You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
binta da kallo. Tamkar wadda kwai ya
fashewa a ciki ta nufi bedroom ɗin nasa. Hannunta har rawa yake yi tasa hannu ta
tura kofar tana haɗawa da ɗan siririn sallama ƙasa ƙasa.
Tana sanya kafafunta a cikin ɗakin ta waro idanu waje, ya subhanallah ɗakin ya haɗu
ne sosai, sai tashin kamshi yake yi. Baya cikin ɗakin, yana balcony yana waya da
Jawad, Jawad ya je office ɗinsa bai same shi bane yasa ya kira waya ya tambayi ina
yake, shi ne ya ce mashi ya dawo gida baya jin daɗi.
Ji ta yi tamkar ta juya a guje ta bar ɗakin, sai dai kuma tana san sanya shi a
idanunta, ta yi kewarsa sosai. A hankali ta fara ɗaga kafafunta ta ƙariso cikin
ɗakin, a kusa da bed ɗinsa ta tsaya tana kallan yadda king bed ɗin nan ya haɗu.
Kamar ance ta ɗan ɗago kai sai ta hangosa saman wasu ƙayatattun kujeru masu laushi
da kyau dake wajen yana zaune yana waya.
Subhanallah tsare shi da idanu ta yi tana kallansa ta cikin glass ɗin, shi baya
kallanta saboda na waje baya kallan na ciki, na ciki ne zai iya kallan na waje.
Tamkar yasan akwai mai kallansa ya kara juyowa da kyau yana fuskantar bedroom ɗin
nasa. Lips ɗinsa kawai ta tsare da kallo tana tina lokacin da yake bata hot kiss a
kauye, yanzu taga lips ɗin nasa su kara tura ja sosai sun ƙara kyau, da yake ya
saba mata a baya sai ta ji tana kwaɗayin yi mashi kiss ɗin a yanzu, amma babu dama.
Ta shagala da tinanin soyayyarsu a kauye bata ga miƙewarsa ya nufo dakin ba sai ji
ta yi ance. "Lafiya? Wacece ke?". Ya yi maganar kuma kallansa a kan zanen flowers
ɗin hannunta.
A ɗan razane ta kyabta idanunta sau biyu tare da yin ƙasa da kai, a ɗan tsorace
cikin sanyin murya ta ce. "Dama abinci ne na kawo maka". Tana matana tana satar
kallan kayan jikinsa, ya yi makurar kyau sosai. Pj ne a jikin nasa masu silky
launin milk color, kyawawan fararen kafafunsa suna cikin bedroom slippers ash colar
mai laushin gaske.
Kawar da kallansa a kan hannunta ya yi izuwa kan face ɗinta, dai'dai lokacin ta
ɗago kai dan ta kalli meyasa ya yi shiru. Unexpext suka haɗa ido. Wani irin faɗuwar
gaba ta ji ya dira mata, shi kuwa wani irin shock ya ji a jikinsa, lokaci guda ya
ji tamkar ya san face ɗinta, ƙwaƙwalensa ce ta amsa mashi, kamar walkiya ya ji
tamkar an ambaci hamma a cikin kwakwalwarsa, kamar yana san tina rayuwarsa a gidan
bappa ɗin.
Dik kunyar da take ji ta kasa iya zare idanunta a cikin nasa, shi ma ya kasa kawar
da kallonsa daga kanta, yana jin ƙwaƙwalwarsa tana juyawa dama ga shi kansa na
ciwo, bugu da kari yana bala'in san kwalliya, haba ai sai abin ya haɗe mashi, domin
kuwa kwalliyarta ta fito sosai ta yi wani irin kyau na ban mamaki, ko iya kwalliyar
kawai ya isa ya sanya ya kasa zare kallansa a kanta tun da yana son kyalliyar bare
kuma ya haɗe da kyanta ga gyara da ta sha, sannan ga shi kamar ya san face ɗin.
Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta
sosai.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
ِإَّنَك َحِميٌد، َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم،الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد
ِإَّنَك، َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم، الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد،َمِجيٌد
️❤َحِميٌد َمِجيٌد
No editing😥
Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta
sosai.
