You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kam bala'i lallai King shahararren ne, iyeeeee, ya aka yi Smart yasan
dikka wannan sirrin wanda su momma basu sani ba? Sannan ya aka yi yasan suna da
alaƙa da maman Hoorain bayan momma da ta yi tinanin ma bata faɗa mashi ba? Gaskiya
Smart hegen kwaro ne, wato akwai badaƙala, wacece uwar Ramish to tin da ba mama
bace? Amma da alama irin son da King yake yi mashi shi ne ubansa, tab QUEEN OF
SURPRISED na fara baku a jikinku, yanzu kuka fara shan surprise ma ai, mu je zuwa.

King da ya gama nuna zallar hasala a face ɗinsa, abin da mutane suke cewa
tabarmar kunya da hauka ake naɗeta, ya ɗaure fuska zai yi magana cikin tsawa kenan
Chuchu ta afko cikin ɗakin a guje tana zunduma ihu, hakan yasa duk suka kai
kallansu a kanta. Tana zuwa a haukace ta nufi King tana faɗin. "Daddy Auta ta rasu,
Yah Abdussalam ne ya faɗa mata cewa Hoorain ɗin da take so ai ya mutu dan haka ta
zo su yi zaman aure, shikenan ta faɗi ta dai'na numfashi!!".

Ai King bai tsaya jin karashin maganar ba ya nufi waje, saboda yasan dama ance
zuciyarta gab yake da bugawa, to ga shi Abdussalam ya fasa abin da suke rufe mata,
ai dole ziciyarta ta buga. Shi kuwa Smart tin da Chuchu ta ambaci Auta ta rasu ya
rigasu barin bedroom ɗin ya nufi in da take. Yana shiga ya sami Abdussalam sai
tattala mata tuwa yake yi a kanta yana ambatar sunanta, amma ko motsawa bata yi ba,
da kallo ɗaya Smart ya yi mata ya fahimci tabbas babu rai a jikinta. Innalilahi wa
inna ilahir rajiun.

Allah sarki kada ku ga laifin Abdussalam, shi bai san ciwon son Hoorain take yi ba,
shi bai san ance kada a sanar da ita ba, da ta fito parlour tana sambatu a kan
Hoorain ne ya biyo bayanta, a nan ya ji ashe san Hoorain ne a ranta, shi kuma yasan
Hoorain ya mutu, shi ne ya sanar da ita ya rasu, hakan yasa ta yanke jiki ta faɗi
zuciyarta ta buga.

A fujaje King ya shigo cikin ɗakin, tamkar ya haukace ya yi kanta zai taɓata, ai
cikin wani irin kuna da fitar hayyaci Smart ya capki wuyarsa, dama ya faɗa mashi in
Zunaira ta mutu to fa sai dai ayi gawa biyu wlh!!.

Page ɗin yau bai samu wadataccen editing ba, nasan zaku samu typing errors dayawa
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




57



Daidai lokacin su uncle Abbas suka shigo cikin parlourn, dan Chuchu sai da ta je ta
kira kowa na familyn, da alama Chuchu ta zauce, dan kalar kukan da take yi sai da
uncle Jahiz ya kamata ya hanata dawowa part ɗin, ya miƙata ga Jawad ya yi mashi
gargaɗin kada ya barta ta fita, saboda za'a samu matsala.

Kin yarda ta yi tana tigewa sai da Jawad ɗin ya sanyata a ɗaki ya rufe kofar da
key, sannan ya kira Dr Raj da ya zo ya yi mata alluran barci ko zai samu hankalinta
ya kwanta. Yau sai da aljannun dake kan Aneesa suka motsa saboda tsananin tashin
hankalin da suka shiga. Uncle Jahiz and uncle Jahiz sun yi sun yi su zare hannun
Smart daga wuyar King amma sun kasa, saboda wani irin damka da ya yi mashi na
takaici da fitar hayyaci, shi kuma King like ruhinsa ya bar jikinsa saboda tashin
hankali, bai taɓa zatan ɗan cikinsa zai yi mashi abin da Smart ya yi mashi ba ko da
wasa, hakan yasa ya yi wannan sumar tsayen.

