You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikinsa kenan yin aikin alkhairi, yana da tausayi da jin kan talaka, hakan
yasa ya kashe motar ya fito, a lokacin yarinyar ta shige cikin gida. A kofar gida
ya tsaya ya daka sallama cikin nitsuwa. Daga waje yana iya hango cikin gidan saboda
rurrujewat ginin, yanayin ginin ma ya ja hankalinsa ya ji yana san bin bayan
yarinyar.

A maimakon ya ga yarinyar ta fito sai yaga wata dattijuwa ta fito, cikin girmamawa
ya yi mata sannu tare da neman izinin yana san yin magana da mai gidan, a tinaninsa
mahaifin yarinyar kenan.

Babu wani ɓoye ɓoye ta sanar da shi babu wani mai gida a nan sai ita da
jikarta, kuma ba gidansu bane na hayane. Sosai ya ji tausayinsu ya kama shi, da
Allah yasa abincinsu na hannunsa sai yazamana sanadiyyar canzawar rayuwarsu, shi ya
sai masu wannan Daula da suke ciki a yanzu, ya canzawa yarinyar school izuwa
makaranta mai bala'in tsada na manyan kai, ya sanya masu tsaronsu da kyau, a yanzu
haka wajen motoci biyar ne suke jerin gwano idan zasu kaita school, rayuwarta
gabaɗaya ya canza tamkar ba su taɓa yin rayuwar ƙaskanci da wahala ba a baya.
Shiyasa idan ka yi hakuri ka miƙa lamuranka ga Allah sai ka huta wlh, dan Allah
idan ya tashi taimakonka ta in da baka yi zato ba zaka ga canjin da babu wanda ya
isa ya baka a duniya.

Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin waɗan nan bayin Allah. Time to time wannan
bawan Allah yana zuwa duba lafiyarsu, ba komai yasa hakan ba kuma face wannan
dattijuwa ta sanar da shi iyayen wannan matashiya sun rasu, marainiya ce, shi kuma
yana bala'in san ganin ya taimakawa marayu, yana jin ƙan marayu sosai, dik wani
abin da suke so ya sayi waya ya basu dan su rinƙa kiransa su sanar da shi, ba kuma
su kaɗai ya taɓa yi wa haka ba, shi ɗabiarsa ce taimakon mutane.

Yana da tarin makudan dukiya sosai, bashi da aiki sai duba marasa karfi yana
tallafa masu sosai, kullum kuma arzikinsa ƙara haɓaka yake ta ƙara yi. Yarinya ta
goge ta zama yar gayu, ga kyau ga ilimi, ga shagwaɓa da kyan diri, kamar ka taɓata
jini ya zuba.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Kwance take a saman wani bed round da shi haka, kamar pool haka bed ɗin yake, irin
rest bed ɗin nan ne wanda mattress ɗinsa yake can kasa haka. Ta tada kai da cinyar
dattijuwa, sanye take da ƙananun kaya na shan iska, rigar mai siririyar hannu ce
izuwa gwiwarta, sai dogon wando mai laushi, dattijuwa ta ɗaure mata gashin kanta
kashi biyu, bakinta sanye yake da wani irin lips balm mai shegen kyau da sheki. Sai
tashin daddaɗar kamshi take yi.

Fuskar nan tata tamkar zata saka kuka, ta shagwaɓesa sosai, tana turo baki ta ce.
"Ammo baby ya jima yanzu bai zo gidan nan ba, ya ɗauki lokaci sosai wannan karan,
ina kewarsa sosai wlh, ni kamar in je nemansa".

