You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaɗai, Allah shi ne malikyaumiddin,
mamallakin ranan sakamako kenan"

"Kasan me ake nufi da tashin alkiyama kuwa? Kasan masifarta kuwa? Kasan
balai'n da tashin hankalin dake cikinta kuwa? Na tabbata da bawa yasan balai'n dake
cikinta da ba'a wayi gari da azzalumi ko guda ɗaya ba a duniya, kai koda sau ɗaya a
samu wanda ya mutu ya dawo duniya ya faɗawa mutane musifar dake lahira da duniya ta
tsabtata daga ƙazantar da take a ciki".

"Amma ni Omaish jika ga Abdul Mutallab ina kalubalantarka da ka je ka karanta
suratun Az-Zalzalah (‫ )الزلزلة‬tana daga cikin surorin da ke cikin Al-Qur’ani mai
girma. Tana da ayoyi takwas 8, kuma tana cikin Juzu’i na 30. Wannan sura ta yi
cikakken bayani game da ranar tashin kiyama, in da ƙasa za ta girgiza da fitar da
dik abin da ke cikinta, wato dikkan mutanen da suka mutu aka binnesu kenan. A
wannan rana, kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa, komai ƙanƙantar su. Wannan
sura tana ƙarfafa imani da ranar sakamako, kuma tana ƙarfafa mutane kan su aikata
alheri domin gudun sakamakon munanan ayyuka, dan haka zan so ka karantata tare da
fassararta dan ko ba komai bakar zuciyarka na tabbata sai ta ragu, babu wanda zai
ji labari game da lahira zuciyarsa bata kaɗa ba, ko shaiɗan ubanku a zalinci shi ma
hantar cikinsa kaɗawa take yi a dik time ɗin da aka yi batu kan lahira".

Ta ɗan dakata tana jan numfashi mai fita dakyar sosai kafin ya daure ta ɗaura da
cewa.

" Bayan suratul Zalzalah akwai wasu surori da Hadisai da suka bayyana Tashin
Alkiyama da Masifunta, ina kalubalantarka da ka karanta su dikka. A cikin Al-
Qur’ani da Hadisai masu yawa, an yi bayani mai zurfi game da tashin Alkiyama,
tsayuwarta, masifunta, da yadda za a yi hisabi kafin Allah ya raba hukunci. Daga
ciki akwai suratul Az-Zalzalah wadda take magana a kan yadda ƙasa za ta girgiza
kuma ta fitar da abin da ke cikinta. Sai suratul Waqi’ah surata 56 ta yi bayani
yadda mutane za a rarrabe su zuwa rukuni uku a kiyama. Na dama sune Ahlul Janna
wato ƴan aljanma, sai na hagu Ahlun Naar, ƴan wuta kenan, da waɗanda suka yi wa
Allah hidima sosai As-Sabiqun. Sai suratul Takwir sura ta 81, ta yi bayani kan
yadda rana za ta narke, taurari su faɗi, da kuma yadda dabbobi za su taru. Sai
suratul Infitar, surata 82, ta yi bayani kan yadda sama za ta tsage, ƙasa ta zube,
kaburbura su bude, kuma mutane su san sakamakon ayyukansu. Sai suratul Inshiqaq
surata 84, ta yi bayani yadda sama za ta tsage kuma mutane su hadu don hisabi".

"Hadisai Masu Bayani Kan tsanani da tsaruwar Alkiyama, masifu da bala’o’in tashin
Alkiyama akwai bukhari, hadisi mai lamba 4635, sai Muslim lamba ta 157, Annabi
Muhammad (SAW) ya ce. Kiyama ba za ta zo ba sai rana ta fito daga yamma. A cikin
Muslim again, a ranar Alkiyama, mutane za su tsaya tsawon shekaru 50,000 kafin a
fara hisabi, shekaru dubu hamsin da, ba kuma irin shekarun duniya ba, wuce nan,
sannan za'a sauko masu da rana dab kansu, wanda ya yi aikin alkhairi ya bi Allah da
manzonsa zai kasance ne a ƙarƙashin inuwar alarshin Ubangiji. (Allah kasa muna daga
cikin masu samun wanna ni'imar) Za a yi tambaya kan imanin mutum, ibadarsa,
arzikinsa da yadda ya kashe shi, da iliminsa da yadda ya amfani da shi, idan aka yi
maka wannan tambaya me zaka ce?"

