You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai kara wayo yake yi yana rikiɗewa yana komawa jinin Akka sak,
dik yadda aka yi akwai alaƙa ta jini tsakanin yaron nan da Abdul Malik family.

Ita kuwa Zee tana nan da wannan hali nata, ta koma bedroom ɗin mama Haulat a part
ɗin Jaish da kwana, dan ta yi fushi ta sallami part ɗin surukarta mama, ta fa kamu
da san Dr Raj, amma ta tsani uwarsa, kai wato akwai dirama a gaba fa.

Ita ma Fanan ta koma bedroom ɗaya a part ɗin Jaish ba tare da sanin momma ko
yarjewarta ba, shi ma Jaish bai sani na, shi yana can ma garden a can ya kwana,
yaki dawowa part ɗinsa, wai baya san kwata kwata su haɗu da momma dan tabbatar
rashin kunya.

A ɓangaren shi kuwa Jawad yau kwanan zaune ya yi yana rarrashi, ita dai ta ce
ba zata zauna da shi ba, sai dai kuma bata da kafar tafiya wajen mummyn nata. A can
kuma mummyn nata tana can tana faman sallar dare tana rokan Allah da ya rabata da
shaiɗanin da yake ƙoƙarin ruɗar zuciyarta dan kawai Smart ya bayyana a matsayin ɗan
kin, shaiɗan na san ruɗarta a in da take ta jin rashin daɗin bayyanar nasa, ance
zuciya bata da kashi, haka ne kuwa, domin kuwa ga shi nan dai mummy ma shaiɗan
nasan kai ta ya barota, tsawon shekaru yana zaune da kowa da zuciya ɗaya da amana,
bata ɗauki duniya da zafi ba, yanzu kawai abu na neman birkice mata.

Sai addu'a take yi tana karatun Alqur'ani mai girma, to fans ɗinta sai ku tayata da
addu'a kada shaiɗan ya yi galaba a kanta.

Idan muka waiwaya ɓangaren Mahnoor kuwa, momma ta kira wayat Jaish har ta gaji ya
ki ɗagawa, dan a cewarsa bai san me zai ce mata ba ɗan albarka. Haka momma ta tsaya
Dr ɗinta mace ta yi wa Mahnoor dik abin da ya dace, ta kuma bata magunguna da suka
dace sannan ta tafi, baiwar Allah ta ga bone ita kam.

Ita kuwa Mahreen sai dai shirin Allah, dan kuwa a cikin dressing room na momma ta
laɓe tana ganin su Omaid suka rinƙa jigila da guyson suna ƙoƙarin gyara ɓarnar da
suka aita. Da kyar suka samu suka iya cire mashi dafin kunamar, amma ya sha kuka
kam, dik abin da suke yi a kan idanun Mahreen suke yinsa, a ranta take cewa.
"Wannan Yah Omar ɗin dai an yi rago, kannen nasa ma sun fishi jarumta, sai ka zauna
kana kukan ciwo dan wauta?".

Daga gefe can kuma uncle Jahiz ne ya je neman Zee a part ɗin mama bayan ya baro
bedroom na Akka, dan ba zai iya barci ba sai ya sanyata a idanunsa, ya kamu da
zazzafar soyayyarta ne da alama. Da ya je bai ganta ba sai ya tambayi Khadijah ina
take?! Nan take faɗa mashi ai bata nan. Bai kawo a ransa matsala suka samu da
Aneesa ba, yasa hannu ya ɗauki babyn Khadija ya nufi waje da shi, Allah ya gani
yana kaunar yaron nan over, kamar shi ya haifesa haka yake jinsa.

