You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi dan ta taushi King.

Cikin zafa ya ɗaga mata hannu alamar baya da buƙatar jin komai daga garesu, infact
su fita mashi a ɗaki baya san ganinsu. Ganin ya ɗauki zafi sosai hakan yasa mummy
ta miƙar da momma tare da ce mata. "Rahilarh ki yi hakuri mu je, zuwa da safe idan
ya huce sai muyi magana ko?".

Hawaye sosai momma take yi, dan ita kanta tasan bata kyautawa King ba, haba wani
irin zalinci ne wannan? A lokacin da ya samu labarin rasuwar Smart yana zaune a
saman kujerar mulkinsa sai da ya miƙe tsaye, bai san lokacin da ya cire crown ɗinsa
daga kansa ba, ya jijjiga sosai, kwana uku bai fita fada ba yana jinyar zuciyarsa,
da taimakon Allah da addu'ar iyaye da abokan arziki ya samu zuciyarsa ta iya ɗaukar
wannan kaddarar, shi ma ya kusa mutuwa, ashe dik shirin momma ne, gaskiya abin
akwai ciwo, babban abin da ya fi kona ran King ma shi ne yadda Smart bai ɗaukesa da
daraja ba, yanayin tarbiyarsa kaf ta sha banban da tarbiyar jikokin Akka, dik ya
damesu a komai ya shanye, King ya yi takaicin hakan matuƙa.

Waje gabaɗayansu suka fita, suka kyale King shi kaɗai a cikin ɗakin yana ta
huci. A bakin kofa mummyn Chuchu ta tsaya ita da Aunty MieMie suka hau sharewa
momma hawaye suna tausanta har sai da ta yi shiru, sannan suka rakata ɗakinta.

A parlour kuwa kowa ya yi mutuwar zaune da jin abin da momma ta faɗa, su uncle
Abbas an rasa abin faɗe, Akka kuwa ta kara ɗaukar zafi, abin ya bakanta mata rai,
momma ta yi masu ba dai'dai ba, a fusace ta miƙe ta nufi part ɗinta domin ta je ta
kira Husaininta wato King Badeen ta sanar da shi abin da ƴaƴansa Momma da baban
yayanta wato daddyn Smart suka aikata.

Da sauri Dr Raj ya miƙe ya bi bayan Akka, a cewarsa kada ciwon zuciyarta ya
tashi ta sume, bari ya yi saurin bin bayanta......................... Sarina kuwa,
dik abin da ake faɗa baya shiga kunnuwanta, hankalinta na'a kan Smart, sai kallansa
take yi kamar zata cinyesa da ido, taga kyau iya kyau, tini ta yi rantsu da Allah
ga mijinta nan ya bayyana.

Mammie ma alkawari ta yi wa kanta a kan lallai ne wannan shi ne mijin Sarina, dama
ta ce first born na King yarta zata aura, to ga shi ya bayyana.

Uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka yi gaggawar bin bayan Akka da Dr Raj. Miƙewa
Jaish ya yi tare da cewa Smart ya zo su je part ɗinsa ya kwanta ya huta zuwa da
safe zasu sake zama, dan case bai kare ba, yanzu ma aka fara.

Jawad da shi ma already ya san da Smart saboda shi ɗin kamar ɗan momma yake, shi ma
miƙewa ya yi tare da riko hannun Chuchu yana faɗa mata ta tashi su raka Yah Omerish
part ɗin Jaish kafin su dawo su tafi nasu dare ya yi.

Smart rike da hannun guyson and Auta da ta yi shiru ya miƙe tsaye, Jaish ya yi gaba
ya rufa mashi baya. Miƙewa Obaid and Omaid suka yi, har zasu wuce su fita Omaid ya
juyo da kallansa a kan Sarina, ƙasa ƙasa ya ce. "Aunty Sarina kinga Yah Omerish ɗin
yanzu ko? Ko dai har yanzu a mafarki kika san shi?".