Ta jefa mashi tambaya tana kallan yadda face ɗinsa yake kara rikiɗewa. Babu alamar
zai iya buɗar baki ya yi mata magana, dan haka sai ta cigaba da cewa.

"Bayan dikka wannan fa akwai hayewa gadar airaɗi, kafin nan akwai musifun kabari,
kasan me siraɗi kuwa?. Annabi (SAW) ya bayyana cewa akwai wata gada mai tsananin
siranta da ke kan wutar jahannama, wato gadar Siradi.
Wasu za su haye gadar cikin sauri kamar walƙiya, masu aiki na kwarai kenan,
wasu kamar iska zasu wuce saboda tsabar kyan aikinsu, wasu kamar doki, wasu kamar
tafiya a kafa, wasu kuwa za su fadi cikin wuta saboda zalincisu. Ga shi gadar tana
da kaifi fiye da takobi kuma tana da duhu mai tsanani, kai da kake aikata zalinci
me kake tinanin zai faru da kai idan baka tuba ba?". Ta kai karshen maganar tana
ciza laɓɓanta da karfi saboda azaban zafin wutar ya kai mata makura.

Allah yasa kun samu karin imani a kan tunatar daku lahira da na yi.💘 Wlh a dik time
da na tina lahira sai na ji gabaɗaya duniya ta isheni ta fita a rai'na, sai in ji
gabaɗaya na rasa me yake mun daɗi, ranar haka nike wuni sukuku, my people's akwai
aiki a gabanmu babba, wlh kiyama ba karya bace, tashin hankalin dake cikinta bawa
ba zai iya ɗauka ba, dan haka ku kullu ɗamara domin neman gobe mai kyau, duniya
dikka kyalkyali banza ce, ruɗin shaiɗan ne ma yake ƙawata maku duniyar, dan haka ku
yi wa kanku kiyamul laili tin kafin dare ya yi maku! Allah kasa mu dace ka yi mana
kyakkyawar karshe.

Ƙasa cigaba da yin magana Sweetie ta yi saboda azabar da ya isheta, ta gagara yin
magana kuma.

Ga dikkan alamu maganganun Sweetie sun yi tasiri a ransa, saboda kuwa ya tsaya cak
ya gagara motsawa, wannan ma a tunaninsa Sweetie tana magana ne a kan Annabi Isa,
kun san shi suka ɗauka a matsayin Allansu, so ya zaci tana faɗa mashi Annabi Isa
zai tuhumesa a kan zalincin da yake aikatawa ne, dan haka sai ya ji kalamanta sun
taɓa zuciyarsa sosai, dama ai komai taurin zuciya sai dai in bata ji batu a kan
Allah ba, dole ta yi laushi sai dai idan mamallakin wanna zuciya ya ki yarda ya
saduda ne kawai.

Ita kuwa Sweetie a hankali ta fara ganin dishi dishi, kafin wani lokaci numfashinta
ya ɗauke cak saboda wutar ta yi mata yawa. A daidai lokacin da numfashinta ya ɗauke
a dai'dai wannan lokacin barci ya ɗauke Ronnie kwance a gadan Black Tiger. Bawan
Allah aman da ya yi ta shararawa ta jijjiga shi matuƙa, jikinsa dik ya mutu shi ya
haifar mashi da barci.

Allah kasa kalaman nan nata su kara tasiri a zuciyar Black Tiger ko dan ta yi
nasara, Sweetie ta sha wuyar rayuwa wlh, tun daga forest fa, ga kuma makanta, kai
ta wahala fa, ina maganar Allah ba wasa ba wlh, dole zuciya ta girgiza wai dan ma
bai da sani a kan hakan, ma'ana bai karanta ya gani muraran ba, ai da yau bashi ba
kwanciyar hankali bare barci. Ina matuƙar kaunar part ɗin BLACK WORLD, saboda
addinina, Allah ka kashemu muna masu imani da kai.💘

🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

In short, sati guda cur Zunaira ta yi a hospital a kwance kafin ta farfaɗo, a cikin
sati ɗayan nan abubuwa sun faru wanda suka haɗa da kwanciyar commander Zafar a
gadan asibiti, yanke jiki ya yi ya faɗi tin ranar da King ya umarcesa da ya hukunta
Hoorain, suna isa bakin kofar ɗakin duhu bayan ya tura Hoorain ciki ya rufe kofar
kawai sai ya yanke jiki ya faɗi, ranga ranga aka ɗaukesa zuwa hospital, yanzu haka
satinsa ɗaya a hospital amma bai farfaɗo ba, doguwar suma ya faɗa, bawan Allah.