Bayansa Khadijah ta bi da kallo, take fuskarta ta bayyana alamar damuwa da rashin
jin daɗi, gabanta faɗuwa yake yi a dik time da ta kalli uncle Jahiz. Kai tsaye part
na momma ya nufa dan duba Zee a wajen. While shi ma Dr Raj yana can bedroom ɗinsa
yana fama da juyi da tinaninta. Ita kuwa ta haye bed ɗin mama Haulat ta yi
kwanciyarta, har da shigewa cikin bargo. My people's anya gaba ƙwaƙwalwarku zata
iya ɗaukar cakwakiyar kingdom of power?......🤔

To kun ji abubuwan da suka faru bayan barin smart kingdom ɗin, dan haka mu koma
Paris ɗinmu.
Auta ta buɗi baki zata wa Hoorain magana sai jin voice ɗin mace ta yi daga
bayanta tana faɗin. "Wacece ke kuma?". A miliyan Auta ta juya dan ganin wacece? Ita
dai tasan babu wata mace a gidan nan tun da suke zuwa, a nan suke sauƙa idan suka
zo, Smart baya kaisu gidansu wajen mom ɗinsa, a nan suke zama, to bata taɓa ganin
mace ko ta ji muryar mace ba, kuma wannan ba muryar Pretty bane gaskiya. To ko
muryar waye?.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Wata kyakkyawar baturiya ce tsaye a kan kafafunta, tana nan dai cikin irin wannan
shiga tasu ta turawa, ta zubo gashinta ta zaman shoulder ɗinta ta gaba, ga wani
shegen high heel a kafafunta mai tsinin gaske. From up to down Auta ta bita da
kallo kafin ta ce. "Ke yakamata in yi wa wannan tambayar".

Tana kai karshen maganar ta cigaba da yin wayar da take yi. Cike da takun
ƙasaita ta tako izuwa gaban Auta, hannu tasa ta kwace wayar dake hannunta, cikin
zafa Auta tasa hannu zata kwaci wayar. Hatana ta yi tare da binta da wani kallan
ƙasƙanci kafin ta ce. "Kin dai ɗan yi kama da baby, dik yadda aka yi kina da wata
alaƙa da shi, amma hakan na shi ne zai sa na ɗaga maki kafa ba, ke har kin isa ina
magana zaki cigaba da yin waya?".

Auta zata yi magana suka ji alamar an buɗe kofar parlour, to jinin sarauta dai ba
karya ba, cike da izza ta ce. "Bani da lokacin shashasshu irinku, bani wayata".
Kallna banza ta bita da shi, zata yi magana kenan suka ji muryan Smart yana kwala
kiran sunan Auta, harara ta dallawa yarinyar kafin tasa kai ta wuce ciki.

A parlour ta iskosa yana zaune saman sofa, kusa da shi ta je ta zauna tana faɗin.
"Yah Omerish gani nan". Kamar zata tambayesa wacece a gidan nan kuma dama akwai
mace a gidan ne, sai kuma ta yi shiru, ranta a ɓace wancan mata katse mata waya da
jaruminta. Hannunta ya riko cikin nasa, a natse ya ce. "Menene yake damunki?".

Wai a ina Smart ya baro mana gawar Pretty ne? Wato ko a jikinsa tun da ba Auta bace
ta mutu ko?.

Da farko kamar Auta zata ɓoye mashi abin da yake faruwa, amma da taga bata da wani
sauran hanya sai ta sanar da shi game da soyayyarta da Hoorain, da ɓatar da ta yi
zuwa forest da taimaka mata da Pretty ta yi da komai dai dik ta sanar da shi, ta
kai karshen maganar tana kuka dan ta tina irin soyayyar dake tsakaninsu.

Shiru Smart ya yi ba tare da wani yanayi ya bayyana a tattare da shi ba, kamar dai
bai damu ba. Miƙewa ya yi tare da riko hannunta suka haura sama, sai sharar kwallah
take yi, dama ga bakincikin an kwace waya an hanata yin magana da shi. Da alama
Smart da King halayyarsu iri guda babu banbanci, amma my people's me kuke tunani
ne, wai shin ya Smart ya yi da Pretty ne? To mu je dai zuwa, koma dai menene lokaci
zai yi mana alkalanci.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Ummie and friend ɗinta hajiya two seater ne zaune a saman sofas a parlourn Ummie,
yanzu hajiyar ta zo, daga gani kasan akwai abin da suke shiryawa, sai kuskuskus
ƙasa ƙasa suke yi, hajiya two seater dai kusan kullun tana cikin nikaf matar nan,
sai idan ta zo keta tsaron gidan Abbie ne securitys suke ce mata sai ta cire nikaf
kafin ta wuce, dan su ga wacece, ko da kuwa Ummie ta yi masu waya ta sanar da su
bakuwarta na zuwa, to basa barin ta wuce sai sun ga face ɗinta. Nikaf or face mask
baya keta gate na farko na gidan Abbie, dole ka ciresa kafin ka wuce.

