You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta koma cikin
ɗakinta.

Juyawa ta yi da nufin ta koma ɗakinta, sai kuma ta tuna Leesharh tana cikin azaba,
nan take ta ji zuciyarta ya karfafa, tausayin ƴar uwarta ya ratsata, da sauri ta bi
bayansa tana karanta dik addu'ar da ya zo bakinta.

Tana sako kafarta cikin room ɗin nasa shi kuma yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa
zai shiga wanka, ya bawa kofar shigowa baya.

Sai da ta ji gabanta ya faɗi time da taga faffaɗar bayansa kamar madara. A bakin
kofa ta tsaya kamar wadda take jira ace pet ta yanka a guje ta fita, like tana
tsoron cikin ɗakin dai.

Sarai ya ji motsinta, sai dai bai juyo ba, ya cigaba da abin da yake yi, tsabar
tabbatar bashi da kunya wandon jikinsa yake ƙoƙari zamewa, dan shi babu ruwansa da
tana tsaye, meyaka kawota ɗakinsa? Ko ɗakinta ne?.

Kamar ta dalla ihu take ji, shi ko kamar wanda bai san da halittarta a wajen ba.

Ai bata san time da ta juya a miliyan zata fita ba ganin ya zame wandan jikinsa,
tana juyowa kuma suka ci karo da Bilal da yake ƙoƙarin shigowa yanzu. Da karfi
sosai ta juya, hakan yasa ta bugesa da karfi, wani irin baya baya ta yi zata faɗi.
Cikin sauri ya damko wuyar rigarta dan taimaka mata kada ta faɗi.

Ai bata san time ɗin da ta kurma ihu ba, wayoyin dake hannunta dikka biyu suka faɗi
ƙasa, ba komai ya saka ta ihu ba face yadda Bilal ya riko wuyar rigarta kusan
hannunsa dikka a saman tudun tula tulanta, shiyasata ihu ba shiri.

Janyota Bilal ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya saketa tare da ɗaure fuska
sosai, a takaice ya ce. "Meyakawoki nan?".

Kasa tsayuwa a kan kafafunta ta yi, cikin sauri ta durkushe kasa tare da fara ruwan
zafafan hawaye, hannu tasa ta fara laluɓar wayoyin da suka faɗi ƙasa, tsikar
jikinta dik sai wani mimmikewa tsaye yake yi.

A karo na biyu Bilal ya sake tambayart me ya kawota nan.............. Sai a
lokacin ta ɗago da kanta a kansa, cikin sarkewar murya haɗe da tashin hankali a
tattare da ita ta ce.

"Yah Bilal dama nazo ne in faɗa maku wancan waya wlh bana Leesharh bace, ashe irin
namu ne da kasaya mana, wlh tana da gaskiya ba nata bane, kaga namu wayoyin". Ta yi
maganar tana ɗagowa, tana kai karshen maganar kuma ta miƙa mashi wayoyinsu dake
hannun, sai kerma hannun nata yake yi yaki tsayawa waje guda.

Sai a wannan lokaci Ramish ya juyo, ya ɗaura towel a waist ɗinsa, kallo ɗaya ya yi
masu ya wuce ya nufi toilet............ Karɓar wayoyin Bilal ya yi haɗe da furta
alhamdulillah da ɗan sauti, da alama shi ma ya ji matuƙar daɗi, bai yi magana ba
sai ya nuna mata hanyar fita kawai, a kan ta je.

Cike da tsoro ta ce. "Yah Bilal to Leesharh ɗin fa? Zaku dawo mun da ita?".

Kai kawai ya jinjina mata tare da kara nuna mata hanya. Da gudu ta raɓa gefensa ta
fice tana toshe bakinta saboda wani iri kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro da ya
kubce mata.

Ajiyar zuciya Bilal ya sauke tare da ɗaura kallonsa a kan wayoyi, tabbas wannan ne
wayoyin da ya saya masu, wancan kenan irin nasu ne kawai? To waye mamallakin wancan
wayar? Ya jefa kansa tambayar.