Ihun da guyson ya zunduma a lokacin da ya shigo cikin parlourn ne yasa Smart
juyowa, Allah sarki, hankalinsa ya yi nisa wajen hukunta King ne, da ba zai taɓa
bari guyson, Omaid and Obaid da Momma su ji batun mutuwar Zunaira a yanzu ba, dan
abin zai yi mashi yawa, yasan ba zasu iya ɗauka ba, kazalika shi ma zai iya ɗaukar
komai ban da tashin hankalinsu.

Ganin cewa labarin yana yaɗuwa a cikin gidan zai iya ja momma ta ji labari ne yasa
ya saki King ba dan ya so hakan ba. Yana sakinsa King ya zube ƙasa a saman
gwiwowinsa idanunsa sun kaɗa sun yi jajir, yau zuciyarsa ta karaya, ya shiga tashin
hankalin da ko a mafarki bai taɓa zatan shiga ba, yana kaunar Zunaira tamkar ransa,
idan ta mutu a gaskiya zai iya mummunar cutuwa. Ɗan uwa ɗan uwan ne my people's,
uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka rungumi King suna tausarsa dik da basu san me
ya haɗa shi da Smart ɗin ba.

Shi kuwa Smart kan Auta ya nufa, Abdussalam yana rike da ita yana ta famar
girgizata yana kwallah, ya tattala mata ruwa a kanta ya kai 5 bottle, hakan yasa
suka yarda da ta mutu ɗin ne, ruwa ba zai tasheta ba sai dai ALLAHN da ya yi ruwan
ne zai iya tashinta.

Wani irin gigitaccen tsawa da Smart ya dakawa Abdussalam har sai da yasa gabaɗaya
waɗan da suke cikin parlourn suka natsu, a zabure Abdussalam ya ja baya da gudu.
Bai bi ta kan kowa ba ya ɗauki gawarta ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa
ya nufi kofar fita, dik an rasa mai bakin iya ce mashi uppan. Har ya kai bakin kofa
ya juyo ya kalli King ido cikin ido. "Ka jira dawowata, sai ka ɗanɗani irin azabar
da ka ɗanɗanawa Zunaira a zuciyarta kafin mutuwarta, kuma sai ka faɗa mun dikkan
amsoshina!!!". Yana kai karshen maganar ya ja hannun guyson da yake tsaye a bakin
kofar tamkar an sassakasa, kamar wanda aka zarewa laka, tin da ya yi ihu sau ɗaya
bai sake ko motsawa ba, amma ransa na jikinsa kuma ba suma ya yi ba.

Shi kuwa King Allah ne kaɗai yasan irin halin da ya shiga, ji ya yi tamkar bashi a
duniya, Zunaira ta mutu? Ina kin yarda ya yi kamar yadda har yau commander Zafar
yaki yarda da Hoorain ya mutu, an je an binne Hoorain, har kabarinsa su Ansar su je
da shi, amma yaki yarda ɗansa ne, dan shi yana ganin Hoorain a gizo. To haka shi ma
King a yanzu yaki yarda Zunaira ta mutu, ya shiga wani irin hali na tsakanin rayuwa
ko mutuwa, wato shi ma a yanzu yana ɗanɗana abin da commander yake ɗanɗana, sai dai
kuma dik da ta mutu wlh bai yi danasanin hanata auren Hoorain ba! Ko kaɗan bai ji
mamar bai kyauta ba da ya hanata Hoorain tashin sense!!.

-------------------------------------🔥

Suna fitowa suka ci karo da Jaish and Omaid da Obaid suna biye da shi a baya.
Cike da tashin hankali Jaish ya tambayi Smart me yake faruwa?. Ko dakatawa Smart
bai yi ba bare yasa ran zai samu amsa daga garesa, kai tsaye ya nufi wajen motocin
gida. Bayansa suka bi gabaɗayansu Jaish yana faɗin ina zai je da ita? Bai amsa
mashi ba sai ya ce ya yi maza ya bashi keyn motarsa bari ya wuce da ita, dan ba
za'ayi jana'izarta a nan ba, ran Smart ya ɓaci over.