••••••••••••••••••••🔥

Jakarta ta buɗe ta ciro kwalin STENDRA guda ɗaya ta miƙawa Ummie tare da miƙewa
tsaye, ƙasa ƙasa ta ce. "To ni zan wuce dare ya yi, yanzu ma ba dan saboda ke ba ba
zan fito ba, ga sakonki nan, kada ki wuce saka mashi guda ɗaya idan ya yi yawa ne
biyu dan gudun matsala a iya ganoki, dan yana da karfi fiye da tinaninki". Yadda
take maganar tsab zaka fahimci wannan ta yi degree a iya munafurci da makirci.

Jinjina kai Ummie ta yi tare da miƙewa tsaye tana zuba mata godiya, sai uban
murmushi take yi burinta zai cika. Gaba hajiya two seater ta yi tana kara jaddada
mata kada ta wuce sanyawa Ramish wannan kwaya guda ɗaya kacal, dan yana da karfi
sosai, daga karshe ta rufe mata da cewa idan ya sha da minti 15 zata fara yi mashi
aiki, dan haka sai ta shirya. Ummie baki har kunne ta amsa da to. Har Hajiya zata
fita parlourn Ummie ta yi saurin cewa.
"To ya batun Leesharh fa? Yakamata mu yi gaggawar kawar da yarinyar nan tin
kan lokaci ya kure mana, kina ji dai ya faɗa maki Abbie yana tarayya da yarinyar
nan a ɓoye, kuma ni ba zan iya jurar hakan ba". Ranta a ɓace ta kai karshen
maganar.

Ajiyar zuciya hajiya two seater ta sauke kafin ta ce. "Kada ki damu, ai yanzu
yazama wajibi mu ɓatar da Leesharh, idan ba haka ba zata zame mana babban barazana,
amma kada ki damu zan dawo gobe dan jin result na maganin nan, a nan zamu tattauna
maganar tata in faɗa maki hukuncin da muka yanke, amma kafin nan ki shiryawa
Leesharh fita barin cikin gidan nan, kin dai san ba ta yadda za'ayi mu iya ɗaukarta
a cikin gidan nan saboda mahaukatan tsawon nan naku masu sanya hantar cikin mutum
ta kaɗa da kuke da shi, amma ki nemo wani aika ko wani dalilin da zai sa ta fita
daga ita sai driver kawai".
Jinjina kai Ummie ta yi, har zuciyarta ya ayyana mata yadda zata aika
Leesharh shopping ita da driver kawai ba tare da Sharifat ko bodyguards ba, tasan
ta yadda zata ɓullowa komai.

Sallama suka yi ta raka hajiya zuwa wajen elvator, sannan suka yi bye bye hajiya
tana yi mata addu'ar samun nasara a kan dikkanin burikanta.

Ciki Ummie ta koma, dama ita take haɗa mashi abinci dayawa lokuta, Sharifat mai
kaiwa ce kawai. Da sauri ta nufi dry kitchen dan shirya mashi cappuccino, dan tasan
zai buƙata. Sai dai fa, bata kai ga fara haɗawa bama sai ga Sharifat ta shigo cikin
kitchen ɗin tana faɗin. "Ummie na je bedroom ɗinki bakya ciki, Yah Ramish yana san
cappuccino"............ Wani irin faɗuwar gaba Ummie ta ji ya dira mata, sai ta ji
shakkar saka wannan magani, amma da yake shaiɗan la'ananne ne sai ya fara kara mata
confidence a kan ta jajirce zata yi nasara, har da raya mata ya yi cikar buri da
biyan buƙata ya fi kwana masallaci, take ta ji kwarin gwiwa, cikin dabara ta ce.

