You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma ta shiga cikin gonarsa ta sanya
shi tashi, dan dik wasu alamu na wanda ya kwanta zai yi barci ta bayyana a tattare
da shi.

Idanunsa suna ɗan lumshe alamar yana jin barci, kwayar idanunsa sun kara tsananta
olive green sosai, sai shining suke yi, haka zalika ita ma olive green eyes ɗinta
sun kara tsananta kala saboda ɗan duhun dake wajen.

Farincikin idanunsa dama idan baku manta ba milk color ne ba fari tas ba, so yanzu
ya yi jajir sosai. My people's Black Tiger karshe ne a kyau wlh, dik wasu cikar
kyau na ɗan adam ya haɗesu sai rashin mutunci cike a kai.

Kafafunsa na sanye da sps, hakan yasa baka iya ganinsu.

Ganin shi ne ya bayyana yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, wato ita fa Sweetie
wlh ko kaɗan bata jin tsoronsa, in short soma take ta ga bayyanarsa a
waje,..........😂


Yanzu da ta ga shi ne har ta ji sanyin ruwan da take ciki ya ragu. Idanunsa a kanta
babu ko kyaftawa, ita ma kura mashi kallo ta yi, suka ga juna ido cikin ido like
wow, ga idanun nasu kalar iri ɗaya sak, sai abin ya bada wani citta.

In a low cool voice sosai ya furta.

"Where is Spender? Live or die!". Lion voice ɗinsa ya daki dodan kunnenta ba tare
da ya buɗi baki ya yi magana ba, abin yana bata mamaki yadda baya buɗe baki kuma
muryarsa take fita har ta furta words.
Wani irin kallo ta yi mashi mai kama da harara kafin ta ce. "What's
Spender?".................... Ko shakka babu ta yi maganar!.

Tashin hankali. Gaskiya Sweetie ƴar yi ce ita ma!.

Jiji da kansa ne ta motsa, dan shi baya bada gurbin wasa a lamuransa, wato
Sweetie bata ji tsoron in da take bama tukun nan ko?.

Da hannunsa ya nunata nan take ta fara nutsuwa kasan wannan tekun. Zaro idanu ta yi
haɗe da fara ƙoƙarin yadda zata kwaci kanta.

Amma ina ta kasa, tana ji tana gani ta nitse can ƙasa. Wasu irin macizan ruwa ta
fara gani a kasan masu kai irin siffar na mutane, abin tsoro, ba halin yin ihu, sai
ma ɗirkar ruwa da take yi.

Wintsila kafafunta ta fara yi gwanin ban tausayi, ga ruwa tana ɗirka, shi kuwa yana
ganinta a kasar ruwan with his magic eyes.

Tana ji tana gani kamar zata mutu haka waɗan nan macizan suka zo suka mannewa
jikinta, sai dai basu cijeta ba, babu yadda zata yi, sai wiwwintsila kafafu da
hannaye take yi, ji take yi kamar ma an shaketa a cikin ruwan ne, yadda take shan
ruwan sai ta baka tausayi.

Yana ganinta har sai da ya ga ta sha ruwa sosai, kamar zata mutu, idanunta sun yi
jajir kamar wuta, ta wahala iya wahala, ta ji kamshin mutuwa, sannan ne ya ɗago da
ita saman ruwan.

Haba tana yin sama ta fara tari kamar zata mutu, ga macizan dake manne da jikinta
tsoronsu take ji kamar ta mutu, amma ba halin ta gudu ko ta rabasu da jikinta,
yanzu ta numfashinta ma take yi, tana ƙoƙarin dai'dai ta shi!.

A karo na biyu ta sake jin Lion voice ɗinsa unexpext a kunnenta yana sake jefa
mata tambayar ina Spender?.

Cak ta dakata da kakarin da take yi kamar zata yi amai. A hankali ta ɗago da
rinannun jajayen idanunta a kansa. Kamar zata yi kuka ta ɗan tsuke fuska, yana
kallonta sosai a cikin ido.

