You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya taɓa faɗa mata na in ya kamata da laifi zai yi mata abin
da ba zata manta da shi ba ta riki maganar a ranta wanda kuma shi ba hakan yake
nufi ba, jama'a ku tauna magana kafin faɗinta dan gudun abin da gobe zata haifar,
shawara ce daga alkalamina!!.

Kalamanta sun kara narkar mashi da zuciya, shi dai burinsa ɗaya shi ne ta yafe
mashi, amma taki sauraronsa ma. Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya saki hannunta ba,
cike da tausayawa da kulawa ya ce. "Dik abin da zaki faɗa a kai'na na yarda na kuma
ɗauka, yanzu dai dan Allah zauna ki sha tea, ni dai ki rinƙa cin abinci koma me
zaki ce a kai'na ki faɗa, lafiyarki shi ne fata na kawai". Ya kai karshen maganar
yana miƙo mata cup dake hannunsa, tea ne mai zafi sai tiriri yake yi.

Allah sarki, a jikinta tana jin ba da gangan ya yi mata hakan ba, sai dai
zuciyarta taki yarda da hakan, wani lokaci har tausayi yake bata yadda yake neman
ta yafe mashi, amma ta gaza yarda da shi, ta kuma rasa dalilin kin yarda da shi da
zuciyartata ta yi.

"Ba zan iya cin komai ba, saboda ban san yanzu ina rayuwata ta fuskanta ba, dan
Allah ka kyaleni ko yunwa zata kasheni in huta tun da kai ba zaka kasheni ba".
Kanta a ƙasa ta yi maganar....... Nisawa ya yi kafin ya ce. "Babu abin da zai samu
rayuwarki, zaki yi rayuwa kamar kowacce mace mai ƴanci, dan Allah zauna ki sha tea
kin ji?". Cikin sigar rarrashin da ya koya dan dolensa ya yi maganar.

"Har abada ba zan taɓa yin rayuwa mai ƴanci ba, a rayuwar yanzu ka kai budurcinka
gidan miji ma ya ka kare da walaƙanci da tozarci in baka samu miji na gari mai
tsoron Allah ba bare ace ka zubar da mutuncin naka a titi ka shiga gidansa empty,
me kake tinanin zai faru? Kana tinanin zan yi rayuwa mai ƴanci ne? Kana tinanin
akwai wata daraja da ta rage mun wanda zai kalleni da ita ne?........."...

Katseta ya yi ya hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce. "Baki zubar da mutuncinki a
titi ba, tabbas babu wanda zai ganki a matsayin mara daraja kin ji ko? Dan Allah
Aesh ki yafe mun, ki yafe mun kin ji? Nasan na cutar dake, amma kin ki yarda ba da
gangan na yi ba, kin ki yarda ba halina bane, da kin san yadda na tsani zina da
baki yi ƙoƙarin danganta ta dani bama, kin san irin hukuncin da nike yi wa mazinaci
wanda ya yi wa mace fyaɗe kuwa?". Cike damuwa a ransa ya kai karshen
maganar............ Sai a lokacin ta ɗago da kanta ta kallesa, hawaye suna cigaba
da gangaro mata masu ɗumin gaske, da kyar ta iya cewa.
"Babu ma wanda zai aureni da har zai ganni da daraja, ka kwantanta
a kanka, shin zaka iya auren macen da wani ya lalata ya yi mata fyaɗe? Ko ka
ɗaukeni a matsayin kanwarka na jini, ya zaka ji idan aka ce anyiwa kanwarka
fyaɗe?"...... Dum!! Dum!!!! Shiru ya yi bashi da bakin bata amsa, dan yasan ko kusa
ko alama ba zai iya ba, ba zai iya auren wanda wani ya lalata ba, haka zalika ba
zai iya barin wanda ya yi wa kanwarsa fyaɗe ya cigaba da numfashi a duniya ba, ba
zai kyalesa ba har sai ya yi mashi mummunar kisa, batun aure kuma, shi yaushe ma ya
taɓa yin tinanin auren bare har ya yi tinanin irin macen da ta dace da shi, iya
abin da ya sani dai shi ne ko soyayya da wani mace ta taɓa yi ba zai kulata ba bare
har a kai ga aure.

Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ka gani ko? Kai kanka ba zaka iya auran ragowar
wani ba, to taya kake tinanin ni zan samu wanda zai iya karɓar ragowarka?". Cikin
zafin zuciya ta yi maganar, tana kai karshen ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi
mata ta juya da nufin ta bar wajen da sauri....... Cikin zafa ya riko hannunta, kin
juyowa su kalli juna ta yi, sai wani irin huci take fitarwa mai ɗimin gaske, kai ka
zaci zata iya haɗiye zuciyarta a lokacin ko kuma ta kone saboda zafin da zuciyarta
ya ɗauka, yana yi mata wani irin suya mai azaba, abin da ciwo matiƙa gaskiya.

"Idan na aureki shikenan zaki yafe mun?" Ya faɗa yana kallanta. Ai a miliyan ta
juyo da kallanta a kansa, ido cikin ido suka kalli juna, wani irin faɗuwar gaba ta
ji ya risketa, ta kasa iya magana, dan bata da abin faɗe....... "Ni zan iya ɗaukar
ragowata ai ko? Budurcin mace shi ne mutuncinta right?". Ya faɗa kamar ya jefa mata
tambaya wanda yasan ba amsa mashi zata yi ba. Dan haka sai ya ɗaura da cewa.
"Tabbas budrucin mace shi ne martaba da kimarta a idanun mijinta, dan haka ni
zan aureki, dama ni na karɓi budurcin naki, dan haka zan kalleki da kima da daraja,
kuma zaki yi rayuwa mai ƴanci kamar kowace mace ko ma in ce fin kowace mace tun da
kema kin kawo mun budurcinki, kin aminta da hakan?". Idanunsa a cikin nata ya yi
maganar, tabbas saboda tausayinta da kalamanta na ta rasa gata yasa ya yarda zai
aureta, domin kuma ta yafe mashi, ba zai so ya yi sanadiyar shigarta kunci na har
karshen rayuwarta ba, gara ya aureta ko ba komai dama shi ya buɗeta, tabbas ba zai
yi mata gori a kan komai ba.

Kai ta fara girgiza mashi alamar bata yarda ba, tsananta kukan ta yi, har wani
shessheƙa take yi, tamkar zata haɗiyi zuciya, cikin kuka mai tsuma zuciya ta ce.
"Ba zan iya aurenka ba saboda ƴar uwata, Sharifat ta mun komai a rayuwata, dan haka
ba zan taɓa bakanta mata ba, da ta shiga cikin ƙunci gara ni na tabbata a cikin
bakinciki, a lokacin da na rasa gata, nike matsayin mara galihu, nike cikin
tsakiyar rana a dokar sahara, a lokacin da duniya ta juya mun baya, farinciki ya
kaurace daga rayuwata, na cire tsammanin yin farinciki har abada, a lokacin
Sharifat ta tsaya tsayin daka wajen ganin sai da ta sakani dariya a rayuwata, ta
sakani na ji cewa ni mutum ce, ta sakani na ji cewa ashe ina da sauran farinciki a
rayuwarta, ta zame mun uwa, uba ƴar uwa, ɗan uwa, bata kyamaceni ba, ta jani a jiki
tamkar ƴar uwarta na jini, ta kyautatawa rayuwata, dalilinta nasan kai'na har nasan
darajar mutuncin da yau nike kuka a kansa dan ka keta mun shi, ba dan ita ba da ban
san darajar mutuncin nawa ba, Sharifat ta wuci tinanin mai tinani a rai'na, dan
Allah kada ka sake yin magana a kan aure tsakanina da kai, dan kai ne burin ƴar
uwata!!". Tana kai karshen maganar ta kwace hannunta da sauri ta haye sama tana
kara rushewa da kuma mai taɓa zuciya.

Gum ya tsaya tamkar wanda aka sassaƙa, yau ya ji sabon labari wai Sharifat na san
shi, abin da bai taɓa ji ba bai taɓa tinani ba ko a mafarki, a cikin ransa ya ce ko
mata sun kare a duniya shi me zai yi da Sharifat? A yadda ya tsani uwarta ina zai
kaita? Tab lallai akwai cakwakiya kuwa.