"Okey zan haɗa mashi, amma jeki ɗaki ki jirani ina zuwa". Ta faɗa tana satar
kallan cameras dake cikin kitchen ɗin. Da okey Sharifat ta amsa mata tare da juyawa
ta komai ciki, tana sanye da jelly dressing. Kamar yadda ta saba haɗa mashi
cappuccino haka ta haɗa yau ma, bata zuba maganin a cikin kitchen ɗin ba, saboda
Cameras dake ɗaukarta, sai ta ɗauki cup ɗin ta fito waje. Kai tsaye bedroom ɗinta
ta nufa, sai dai bata kai ga shiga ciki ba ta tsaya a wani ɗan corridor dake
tsakanin parlour da bedroom ɗin, a wajen babu Camera kuma akwai ɗan duhu, a nan ta
tsaya ta fito da maganin, a maimakon ta saka mashi guda ɗaya ko biyu kamar yadda
aka yi mata kashedi, sai ta ɓallo guda huɗu ta banka mashi a ciki. Tsayawa ta yi
har sai da maganin ya narke a ciki, sannan tasa spoon ta gauraya shi sosai, sai ta
bar spoon ɗin a cikin cup ɗin.

Kana ganinta kaga maras gaskiya, amma da yake Sharifat yarinya ce sai bata iya
fahimtar halin da Ummie take ciki ba, fargaba kamar zai kashe matar nan, amma
saboda karfin hali sai dannewa take yi. Ta zo ta miƙawa Sharifat plate and cup ɗin,
sannan ta wuce cikin toilet ɗinta tana jin kirjinta tamkar zai fashe saboda fargaba
da tsinkewar zuciya. Ita kuwa Sharifat, karɓa kawai ta yi ta wuce abinta, zuciyarta
na ta tuna mata Leesharh.

•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Zaune yake a cikin bedroom ɗinsa yana tinanin yadda aikinsa yake gudana, ga mama ta
sako shi a gaba tana saka mashi pressure sosai a kan bayyanar Smart, ta matsa mashi
wai sai ya yi mata bincike dan ita bata yarda Smart ɗan King bane, wai sai dai
momma saboda kwaɗayin mulki ta hayo Smart a matsayin ɗa.

Jama'a kun ji mun wata lukutar bala'i a wajen mama, fisabilillahi momma ta yi kala
da masu yunwar mulki? Kada ku manta fa ita momma ƴar King Badeen ce! Sannan kanwa
ga su Abu Abdussalam ƙososhin gwamnati, ga daddyn Smart wato babban yayanta
president ne, su uncle Rahab dik jiga jigan ƴan siyasa ne, bayan haka shi kansa
Smart ya isheta har ta gama rayuwarta bazata nemi komai ta rasa ba, kuna dai gani
Auta Gimbiya Zunaira yar karamar kanwarsa ma ya mallaka mata tampatsetsan gida har
haka bare mommarsa? Jama'a ku tayani gani, Jaish kawai yana da dukiyar da zai iya
rike gabaɗaya ahalin King har da su mama ɗin har karshen rayuwarsu ba zasu nemi
komai su rasa ba, kai in short auta kawai ta mallaki dukiyar da ya take na uncle
Abbas a yawa daga hannun brothers and uncles ɗinta, ji da ita suke yi, amma wai
irin wannan mata mama take cewa ta hayo yaro dan yunwar mulki? Hankali zai ɗauki
wannan batu kuwa?.
Shiyasa Ramish bai wani bi ta kan batun ba, saboda shi yasan wacece momma da
ahalinta, kada ku manta a hannun Abu Abdussalam ya girma, Abu Abdussalam kuma ai
kunga yayan momma ne dik da cewa yayan daddynsu ne ma, dan haka shi yasan momma ba
zata yi hakan ba, shi zai fi kowa bada labari a kan kirki da adalcin familyn momma.

Akwai lokacin da ya so barin gidan Abu Abdussalam ya koma gidansa da ya mallaka da
ɗinbin dukiyarsa, amma Abbie ya ce babu in da zai je su kasance a tare, so shi
yasan halin gabaɗaya ƴaƴan King Badeen.

