You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamakin ganin ta nuna tamkar bata san da mutum a
wajen ba.

Karisawa ya yi tsakiyar parlourn, a saman sofa mai zaman mutum biyu ya zauna, cikin
natsuwa ya sanar da momma so yake ya koyar da daddynsa cewa babu banbanci tsakanin
talaka da mai kuɗi menene shawararta a kai?. Yana magana yana kallan ɗan bakin
Pretty da take ta fama hura tea ɗin wai dan ya yi sanyi, ya yi mata zafi ne.

Daga ɗayan ɓangaren momma ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau, amma dole da kanka
zaka yi amfani, idan ba haka ba ba zaka taɓa iya juya zuciyar daddynka ba". .....
Da ɗan mamaki a tattare da shi ya ce. "Ni kuka momma? To meyasa ni?". Ajiyar zuciya
ta sauke tare da miƙewa ta nufi waje dan ma kada King ya jiyota, kai tsaye rest
parlourn ɗinsa ta nufa, saman sofa ta zauna sannan ta ce. "Saboda kai ne raunin
daddynka, idan akwai wani abin da yake tsananin so to ya biyo bayanka gaskiya, dan
haka dik abin da zaka yi mashi ko tarko da zaka kafa mashi ya kasance ka haɗa da
kanka hakan ce kawai zata sa ya yi gaggawar saukowa har ya gane abin da kake so ya
fahimta".

Shiru ya ɗan yi, ya fahimci abin da momma take nufi, amma dan ya tabbatar sai ya
ce. "Momma I didn't understand".... Sarai tasan ya fahimci abin da take san faɗa,
dan tasan yaranta da saurin ɗago abu, amma tun da ya nemi bayani dallah dallah bari
ta yi mashi yadda zai fahimta.
"Ka samu ƴar gidan mutunci ƴar gidan talakawa ka kawo mashi da sunan zaka aura,
ka nuna mashi idan ba ita ba zaka iya mutuwa, ta hakance kawai zai sa zuciyarsa ta
sassauto tun da abin ya biyo ta kan sanyin idanuwansa.........."

Katseta ya yi a hanzarce da cewa. "Kuma sai na aureta ɗin?"........ Ta jima tana
san ya yi aure yaki yarda, da ta kawo mashi maganar ma sai ya sauya zance, to yanzu
tana ganin dama ne ta samu wanda idan ta bari ya kubce mata bata san ranar yin
aurensa ba kuma, dan haka zata iya yin komai dan ya aminta da wannan shawarin nata,
cikin sanyin murya da tausasawa haɗe da kalamai masu kaifi ta ce. "A'a ba sai ka
aureta ba ai, kuma zaka iya auren nata ma idan ya so daga baya in daddynka yaga yau
an wayi gari da kafarsa ya taka ya je gaban talakawa ya nemi alfarmar su baka aure,
ya gane ashe talaka yana da rana kuma yana da darajar da za'a je neman abu a
wajensa wani lokaci, to kana iya sakinta idan buƙatarmu ta biya".

A hanzarce ya ce. "No momma, ban yarda da hakan ba, ban yarda na aurenta na saketa
ba, ni auren ma ba zan yi ba, kawo wata shawara!". Ya kai karshen maganar yana kai
kallansa saman cinyoyin Pretty, da yake rigar tata zuwa gwiwowinta ne, ga shi kuma
tana zaune sai rigar ta ɗan yi sama kaɗan, lokacin guda ya ji wani abu a ransa.

"Okey to yanzu ka fara soyayyar karya da yarinyar, sai mu bi iyayenta a bayan
fage mu faɗa masu idan daddynka ya turo a nema maka auren su ce ba zasu iya bashi
ba, dan ma ya kara sanin talaka ma yana da abin da za'a iya nema a wajensa, su
hanaka yarinyar kai kuma kace idan ba ita ba mutuwa zaka yi, daddynka zai sha fama
sosai, yana tsoron ka mutu hakan zai sa ya yi learning lesson, daga nan zaka iya
rabuwa da yarinyar ba sai an kai ga aure ba, please don't say no to me my son,
wannan ita ce kawai shawarar ta hanyar da ya dace mu koyawa daddynka darasi mu kuma
sanya ya yarda da Hoorain, na san zaka so farincikin Zunaira fiye da kowa a
cikinmu".