Abin ku da sun taɓa kasancewa masoya masu san junansu sosai a baya, kun san wannan
abin ba zai taɓa barin zuƙatansu cikin sauki haka ba, shi kansa Jaish ɗin dik da ya
dawo dai'dai ai soyayya ba karya bace, dole idan ya ga face ɗinta ko bai tinata ba
zai ji a jikinsa kamar ya santa.
Nisawa ya ɗan yi, sannan ya ƙara ɗaure fuska tamau kamar bai san me murmushi ba,
a takaice ya nuna mata hanyar fita da hannunsa tare da furta out. Tabbas bata san
ma'anar kalmar out ba, amma ta fahimci fita ya ce ta yi ta hanyar hannunsa da ya
nuna kofa da shi. Tamkar zata sa kuka haka ta juya ta nufi hanyar fita.
Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana tinanin wacece ita da har momma zata sanya
ta kawo mashi abinci? Idan baku manta ba dama shi bai kalli matar da momma ta sanar
da shi mallakinsa bace, an dai ce mashi yana da mata, amma bai ga face ɗinta ba, so
yanzu bai san ita ce wannan ƴar kauyen ba, ya fi tinanin ma daga cikin ƴaƴan ƴan
uwan momma wato su uncle Rahab daga can ne ta zo ziyara momma ta aikota kawo mashi
abinci.
Siririn tsaki ya ja tare da hayewa bed ɗinsa ya kwanta, a ransa ya zayyana ba
zai ci wannan abincin ba tin da momma ta aiko mashi wata. Hmmmm dama Jaish ai da
wuyar sha'ani yake, kowa kuma yasan da haka, sai ka yi kamar zaka fahimci in da ya
dosa sai ya sake watsawa mutum ƙasa a ido, ji abin da ya aikata yanzu fa, harda
wani ba zai ci abincin ba.
Da sauri Mahnoor ta isa ga mama Haulat, wani irin kuka ne ta ji ya kubce mata,
dan yadda taga ya ɗaure fuskar nan dik da bata jin turanci sai taga kamar zaginta
ya yi, abin ya ƙona mata rai.
Tararta mama Haulat ta yi, sam bata yi mamakin ganinta ta fito cikin ɓacin rai har
da guzurin kuka ba, dan ita tasan halin Jaish fiye da tinanin mai tinani, tasan
dama ya yarda da Mahnoor cikin ƙankanin lokaci haka abu ne mai wuya gaskiya.
So bata tambayi Mahnoor ɗin menene ya faru ba, kawai ta riko hannunta suka koma
wajen momma. A saman bed suka isko momma ta kwanta tana tinanin duniya, Mahreen ta
tafi tare da Chuchu da suka dawo daga school ba jimawa, momma ta ce ta bi Chuchu ta
kara koya mata abubuwa.
Momma na ganinsu ta miƙe zaune tana kallan Mahnoor dake sharar kwallah, dama tasan
za'ayi hakan, kawai shahada ta yi ta gwada dama, to ba'ayi nasara ba.
Mahnoor na ƙoƙarin durkusawa ƙasa momma ta yi saurin ce mata ta hauro saman bed. Ba
musu ta zauna bakin bed tana cigaba da sharar kwallah. Rungumota momma ta yi tare
da bin mama Haulat da kallo alamar tana jiran karin bayani. Girgiza kai mama Haulat
ta yi alamar bata da masaniya a kan komai.
Da hannu momma ta yi mata alama da ta tafi kawai. Cike da girmamawa ta amsa da to,
sannan ta juya da sauri ta fita. Dawo da hankalinta kacokam a kan Mahnoor momma ta
yi, cike da kauna haɗe da sigar rartashi ta fara tambayarta me ya faru?.
Kamar ba zata faɗa ba, sai kuma ta daure ta ce ya koreta daga ɗakinsa. Ajiyar
zuciya momma ta sauke, dama ta yi expecting hakan, so sai ta rarrashi Mahnoor har
ta yi shiru, sannan ta ce.