Shiru ya yi yana tinanin yadda zai kama masu nikaf, shi yanzu wannan ne a gabansa
ba bala'in mama ba. Sallamar Sharifat ya dawo da shi daga duniyar tinanin da ya
afka. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa. Ita kuwa kallonsa ta shiga yi babu
kakkautawa, yana sanye da pj's a jikinsa launin light milk.

Hannunta ɗauke da cup na cappuccinon da ya buƙata ta kawo mashi, gabansa ta kariso
ta ɗaura cappuccinon a saman table tare da komawa gefe guda ta tsaya tana jiran ko
zai buƙaci wani abin. Yunwa yake ji, tin safe rabonsa da abinci, abubuwa sun sha
kansa, dan haka sai bai ɓata lokaci wajen ɗaukar cup ɗin ba.
Cikin natsuwa yake sipping na cappuccinon ba tare da ya kawo a ransa akwai
wani abin a ciki ba, saboda kullum ita ta saba kawo mashi abincin, kunga ba zai
taɓa yin zaton ansa wani abin ba. Sai dai fa ya ji ɗanɗanon cappuccino ya ɗan
canza, kamar ya yi zaƙi dayawa fiye da kullum, amma sai ya yi tinanin sugar ce ta
kubce, yana jin yunwa dan haka ba zai tsaya ƙaƙalen nan nasa da ya saba ba.

"Yah Ramish in tafi?". Ta faɗa tana kallan face ɗinsa. Kai ya gyaɗa mata
alamar e ta tafi. Juyawa ta yi tana tafiya tana waigosa, while ita kuma Ummie tana
can tana murnar burinta ya cika, so take kawai Sharifat ta dawo ta tambayeta ya sha
ko bai sha ba.

Sharifat na fita ya miƙe tsaye yana cigaba da shan cappuccinon, da yake yana jin
yunwa har ya kusa shanyewa ma saura kaɗan. Parlournsu ya fito, babu kowa, da alama
Bilal ya yi barci, dama shi Rizwan baya nan. Kai tsaye ya nufi ɗakin da Leesharh
take kwance rike da cup ɗin. Ƙasa ƙasa ya yi sallama, tun daren jiya da ya fita
ɗakin bai sake dawowa ba, dan baya san sake haɗa idanu da ita, ta caza mashi kai
jiya.

Zaune take a bakin bed ɗinta, ta fito daga wanka kenan ba jimawa, yanzu tana iya
yin wanka saboda ciwon ya warke, sai dai har yanzu tana karkashin dokar kada ta bar
ruwa ya taɓa wajen, so cikin dabara take wankar. Yau tana sanye da riga mai siririn
hannu zuwa gwiwowinta, sai doguwar wando daga ƙasa, Dr ya ce ta rinƙa barin wajen
ciwon nata yana shan iska, shiyasa yanzu riguna masu siraran hannu kamar vest kawai
Sharifat take kawo mata, anma kusa sallamarta, dan sauki ya samu.

Jin motsin mutum yasa ta ɗago idanunta, dama tana rike da wayarta tana latsawa
ne. Tana ɗagowa ya yi saurin cire idanunsa a kanta, dama kallan tsab ya tsaya yake
yi mata kamar an ce mashi tana kama da wata ko ance mashi idan ya zo ya kare mata
kallo za'ayi mashi tambaya a kanta a ɗakin jarabawa. Kuma abin da zai baku dariya
surar jikinta yake kallah ba ita ba, bare ma shape ɗinta, in baku manta ba na faɗa
maku Leesharh tana da shape sosai, tana da diri.

Ji ya yi kamar an sungulesa da ya tsaya kare mata kallo. "Barka da dare Yah
Ramish". Ta faɗa tana mayar da kallanta ƙasa. Shiru ya yi bai amsa ba. Almost 3
mins yana tsaye, sai can kuma cikin natsuwa ya ce. "Zaki iya zuwa ɗakin binciken
mu? Dan ina buƙatar hakan, akwai wasu tambayoyi da nike san amsoshinsu daga
gareki". Ya kai karshen maganar tare da ɗan gyara tsayuwarsa da kyau.