Ta fahimci gatse ya yi mata cikin maganar, amma sai ta danne ta ce e ta gansa, a
cikin zuciyarta kuma mamakin Omaid take yi, dan lokacin da tambayesu wanene Omerish
shi Omaid bai yi magana ba, ya yi ma kamar bai jita ba, ashe ya ji ɗan kaniya,
rashin kunya yasa ya yi banza da ita.
Wucewa suka yi suka nufi waje abinsu. Mammie ce ya miƙe tana cewa Sarina su
tashi su tafi dare ya yi. Miƙewa suka yi suka fita, parlourn ya rage mama, uncle
Taheer da kuma Aneesa, mama ta gaza motsawa daga in da take zaune, tamkar ruwa ya
cinyeta, ta rasa ganewa kanta, momma ta rusa mata plan, a ranta ta kuduri niyar wlh
ba zata hakura ba, ba zata bari ba gaskiya, sai ta ɗauki mataki.

Bedroom dake kusa da nasa Jaish ya kai Smart, cike da kauna ya ce mashi. "Yah
Omerish wannan bedroom ɗin ya yi maka ko dai na canza maka wani?".

Hannu Smart ya ɗaga mashi bayan ya saki hannun guyson, sannan ya ce. "Is okey, Omar
ku zauna bari in yi take bath ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sake hannun
Auta. Juyo da kallansa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Sorry our baby,
daddy sai ya biya wannan marin da ya yi maki, bari Allah ya kaimu wayewan gari kin
ji?".
Ya yi maganar yana ɗan shafa kumatunta in da shatin hannun King suka fito
ruɗu ruɗu.

Kai ta jinjina mashi tana kara shagwaɓe fuska.
"Hau saman bed ki kwanta ina zuwa". Ya faɗa yana nuna gadan da hannunsa. Ba
musu ta haye har lokacin tana ɗan sauke shessheƙar kuka a hankali hankali.

"Yah Omerish ni ma bari in je in yi wanka sai in sa a kawo maka abinci". Cewar
Jaish.
Jinjina kai Smart tiger ya yi, kafin ya ce. "No need anything now, ka dai je
ka yi wankarka, ba sai kasa an kawo mun komai ba". Ya kai karshen maganar tare da
ɗan rungumar Jaish ɗin kamar yadda suka saba a al'adarsu ta France, sannan ya nufi
toilet.

Matsawa kusa bed ɗin Jaish ya yi, cike da kauna ya kara rarrashin Auta da
guyson kafin ya wuce ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin. Yana fita kai tsaye nasa
bedroom ɗin ya nufa. Wani irin daddaɗar kamshi na daban ne ta dokin hancinsa ba
wanda ya saba ji ba, alamar an canza mashi room freshener kenan. Shakar kamshin ya
yi haɗe da ɗan lumshe idanu, alamar kamshin ta ratsa shi sosai, akwai daɗi kam.

Mamaki ya yi a kan waye ya canza mashi room freshener kuma?. A bakin bed ya zauna
tare da rage kayan jikinsa, short and singlet kawai ya bari a jikinsa, miƙewa ya yi
ya nufi toilet yana tinanin wannan cakwakiya na.

Tura kofar toilet ɗin ya yi tare da yin addu'ar shiga ya sanya kansa. Tura kofar da
ta ji anyi ne yasa ta juyo a miliyan dan taga wenenen? Tana tsaye a gaban jacuzzi
wajen shower, ta kunna ruwa ta cika boket tana wanka, dan ita bata san shiga cikin
jacuzzi, tafi yarda da ta tara ruwa a boket sai ta yi wankanta.