Sannan ciwon guyson yaki sassautawa har sai da Dr Raj ya bar Leesharh ya tsallako
ya taho kingdom of power da kansa domin shi ya saba da yi mashi dik abin da ya
dace. Kwana uku da kwanciyar guyson ya yi dirar mikiya a kingdom of power ɗin, a
ranar da ya zo a ranar ya shawo kan matsalar, amma har yau bai koma ba yana nan,
Bilal ya ɗauko wasu Drs suna kula da Leesharh a Dubai

Tin ranar da Auta ta dawo Mahnoor bata sake haɗa ido da Jaish ba, dan baya zama
kwana biyun nan, tin asuba yake fita, baya dawowa wani lokaci sai karfe 12 ko 1 na
dare, shi ma aikinsa ta sako shi a gaba.

A ɓangaren King kuwa, babu gudu babu ja da baya a kan hukuncin da ya yanke a kan
Hoorain da Zunaira, dik da commander yana asibiti hakan bai hana shi jefa Hoorain a
ɗakin duhu ba, saboda kun dai san yadda zuciyarsu take, ina da tabbacin a cikin
kaso ɗari da wuya a samu kaso ɗaya na sarakuna da zasu iya bawa mayaƙa ko bayinsu
auren ƴaƴansu, abu ne wanda baya yiwu sai wani nufi na Allah.

Lets cut the story saboda labarin dake gaba mai muhimmanci ya fi na baya yawa, dan
wlh ainahin rikicin bai fara ba, so nike in haɗa kan familys ɗin waje guda, idan
baku manta ba na faɗa maku family's daban daban ne ko? To so nike in haɗa family's
waje guda, sannan kowanne ya komawa ahalinsa, a nan ne za'a fara ainahin
cakwakiyar, masu yawan damuna a kan ban juyo story a kan Kamran ba, to Kamran yana
nan, shi ma shugaban wani ahali ne na daban, bayyanarsa kuwa zai zo da ruɗani da
cakwakiya, dan kusan shi ne key na buɗe bakin zaren dikkan waɗan nan cakwakiyoyin,
soon zai dawo cikin labari da bazata na ban mamaki. (Amma bari matarsa Pretty ta
kara girma😅 dan yana dawowa sai aure😅 kada ku manta mom twin's ta bashi aurenta
fa, matarsa ce, saura mammarsa ta yarda kawai mu sha biki ko ba sadaki🥱 ƴan special
grp zaku biya mashi sadakin ko?)

To masu matsawa a kan Pretty and Sweetie ƴaƴan King Zuhair ne na ce sannunku,
wato kuna nufin King ya auri mom twin's kenan ko? Amma fa kun iya hasashe, to muje
dai zuwa, yanzu zamu buɗe babin surprise, get ready, bari in fara tashin kanku a
cikin pages na kwanaki nan, an sha gwagwarmaya a pages ɗin baya, na week ɗin nan
kuma bari mu sha surprises, gaba sai ayi cakwakiyoyi, let's go.

So lets cut the story kaɗan a nan. Tin da Zunaira ta dawo gida take yi wa momma
kuka a kan ta taimaka tasa baki daddynsu ya kyale Hoorain, ita ta yarda a rabata da
shi amma dan Allah a barmata shi ya shaki iskar ƴanci, a yafe mashi hukuncin da ya
hau kansa.

Momma ta tsausayawa Auta matuka, amma babu yadda zata yi, domin a kan batun Hoorain
King zai iya saɓawa kowa, momma ta same shi da maganar daren jiya, warning sosai ya
daka mata tare da rantsuwa da girman Allah ba zai taɓa bawa Hoorain auren Zunaira
ba, kuma idan suka matsa mashi tabbas ran Hoorain suke yi wa, saboda a kan wannan
magana zai iya sanyawa a kashe Hoorain mai gabaɗaya kowa ya huta. Tashin hankali.