Ɗaure fuska sosai ta yi kamar bata san menene dariya ba, sak irin yadda ya wani
uban ɗaure fuska, wani irin harara ta dalla mashi ko tsoro babu, a karo na biyu ta
sake cewa.

"What's Spender?" Babbar magana!.

Ta yi maganar ne a kule, wato idan zai kasheta ma gara ya kasheta ba faɗa mashi in
da Spender yake zata yi ba.

Hannunsa ya sake saitata da shi da nufin ya sake mayar da ita kasar ruwan dan
mugunta, ko tausayi bata bashi ba, ko da yake shi wannan mai bakar zuciyar ina ya
san wani abu wai shi tausayi? Ai bai santa ba.

A hanzarce ta sanya hannunta irin mutum ya tare fuskarsa ɗin nan, haka ta yi saboda
tana tsoron komawa cikin ruwan, kuma bata jin komai azabar da zai gana mata zata
iya bashi Spender, sai dai ya kasheta amma wlh ba zata bayar ba!.

Tana sanya hannunta unexpect magic ɗinta ya fita, ga shi suna saiti da juna, kai
tsaye sai kan saitin zuciyarsa magic ɗin nata ya dakesa.
Da yake unexpect ne abin hakan ya haifar mashi da jijjiga mai karfin gaske, wani
irin jiri ne ya kwashesa ba zato ya afaka da karfi cikin ruwan tekun shi ma, dab
kusa da ita ya faɗa.

Ba ƙaramin razana ta yi ba na ganin irin jijjigar da ya yi kafin ya faɗo cikin
ruwan, ga shi kuma ya faɗo kusa da ita.

Wani irin tsoro ne ya lulluɓeta, sai ta kasa juyowa ta kalli in da yake. Shi kuma
miƙewa tsaye a kan kafafunsa ya yi a cikin ruwan bayan faɗawarsa kenan.

Sai da ya ji a jikinsa lokacin da ruwan sanyin nan ta ratsa jikinsa, ashe babu daɗi
ya jefata cikin ruwan sanyin, dik jikinsa sai da ta amsa har ƙashi da ɓargo.

Idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, nan take Black heart ɗinsa ta matso kusa, a
fusace ya juyo gareta.

Wannan juyowa da ya yi sai da gashin kansa ya pyaɗe mata rugun wuyarta, sannan ya
watsa mata ruwan da ya tattaro daga gashin nata a saman face ɗinta.

Hannu tasa dan ta sharce ruwan da ya watsa mata ɗin. Kamar daga sama ta ji
saukar hannunsa a bayan wuyarta. Da karfi ya damketa.

Babu tausayi babu imani ya danna kanta a cikin ruwan nan, da alama kasheta yake da
niya.

Buga buga ta fara yi tana shan ruwa.

Azaba da ya ratsata bata san lokacin da ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ba, ƙoƙarin
juyowa garesa ta fara yi, ko kaɗan ta kasa iya motsa shi, fafutuka ta fara yi da
hannunta tana neman abin da zata kama dan ta cece ranta, ta ji azaba ƴar kaniya,
har ta ji a ranta Spender banza zata iya bashi a yanzu kam, saboda taga alamar
mutuwa.

Unexpect hannunta ya kai kan heronsa (bananarsa) saboda tana neman abin kamawa sai
kawai ta capkoshi da karfi.

Ai bai san lokacin da a miliyan ya saketa ba, har baya kaɗan ya yi, ya ji abin
da bai taɓa tsammanin zai ji ba a rayuwarsa, dan ma Allah yasa a cikin ruwa suke.

Sweetie akwai zuciya, ko da yake haka twins or triplets or quadruple suke, abin a
jininsu yake.

Yana saketa ta ɗago kanta da karfi, wani irin numfashi da ta ja da karfi sai ta
baka tausayi, da karfi ta fara layi a cikin ruwar kamar wadda ta sha wine ta bugu,
neman in da zata tsaya domin ta samu numfashinta ya dawo daidai take yi.

Tana tsaka da juyi a cikin ruwan ta matso kusa da shi, dama in baku manta ba ai
ya ɗan ja baya kaɗan.