Jaish bai yi musu ba ya ɗauki mashi keyn motarsa, sai dai a tare suka nufi airport,
da jet ɗin Smart ɗin zasu yi amfani. In short kai tsaye ya ɗauki gawar Auta zuwa
Dubai, rabonsa da Dubai tin wani zuwa da ya taɓa yi bincike a kan Ramish, tin
lokacin bai sake zuwa ba, yanzu tsawon shekaru wajen 10, amma yau saboda mutuwar
Auta ya wuce da gawarta can. Bai sanar da momma zai zo Dubai ba, babu wanda ya sani
sai Jaish and guyson da suka tafi a tare, Omaid and Obaid ma sun barosu a kingdom
ɗin sai kuka suke yi, ya ɗauki guyson ne ma dan yasan sai ya yi jinya, kada ya tafi
ya barshi matsala ta afku da shi.

Tin kan su hau jirgi ya kira Ramish a waya, ya sanar da shi ya zo airport ya
ɗaukesu, ya ɗan yi mamakin jin sun zo Dubai, amma sai ya shirya tsab cikin suit
masu bala'in tsada, ya ce da Leesharh bari ya je airport yana zuwa. Da yake ita
tasan me a gidan, tasan tana tare da bakar azzaluma yarinya mai ɓadda kama a
matsayin tsohuwa, sai ta shiga tashin hankali da damuwa over, a tsorace take ya
tafi ya barta da wannan tsohuwa.

Hannayenta ya riko cikin nasa yana kallan face ɗinta. "Aesh ba zan jima ba,
babban yayanmu ne ya zo, shi kawai zan je in ɗauko kin ji?". Shiru ta yi kanta a
ƙasa, kamar mai tinanin wani abin, tana zaune a saman bedside drawer ɗinsa, shi
kuma yana zaune gefen bed ɗin suna fuskantar juna.
Kafin ya ankara sai ganin hawaye ya yi yana ɗiga a ƙasa, ashe kuka take yi da ta
sunkuyar da kanta ƙasa.......... "Aesh lafiya kuwa? Meyasa kike kuka?"........
Shiru bata amsa shi ba, ita tasan bala'in da zata shiga idan ya tafi, tsoron matar
take ji......... "To zaki bini mu je tare ne?". Ya jefa mata tambayar yana sakin
hannunta ɗaya ya ɗago haɓarta. A gaggauce ta gyaɗa mashi kai alamar e zata bishi.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To shi ne sai kin yi kuka? Ai da sai ki faɗa
mun kina tsoron gidan ne mu tafi tare". "Kina tsoron mutanen da suka zo ɗin nan
ko? Ba zasu sake dawowa ba In Sha Allah, so feel free and enjoy your life with your
husband to be In Sha Allah". Ya kai karshen maganar yana ɗan leƙa face ɗinta.

Wani irin shessheƙa ta yi kafin ta kai hannu tana goge hawaye, ta kasa yin magana.
Ƙasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "Yau ɗaya naga abin da kike tsoro Aesh, dik
yadda aka yi akwai abin da yake baki tsoro kuma yake ɗaga hankalinki a gidan nan!
To faɗa mun menene sai in kawar maki da shi kada ki rinƙa jin tsoro". ....... KAI
WATO RAMISH MA FA AKWAI ƘWAƘWALWA, A RANSA YA JI AKWAI ABIN DA YAKE BATA TSORO NA
DABAN, BA WAI DAN MUTANEN CAN SUN KAWO MASU HARI BANE, AKWAI WANI ABIN DAI!!.