My people's da ni da ku idan baku manta ba mun san ya aka yi wayoyin nan suka fita
iri ɗaya, in baku manta ba a baya na gaya maku masu nikaf sun canza mata ainahin
wayar da suka bata da farko, har na ce maku sun bata wani irin wanda Bilal ya saya
mata ita da Sharifat sak ko? To wannan shi ya kawo ruɗani a cikin al'amurran,
wayoyin iri ɗaya ne, Sharifat guda ɗaya tasan Leesharh da shi shi ne wanda Bilal ya
basu, bata san da na masu nikaf ba! Wannan shi ne, kunga Sharifat zata wanke
Leesharh ba tare da tasan da gaske wancan wayar ma na Leesharh ɗin bace. Wai akwai
case a gaba gaskiya!!.

Dama kuma tun farko Leesharh ta ce da su Bilal ba wayarta bane, kunga kuwa yanzu
da Sharifat ta kawo wannan tsab zasu iya yarda ba nata ɗin bane, akwai cakwakiya fa
sosai, shin masu nikaf zasu ɗauki mataki ko dai shirun banza suka yi? Muje zuwa!.

Karisawa cikin ɗakin Bilal ya yi, saman bed ya haye tare da jawo laptop na Ramish
ya fara latse latsensa.

•••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥

Tsaye take gaban wannan korama dake aman ruwan, yanayin yadda ruwan yake zuba abin
gwanin ban sha'awa, ka korayen ganyayyaki kewaye da wajen, sannan ga ruwa gudu a
kasan koramar yana ta gudu mai haske tar, tsabar haskensa har ya ɗauki kalar
sararin samaniya wato sky blue.

Ta ko'ina kamshin furanni ne yake tashi saboda yawaitansu a wajen, daga gefe can
tsuntsaye nau'ika daban daban ne suke dira a kasa bakin ruwan dake gudun suna shan
ruwa sai su sake tashi, yanayi mai daɗi ga iska na ɗan kaɗawa a hankali hankali
yana kaɗa furannin dake wajen kamshinsu yana kara tashi.

Wajen zai yi matukar dacewa da masoyan dake bala'in kaunar junansu. Ta yi shiru
kamar mai kallan ruwan dake kwaranya daga koramar, amma kuma ba shi take kallah ba,
hakika hankalinta ya luluƙa duniyar tinanin kingdom of power da kuma Hoorain,
wannan abin da ya yi mata ya zame mata babban tabo a rayuwarta da ba zai taɓa
gogewa ba.

Pretty bata a tare da ita, ta tafi ɗauko masu fruits, so ita kaɗai take tsaye a
wajen.

Ta yi nisa cikin tinaninsa da take yi ba zato ba tsammani ta ji an rufe mata idanu
daga ta bayanta. Hakika ta tsorata matuƙa, dan yanzu abu kaɗan yake razanata yake
kuma ɗaga mata hankali.

Ihu ta zunduma tare da fara ƙoƙarin kwatar kanta zata zulle. Saura kaɗan ta afaka
cikin wannan ruwan gudu a ƙoƙarinta na zullewa. Da sauri ya riketa da kyau, kamar
mai raɗa ya ce mata shi ne fa ta nitsuwa kada ta jewa kanta ciwo.

Dik da ta ji muryarsa bata yarda ba, dan yanzu bata jin zata yarda da wani a
rayuwarta, babu wani sauran yarda a zuciyarta, ƙoƙari ta cigaba da yi dan kwatar
kanta.

Da yaga haka sai ya zame hannunsa daga idanun nata, dan taga zahiri, sai dai bai
saki hannunta da rike dan kada ta faɗi ba, sai ya sanya ɗayan hannunsa a saman
Waist ɗinta.

Cak ta tsaya da ƙoƙarin zillewa da take yi, nan take ta ji mummunar faɗuwar gaba,
da sauri ta yi ƙoƙarin jiyowa dan ta tabbatarwa da kanta shi ne ko ba shi bane.

Ganin yadda ta juyo da sauri yasa ya yi saurin saketa tare da ce mata. "Kiyi
hakuri"........... Jinjina mashi kai kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba, sai ta
buƙaci matsawa daga kusa da shi.

Bai bari ta yi hakan na shi sai ya ɗan matsa baya yana kara ce mata ta yi hakuri.
Da okey ta amsa mashi tana mayar da kallonta a wajen koramar.

