You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana buɗe idanu ta yi arba ta kyakkyawar tsuntsuwar dake hannunsa, kara ɗan
zaro idanunta waje ta yi, cike da yarinta ta saki murmushi ga hawaye basu gama
bushewa ba.
A hanzarce ta kai hannu zata taɓa tsuntsuwar. Ɗan ja baya kaɗan da ita ya yi
alamar baya san ta taɓa kenan, cike da mamaki ta ɗago da kallanta a kansa.

Tin bata nemi jin ba'asin hanata taɓawa da ya yi ba ya yi saurin cewa. "Amin afuwa,
ina tsoron ya cizan mun kene yasa na ja baya".

Sosai ta yi daɗi ya ratsa zuciyarta, irin wannan kulawa haka, ai sai yasa mutum ya
mance a duniya yake, ya mance kowa da komai.
"My Hero shi fa tsuntsu baya cizo, ya mun kyau ne sosai fa shiyasa zan taɓa".
A ɗan shagwaɓe ta yi maganar, ga murya a ɗan dashe.

Kai ya ɗan girgiza mata. "Ni dai gaskiya a'a, banyarda ba, kada in saki jiki baya
ciwo ya zo kuma ya cijeki".

"Shikenan to, dik yadda kace hakan za'ayi, amma na so riƙesa a kusa da ni in
gani, dan yana da kyau". ....... Takowa step biyu ya yi ya kariso dab da ita, a
hankali ya ɗan rage tsawonsa, sannan ya matsar mata da ɗan tsuntsun kusa da ita.

"Ki gansa a kusa da ke, amma a hannuna".

Iyayi ne fa kawai irin nata, dan kuwa tana tsoron tsuntsun, da ya matsar mata da
shi kusa da ita sai ga shi tsoronta ya bayyana, wai da ita zata nuna ita jinin
bamodare ne, wato jinin King, shi ne har da wani nuna bata tsoro a farko.

Yanzu kuma sai ga shi ta koma har da ɗan ja baya, abin dariya ma shi ne ta ɗan
kai yartsarta manuniya tana san taɓa jikin gashin tsuntsun, kun san yadda mutun
yake dankwalar abu mai zafi ko? To haka take sanya yarsarta a miliyan tana ɗan taɓa
gashin ta sake janyewa da gudu.

Shi dai Hoorain hakan ba ƙaramin birgesa ya yi ba, a duniya dik abin da ta yi
birgesa take yi, sai ma idan ta haɗa da murmushi, ya ilahi ya lilliahi, sai ya ji
tamkar ta yi ta cigaba har abada su kasance a haka. SOYAYYA MUGUN WASA.

Sai kallan face ɗinta yake yi, tana murmushi da guntun hawaye. Cigaba da wasa
da tsuntsun ta yi tana taɓa shi kaɗan kaɗan. Zuciyarta ce ya raya mata yana kallan
face ɗinta, dan haka sai ta ɗago kai da sauri.

Aikuwa karaf suka haɗa idanu da shi, da sauri ya yi yunƙurin kawar da kallonsa.
Yatsunta ta fyasta mashi a saitin face ɗinsa, hakan yasa bai kawar da kallonsa ba,
ya cigaba da kallonta ko da akwai wani sakon da zata faɗa mashi.

"Meyasa baka san haɗa idanu da ni my Hero?"........... Sake tsuntsuwar dake
hannunsa ya yi ta tashi sama, sannan ya ce. "Zo mu je in baki ruwan da kika ce zaki
sha".

Make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai a'a, sai ka faɗa mun abin da yasa baka san mu haɗa
ido".
Ajiyar zuciya ya sauke, Auta ita ma ashe ta iya rigima da yake ganinta kamar
ba haka ba, ashe dai ta iya ita ma.
"A da ne bana san mu haɗa ido saboda ban san ya zaki fassara kallona a gareki
ba, kuma ke ma kin san dokace da take a kanmu na haramta mana ɗaura kallonmu a
kanku, kin san ba wani mayakin da ya isa yake da ƴancin ya kalleku, kin san
hukuncin da yake kansa idan ya yi hakan, ni kuma bana iya ƙasa kallanki a dik time
da muka haɗu, shiyasa idan kika ɗago kika kalleni nike kauchar da kallona". Ya kai
karshen maganar yana mayar da kallonsa kasa kan kafafunsa dake cikin ruwan gudun.