Tana matsowa kusa da shi, idanunta a datse kam, jin alamar abu yasa ta sanya hannun
bibbiyu ta riko shi tana wani irin numfashi mai ban tausayi, da alama ta fita
hayyacinta sosai, shiyasa ma bata ji abin da ta kama da farko ba!.

Kirjinsa ta kama a yanzu kuma, hakan yasa ta ji kamar dutse ta kama, saboda a
dake yake sosai. Da hannunta dikka biyu ta dafa kirjin nasa tana ƙoƙarin fara
kwararo amai na uban ruwan da ta sha.

Shi kuwa tun da ya koma baya ya datse idanunsa gam, ko me yake tunawa? Kamar dai
abin ya yi mugun baƙanta mashi rai ne!.
After some minutes.......... Suna tsaye haka. A hankali ta fara dawowa cikin
hayyacinta.

Idanunta ta fara kokarin warowa waje dan ta ga ina yake? Yanzu kam ta iya tuna in
sa take.

Tana buɗe ido sai a kansa, yana tsaye idanunsa a datse kam kamar wanda ruwa ya
cisa.

Wani irin karfinta dikka ta tattaro, da karfi ta danna hannunta dake dafe da
kirjinsa, dagewa ta yi harda ciza laɓɓanta da karfi, wureshi ta yi a cewarta ta
samu hanya ta fita.

Sai dai kash, ko motsawa bai yi ba, kamar dutse mai girman gaske ta yi yunkurin
turewa, ko gezau bai yi ba.

Ransa ne ya kara ɓaci, da karfi ya waro idanunsa waje, idanunsa sun juya izuwa
magic eyes.

A maimakon ya bawa Sweetie tsoro sai ma kafe shi da kallo ta yi, dan ita magic eyes
ɗin nasa ma kyau suke yi mata........... Trust me Sweetie ƴar duniya ce, ƴar ikka
ce, wai magic eyes ɗinsa suna yi mata kyau, kai wannan yarinya tana goge mun hadda.

Kamar walkiya haka ya yi amfani da magic ɗinsa ya janyeta baya nesa daga kusa da
shi. Ganin ya buɗe hannunsa ya janyeta baya yasa ita ma ta tuna a ranta cewa bari
ta gwada buɗe hannunta taga me zai faru tun da ranar taga ta buɗe hannu ta iya
sarrafa chandelier.

Tana buɗewa magic ɗinta ya fita, da karfi magic ɗinta ya janyo shi kusa da ita,
suka sake haɗewa kamar chewing gum, har sai da kanta ya bugi kirjinsa. Yau Black
Tiger ya haɗu da ƴar bala'i dai'dai da shi!.

Magana ta gaskiya ya fi Sweetie karfin magic, yana dannewa baya san kashetan ne
kawai, yasan idan zai kara karfin magic ɗinsa ya fi yadda yake a yanzu yana yin
amfani da shi sau ɗaya a kanta zata rasa ranta, baya san ta mutu, saboda yana da
buƙatar Spender a hannunta ta kowace hali ne, ita kaɗai ce kuma yanzu a duniya
tasan in da yake, kunga dole ya danne.

Ita kuma Sweetie dama bata tsoronsa sosai, sai kuma Ronnie ya ce mata yayansa ba
zai taɓa kasheta ba har sai ta bashi Spender, sai dai ta sha wahala a hannunsa, dik
ranar da ta bashi Spender to ta sani tana yi mashi abu kaɗan zata mutu. Jin ba zai
kasheta bane yasa ta kara samun kwarin gwiwa haɗe da kara rage tsoronsa da take ji,
shiyasa zaku ga tana yi mashi wasu abubuwa bata nuna tsoronsa.

Wannan shi ne dalilan da yasa kuke ganin in sun haɗu kamar magic nata ya fi
nasa, kuga kuma kamar bata jin tsoronsa, to ba haka bane, kun ji dalilan.

Ƙoƙarin danne Black heart ɗinsa ya fara yi dan kada ya kasheta, ita kuma ture shi
daga kusa da ita ta fara ƙoƙarin yi.

