You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasu yi
nasara, dan haka sai ya ce. "Zan koya maki amfani da shi, amma yanzu dai ki bani
wani amsa da tin last week nike ta san sanin shi, daga nan sai ki bani labari a kan
bayyanar Imam Mahadi, sai ki koya mun yadda zan yi ibada".

"Yayanka baya kallanmu ko?". Ta jefa mashi tambayar cike da damuwa tare da addu'ar
Allah yasa Black Tiger bai gansu ba, ta manta ne kwata kwata ta saki baki tana ta
magana.

"Nan cikin ɗakinsa ne, kuma na faɗa maki yana iya kallan ko'ina a cikin birnin nan
amma ban da cikin ɗakinsa, dan yana ganin wannan mallakinsa ne komai dake ciki sai
da izininsa zai motsa".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa godiya ga Allah da yasa a ɗakinsa suke, sannan
ta ce. "Me kake san tambayata tin last week?".

MY BEST PART AGAIN💘🦋

"Kin san na faɗa maki ina kaunar annabi Isa sosai, to shi ne fa na duba cikin
litattafan addinin Kiristanci wato Bible dan na duba tarihinsa da ƴan uwansa, a nan
ne na duba tun daga kan Annabi Ibrahim wato daga tushensa kenan, tsawon sati ina
bincike ina karantawa, sai da na zo kan ƴaƴan Annabi Ibrahim ɗin ne na rikice, abin
ya tsaya mun a rai ina san sanin gaskiya".

Ko kaɗan bata yi mamakin jin maganarsa ba, kuma bata so ta ji me ya rikita shi
ba, dan a tarihin Annabi Ibrahim akwai abin mamaki, tasan bai wuce batu a kan
Annabi Isma'il da Annabi Ishaq bane, dama su tarihinsu yana da ban mamaki da ɗan
rikitarwa, sai ka yi karatu mai zurfi zaka iya ganewa, shi kuma bai zurfafa ba dole
ya ɗan rikice.
"Kin san me ya rikitar da ni?". Ya katse mata tinani ta hanyar jefa mata tambaya.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba..
"Abin da ya rikitar da ni shi ne, ance Annabi Ishaq shi ne rushen bani
Isra'ila, shi kuma Annabi Isma'il shi ne tushen larabawa, kuma naga dikkansu ubansu
ɗaya ne wato Annabi Ibrahim kenan, to ina san ki babbance mun ya aka yi zuri'arsu
ta banbanta bayan kuma iyayensu guda ne, basu taso dikka a matsayin tushen larabawa
ba, ya aka yi bani Isra'ila suka fito a tushen larabawa kuma?".

Ɗan gyran murya ta yi, wuyarta ya fara ɗan yi mata zafi, saboda jimawa da ta yi
tana magana, bata gama samun sauki ba. Abin mamakin kuma shi ne Ronnie fa bai samu
damar ganin ciwon wuyar nata ba, sam bai gani ba, shi a tunaninsa ma zazzaɓi ko
ciwon kai ya kawota wannan ɗakin, shiyasa kuka ga hankalinsa bai wani tashi sosai
ba, da ya gani ai da tashin hankalin da zai shiga abin zai sha gaban tinani, sanin
zai shiga damuwa yasa Black Tiger ya yi amfani da magic wajen rufa mashi ciwon ya
hanasa gani.

Kuma da ya ga ciwon na zai sanyata yin surutu dayawa ba.

Cikin nitsuwa da sanyin murya ta fara faɗin.
"Haƙiƙa Annabi Ishaq da Annabi Isma'il Alaihimus Salam sun kasance ƴaƴan
Annabi Ibrahim (AS) ne, amma sun bambanta ta fuskar zuriyarsu da yadda aka danganta
su da al'ummomi. Ga bayanin yadda suka banbanta da dalilin da ya sa Annabi Isma'il
(AS) ba a danganta shi da Bani Isra'ila ba ya kasance shi ne tushen larabawa".

