You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zauna.

A ranta ta kuduri niyar ba zata sanar da momma abin da yake faruwa ba, zata yi
shiru har ta ga me zai iya faruwa gaba, tana da hankali ta fahimci ba komai zata
rinƙa faɗawa momma ba, yakamata tasan abin da yakamata ta rinƙa faɗa mata da wanda
bai dace ba.

Shiru ta kwanta a saman bed ɗin cike da tunane tunane a ranta. Shi kuwa sai da
ya gama zaman da zai yi a balconynsa har zuwa karfe 8:40, sannan ya miƙe ya dawo
cikin bedroom ɗin, shikaɗai ba wanda ya taɓa shi yake ta faman ɗaure fuska kamar
wanda aka cewa wutar jahannama zai zama makomansa, yana ta faman jan tsaki, sai
wani haɗe gera yake yi, a fili ya furta momma tana san lalata mashi komai ta ja
mashi raini dama ga Jawad ya gama zubar mashi da mutunci ya auri Chuchu, wannan
abin ta kona mashi rai sosai.

Mu fa mun san silar dik wannan ɗaure fuska da kake yi yaron Mommarsa, in zaka cire
girman kai ka ajiye batun zata rai'naka ka daure ka rungumi ƴar matarka ka kawar da
kai ma da ya fi maka, ko ya kuka ce my people's? Mu zaka ce baka san raini? Uhm na
dai yi shiru.

Saman bed ɗinsa ya haye, har ya kwanta sai kuma ya tina da batun Auta, da sauri ya
miƙe zaune, a hanzarce ya ɗauko wayarsa, call ya danna na wata number da aka yi
saving da pure heart. Kara wayar a kunnuwarsa ya yi yana sauraron yadda suke
zayyana mashi cewa number a rufe take. Yau kwanaki uku kenan yana kiran number a
kashe, haka kawai a ransa ya ji tabbas akwai abin da ake ɓoye mashi dangane da
Auta, dan kuwa ko Dubai ta tafi suna waya a kullum, ya za'ayi ya kira su Yah Ramish
ma su ce mashi bata zo gidan Abu Abdussalam ba, ya kira kakansu King Badeen ya ce
mashi bata nan, ya kira uncle Rahab kuma sai ya rinƙa ce mashi ko ta yi barci ko
bata kusa, to gaskiya shi yanzu ya fara tantama a kan wannan lamari.

Yunkurawa ya yi zai miƙe ya nufi waje, dan ya je ya samu momma ta faɗa mashi
gaskiya ina Auta take? Shi yanzu dik bai yarda da maganganunsu ba. Yan yunkurawa
sallamarta ta daki dodan kunnnesa.

Ta wutsiyar idanu ya kallenta. Tin daga kan kyawawan fararen kafafunta da ya kalla
ya gane wacece, dan lallenta. Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana jan siriri
tsaki, a ransa yake faɗin ba dan wannan yarinyar marainiya bace babu abin da zai
hana shi sakinta a daren nan, amma yanzu ma bai sanya a ransa zai zauna da ita ba,
yana dai ƙoƙarin tina mafita, saboda shi dai wlh ba zai zauna da wannan yarinya ba.

A gabansa ta zo ta tsugunna, tana sanye da hijabi black color zuwa gwiwowinta, ya
dai rufe kayan barcin jikinta, hannunta ɗauke da cup of cappuccinon. Cikin sanyin
murya ta ce. "Hamma ga cappuccinonka nan".

Tsawa ya daka mata mai firgitarwa a kan ba ya ce kada ta sake bari su haɗu ba?
Tsawar da ya yi mata ne har yasa ta saki cup ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse, hakan
yasa ransa ta kara ɓaci har ya ɗaga hannu zai dallah mata mari, sai ta yi saurin
sunkuyar da kanta ta ɓuye shi a tsakanin cinyoyinta.

Wani tsawa da ya sake daka mata a kan ta fita mashi daga ɗaki koku ma ya
ɓaɓɓallata ne yasa ta yi saurin miƙewa da gudu zata fita. Mama Haulat kuma jin
tsawan yasa ta shigo da gudu domin ta duba menene?.