Ta gama sanya kumfar sabulu a gabaɗaya jikinta ta juyo gatesa. Ɗan zaro mata
idanunsa ya yi yana binta da kallo kamar ba shi ne ya ce kada ta bari su sake
haɗuwa ba, ya ga kaya ɗan rainin wayo, dama da guntun jarabarsa ta kwanaki uku da
suka wuce da ya sameta tana barci a parlournsa, to bai gama watsakewa daga wancan
bama sai ga shi yau ya sake yi babban kallo wanda da wuya ya iya tsallekawa ko kuma
ya ce zai kwantar da wannan tarzoma dake shirin tashi

Saboda da alama abar ta motsa. Kasa gaba ya yi ya shigo cikin toilet ɗin, ya kuma
kasa yin baya ya fita, ya tsare yar mutane da ido, yasata jin kunya in ban da
rashin kunya irin na jikokin Akka.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



Love page, yauwa kwana biyu mun sha gwagwarmaya sosai, to yau kam bari mu ɗan yi
nishaɗi mu leƙa duniyar masoya kafin mu ɗaura da surprises ɗinmu.


Ita kuwa tana ganinsa ta saki kara tare da juya mashi baya. Ɗan ɗaure fuska ya yi
tare da jan siririn tsaki, wai irin shi zai basar kada a rai'na shi ɗin nan, sai ya
wani tsare gida, cikin dakiya ya ce. "Ke bana ce kada ki bari mu sake haɗuwa ba?".
Yana maganar kuma yana karewa halittar jikinta kallo dan tabbatar rashin kunya irin
na jinin Akka.

Shiru ta yi, ta ƙasa amsa mashi, ji ta yi tamkar ta nitse ƙasa saboda kunya.
Wani siririn tsaki ya sake ja kafin ya juya da sauri ya fice yana haɗiyar yawu, wai
shi a dole zai basar ya danne.

Saman bed ɗinsa ya haye ya kwanta, janyo wayarsa ya yi domin ya ɗan rage lokaci
kafin ta fito. Sai dai kuma yana taɓa wayar tamkar ya kunnawa ƙwaƙwalwarsa
tinaninta ne, gabaɗaya ya nemi sukuninsa ya rasa, har wani zufa ne ya fara keto
mashi a gefe da gefen face ɗinsa, gabaɗaya a matse yake amma ya nuna zai danne
hakan.

A hankali ya jefar da wayar tasa ba tare da ya farga ba, wasa wasa ya ɗan fara juyi
a saman bed ɗin ƙwaƙwalwarsa na kara tinano mashi kyan surar jikinta, ga shi sai
glowing take yi, hasken fatarta ya ƙara fitowa sosai, har wani yellow yellow ta yi.
Haba tini notikan ƙwaƙwalwarsa suka fara kwancewa.

A haka ta fito ɗaure da towel ɗinsa a kirjinta ta same shi, yana jin motsin
fitowarta sai ya danne juyin da yake yi, ya kwanta ya kifu tsit kamar wanda ya yi
barci, ɗan rainin wayo kuma abar tana damunsa sosai, amma wai irin kada ta rainasa
ɗin nan, sai ya dake.

Ita kuwa baiwar Allah, bata wani kallesa sosai ba, saboda kunyar babu kaya a
jikinta, da sauri ta shiga dressing room dan ta shirya.

Yana ganin ta shiga ya yi saurin miƙewa ya nufi toilet wai dan ma kada ta dawo ta
same shi a haka har ta gane halin da yake a ciki, sai ya gudu cikin toilet yana
matse bananar tasa dan ya samu sauki.

Cikin ɗaya daga cikin kayan da momma tasa mama Haulat ta kawo mata na barci ta
shirya. Ta yi wani irin kyau da in dai namiji lafiyaye ne ya ganta to fa ba zai iya
hakura ba. Hijabin da take sallah ta ɗauka ta ɗaura a saman kayan, sannan ta fito
ta nufi part ɗin momma dan ta ɗauko mashi cappuccinon, Allah sarki sam bata gajiya
da kyautata mashi dan tana san kayanta, shi kuma sai sinki sikin iskanci da
iyashege cike da ƙwaƙwalwarsa.

Mama Haulat ce kullum take kara karfafa mata gwiwa a kan ta cigaba da matsar da
kanta a garesa tabbas watarana zai waiwayeta, shiyasa kuka ga har yanzu take shiga
bedroom ɗinsa bata dai'na ba, ita kuma Chuchu tana kara koya mata yadda zata narka
zuciyarsa a soyayyarta, yanzu ta ɗauki darasi sosai abinta, jira take yi kawai wani
abin ya haɗasu yaga zallar madarar soyayya.