"To ai a da kace, yanzu kuma meyasa kake kin yarda mu haɗa ido?". A ƙagare da
san jin amsa ta jefa mashi tambayar.

"Babu wani dalili yanzu kam, na dai saba kaucewa a da ne yasa har yanzu ma nike
yin hakan".

Murmushi ta ɗan sakar mashi kafin ta riko hannunsa da ya harɗe a saman kirjinsa, a
hankali ta sauko da ƴan kafafunta cikin ruwan da nufin ta miƙe tsaye.

Warware hannunsa ya yi da sauri ya riko nata, a hankali ya taimaka mata ta sauƙo
kasa. Unexpect ta sauke ƴan kafafunta a saman nasa dake cikin ruwan. Sosai ya ji
wani irin har cikin ransa, ita kuwa sai ta yi baya kamar zata faɗi. A hanzarce ya
sanya hannunsa ɗaya ta baya ya riko waist ɗinta.

A wani irin slow ya dawo da kallansa saman face ɗinta, sai yaga ashe shi take
kallo, yanayin yadda suka tsaya abin ya ƙayatar matuƙa, dama ga yanayin wajen fili
ne na masoya, abin ba'a magana.

Hannunta ɗaya da ya saki ya riko waist ɗinta da nasa ta kai saman shoulder ɗinsa,
da yake ya ɗan rage sawonsa hakan yasa ta iya dafa shoulder ɗin nasa. A kusa da
kusa suka kalli zuna, wani azababben kaunar juna ne ya kara ratsa zuƙatansu, sanyi
mai ni'ima ya ratsa fatar jikinsu, dikkansu basu ki su dawwama a haka ba.

"Hoorain". Ta ambaci sunansa a kurkusa kurkusa ba tare da ta zare kallanta
daga kansa ba. Ya ƙasa iya amsa mata, saboda yadda ta yi magana a kusa tasa ya rasa
control ɗinsa. He's in out of his control yanzu.

"Idan nace zan faɗi kyanka tabbas sai dai na rageta, dan baki ba zai iya zayyana
shi ba, meyasa ka ɗauki tsawon lokaci kana mun rowar ganinka?". Ta jefa mashi
tambayar tana ɗaga mashi gera guda.

Still dai da ido kawai ya bita, ya kasa iya amsawa.
"To shikenan mu je ka bani ruwan sha tin da ba zaka yi magana ba". Ta
faɗa tana sauƙo da hannunta daga saman shoulder ɗinsa izuwa damatsan hannunsa.

Rike waist ɗinta da kyau ya yi, ya kara rage tsawonsa ya ɗauketa cak, bai yi magana
ba, kuma ya gagara zare kallansa daga kanta. Ba komai yasa ya ɗauke wuta yaki yin
magana ba face zai iya ketare iyakar musulunci idan ya ce zai cigaba da biye mata,
dan haka shirunsa shi ne mafi a'ala a garesa!.

Bai zame ko'ina da ita ba sai dab in da koramar nan take ta aman ruwa, saman
wani dutse ya tsayar da ita a kan kafafunta, da yake dutsen yana da faɗi sai ya hau
sama shi ma.

Da kyar ya iya faɗin. "Wanke hannunki sai ki tara ruwan ki sha". Ya yi maganar
voice ɗinsa tana sarkewa.

Cikin wani irin shagwaɓa mai ɗaukar hankali ta furta. "Ni dai a'a ba zan iya ba,
kawai ka cire ɗayan hands gloves ɗin nan naka ka tara mun ruwan da hannunka sai na
sha".

Wani irin bargon sanyin kauna ce ta ƙara lulluɓe zuciyarsa, ya ji matuƙar daɗin
maganarta, ga shagwaɓarta dake ƙara kashe shi a koda yaushe ta yi, sai ya ji kamar
shi kam an gana sallamarsa a duniya.