Wai shin me ya dawo da shi bayan ya ce ya tafi?. E to tinanin Zunaira ya hana shi
tafiya, dan haka sai ya samu waje kasan wani bishiya ya zauna yana ƙoƙarin yankewa
kanshi shawarar ya dawo ya sake ganinta ne ko kuma ya hakura ya tafi sai gobe?.

Yana tsaka da wannan tinani ya hango gungun mayaka sun dinfarko cikin dajin wanda
ko ba'a faɗa mashi ba yasan su Pretty suke nema, tun da ya sha artabo da su a kan
hakan. Wannan dalilin yasa ya hau saman bishiyar da yake karkashin ya ɓuya, sai da
suka wuce sannan ya sauko ya bi bayansu dan yaga ina suka nufa.

Ganin sun bi wani hanya ba ta in da su Pretty suke bane yasa ya ce to bari ya leƙo
su Pretty su ɗan sake ɓata lokaci a tare kafin nan ya wuce, kun ji dalilin
dawowarsa. Har zai wuce wajen nasu sai ya hango Zunaira tsaye a bakin koramar nan
shi ne ya ƙariso gareta, dama tinaninta ne a ransa.

"Ina Omnish?". Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.

Kamar ba zata amsa mashi ba, amma ita ɗin ƴar halak ce, akwai tina alkhari, dan
haka sai ta daure ta ce. "Ta je kawo fruits".

"Amma ba nace kada ku fita waje ba?".

Kasa ta yi da kanta tana tinanin amsar da ya kamata ta bashi, a dai'dai lokacin
Pretty ta dawo hannunta ɗauke da fruits a kwando.

Shiru suka yi daga shi har Auta, cike da mamaki Pretty ta ce. "Kai ne ka dawo?".
Yadda ta yi maganar sai ku zaci bata yi wani laifi ba.

Binta da kallo ya yi yana mamakin halin Omnish ɗin nan nasa, yarinya ce sai ka rasa
a wani mataki zaka ajiyeta.

"Omnish wai ba nace kada ku fito waje ba? Ke kika ja Zunaira kuka fito
ko?"............ Baki ta turo ba tare da ta bashi amsa ba, saboda ita dai magana ta
Allah bata san zaman cikin nan.

Jin ta yi shiru yasa ya sake cewa. "To ku wuce mu tafi". Ya faɗa ba tare da wasa
ba.............. Ran Pretty bai so ba ta wuce gaba tana tura baki, Auta ta rufa
mata baya. Haka suka wuce izuwa ma kwancinsu.

Ko da suka shiga sai da ya jima tsaye a wajen yana satar kallon Auta kamar bakinsa
da magana, kamar yana san amayar da ita kuma, sai dai kamar yana tsoro, wato dik
zafin kan mutum da izzarsa abu guda ɗaya tana ɗarsa mashi tsoro a cikin zuciyarsa,
wannan abin kuma ba komai bane face soyayya, wlh in dai namiji soyayyar gaskiya ce
a ransa yana ɗarsa mashi tsoro da ɗarɗar a kan ua faɗa ko kada ya faɗa, yana jin
matuƙar tsoron ya furta bai yi nasara ba, tinanin abin da zata je ta dawo da abin
da rashin nasararsa zai haifar masa yasa yake dasa mashi tsoro a zuciyarsa.

Haka ya rufesu, ya ɗan jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya tafi. A wannan karon
ma yana tafiya suka buɗe suka fito, wlh ita dai Pretty Allah ya gani ba iya zama a
wannan waje take yi ba, burinta ta fito waje, gara ma lokacin da Auta take jinya a
cikin wajen, a wannan lokaci kullun tana ciki, saboda tana kula da Auta.

Sadauki ne ya tsinto Auta a cikin ruwa ya kawota wajen Pretty, shi kuma ya yi
jinyarta tsawon lokaci, shiyasa kuka ga ta shiga ransa sosai, dan dik wasu
magunguna shi yake saka mata a ciwon, Pretty kullum tana manne da ita, ko nan da
can bata san matsawa, suna tare, kusan a tare ita da sadauki suka yi kinyarta.

A ranar da Auta ta buɗe idanu da Pretty ta fara yin arba, shiyasa take balain jinta
a ranta sosai.