Allah sarki momma uwa ta gari, dik da tana cikin damuwa a kan abin da ya faru
a tsakaninta da King, hakan bai hanata ta shiryawa ƴaƴanta abin da suke so ba, ta
shiryawa Jaish and Omerish cappuccino kamar yadda suka saba sha a kowacce dare
kafin su kwanta.

Mahnoor tana zuwa ta ɗauki cappuccinonsa kamar yadda ta saba, a lokacin momma tana
cikin toilet tana wanka dan ta koma wajen dearlyn love ɗinta ta rarrashi
kayanta......🤭👀

Bata tsaya jiranta ba ta ɗauki cappuccinonsa ta fito. Har lokacin da ta koma
bedroom ɗin yana cikin toilet bai fito ba....... Wai me ya tsayar da Jaish a cikin
toilet ne?........👀🥱

Ɗan ƙaniya yana can yana ƙoƙarin controlling na kansa ya haɗiye kwaɗayinsa ya danne
abar gadon, sai dai ya gaza iya yin hakan, sai ma kara tashi hankalinsa yake yi ta
sanadiyyar tinano mashi surarta da ƙwaƙwalwarsa yake ta yi, dik ya kiɗime, abin
tausayi kuma abin dariya.
Saman table ta ɗauka cappuccinon, sannan ta ɗauko perfume da Chuchu ta bata
mai sanyin kamshi ta feshe jikinta da shi. Kamar zata fice waje izuwa bedroom
ɗinta, sai kuma ta tina da kalaman mama Haulat da kuma Chuchu ɗazun in da suke ce
mata ta dai'na kwana a wani waje in ba a saman bed ɗinsa ba, komai zai ce mata kada
ta damu ta daure watarana zai wuce kuma zata yi nasara.

Tina waɗan nan kalaman yasa ta cire hijabin jikinta ta mayar da shi d-room ɗinsa,
sannan ta dawo ta haye saman bed ɗin, kwanciya ta yi haɗe da rufe idanunta tana
tinanin abin da zai faru idan ya fito ya sameta kwance a saman bed ɗinsa.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A gefe guda kuwa, Dr Raj da ya bi Akka yaga babu wata matsala, ga kuma su uncle
suna tare da ita, sai ya yi saurin ficewa daga ɗakin, dan dik hankalinsa yana a kan
yarinyar da suka yi karo ɗazun. (Zee) Burinsa kawai ya sake sanyata a idanunsa dik
da bai san wacece ita ba.

A karon farko yau ya yi wa garden sallama da ɗan sauti. A lokacin Zee tana
kwance saman sofa ta takure jikinta waje guda, har barci ya fara ɗaukarta, dama kun
san ta ce ba zata koma part ɗin mama ba, gara mata ta kwana a waje, so shi ne ta yi
kwanciyarta a nan har barci yana shirin ɗaukarta.

Ganin alamar bata ji sallamarsa bane yasa ya sake yi mata sallama cikin
natsuwa. A ɗan razane ta waro idanunta. Da yake ta fara barci sai bata iya gane
wanene bane dik da hasken dake wajen. Ganin mutum yasa ta yi saurin miƙewa zaune
idanunta a kansa, tana san tantance wanene?.

Wucewa ya yi izuwa saman sofa ya zauna yana kallanta shi ma, sai yanzu ta iya gane
ashe mutumin da take mafarki ne a yanzu, wannan ɗan barci da ya ɗauketa har
mafarkinsa ta fara yi. Ƙasa ta yi da kanta tare da cewa. "Good evening".

Kallanta da yake yi irin kallan nan ne na ke special ce da kika sace zuciyar jinin
Zuhair lokaci guda. Ta tafi da imaninsa ta yadda kunnuwansa suka ƙasa iya jiyo
mashi sanyayyar muryarta tana ɗaga mashi gaisuwa. Sai da ta sake ɗaga mashi
gaisuwar sannan ne ya fahimci ashe magana take yi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya
amsa mata.