"Amma ba nace maki in dai ba a cikin ɓacin rai yake ba ko ya hantareki kada
ki matsa kada ki damu ba?". Momma ta jefa mata tambayar.
Cikin kuka ta ce. "Momma tsoronsa nike ji"........... Tabbas ta fahimci tsoronsa
sosai take ji, dan haka sai ta shiga bata wasu dabaru ta yadda zata bi har Allah ya
bata ikon shawo kansa. Ƙasa kunne ta yi tana saurara sosai saboda kaunar da take yi
wa mijin nata, dik wasu shawarin momma ta naɗesu a cikin kwakwalwarta, momma bata
jin kunyar nuna mata hanyar da ake bi dan maganin mazan gidan King ba, kun san ita
ai ta kware, wannan hanya da take bi dan yin maganin King har ya amsa abin da bai
niyya ba, shi ta zauna ta warwarewa Mahnoor komai tsab, daga karshe ta rufe mata da
cewa in dai har tana san shi da gaske to ta jure ta bi dik shawarin da ta bata.
In ta dage ta yi komai cikin nitsuwa tabbas yau Jaish ba zai zulle mata ba, dan
rauninsu kenan.
Kunya tamkar Mahnoor zata shige cikin ƙasa, ta yi ƙasa da kai kamar ba zata
sake ɗagowa ba, sai dai da yake tana san Jaish, zuciyarta ruwan madarar albarka
take kwaranyawa momma da ta jajirce a kansu.
Momma kuwa, da bata ji kunyar komai ba har da cewa. "Zan yi magana da shi, kuma a
daren yau, zan kira shi in sanar mashi da matsayinki a wajensa da kai'na, zan
tayaki da yi mashi nasiha, daga karshe zan ce ya kama hannunki ku tafi part ɗinsa,
ba zai yi mun musu ba, dan bai taɓa yi ba, tabbas zai karɓe ki idan na buƙaci
hakan, amma ni da ke mun san ba dan ransa ya so zai yi hakan ba, dan haka ya rage
naki sauran aiki, in kina san ransa ya so kuna shiga part ɗinku ki yi wanka a
toilet ɗinsa, kada ki matsa ko nan da can, ki sanya ɗaya daga cikin kayan da zansa
mama Haulat ta baki anjuma, ki shirya ki haye bed ɗinsa ki kwanta,kada ki damu da
sai ya kulaki ya yi maki magana a daren, kada fa ki rusa mana shiri, kuma kada ki
damu da dik abin da zai ce maki dan kin kwanta a bed ɗinsa, in kin kwanta ki yi
gaggauwar rufe idanu dan ma ya zaci barci kike yi, tabbas ina da yakinin zai dawo
gareki".
"Sannan kada ki ji tsoron kwanciya a jikinsa idan har ya hau gadan, dik
zafin kansa da kike ganin nan bai kai mahaifinsa a lokacin da yake matashi ba, so
ni na faɗa maki dik zafin nan nasa ba zai iya taɓuƙa maki komai dangane da faɗa ko
kyara ba a lokacin da zaki zo garesa, in dai kin bi dik tsarin da na tsara maki,
lastly dik abin da zaki yi ki sanya nitsuwa a ciki, dik da naga kina da nitsuwa,
amma ki kara, dan dik wani namiji yana san mace mai nitsuwa, nitsuwar tana jan
hankalinsu sosai".
Tsabar daɗin kalaman momma har ji ta yi tamkar ta jawo dare ya yi, a yanzu dai gani
take yi tamkar zata iya aikata dik abin da momma ta ce, sai ta ji ta matsu lokacin
ya yi, har ga Allah tana kewarsa, kuma ya saba mata da hot kiss kafin su yi barci a
Jimeta, to yanzu babu, da kyar take iya yin barci, ga ɗamin jikinsa dik bata samu,
kuma tana buƙata, sai ta ji tana buƙatar dare ya yi da wuri yau ta kwana a saman
kirjinsa....... Wayyo my belly, Mahnoor is to much, love ya rufewa yarinyar nan
idanu fa, Jaish ɗan duniya ne wlh, ya koyawa yarinya abu dan iskanci yanzu kuma ya
ce bai san wannan ba, zaka yi bayani ne bari Queen Zarina ta aure samartakanka nan
ne zaka gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah Sallallahu........😅
Momma ta karanceta tsab, dan akwaita da iya harbo jirgi mutun da wuri, tuni ta
gano Mahnoor fa ita ma a hannu take tana san kasancewa da mijinta, ta ji daɗin
hakan, ba ƙaramar dama hakan ya bata wajen kara karfafawa Mahnoor ɗin gwiwa ba.