Ga dikkan alamu Auta ma bata san zaman cikin ramin nan, saboda da Pretty ta ce tazo
su je waje zata ce to, ta bita su tafi, ga shi ita bata gama samun lafiya ba, har
yanzu akwai sauran magani a jikinta da ba'a ɓare shi ba.

Kuma ita Auta bata san cewa akwai waɗan da suke farautar rayuwar su Pretty tsawon
lokaci ba, bata taɓa kawo hakan a ranta ba, a dik tinaninta fita ne kawai sadauki
baya san su yi yasa kullun yake yi masu gargaɗi a kan fita, basu san cewa abin ya
wuci haka ba.

Fitowa suka yi, suka jero kusan tsawonsu ɗaya, Pretty ce ta ce. "Zo mu canza waje
tun da nan wajen yasan muna wajen, zo mu je ta can baya akwai wani wajen korama ba
zai san muna wajen ba, sai mu zauna mu yi hiranmu a wajen sai can yamma mu koma.

Da to kawa Auta ta bita suka cigaba da tafiya. Sun yi tafiy mai nisa sosai har Auta
ta fara dafe cikinta wajen ciwon nata, kunsan bata gama samun sauki ba, so sai ya
fara yi mata ciwo.

Tun tana ji a hankali hankali tana daurewa har ya fara fin karfinta, karkashin wani
bishiya ta samu ta zauna tare da dafe wajen tana ƙoƙarin fara kuka. A tsorace
Pretty ta dawo kusa da ta zube gwiwowinta, kamar zata yi kuka ta fara tambayarta
lafiya? Meyake damunta.

Auta bata kai ga buɗe baki ba suka sinkayo sukuwan dawakai masu karfin gaske. Kafin
su yi wani ƙwaƙƙwaran motsi dawakan sun bayyana a wajen. Waɗan nan warriors ɗin na
ɗazun da sadauki ya biyo bayansu su suka kewayesu.

A tsorace Pretty ta fara binsu da kallo tana mamakin ganinsu. Hannun Auta ta riko
tare da janta tana faɗin ta tashi su gudu su koma ma kwancinsu.

Auta da ciwo ya ci karfinta ne ta kasa motsawa ne yasa ta saki wani wahalallen ihu,
janta Pretty ta cigaba da yi tana faɗin ta tashi su gudu. Sai dai ina Auta ba zata
iya tashi su gudu ba, haka suna ji suna gani waɗan nan warriors ɗin suka ɗaukesu
suka saɓasu saman dawakansu.

Sai kuka Auta take yi saboda ciwonta, ita ma Pretty sai kuka take yi saboda an
rabasu kowacce warriors daban ne ya ɗauketa. Haka suka juya kan dawakansu suka
kutsa da su cikin daji.

To nima dai na juya na kama hanyar gida dan maltina ta ta yi sanyi dai'dai sha.
Good bye my people's.

Wani fata zaku yi wa Auta! Pretty! Leesharh da kuma Sadauki a halin yanzu?.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Sai kuka Auta take yi saboda ciwonta, ita ma Pretty sai kuka take yi saboda an
rabasu, kowacce warrior daban ne ya ɗauketa. Haka suka juya kan dawakansu suka
kutsa da su cikin daji.

Sosai dawakan suke gudu, dan a tunaninsu Auta da Pretty ƴan uwana ne, dama in baku
manta ba Sweetie and Pretty suke nema, so sai suka ɗauki Auta a matsayin Sweetie
kenan.

Suyi nisan zago a tafiyar tasu, dan sun yi tafiya a kallah na good 20 mins a
cikin wannan dajin, kuma basu kusa fita ba, sai a lokacin Pretty ta gane ashe fa
dajin nan duniya ce guda mai zaman kanta, da a tinaninta iya wajensu ne kawai.