Ɗan jan dogon numfashi ta yi kafin ta ɗaura da cewa. "Annabi Isma'il (AS) ɗan
Annabi Ibrahim (AS) ne daga mahaifiyarsa Hajara, wacce ta kasance daga ƙasar Misra.
Zuriyar Annabi Isma'il kuma ta yi ƙaura daga Misra zuwa yankin Makkah, inda aka
kafa zuriyar Larabawa ta asali keman, wato Larabawan Adnaniyya. Annabi Muhammad
(SAW) fiyayyen halitta kenan shi ma ya fito ne daga zuriyar Annabi Isma'il (AS)".

"Annabi Ishaq kuma, ɗan Annabi Ibrahim (AS) daga mahaifinsa Sahra, wacce ta kasance
matar farko ta Annabi Ibrahim (AS). Zuriyar Annabi Ishaq ta ci gaba da rayuwa a
yankin Sham (Palastine a yanzu kenan) daga cikinsu ne Bani Isra'ila suka fito,
waɗanda suka hada da Annabi Ya'qub (AS) mahaifin Annabi Yusuf kenan".

"Wannan suna na bani Isra'ila yana nufin zuriyar Annabi Ya'qub (AS) shi Annabi
Yaqub ɗim shi ne Isra'ila, ainahin sunansa kenan Isra'ila, waɗan nan ƴaƴansa goma
shabin nan da suka cutar da kaninsu Annabi Yusuf su ne suka ci sunan bani Isra'ila,
wato yayan Isra'ila kenan. Dan haka dik manzannin da suka fito daga cikin zuriyar
Ya'qub, irin su Annabi Musa, Annabi Dauda, Annabi Sulemanu, Annabi Isa (AS), duk
daga zuriyar Annabi Ishaq (AS) suka fito, kuma sunan bani Isra'ila ya shafesu".

"Annabi Isma'il ba ya cikin zuriyar Isra'ila saboda shi ba ɗan Annabi Ishaq ba
ne, kuma ba daga zuriyar Ya'qub yake ba. Dan haka Annabi Isma'il (AS) shi ne asalin
zuriyar Larabawa waɗanda suka rayu a yankin Makkah".

"A taƙaice yadda zaka fi ganewa shi Annabi Isma'il (AS) ya yi rayuwa a Makkah, kuma
an kafa al'adar ibadar Hajji tare da mahaifinsu Annabi Ibrahim (AS). Annabi Ishaq
(AS) ya rayu a Palastine kuma ya zama tushen addinin yahudawa da kiristoci, ta
hanyar zuriyarsa Isra'ila. Saboda haka dik wanda ba ya cikin zuriyar Annabi Ya'qub,
ba a kiransa Bani Isra'ila, to kaga Annabi Isma'il (AS) ba shi da alaƙa da zuriyar
Ya'qub saboda shi wani reshe ne na zuriyar Ibrahim (AS) wanda ya yi rayuwarsa a
yankin Larabawa".

"Alqur'ani mai girma ma ya ya yi magana a kan, cikin Suratul Saaffaat, aya ta 112
zuwa ta 113, Allah ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (AS) ya kasance asalin dukkan
Annabawa, amma Allah ya sa zuriyarsa biyu daban daban, haka cikin suratul Maryam
Allah ya bayyana Annabi Isma'il a matsayin manzo ga Larabawa, ka fahimta ko akwai
sauran abin da baka gane ba?". Ta yi maganar tana kallansa.

Sosai Ronnie ya fahimci dik abin da ta faɗa, kuma hakan tasa ya kara ganin
girman Allah matuƙa, ya samu karin ilimi, yanzu yasan cewa ga daga zuriyar da
Annabi Isa ya fito, ashe da Annabi Isa da Annabi Muhammad dik kakanninsu guda ne,
ɗaya dai ya fito ta gefen Annabi Ishaq ɗaya kuma ya Annabi Isma'il, amma dikkansu
kakansu ɗaya ne wato Annabi Ibrahim, lallai Allah da girma sa hikima yake.

Ganin ya yi shiru bai bata amsa bane yasa ta ce. "Ko dai baka gamsu bane Ronnie?".

A hanzarce ya girgiza mata kai haɗe da faɗin. "Sosai na gamsu, jinjinawa girman
lamarin Ubangiji nike yi shi ya ja hakan, amma kema ai kinsa ba zai taɓa yiwuwa ki
yi wa mutum bayani bai fahimta ba ko? Dole ya fahimta dik toshewar ƙwaƙwalwarsa,
magana cike da hujoji yadda yakamata, kai ke dai kin ji daɗi".