Kanta a ƙasa ta ce. "A shirye nike dan amsa dikkanin tambayoyinka". Jinjina mata
kai ya yi, ya kuma ji daɗin amsarta da har yasa ya sauke ajiyar zuciya. "Zamu iya
tafiya yanzu". Ya faɗa tare da juyawa ya yi gaba. A hankali ta miƙe tsaye, vail
dake ɗaure a kanta ta ware ta yafa a kan nata dan ya ɗan rufe mata shoulder ɗinta,
bata jin daɗin ganin jikinta a buɗe ko da kaɗan ne, kun dai san mu Nigerians wlh
mun fita daban, mun fi kowa kunya fa nike faɗa maku, kunya kuma shi ne cikon
addini, idan babu kunya ba za'a samu tausayi ba, idan babu tausayi ba za'a samu
imani ba, idan kuma babu imani ku faɗa mun me amfanin mutum?.......🤔

Bayansa ta bi yana tafiya kamar wanda bashi da lafiya saboda kasala. Ta yi
mamakin ganin ta hanyar da suka bi, ta kai shekara a gidan amma bata taɓa sanin
wannan waje ba, kuma a part ɗinsu ne, bata taɓa zatan akwai wani hawa a sama bama,
saboda a tinaninta su ne a hawa na karshe, ashe akwai wani hawa, ta sha madarar
mamaki lokacin da ta kalli wani siririn stair case mai amfani da remote a cikin
part ɗin nasu. Har tsoron haurawa sama ta ji, dan taga stair case ɗin kamar zai
nitse da ita ne, yana nan a kanannane kamar indomie, fargabarta na biyu ma kada su
hau ya karye da su dan ya yi sirantaka.

Sai da ta ga ya hau babu abin da ya faru sannan ita ma tasa kafarta kamar ba zata
taka ba ta hau. Ai a miliyan ta sauko jin stair ɗin yana yin kamar akwai spring a
jikinsa, irin idan ka taka sai ya yi ƙasa, in ka cire kafa sai ya yi sama, dik
confidence ɗinta ta ji ba zata iya hawa wannan waje ba. A jikinsa ya ji kamar ta
kasa haurawa, dan dama already yasan wannan stair case ɗin matsoraci ko mai hawan
jini ba zai iya hawa ba, sai su jaruman maza.
Sai da ya haura sama gabaɗaya sannan ya juyo da kallansa a kanta, while
ita ma shi take kallah. Da hannunsa ɗaya ya yi mata alamar ta hauro. Without any
scare ta amsa mashi da. "Ina jin bazan iya haurowa ba ne". Shi mamaki take bashi
yadda take magana with full confidence a koda yaushe, tin lokacin da take cikin
azabarsa in zai tambayeta sau dubu to sau dubu zata bashi amsa cike da gwarin
gwiwa, bata taɓa sarewa ba, lokacin da ta amsa masu wancan wayar ba nata bane ma ya
dan yi mamakin jin yadda ta amsa ɗin, babu ko shayi, so hakan yana ɗan bashi mamaki
gaskiya.

"Babu abin da zai faru ki hauro". Ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa. Kai ta girgiza tare
da cewa. "Dama ban ce akwai abin da zai faru ba ai, saboda ka hau a gabana babu
abin da ya faru, kawai dai ni ɗin ce ba zan iya haurawa ba saboda hankalina bai
kwanta da stair ɗin ba". Babbar magana, a gaisheki Leesharh iyalan Nigerians, ina
san ƴan kasata wlh, mu ɗin na daban ne fa!!.

Cak ya dakata tare da juyowa gareta, yama rasa abin faɗe, wai dama bata ce
akwai abin da zai faru ba ai. To tin da shi yake da buƙatarta dole ya yi abin da
take so, dan haka ba dan ya so ba ya ajiye cup ɗin dake hannunsa a saman wajen,
sannan ya sauko ƙasa, da hannu ya nuna mata hanya yana faɗin. "To yi gaba zan
biyoki a baya". Kai ta sake girgizawa. "Ni ai ba wai cema na yi ba zan iya hawa ni
kaɗai ba, hawan ne gabaɗaya ba zan iya yi ba".