Sun jima a wajen suna hira har 1:30 na rana, sannan momma ta buƙaci da ta tashi
suje lokacin sallah ya yi. Miƙewa ta yi ta fita ta nufi part ɗin mama Haulat.
Momma na ƙoƙarin miƙewa ta shiga toilet sai ga mama Haulat ta shigo baki a ɗauke da
sallama. Dakatawa momma ta yi haɗe da amsa mata sallamar. Zuba mata idanu ta yi
tana jiran ta ji dame ta zo. Cikin girmamawa mama Haulat ta sanar da ita Jaish fa
yaki cin abincin da aka kai mashi, da mama Haulat ɗin ta je ta sake kiransa a kan
ya zo ya ci sai cewa ya yi ba zai ci ba, kada mama Haulat ta sake dawo mashi cikin
ɗaki a kan wannan abincin.
Jinjina kai momma ta yi tare da yi mata almar ta je kawai babu damuwa. Juyawa ta yi
ta fice tana jinjina zuciya irin na yaran King.
Toilet momma ta shige ta ɗauro alwala ta fito. Sai da ta yi sallah ta yi addo'inta
sannan ta tashi ya nufi dry kitchen nasu, a nan ta sake shirya mashi simple things
da zasu ɗan rike mashi ciki, ta ɗauka izuwa part ɗinsa.
Tana shiga yana dawowa daga musque sanye da arab jallabiya milk color. Yana
ganinta ya ɗan turɓune fuska tare da zama a saman sofa. Kasa saman sinfiɗar gashin
jimmina dake parlourn ta ɗaura tray ɗin abincin, sannan ta koma saman sofa ta zauna
suna fuskantar juna.
Sai kallanta yake yi yana jiran ya ji me zata ce mashi. Sallamar Jawad ya
katse maganar da take san yi mashi, so sai ta fasa faɗin abin da zata faɗa ta miƙe
ta nufi waje tana faɗin su ci abinci to.
Allah sarki Jawad ya kasa zama a office ɗinsa ne jin cewa Jaish bashi da lafiya,
dik ya rasa sukuninsa har sai da ya dawo ya gansa.
Kallon time a wayarsa Jaish ya yi 2:00 dai'dai yanzu, dawo da kallansa a kan
Jawad ya yi. "Bro me ya dawo da kai by this time around?".
Zama ya yi kusa da shi tare da kai hannu ya taɓa forehead na Jaish ɗin yana faɗin.
"How's your body?".............. "Feeling better Alhdulillah" jinjina kai Jawad ya
yi kafin ya ɗaura da cewa. "Ka tayar mun da hankali, all my tougth ciwon ya fi
haka". Yana magana ya shafa goshin Jaish.
"No ba wani ciwo bane bafa, is just only headache, and momma ta ce rashin cin
abinci ya kawo shi". ............ Allah mai iko, gasu dai kamar twins, amma shi
Jawad a kan lokaci yake cin abinci, shi kuma Jaish sam bai damu da ci ba, wani
lokaci sai yunwa ta yi mashi over ya ji zai iya faɗuwa sai ku gansa ya ɗan ɗauko
maltina ko wani drinks ɗin ya sha, dik gudun cin abincin ne fa.
Jin haka yasa Jawad ya sauko ƙasa wajen da momma ta ajiye abincin. Buɗewa ya yi ya
fara zubawa ɗan uwan nasa abin da ya dace da shi yana faɗin. "Since nike faɗa maka
cewa sometimes yunwa zai janyo maka wani big problem ɗin, amma baka yarda, anyway
come down and eat yanzu kam".