Ajiyar zuciya ta sauke, a nitse ta ce. "Kana burgeni Ronnie saboda son neman
iliminka, kana san sanin dikkan abin da baka sani ba, ina addu'ar Allah ya kara
buɗa maka ƙwaƙwalwarka, ka cigaba da bibiya kana tambaya ta dik wani abin da baka
sani na, In Sha Allah idan na sani zan sanar da kai".

Jinjina kai ya yi alamar to, sai ya ji tamkar ya kwace dikkan ilimin dake kanta ya
zuba a nasa kan, baya gajiya da neman ilimi shi dai a rayuwarsa.

Cigaba da jefa mata tambayoyi dangane da addini ya yi tana bashi amsa, haka suka
kasance cikin farinciki har time da barci ya ɗauketa, kin fita daga ɗakin ya yi ya
zauna yana ya kallanta cike da farinciki, Allah sarki har yanzu kuma bai san da
ciwo a wuyarta ba.

Ina kaunar addinina my people's, hakan yasa nake bala'in san part ɗin birnin Black
world da kuma Sweetie, dan addinina, wayyo musulunci duniya ce jama'a, Allah ka
kashemu muna masu yi maka bauta babu gajiyawa, kasa kalmar shahada ta zama kalmarmu
ta karshe a duniya.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

KINGDOM OF POWER.

Alƙalamina ba iya nishaɗantarwa da faɗakarwa haɗe da ilmantarwa kawai ya tsaya ba,
har da bawa ƴan uwana Sa'a da zai canza ya kuma inganta masu rayuwa, ba sai kin
zauna kina ta bani bani bani, za'a yi taro a cikin dangi kece a baya dan baki da
shi, miji ya gaji da baki kuɗin shiga ƴan uwa, kina zaune dirshan ba zaki nemawa
kanki mafita ba. To Alhamdulillah Allah ya bamu ilimin sanin wasu abubuwa, dan haka
na zaɓi sanar da mutane na dan ki fita daga jerin bani bani da kike ta famar
ɗaurawa miji, kema ki nemi kuɗinki a dama dake, ko ke budurwace a gida zaki rinƙa
yin saarki dan ki ragewa mama da baba wasu ɗawainiya, fatana dai kowacce ta kasance
cikin farinciki a rayuwarta duniya da lahira, Allah yasa mu dace, bari in koya maku
yadda ake yin sabulun wanke kaya, yana da riba sosai, zaku samu na kanku, kuma shi
abu ne wanda ake saya kullum dan wanke dauɗa, a yadda komai ya yi tsada idan kika
haɗa shi kika ɗan yi ƙasa da farashi wlh ba ƙaramin alkhairi zaki samu ba, ki jikan
na kasa dake a dik abin da zaki sa a gaba sai Allah ya jikanki ya dafa maki kema,
wlh zaki samu alkhairi sosai a wannan sabulu, makota zasu yi ta shigowa su saya
hankalinki a kwance kina ajiye ƴan kuɗaɗenki ki huta da bin miji ya baki ya baki.

Ga abubuwan da zaki buƙata.

Sabulun wanke kaya yana buƙatar kayan haɗi masu wanke ƙazanta sosai, musamman
sinadaran da ke yaki da maiƙo da datti. Ga yadda ake haɗa shi:

Kayan Haɗi. Caustic Soda shi wannan ana amfani da shi ne don samar da tushe (base)
ga sabulun. Shi ne na farko. Sai ki samo soda Ash (Sodium Carbonate) Sai sulphonic
Acid, wannan yana bayar da kumfa sosai. Sai STPP (Sodium Tripolyphosphate) sai
Perfume don ƙamshi. Colorant Idan kuna son ƙara launi. Sai Ruwa don haɗin.

Yadda zaku haɗa.

Ki zuba Caustic Soda (10%) a cikin ruwa wanda ya danganta da yawan kayan haɗinki,
sai ki barshi ya narke na tsawon awa 24.