Waɗan nan mayaƙa sun kware wajen iya sarrafa dawakai sosai. Dai'dai tsakiyar wasu
manya manyan dogayen bishiyoyi masu tsayin da kaurin gaske, basu da cikar ganye
sosai, sun yi sama sai suka yi runfa hakan ya haifar da inuwa mai daɗin gaske a
wajen, wajen yana da faɗi sosai, waɗan nan dogayen bishiyoyi ne suka yi wa wajen
zobe, kasan wajen kuma wani irin tashi ne mai laushin gaske, idan ka matsa gaba
kaɗan akwai wani irin yashi mai bala'in laushi wanda ya fi na wannan wajen da suke,
shi har lumewa bawa zai yi a cikinsa idan ya shiga, irin wannan yashin da ake iyo a
cikinsa ne, idan ka iya ka fitar da kanka in ka faɗa, idan kuma baka iya ba ka lume
ƙasa ka mutu.

Kunsan dawakai basa iya gudu a cikin yashi mai yawa ko? Hakan yasa dawakansu
gabaɗaya suka dakata a wajen suka ki yin gaba suka kuma kin yin baya, kunsan idanun
doki daban yake dana sauran dabbobi, shi da kare sun banbanta da sauran dabbobi, su
suna iya kallon masifa, misali suna iya kallan shaiɗanu da abin cutarwa, so sun
hango yashin dake gabansu mai lumar da mutane ne yasa suka ki yin gaba, dan sun
hango mutuwa.

Waɗan nan warriors sun yi sun yi waɗan nan dawakai su yi gaba, amma ina sun ki
tafiya, sun tsaya a wajen. Dan dole ya tilastawa kowannesu ya sauko kasa daga kan
dawakan.

Cike da jarumta suke taka kasa, haka suka fara kewaye arear wajen suna duba me
dawakansu suka gani da yasa suka ki tafiya gaba suka tsaya a in da suke?.

Sauke Auta da Pretty ma suka yi, da gudu Pretty ta zo ta rungume Autar dake ta
faman kuka kamar ranta zai fita, har jini wajen ciwonta ya fara yi.

Wani dakakken warrior ne ya tinkaresu da nufin ya rabasu, wasu warriors
biyu suka rufa mashi ba. Suna zuwa suka kamasu suka ɓallesu, ma'ana suka rabasu,
sai ihu yaran nan suke yi, amma ko kaɗan basu tausaya masu ba.
Wani tsawa mai sauti wannan warrior ɗin ya daka masu a kan su yi mashi shiru.
Ƙoƙarin kwatar kansu daga hannunsu suka fara yi, hakan ya bawa warrior ɗin haushi
har ya ɗaga hannu zai dallawa Aura mari, da yake shi ya riketa su kuma warriors
guda biyun nan suka rike Pretty, kunsan Pretty ta fi Auta lafiya, so sai fisge
fisge take yi yasa su biyu suka riketa.

Auta kuma a nitse take sai dai kuka da take ta fama, kuma kukan ma wlh na ciwonta
da ya fama take yi. Tsabar rashin imani irin na wannan warrior ɗin da gashi kan
Auta ya riketa, ta rasa da wanne ɗaya zata ji, da zafin da gashin kanta yake yi
mata na rikonsa ne ko kuma da ciwon dake cikinta?.

Da karfi ya ɗaga hannu zai mari bakinta dan su yi mashi shiru, sauran warriors ɗin
suna ta kewaye a wajen suna diba menene ya hanasu cigaba da tafiya.

Lokacin guda wajen ya ɗauki wani irin shiru na unexpext haka, irin shirun na ban
mamaki wanda kamar an datse komai da sauti zai iya fita. Nan take wani irin iska ya
fara kaɗawa da karfi karfi. Wani irin haniniyar ƙosasshen jibgegen doki ne ya
karaɗe ko'ina a yankin wajen, ya doɗe masu dodan kunnuwa, haka zalika ya razana
dawakansu da suke hawa.

Wannan warrior da zai mari Auta ne ya fara janyo numfashinsa da karfi sannan ya
kurma wani irin ihu mai amsakuwar da sai da gabaɗaya arear wajen ta amsa. A miliyan
sauran mayakan suka yi kansa suna tambayar meya faru yake ihu haka?.

Kowannensu bai iya kai kashen tambayarsa ba idanunsu suka sauka a kan hannunsa da
baya tare da jikinsa. A miliyan suka kai kallonsu kan jikinsa, tabbas babu hannunsa
an datse mashi shi. To waye ya datse mashi? Yaushe kuma aka yi hakan? Ba yanzu ya
ɗaga hannun zai mari Auta ba? Meyasa hannnun ya fita daga jikinsa?.