Kalamai dai masu daɗi ta rinƙa zuba mashi, dik dan ya aminta, kun san uwa ta gari
tasan yadda zata shawo kan ɗanta har ma ta yi mashi wayau, wanda ya haifeka ya wuci
gaban tinaninka, sai dai ya ganka kawai.

Shiru ya yi yana tinanin maganganunta, tabbas tana da gaskiya, wannan hanya ita
ce kawai zata sanya King ya yarda talaka ba abin walaƙantawa bane, dan watarana
za'a iya zuwa neman wani abin a wajensa, sai dai shi kuma how comes zai yi soyayya
abin da bai iya ba, bai taɓa yi ba, ya zai yi yanzu?.

Katse mashi tinani momma ta yi da cewa. "Ka amince ko my son? Allah ya yi maka
albarka yasa ka gama da duniya lafiya". ...... Momma na kalaman yaudara my
people's, har da addu'oi tun bai amsa ya aminci na, kawai dan tasa ya ji ba zai iya
karyar mata da gwiwa yaki yarda ba, har da kara nuna confidence ɗinta, dik ta sare
mashi gwiwa ta kashe mashi jiki har bai san lokacin da ya amince mata ba. Ai wani
irin sanyayyar ajiyar zuciya da ta sauke sai da ya ji ransa ya yi sanyi shi ma,
mahaifiyarsa ta yi murna saboda shi har tana sauke sayyar ajiyar zuciya, kai abin
ya yi mashi daɗi, a ransa ya kudurta ba zai taɓa bata kunya ko yasa ta ji babu daɗi
ba, In Sha Allah zai kasance mai sanyata farinciki kamar na yau.

Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi sai magana take yi mashi tana zuba mashi ruwan
albarka amma bai ji ta ba, hankalinsa ma ya koma kan Pretty da ta miƙe ta nufi
kitchen dan ta gama shan tea ɗin. Sai da ya ga shigarta cikin kitchen ɗin sannan ya
kawar da kallansa daga kanta, yana ƙoƙarin amsawa momma addu'oin da take yi mashi
Pretty ta zumduma ihu tare da kwasowa a miliyan ta fito daga cikin kitchen ɗin.
Kai tsaye wajen shi ta nufa, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana ihu. Shiru ya yi
yana ƙoƙarin gane a wani irin yanayi yake ne?. Da gudun gaske tigernsa ya fito daga
cikin kitchen ɗin ya biyo bayan Pretty, tun da suke gidan bata taɓa sanin yana da
zaki da kuma damisa ba, dan bata taɓa ganinsu ba, idan baku manta ba a sama
gabaɗaya damisa da zakin suke, so basu cika saukowa ƙasa ba sai cikin dare, in baku
manta ba a farko farkon littafin na faɗi hakan, so shiyasa Pretty bata taɓa saninsu
a cikin gidan ba, gata mayyar tsoro, na tabbata da tasan da su a gidan ba zata
yarda ta zauna ba, idan kuma ta zauna to fa ba zata yarda da fito waje ba, zata
koma zaman ɗaki kan gado.

Wani irin tsalle tiger ya daka ya yi kansu zai yagusheta, dan ta je garin ajiye
cup a saman table ta taka mashi bindi, bata lura da shi ba, shi ne ya biyo ta.

Ai a miliyan Smart ya rungumeta suka kwanta a sanan sofar sannan ya juya da ita
ya zamana ita ta koma saman sofar shi kuma ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa ya
tare mata damisan, hakan yasa damisan ya sauka a kansa.