Karo suka yi da Mahnoor a bakin kofa zata fita, da sauri ta yi ƙoƙarin riketa dan
ta tambayi ba'asi, sai dai ina, Mahnoor bata bada damar a riketa ba, da gudu sosai
ta danna waje tana sakin kuka mai tsuma zuciya.

Dawo da kallonta a kansa mama Haulat ta yi, cikin girmamawa ta ce. "Ranka ya daɗe
lafiya?". Wani irin hararar da ya dallawa mama Haulat ɗin ma har sai da yasa ta ji
ƴaƴan hanjinta sun kaɗa. Siririn tsaki ya ja tare da miƙewa ya zo ya wuceta ya nufi
waje yana huci kamar ba lafiya ba.

Kai tsaye part na King ya nufa, dan ya fahimci momma a kan Mahnoor bazata wani
goya mashi baya sosai ba, King ne kawai zai rarrashesa. Sai dai kuma maganganu suka
yi a kan Auta sosai kafin ya sanar da King shi fa baya san Mahnoor, ya tsaneta a
kusa da shi, dan haka shi ko a rabata da in da yake, ko kuma shi ya bar gidan ya
koma Dubai.

Rarrashinsa sosai King ya yi kafin ya faɗa mashi cewa ya bashi nan da kwana goma
zasu tsai da matsaya a kan hakan, amma yanzu dai ya yi hakuri suna tsaka da wani
muhimmin aiki ne. (Aikin neman Auta kenan, kun san Jaish bai san ta ɓata ba, kuma
an ɓoye mashi, so shiyasa ya ce mashi suna aiki kawai.)

Aminta da zancen King ya yi, dan haka sai ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ransa a
ɓace sosai. Kafin ya koma mama Haulat ta goge wajen da cappuccino da Mahnoor ta kai
mashi ya zuba, so ta gyara ko'ina tsab.

Yana zuwa ya haye bed ɗinsa ya kwata, yau ba za'a sha cappuccino ba kenan. Amma fa
ko da ya kwanta barci ta gagara zuwa, gabaɗaya ya rasa me yake yi mashi daɗi, shi
kaɗai sai kunci yake yi har zuwa karfe 2 na dare. Ganin bashi da wata manufa yasa
ya miƙe jiki ba kwari ya shiga toilet, alwala ya ɗauro ya zo ya fara gabatar da
nafilfili, surorinma dik a daddafe yake karantasu, sai dai kafin ya idar da raka'a
biyun farko tuni jikinsa ta wastsake ya koma normal. Qur'ani kenan my people's, dik
damuwar da kake ciki kana fara karanta shi cikin ƙanƙanin lokaci zaka ji ka
wastsake watsau, Allah dai ya ƙara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya.

Sai da ya yi sallar rakatainil fajir sannan ya bar saman daddumar ya wuce
toilet, wanka ya yi ya shirya cikin arabs jallabiya brown color, ya nufi masallaci.
Bai tawo ba sai karfe 8 na safe, jiya kwata kwata bai yi barci ba kenan.

Yana dawowa karfe 8 ɗin ma dan kada su haɗu da momma sai ya wuce part ɗin King kai
tsaye, dan a tinaninsa Mahnoor ta sanar da momma walaƙancin da ya yi mata daren
jiya, shiyasa ya gudu.

Sai dai abin mamakin shi ne ko da ya je part na King baya nan, ya tafi fada, ya sha
madarar mamakin jin hakan, me ya fitar da King fada da safe haka? Ya jefawa kansa
tambaya. Ganin babu mai bashi amsa yasa ya wuce kai tsaye ya nufi fadan.

Sosai ya kara shan madarar mamakin ganin dik wasu masu muƙami a fada sun
hallara, dik wasu manyan fada suna ciki, Aunty MieMie, uncle Abbas, uncle Jahiz,
uncle Taheer, harda Guyson dik suna ciki, abin ya yi matuƙar ba shi mamaki.

Dai'dai lokacin da ya sako kansa a cikin fadar sai ji ya yi uncle Abbas ya ce.
"Wannan babbar gazawa ce a garemu ace katafaren kingdom kamar wannan wanda babu
biyunsa a kasar nan, ga tarin tsaro wanda ba'a taɓa yin biyunsa a duniya ba, dik
wasu abubuwa muna da su, amma har a shigo a ɗauki Zunaira a cikin masarautar nan a
fita da ita yau tsawon satika shidda, kai gaskiya wannan babbar gazawa ce a garemu,
kuma a gaskiya Zafar na rai'na tsaronka, ka bani kunya".