Jaish bai yi wani gardama ba ya sauko kasan suka fara ci a tare cikin plate ɗaya,
suna ci suna hira sama sama.
3:00 dai'dai har lokacin suna tare momma ta kira Jawad a waya a kan ya zo. Tashi ya
yi cikin sauri ya nufi bedroom ɗinta yana sanar da Jaish ya kwanta ya huta even for
one hour bari ya zo. Jinjina mashi kai kawai Jaish ya yi ba tare da ya yi magana
ba, hayewa bed ɗinsa ya yi ya kwanta da nufin ya yi barci ko da na 30 mins.
Sai dai kuma yana kwanciya tinane tinane suka cika mashi barin har da tinanin
yarinyar da ta kawo mashi abinci a yanzu, haka kawai ya tsinci kansa da tinanin
face ɗinta yadda ta tsare shi da idanu tamkar ta san shi, da tinanin yadda ta sha
kwalliya har lallen hannunta yake fisgarsa gareta.
Siririn tsaki ya ja tare da ƙoƙarin kawar da banzan tinanin a cewarsa, sai dai kuma
tinanin taki tafiya, saboda idan baku manta ba dama ya ce kamar da akwai wani gurbi
da yake ji a cikin zuciyarsa ya rasata, to zuciya kuma yau taga burbin da ta rasa
ba dole ta takura mashi ba, ai ya yi ya yi ya dai'na tinanin yarinyar nan sai ya
ƙasa.
Daga karshe wayarsa ya ɗauko tare da miƙewa zaune a zuwan ya fasa yin barcin tin da
wani banzan tinani ya sako shi a gaba. Balcony ya koma ya zauna ya shiga latsa
wayar tasa bayan ya kunna data.
Sai dai fa ko da ya koma balcony ɗin tinaninta yaki sakesa, dik abin da yake yi
face ɗinta ƙwaƙwalwarsa take kwaso mashi, abin har ya fara ɓata mashi rai.
A ɓangaren momma kuwa, magana ta sirri suka yi da Jawad har karfe 4 daidai ta cika,
sannan suka rufe maganar tasu kowanne ya miƙe dan ya yi sallah, momma na miƙewa ta
ce mashi kada ya manta ya turo mata Jannat ɗin fa.
Da okey ya amsa mata tare da fita ya nufi wajen Jaish dan su tafi masallaci a tare.
After some hours. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i. Momma da Chuchu
ne zaune a saman bed ɗin Momma suna jiran mama Haulat ta kawo masu Mahnoor, sai
hira suke yi irin ta uwa da ƴa cike da so da kauna.
Sallamar mama Haulat ta dakatar da su a in da suka mayar da kallansu a kanta, tana
rike da hannun Mahnoor dake sanye da kyakkyawan abaya mai shegen tsada launin army
green.
Ɗan zaro idanu Chuchu ta yi tana kallan Mahnoor, da yake shekarunsu kusan
ɗaya sai girmansu ma yazamana ɗaya.
Ƙasa shanye mamakinta Chuchu ta yi har sai da ta ce. "Momma wacece wannan?"....
Da hannu momma ta nunawa Mahnoor gefenta da ta zauna, sannan ta buƙaci da mama
Haulat ta basu waje kuma nan da 30 mins ta kawo mata alkyabbar Mahnoor zata kaita
wajen King. Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa sannan tasa kai ta fita.
Haɗe Mahnoor da Chuchu momma ta yi a in da ta yi masu nasiha mai ratsa jiki da
kyau, sannan ta tambayesu da ya ake yin wankan haila da na janaba?. Ita Mahnoor ta
karanta wannan, amma kunya ya hanata faɗa, ita kuma Chuchu iliminta bai kai nan ba,
so bata karanta ba, dikkansu biyu babu wadda ta fara period a cikinsu, shiyasa ma
Chuchu bata nemi yadda ake yi ba.