Zubawa wuyarta idanu Smart ya yi yana kallan tsokan wajen gwanin ban sha'awa, idan
baku manta ba suna da gurun wuya mai shegen ɗaukar hankali, aikuwa ya ɗauki
hankalin Smart namu na amana. Ita kuwa ta datse idanu gam tare da kankame rigarsa
ta wajen kirjinsa. Dirowa kasa tiger ya yi daga jikinsa yana wani girgiza, da karfi
ya fara jan hannun Smart da bakinsa irin ya matsa ma bashi Pretty. Jan da tigern
yake yi mashi ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka yana kallan
wuyarta, komawa saman sofar ya yi ta gefenta ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,
hannunsa rike da wayarsa momma na jin dik abin da yake faruwa, sai tambayarsa take
yi waye mai wannan ihu amma bai ji ba, dan ya zare wayar daga kunnensa.

Tsalle damisan ya yi zai haye kanta Smart ya yi saurin riƙosa ya rungume irin
alamar rarrashi, ita kuwa har lokacin bata motsa ba, kamar dai suma ta yi. Da kyar
ya rarrashi damisan ya tafi, dawo da kallansa a kanta ya yi, yadda ta faɗa jikinsa
ne kawai a ransa, a lokacin sai da ya ji gabaɗaya komai nasa ta ɗauke diff. A yanzu
ma sai da momma ta katse kiran ta sake kiransa, doguwar numfashi ya ja tare da
saukewa a hankali, sannan ya katse ya kirata. Tana ɗagawa ta hau tambayarsa lafiya
wacece take ihu haka. Bai ɓoye mata ba ya sanar da ita dik abin da ya faru.

Yana gama faɗa mata ta tari numfashinsa da cewa. "Shikenan ma mun sa yarinyar da
zamu yi wannan aiki da ita, kuma ga shi Zunaira ma tana kaunarta, daddynku zai koyi
darasi sosai, kuma yarinyar tana da natsuwa, ka kula da ita bari in binciko
iyayenta, nasan mara galihu ce itama, dan Zunaira ta ce mun a daji suka haɗu da
ita, bata da kowa, ni kuwa nasan ba zai taɓa yiwuwa bata da kowa ba, dan haka bari
in fara bincike a kan iyayenta kai kuma ka fara kulla soyayya a tsakaninku"..
Tashin hankali!!! My people's momma zata jijjigo babbar aiki, domin binciko iyayen
Pretty ba ƙaramin abu bane,!! Kuma zai iya zama abu mara daɗi a garezu, akwai show,
momma zata tono wani babban............ Na dai yi shiru amma akwai cakwakiya.

"Momma wannan yarinya ce karama and......" Katse shi ta yi da cewa. "Ai yarinyar
ta fi, saboda ka ga ba aurenta zaka yi ba, idan babbar mace ce ka yi soyayyar karya
da ita zata iya fara sanka da gaske, kaga in ka barta baka aureta ba kuma an cutar
da zuciyarta, amma ita yarinya bata san soyayya ba, ko ka rabu da ita a lokacin da
buƙatarmu ta biya lafiya lou ne"..

Ni kuwa na ce ba dai yaran yanzu ba, da sanin komansu ake haifansu ato, dan haka
kamar Pretty ta san soyayya mana momma!.

Ya gamsu da zancen momma, amma sai ya ce ta bashi lokaci ya yi tunani ko zuwa gobe
ne. A kan haka suka tsayar da zance, daga haka suka yi sallama. Katse wayar ya yi
ya tura cikin aljihu tare da ɗan sunkuyo da kansa a kan Pretty, sai a lokacin ya
fahimci suma ta yi, mayyar tsoro kawai.

Miƙewa ya yi ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya nufi switch, kashe wutar parlourn
ya yi ya haura sama yana tinanin a kan zantukan momma..... My people's me kuke
tunanin zai faru? Momma zata gano iyayen Pretty? Su waye iyayen nata? Smart zai yi
accepting soyayyar karya da Pretty idan ya gama tunanin nasa ko ba zai yi ba? Muje
zuwa, kada ku manta Pretty dai an yi mata miji, mom ɗinsu ta bada ita wa Kamran
kafin ta ɓata ko? In kun manta na tina maku!!.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥

Ko kaɗan kalamanta basu huda zuciyarsa ba, babu sassauci a tattare da shi, ta
kankame hannunsa gam tana yi mashi magiya, amma ina babu alamar zai sassauta. Sun
kwashi good 30 mins a haka tana mashi magiya bai kulata ba, taki sakar mashi
hannunsa, kuka take yi hawaye bibbiyu wai ko zai tausaya mata, amma ko kaɗan bai ji
komai ba, kuma idanunsa suna kan face ɗinta fa, yana ganin yadda take kuka, amma
ina zuciyar ta riga da ta bushe.