Tana da sanyayyar murya mai daɗin sauraro, akwai nitsuwa sosai a cikin kalamanta,
sai dai akwai shegen shagwaɓa kuma. Baby shi ne sunan da take kiran wannan bawan
Allah da ya taimaka masu, tun tana karama yake ce mata baby ita ma tana ce mashi,
so hakan tasa sunan ya zauna, a da idan tana kuka ne yake amfani da wannan suna
yana rarrashinta, har dai sunan ta zauna.
Shafa kanta Ammo dattijuwar kirki ta yi, cikin nuna tsantsar kulawa ta ce. "Ni
kai'na ina kewarsa, ban san me ya hana shi kawo mana ziyara ba, an ɗauki lokaci
gaskiya". Cike da tausayawa babyn ta yi magana, dan kuwa tasan yadda suka shaku
sosai, tin yarinyar tana karama bata da wajen wasa ko zama sai jikinsa, yana da
bala'in san yara kuma yana san ganin yana wasa da su.

"Ammo dan Allah mu kirasa a waya mana yau kam". Ta yi maganar tana miƙewa zaune.
"Jeki ɗakina sai ki ɗauko wayar ki kawo mu kirasa". Cewar dattijuwa.

Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyarta, har sai da ta saki ɗan siririn
murmushi wanda ya ƙara fito da kyanta. Da sauri ta fito daga cikin wajen, ta nufi
ɗakin kakar tata tana sakin murmushi. Da kallo Ammo ta bita tana tausaya mata.

Har zata shiga cikin ɗakin sai kuma ta tsaya cak, a hanzarce ta juyo da kallonta
baya, shiru ta ɗan tsaya kaman mai nazarin wani abin, kamar mai raɗa ta ce. "Baby
come out, I heard your breath, my heart beats with your name". Ta faɗa tana ɗan
tura baki.

Shiru bata ji alamar komai ba, ɗan motsawa ta yi kamar zata dawo baya, sai kuma ta
cigaba da tafiya tana faɗin. "Tsabar kewarka da nike yi ne ya ja nike jin zuciyata
tana bugawa da sunanka a kurkusa, ashe ba haka bane".

Tana ƙoƙarin tura kofar ɗakin kakar tata sai ta juyo da sauri. Tana juyowa suka yi
4 eyes da kyakkyawan face ɗinsa tana ɗan sakar mata siririn murmushi.

Tsayayyan cikakken namiji ne mai cikar surar mazanta, yana sanye da three-piece
suit launin ash colar, kyakkyawa ne sosai fari tas da shi, murmushinsa tana da
laushi mai kwantar da hankali haɗe da ƙayatarwa, idan ya yi maka shi sai ka ji
hankalinka ya kwanta.

"Baby waye ya ce ki juyo ne?". Ya faɗa murya a sanyayye ga zaƙi da daɗin
sauraro.

Idanunsa a kanta, kirjinsa sai da ya buga ganin irin shigar dake jikinta, gata
budurwa, komai a cike fam.

Turo baki ta yi, tamkar zata fashe da kuka ta ce. "Baby ina kaje kwana dayawa
baka zo ba?".

Nisawa ya yi, ɗan lumshe idanunsa ya yi. "Baby bana ce ki rinƙa sanya hijabi ba?".
Shiru ta yi tana kallansa. Gera ya ɗan ɗaga mata, hakan yasa ta yi saurin cewa. "To
ai a cikin gida nike yasa ban saka hijabin ba, amma yanzu zan je in saka".

Jinjina kai ya yi. "To jeki ki saka sai ki zo parlon in faɗa maki dalilina na
rashin zuwa kwana biyu". Da okey ta amsa mashi tare da shigewa ciki da sauri.
Bayanta ya bi da kallo yana ganin yadda take tafiya mazaunanta suna yi mashi
kwalele ta baya. Sai da ta shige cikin ɗakin shi kuma ya juya ya koma wajen Ammo
yana sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Bawan Allah yanzu ma daga gidan gajiyayyu marasa karfi ya fito, kayan tallafi ya je
ya kai masu. Yana da farar zuciya sosai fiye da tinaninku.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Saman sofa ya zauna yana fuskantar Ammo dake zaune saman nata sofan ita ma,
ganinsa ya zo gidan yasa ta dawo saman sofa ta zauna.

Cikin girmamawa ta ce mashi. "Ka ganta kuwa?".
Kai ya ɗan jinjina mata yana faɗin. "Ai da ban sanyata a idanu na ba ba zan
iya fitowa in dawo nan ba".