Dik wasu masu karfin gwiwar tinkarar King su yi magana da shi sun kasa iya shawo
kansa a kan wannan magana, kai in takaice maku Queen mother da kanta sai da ta
sararawa King a kan wannan batu, domin ya ɗauki zafi fiye da tinaninku, Akka dan
dolenta ta kyalesa, uncle Jahiz ya yi iya yinsa a kan King ya duba ya yafewa
Hoorain, sai dai ina, ya ce wlh ba zai yiwu ba, daga karshe ma da aka ce mashi Auta
taki cin abinci zata iya cutuwa.

Murje idanunsa ya yi ya ce ta mutu idan taga dama, amma babu ita babu auren mayaki,
da ya bata shi gara ta mutu ɗin. Tashi sense, jin wannan furuci na King yasa suka
fahimci ba fa zai saussatawa Hoorain ba tun da dik yadda yake san Auta ya ce ta
mutu ai shikenan kuma sai dai a bishi da ido. Daga haka suka sallama babu Auta babu
Hoorain.

Dik wannan bidiri da ake yi wlh Jaish yana jinsu bai saka baki ba, dan bai ga abin
faɗe ba. Dik duniya an rasa mai shawo kan King a wannan gaɓa, yaki bawa momma damar
ta zauna da shi ma, dan yasan zata iya kuresa, da ta zo ɗakinsa zai fice izuwa part
na Akka, saboda baya san sassautawa kowa a kan wannan al'amari.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

AUTA😥

Kwance take a saman bed ɗin momma, yanzu King ya saka mata tsaro da idanu sosai wai
dik dan kada ta je wajen Hoorain, bata fita ko nan da can, tana cikin ɗaki, ita ma
ba dan bata da lafiya ba King ya yi niyar hukuntata saboda kawai dan ta so Hoorain
ta yi laifi, rashin lafiyarta ya ja ya kyaleta.

Guyson yana zaune kusa da ita yana cigaba da dannar zuciyarta yana bata hakuri, su
Mahnoor suna tare da momma a parlour suna hira, momma dai tana ganin musifa kala
kala a cikin gidan nan, sai dai ta dogara ga Allah shiyasa har yanzu bata faɗi ƙasa
ba.

Wayar momma dake kusa da ita ne ya fara kara alamar shigowar kira. Ɗauko wayar ta
yi, lokaci guda ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, a fili ta furta Hasbunallahu
wani'imal wakil, sannan ta yi picking call ɗin.

Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Hello momma". Gabanta ne ya sake bada dum dum, da
kyar ta iya amsawa. Kai tsaye ta cikin wayar aka ce mata. "Ina Zunaira?". Mai
maganar kamar muryar Abu Abdussalam haka.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Zunaira tana barci......." Bata gama faɗar hakan na
diff aka katse kiran. Miƙewa tsaye ta yi, cikin hanzari ta nufi part ɗin King tana
faɗawasu Mahnoor kowacce ta wuce ɗakin mijinta dare ya yi.

Miƙewa suka yi gabaɗayansu, Mahnoor ta wuce part ɗin Jaish, a sati ɗaya da Mahnoor
ta yi da Chuchu har ta koyi wasu abubuwa, Chuchu tana koya mata kula da miji,
Mahreen ma sai kara wayewa take yi a wajen mama Haulat, Pretty tana tare da Mahreen
a wajen mama Haulat, yanzu hankalin kowa a tarshe yake a kingdom of power.

Mahnoor ta nufi part ɗin Jaish, Mahreen and Pretty suka nufi wajen mama Haulat,
dama ita Chuchu tana kirjin Yah Jawad a yanzu, Zee ma miƙewa ta yi ta koma bedroom
na Aneesa, yau Khadijah ta dawo cikin family part, an sallamota daga asibiti, shi
kuma mai napep ɗinsu da yake ya samu karaya har yanzu bai samu sauki ba.

Sai kuka Auta take yi guyson yana ta rarrashinta, shi ma dai ba wani ƙoshin
lafiya sosai ke garesa ba, amma ya daure yana ta lallaɓata.