Ihu Ronnie ya kurma tare da matsawa kusa da su yana faɗin. "Please big bro for give
them, Sweetie konasu fa ake yi". A rikice ya yi maganar cikin fitar hayyaci.

Kun san already kafin Sweetie ta rike hannunsa ta hana shi latsa laptop ɗin ya
rigada ya shigarwa da Robbot ɗin umarnin abin da zasu yi, so ita Sweetie a
tinaninta tun da ta rike hannunsa shikenan ba zai samu damar bada umarnin ba, bata
san aikin gama ya rigada ya gama ba, ta tsaya tana yi mashi magiya already su kuma
robbot suna aiwatar da aikinsu. Injuna na zamani suka yi amfani da su wajen haka
ramin cikin ƙanƙanin lokaci, sannan suka hura wuta tamkar yadda ya umarcesu. Dik
wanda ya bijirewa Black Tiger sai su kama shi su jefa shi cikin wanna balbalin
wutar, yana ihu yana basu hakuri haka zasu jefa shi ciki gwanin ban tausayi.

Wannan ihu da Ronnie ya kurma abin da ya gani kenan ya razana shi ya tashi
hankalinsa, sai jefa mutane cikin wutar robbot suke yi. Hankalin Sweetie idan ya
kai miliyan to ya tashi, wai abin takaicin ma har da ƙananan yaran da basu suka yi
mashi laifi ba, iyayensu ne suka bijire mashi, to uwa ta yi gabas ai dole ta kama
hannun ƴaƴanta su wuce gabas ɗin da shi ko? To idan aka jefa uwar cikin wuta sai a
jefa ƴaƴan ma su da ba su san komai ba uwarsu kawai suke bi. Gabaɗaya birnin ya
rikice da ihu da magiya na ban hakuri, amma Black Tiger yana tsaye yana ganinsu
tamkar wani dutse ko karfe bai sarara masu ba, tamkar babu zuciya a kirjinsa, babu
alamar ma sun bashi tausayi ko ɗigo a ransa.
Ihu Sweetie ta kurma, da karfi ta fara kai mashi duka a kirjinsa da hannunta dikka
biyu tana jijigasa da karfi tana faɗin ya rabu da mutanen nan ya kyalesu, ya rabu
da yaran da ba su ji ba basu gani ba, ya dubi girman Allah ya sauke RAWANIN
ZALINCIN dake kansa ya ɗaura na adalci, sambatu take cikin fitar hayyaci tana kai
mashi duka babu kakkautawa. Yana tsaye tamkar gunki, ko kaɗan babu alamar zai
tausaya. A cikin kwakwalwarta Sweetie take jiyo ihun mutanen nan ta cikin mirrorsa,
sai dai ba zata iya taɓuka masu komai ba. Tashin hankali da firgici ne suka yi mata
yawan da ba zata iya ɗauka ba, hakan yasa tana cikin sambatu tana kai mashi duka
kawai numfashinta ya ɗauke diff ta zuba ƙasa a gabansa... BA SHAKKA YAU BLACK TIGER
YA FITO A AINAHIN BLACK TIGER ƊIN NASA, BABU SASSAUCI.

A miliyan Ronnie ya yi kanta yana ambatar sunanta, shi ma hawaye yake yi bibbiyu,
zuciyarsa ta gaza iya ɗaukar wannan masifa da tashin hankalin, tun yana ambatar
sunan Sweetie cikin ɗaga murya da kaushi, har voice ɗinsa ta dai'na fita, kan kace
me shi ma ya sulale ƙasa a wajen ya sume... Innalillahi wa inna ilahir rajiun.
BLACK TIGER dai ko a jikinsa, sai ma cigaba ya yi da yin aikinsa yana latsa laptop
ɗinsa.