Shi ma Soda Ash (5%) ki saka shi a nasa ruwan daban ya narke na tsawon awa 12 zuwa
24. Haka shi ma STPP (2-3%) ki narkar da shi a nasa ruwan kamar dai sauran na baya.
Idan suka kai waɗan nan awanni sai ki ɗaukosu, soda ash zaki juye cikin caustic
soda, ki gauraya sosai, sannan sai ki juye sulphonic acid, shi ma ki gauraya sosai,
sai ki zuba stpp shi ma, a cikin babban waje da zasu samu space zaki zubasu ki haɗe
fa. Ki zuba ruwan dai'dai da yanayin kayan haɗinki, idan kinga ya yi kauri sosai
zaki iya kara ruwa.

Ki tabbatar kin juya sosai ya haɗe jikinsa ko in ce sun haɗe jikinsu. Sai ki zuba
perfume and colorant, sannan ki rufe ki barshi na awa 24 kafin ki yi amfani da shi,
idan kina son fitar da shi shape by shape zaki iya sayan shapes ɗin ki zuzzuba a
ciki ki barsu su kame jikinsi.

SHIKENAN KIN HAƊA SABULUNKI, IN SHA ALLAH ZAKU RINƘA SAMUN SANA'O'IN DA ZASU RINƘA
YI A CIKIN GIDA DAN TSIRA DA MUTUNCINKU WANDA KUMA JAMA'A ZASU SAYA, DAN DIK KAYAN
AMFANI WAƊAN DA AKE AMFANI DA SU YAU DA GOBE ZAN KOYA MAKU, WAƊAN DA DOLE ZA'A
SAYESU DA AMFANI.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬
19



••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

KINGDOM OF POWER.

Zaune Momma, Mama Haulat and aunty MieMie suke a parlourn momma, mama Haulat tana
zaune a ƙasa, Aunty MieMie da momma a saman sofa, babyn Khadija yana rike hannun
momma, ya sha kwalliya cikin wasu irin kayan sanyi masu bala'in kyau wanda momma da
kanta tasa uncle Taheer ya je shopping ya saya mata su, kayan baby dayawa ya sayo
mata, yaro sai sakawa yake yana kara canzawa abinsa, har ya murmure, amma matsalar
ɗaya shi ne bai samu nonon uwa ba, ko sau ɗaya bai ɗanɗana ba, Allah sarki.

Cikin sanyin murya momma ta fara magana tana kallan Aunty MieMie. "Raeesa kamar
yadda na faɗa maki cewar wannan yarinya matar Jaish ce to hakan take, yau da safe
na same shi a bedroom ɗinsa domin muyi maganar da shi, sai ya nuna mun shi wlh baya
santa, hasali ma ba zai taɓa zama da yar kauye wadda bata yi karatu ba, ya nuna
baya santa kuma ba zai taɓa santa ba, har da ce mun shi bashi da lokacin mace a
yanzu, shi ma daddynku ya kafe a kan bayan santa, wai sai dai a warware wannan
aure".

Ɗan zaro idanu Aunty MieMie ta yi, cike da mamaki ta ce. "Amma kuma momma menene
laifin yarinyar nan da zasu ce basa sonta?". Allah sarki, ita Aunty MieMie ko kaɗan
bata ji kyamarsu Mahreen ba, wato mufa Nigerians dik in da muke mun fita daban,
jinin ɗan Nigeria musamman ɗan arewa ci wlh baya kyamar kowacce yare da kabila,
zama muke da kowa da zuciya ɗaya, sai dai a nuna mana kabilanci da wariya, amma mu
bana nunawa, kowa ɗaya muka ɗaukesa, lallai ya tabbata jinin Nigerians na gudu a
jikin Aunty MieMie, jama'a ku tafa mata, bata bar gida ba baiwar Allah.

"Hmmm shi dai Jaish kin ji dalilinsa, wai saboda yar kauye, yar datti, ba karatu
ce yasa baya santa". Cewar Momma kenan.

Ɗan siririn tsaki Aunty MieMie ta je. "To shi kuma daddy menene dalilansa na
kinta?". Cewar Aunty MieMie.

Shiru momma ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Saboda kin san halinsa ai, wai akwai
qualities da yake sanwa ƴaƴansa a matan da zasu aura".