Haba wani irin dum dum Jaish ya ji kirjinsa ta buga, har wani sara mashi ya ji
kansa ya yi.

Uncle Jahiz zai yi magana suka farga da Jaish dake tsaye a bakin kofa yana binsu da
kallo yama rasa abin faɗe, sai yake jin kamar karya kunnuwansa suke yi mashi, kamar
kuma mafarki yake yi, kenan dama Auta ba Dubai ta tafi ba? Kenan abokan gaba ne
suka ɗauketa? Babbar magana lallai yau babu zaman lafiya.

Ganinsa tsaye a bakin kofar shigowa ne yasa gabaɗaya suka yi shiru, King ne ya
bishi da kallon mamaki, dan bai yi zatan zai zo fada a yanzu ba.

Uncle Abbas ne ya yi karfin halin cewa. "Jaish ka shigo ciki mana, me ya tsayar da
kai a bakin kofa kuma?".

Ba musu ya ƙariso ciki, sai dai yana addu'ar Allah yasa karya kunnuwarsa suka
jiyo mashi, har zuciyarsa ta fara yi mashi tsananin zafi, dan ba zai iya ɗaukar
maganganunsu ba in dai gaskiya ce. A sofar kusa da uncle Abbas ya zauna, kansa a
ƙasa cike da fargabar amsa da zai iya samu daga bakin uncles ɗin nasa ya ce.
"Uncles ku faɗa mun da gaske abin da na ji kuna faɗa haka ne? Kada ku ɓoye mun
kamar yadda daddy ya yi, dan Allah ku faɗa mun, daddy ya ce tana Dubai, and kowa na
kira a Dubai kame kame kawai yake yi mun, ga wayarta a kashe baya shiga, please
second dad ka faɗa ina Zunaira take? Kasan ni mai iya karɓar kaddara ce a dik yadda
ta zo mun, to ka faɗa mun zan yi imani da koma menene ya sameta in kuma hakura".

Dik wanda ya ji zantukan Jaish yasan cikin tsananin damuwa da ɓacin rai yake
kalamansa, kuma sun san wlh karya ne ba zai iya ɗaukar wannan kaddara ba, kawai
yana san su faɗa mashi ne ya ji wani hali Auta take ciki, idan suka faɗa mashi
kuma sun san idan akwai abin da ya fi hauka ma zai yi masu, dan ba karamar yaki
za'ayi ba, ba zai saurari kowa ba!.
Shiru fada ya yi suna sauraron kalamansa masu kama da sambatu, dan kamar bai san me
yake faɗa sosai ba, dik cikin fadan nan babu wanda bai tausaya mashi ba, saboda
kowa yasan yadda yake da Auta, shi fa ya yi renonta, dik wanda ya ga Auta a lokacin
yarintarta to tabbas zai ga Jaish a bayanta, a tare suke koda yaushe, shiyasa suka
yi sabo sosai, har su commander sun tausaya mashi matuƙa.

Allah sarki commander har ya yi wani irin mummunar rama sosai, saboda tashin
hankalin da yake ciki a kan Hoorain, babbar abin da ya ɗaga mashi hankali ma shi ne
King ya bada umarnin gani da kisa a kan Hoorain, saboda a tinaninsu amanarsu ya ci,
kun san ya gudu ne ai, so sai aka saka dokan gani da kisa kai tsaye kawai a kansa.

Tsit fada ya yi, kowa jiran abin da King zai ce suke yi, gabaɗaya hankulansu a
tashi. King kuwa, sai da ya ɗauki a kallah 5 mins yana nazarin abin da zai faɗawa
Jaish ɗin, dan yana fargabar kalar balai'n da Jaish zai tayar masu, shi kansa yasan
bafa za'a wanye lafiya ba.
Gyara zamansa ya yi tare da ɗan yin gyaran murya, cikin natsuwa ya ce.
"Zan faɗa maka komai, amma ba yanzu ba sai mun haɗu da daddare a ɗaki, yanzu
kaga muna wani tattaunawa ne mai matuƙar muhimmanci dan haka ka bari sai mun
kammala".