My people's kuna tinanin Black Tiger zai iya canzawa kamar yadda Sweetie da Ronnie
suke so kuwa? Zai iya sauke RAWANIN ZALINCIN dake kansa kuwa? Kuna ganin team
Ronnie and Sweetie zasu yi nasara kuwa? Sweetie tana yawan cewa zuciyar Black Tiger
mai kyau ne akwai dalilin rikiɗewarsa izuwa bakin mugu, shin menene wannan dalilin?
Ya Ronnie zai ji idan ya ji Floris ta mutu? Har da iyayenta suka bijirewa Black
Tiger,.shin suma har da su aka kona? Wani irin hukunci master Devil zai karɓa a
hannun Ronnie and big bro?.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Zaune ya isko Ramish a saman bedside drawer yana ƙoƙarin treating na hannunsa.
Cikin zafa ya ƙariso wajen yana tambayarsa meya same shi a hannun nasa? Ina ya je
daren jiya?, meyasa yana ta kiran wayarsa baya ɗagawa?. Cikin tashin hankali ya yi
maganar.

"Get out from here!". Shi ne abin da Ramish ya faɗa cikin kakkausar murya.
Gadan gadan Bilal ya nufosa. "Babu in da zanje har sai ka faɗa mun abin da ya
sameka". Tsawa ya daka mashi a kan ya fita mashi a ɗaki kuma ya tabbatar kafin nan
da 30 mins ya gyara mashi kofar da ya ɓallah. Da ya fahimci Ramish yana kan tsini
sosai sai ya juya ya fita gudun a samu matsala, kai tsaye ya nufi wajen Abbie.

Yana fita shi kuma Ramish ya miƙe ya nufi in da Leesharh take kwance a balconynsa
saman kujera, rufe kofar balconyn ya yi ya ƙarisa wajen a gaggauce, dan bai gama yi
mata abin da ya dace ba.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥

Bayan wasu kwanaki da basu haura one month ba, akwai dalilin da yasa na yi maku
wannan tsallake, idan mun yi gaba zan dawo baya domin yi maku bayanin abin da ya
faru a waɗan nan kwanaki, muje dai zuwa.

Ramish da kansa ya yi jijyar Leesharh ba tare da sanin kowa ba, bai bari kowa
yasan da abin da ya faru ba sai babban yayansu wato Smart, dan ya gane mai taya shi
aiki shi ne babban yayansu da mama ta takura mashi a kan ya yi mata bincike ba ɗan
King bane, yana ganin hoton Smart ya gane yayansu ne saboda kamanninsa da su
Zunaira, to yarasa wani irin shaida kuma mama take so bayan kamanninsa da kannensa.

Amma fa ko da ya faɗawa Smart ga abin da ya faru bai sanar da shi ya yi mata fyaɗe
ba, ya dai faɗa mashi yana zargin Ummie and Bilal, da Smart ya tambayesa dalilinsa
na zarginsu sai ya sanar da shi cewa akwai wata rana da ya fita cikin hayyacinsa
har ya kusa yi wa mai aikinsu fyaɗe, lokacin da ya dawo cikin hankalinsa ya zauna
yana tinanin meyasa ya birkice har haka, meyasame shi? A lokacin ya ce bari ya
gwada jinin jikinsa ya gani, a nan ne ya gane wasu kwayoyi sun ratsa jininsa wanda
kuma yana da tabbacin ba alluransu aka yi mashi ba, da bakinsa ya sha, in kuwa haka
ne to dole ko Ummie ko Sharrifat ɗaya cikinsu akwai wanda ya sanya mashi waɗan nan
kwayoyi cikin abin shansa, dan baya cin abinci a waje, dik in da ya je sai ya dawo
gida yake ci, kuma Sharifat ce kawai mai kawo mashi abu ya ci, to kun ji yadda aka
yi Smart yasan abin da ya faru.