Murmushi Ammo ta saki tana mamakin irin shakuwar dake tsakaninsu, tana ganin
shakuwar ta yi yawa sosai, a ganinta basu kai ya yi masu irin wannan ba, sai ga shi
kuma ya shaku da su sosai haka.

Sallamarta ya katse su. Tin da ta shigo kallonsa a kanta, a saman sofar da yake
zaune ta zo ta zauna, cike da zumuɗi ta fara jero mashi tambayoyin meyasa ya kwana
biyu bai zo ba?.

"Sorry baby, aiki ne ya mun yawa, yau ɗin ma da kyar na samu lokaci na leƙo,
kuma yanzu ma ba jimawa zan yi ba, dan yanzu haka jirana ake yi, amma dai ki sani
koma menene kina rai'na a koma ina nike". Ya kai karshen maganar idanunsa a
kanta........

Zata yi mashi magana suka haɗa idanu da Ammo, girgiza mata kai Ammo ta yi dan tasan
abin da zata faɗa, gardama zata yi mashi a kan kada ya tafi, kuma Ammo ta hanata yi
mashi haka, ta hanata yin gardama da shi.

Shiru ta sunkuyar da kanta tana san yin magana amma ba dama. Ganin kamar taso yin
magana sai kuma ta yi shiru ne yasa ya saci kallan Ammo ta wutsiyar ido, dan yana
zargin ita ta hanata magana. Dai'dai lokacin Ammo ta miƙe haɗe da cewa bari ta zo.
Dabara ta yi zata basu waje, dan ta lura idan tana wajen bai cika yawan magana ba,
kamar tana takura masu. Wani lokaci idan baby tana faɗa mata irin hiran da suka yi
sai ta yi ta mamaki, a gabanta shiru shiru yake, ba dan tasan halin jikar tata baya
karya ba da sai ta karyatata. So a gaban Ammo baya magana sai ta basu baya ne yake
zuba hira da baby kamar ba gobe.

Aikuwa tana tafiya ya juyo suna fuskantar juna da ita, a nitse ya ce. "Faɗa mun
abin da kike san faɗa mun Ammo ta hanaki". Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Ammo
zata yi mun faɗa idan na faɗa maka".

Hannayenta ya riko cikin nasa da nufin ya yi mata dabara ta faɗa mashi, sai dai
kuma wani irin shock da ya ji har tsakiyar kansa ne yasa ya yi saurin sakin hannun
nata yana ɗan jan numfashi a hankali, yarasa me ya shiga tsakaninsa da ita, wata
ɗaya ne kawai bai kawo masu ziyara ba, amma kuma a wannan wata ɗayan kullun yana
cikin tunaninta, ga shi ya zo kuma ya kasa iya rike koda hannunta saɓanin da da
kullum suna manne da juna idan ya zo.

"Ba zan faɗawa Ammon kin faɗa mun ba ai, ni kaɗai zan ji, kin ga bata nan ai
ko?".

Kai ta gyaɗa mashi alamar e ...... "Good my baby, to faɗa mun menene?". Tsabar
shirinta sai da ta fara jujjuyawa wai dan taga da gaske Ammo bata yi masu laɓe ba,
kada ta jiyosu, sai kace akwai masu shigowa parlourn dama, ta wani tsaya tana waige
wiage. Binta da kallo kawai yake yi, idan tana wannan shirirtar tata ba ƙaramin
tafiya da tinaninsa take yi ba, yana jin daɗin ganin tana ire iren wannan abin.

Sai da tabbatar babu kowa, sannan ta yi ƙasa sosai da murya, kamar mai raɗa ta ce.
"Dama cema maka zan yi kada ka tafi, ni ban gaji da kallanka ba, kuma na yi kewarka
sosai"..................... Ajiyar zuciya ya sauke. "Ammo ta hanaki ce mun kada in
tafi ne idan na zo?". Ya jefa mata tambayar kallansa a kan yatsun hannunta da suke
dogaye kyawawa.