Wannan shi ne tambayoyin da suke jefawa kawunansu. Kururuwan wannan doki ne ya sake
dakar dodannin kunnuwansu, hakan yasa suka ɗaga kai sama suna neman ta ina ne? Ita
kuwa Auta da taga abin da ya faru kuma taga lokacin da aka datse mashi hannu sai
abin ya yi mugun rikitar da ita da har yasa ta haɗiye kukanta diff, ita ma Pretty
shiru ta yi diff.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Can suka hango wani namijin gaske a saman wannan doki dake ta zuba uban
haniniyar. A miliyan suka mimmike tsaye suna kallonsa. Yana zaune zaman cikar
jarunta a saman dokin, ya rike linzaminta da kyau da hannunsa ɗaya, da alama dokin
nasa ma ɗan yi ne, dan kuwa ga shi sai ɗaga kafafun gaba sama yake yi yana wani
haniniyar ƙasaita.

Wannan namijin gasken rike yake da zabgegiyar takobinsa mai bala'in kaifi wanda
jini ya gama wanketa har ɗiga yake yi a ƙasa. Da gani ba tambaya zaka san jinin
wannan warrior da zai mari Auta aka datse mashi hannu ne, ga jinin jajir da shi.

Mamaki waɗan nan mayaka suka shiga yi a kan yaushe wannan namijin gasken ya zo ya
datsewa wannan mayakin nasu hannunsa har ya wuce basu gansa ba?. Kunga a iya nan
kawai ya gwada masu fifikon kwarewa a fannin yaki da jarumta, dan kuwa shi ba
tsayawa ya yi ya datse hannun nashi ba, yana kan dokin tsabar yana da saiti mai
karfi, a miliyan ya tsaga tsakiyarsu ya wuce tare da wucewa da hannnun mayakin da
takobinsa, kafin su ankara kamar kiftawa da bismilla ne ya wuce.

Faɗuwa ƙasa wannan mayaki ya yi azaba tana ratsa kashi da ɓargonsa. Su kuma
sauran mayakan zaro takubansu suka fara yi daga kwankwasonsu. A guje suka dimfari
in da yake a saman dokin nasa.

Bai bari sun kariso garesa ba ya sauko ƙasa daga saman dokin nasa, kan dokin ya ɗan
shafa kafin cikin harshen larabci ya ce da dokin ya je bari ya ɗan buga wasa da
waɗan nan ƙananan kwarin. Da gudu dokin ya matsa gaba, wato dokin nan ya horu iya
horuwa, gudun bala'i ne da shi na wuce misali, ga karfin gaske, sannan yana jin
maganar ogan nasa idan ya yi mashi, da alama sun yi sabo sosai.
Mayar da takobinsa mazauninta ya yi, a cewarsa waɗan nan ƙananan kwarin warriors
ɗin ba sai ya taga hankalin takobinsa wajen faɗa da su ba, hannunsa ya wadatar,
cikin ƴan mintuna zai murkushesu a wuce wajen.

Su kuwa da karfin gaske suka dimfaresa, sai wani ihu suke yi suna wani irin haki
kamar waɗan da suka je babban filin daga mai cike da mayaƙa dubu zasu yaka.

Dikkansu da takobi shi babu komai a hannunsa suka fara gwabza faɗa babu kama hannun
yaro. Pretty ta taso da gudu ta zo ta rungumi Auta tana yi mata sannu da jiki.
Ganin ciwon na jini yasa Pretty ta kara tsorata, nan take ta kara sautin kukanta,
ni da ku dik mun san halinta da balai'n tsoro, bare kuma taga jini, ai tsoro
ninkuwa ya yi.

Ƙoƙarin tallafawa Auta ta yi da ta tashi su gudu su bar wannan waje. Ina ai Auta ko
motsawa daga in da take durkushen saman gwiwowinta nan ba iyawa zata yi ba, dik
Pretty ta rikice, ta rasa me zata yi mata sai kawai ta rungumeta suka cigaba da
kuka.