Kirjinsa ne ta amsa da karfi, ɗan dafeta ya yi kafin ya ce. "No Please dad, ba
zan iya kara koda one minute bane idan har ban ji gaskiyar in da Auta take ba, you
know my condition dad, please kada.............."

Hannu kin ya ɗaga mashi alamar ya yi ba sai ya ƙarisa ba. Dakatawa da yin maganar
ya yi yana sunkuyar da kansa ƙasa, saboda wani irin bugawa da karfi da kirjinsa
take yi.

"Zan faɗa maka menene yake faru". King ya faɗa.............. Da sauri Jaish ya ɗago
kansa zuciyarsa na harbawa da ɗan karfi karfi, cike yake da fargabar abin da zai
ji, baya san jin zancen da gaske bata nan.

"Lallai ne tabbas Zunaira ta ɓata". Cewan King agin........... Dum dum ya ji
kirjinsa ta sake bugawa, take ya ji hankalinsa na neman gushewa, a wani irin zabure
ya miƙe tsaye kamar wanda ya rasa control ɗinsa.

Hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙe tsaye, uncle Abbas ne ya yi saurin riko hannunsa
yana ƙoƙarin mayar da shi ya zauna, ya ƙasa yin magana, yau tsawon sati shidda babu
Auta babu labarinta, gaskiya wanna abin ya girgizata shi. Dole ya koma ya zauna
yana tunanin yadda zai yi?.

King ne ya cigaba da bashi labarin yadda komai yawakana. Daga karshe ya rufe mashi
da cewa.
"A yanzu dai bayan assistant commander Hoorain babu wanda ya rage muke zargi
da sace Zunaira! Dik wanda muke tunanin tana hannunsu ko suna da sa hannu a saceta
mun bincika bata nan a hannunsu, Hoorain ne kawai bamu san in da yake ba, kuma muna
kyautata zaton shi ya ɗauketa!!".

Tashin hankali, wani irin zaro idanu commander Zafar ya yi, kenan dama King yana
zargin Hoorain har haka ne? Sam bai taɓa yin wannan tinani ba.

Shi kuwa Jaish zaro idanu ya yi, a miliyan ya sake miƙewa tsaye, zuciyarsa ce take
tafasa tamkar an ɗaura dalma a wuta, jikinsa har tsuma yake yi yana tuna idan da
zai ga Hoorain a yanzu sai Allah kaɗai yasan me zai faru.

Dik su uncle Abbas kallansu a kansa, sun tausaya mashi matuƙa, sun kuma shiga
damuwa dan abin da suke gudu shi ne yake shirin faruwa. Su commander Zafar dik
kallansu a kansa, suma sun tausaya mashi matuƙa.
Yana tsaye yana fuskantar King, a take ya fara zuba huci kamar mayinwacin zaki, ya
buɗe baki cike da ɗacin rai zai yi magana unexpect aka turo babbar kofar fadar aka
buɗeta.

Gabaɗayansu kai kallansu a kan kofar suka yi. Ai a miliyan commander Zafar ya miƙe
tsaye daga zaune a saman sofar da yake yana kallan kofar shigowar. A tare uncle
Jahiz da Aunty MieMie ma suka miƙe tsaye. Shi kansa King abu kaɗan ya hana bai miƙe
tsaye ba. Guyson and uncle Abbas suma a tare suka miƙe tsaye.

Dikkansu sun zaro idanu tamkar idanunsu zai faɗi ƙasa, a matuƙar razane suke binsa
da kallo. Tsaye yake cikin jarumta sosai, yana ɗauke da Auta a saman shoulder
ɗinsa, gabaɗaya jikinsa jini ya lalata, ga fuskarsa babu hularsu na mayaƙa, so face
ɗinsa ma dik ya yi dama dama da jini, da alama yaki ya gwabza kafin ya iso kingdom
of power.

Pretty na tsaye a gefensa ta riƙe hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya tallabo
Auta da shi dan kada ta faɗi, ita ma sai jini ne yake zuba a jikinta........... To
me ya faru da su kenan?.