Kai ta gyaɗa mashi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa. "Ta ce in dai'na takura
maka ina maka kuka zaka dai'na sona, wai idan ina yi maka haka zaka dai'na zuwa ma,
zaka ce ina damunka". Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa da kwallah.

"Da gaske zaka dai'na zuwa idan ina cewa kada ka koma?"....... Girgiza mata kai
ya yi, a karo na biyu ya sake riƙe hannayenta, Allah sarki ya saba ne, wani irin
shock ya sake ji, hakan yasa ya yi saurin sakinta. Jingina kansa da jikin sofar ya
yi, ya fara mamakin wannan abin gaskiya.

"Kenan da gaske Ammo take yi zaka dai'na zuwa kuma zaka dai'na sona?". Muryarta
ta daki dodan kunnnesa, hakan yasa ya yi saurin dawo da kallansa a kanta. "Ko kusa
ko alama, hasalima daɗi nike ji idan kina ce mun kada in tafi".
Wani irin daɗi ta ji, har ta saki murmushi, zata sake yin magana Ammo ta shigo
hannunta rike da waya hakan yasa ta haɗiye maganar tare da dawo da kallanta a kan
Ammo ɗin.

"To tashi ki je uncle ɗin islamiya ya zo". Cewar Ammo kenan. Turo baki ta yi, sam
bata san rabuwa da shi, amma ba yadda ta iya, miƙewa ta yi yana turɓune fuska ta
ce. "Baby na tafi islamiyya". Kai kawai ya jinjina yana kallanta ba tare da ta yi
magana ba. Shigewa cikin ɗakin ta yi.

Waje Ammo ta samu saman sofa ta zauna idanunta a kansa, sai kallan baby yake yi har
ta shige ciki, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yana ƙoƙarin lumshe idanunsa muryar
Ammo ta katse shi da cewa. "Har yaushe zaka cigaba da ɓoye mata waye kai?".

Wannan kalma tasa ya fasa lumshe idanun nasa a in da ya sauke kallansa a kanta.
Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya amsa da. "Bansan har izuwa yaushe ba, abin
da kawai na sani shi ne ba yanzu zata san wanene ni ba, ni yanzu zan tafi saboda
ana jirana, kila in dawo da daddare, kila kuma sai gobe". Ya kai karshen maganar
tare da miƙewa tsaye.

Da kallo Ammo ta bishi tana mamakinsa, ta ƙasa amsa sallamar da yake yi mata, har
sai da ya fice sannan Ammo ta farga da ya tafi. TO FA WANENEN SHI KUMA?.

Yana fita ta fito sanye da hijabinta har ƙasa, hannunta rike da kyakkyawan jaka
mai ɗauke da litattafan addini da Alqur'ani mai girma. Sallama ta yi wa Ammo tare
da nufar waje.

Da kallo mai kama da kallan tausayi Ammo ta bita har ta fice. A tinaninta babyn
nata ya tafi, sai kumbura kumatu take yi tana ɓata rai ya isa wajen kyakkyawan
rumfar da suke karatu, already malam ya zo yana jiranta. A saman table dake wajen
ta ɗaura jakarta, saman chair ta zauna tana turo baki. Tin da ta shigo wajen malam
yake kallanta, yaga alamar kamar ranta a ɓace, bai iya hakura ba har sai da ya ce
baby yau lafiya kuwa?.

Babu komai ta amsa mashi da shi tare da janyo jakarta ta fito da Alqur'ani ta fara
buɗe in da zata bada hadda.

Shi kuwa yana zaune a cikin motarsa, tin da ta fito daga cikin gida ya kafeta da
idanu har ta isa wajen karatun nasu, ya kasa tada motar ya tafi, da alama maganar
da Ammo ta yi mashi ya taɓa zuciyarsa, kamar ya tado mashi da wani abin. Dik abin
da take yi yana kallanta, bai ta fi ba har sai da ta gama bayar da haddanta cikin
Suratul tauba, malam ya yi bismillah ya fara ƙara mata, dan ta kawo si dai'dai babu
tangarɗa.