Zuciyarta kamar zai fashe ta ɗago kanta, fuskar da ya yi jaga jaga da hawaye,
muryarta a dashe ta ce. "Yah Omar ka faɗa mun me Hoorain ya yi da ya cancanci
wannan hukunci daga wajen daddy? Bafa shi ya ce yana sona ba, ni na fara cewa ina
sonsa, kenan laifine in so wanda zuciyata take so?". Ta kai karshen maganar tana
mai da kanta ta kifa a saman pillow.

"Ba laifi bane, amm kuma ki sani abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba
zai hangosa ba, tabbas daddy ya ɗan kauce a wani gaɓar, amma ki sani saboda sanki
yasa ya yi hakan dikka". Cewar guyson.

"No Yah Omar, ba so bane, idan so ne ku so abin da nike so, zuciyata zafi take mun
Yah Omar, ni kam ina ganin mutuwa kawai zan yi".

Da sauri ya katseta da cewa. "Kada ki sake cewa ba sanki muke yi ba, kin san yadda
kike a zuciyar kowa dake gidan nan kuwa?". Miƙewa zaune ta yi tana goge kwallah.
"Yah Omar idan har kana sona kuma kana supporting ɗina to ka tabbatarmun da hakan
yanzu ta hanyar kaini wajen Hoorain!".

Tashin hankali, zado idanu guyson har kamar idanunsa zasu faɗi ƙasa. "Kin san me
kike faɗe kuwa?".
Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas tasan abin da take faɗe....... "No
Zunaira, no, i can't do that, kin san hukuncin da zamu fuskanta a kan hakan kuwa?
Kin san daddy zai iya tsaremu a prison ko baki sani ba? Kin manta cewa dik wanda ya
taka dokar daddy hukunci na hawa kansa ko da ɗansa ne ko?". Ya jefa mata tambayar
cikin ruɗu da tashin hankali.

A hankali ta koma ya kwanta, wani irin kuka ne ya ci karfinta, tana wani irin
shessheka ta fara magana ƙasa ƙasa. "Ni dama nasan kai ma kana cewa kana supporting
ɗina ne kawai dan ka kwantar mun da hankali amma ba wai dan kana san zaɓina ba".
Tana kuka tana faɗa.
Allah sarki guyson, idanunsa sun ciko da kwallah sosai, kamar zasu zubo, murya
ya karaye ya ce. "Zunaira ki dai'na faɗin hakan, wlh da gaske ina san zaɓinki, ina
sansa sosai, dik abin da kike so ina sonsa, amma ki fahimceni, babu ta yadda za'ayi
na kaiki wajen Hoorain, idan daddy ya sani kinsan ransa zai yi mummunar ɓaci, kuma
zai hukunta mu".

Miƙewa zaune ta yi, so take yi ta yi mashi wayo ya kaita taga jaruminta, kasan bed
ɗin ta sauko a in da ta nufi jikin bangon kusa da toilet, binta da kallo ya yi yana
mamkin in zata je. Kafin ya farga sai yaga ta fara buga kanta da jikin bango tana
sambatu a kan kowa baya san zaɓinta gara kawai ta kashe kanta kowa ya huta. Dim fa
salan yaudarar guyson take san yi, tasan halinsa da raunin zuciya, zai iya aikata
komai idan yaga zata cutu, shiyasa ta yi mashi dabara haka.

Da gudu ya diro kasan bed ɗin, kai tsaye ya nufeta, cikin zafa ya damko hannunta ya
janyota ta faɗa jikinsa, hat gaban goshinta ya fashe ya fara jini, hawaye guyson ya
fara yi, cikin kuka ya ce mata. "Ba zaki kashe kanki ba, tabbas zan kaiki ɗakin
duhu wajensa koda daddy zai hukuntani, ɗauko alkyabbarki ki zo mu tafi". Ya faɗa
tare da saketa yana kai hannu ya fara goge hawayensa.

Bata bi ta kan kukan da yake yi ba, da sauri ta ce. "Yah Omar ba sai na saka
alkyabba ba, kawai mu tafi". Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "No ki sitirta
jikinki, kinga dai kayan barci ne a jikinki, maza ɗauko alkyabbarki bari in duba
akwai mutane a parlour ne". Ya kai karshen maganar tare da nufar parlourn yana
cigaba da goge hawayensa.