Hakan ya kona ransa matuƙa, har da sanya hannunta bibbiyu zata ture shi. Cikin
fusata ya capko wuyarta ta gaba da hannunsa ɗaya. Da karfi ya shaketa har sai da ba
shiri tongue ɗinta ya yo waje.

Zaro mata dara daran idanunsa ya yi ba shiri ta lumshe nata idanun, saboda
kaifin idanunsa ya ratsata har sai da ta ji kamar an tsira mata allura a jikinta.

Hannunta ta ɗaura a saman nasa tana son ya sake mata wuya. Tin da Allah ya
haliccita a duniya bata taɓa jin hannu mai laushin nasa ba, she has a very very
smooth and soft skin, ko da yake baya fita rana ai dole dama skin ɗinsa ta yi haka.

Sai dai akwai yawan jijiyoyi a hannun nasa sosai, gasu ɓaro ɓaro. Bubbuga
hannunsa da karfi ta fara yi tana neman agaji.

Kada ku manta basu nitse kasan ruwan bane saboda magic ɗinsa, shiyasa suke a
sama.

Azaba ne ya yi azaba kuma taga bashi da miyar sake mata wuya. A hankali ta sauke
hannayenta kasa daga saman nasa, jikinta ne ya fara sakewa alamar rai ya yi
halinsa.

Sake hannunta da ta yi ya ja magic nata ya fara nitsar da su kasar ruwan.

Yana rike da wuyarta unexpect ya ga sun fara nitsewa kasan ruwa, ko kaɗan bai damu
ba, da alama ɓacin rai yasa ya fita a hayyacinsa, ya manta ita kaɗai tasan in da
Spender yake ga shi ya kasheta bai ankara ba. Zuciya ta ja mashi.

Har sai da suka ka kai kasan wannan tekun ne ya farga da in da suke da kuma ta
mutu.

A hankali ya zame hannunsa daga wuyar tata.

Sulalewa ta yi ta kwanta a kasan wannan ruwa ta zama gawa.

Ransa a tsananin ɓace, yana ta huci mai zafi ya yi amfani da magic ya dawo da su
saman ruwan. Da hannu ɗaya yasa ya saɓi gawarta a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa
ya fito daga cikin ruwan. Idanunsa a datse ya tsaya a bakin ruwan, ko kaɗan bai yi
nadamar abin da ya aikata ba. Cikin kungurmin dajin ya kutsa da ita, yana taku
cikin zafa, daga shi har ita jikinsu na ɗigar da ruwa!.

To ina kuma zai kai gawarta? Me kuke tunanin zai faru?.

=========================🔥

•••••••••••••••FOREST••••••••••••••🔥

Zaune take saman wani dutse wanda ruwa yake ɓulɓula daga kasansa, daga gaba kaɗan
tabkeken kogi ne a wajen, ita kaɗai take zaune kamar marainiya, tana sanye da kusan
irin kayan da suka rabu da Sweetie a wannan rana da damusa ta far masu, sai dai
wannan kayan milk color ne.

Ta yi shiru haɗe da buga uban tagumi, kamar dai akwai abin da take tunawa. Allah
sarki har ta rame, Sweetie ta matsa mata akan ƴar dumurkurewa da ta yi a lokarin da
suke a tare, har tana gayawa Kamran cewa Pretty ta fita kiɓa saboda ta fita cin
abinci.

To yau ina Sweetie take? Ta zo taga Pretty ta yi rama sosai, ta canza kamar ba ita
ba, wuyarta sai layin guru zaa gani alamar tsokar nama ya taɓa taruwa a wajen.

Kan nan nata ba ɗan'kwali, gashinta a watse, ko gatan tarawa a ɗaure bai samu ba,
dama Sweetie take ɗaure mata, to yanzu Sweetie bata nan babu mai yi mata, ita kuma
bata iya ba, sai ta barshi a watse har gadon bayanta, dik ya yi datti ma bata wanke
ba.

A hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa a jikinta, tsabar ta yi nisa cikin
duniyar tunanin da take yi ma bata ji alamar ruwan saman ba.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




A hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa a jikinta, tsabar ta yi nisa cikin
duniyar tunanin da take yi ma bata ji alamar ruwan saman ba.