Ya jima dai yana ganinsu kafin ya tashi motarsa da kyar ya tafi. Da yake baby
bata san da wace mota ya zo ba, hakan yasa bata fahimci hana nan ko ya tafi ba,
saboda dik motocin da suke parking space ɗin gidan nasa ne. Sai da ta ji tashin
mota a yanzu ne ta fahimci ashe yanzu zai tafi. Ta so ta sake ganinsa, amma ba
dama, tana ganin motarsa ya danna waje, shi ma ta cikin mirror yake ganinta har ya
fita. Yana fita ya kara gudun motar, a miliyan ya keta kan titi ya tafi.

Ita kuma ta cigaba da karatunta rai babu daɗi. Dik abin da yake faruwa Ammo tana
tsaye a gaban windown parlour dake fuskantar harabar gidan tana kallansu.


🔥🔥🔥🔥FOREST🔥🔥🔥🔥

Sun ci karfin dafiyar da suke yi, abu kaɗan ya yi masu saura su fita daga cikin
wannan dajin, sai dai yamma ta yi masu sosai, Hoorain ya fahimci dole sake kwana a
forest ɗin nan ya kamasu, dan haka tin kafin rana ya faɗi dare ya yi masu sai ya yi
saurin samun waje mai tsaro, mai ƙawa da ɗaukar hankali ya tsaya. Daga in da ya
dakata zuwa in da mammar Kamran take basu da nisa, kun tuna wajen zaman su Sweetie
na farko kafin Sadauki ya canza masu? To a arear wajen ya dakata ya fara ƙoƙarin
haɗa masu wajen da zasu kwana gobe da asuba su cigaba da tafiya.

Suna dakatawa Auta ta hau takura mashi da shagwaɓar yunwa take ji, hakuri ya bata
har sai da ya gyara masu in da zasu kwanta ba tare da wata matsala ba, saboda kada
duhu ya riskesa bai kammala ba. Waje mai kyau da haɗuwa ya gyara mata ita da Pretty
kafin ya fara tinanin im da zai samo masu abin da zasu ci.

Cike da mama Auta ta ce. "Kai kuma ina wajen kwananka my hero?".

Idanunsa a kan kyawawan hannayenta ya amsa mata da. "Ko lokacin da muke gida ma ai
bana da wajen kwana, kullun ina kasancewa ne a kusa da family part dan gadin abin
da zuciyata ke muradi".

Dik da tasan ita yake nufi, amma saboda ta ji ya furta ita ɗin da bakinsa yasa ta
ce. "Wacece kuma ko mecece kuma abin da zuciyarka take muradi?".

Sarai ya fahimci Zunaira a kullum tana san ganin yana nuna irin zallar son da yake
yi mata, hakan yasa take san jefa mashi ire iren waɗan nan tambayoyi. Allah sarki
tana san taga yana nuna yana santa tare da yi mata kalamai masu zafi.

"Wata ce wadda zuciyata ke kauna". Ya bata amsa cike da tsoron abin da amsar zai
haifar, dan yasan halin kayassa.

"Ban gane wata ba! Wakenan?". Ta yi maganar tana ɗan ɗaure fuska.

"Wata kyakkyawa mai kyan fuska dake ɗauke da lallausan murmushi mai kwantar da
hankalin assistant commander, murmushinta yana sakani manta in da nike, murmushinta
yana sawa in ji kamar an bani kyautar gida a aljanna, tauraruwar zuciyata wanda
haskenta ya haske kirjina dikka, shekin haskenta ya wuci tinaninki, tin daga nesa
idan ta doso haskenta yake disashe hasken dikkan wasu halittu dake gefenta,
tauraruwar da bana jin za'a samu irinta".

Tin da ya fara waɗan nan zafafan kalaman ta tsaresa da idanu tana kallan kyawawan
lips ɗinsa yadda yake ɗan motsasu, yana magana one by one, bata san tana sakin cool
murmushi ba ma, ta nitsu tana jin ta a wani duniya da babu hayaniya babu wata yana
da zata yi mata tsakani da farinciki. Haƙiƙa akwai tsananin daɗi masoyi ya aika
saƙon kalamai ga zuciyar da yasan tana matsanancin kausarsa, tabbas zai ɗarsa
bishiyar yarda da kauna mai zafi da bata da iyaka a wannan zuciya.