Dressing room na momma ta nufa da gudun gaske. Alkyabba ta ɗauko ta fito, tana
fitowa shi ma yana shigowa cikin room ɗin, ya duba parlour babu kowa. Murya ƙasa
ƙasa ya ce. "Zo mu tafi babu kowa a parlour".

Ai tin kan ya faɗi haka ta yi saurin wucewa. Hannunta ya riko suka fito, ina wannan
hanyar sirrin nasu da Hoorain ya taɓa kawota wajen a lokacin da mayakan Queen
Zarina suka kawowa kingdom ɗin hari? Kun tuna lokacin da ya ɗaukota daga gonar King
ya kawota wajen su momma a wajen?.

To ta wannan hanya suka bi, underground kenan, ko da suka shiga wajen sun rufo
kofar kamar ba'a taɓa buɗewa ba, da sauri ya kunna hasken wutar wayarsa, saboda
babu haske a wajen. Hannunta ya ja da sauri suka bi ta wajen, sai shera hawaye take
yi, shi kuma sai rarrashinta yake ta kara yi. Sun yi tafiya mai nisa kafin su tsaya
a wani waje mai ɗan faɗi idan da hanyar suka rabu kashi uku, tsayawa ya yi yana
tinanin wani hanya ce wadda zata sada shi da prison na kingdom ɗin nan? Dan a cikin
prison ɗin ɗakin duhu yake.

Ya ɗauki a kallah 5 mins yana tinani kafin ya jata suka sake miƙewa kai tsaye suka
nufi wajen. Kunsan masarauta idan ta kai masarauta akwai ire iren waɗan nan hanyoyi
na sirri ta ƙarƙashin ƙasa waɗan da zasu sadaka da kowani ɓangare na cikin Kingdom
ɗin ya kasa, dik salan dabarun yaki ne.

Guyson kamar bai san komai ba, amma sai ga shi yasan hanyar sirri, kai tsaye ya
kaita har in da ɗakin yake, sannan ya tsaya da kyau wajen tinanin a dai'dai ina
kofar take? Amfani ya yi da ƙwaƙwalwarsa da Allah ya bashi wajen gano kofar,.
Duƙawa ƙasa ya yi Auta ta haye saman shoulder ɗinsa, karfinsa yasa wajen miƙewa da
ita tsaye, dan shi tsawonsa ba zai kai ya iya buɗe kofar ba, sai ya ɗagata dan ta
buɗe.

Hannunta tasa wajen tura kofar, ba koface kamar kowacce kofa ba, tiles ce ta
yadda ba za'a taɓa gane akwai kofa a wajen ba sai wanda yasan da wajen, so dikka
kofofin hanyar underground ɗin nan tiles ne ta ciki.
Tura tikes ɗin ta yi ta buɗe ta ciki kenan, tiles ɗin ya buɗe ta in da Hoorain yake
kenan.

Ganin ya buɗe yasa guyson ya ce. "Ki haura ki je ki gansa, kada ki wuce 5 mins dan
kada a nememu, sannan ki kula akwai masu gadinsa daga ta waje, kada ki bari su
ganki".

Okey kawai ta amsa da shi kafin ta yi gaggawar haurawa ta fito ta cikin ɗakin,
Allah sarki guyson, saboda yana san farincikinta saman shoulders ɗinsa ta taka da
kafafunta ta haura sama, amma ko kaɗan bai damu ba, shi dai taga Hoorain ta yi
farinciki ya wadatar.

Tana hayewa ta ce ya mashi. "Yah Omar ɗakin akwai duhu sosai, ka miƙo mun
wayarka zan haska in gansa".

Kai ya girgiza mata kafin ya ce. "A'a ki je haka kawai, idan kika saka haske a
ɗakin masu gadinsa dake waje zasu san an shigo ciki, da waje haka ki laluɓi in da
yake kawai a cikin duhun".
Juyawa ta yi ta kalli cikin ɗakin, wani irin bakin duhu ta gani mai
razanarwa, a hankali ta sake jiyowa ta kalli guyson dake kallanta.