Wani irin narkakken hadari bakinkirin ne yake tasowa a gajimare, sai walkiya da
tsawa ake yi, amma tamkar sassaka Pretty aka yi a wannan waje, sam bata motsa daga
in da take ba.

Lokacin guda ruwa ta barke kamar da bakin kwarya, amma Pretty tana zaune shiru,
kamar wadda babu rai a tattare da ita.

Allah sarki abar tausayi, ga rashin uwa, ga rashin madogara, yanzu kuma ga rashin
ƴar uwa, babu Kamran, abin ya yi wa kakanun shekarunta yawa wlh.

Tun farkon ruwan saman nan har karshensa a kanta ya kare, daga karshe ma haɗe
kai da gwiwonta ta yi tana ruwan hawaye sosai. Ruwa sai dukanta yake yi.

Har ruwar ta dakata Pretty bata da niyar motsawa daga in sa take zaune, yadda kuka
san ba mutum bace. Ko ɗago kanta taki ta yi.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Omnish". Daga bayanta ta ji wata murya an furta hakan.
Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta ɗago kai tare da juyowa ga muryar.
Idanunta sun yi jajir kamar wuta saboda kuka ga ruwan da ya dakata.

Yana tsaye cikin wannan shiga tasa ta kullum, face ɗinsa a rufe da hular mayaƙa,
tsayuwa cikin jarumta da nuna cikar zarra, ya ɗaura hannunsa ɗaya saman tabkekiyar
takobin dake manne a waist ɗinsa, jikinsa dik yayyafin ruwan sama.

Tana ɗaura idanunta a kansa ta yi maza ta miƙe tsaye, sai a lokacin ta fara
jin sanyin ruwan saman da ya jiƙata, takure jikinta waje guda ta yi, fuskarta
gwanin ban tausayi, idanu cike tab da ruwan hawaye, ta kasa yin magana sai dai ido
take binsa da shi.

Cikin harshen tsabtataccen larabcinsa, ga nitsuwa da kamala a tattare da voice
ɗin, kamar baya san yin magana ya ce.

"Omnish meya tsayar dake cikin ruwan nan haka?".

Tamkar jira take yi a yi mata magana, ai sai kawai ta fashe da kuka mai ɗan sauti.

Cikin jarumta da zafa ya tako ya matso kusa da ita, ɗan rungumota kaɗan ya yi a
jegen takobin dake waist ɗinsa, ya fara bubbuga bayanta alamar rarrashi.

Yadda suke tsaye a wajen sai sun yi maku wani iri idan kuka gansu, in baku manta ba
na ce maku wannan sadauki idanunsa iri ɗaya da Pretty, kamar an tsaga kara, dik da
fuskarsa a rufe take, in kaga idanunsa da nata sai ka yi zaton kanwarsa ce ita ko
yarsa dik da bamu san babban mutum ne ko yaro ba, tin da bamu taɓa ganin face ɗinsa
ba.

Hannunsa dake cikin wani irin hands gloves mai karfi ya ɗaura saman lallausan
kumatunta yana goge mata hawaye, tamkar kara ingizasu yake yi, yana gogewa wasu
suna fasowa.

Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna, ya ɗan rage tsawonsa dan ya dai'daita
kansa da tata.

"Omnish menene ya faru kuma? Kin manta jiya kin mun alkawarin ba zaki sake yin
kuka bane?".

Shiru bata amsa mashi ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin.

"Omnish ya isa haka kukan, yi shiru ki faɗa mun me ya sameki kuma?".

Still shiru bata amsa mashi ba. Dik sai ya ji babu daɗi, ga dikkan alamu ya ji
jikinsa ya yi mugun sanyi, da alama tausayinta ya kara ratsa heart ɗinsa ne.

"Yau kuma ba za'ayi magana dani bane Omnish?".
Cike da tausayawa ya yi maganar, yana jin tausayinta matuƙa.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a, a take ta tsuke fuska zata fara yi mashi shagwaɓar
da ta saba, ashe dai har yanzu halin nan nata na shagwaɓa yana nan.