A hankali ya zare hands gloves ɗayan, ya sanya hannunsa cikin ruwan dake zubowa,
tas ya wanke hannayen nasa kafin ya fara tara mata ruwan. Ɗan ƙara matsawa gaba
kaɗan ta yi dan ta samu damar sha yadda yakamata.

A hankali ta fara sha, ji ta yi tamkar ruwan zuma ne saboda daɗi, ya ilahi ya
lillahi, wato ruwan hannun masoyi daban yake in ji gimbiya Zunaira Auta.

Zuba mata idanu ya yi sosai yana ganin yadda take shan ruwan gwanin ban sha'awa.
Har ta ƙoshi ta cire ɗan bakinta bai farga ba, sai ji ya yi tana faɗin. "Ga shi
nima na tara maka da hannuna ka sha".

Mamakinta ne ya ɗan kama shi, wai ba ta ce ba zata iya tara ta sha ba? Ya aka yi ta
iya tara mashi?...............Ni kuma na ce kanta ne ba zata iya tarawa ba, amma
heronta tsab zata iya tara mashi ya sha cikin nitsuwa.
Sam baya jin ƙishin ruwa, amma da yake da hannunta mai tarin albarka ta tara
mashi nan take ya ji wani irin ƙishin ruwa ta kamashi.

Matsawa ya yi ta bayanta, ya haɗe hannayensa da nata, ya tallabo nata cikin nasa
kenan, ya kwanto da kansa ta gefen shoulder ɗinta, cikin nitsuwa ya kai bakinsa ya
fara shan ruwan. A hankali ta juyo da kallanta a kan wuyarsa, da yake yana da tsawo
sosai sai wuyarsa ma ta zamana tana da tsawo da kauri.

Bayan wuyarsa wani irin bakin gashi mai curlyn ne a kwance a wajen, gwanin ban
sha'awa da burgewa. Ji ta yi tamkar ta kai hannunta ta taɓa wannan gashi, ya tafi
da imaninta.

Shagala ta yi da kallansa bata ankara ba sai ji ta yi ya hura mata iskar bakinsa a
fuska yana ɗan limshe idanu. Ajiyar zuciya ta sauke, bata san time da wani haɗaɗɗen
murmushi ya subce mata ba. Shi dai bai yi murmushi ba, kuma babu alamarta ma a face
ɗinsa, amma ya ji sanyi a ransa na sakin murmushin da ta yi.
Ya shagala da kallan murmushinta unexpext ya ji saukar ruwa a face ɗinsa.

Wani irin jan numfashi ya yi tare da limshe idanu, a hankali ya saki numfashin. Ita
kuwa kara faɗaɗa murmushin nata ta yi tana ƙara watsa mashi ruwan.

"Sai ka yi ta kallanwa daddyna ƴan'matansa ba tare da ka nemi izni ko ka biya ba
ko? To ni ba zan bar hakan ta cigaba da faruwa ba". Cewarta kenan, tana magana tana
ɗan watsa mashi ruwa....... Oh my people's kun ji Auta da tsara zance, wai ayi ta
kallewa King ƴarsa ba'a biya ba.

Hannu ya kai saman face ɗinsa, a hankali ya sharce ruwan da ta watsa mashi ɗin,
sai ya yi kamar ya datse idanunsa da karfi ya rungumeta a jikinsa kawai kada ya
saki idan ya so daga baya ya yi istigifari, dan tana tafiya da imanisa, sai ma idan
yana kallan lips ɗinta a yayin da take magana, ohohohoho, ji yake tamkar ya sa
hannu ya matse ɗan bakin nan nata ya yi ta sha ba hutawa.

Zuba mashi ido ta yi tana jiran taga me zai yi next da ya datse idanu kam haka. A
miliyan ya zaro mata idanunsa.