Ciwon dake cikinta ne ya fama yasa jininta yake zuba, kallo ɗaya zaka yi wa Hoorain
sai ka razana matuƙa, saboda yadda face ɗinsa take ɗaure kamar hadari, ga wani irin
fusata dake kan face ɗinsa, jikinsa har lokacin tsuma yake yi.

Guyson ne ya katse masu wannan shirun da cewa. "Tabbas Auta ce, tabbas ita ce
a saman shoulder ɗinsa".

Kafin guyson ya gama yin magana Hoorain ya tako cikin jarunta ya nufi cikin fadar.
Sai dai yana zuwa tsakiya wasu zaƙwaƙuran warriors dake cikin fada su huɗu suka
zare takubansu tare da yi mashi zobe, saboda sun san hukuncin da King ya yanke
mashi shi ne hukuncin kisa. So sai suka kewayesa suna jiran King ya bada umarni su
datse mashi kai.

Cikin fushi da kakkausar uncle Taheer ya ce. "Kai ƙasƙantacen bawa har ka isa
ka ɗauki Zunaira da dattin hannunka? Baka san doka irin na masaurar nan bane?
(Dokar dik wanda ya taɓa jikin wata gimbiya hukuncin sare hannu ne ya hau kansa) Ko
ka manta da dokar ne kare kawai?". Ransa ta sosu ne matuƙa.

Ko kaɗai Hoorain bai yi kamar ya ji abin da ya faɗa ba, haka zalika ko kaɗan bai ji
tsoron warriors da suka kewayesa ba, hasalima bai dakata daga tafiyar da yake yi
ba, kai tsaye ya nufi King. Sai binsa warriors ɗin suke yi suna jiran umarnin King
da ya tsaresu da idanu yana ganin ikon god.

Su commander Zafar dik sun rasa bakin magana, kowa King yake jira kawai. Hoorain
bai dakata ba har sai da ya isa gaban King, a nan ya sauke Auta da idanunta biyu
amma azaba ya gabata koda motsawar kirki. Allah sarki, a yau Hoorain ya sha azabar
wahala wajen cetarta ita da Pretty, mayakan da suke neman su Pretty ne suka kawo
masu hari a dab hanyarsu na dawowa gida, an gwabza yaki ba karya, da kyar ya iya
kashesu, wani mayaki ne ya ture Auta ta faɗa saman wani dutse ta fama ciwonta.
Almost mayaƙa 30 ya yi faɗa da su, ya sha wahala sosai.

Yana sauke Auta cikin fushi uncle Taheer yasa kafa ya takesa a kirji da karfi
har sai da ya ɗan yi baya baya kamar zai faɗi, bawan Allah a gajiye yake, bai shi
da kuzari sosai shiyasa uncle Taheer ya iya turesa ɗin.

Wani irin zabura commander ya yi, tamkar shi uncle Taheer ya ture, har wani girgiza
ya yi, wlh idan kuka ga commander sai kun tausaya mashi, saboda yadda idanunsa suka
yi jajir ganin irin abin da aka yi wa Hoorain.

Uncle Taheer cikin ɗaga murya ya sake cewa. "Kai kare ba da kai nike magana
bane?".

Shiru Hoorain bai yi kamar yasan da halittarsa a cikin fadan ba, sai ma juyawa da
ya yi yana san sauka kasan stage ɗin dan ya isa ga Abbonsa.

King dai ya rasa bakin magana, banda kallansu babu abin da yake yi, yana ƙoƙarin
gane gaskiya ne shiyasa ya yi shiru, kun san dama yana zargin Hoorain shi ya
saceta, to ga shi kuma shi ya dawo da ita, abin ya sanyasu a ruɗani, shiyasa King
ya yi shiru yana ƙoƙarin tantance gaskiya.

Ran uncle Taheer ne ya kara baƙanta matuƙa, cikin fusata ya umarci warriors da
suka kewaye Hoorain ɗin da su yi mashi dukan mutuwa har sai ya durkusa a saman
gwiwonsa. Da yake suma sun jima da takaicin Hoorain a ransu, sun jima suna
bakincikin yadda ya zama shugaba a garesu, shi ne mai basu umarni kuma sun fisa
shekaru, so hassada na cinsu sai basu tsaya jiran umarnin King ba, a hanzarce suka
fara kai mashi duka wai dan ma kada King ya dakatar da su basu daka shi yadda
yakamata ba.