"To yaga ita Mahnoor ɗin ne da zai ce bata yi ba?".
Kai momma ta girgiza mata kafin ta amsa da. "A'a bai ganta ba tukun nan, na dai
ce ya bani sati guda zan kawota ya ganta, in ya ganta sai ya yanke hukunci".

Shiru suka yi Aunty MieMie tana tinanin mafita.

Katsesu momma ta yi da cewa. "To shi ne yanzu nike san mu yi shawarat ta
yadda zamu haɗa mata dik wasu qualities ɗin da suka dace ta yadda idan ya ganta zai
bada goyan bayan Jaish ya zauna da ita, ni bani da matsala ta ɓangaren Jaish, dan
nasan ba zai saɓa umarnina ba, matsalar daddynku ya aminta da ita ne kawai, kunga
idan aka raba auren nan magana ta domin Allah an cutar da yarinyar nan da iyayenta,
bana jin kamar ko shekaru 15 ta cika, sannan dik bama wannan ba, Mahnoor ta dace a
matsayin matar Jaish wlh, iyayenta sun yi mana halacci na wuce misali, bai kamata
mu saka masu da sharri ba".
Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, tabbas dik abin da momma ta faɗa gaskiya ne, bai
kamata a yi wa Mahnoor wani abin da ba dai'dai ba, domin yarinyar ta kai dik wani
matsayin da ake buƙata matar Prince ta kasance, ta cike dik wasu qualities, ilimin
bokon ne dai kawai ya rage mata wanda shi dama ai ba dashi ake zuwa lahira ba, bai
zama wajibi ba, rashinsa ba zai hanata zaman aure da kyautatawa mijinta ba, ta samu
babban wato ilimin addini, dik wasu abin da ake koyarwa a bokon tushensu daga
inane? Dik daga litattafan addini ne, dan haka Mahnoor bata da wata gazawa. Iya
shege ne kawai irin na Jaish.

"Ranki ya daɗe zan iya yin magana?". Cewar mama Haulat dake binsu da
kallo....... Jinjina mata kai alamar e Momma ta yi ba tare da ta yi magana ba.

"Ni a ganina tin da haka ne ai matsala ce mai sauki, sai mu gyarata, ta sha gyara
sosai, a samu wanda zai fara koya mata karatu Kafin wani ɗan lokaci, ta goge ta
canza, In Sha Allah zai sota, kuma shi ma mai martaba zai kaunaceta ya karɓeta a
matsayin sirika".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi tare da cewa. "Wannan shawara ce mai kyau, sai dai
kuma ina da kari a kan shawarar".

Zuba mata idanu momma ta yi alamar tana sauraronta kenan.

Cigaba ta yi da cewa. "Momma kada ki sake yi wa Jaish maganarta, tun da kin bawa
daddy sati ɗaya, to a cikin wannan sati ɗayan kada a yi magana da kowa, mama Haulat
ki gyara mana ita, sai ki fara koya mata wasu abubuwan da suka dace dan kauyancin
nan da rayuwa kamar na dabobi ya fita a kanta, kun san idan nan da sati ɗaya aka
kaita gaban daddy ya aminta da ita to a bisa doka daga ranar zata koma part ɗin
Jaish, sannan zata zamana ita kaɗai alhakin kula da cinsa da shansa zai rataya a
wuyarta, kun san yadda doka yake babu wadda zata sake kusantar abin da ya danganci
cinsa, shansa da wasu privacy nasa ko?".

Jinjina kai mama Haulat ta yi, ita kuma momma still dai tana binta da ido bata
furta word ba.

Cigaba ta yi da cewa. "Dole za'a haɗata da mama Haulat a part ɗin nasa dan ta
tayata yakarsa, kun san halin Jaish da shegiyar murɗiya, mama Haulat ai ɗan ɗakinki
ne shi kin san halinsa, dan haka ke zaki ɗaurata a hanyar da ta dace domin ta
tabbata a matsayin matarsa ya kuma sota, dan haka wannan ragama mun rataya maki shi
a wuyarki ko ya kika ce momma?". Ta kai karshen maganar tana tsayar da idanunta a
kan momma.