Ai tsabar tsorata sai da ta yi baya baya wai zata gudu sai ta tafi luuuu zata afka
kasa cikin ruwan dake wajen. A miliyan ta kai hannunta ta capki rigarsa ta saitin
kirjinsa, unexpext ta damkosa ɗin, dan haka bai rike jikinsa ba, sai suka tafi a
tare suka afka cikin ruwan da karfi. Da karfi ta riƙosa ta kuma datse idanunta gam
tana jiran ta jisu a cikin ruwan kawai.

Kafin su kai cikin ruwan ya yi zafin namar janyota jikinsa shi ya faɗi ƙasa cikin
ruwan, ita kuma ta faɗa saman kirjinsa. Kusan a tare suka sauke nannauyar ajiyar
zuciya.

Shiru suka ɗan yi na ɗan lokaci, da yake ruwan wajen ba zurfi sosai. Ita ta tara
motsawa bayan ɗan lokaci, da kyar ta iya tashi daga jikinsa. Shi ma da kyar ya iya
miƙewa, hannunta ya riko tare da cewa. "Zo mu je mu leƙa Pretty".

Ya faɗa mata hakan ne ba dan komai ba face dan su bar wajen, yana tsoron ta jefa
shi cikin wani halin da zata sa ya kauce koyarwar addininsa.

Wucewa suka yi izuwa in da ya tsaya ɗazun yana wanke takobinsa. Hular
yakinsa ya ɗauka tare da hands gloves ɗinsa ɗaya. Yana ƙoƙarin maida hular a kansa
ta yi saurin sanya hannunta a kumatunsa. Hakan yasa ya tsaya yana kallanta. Girgiza
mashi kai ta yi alamar bata san ya saka.

"Meyafaru?. Baki san in saka ne?". Murya can ƙasa ƙasa ya yi maganar.......... Kai
ta gyaɗa mashi alamar e bata, ta yi hakan tare da karɓe hular ta wuce gaba. Shiru
ya ɗan tsaya kamar wani mai tinani. Da yaga ta ɗan yi nisa a tafiya sai ya yi
saurin bin bayanta suka nufi wajen Pretty.

Tun daga nesa Auta ta hango babu Pretty a wajen, hakan yasa ta ƙara ɗaga kafa dan
ta isa wajen da sauri, shima cikin zafa ya kara sauri dan isa wajen, saboda a ɗan
zamansa da Pretty kafin Auta ta farfaɗo sun saba, kunsan halin Pretty da san jiki
da shagwaɓa, hakan yasa suka yi sabo, har fargabar isa wajen yake yi, dan ba zai
juri rashin samunta a wajen ba.

To nima dai bari na leƙa Black world wata kila kafin na dawo sun samu matsa, amma
ina kuke tinanin Pretty ta tafi? Ko waye ya ɗauketa?.

••••••••••••••BLACK WORLD••••••••••••🔥

Wani irin haɗaɗɗen ɗaki ne wanda yake tamkar hospital, komai da kuka sani wanda ya
danganci kula da lafiya cikin gaggawa akwaisa a cikin wannan ɗaki, ga bed na
majinyata guda uku a ciki manya manyan suna shinfiɗe da kyakkyawar bedsheet na
alfarma.

Na'urorin gwaje gwaje da na bincikar cuta dik akwai su. Komai na cikin ɗakin nan
white color ne, ɗakin ya haɗu matuƙa, ga shi ko'ina tsab tsab sai tashin daddaɗar
kamshi yake yi tamkar ba ɗakin jinya ba.

Tsaye yake a gaban bed ɗin da take kwance, yana sanye da long coat fari tas har
zuwa gwiwarsa, daga ƙasa wandon jeans ne mai bala'in tsada a jikinsa, idanuwansa na
sanye da wata iriyar na'ura mai kama da glass, idan ka ganta zaka yi zatan glass ya
sanyawa dan fashion ne, amma ba haka bane, na'ura ce da ake iya ganin cikin jikin
mutum dan bincike.

Duniya ta cigaba sosai, dik in da ya tsayar da idanunsa a nan na'urar zata ɗauko
mashi dik abin dake waje a cikin fata da tsoka. Ya zubawa wuyarta idanu yana kallon
yadda wani irin kululun jini bakin kirin ya taru a wajen, ba komai ya haifar da shi
a wajen ba face take mata wuya da ya yi a daren jiya.