Ya jima tsaye a wajen ya rasa madafa, daga karshe ya yanke shawarar bin bayanta,
dan ba zai iya jurar ganinta da yunwa ba. Sama ya haye yana tinanin mafita a garesu
gabaɗaya, dan a gaskiya ba zai iya jurar ganinta a halin da take ciki ba, yana da
ilimin addini yasan cewa mutum ya shiga damuwa a dalilinka na wuni ɗaya ma babban
musifa ce a gareka bare ace tsawon wata kuma yana neman zarcewa har abada idan bai
ɗauki mataki ba? Ina zai kai wannan zunubi haka? Gaskiya da sake.
Kwace ya iskota a saman bed ta kifa kanta a saman pillow tana kuka tamkar ranta
zai fita. Wani irin tausayinta ne ya kara kama shi, tabbas yasan da ciwo abin, amma
ya zai yi to? Kaddararsu ce ta zo a haka. Gaban bed ɗin ya karisa, a saman bedside
drawer ya ɗauka cup ɗin hannunsa kafin ya zauna a gefenta, hannunsa dikka biyu yasa
ya ɗagota tare da juyo da ita suna fuskantar juna, Allah sarki ta datse idanunta
gam tamkar zata fashesu. Slowly santa ya fara shigarsa ba tare da ya sani ba, a da
iya tausayi ne kawai, amma yanzu gangar jikinsa ta fara karɓan wani sabon saƙon na
daban!.

"Aesh nasan na yi abin da baki ba zai iya zayyana kuncin da kike ciki ba, yanzu
da bakinki ina san ki faɗa mun me kike san na yi dan ki shiga cikin farinciki kamar
a baya?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar...... Tana san kwace kanta daga garesa
amma ta rasa kuzarin yin hakan, sai ta hakura kawai ta natsu tana cigaba da
kukanta. Ganin bata da niyar bashi amsa ne yasa ya kai hannunsa ɗaya saman ƙuncinta
ya fara goge mata hawayen da basu da niyar dakatawa daga zuba, hannunsa ɗaya kuma
ya tallabota........ "Please talk to me Aesh". Cikin wani irin slow ya yi maganar,
ga murya ƙasa ƙasa.

Ganin waɗan nan hawaye basu da niyar dakatawa ne yasa ya mannata da kirjinsa dan ya
rarrasheta, hankalinsa yana tashi sosai idan ya ji kukanta, sai ma idan ya tuna da
cewa marainiya ce ita, sai ya kara jin hankalinsa ya tashi...... "Aesh ki faɗa mun
abin da kike so in yi maki ki dai'na wannan kuka ki fita a halin da kike ciki". Da
ga ji voice ɗinsa kasan yana cikin damuwa matuƙa. Kai ta hau girgiza mashi alamar
babu komai, ƙanƙameta a kirjinsa ya yi yana jin wani irin abu da ba zai iya gane ko
menene mane yana ratsa kashi da ɓargo har zuwa ƙwaƙwalwa da zuciyarsa.

Tun tana iya kuka mai ɗan sauti har sautin ya dai'na fita, daga karshe ta yi diff
alamar barci ya ɗauketa a jikinsa babu shiri, kun san idan mutum ya yi kuka sosai
yana saurin yin barci, to ita ma dai ta yi ba tare da ta shirya ba, kuma bata sanya
komai a cikinta ba, da yunwa ta yi barci, hanjinta dik a tattare sun naɗe. Jin
numfashinta ya sauya zuwa irin na mai barci ne yasa ya dawo da kallonsa a kanta, a
nan ya tabbatar da ta yi barci. Kwantar da ita ya yi a hankali cike da kulawa,
sannan ya zubawa face ɗinta da ya yi jaga jaga da hawaye kallo na ƴan mintunan da
basu gaza biyar ba. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan matsar da bakinsa
kusa da ita kaɗa, a fili ya furta. "Isn't all my fault Aesh, am so so sorry, by the
grace of god I will make you happy irin wanda haki taɓa samu ba a rayuwarki, ba zan
bari ki sake yin kuka a kan wani abin ba, zan gyara abin da na ɓata da kai'na". Ya
kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye. Bargo ya ja ya lulluɓa mata kafin ya nufi
switch. Wutar ɗakin ya kashe sannan ya nufi waje, zuciyarsa cike da tinanin bata
sanya komai a cikinta ba, tabbas kuma yasan tana jin yunwa, amma haka ya nufi nasa
bedroom ɗin.