Batun fyaɗe ya rufesa iya shi da ita kawai, ita ɗin ma da farko ya so yi mata
allura ya mantar da ita komai, amma daga baya da ya yi dogon tunani sai ya ce kila
tana da ƴan uwa bayan iyaye, idan ya yi hakan ya yi mata zalincin da ba zata iya
yafe mashi ba, gara ma fyaɗen da ya yi mata a kan wannan alluran, da ya kwantata
hakan da kansa, ya ce yanzu shi ayi mashi allura ya manta su Smart gabaɗaya a
rayuwarsa, sai ya ji ina ba zai iya yi mata ba, dama kullum a rayuwar nan idan zaka
yi hukunci ka kwatanta da kanka ka gani, hakan ce zata sanyaka yin adalci, yana
ɗaya daga cikin abin da yasa kuka ga ni Princess Teema bana san kashe mutane a
cikin littafina, saboda kwatanta abu da kai'na ya zame mini jiki, so idan na
kwantanta irin raɗaɗin da zasu ji a kai'na sai in ji kai ba zan iya jurewa ba, wlh
shawara nike baku domin tsira, kasance mai kwatanta abu da kanki tabbas zaki zama
adila mai yiwa mutane adalci cikin sauki, Allah dai ya shige mana gaba ya dafa
mana.
Ba zan baku labarin abin da ya faru bayan farfaɗowar Leesharh tsakaninta da Ramish
ba, saboda ina da dalilin ɓoye hakan, sai gaba zaku ji komai, iya abin da zan faɗa
maku a nan shi ne Leesharh dai ta shafe complete sati yana wahalar jinyarta kafin
ya iya shawo kan matsalar, a jinyar tata ma abubuwa da dama sun faru, jinyarta yasa
bai bi ta kan bincikar dalilin da ya kawo kwayoyi a cikin jininsa ba, yana busy
sosai, ga shi jinyar tata cikin sirri yake yinsa, abin ku da rashin gaskiya yana
cikin tashin hankali a koda yaushe, bashi da wata natsuwa, sannan ya jefa kansa a
cikin damuwa da rashin walwala dik dan abin da ya aikata wanda bai taɓa zatan ko a
mafarki zai aikata ba, ya shiga zulumin kullum cikin fargabar asirinsa zata iya
tonuwa, ya zama wani irin sukuku haka.

A haka ya shafe makonni uku yana fama, sai a cikin mako na huɗun nan ne ya sami
natsuwa da kwanciyar hankali dalilin komawarta dai'dai, sai dai fa idan zai kwana
yana yi mata magana bata amsa mashi, har yau ta gagara ɗaga idanu ta kallesa, wani
irin tsananin bakinciki ne a ranta wanda take jin tamkar ta kashe kanta, abin
takaici, shi kuwa Allah ya jarrabesa da tausaya mata matuƙa, ya gagara watsar da
alamarinta ya kama aikin gabansa, yana ganin koma me ta yi mashi ya cancaci hakan,
saboda shi ne silar kuncinta a rayuwa, dan haka baya jin komai idan ya yi magana
bata kula shi ba.

Sharifat ta yi haukar nemanta har ta gaji ta fawwalawa Allah komai, ta sanar da
Ramish and Bilal sai dai da ta cika matsawa Ramish ya ce mata kada ta sake yi mashi
maganar Leesharh idan ba haka ba zai saɓa mata. Shi ma Bilal ya yi haukar nemanta
kamar menene, ya shiga damuwa matuƙa. Amma shi Abbie bai damu da rashin ganinta ba,
dan ya tambayi Ramish ya ce mashi tana nan suna tsaka da aiki ne ta bashi haɗin kai
tana gabatar mashi da wasu hujoji, sai ya yi amfani da abin da ya faru da ita a
ranar na kasheta da aka shiga za'ayi a ɗakinta, sai ya ce wa Abbie ai ya ɗauketa
daga gidan nan ne dan kada a sake yunkurin kasheta, ya kaita waje mai tsaro sai sun
gama aiki zata dawo, Abbie ya yarda da maganarsa, yasan baya yi mashi karya.