Da ganin yadda suka rufesa da jibga zaka iya fahimtar dukan huce takaici suke yi
mashi. Wani mayaki ne ya taka shi a kirji da karfi har sai da ya yi baya baya zai
faɗi ɗayan mayakin ya sake taka shi ta baya ya yi gaba gaba ya faɗi ƙasa ya buga
kansa da jikin bakin stage ɗin.

Ko kaɗan bawan Allahn nan bai yi yunƙurin zai rama dukan da suke yi mashi ba,
saboda yasan koma me ya faru laifinsa ne, shi yake ƙoƙarin kai kansa in da Allah
bai kaisa ba, so a ganinsa ya cancanci wannan hukuncin. Amma ku kunsan da Hoorain
zai motsa dik waɗan nan mayaka sai sun gaza tafiya a kan kafafunsu ko? Dan dai ya
barsu ɗin ne.

Sosai suka shiga jibgarsa kamar waɗan da aka saukarwa da wahayin yin hakan.

A hankali Auta ta motsa, da kyar ta miƙe tsaye a kan kafafunta, idanunta har sun
rine saboda kuka, ta ƙasa iya buɗan baki ta yi magana. King yana kallanta ta fara
lallaɓawa zata sauƙo kasan stage ɗin, amma kuma King ɗin bai dakatar da ita ba, ya
bita da kallo kawai kamar dai babu shi a fadan.

Anya ba wani abin King yake shiryawa ba kuwa, irin wannan shirun?.

Cikin mayaƙan ta keta ta isa gaban Hoorain dake kwance suna dukansa, da kyar ta
iya buɗan baki maganarta can ƙasa bata fita ta fara faɗin. "Ku kyale shi, ku barmun
kayana, kada wanda ya sake dukan mun shi, ni ku dake ni a madadinsa, ku kyale mun
shi".

Su uncle Abbas dik an rasa mai bakin magana, shiru kawai suke binsu da kallo. Sai
da suka ga Auta ta nufi wajen nasa ne uncle Abbas ya yi yunƙurin sauka ya kamata
kada su jimata ciwo. Sai dai bai kai ga sauka ba uncle Taheer ya rigasa sauka cikin
zafa, yana wani huci na kishi kamar zai haɗiyi zuciyarsa.

Ita dai Pretty tana tsaye a bakin kofar shiga fada. Commander Zafar tamkar
zuciyarsa zata fashe saboda tsananin tashin hankali, ga shi kuma babu halin ya yi
magana bawan Allah, dole ya daure ya ɗauki dik hukuncin da aka yankewa Hoorain. Ta
wani ɓangaren kuma fa commander ya sha jinin jikinsa ya kuma shiga ruɗani na ganin
Hoorain da Auta, shi dai yasan sun yi yaki da Hoorain da mayakan Queen Zarina, to
ta ya aka yi yanzu kuma Hoorain ya dawo tsaginsu, shi fa wannan abin ya ɗaure mashi
kai...... Na tabbata kuma my people's kanku ya ɗaure sosai a kan wannan al'amari,
kada ku damu alkalamin princess Teema taku ta amana zan warware maku komai dallah
dallah.

Uncle Taheer yana saukowa ya damko hannun Auta, da karfi ya ɗan jata ya mikar yana
mai daka mata tsawa a kan wani dalili zata je wajen Hoorain dake matsayin bawa
ƙasƙantacce mai gadinta.

Fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, soyayyarsa ya rufe mata idanu, bata
ji bata gani ta sake komawa zata tsugunna a kusa da Hoorain ɗin dan ta hana
warriors ɗin nan dukansa.

Kunsan jinin Modarawa da balai'n kishi, to haka larabawa ma suke da kishi, kishi
bala'i ya rufe idon uncle Taheer, cikin fushi ya sake fisgo hannunta, da karfi ya
fincikota, yana san janta su bar wajen. Ƙoƙari kwace kanta ta fara yi tana kuka
hawaye bibbiyu. Ransa ne ya kara ɓaci cikin zafa ya cire hannu ya dalla mata mari a
kumatu, shi kansa bai san ya yi wannan mari ba, kishi ce kawai.