Saman bed ɗinsa ya kwanta, tunaninta ne kawai a cikin kwakwalwarsa, tin da wannan
abin ya faru a tsakaninsu bai sami barci mai natsuwa da daɗi ba, kullum a daddafe
yake yi kamar dai yau ɗin dai, da kyar ma barcin ta yi awon gaba da shi. Ransa cike
da tinaninta

(Oh ni Princess Teema, kowa da kalar nasa cakwakiya da kaddarar a cikin RAWANIN
ZALINCI, ita kuma Sweetie tana can tana fama da mai black heart ɗinta, shi ne
kaddararta kuma ita ma ita ce kaddararsa, Auta da nata kaddarar, kai kowa ma da na
shi bala'in da yake ciki, to ni kuma ina da Maltina mai sanyi, ba abin da ya fi
rai'na, idan komai ya ɗauki zafi sai na kora kayana.)

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥

Kai tsaye bedroom ɗinsu Smart ya nufa da ita, kwance ya isko Auta idanunta a rufe,
ya yi zatan barci take yi, dan haka sai ya shinfiɗe Pretty a gefenta, ya zauna
saman bedside drawer ya hau tofa masu addu'oi. Dik abin da yake yi Auta na jinsa,
sai da ya kammala ya rufesu da bargo ya fito ne ta miƙe zaune, ta gagara yin barci
saboda tinanin Hoorain ɗinta, ta gaza samunsa a waya. Uban ta gumi ya buga a
tsakiyar bed ɗin tana tinanina mafitarsu ita da shi.

Wayar ta ne ya fara kara alamar shigowar kira, jikinta har yana kerma wajen miƙa
hannu a gaggauce ta ɗauko wayar. Wani irin zabura ta yi har ta miƙe tsayea tsakiyar
bed ɗin ba tare da ta san ta yi hakan ba, dik kawai saboda murnar number Hoorain ne
ya kirata. Jiki na tsuma hannu na kerma ta yi picking tare da kara wayar a
kunnenta.

Kasancewar bai san number ba saboda number waje ce ba ta ƙasarsu ba sai ya yi
sallama haɗe da tambayar wanene?. Da ka ji yadda yake yin magana zaka fahimci yana
cikin tsananin ciwo da rashin kwanciyar hankali...... Idanunta ne suka cicciko da
kwallah, a raunace ta ce. "My Hero Hoonairar kace, ni ce". Ta yi maganar tana zube
gwiwowinta a saman mattress ɗin.

Shi kuwa yana jin haka yana daga kwance a gadan asibitin ya zabura ya miƙe zaune,
tamkar zai ganta a gabansa ya ce. "Hoonaira, Hoonaira dama........dama......". Ƙasa
yin maganar ya yi saboda sarkafewa da voice ɗinsa yake yi. Commander dake kwance a
gefensa saman bed na masu jinyar majinyata ya fara yin barci ne ya tsinkayo muryan
ɗan nasa cikin kuka kaman yana sambatu, hakan ya sa ya tashi zaune, dama wutan room
ɗin a kunne. Ganinsa manne da waya a kunne ne yasa ya fahimci waya yake yi da Auta,
dan ita kaɗai zai yi wa wannan rikicewar. Binsa da kallan tausayi commander ya yi
yana jin zuciyarsa na kara raunata.