Gaskiya Leesharh yar air ce. To ya zai yi? Dole ya ɗan duka ba tare da ya sake yin
magana ba ya ɗauketa cak ya nufi sama. Sai kuma me, ƙoƙari sauka daga jikinsa ta
fara yi tana faɗin. "Ni ka saukeni bana so".

Ai tamkar ba shi ba, ya bawa banza ajiyarta, bai sauketa ba sai da ya shiga
tsakiyar ɗakin ya sauketa, bai bi ta kanta ba ya juya ya koma ya ɗauko cup ɗinsa,
saman chair dake gaban wata computers ya zauna domin ya fara aikinsa. Ba tare da ya
kalli in da take ba ya yi mata nuni da chairn kusa da shi sannan ya yi magana cikin
bada umarni a kan ta zo ta zauna. Ta tsaya sai kuncin rai take yi wai dan ya
ɗauketa, tana ɗaure fuska ta nufo shi, ya bata haushi.

A natse ta tako ta iso wajen chair ɗin, tana zama shi kuma ya ɗaura cup ɗin
hannunsa a saman table ɗin tare da juyo da gabaɗaya jikinsa a gareta, ya zamana
suna fuskar juna, sai dai kallansa naa kan computer gabansa.
"Ki mun alkawarin dik abin da zaki faɗa mun gaskiya zaki faɗa!". Ya faɗa yana
dawo da kallansa a kanta. kai ta ɗan jinjina. "Ko a da can baya ni bana karya, wani
dalili yasa na yi maka sau ɗaya kuma bana fatan na kara yi". Mamaki ya ɗan yi jin
ta ce ta yi mashi karya sau ɗaya. "Ƙaryar me kika yi mun a baya?".
Ba tare da shayi ko shakkar komai ba ta amsa da. "Cewa da na yi wancan
wayar ba tawa bace, hakikanin gaskiya tawace!".

Ɗan zaro idanunsa ya yi, like so much of surprise. Nisawa ya yi kafin ya ce.
"Nasan da hakan, sai dai ban yi tinani zaki amsa mun da bakinki naki bane a yanzu,
nasan cewa wayarki ne tin a ranar da muka kamaki".
Mamaki ne sosai ita ma ya kamata, a ƙagare da san jin cikakken bayani
daga bakinsa ta ce. "Ya aka yi kasan waya ta ce sannan kuma meyasa kasan nawane ka
sakeni?".

Hankalinsa ya mayar kan computer dake gabansa, da yake irin torch screen computer
nan ne sai ya sanya yatsarsa yana latsata. Cikin natsuwa ya ce. "Na sakeki ne
saboda na fahimci controlling ɗinki ake yi, komai da kike aikawa command ake baki,
to ba ke nike da buƙata ba, masu sakaki ɗin nike da buƙata wanda kuma sai na sake
ki ɗin zan iya cin masu". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa a kan
computer sannan ya dawo da kallansa a kanta, da yatsarsa manuniya ya nuna mata
screen na computer yana faɗin.

"Zanen hannunki da zanen hannun dake jikin wayar dikka ɗaya ne, ta haka na san
wayarki ne".
Da sauri ta kai kallanta a kan screen na computer, hotunan zanen hannunta da kuma
zanen hannun dake kan wayar ta gani, lokacin guda ta haɗiyi wani irin yawu mai
wuyar wucewa, ashe kenan yasan komai ya zuba mata idanu, tab lallai ya cika
cikakken jami'i, yasan kan aikinsa da kyau. Wani zuciya ce ta jefa mata tambayar
amma meyasa ya azabtar dake dik da yasan zai sakeki kuma ba ke yake da buƙata ba?
Shiru ta ɗan yi dan bata san wannan amsa ba.

Shi ma dai shiru ya dakata yana jin wani irin sauyi a jikinsa, lokaci guda zufa ta
fara ketowa daga gefe

Please Login or Register in order to submit comment