Jinjina momma ta yi, sannan ta ce. "Tabbas wannan shawara ta yi, yanzu Haulat ki
dage kafin nan da sati guda ki canza mun ita, ta yi kyau sosai, idan Allah ya
ɗoramu a kan daddynsu muka yi nasara sai ki bita part ɗin Jaish ɗin kina cigaba da
koya mata abubuwa da yi mata gyara, ban yarda da wata kuyanga da ta shiga lamarinsu
ba face ke, da ke kaɗai na yarda a gidan nan, nasan zaki kula da su dikkansu biyu,
kin san abin da yake so da wanda baya so, dan haka sai ki ɗaurata a kan hanyar da
ta dace, wlh ina san Jaish da wannan yarinya, ban san dalili ba".

Cikin girmamawa mama Haulat ta karɓi wannan ragama da suka bata tare da tambayar ko
akwai wani abin da za'a ƙara sanar da ita?. Aunty MieMie ce ta amsa mata da babu
komai zata iya tafiya ta je ta fara aikinta daga yanzu, wato ta je ta ɗaukesu izuwa
wajen gyara yanzu kenan, tare da Mahreen za'ayi masu komai dan a ragewa Mahreen ɗin
ma wannan hauka da yake a kanta.

Miƙewa mama Haulat ta yi ya nufi waje tana yi masu addu'oi masu tasiri da ratsa
zuciya.
Tana fita uncle Jahiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Zeezee tana biye da
shi a baya, dama Aunty MieMie tana ƙoƙarin ɗaukowa momma zanjen babyn nan dake kama
da shi ne sai ga shi ya shigo.

Dan haka cikin girmamawa suka gaisa. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare
da umartan Zee da ta zauna a kusa da Aunty MieMie.

Kin yarda ta yi, ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai, ta ji sauki sosai jiki ya yi
kyau Masha Allah, ita dai ta samu sallama, saura Khadija da mai keken napep ɗinsu
da shi ma ya farfaɗo yana ta fama da nashi jinyar bawan Allah.

Zee na ƙoƙarin zama a ƙasa idanunta suka hango mata babyn Khadija dake hannun
Momma, ai kuwa zubur ta miƙe, ita da bata san a ina take ba, bata san ba a gidan
wargi take ba, bata san a gidan sarauta masu izza da ji da kansu take ba, sai ta
miƙe a zabure tare da nufar momma da nufin ta kwace babyn.

Tsawa Aunty MieMie ta daka mata tana faɗin basa san shirmen banza, ita bata san a
gaban wa take bane? Gaban princess Rahilarh take, dole ta nitsu ta jira komai sai
an bata izini, su sarauta ba'ayi masu irin wannan wautar.

Shi ma uncle Jahiz dama ya buɗe baki zai dakatar da ita daga tinkarar momma ɗin ne
sai Aunty MieMie ta rigasa, dan haka sai ya ja bakinsa ta datseta cif.

Allah sarki Zee, jikinta sai rawa yake yi, burinta ta karɓi ɗanta ɗan ƴar uwarta,
yau sama da sari biyu kenan tana rokon da abata shi ta ga jininta, amma bata samu
dama ba, ta tsumu da san ganinsa har ta gaji, kullun idan uncle Jahiz ya je dubasu
sai ta yi mashi kukan ina yaronta, yau dai da aka basu sallama sai ya ce ta zo su
je ta ga ɗanta, shiysa yanzu da ta gansa ɗauki yasa ta rasa nitsuwarta, ta rasa
control ɗinta, kuma ya haɗu da bata san a gaban wa take ba, shiysa ta yi saurin
miƙewa zata je ta karɓesa, shi kawai idanunta yake hango mata, sam bata ga su momma
ba baiwar Allah.

Ai ƙasa komawa mazauninta ta yi, sai kawai ta tsaya a wajen cak tare da rushewa da
kuka mai tsuma zuciya, dama a kusa take, kiris take jira ta fashe dama.

Da saurin uncle Jahiz ya miƙe ya nufota, cike da gimamawa ya fara faɗin. "Sarauniya
momma ayi mana afuwa, na tabbata ɗauki ganin babyn yasa ta rasa control ɗinta, and
bana tinanin tasan in da take shiysa dik ta yi wannan shirmen". Ya kai karshen
maganar yana rike hannunta.

Baya kaɗan ya jata izuwa in da ta miƙe, cikin nitsuwa ya mayar da ita ya zaunar.

