta ce ai ɗan iska ne shi, shi dai kome take
faɗa murmushi kawai yake yi, dan burgesa take yi, kuma burinsa ya cika idan ya
ganta.

Daga gefe guda kuwa Sareena da team ɗinta ne suke ta shirya munafurcin da zasu yi
wa Pretty. Ta ce su zuba mata Acid, Omaid ya ce. "Amma ke Aunty Sareena kanki baya
ja, ai kina zuba mata acid ko zaki mutu cikin minti ɗaya Yah Omerish zai kamamu,
hmmm baki san shi ba ko? Shegen kwarone in faɗa maki, yana ganin idonmu zai san mu
muka aikata!. Ke da zaki kawo shawarar da zaki sanya ya tsaneta ko ta tsanesa! Baki
san soyayya bako? Ai ko kin zuba mata acid idan sonta yake yi da gaske ba zai
dai'na sonta ba, dan soyayya babu ruwanta da kyau or muni".

Obaid ne caɓi zancen da cewa. "Haka ne, acid ba zai sa Yah Omerish ya rabu da ita
ba, kuma wlh in dai acid ne zamu zuba mata to watan cin ubanmu ne ya tsaya, abin da
zai sa ta tsane shi ko ya tsaneta shi zamu kirkira". KAI WATO GASKIYAR SMART, ƳAƳAN
MOMMA BA DAI KAI BA, UHMM SU TWIN'S SHEGUN KWARI NE YARAN NAN, AKWAI BASIRA, A
MAIMAKON SU YI AMFANI DA BASIRAR DAN TAIMAKO, SAI SUNA KARAR DA SHI A MUGUNTA DA
SHIRYA TUGGU, KAI WAƊAN NAN YARA SAI SHIRIN ALLAH.

Shiru Sareena ta yi, sai yanzu ta ɗauki haske da suka faɗa mata, cikin zaƙuwa da
zan jin meyakamata su yi mata ta ce. "To ku bani idea, kai'na dik ya kulle, ban iya
tina komai".

Omaid ne ya ce. "Zamu faɗa maki abin da zamu shirya amma ba yanzu ba, bari mu yi
tinani da shawara". ....... Sosai ta ji daɗi, dan bata taɓa kawo kukanta garesu
basu share mata hawaye ba, shiyasa take sonsu, dan haka cike da murna ta bar ɗakin
ta nufi part ɗinsu. Su kuma suna shiga tsara tsarin yadda zasu yi da Pretty ba tare
da kowa ya ganosu ba!! ME KUKE TINANIN ZASU SHIRYA MATA?.

---------------------------------------------🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Wasu irin shegun kaya Big Bro ya saya masu, kayane da basu taɓa ganin irinsa ba,
kuma iri ɗaya ne ita da shi, komai nasu iri ɗaya tamkar tagwaye, har takalma dik
iri guda, sai dai na Ronnie takalmar akwai ratsin baƙi kaɗan a ta kasa, nata kuma
babu, amma ban komai iri ɗaya ne. Wani irin daɗi da ta ji bata san lokacin da ta
daka tsalle ta haye jikin Ronnie tana dariya ba, shima rungumeta ya yi yana
murmushi, kayan sun yi fitina ba kaɗan ba, gown ɗin nan nata ba'a magana.

Juyi da ita Ronnie ya fara yi a cikin ɗakin suna dariya gwanin birgewa. Lokaci guda
kuma Ronnie ya dakata cak, a hankali ya sauketa ƙasa, saboda ya tina Floris, last
year da ita aka yi shagali, yanzu kuma babu ita, take idanunsa da mood ɗinsa suka
canza, wucewa ya yi ya sauna a gefen bed kusa da kayan. Sweetie sarkin basira ta
gane me matsalarsa, ga kuma alkawarin da ta yi wa Big Bro na ba zata taɓa barinsa
ya shiga damuwa ba.