Ganin sun yi mata shiru ne yasa ta fahimci basu sani ba ne, dan haka sai ta ɗan yi
gyaran murya kaɗan kafin ta fara magana kamar haka.
"Wannan tambayace da yakamata ace kowacce mace tasan amsarsa, nasan yanzu
mata dayawa basu san yadda ake yi ba, amma bari in yi maku bayani dan dayawan mata
su karu".
Shiru dai suka yi babu wadda ta yi magana, Mahnoor dai ta lura su fa ƴan gidan nan
basa jin kunya kwata kwata, mijinta Jaish da guyson ne kawai masu kunya, su biyun
nan ne masu kunya a ganinta.............. Lallai Mahnoor baki da kunya in ji ni
princess Teema, wai har da uwar mijin nata ma bata da kunya kenan? Amma kuma fa
gaskiya ta faɗa, ko shi Jaish daga ina ya samo nasa kunyar? Dan dai momma kam bata
da shi, kada ku ce na ce na ce ɗin...........🥱
"Wanka a Musulunci yana da matakai daban daban bisa ga dalilin yin sa. Wankan Haila
wanka ne da mace take yi bayan gama al'ada domin komawa cikin tsarki. Ga yadda zaku
yi shi. Abu na farko niyya, a zuciya ki yi niyyar wanke jikinki daga haila zuwa
tsarkin. Sannan sai bisimillah. Ki ambaci sunan Allah Idan ba a cikin banɗaki kike
ba, dan ba'a ambatar sunan Allah a waje mai najasa, so in dai a ɓanɗaki ne no need
for bismillah. Abu na uku wanke hannaye, ku wanke hannayenku sau uku. Abu na huɗu
alwala. Ku yi alwala kamar yadda ake yi don sallah. Na biyar wanke kai. Ku jika
gashin kai da ruwa sosai har ya gama jika. Abu na shidda shi ne wanke jiki
gabaɗaya. Ki fara daga gefen dama, sannan ki wanke gefen hagu. Bayan kin kammala
wankar zaki iya shafa sabulu mai kamshi ko turare a gefe gefen gabanki don kawar da
warin haila. Ku lura da kyau wajen wanke gashin nan, Idan mace tana da gashin da ke
tattare, ma'ana ta tsefe kai, to dole ta tabbatar da ruwa ya isa har fatar kanta,
kunga kuwa sai ta jiƙa gashin sosai, a wannan gaɓar ana samun matsalar fahimta,
wasu suna cewa sai mace ta tsefe kai zata yi wankar haila, to ingantaccen magana ba
gashin kanta ake san ruwan ya taɓa ba, fatar kanta ake san ruwan ya jiƙa wanda idan
bata tsefe kai bama tabbas sai ruwa ya fi shiga fatarta, dan haka ku lura da
wannan".
Tin da momma ta fara magana dik suka wani yi ƙasa da kai suna sauraronta da kyau,
sai satar kallan Mahnoor Chuchu take yi, taga kyakkyawa ƴar gayu kamar ita.
Cigaba momma ta yi da cewa. "Wannan shi ne wankar haila cikakke, shi kuma wankan
janaba ana yin sa ne bayan saduwa ko mafarki (nocturnal emission.) Yana daidai da
wankan haila, sai dai ba dole ba ne mace ta yi amfani da turare bayan sa. Shima
matakan yinsa gasu nan kamar haka. Niyya, bisimillah, wanke hannaye sau uku, wanke
al'aura, yin alwala, jika gashin kai da ruwa, wanke jiki gabaɗaya, wannan shi ne
wankar janaba".
Shiru suka yi, gara mah Mahnoor ta daure ta ce da momma sun gode. Ina fatan ba iya
su Mahnoor bane kawai suka ilmantu da ilimin alkalamina? Allah ka kara mana ilimi
mai albarka mai amfani ka sakawa iyayenmu da suka tsaya mana wajen ganin mun samu
ilimi ingantacce wanda har jama'a suna ilmantuwa daga garemu, a koda yaushe ba zan
gaji da cewa ku mun addu'a kowace iriya ce in dai na alkhairi ce a gareni ina kauna
kuma zan ji daɗi sannan ina godiya Allah ya bar kauna, ni ko baki kaunata ma ki
daure ki mun addu'ar alkhairi please.