•••••••••••••••••••••🔥

"Calm down my hero, na dawo gareka ai a yanzu, kuma ba zamu taɓa rabuwa ba, please
ka kwantar mun da hankali ka ji?". Cewar Auta...... Allah sarki soyayya, jinjina
mata kai ya yi tamkar yana a gabanta tamkar kuma wani ƙaramin yaro wanda ake san yi
wa dabara da alawa, dik ya susuce kamar ba jarumin assistant commander namu
ba...... Abbo dai kallan tausayi kawai yake binsa da shi.

"Promise me that zaka dai'na damuwa ka ji?". Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo
mata....... "Na yi alkawarin zan dai'na damuwa, ni ma ki mun alkawarin zaki dai'na
kuka, kuma ki share hawayenki na yanzu da suke zubowa, kada ki bari su sake zuba
kin ji my life?". Kai ta gyaɗa mashi alamar to ba tare da ta iya amsawa ba........
"Kece rayuwata Hoonaira ta, kece farincikina, ina san ganinki, na yi kewarki,
please kizo in ganki kin ji?"....... Da kyar ta iya faɗin. "Bana nan my hero, ina
wajen Yah Omerish, amma zan zo muga juna ka ji?".

A dai'dai lokacin da suke yin wannan magana shi kuma King suna yin meeting shi da
uncle Jahiz, uncle Abbas and Akka, suna ƙoƙarin tsayar da magana a kan aurenta da
Abdussalam and dawowar Smart kingdom of power saboda ya zo ya riki mulkinsa, dama
nasa ne, tashin hankali kenan, akwai cakwakiya.

Sake jiki suka yi suka zubawa juna kalaman soyayya masu narka zuciya, tin Auta
tana kuka har sai da ya sanyata dariya kai ɗan sauti, tini yasa ta mance da ta taɓa
shiga kunci a rayuwarta, haka ta koma ta kwanta ta rungumo pillow, har da ce mashi.
"My Hero da na rungumi pillown nan sai na ji kamar kai a ruguma, ka tuna mun
forest".

Shi ma komawa ya yi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, cike da kauna da kulawa ya
ce. "Soon watarana zaki rungume ɗin ba pillow ba" ....... Hoorain fa bai lura da
Abbonsa ya tashi ba, kawai ya hau zuba love word abinsa. Ai taɓe baki commander ya
yi yana mamakin ɗan nasa, tinani yake yi wai yaushe Hoorain ya iya magana haka? Shi
dai yasan ko magana ta minti guda ɗansa baya yi, mutum kamar kurma, amma ji yanzu
yadda yake zuba wasu zafafan kalamai kamar ba shi ba, har tantama commander ya yi a
kan anya jarumin zakin ɗan nasa ne kuwa?.
Shi kuwa Hoorain lumshe idanu ma ya yi yana cigaba da bawa flower ɗinsa ruwa, daga
karshe ma ya juyawa Abbo baya yana faɗin. "Kin tabbatar?". Tana daga kwance ta kara
matse pillow a kirjinta kafin ta ce. "Tabbas da safe zamu yi video call, na
tabbatar"....... Ajiyar zuciya ya sauke, wani bargo mai sanyi ne ya lulluɓe
zuciyarsa, ya yi kewarta over.

"I really love you my Hoonaira, i promised to be with you with happy or not,
kece farincikina kuma kwarin gwiwata". Da kyar ya iya kai karshen maganar, saboda
bai saba dogon magana ba. Yau dai Auta baki har kunne, sai murmushi take saki. Ba
su suka rabu da juna ba sai karfe 3, nan ma shi ya ce ta kwanta ta yi barci kada ta
makara tashi sallah, da safe zai kirata. Bata yi mashi musu ba ya amsa da to, cike
da kwarewa a iya bawa flower ruwa ta sumbaci wayar tata tare da ce mashi ya sanya a
ransa kumatunsa ta sumbata, ƙara lumshe idanunsa ya yi yana jin wani irin yanayi
mai daɗi, sai ya ji dama da gaske ne mana kumatun nasa ta sumbata, ai da ba zai iya
yin barci ba yau.