Wannan mari tamkar zuciyar uncle, uncle Jahiz, Guyson, King and Jaish ya mara,
barema Jaish da sai da ya wani ja dogon numfashi a lokacin da marin ya sauka a
kumatunta, a take idanunsa suka rikiɗe suka yi jajir, gabaɗaya gashin jikinsa har
wani mimmiƙewa suke yi saboda ransa ya ɓaci.

Guyson bai san lokacin da ya ce. "Uncle Taheer who the hell are you da zaka mareta?
For what reason ma?".

Uncle Taheer da yake cikin fushi ai bai ma san ya yi ba, kuma bai san guyson yana
magana ba, sake cire hannu ya yi zai kara mata mari sai ji ya yi cak an damki
hannunsa, ita kuma sai kuka take kara yi, a take yatsunsa biyar suka fito ruɗu ruɗu
a face ɗinta.

Wani irin zufa ne yake ketowa Hoorain a gefe da gefe face ɗinsa, jikinsa na wani
irin tsuma, wasu zara zaran jijiyoyi ne suka bayyana a wuyarsa, da karfi ya damki
hannun uncle Taheer, zuciyarsa na tafasar marin da ya yi wa kyakkyawan face ɗin
Hoonairarsa. Ita kuwa dakatar da kukanta cak ta yi ganin Hoorain ya miƙe, sosai ta
ji daɗi, dama ita bata san ya kwanta ya bari su yi ta dukansa ɗin nan.

Da karfi Hoorain ya murɗe hannun uncle Taheer baya, ji kame kass ya karya
mashi kashi, cikin ɓacin rai ya ɗauke fuskarsa da wata azababbiyar mari mai sanya
mutu zuwa duniyar shaiɗanu a mafarki ya dawo. Take uncle Taheer ya gansa a wata
iriyar duniya mai cike da wasu dodanni masu ban tsoro, marin assistant commander
yasa ya bar duniyar mutane ya rasa hankalinsa.

Sake kara mashi wani marin Hoorain ya yi take uncle Taheer ya zube ƙasa tamkar
fawa, da alama sumewa ya yi. A hankali ya dawo da kallonsa a kan Auta, har lokacin
huci yake yi kamar me.

Su kuma warriors dake dukansa cak suka dakata suna binsu da kallo, har lokacin King
bai yi magana ba, bai ma yi niyar yin magana ba, uncle Jahiz nema ya ɗan yi ƙoƙari
wajen buɗe baki yana san cewa kowa ya samu waje ya zauna su jira umarnin King, sai
dai bai iya yin magana ba sakamakon nufar su Hoorain ɗin da Jaish ya yi cikin zafa.

Miƙa hannun Hoorain ya yi ya riko hannun yana ce mata sorry, a hankali ya ɗaura
ɗayan hannunsa a saman lallausan kumatunta in uncle Taheer ya mareta, yana ƙoƙarin
rarrashinta sai gani suka yi Jaish ya sanya kafa ya taka shi da karfi, sai wani
huci shi ma yake yi tamkar wani zaki.

Shi ma Jaish ba dukan uncle Taheer da Hoorain ya yi bane ya bakanta mashi rai har
yasa ya taka Hoorain ɗin, a'a shi dan me Hoorain zai taɓa Auta da hannunsa a
matsayinsa na mayaki? Wannan shi ne ya bakanta mashi rai har yasa ya takasa.

Baya baya Hoorain ya yi saura kaɗan ya faɗi, amma abin ku da jarumi sai ya rike
kansa yana mai ɗago da kallonsa a kan Jaish ɗin. Cikin fushi Jaish ya yi kansa,
zaro takobi daga ƙugun ɗaya daga cikin warriors dake wajen jaish ɗin ya yi da nufin
y sare hannun Hoorain dan ya taɓa Auta.

Allah sarki rashin sani ya fi dare duhu, basu san irin gwagwarmayar da Hoorain ya
sha wajen kare Auta ya ceci ranta har suka samu damar sake iya ganinta ba, ai ba
dan shi ba da sai dai wata ba dai ita ba, amma saboda basu sani ba har ƙoƙarin
datse mashi hannu suke yi.

Ganin Jaish ya zaro takobin mayakin nan ne yasa Auta yin zafin namar shiga
tsakaninsa da Hoorain, kuka take yi sosai kamar ranta zai

Please Login or Register in order to submit comment