Cigaba da goge mata hawaye ya yi yana kara rarrashinta. Da kyar ya samu ta yi
shiru, amma taki ta yi mashi magana. Hakan yasa ya miƙe tsawonsa ya riko hannunta
suka kutsa cikin daji a tare yana mai kara rarrashinta.

Wanenen kuke tunani zai kasance wannan sadaukin? Meyasa kuma sai dai ya taimaka
masu a daji ba zai ɗaukesu ya fitar da su ya kaisu cikin gari ba? Meyasa baya san
su bar wannan dajin? Menene alakarshi da su? Ina mom ɗinsu? Ina ne tushensu? Ina
dad ɗinsu?.
Dik cikin nutswa amsoshinku zasu bayyana, yanzu dai muje zuwa!!.

•••••••••KINGDOM OF POWER••••••••🔥

Sai misalin karfe 1 da rabi na dare aka tashi taron dinner. Har lokacin guyson bai
rintsa ba, yana ta bin part part na kowa yana neman Auta.

Daga karshe ya dawo ɗakin momma dan ya ɗauki wayarsa ya kira numberta, a lokacin
momma tana sallah, wayar kawai ya ɗauka ya fito waje.

Ya kirata ya fi miss call talatin, amma ina bata ɗauka na.

Idanun Hoorain biyu bai rintsa ba, yana ganin call ɗin guyson amma bai ɗauka ba, ya
kasa iya yin barci, yana zaune saman bed ɗinsa kamar mai nazarin wani abin,
gabaɗaya ji yake kamar jikinsa ba mallakinsa bane ba.

Idan hankalin guyson ya kai miliyan to fa ya tashi a wannan dare, ya shiga
damuwa na wuce misali.

Baya shiri da Mammiensu Sarina amma a cikin wannan dare sai da ya je part ɗinsu ya
buga mata kofa, dan dole yasa ta fito ya tambayeta Auta, ta ce mashi bata a part
ɗin nan, hankalinsa ne ya kara ɗugunzuma ya tashi.

Wajen mommarsa ya dawo dan ya sanar da ita, tana sallah har lokacin, dan haka sai
ya samu waje saman bakin bed ya zauna yana jiranta.

Ita kanta ganin shege da fice da yake yi mata a ɗaki yasa ta ji ta kagu da ta
sallame sallar dan ta ji me damuwarsa da yasa bai yi barci ba har karfe ɗaya da
rabi.

A ɓangaren ƴan dinner kuwa, Fanan ta ja hannun Chuchu a kan ta zo su wuce wannan
ɗaki da yake mallakin amare dan gyarasu, a ka'ida amarya ba zata fita daga cikin
wannan ɗaki ba har sai lokacin da za'a kaita ɗakin mijinta, ko dinner aka je nan
zata dawo.

So ana tashi Fanan ta kama hannunta a kan su tafi can.

Wani irin hararar da Jawad ya wurga mata ne yasa Fanan ta yi gaggawar sakin hannun
nata tana ɗan sunkuyar da kai.

Abdussalam yana ganinsu dik abin da suke yi, dariya suka so ɗan bashi, wato dai
Jawad rashin kunyarsa a fili zai nuna? Abdussalam ya tambayi kansa yana kunshe
murmushi.

Ita kuwa Fanan kasa ta ɗan yi da kai tare da cewa. "Yah Jawad zamu koma ciki ne
fa!".

Tamkar bai ji me ta ce ba ya yi shiru yana kallon Chuchu dake tsaye kusa da shi.

A karo na biyu Fanan ta sake maimaita mashi abin da ta faɗa ɗazun.

Kallo mai kama da harara ya wurga mata, cikin sanyin murya ya ce. "Ke kika kawo mun
ita ne dama?".

Kamar zata gyaɗa mashi kai alamar e, saboda ita ta kawota kam, amma sai taga rashin
dacewar ta yi mashi hakan tun da yayanta ne, kuma tana tsoron ya hukuntata, dan
haka sai ta girgiza mashi kai alamar a'a ba ita ta kawo ta ba.
Hannu yasa ya nuna mata hanya. "Jeki zan dawo da ita da kaina".........Ya faɗa
idanunsa a kan Chuchu da ta sunkuyar da kai tamkar bata a wajen, tinanin Auta ce
kawai a cikin kwakwalwarta.