Jin ya yi shiru bai yi magana bane yasa ta ce. "My Hero ni ba zaka bani na barcin
bane?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Sumbatar take nufin shi ma ya yi mata
tamkar yadda ta yi mashi. Haba ji tamkar an yi mashi bushara da aljanna, juyowa ya
yi tare da kai wayar ɗan bakinsa ya manna mata sumbatar kenan idanunsa suka sauka a
kan Abbonsa da ya buka tagumi yana kallansa, commander ya bushe a zaune kamar wanda
aka sankarar, a ransa yake faɗi ashe har da sumbata ɗansa ya iya bai da labari? Kai
wannan abin mamaki ne a wajensa.

Wani irin kunya ne ta lulluɓe Hoorain, ga shi ya rigada ya kai sumbatar, sai
ya rasa ya zai yi kawai ya yi gaggawar cire wayar daga bakinsa tare da fara kame
kame kaman maras gaskiya, yana jiyo sanyayyar muryarta tana faɗin. "My Hero wannan
sumbata ta isa ya rikeni daga nan har zuwa safiya in kwana cikin farinciki haɗe da
mafarkinka". ...... Amma ya ƙasa iya bata amsa, sai ma ya yi gaggawar katse kiran
kawai yana kallan Abbo...... Ajiyar zuciya commander ya sauke, can ƙasa ƙasa ya
furta. "Dole in yi maka aure my lion". Ya yi maganar ne ta yadda Hoorain ɗin bai ji
me ya faɗa ba. A hankali ya koma ya kwanta tare da juyawa Hoorain ɗin baya irin
alamar bai ji komai ba.

Ajiyar zuciya Hoorain ya sauke, kunya ta gama rufesa, tamkar wanda kwai ya fashewa
a ciki ya juya ya bawa Abbon nasa baya yana lumshe idanunsa. A maimakon ya yi barci
sai ya hau tinanin Hoonairansa yana nishaɗi. Ita kuwa yana katse kiran ta kara
rungume pillow tana sakin murmushi har barci ya yi awon gaba da ita.

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

After one day. A hankali ta fara motsa idanunta tana san farkawa, Ronnie dake kusa
da ita ne ya yi gaggawar matsawa ya riko hannunta, cikin sanyin murya ta fara
ambatar sunanta a natse, shi tun daren jiya ya farfaɗo bawan Allah, ita kuwa da
yake ta fisa tausayi sai yau ta farfaɗo, dan zuciyarta ya raunata sosai.

Waro idanunta da suka kumbura luhu luhu suka yi jajir waje ta yi, saman celling
ta kafe da kallo kamar wadda bata a dai'dai, kamar taga bakon abu, sai ambatar
sunanta Ronnie yake yi amma ina kamar bata a wajen, sai da ya sa hannu ya shari
kumatunta ne ta juyo da kallonta a kansa. Suna haɗa idanu ta zabura ta miƙe zaune,
cikin fitar hayyaci ta fara sambatu kamar haka. "Lovely bro yanzu big bro ya kashe
mutanen nan dikka har da yaran da basu ji ba basu gani ba? Ko kuma ya hakura ya
kyalesu?". A ruɗe take maganar tana jan numfashi da karfi karfi tamkar zata sume.

Ya lura bata a daidai, dan haka sai ya ce mata. "A'a ba dikka ya kashesu ba, ya yi
wa wasu afuwa". Tabbas karya ya yi mata, kuma wannan shi ne karyarsa ta farko a
duniya, shi baya karya wlh, amma saboda kwanciyar hankalinta ya yi.
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta furta. "Alhamdulillah, ko ba komai
mun yi nasara tun da muka iya sanya shi ya yafewa dubban al'umma"...... Ronnie dai
jinta kawai yake yi, a cikin zuciyarsa yana cewa, lallai yarinya baki san waye big
bro ba, bai taɓa yafiya ba a rayuwarsa, idan ya zartar da hukunci to fa dik abin da
zai faru sai dai ya faru amma babu mai canza wannan hukunci, a haka suke rayuwa tun
daga kan mulkin mahaifinsa har shi ɗin, babu wanda aka taɓa yi wa afuwa daga
hukuncin da ya yanke a wannan birni, harta iyayen Floris Black Tiger ya kashe, an
konasu a cikin wannan wuta, bai ragawa kowa ba, master Devil kawai ya bari a cikin
maciya amanar nasa, shi ma akwai dalilin da yasa ya barshi, nasa hukuncin ta
musamman ya tanada mashi.

Zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, jikinta na rawa saboda murna ta ce.
"Lovely bro bari in je in ga big bro, dole na yi mashi godiya bisa wannan abin da
ya yi, ya yi namijin ƙoƙari wajen yi masu afuwa". Ta kai karshen maganar tare da
yunkurawa zata miƙe. A nan ne ta fahimci akwai drip a manne a hannunta, saboda
zafin da ta ji, ta lankwatsa hannun ne ta dafa jikin mattress zata miƙe, shiyasa ya
yi mata zafi. Shi kuwa tana wannan magana ya yi gaggawar kai hannu zai dakatar da
ita saboda bai san a wani irin hali Black Tiger yake a yanzu ba, kada ta je yana
kan tsini ya yi mata illah, dan ba imani ne da shi ba kuma ba gane kansa ake yi ba.

"Ronnie yaushe aka saka mun wannan abin kuma?". Ta faɗa tana kallan drip da ya
kusa karewa, ɗan kaɗan ya rage. Sake hannun nata ya yi kafin ya amsa mata da tin
wuraren la'asar, yanzu kuma mangariba ta kawo kai. Zaro idanu ta yi tana tambayarsa
wai yau yaushe ne ma? Nan ya sanar da ita ai kwana ɗaya ta wuce, tun jiya take sume
ai. Kara zaro idanu waje ta yi, jikinta har kerma ya fara yi, a natse ta furta
Hasbunallahu wani'imal wakil.

Rarrashinta Ronnie ya shiga yi yana bata baki har ta hakura ta koma ta kwanta zuwa
san da drip ɗin ya kare, sannan ya cire mata, a gaggauce ta sauko ta nufi toilet
dan yi wanka ta ɗauro alwala ta hau biyan bashin sallolin dake kanta, shi kuma
Ronnie ya fita ya nufi bedroom na Black Tiger dan ya yi sallah a can, baya sallah a
ɗakinsa saboda kada Black Tiger ya gano ya musulunta.

After some hours da basu wuci biyu ba, shirye take tsab cikin sleeping dress masu
shegen kyau, riga ce mai ƙaramar hannu da dogo wando launin ash mai ɗan duhu, hakan
yasa ta yi balai'n kyau saboda hasken fatarta, ta gyara golden hair ɗinta sai sheki
yake yi, sai tashin kamshi take zubawa, ta yi sallar isha'i saura cin abinci, tana
tsaye a gaban mirror tana kallan kanta tana kuma tinanin su Pretty, kewarsu ce a
ranta yau sosai, har ta ji hawaye sun cika mata idanu, ta matsu ta ga Kamran ɗinta
ido da ido, har mafarkinsa take yi, yana ranta a kowani dakika na rayuwarta. Ta
nausa cikin tinaninta sai ji ta yi ya ɗan rungumeta ta baya yana faɗin. "Lovely sis
tinanin me ake yi har na shigo baki ji ni ba?".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗago kallanta, ta cikin mirror suka kalli juna,
cool murmushi suka sakarwa juna kafin ta amsa mashi da. "My twins sis and my Kamran
nike tinawa, yau da kewarsu nike tare"....... Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa mata
da. "Soon zaki je ki gansu, yanzu dai bari in dubi Floris ina dawo, tun jiya da
safe da na ganta ban sake ganinta ba"........ Allah sarki, bai san tun jiya ɗin ta
mutu ba, tana kunshe cikin toilet master na gidan yari.

"Okey nima zan je duba big bro, amma ni fa ina ganin kamar Floris fushi take yi
da kai". Tana magana tana kallansa ta cikin mirror. Jinjina kansa ya yi kafin ya
amsa da. "Tabbas haka ne, nima na lura da tana fushi dani, shiyasa zan je bata
hakuri, kin san yadda nike kaunar Floris kuwa my sister?"...... Kai ta girgiza
mashi

Please Login or Register in order to submit comment