Da sauri ta matso kusa da shi. "Lovely bro!". Ta kira sunansa da ɗan sauti. Shiru
bai amsa mata ba, tin da take a rayuwarta bata taɓa yin rawa ba sai yau saboda shi,
playing na music mai sauti ta yi a cikin tvnsa, sannan ta riƙo hannunsa a kan ya
tashi su yi rawa. Da farko tirge mata ya yi, amma da ta ja shi da karfi sai ya
miƙe, jikinsa a mace ya fara, amma da suka yi nisa take ya mance da damuwa ya saki
jiki yau suka taka rawa tamkar ba gobe, ashe ita ma ta iya, yi ne kawai bata yi
dama.

Dik abin da suke yi Big Bro yana kallansu, yana zaune yana shan green tea, ba
karamin burgesa suka yi ba, sai ma indan suna tsaka da rawa Ronnie ya ɗagata sama
ya ɗaura a saman wuyarsa, ta buɗe hannayenta kamar fanka ya fara juyi da ita suna
sakin murmushi. Ronnie ya samu Sweetie ba kiba, ƴar caras sai ya yi ta ɗagata kamar
ƴar tsana. Sosai suka sanyaya ran Big Bro yau.

Buga karfe 7 dai'dai da agogo ya yi ne ya dakatar da su da abin da suke yi, lokacin
sallah ya yi kenan, sauketa Ronnie ya yi tare da manna mata sumbata a kumatu,
sannan ya ce. "My only sis much love one in million". Sumbatarsa ita ma ta yi kafin
su haɗu tare su tattare kayan nasu suka je suka shirya shi a wajen da ya dace,
sannan ta shiga toilet. Shi kuma ya haye bed yana jiran ta fito!!.

AFTER SOME MINUTES.

Zaune suke a saman bed yana koya mata yadda ake amfani da waya, dan ya ce zai saya
mata mai kyau, ta mai da hankalinta gabaɗaya a kan abin da yake nuna mata, cikin
sanyin murya ya ce. "Sis ina san kin mun karin bayani a kan tsafi da kuma yadda
yayana yake kwace ƴaƴa maza daga hannun iyayensu ya sanyasu a cikin sojojin yaki a
renesu a matsayin warriors, iyayensu basu da ƴancin morarsu ko kaɗan, dik warriors
ɗin nan namu da kika gani ta haya Big Bro ya tarasu". Ya kai karshen maganar tare
da kashe hasken screen ɗin wayar ya ajiyeta a gefe, dan karatu zasu yi.

"Tsafi wannan dogon karatu ne, zan ɗauko maka tarihinsa daga farko ne yadda aka yi
ya wanzu a duniya, shi kuma raba uwa da ɗaya wannan babban kuskure kuma babban
laifi wanda Allah yana iya yi wa wanda ya yi hakan mummunar hukunci ko ya aiko
mashi da bala'i mai girma". Natsuwa ya yi yana sauraronta, cigaba ta yi da cewa.

"A cikin Al-Qur'ani mai girma ALLAH ya bayyana wahalar da uwa ke sha wajen samun
ɗanta, wanda ke nuna girman soyayya da tausayin uwa ga ɗanta, dik wannan wahala ba
zata taɓa tsanar wannan ɗa ba sai ma kauna da take yi mashi. Cikin suratul luqman
sura ta 31 aya ta 14 Allah ya ce. Mun yi wa mutum wasiyya da mahaifiyarsa.
Mahaifiyarsa ta ɗauke shi a cikin rauninsa da ƙari, kuma ta shayar da shi a cikin
shekara biyu. Mun ce masa ka gode wa ni da iyayenka, zuwa gare ni makomar ku take,
wanna yana muna maka girman uwa!!".

"Kazalika cikin suratul Abasa sura ta 80 aya ta 34 zuwa 36 Allah ya ce. A ranar da
mutum zai guji ɗan'uwansa, mahaifiyarsa da mahaifinsa, matarsa da ƴaƴans. Mafi
girman mutanen da zaka ji zafin rabuwa da su kenan, shi ne yasa ake kwatance da su.
Wannan yana nuna cewa a duniya soyayyar uwa da ɗa tana da matuƙar ƙarfi, har yana
da wahala a raba su. Rabasu ma shi ne karshen zaluncin da bawa zai yi wa mata!!"

"A cikin Bukhari Manzon Allah

Please Login or Register in order to submit comment