Ganin alamar zama ya zo yi a wajen yasa ta miƙe tsaye domin ta koma ciki, sai satar
kallansa ta kasan ido take yi, taga ɗan kyakkawan mamansa kani a wajen Ramish namu
na amana.
Step biyu ta ɗan taka zata taka na uku kenan ta tsinkayo sexy voice ɗinsa yana
faɗin. "Ina kuma zaki je?".

Cikin natsuwa ta juyo, dik da bata san wanenne shi ba tana respect ɗinsa sosai.
"Ciki zan koma". Ta bashi amsa tana ɗan ɗago kallanta dan ta saci kallansa da kyau,
tana san ganin face ɗinsa sosai amma bata san su haɗa ido. ........... "Ciki
kuma?". Ya maimaita maganar da alamar mamaki a saman face ɗinsa. Kasancewar da
turanci ta ɗaga mashi gaisuwa sai kawai ya cigaba da yi mata magana da English ɗin.

Kai ta gyaɗa mashi alamar e ciki. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "To kafin dai ki
shiga cikin z ki bani abata da kika sace kada ki tafi da ita". Ya yi maganar yana
kara gyara zama haɗe da ɗan wasa murya.
Zaro idanu sosai ta yi, take tsoro ya bayyana a saman face ɗinta, a ɗan
ruɗe ta ce. "Wani abu kenan? Ni ban ɗauki komai ba wlh". Ta kai karshen maganar
tamkar zata yi kuka.

Miƙewa tsaye ya yi, a hankali ya yi step biyu ya matsa kusa da ita sosai, ƙasa ya
yi da murya kafin ya ce. "Kawai ki bani abata tin kafin kowa ya jimu, kin san da
cewa a wannan masarauta dik wanda ya yi sata cire mashi hannu ake yi ko?".
Kai ta girgiza alamar bata sani ba tana zaro idanu.
Kara taka step ɗaya ya yi ya sake matsawa kusa da ita sosai, kashe muryansa kaɗan
ya ɗan yi, kun san doctors da shegen iya soyayya da iya magana. Da sauri ta ɗan ja
baya ganin ya matsota sosai, har cikin ranta ta ji tsoron kalamansa, dan ta ɗauka
da gaske an sace mashi wani abin ne zai kala mata sharri.

"To in baki sani bama yau kin sani, dik wanda ya yi sata datse idanunsa muke yi, ga
shi ke kuma kin mun sata, amma babu komai ki dawo mun da abata da kika sace zan
rufa maki asiri ba zan sanar da kowa ba bare a cire maki hannu". Yana maganar yana
kara matsawa kusa da ita.

Kara tsananta tsorata ta yi, a hankali ta fara ja da baya tana san matsawa daga
kusa da shi, dan yadda ya matsota ɗin nan kwarjininsa ya kara yi mata yawa. Sai dai
kuma dik in ta taka taku ɗaya ta matsa baya, shi kuma zai taka taku ɗaya ya matsa
kusa da ita, a haka suka rinƙa yin baya baya tana ce mashi ya yi hakuri ita wlh
bata yi mashi satar komai ba, shi kuma yana ce mata a'a bai yarda ba sai ta bashi
abarsa da ta sace kafin ta tafi.

A haka har suka kurewa bangon wajen, a ɗan tsorace ta juya taga sun isa wall glass
dake wajen rumfar, a tsorace ta juyo da nufin ta kallesa sai ta ga ya matsa dab da
ita sosai, har suna iya jiyo numfashin juna, ya kuma yi mata rumfa da faffaɗar
kirjinsa yana kallan face ɗinta. Lokaci guda ta ji ta yi nadamar fitowarta, gara
mata ɗakin mama ashe a kan wajen nan, dik sai ta shiga tashin hankali, a tinaninta
wani abin zai yi mata.