"Kai malam kamar ya zaka mayar da ita da kanka? Ban gane ba?"...........Cewar
Abdussalam, ya yi maganar cike da tsiya da iyashege.

"E zan mayar da ita time da na yi ra'ayi"....... With his full confidence Jawad
ya mayar mashi da amsa.

"Kai ka kawota ne daman? Ji mun wani karfin hali, kinga Fanan kama hannunta ku
tafi hai"........... Cewar Abdussalam, yana magana yana ɗaure fuska irin shi fa da
gaske yake yi.

Gum kamar gunki Fanan ta tsaya ta kasa kama hannun Chuchu saboda tana tsoro,
jama'a dik sun watse sun barsu tsaye a wajen.

"Fanan kama hannunta na ce ku tafi ko.........".......... Cewar Abdussalam. Bai
ƙarisa maganar ba ya dakata saboda wani irin harara da Jawad ya wurga mashi.

Murmushi Abdussalam ya ɗan saki tare da riko hannun Fanan yana faɗin. "Zo mu tafi
hai sister, kada ya fara saka mana duka".

Ba musu ta bishi suka tafi, wajen ya rage daga Jawad sai Chuchun.

A hankali ya kai hannunsa ya riko hannayenta, kamar mai raɗa ya ce. "Menene kuma?".

Kamar jira take yi ya yi mata magana ta fara kuka, nan take hawaye suka fara ƴar
tsere a saman face ɗinta.

A ɗan rikice ya ce. "Jannat lafiya kuwa?".

Da ɗan daga murya ta ce. "Yah Jawad Auta, ban ga Auta ba, tun da yamma nike nemanta
ban ganta ba, tun da rana rabona da ita, ina kiran numberta baya shiga, ya zan yi
da rai'na?".

Ɗan jawota jikinsa ya yi, shi kansa yana cikin damuwar rashin Autar nan, amma bai
taɓa kawo mummunar abu a ransa ba, ya fi zaton tana wajen bakin Dubai tun da ta yi
sabo da su sosai.

"Auta tana nan a ciki gida, muje zuwa da safe da kai'na zan ɗauko maki ita".

Bata san yin ja in ja da shi ne kawai yasa ta yarda da abin da ya ce, ta kuma miƙa
wuya a garesa, cak ya ɗauketa suka fito daga cikin hall ɗin.

Bai zame ko'ina da ita ba sai cikin bedroom ɗinsa, shi tun ba'a kai mashi ita ba ya
kaiwa kansa ita.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Momma tana sallame sallah ko numfashin guyson bai bari ta ja ba ya yi sauri wurga
mata tambayar ina Autarsa?

Wani irin dum dum Momma ta ji kirjinta ya buga, sai dai bata yi wani mummunar
tunani ba, cikin nutswa ta ce.

"Ina jin tana tare da Jannat a wajen dinner.........."

Tun bata dasa aya a maganar ba ya tari numfashinta da cewa. "Naje wajen bata nan,
Yah Jawad ma ya ce rabonsu da ita tun da rana.........."

Bai ƙarisa maganar ba momma ta zabura kamar wadda aka kwalawa guduma a kai ta miƙe
tsaye, dan ita ma rabonta da Auta tun da rana, dik tinaninta tana a tare da su
Chuchu ne yasa bata wani damu ba, sai yanzu ta tuna yadda ta rinƙa ganin giftawarsu
Fanan and Chuchun ba a tare da ita ba, kwata kwata bata ga giftawarta ko kaɗan ba,
to ina take kenan? Ta jefawa kanta tambaya.

Shi ma guyson miƙewa tsaye ya yi yana jiran amsa. Cikin ƙanƙanin lokaci face ɗin
momma ta rikiɗa izuwa na tashin hankali.

Wayarta dake gefen bed ta ɗauko domin ta gwada kiran number Auta.

"Momma don't west

Please Login or Register in order to submit comment