Ba ƙaramin kyau Black Tiger ya yi a cikin wannan shiga ba, wlh kamar ka zauna ka
tasa shi gaba ba ci ba sha ka yi ta kallansa babu kawar da ido.

Ita kuwa tana sanye da kayanta na jiya ɗin, ba'a canza mata ba, Sweetie ta ji
wuya maras kunya, da ta ce bata ji ai.

Hannunsa dake cikin white hands gloves ya kai saman wani kyakkyawan table dake
kusa da bed ɗin wanda yake shake da kayan aiki da dik wani abin da zai buƙata.

Cotton and zolpidem ya ɗauko, fasa zolpidem ya yi, cikin kwarewa ya kai hannunsa
saman ɗan bakinta, da ɗan karfi ya buɗe bakin nata ya ɗaura mata kwayar zolpidem
ɗaya a saman tongue ɗinta, sannan ya sanya cotton dake hannunsa a saman bed saitin
wuyar tata ta yadda jini ba zai taɓa bedsheet ba idan ya fasa wuyar tata.

Scalpel ya ɗauko don yin yankan, ko ɗigon tausayi babu a ransa yasa wannan Scalpel
ɗin a saman fatar wuyarta, ɗago idanunsa ya yi ya kalli face ɗinta na ƴan sakanni
kafin ya mayar da kallansa a saman wuyar tata.

Cikin nitsuwa ya yanka fatar wuyar yanka mai ɗan girma. Nan take wani irin jini
jajir ya faso hanya, wai a haka ma fa ta gefen wuya ne jinin ya taru ba ta gaba ba.

Wani cutton ya ɗauko mai ɗan girma ya fara goge jinin dake bulbula kamar famfo.
Tiyata fa likita guda ɗaya baya yinsa, saboda babban aiki ne, dole sai da
taimakawan wasu a kusa suna miƙo maka wasu abubuwan, amma shi saboda kwarewa shi
kaɗai yake yinta.
Ganin jinin yaki raguwa ya samu ya yi aikinsa yadda yakamata ne yasa ya ɗauko
suction device dan tsotse jinin dake waje a hankali. Nan take kuwa jinin ta tsotse.

Sake ɗauko ecy da hemostat ya yi dan ya tsaida jinin da zasu iya yi wa aikinsa
barazana daga ƙananan jijiyoyi.

Cikin nitsuwa ya sake sanya Scalpel ya yanka namar ciki in da jinin ya taru. Nan
take jini bakin kirin ya fara zuba, kurawa namar wajen ido ya yi, sai yaga wajen ya
yi wani irin dark brown haka alamar kamar ya samu matsala, ya taketa sosai ne wlh.

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan ya gano dole ya yanke namar dake wannan wajen, dan
haka sai ya ɗauko electrocautery bayan da wannan bakin jinin ya gama zuba. Amfani
da shi ya yi ya yanke namar dake wajen haɗe da tsotse jinin tas.

Dik da tana sume sai da ta tsuke fuska alamar azaba. Tsab ya fitar da jinin kafin
ya kara sa cotton fari tas mai tsabta ya kara tsabtace wajen. Sannan ya ɗauko
needle holder da zaren tiyata dan ɗinka wurin.

Ko kaɗan babu tausayi a ransa, haka ya ɗinke mata wajen tas ya kuma sanya plaster,
daga nan ya tattare dik wasu abubuwan dake wajen ya mayar da su mazauninsu, ya
ɗauki s-z ya matsar da shi kusa da shi, sannan ya zare hands gloves dake hannunsa.
Ya yi amfani da s-z a hannun nasa dan tsabtaceta. Cikin kwanciyar hankali ya ɗauki
remote ya kashe A.c dake ɗakin mai gabaɗaya.

Sannan ya cire coat dake jikinsa. Yana cirewa wani Robbot ɗaya daga cikin masu yi
mashi aiki ya matso ya karɓi coat ɗin, shi kuma ya nufi waje da sauri cikin zafa
abinsa.