Su kuwa waƴan can suna ta gwabza yaki har suka isa ga wannan yashi mai lumar da
mutum ɗin nan. Namijin gaske ya kashe mayaka biyu, su kuma ko kwarzane basu samu
damar yi mashi a fatarsa ba, da alama yasan irin wannan yashi sosai, hakan yasa
suna kaiwa wajen ya tura mayaka biyu ciki.

Nan take suka fara ƙoƙarin yin iyo dan su fitar da kansu, sai dai ina, ba zasu iya
yi ba, suna ji suna gani ga azaban zafi cikin yashin haka suka lume can kasa sai
gawarwaki.

Haka suka cigaba da gwabza yaki suna gwada mazantaka................... A hankali
Auta ta fara ganin dishi dishi sakamakon jinin da ta zubar, jiri ne mai karfin
gaske ya fara ɗibarta, kanta yana sara mata da karfi kamar zai fashe. Pretty tana
rike da ita sai ta ji ta sakar mata nauyinta gabaɗaya.

Kasancewar Pretty ba iya riketa gabaɗaya zata yi ba sai suka tafi gabaɗaya zasu
zube a ƙasa............... Kamar daga sama suka ji an taresu, gabaɗayansu ya haɗesu
ya capko suka faɗa jikinsa.

A tsorace Pretty ta juyo garesa dan taga wenenen? Cikin ranta tana tinanin Sadauki
ne, dan ta san shi kaɗai ne mai taimaka masu a dik time da suka shiga matsala. Sai
dai kash a wannan karon tana juyowa sai taga bashi bane, dik da shi ma wannan yana
cikin shigar mayaka kuma fuskarsa a rufe, tabbas ba Sadauki bane, dan ko da bata
san fuskar sadauki ba ta san kirar jikinsa, kuma ba zata kasa iya ganesa ko cikin
millions masu rufe da fuska ba!.

Zame jikinta daga nasa Pretty ta yi, ta barshi da Auta kawai, cikin nitsuwa ya
ɗauki Auta cancak. Ya gama kashe waɗan can warriors ɗin gabaɗaya, kisan walaƙanci
wanda ko kare ba zai ci ba ma ya yi masu,

Fito ya yi da ɗan karfi, Pretty na ta binsa da kallo tana san sanin wanenen
shi?......... A guje dokinsa ya danno zuwa in da suke, wannan fito da ya yi kiran
dokin ya yi. Da gudu Pretty ta juya zata bar wajen, dan a tinaninta wajenta dokin
zai zo. Cikin zafa yasa hannunsa ɗaya ya riko hannunta bai bari ta gudu ba. Ihu ta
saka mashi tana ƙoƙarin kwatar hannunta dan ta gudu.

Sai dai ina, bata iya yin hakan ba, yana tsaye har dokin ya ƙariso gabansa, saketa
ya yi tare da gyara Auta a jikinsa sosai, sannan ya haye saman dokin da ita. Pretty
tana kallonsa tana san guduwa, bata hankara ba sai ganinta ta yi a saman bayan
dokin, da hannu ɗaya ya ɗagata sai saman dokin, sannan ya umarci dokin da su
tafi............
Shin wanenen shi ɗin?.ina kuma zai kai su?.

============================🔥
•••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••🔥

Kwace rikon da Jawad ya yi mashi ya yi, da sauri ya nufi hanyar fita waje dan ya je
ya cire kayan jikinsa dan ta taɓa, in baku manta ba mugun kyankyani Jaish yake da
shi, kun tuna farkon zuwansa garinsu yadda ya rinƙa kwarara amai saboda bappa ya
taɓa shi? To yanzu ma hakance.

Binsa da kallo suka yi har ya fice daga ɗakin, momma bata yi magana ba, dan ta lura
ransa a ɓace yake sosai, kada ta shiga hakkinsa. Da sauri Jawad ya rufa mashi baya
dan ya je ya ji menene dalilinsa na shiga ɓacin rai haka? Ya kuma rarrashesa,
kunsan su ɗin amanan juna ne.

Mahnoor ta rungume Mahreen, sai a lokacin ita ma ta samu damar sakin kukan da
tun shigowarta arear kingdom of power take san yi amma ta danne.

Ƙarisowa wajensu momma ta yi da nufin ta rarrashesu, hakan ya yi dai'dai da
shigowar Aunty MieMie da kuma Fanan a

Please Login or Register in order to submit comment