Narai narai da idanunta da suka ciko da kwallah ta yi zata yi mashi kuka, dik
zafinta dai shi ta kasa zazzaga mashi masifa ko ta faɗa mashi san ranta, ya yi mata
kwarjinin da ba zata iya yin hakan ba. Yana tsaye ya dafa hannunsa ɗaya a jikin
bango ta bayanta, ɗayan kuma yana rike da wayarsa yana kallnta.

Sai da ya ga hawayenta sun fara salwanta a banza suna bin saman kuncinta ne ya
ɗan waro idanu kaɗan, calmly ya furta. "Ashe haka kike da tsoro da saurin kuka?".
Ya yi maganar ba tare da ya zare kallansa daga kanta ba.

Cigaba ta yi da kukanta bata bashi amsa ba, dan bata da abin faɗe. Ɗan nisawa
ya yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi daga bakinsa, sannan ya ce. "To ai ke
bama ki tambayi abin da kika sace mun ɗinba da kika tsaya kina mun asarar
hawayenki".

Sai a lokacin ta ɗago manyan idanunta kaman na kawunta Sadiq, a cikin nasa
idanun ta sauke kallanta, lokaci guda sai ta ji kukan nata ya tsaya cak sakamakon
wani irin kallo da ya wurga mata mai narkar da zuciya, bata san time da ta shanye
kukan ba, sai ji ta yi hawayen sun dai'na zuba. Da sauri ta yi ƙasa da kanta, kun
dai san mu Nigerians da kunya kamar me muke.............🥱

Zira wayarsa a cikin aljihun wandan sleeping dress dake jikinsa ya yi, sannan
ya sanya hannunsa ya riƙo hannunta ɗaya, ƙasa ya yi da murya cikin wani irin salo
mai kwantar da hankali ya ce. "Malama wadda ban san sunanta ba, kuma ɓarauniyata
maza bani abata da kika sata, dan babu in da zaki je sai kin bani kayana". Yana
magana yana ɗaga gera guda kamar wani...................🤫

Muryarta na sarkafewa saboda kuka, ga wani shessheƙa da take yi, kun san
mutuniyar akwai zuciyata, so sai shessheƙa take yi alamar zuciyar tana a kusa, da
kyar ta ce. "Allah ni ban sace maka komai ba, dan Allah ka yi hakuri ka barni in ta
fi ciki". Ta yi maganar cike da san ta kwace hannunta daga rikon da ya yi mata,
saboda a takure take, bata saba ba.

Shi kuwa kara rikota da kyau ya yi, a karo na biyu ya sace cewa. "To ai baki ma
tambayi abin da kika sata mun ɗin ba"........ Kawar da kallanta daga kansa ta yi
tare da cewa. "Me na sace maka to?".
Ɗan rankwafo kanta kaɗan ya yi, dan ya fita tsawo sosai, a dai'dai saitin
kunnenta ya kawo ɗan bakinsa, kasa kamar mai raɗa ya ce. "Zuciyata kika sace mun,
kuma sai kin bani ita kafin ki tafi daga nan".

Abin ku da ita ba soyayya ta taɓa yi ba, hasalima kunga ta tsani maza, so bata san
komai ba, sai ta zaro idanu sosai, cike da ruɗani ta ce. "Zuciya kuma?". ......Kai
ya jinjina mata alamar e.
"Ta yaya ake satar zuciya kuma shi da yake cikin jikin mutum?". Ta yi maganar
tana dawo da kallonta a kansa...... Ya fahimci tabbas wannan yarinyar bata san me
soyayya ba, infact bama ta taɓa yin soyayya ba, ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba,
dan dama kun sansu da bala'in kishi, sun fi dik wasu nau'i na larabawa kishi, so
sai ya ji daɗin ya yi sa'a shi zai fara koya mata soyayya kuma ya aureta da wuri
dan ma kada wani ya ganta ya ce yana so.

Tab kuna ganin King zai aminta Dr Raj ya auri Zee kuwa? Kun dai san shi da
kabilanci ko? Ya aka yi na Mahnoor da Jaish ma? Kuma kun ji ya ce dikka ƴaƴansa a
cikin ƴaƴansu uncle Rahab zasu yi aure ko? To muje dai zuwa, zamu gani yadda
za'ayi.