Momma da tausayin Zee ya gama narkar da zuciyarta ne ta umarci da su rabu da ita ta
matso taga ɗanta, ai jini ba wasa ba. A tinanin momma Zee ita ce uwar ɗan.

Ai Zee tana jin an bata dama ta yi saurin miƙewa ta isa gaban momma, jikinta har
rawa yake yi wajen kai hannu, tin ba'a miƙo mata shi ba ta karɓesa. Aunty MieMie ma
tausayinta ta ji ya kamata, Allah sarki jini ba wasa ba, sai kerma hannunta yake yi
ta rike yaron gam idanunta suna ciccikowa da kwallah.

Momma mace mai dattaku, hannu ta kai tana dan shafa kanta da yake Zee ta zube
gwiwowinta a ƙasa gaban momma ɗin ne da ta karɓi yaron. Rarrashinta momma ta fara
yi tare da ƙara mata kwarin gwiwa a kan ta koyi jajircewa.

Aunty MieMie ma data ga hakan sai ta tsoma baki suka fara rarrashinta a tare. Uncle
Jahiz ne ya fayyace masu cewa Zee fa ba ita ce uwar yaron ba, sisterta ce uwar
yaron. Dik da suka ji hakan sun tausayawa Zee sosai, dan daga yadda ta nuna
reaction ɗinta a kan yaron nan alamu sun nuna akwai damuwa.......... Wai dan ma
basu san tarihinsu ba kenan, da sun sani sai yaya kenan?. Ai su Zee su suga rayuwa,
sun sha gwagwarmaya kam ba kaɗan ba.
Shiru parlourn ya ɗauka na ɗan lokaci, sai shessheƙar kukan Zee ne yake tashi a
hankali hankali gwanin ban tausayi.

Aunty MieMie da ta lura kamar akwai yunwa sosai a tattare da Zee sai ta ce
yakamata a kawo mata abinci ta ci. Momma ma ta lura da hakan, sai ta amsa da
yakamata kam.

Aunty MieMie ce ta mika hannu ta karɓi babyn daga hannunta, sannan ta ce uncle
Jahiz ya sanya a kawo mata abinci ta ci. Sam bata tambayi wacece Zee ba, dan su
suna da ɗabi'ar dik wanda suka gani a tare da ɗan uwansu to fa zasu bashi
mahimmanci. Tun da suka ganta tare da uncle Jahiz sun san ba banza take ba, saboda
su basa kula abu idan ba ya kasance ya shafesu ba.

Miƙewa uncle Jahiz ya yi ya nufi waje. Jim kaɗan ya dawo tare da wasu kuyangu
guda biyu da suke ɗauke da tampatsetsan tray mai girma, shake take tap da abinci
launika daban daban da a kallah zasu kai kala goma. Kun san larabawa da yawan girke
girke kala kala.

Kai tsaye saman dining table na momma suka nufa suka shirge abincin, ga kayan
drinks kala kala, ferfesu kaji dana ɗawisu, kun san gidan sarauta suna da ɗawisu
sosai, ga dahuwar Chinese rice kala daban daban, kai waɗan nan tray sun haɗe komai,
har da kayan marmari.

Umartar Zee ya yi da ta tashi ta je ta ci abinci, da yake parlourn yana da girma,
daga wajen da table ɗin yake zuwa in da suke akwai tazara mai tsayi.

Da yake yunwa baiwar Allah take ji sai bata musa ba ta tashi, jikinta har ɓari yake
yi ta nufi wajen table ɗin. Da kallo suka bita har ta kai wajen, sannan suka dawo
da kallonsu a kan uncle Jahiz dan jin wacece ita daga ina kuma ya samosu.

Yasan abin da suke wa binsa da kallo, karin bayani suke jira ya kora masu. Dan
haka cikin nitsuwa ya yi gyara murya kafin ya fara kora masu dik abin da suke
tsumayan jira daga garesa. Ya yi masu bayanin ne kuma ba tare da ya bawa kowa damar
jin abin da ya faɗa ba, zance ake ta sirri!!.

Ko ita Zee dake zaune saman table bata ji abin da suke tattaunawa ba, ita dai ta
zauna shiru tana bin kayan abincin da kallo,

Please Login or Register in order to submit comment