Chuchu ce ta tambayi momma wacece Mahnoor?. Cikin nitsuwa momma ta fayyace
mata ita tsab, sannan ta ɗaura da cewa tana fatan zasu haɗa kai tamkar yadda Jawad
da Jaish suke tamkar twins.
Riko hannun Mahnoor Chuchu ta yi, fuska ɗauke da fara'a ta ce. "In Sha Allah momma
muma zamu kasance tamkar twins kamar dai su Yah Jawad.
Sosai momma ta ji daɗin furucin Chuchu, miƙewa ta yi ta nufi toilet tana faɗin bari
ta yi wanka tana zuwa. Tana shiga toilet Chuchu ta dawo da kallanta a kan Mahnoor.
"Ina fatan zaki ɗaukeni kamar twins sis ɗinki?". Ta tambaya tana kallanta.
Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tare da cewa In Sha Allah sun zama ƴan uwa. Ɗan
rungumeta Chuchu ta yi tana faɗin. "Gaskiya kina da kyau sosai".
Ɗan siririn murmushi Mahnoor ta saki kafin ta amsa mata da. "Kema kyakkyawa ce
sosai ai".
Sallamar Jawad ya katse masu hirar tasu. Da sauri Chuchu ta dawo da kallonta a
kansa. Ganin shi ne yasa ta yi saurin sakin Mahnoor ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa
tana murmushi. Rungumeta ya yi yana faɗin. "Shi ne aka barni aka zo wajen momma
ko?".
"Kai Yah Jawad, yanzu fa nazo kuma momma ɗin ce ta kirani". Jinjina kai ya yi
kafin ya ce. "Nima momma ɗin ce ta tura mun text a kan inzo, ina take?". "Ta shiga
wanka, Yah Jawad ga matar Yah Jaish fa". Ta yi maganar tana ɗan raba jikinta da
nasa.
Kai kallansa a kan Mahnoor ya yi, maganganun sirrin da suka yi da momma ɗazun ne
kawai ya faɗo mashi a ransa, ƙaƙalo siririn murmushi ya yi ya sakar mata kafin ya
ce. "Sannunki".
Kasa ta yi da kai tana ɗaga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Chuchu sarkin iya
soyayya sai ta ce. "Mahnoor kin ji momma ta ce mu zama kamar twin irin Yah Jawad da
Yah Jaish ko?". Gyaɗa mata kai Mahnoor ta yi alamar e ba tare da ta yi magana ba.
"To wannan shi ne Yah Jawad ɗin da ake magana a kansa, shi ne twins ɗin mijinki,
kuma shi ne mijina ni". ....... Dogon hancinta Jawad ya ja, kasa kaɗan ya yi da
murya kafin ya ce. "Da gaske ni mijinki ne my Jannawad?". Ya yi maganar yana ɗaga
mata gera guda.
Dukan wasa ta kai mashi a kirji tana faɗin. "A'a ba kai bane". Hannun nata ya
riko. "Sarkin rigima, zo mu je ki bani abinci yunwa nike ji".
"Ka manta momma ta ce ka zo ne?". Ɗan jinjina kai ya yi. "Yeah na manta ne, to bari
in jirata". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta suka koma saman sofa suka
zauna. Shigewa jikinsa ta yi ta hau bawa flowers ɗinta ruwa. Sai datar kallansu
Mahnoor take yi tana ayyana irin haka zasu yi da Jaish ɗinta idan ya fara sonta.
Lokaci guda ta tina lokacin da suke Jimeta suke soyayya a gonar bappa, gabanta ne y
faɗi dik sai ta ji babu daɗi.
Jawad da Chuchu basu ji kunyarta ba suka cigaba da zuba soyayyarsu har momma ta
fito daga wanka. Umarni ta ti wa Jawad a kan shi da Jaish su sameta a part na King
nan da 20 mins. To okey ya amsa mata sannan ya miƙe ya
Book Chapters
Chapter 42
Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500