Ganin tana zuba sanyayyar murmushi ba tare da tasan tana yi bane yasa bai san
lokacin da ya kashe mata ido ɗaya ba. Sai ganinta ya yi ta ɗan zaro idanu tana ɗage
mashi gera ta kuma faɗaɗa murmushinta.

"Murmushinki abin so ne har ga makiyanki gimbiyata, dik wanda baya san murmushi
tabbas bai ga naki bane sarauniya............".

Katse shi ta yi da cewa. "A fadar birnin zuciyar my Hero" . Wato sarauniya a fadar
birnin zuciyarsa kenan, ta ƙarisar mashi da maganar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin sanyi tana ratsa zuciyarsa.

"My Hero kasan me?". Cike da farinciki ta yi maganar. Kai ya girgiza mata alamar
a'a ba tare da ya yi magana ba. "Kalli cikin idanuna bari mu yi magana". Ta faɗa
tana kallansa.

Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "A'a ba zan iya kallan cikin idanunki ba". In
a silent talk mai kama da raɗa ta furta. "Why?".

Ƙasa sosai shi ma ya yi da murya kafin ya amsa da. "Saboda sirrikan da kyawawan
idanunki suke ɗauke da su zasu sa zuciyata ta kasa iya shanyewa, ba zan iya ɗauka
ba"................. Pretty dai kallansu kawai take yi, yo ita da bata ma gane me
suke faɗe, ai gani take yi wani sabon haukan ne suke yi.

"Kai da kake matsayin jarumi, namijin gaske, sadaukin da dauloli suke tsoron jin
an ambaci sunansa a cikin mayakan da zasu kai masu hari, sadaukin da ya ciri tuta
ya kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinta ba a kaf faɗin kingdom of power, sadaukin
da sunansa ke firgita manyan maza yasa hantar cikinsu ta kaɗa, kai fa assistant
commander ne na gabaɗaya dangerous warriors, shi ne zaka ce kana jin tsoron kallan
cikin kwayar idanu na? Meyasa?". Cike da kwarin gwiwa ta yi maganar.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ranki ya daɗe dik ajiye wannan a gefe, mata suna da
kwarjinin da dik wani girman namiji da ji da kansa yana jin shakkarsu, ga su dai
sune ƙasa da mu, amma Allah ya basu wannan dama a kanmu, wlh wannan gaskiya nike
faɗa maki, dik namiji yana jin shakkar mace, sai dai ya danne kawai, dik bama
wannan ba".............. Ƙasa sosai ya yi da murya kamar sillent talk, sannan ya
cigaba da cewa.

"Ke idanunki daban suke da kowace mace, tsoron ganin cikinsu nike ji
kada ki hanani yin barci yau". Cikin nitsuwa ya yi maganar................Siririn
murmushi ta sakar mashi. "Zan iya samun sunan love apart from ranki ya daɗe?".

Unexpect garin amsa mata idanunsa suka sauka a cikin nata. Wani irin azabbabben
shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafin ƙafarsa dake cikin takalmarsu
na mayaƙa. Cikin sauri ya zare idanunsa unexpext ya sake sauke kallansa a saman
kyawawan laɓɓanta da ta ɗan ciza na kasan kaɗan hakan yasa ya kara pink sosai.

Oh god, zuciyar maza ne ta amsa, nan take ya ji shi a matse kamar yana ƙoƙarin
shiga out of control, wani irin jan numfashi ya yi mai cike da fassarori dayawa.
Ƙasa iya amsa mata ya yi, sai ya ji gabaɗaya kamar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa.