Da yake ita ma tana da basira sai rashin yin tinani kafin ta yi abu, sai ta ce
mashi. "Yah Ramish tin da ka iya gano cewa akwai abin da yake bani tsoro, to ka
gano ko menene da kanka ba sai na faɗa ba". "Haka kika ce?". Kai ta gyaɗa mashi
alamar e haka ta ce. Ɗaura yatsarsa a saman kumatunta ya yi. "Zaki gani, cikin
ƙankanin lokaci zan gano". Ya faɗa yana ɗan ja baya kaɗan daga kusa da ita. Tab
kunga Leesharh ta yi amfani da basira a nan ko? Tasa zai fara binciken me abin
tsoratarwa a gidan, idan Allah ya taimakesa sai ya kama tsohuwar nan da hujja dumu
dumu, kamar Leesharh tana highlighting ɗinsa a kan abin ne.

"Shirya ki zo mu je, saura bai wuce 20 mins jirginsa ya sauƙa ba". Ya faɗa yana
kallanta. Miƙewa ta yi ta nufi waje ba tare da ta yi magana ba. Da kallo ya bi
bayanta, idanunsa a kan mazaunanta dake motsawa a hankali, nisawa ya yi tare da
haɗiyar siririn yawu kamar wadda aka ajiyewa kayan fresh marmari a gabansa!.

Tana fita suka yi karo da tsohuwar nan, gabaɗaya tray ɗin hannunta ya faɗi kasa
abincin da ta shiryawa Ramish ɗin ya zube ƙasa. A razane Leesharh ta ɗago ta kalli
face ɗin matar kafin ta mayar da kallonta a kan kayan abincin da suka watse a
wajen. Idan ran tsohuwar nan ya kai dubu to ya ɓaci, sannan hankalinta ya tashi
sosai, Leesharh ta lura da hakan, sai ta ce. "Mama kada ki damu ba sai kin ɓata rai
ba, Yah Ramish ba zai ci abinci a gida ba yau, zamu ci a waje, ki gyare wajen kawai
ki je ki huta abinki". Ta kai karshen maganar tare da wucewa zata bar wajen.

Ai tsabar ɓacin rai tsohuwar nan bata san lokacin da ta kai hannu ta damko wuyar
rigar Leesharh ta baya ba, tana zazzare ido ta kasa yin magana. Ko kun san meyasa
bata yin magana? Saboda muryan yara ne da ita, za'a iya gane ba tsohuwa bace,
shiyasa ta yi acting matsayin kurma, yanzu kunga ne dalilin da yasa na ce maku tun
da take kula da Leesharh bata taɓa yin magana ba?.

Da mamaki Leesharh ta juyo da kallonta a kan matar. A miliyan ta saketa tare da
girgirza kai alamar tana bawa Leesharh hakuri kenan, mamaki kamar zai kashe
Leesharh, me dan an ɓarar da abinci zata tashi hankalinta? Sai kace babu wani
abinci a gidan? Abin da mamaki!. Alama tsohuwar ta nuna mata a kan zata iya haɗa
masu wani abincin yanzu ba sai sun ci a waje ba!.

Shiru Leesharh ta yi tana san gane nufin tsohuwar nan a kansu, meyasa ta damu da
abinci yau bayan a da ko ta kawo masu basu ci ba bata damuwa, wata rana ma a waje
suke fita su ci, bata damuwa sai yau? To why? Leesharh ta jefawa kanta tambayar,
lokacin guda ta ɗan ɗauke wuta. Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta saki wani ƙayataccen
murmushi, kai ta jinjinawa tsohuwar a kan ba damuwa ta shirya masu wani abinci, a
cikin ranta ta ce. "Zaki san da jinin Nigeria kike yi, yo mu da dik duniya ta
jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwa mu bare ke da iskancin naku ma bai da lasisi, mu kuma
Najeriya dik iskanci masu iskanci sai ya jira, sai da suka sara mana, ni kaɗai na
isheki ba sai Yah Ramish ya sa baki ba, zaki gane ke karamar ƴar iska ce, ba zan
taɓa bari ki san nasan komai a kanki ba! Cikin ruwan sanyi zamu yi amfani dake mu
kama iyayen gidanki, ai ke yanzu kina da amfani a wajenmu, zan taya shi bincike
wajen yin amfani dake". JAMA'A KU TAFAWA NIGERIA!! KU TAFAWA LEESHARH!! HABA AI
JININ NIGERIA BADAGA NAN BA, KOWA SAI YA JIRA ALLAH KUWA!!.