"Ki je babu abin da zai faru In Sha Allah, ki kula sosai". Shiru ta tsaya tana jin
tsoron shiga cikin ɗakin, saboda duhun. Kara mata kwarin gwiwa sosai guyson ya yi
har sai da ta yarda ta miƙe tsaye, a hanzarce ta mayar da tiles ɗin ya rufe, ta
fara laluɓen Hoorain a cikin duhu tana ambatar sunansa ƙasa ƙasa.

Ɗakin tsit baka jin motsin kowa, tamkar babu halitta mai rai dake a ciki. Sai yawo
take yi a cikin duhu amma sam bata ga alamar zata ga halitta a ciki ba, har ta fara
karaya ta fara jin kamar zata hakura. Can wani tinani ya zo mata a kan ta yi shiru
tsit in dai yana cikin ɗakin tabbas zata ji sautin numfashinsa ko kuma bugawar
zuciyarsa. Haka kuwa aka yi, ta tsaya shiru tare da kasa kunnuwanta dan saurara.

A hankali sautin numfashinsa haɗe da bugawar zuciyarsa dake fita da karfi
karfi ya fara ratsa dodan kunnenta. Natsuwa ta kara yi domin sauraron ta ina sautin
yake fitowa. Fahimtar daga ina ya fitowa yasa ta fara takawa ta nufi wajen a
hankali hankali tana sanɗa.

Unexpectly ta ji ta daka tuntuɓe a in da ta buga kanta da kirjinsa, ko bata ga
face ɗinsa ba tasan kirjinsa ne daka, da sauri tasa hannunta ta fara laluɓar
jikinsa dan ta ji a wani hali yake ciki. Allah sarki, ɗaure yake cikin sarkoki masu
girma da kauri, a tsaye yake a kan kafafunsa, a horon dama babu kwanciya, idan wata
guda aka yankewa mutum haka zai kasance a tsaye tsawon wannan wata gidan, abinci ma
masu gadi zasu bashi a baki, bashi ba motsawa, shiyasa dik wanda ya shiga ɗakin
dubu dik ranar da aka fitar da shi kafafunsa basa iya takawa. Dan ko dare ne a
tsaye zaka yi barci, kafafu da hannaye dik a ɗaure suke da sarƙa, kuma an ware maka
su ba ta yadda zaka yi ka zauna, abin dai gwanin ban tausayi.

Sosai hankalin Zunaira ya tashi, bugawar da kirjinta yake yi ne ya kara tsananta,
kuka ta fashe da shi tare da fara jijjiga Lion chest ɗinsa tana ambatar sunansa a
hankali.

Shiru bai amsa mata ba, babu alamar zai amsa mata ba, kuma yana numfashi bare ace
ya suma, yana jiyota, magana ne ya ƙasa yi mata tamkar an ɗaure tongue ɗinsa, Allah
sarki azaba ce ta yi mashi yawa, a yadda yake ɗauren nan jini ne yake zuba daga
damatsan hannunsa da ya sha horo wajen warriors da King ya wakilta dan hora shi,
sun dakesa da bulalar kaca mai kifiyoyi a jiki, sannan suka zanya mashi gishiri a
dik in da fatarsa ta fashe dan tsananta mashi horo, ya kara jin azaba kenan.

Da yake a cikin duhu ne ɗin Zunaira bata ga wannan ba, ita dai kuma kawai take yi
tana jijjiga ɓulɓul ɗin breast ɗinsa. Ganin ba zai amsa mata ba yasa ta laluɓi
saman face ɗinsa ta ɗaura hannunta a kumatunsa, a hankali ta ɗaga kafafunta ta kara
tsawo, a saman kirjinsa ta kwantar da kanta tare da laluɓar ɗan bakinsa da hannunta
dan ta yi shin an rufe mashi baki ne.

Yatsanta ta tura cikin bakinsa tana cigaba da ambatar sunansa, gabaɗaya kayan
jikinta sun ɓaci da jininsa ba tare da ta sani ba.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, can ƙasan maƙoshinsa, da kyar ya iya furta. "My
Hoonaira".

Jin alamar kamar ya yi magana yasa ta yi saurin ɗago kanta daga kirjinsa tare da
kara ɗaga kafafunta ta haɗe fuskokinsu, hankalinta a tsananin tashe ta ce. "My Hero
ka yi magana ne? Ka yi mun magana ne? Please kana jina? Meyasa ka yi mun shiru?".
Out of control take

Please Login or Register in order to submit comment