A zahirin gaskiya ya ɗauketa daga gidan Abbie tun washe garin ranar da abin ya
faru, tun time da Bilal ya ruguje mashi kofa, a wannan rana da daddare ya fita da
ita daga gidan ya mai da ita gidansa, a nan ya yi jinyarta, shiyasa su Bilal basu
san in da take ba, sun yi neman duniyar nan babu ita babu labarinta.

•••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Zaune take a saman sofa mai zaman mutum uku a cikin parlonsa, ta yi shiru tare da
buga uban tagumi tana tunanin irin rayuwar da ta sha, ta fuskanci challenges dayawa
baiwar Allah nan, yanzu kuma ɗan mutumcin da take ji da shi ɗin ma babu, tinaninta
ɗaya shi ne waye zai aureta a haka? Shikenan ita ta zo duniya a wahalce kuma zata
koma a wahalce babu wani gata?. Kanta a kasa tana kallan yatsun kafafunta da suka
ɗan ya fayau, dik ta yi rama sosai saboda bata cin abinci, kullum tana cikin
tinani. Size ɗin kayan da take sakawa a da yanzu sun yi mata yawa, sai dai ƙasa da
su, saboda rama, sai idanu kawai zaka gani.

Sleeping dress doguwar riga ce a jikinta launin maroon color, ta sanya ɗan ƙaramin
hijabi a kanta, rabonta da abinci tin daren jiya da ta sha tea, bakinta sam babu
ɗanɗanon komai, bata sha'awar cin komai kamar wata mai ƙaramin ciki.

Ko kaɗan bata ji motsin shigowarsa cikin parlourn ba, dan ta yi nisa a cikin
tunanin da take yi, har ya shigo ya wuceta ya nufi kitchen, ta luluƙa duniyar
tinani. Haka zalika bata ji dawowarsa ba sai ganinsa ta yi ya zauna a saman sofar
da take zaune hannunsa ɗauke da cup and small chop a cikin plate, yana sanye cikin
sleeping dress riga da wando launin milk color, ya yi kyau sosai, sai dai shi ma ya
rame sosai alamar yana cikin damuwa, dik wanda ya yi complain a kan ramansa sai ya
ce aiki ne ta yi mashi yawa. Har Smart ya yi complain a kan ramansa, amma sai ya ce
zai rinƙa kulawa yana ragewa kansa pressure dan ya maida jikinsa.
Yana zama ta zabura ta miƙe zata bar wajen. A hanzarce ya ɗaura plate na small
chop a saman table dake kusa da su ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun, in a low
voice sosai ya ce. "Please Aesh, ya isa haka gudun nawa da kike yi, dan Allah ki ji
tausayina, ko iya haka ya kamata ki fahimci ba da gangan na yi maki hakan ba, idan
da da gangan ne ba zan kwashi up to one month ina kula dake ina kuma yi maki
magiyar da ki yafe mun ba, ki mun magana ba, dan Allah".

Jikinta ne ya hau kerma, dan a duniya tsoronsa take ji matuƙa, murya na rawa ta ce
mashi. "Tabbas da gangan ka ci mun mutumci, ka mun tabon da ba zai taɓa gogewa a
cikin zuciyata ba, ka zalinceni, dama a lokacin da ka kamani ka sakeni ka ce mun in
ka yi bincike ka ga da sa hannuna a abubuwan da suke faruwa zaka mun abin da ba zan
taɓa mantawa da kai ba a rayuwata, ga shi kuma ka mun ɗin kamar yadda ka faɗa,
tabbas ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata! Ka cuceni ka zalinceni! Dan Allah
ka kashe ni in huta da wannan rayuwa". Ta kai karshen maganar zafafan hawaye suna
zubowa a saman kumatunta.

Shiyasa aka ce ka rinƙa tauna magana kafin ka faɗeta, baka san me gobe zata haifar
ba, ga shi maganar

Please Login or Register in order to submit comment