Wucewa ta yi tana tinanin in dai tana san yin magananinsu to dole ta kasance tana
da kusanci da Ramish sosai, ta hakance zata sanyasu su da kansu su kama kansu. Da
wannan tinani a ranta ta yi wanka ta shirya cikin haɗaɗɗen arabs abaya, ta ji
yayansa zai je ɗaukowa, sai ta shirya da kyau dan kun san siririki ne
Smart........... 😅

Ba karya ta yi fitina sosai cikin white abayan, ta yi rolling veil a kanta, ta
ɗauki karamar fashion bag and flat shoe dik white color kalar rigar, sai tashin
kamshi take zubawa ta nufi bedroom ɗinsa. Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo cikin
room ɗin. Yana zaune a in da ta barsa hannunsa rike da cup of cappuccino, yanzu
tsohuwar ta kawo mashi cappuccinon da kayan abincin ta fita, har ta sake shirya
masu wani kenan, yanzu ya ɗauki cappuccinon bai kai ga sha ba!!.

Ai tana gani bata san lokacin da ta ƙariso cikin room ɗin da sauri ba, shi kuwa
yana ɗaura idanunsa a kanta ya kafeta da kallo, ta yi fitina sosai, yanzu a ƴan
kwanan nan wani irin sihirtatcen kyau take karawa na musamman. "Yah Ramish
cappuccino zaka sha?". Ta jefa mashi tambayar a ya yin da ta iso wajensa. Kai ya
jinjina mata haɗe da cewa. "Aesh you're so pretty, zo ki sha cappuccino sai mu tafi
ko? Lokaci na kurewa". Ya kai karshen maganar tare da kai cup ɗin bakinsa da nufin
ya kurɓa.

Ai bata san lokacin da ta tafi kamar zata faɗi cikin dabara ta buge cup ɗin ya faɗi
ƙasa ba, cup ɗin ya fashe cappuccino ya zube a ƙasa. A hanzarce ya ɗago kai yana
ƙoƙarin yin magana sai faɗowa ta yi jikinsa mai gabaɗaya tare da fara salatin karya
a zuwan zamewa ta yi ta faɗo jikinsa ba da gangan ba.

"Aesh lafiya kuwa?". Ya faɗa yana kallon face ɗinta, ta datse idanu wai irin ya
zaci da gaske ne ma. Yunƙurawa ta yi zata bar jikinsa saboda shegen iya basaja.
Rikota ya yi yana kallan face ɗinta. "Aesh yakamata in kai ki hospital a dubaki,
naga kamar jiri yana damunki".

Ya bata satar amsa, sai kuwa ta ce. "Nima abin yana bani mamaki, kawai ina tsaye na
ji jiri ya ɗebeni". Sorry ya ce mata tare da kai hannunsa ɗaya saman goshinta ya
taɓa. "Ga shi jikinki babu zafi, amma dik da haka bari mu dawo zan ɗauki mataki".
Langwaɓewa ta yi a jikinsa wai irin ta kara nuna bata da lafiyar nan.
"Aesh ko dai mu wuce hospital ɗin nan ne?". A ɗan rikice ya yi maganar. "A'a mu
je airport ɗin dai mu dawo". Ta faɗa tana sake yunkurwa zata bar jikin nasa. Sake
riƙota ya yi, take suka zubawa juna idanu a kurkusa, wani irin kallo mai cike da
sirrika suke aikawa junansu.