"Kin taɓa yin soyayya?" Ya jefa mata tambayar cike da fargabar amsar da zata
bashi, dan in ta taɓa yin soyayya Allah zuciyarsa zata yi ciwo sosai saboda kishi,
dik da yana ganin alamar kamar bata taɓa yin soyayyar ba, amma dai gara ya tambaya
ya ƙara tabbatarwa. Sai harbawa zuciyarsa take yi kamar wanda zai shiga court kuma
yana sa ran hukuncin kisa za'a yanke mashi, dik saboda fargabar amsar da zata iya
fitowa daga bakinta ne fa.

Kai ta girgiza mashi kafin ta buɗi baki ta amsa da. "No, ban taɓa yi ba kuma
bana sha'awar in yi".................... Wani irin daɗi da ya lulluɓe zuciyarsa ne
har bai san time da ya ɗan matse hannunta da yake rike da shi a cikin nasa ba,
sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke a bayyane har sai da yasata kallansa a cikin ido.

Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, cikin salo mai tafiya da imani sosai ya ce.
"Har da ni baki sha'awar yin soyayya ko kuma ban da ni?". Ya kai karshen maganar
tare da ɗaga mata gera guda saboda yaga tana kallansa............... Ya
subhanallah, Zee bata san lokaci da ta kara waro idanunta haɗe da afkawa duniyar
tinani ba.
Hannunsa dake saman wall glass ɗin ya dawo da shi saman face ɗinta, a hankali
ya ɗan goge mata hawayen da ya yi saura a face ɗinta, wato Dr Raj ba iya Dr bane
kawai, shahararren ɗan love ne, kawai dama bai samu wadda ta sace zuciyarsa bane
yasa yake wani jiji da kai, yanzu ba ga shi ya yi la'asar har da rarrashi ba.

"Answer me mana, har da ni baki sha'awar yin soyayya?". Yadda ya yi mata
maganar cikin wani irin salo sai da yasa Zee ta yi saurin girgiza mashi kai alamar
a'a ban da shi, shi kam za'a iya yin soyayya da shi, bata san ta girgiza mashi kai
ɗin ba, kawai salon maganarsa cikin natsuwa mai kwantar da hankali yasa ta bashi
wannan amsa.

Wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa. Matsawa kusa da kunnenta sosai ya yi,
cikin raɗa yana rike da hannunta yana kuma kallan face ɗinta ya ce. "Kina so na?".
Ya yi maganar yana kashe mata idanu ɗaya yana ɗan canza yanayin face ɗinsa, dan
yana fargabar amsar da zata iya bashi, ba zai iya ɗaukar ta ce bata san shi ba, dik
da yasan mawuyacin abu ne ta ki yin accepting ɗinsa, dan jinin Akka fa sai dai mata
su kawo kansu garesu, basa tambayar soyayya su, a karon farko ya roki soyayya a
hannun ƴar Nigeria, yo to mu Nigerians dama wasa ne? Haba dole ka roki soyayya
malam Dr Raj, dan mu ɗin na daban ne malam.

Shiru Zee ta yi ta kasa magana, da alamu kamar suman tsaye ta yi, wato a
duniyar nan idan Allah ya kaddara ga mijinka fa shikenan babu wanda ya isa ya
canza, idan ba wata kaddara ta Ubangiji ba fisabilillah ina Zee ina Dr Raj? Mutanen
da ƙasa ba ɗaya ba, babu abin da ya haɗa, babu dangin iya bare na baba, kaddara
kawai ya kawo ƙasar, shi kansa Dr Raj kun san suna shafe shekaru 6 zuwa sama basu
leƙo kingdom of power ba, amma da Allah yasa dole a kaddararsa akwai haɗuwa da Zee
sai ga shi ya zo ta sanadiyyar ciwon guyson, wato komai yana da sanadi, jama'a
kawai ku bawa

Please Login or Register in order to submit comment