"My Hero lafiya?". Ta yi mashi tambayar bisa famintar da ta yi na ya shiga wani
hali. Nisawa ya yi kafin da kyar ya iya buɗan baki yana ɗan girgiza kai ya ce.
"Babu komai Hoonaira". ......... Hoonaira ta maimaita sunan tana kallansa, har
cikin ranta ta ji wannan lallausan suna mai daɗin ambato, sai ma da ya faɗa da
bakinsa ne ta ji wani irin daɗi na daban. HOORAIN AND ZUNAIRA SHI NE YA BADA
HOONAIRA LIKE WOW, ABIN YA ƘAYATAR.

"Zan iya tafiya in je in samawa gimbiyata abin da zata ci?". Ya jefa mata tambayar
yana kallan gefenta a zahiri, amma a bayan fage face ɗinta yake kallah.

"Ni dai a'a ban yarda ba, ni sai ka kalli cikin idanuna sannan zaka tafi, idan
ba haka ba ni bazan ci abinci ba". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

Ɗan jinjina kai kawai ya yi, shagwaɓaɓɓiyar nan tasa tana san ɓallo mashi
ruwa ne yana zaman lafiyansa. "So kike yau ki hanani barci ko?"........... Kai ta
ɗan girgiza mashi. "Zaka yi barci In Sha Allah in dai muna tare".

"To amin afuwa na je na kawo wa sarauniyata abincin dai tukun nan, idan na dawo
sai ki tsareni ki sakani yin dik abin da kike so"........ Jin in ya dawo ta saka
shi yin dik abin da yake so yasa ta aminta da ya je to. Cikin zafa ya wuce yana
taku cike da jarumta.

Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta riko hannun Pretty suka
zauna a wajen da ya tanada masu, cike da tsananin kaunarsa ta fara bawa Pretty
labarin irin tsantsar madarar san da take yi mashi.

Shi kuwa neman masu abin da zasu ci ya tafiyi dokinsa na biye da shi a baya.
Dai'dai zai gifta tsakanin wasu dogayen bishiyoyi ya hango kamar mutun kuma mace
tana ƙoƙarin jan abu a kwando. Da yake yana da zuciya mai kyau sai ya nufeta domin
ya taimaka mata.

Ba kowa bace face mammar Kamran, ta ɗebo kayan lambunta dayawa a cikin irin wannan
kwando da Kamran yake ɗebo mata ɗin, kwandon yana da girma sosai hakan yasa take
jansa da kyar, dan ya yi mata nauyi. Allah sarki Kamran mai yi mata hidimar baya
nan, daga ganinta bata da ƙoshin lafiya, da alama tsananin damuwan rashin Kamran ya
haifar mata da ciwo, ta yi rama sosai tamkar ba ita ba, shiyasa ma ta kasa iya
ɗaukar wannan kwando, jikinta har wani kerma yake yi.

Taimaka mata ya yi ya ɗauka mata suka haura saman tsauninsu, kun san Mamma bata
yarda da baki, dan haka shi ma bata aminta da shi ba, sai dai shi ko da ya nufota
bai yi mata magana ba, kwandon kawai ya ɗauka mata da hannu ɗaya ya haurar mata
sama, a bakin kofar kogonsu ya ajiye mata ya juya ya sauka, bai yi mata magana ba
ya wuce abinsa.

Dik yadda bata san mutane yau karo na farko da aka taimaka mata ta ɗan ji a ranta
ashe ba dikka mutane bane na banza, ashe akwai na kirki? Ashe akwai masu taimako?
Bata taɓa zatan akwai wanda zai iya taimaka mata ba a rayuwarta, Allah mai iko, yau
ta ga sabon abu.

Shi kuwa yana sauka ya bazama nemanwa gimbiyarsa abinci, bai dawo ba sai da duhu ta
fara yi, sannan ne ya dawo ɗauke da kala kalan kayan cima da za'a iya samu a wannan
dajin. A lokacin Pretty da Auta sun yi alwala sun yi sallah suna zaune a waje guda
suna hira.

Suna ganinsa suka miƙe, a gabansu ya dire masu kayan da ya kawo masu, Auta ce
ta kallesa cikin ido. "My Hero muna godiya da kulawan da kake bamu, Allah ya barmun
kai ya kare mun

Please Login or Register in order to submit comment