"Idan kika tashi jiri ba zai sake ɗibarki ba? Ko in kaiki mota da kai'na?". Ya faɗa
idanunsa sosai a cikin nata. Ƙasa iya basa amsa ta ta yi, abin da yake cikin
zuciyarta yana neman fin karfinta.
"Aesh" ya faɗa yana mai da kallansa kan soft lips ɗinta da suke ɗan kerma kamar
mai jin sanyi. Bata iya amsawa ba. Zai sake yin magana wayarsa ta fara ringing.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Let's go, kinga kin sa har jirginsu ya sauka
ban isa airport ba, dan ma babu nisa nan da 5 mins zamu isa". Ya kai karshen
maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa. A haka suka nufi waje. Ajiyar zuciya ta
sauke, hankalinta ya kwnata, burinta na ɓata mashi lokaci ta hana shi shan wani
cappuccino ko cin wani abin ya cika.

Sai dai daga shi har ita basu lura da cappuccinon da ya zube a kasa ba, ya canza
kala daga brown zuwa dark green sosai, kamar ba cappuccino ba, suna fita wannan
tsohuwa ta yi gaggawar zuwa domin tattare komai, a gaggauce ta goge cappuccinon da
ya zube, tasan basu sha komai ba, dan dik abin da suke faɗa kada ku manta tana
jinsu, ranta bai so hakan ba sam, ranta ya sosu, haka ta kwashe kayan abincin ta
fita da shi tana tinanin irin hukuncin da zata yi wa Leesharh, ba zata kyaleta ba
sai ta hukuntata! Dan tana ganin kamar ita take sanya Ramish yana tsallake
tarkonsu, kuma hakan ce, sau da dama Leesharh tana shiga tsakaninsu ba tare da ta
san ta shiga ba, kamar dai yadda ta ɓarar da abincin ɗazun da suka yi karo, kun ga
bata san akwai wani abin a cikin abincin ba ta ɓarar, to haka dayawan lokuta sai
sun yi shiri a kansa sai ta shiga tsakani ta watsa komai.

Daren jiya Ramish zai fita ta hana shi ta hanyar ce mashi tana tsoro kuma ita ba
zata iya fita waje a daren nan ba bare ta bisa, haka ya fasa fita, kuma sun shirya
mashi mugun abu a fitar da zai yi, kunga Leesharh ba tare da saninta ba a nan ma ta
shiga tsakaninsa da su!!.

---------------------------------------🔥🔥

Bai direta a ko'ina ba sai a cikin mota, da gudun gaske ya shiga ya figi motar suka
bar gidan. Saboda gudun da yake yi yasa suka yi saurin isa airport, a dai'dai
lokacin su Smart suka fito daga cikin jirgin yana rungume da gawar Auta. Ai Ramish
yana ganinsu haka bai san lokacin da ya ɓalle kofar motar ya fito waje ba, take ya
ji zuciyarsa ta amsa, hankali nan da nan ya tashi, a ruɗe ya ce. "Yah Omerish
meyake faruwa? Meyasameta?".

Dai'dai lokacin Bilal ya yi parking motarsa shi ma ya fito. Smart bai yi magana ba
ya buɗe gidan baya na motar Ramish ya kwantar da Auta a ciki, sannan ya yi juyo ga
su Jaish. "Ku bi Bilal izuwa gidan uncle, bari in je ni da Zunaira, ka kula da
Omar". Fitowa ita ma Leesharh ta yi daga cikin motar tana kallan Smart, sai da
gabanta ya faɗi yadda ta ga face ɗinsa.

"Aesh shiga gidan baya ku zauna da Zunaira". Cewar Ramish kenan. Da sauri ta
shiga tana kallan Smart, ta ɗaga kan Auta ta ɗaura a saman cinyarta, sai a lokacin
ta lura da guyson, Allah sarki ta jima rabonta da shi, tin da ya koma kingdom of
power bai sake zuwa Dubai ba, ta yi kawarsa sosai mutumin kirki. Gidan gaba na
motar Ramish Smart ya shiga ba tare da ya yi masu magana ba, yau first time na
haɗuwar Smart and Ramish face to face kenan, Ramish ya ci burin ya haɗu da yayan
nasa mai tayasa aiki mai taimaka mashi, sai dai sun haɗu a wani irin yanayin da
word can't explain how they're feeling, sai ma lokacin da su Ramish zasu fahimci
Zunaira bata raye, uhm!!.

Bilal na kallon Ramish har cikin ido, ba dan Smart dake wajen ba da babu abin da
zai hana bai ci kwalar rigar Ramish ya faɗa mashi dalilinsa na gudunsa ba, ya
kirasa a waya baya ɗauka, ya nemesa kamar hauka bai gansa ba, wlh har kuka sai da
ya yi da hawayensa, ashe dama Ramish yana cikin Dubai, to me ya yi mashi da zafi
har haka da zai yi mashi irin wannan hukunci? Tare suka taso, tare suke komai, rana
tsaka Ramish ya gujesa dole abin ya gigita shi, har rama sosai ya yi wlh,
albarkacin Smart yasa bai yi magana ba, yasan koma menene yanzu tin da yayan nasu
yana nan zai warware masu komai, zai aje ye su ya ji menene ya haɗasu faɗa.

Shi ma Ramish kallon Bilal ɗin ya yi ido cikin ido, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta
damu, wlh yana bala'in son ɗan uwan nasa fiye da kansa, dik sai ya ji bai kyauta
ba, ko da Bilal yana da sa hannu a cutar da shi bai kamata ya juya mashi baya ta
irin wannan sigar ba, kuma yasan Bilal ɗin ba zai iya jurewa ba, amma haka ya
sharesa, gaskiya bai kyauta ba, take ransa ta ɗacaca, haka ya shiga mota ya tayar
suka bar airport ɗin zuciyarsa cike da tinani kala kala. Bilal ma zuciyarsa tana
zogi ya tada motar suka wuce gidan Abbie.

Suna fitowa airport Ramish ya ce. "Yah Omerish ina zamu je?". Kai tsaye Smart ya
ce. "Gidanka, and kada ka bari kowa ya san muna nan, kada momma ta sani shiyasa ban
wuce family house ba".

Shin kun san dalilin zuwan Smart Dubai kuwa? Zai fara ne daga kan King Badeen
kakansu kenan, wato Akka bata isheshi gani ba, bari ya fara da mai bawa Akkan da
kanta umarni kafin ya koma kansu, yanzu zuwan na King Badeen ne, sai sun faɗa mashi
a wace aya ce Allah ya banbanta mutane, ya ce kuma a yi banbaci kamar yadda suke
yi, tun daga nasi har bakara sai sun nuna mashi a in da ya ce mai arziki mai daraja
ne mara arziki kuma mara daraja ne, uhm abin babba ne. My people's ni fa bana san
kanku ya ɗauki zafi sosai shiyasa nike sake maku cakwakiyar nan a hankali hankali,
kun gane ai?. Ina tausaya maku ne.......🥱

"In Sha Allah babu wanda zai san kuna nan, amma Yah Omerish please tell me meya
samu Zunaira". Cikin raunin murya ya yi maganar. "Mutuwa ta yi". Smart ya faɗa can
ƙasa ƙasa. Ai wani irin mahaukacin birki da Ramish ya taka sai da Smart ya buga
kansa da jikin glass na door, tashin hankali, ita kanta Leesharh bata san time da
ta zabura ba!!.

Ƙasa iya yin magana Ramish ya yi, tamkar wanda aka datsewa baki, da bai taka burki
bama ai da mutuwa zasu yi, dan babu abin da zai hana bai saki kan motar nan ba,
irin wannan tashin hankali. A miliyan ya juyo da kallansa a kan Smart da yake
kallon hanya, da hannu ya yi mashi alamar da ya kunna motar su je. Kasa yin magana
Ramish ya yi, sai yake jin kamar kunnuwarsa basu ji mashi abin da yayan nasa ya
faɗa daidai ba, yana san sake tambayarsa tongue ɗinsa ta yi mashi wani irin balai'n
nauyi. Sake nuna mashi hanya Smart ya yi a kan su tafi, dan dole ya tashi motar
yana ta faman sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah yasa ba dai'dai kunnuwarsa
suka ji mashi ba.

Sai ƙoƙari haɗa kalmomu dake kama da mutuwa a cikin zuciyarsa yake

Please Login or Register in order to submit comment