A ɓangaren Ronnie kuwa, tun da ya yi wannan barci na dare jiya sai da rana ta
take sannan ya iya farkawa. Da sunanta a bakinsa ya farka, a razane kuma. Sai dai
kuma da kyakkyawar fuskar yayansa ya fara yin tozali ba ita ba.

Hankali a tsananin tashe ya ce. "Yaya where's Sweetie?".
Black Tiger yana zaune a gefen bed ɗin yana kallansa, yana sanye da kayan shan
iska da suka kara bayyanar da kyakkyawar surar jikinsa, shi kuma ya kara haska
kayan yadda yakamata.

Miƙewa tsaye ya yi ya bar wajen. Cikin Zafa Ronnie ya miƙe zaune a saman gadon,
hankalinsa a tsananin yashe ya ce. "Please big bro where's Sweetie? Talk to me
please and please". Hankalinsa a tashe ya yi maganar.

Black Tiger bai goge mashi tinanin kwakwalwarsa bane kawai saboda Sweetie tana
raye, a tinaninsa ta mutu shiyasa ya yi niyar shafe mashi brain, ganin tana raye
yasa bai yi hakan ba, ya ɗaga masu kafa.

Ƙasa Ronnie ya diro, da sauri ya bi bayan yayan nasa yana cigaba da bashi hakuri
da ya faɗa mashi ina Sweetie take, har kuka sai da ya yi, ya cigaba da magiya.

Dik kaunar da Black Tiger yake yi mashi yaki faɗa mashi in da take har tsawon sati
biyu cir, har zazzaɓi Ronnie ya yi amma Black Tiger yaki kula shi ya faɗa mashi ina
yake, shi da ya yi mata aiki dai yana zuwa ya dubata ya canza abin da yakamata a
canza, amma yaki sanar da Ronnie har sai da ta farfaɗo cikin ƙoshin lafiyarta,
sannan ne ya faɗa mashi tana cikin wannan ɗaki.

Ɗakin ma a cikin bedroom ɗinsa take ta wata hanyar sirri da aka yi ta da da glass.
Ni kam na ce ko ba komai Sweetie ta ciri tuta tun da ta shiga wannan ɗaki da iya
shi da Ronnie kawai suke jinya a ciki, ɗaki na musamman, amma saboda Spender sai ga
shi ita ma yau ya kasance a ciki, ɗakin da da ace mutuwa tana da magani to da
tabbas za'a iya samun maganinta a cikin wannan ɗaki, saboda kwarewarsa a iya aiki.

Sai dai wani abin da baku sani ba, Black Tiger ya fahimci Sweetie ba zata bashi
haɗin kai wajen mallakar Spender ba, dan haka ya fara tinanin zai yi mata aiki
wajen zare tinanin kwakwalwarta ya sakawa wani daga cikin Robbot ɗinsa dan ya samu
Spender.

Idan kuma ya yi mata wannan aiki to tabbas ba zata tashi ba, yanzu haka ya sanya a
kowacce irin yanayi a shigo mashi da kayan aikin cikin kasarsa domin ya kaddamar da
wannan aiki, saboda ya ga Sweetie fa ƴar a mutu ce, bata tsoron mutuwa bare ya yi
mata barazana da shi ya ci galaba. Abu mai sauki kawai ya cire ƙwaƙwalwarta ya yi
dashenta ga Robbot ɗinsa, sai dai kuma fa, in ya cire ƙwaƙwalwarta ya haura 30 mins
bai yi saurin sanyawa robbot ɗin ba to zasu rasa tinaninta, dan kwakwalwar zata
dai'na yin aiki kwata kwata......... Babbar magana. Akwai matsala fa.

Jin in da take yasa bai wani ɓata lokaci wajen kai kansa gareta ba, a lokacin
ta kai sati da farfaɗowa, da yake ciwon ma ba wani babba sosai bane har ta samu
sauki ba laifi, tana iya yin magana dik da ba wani sosai ba, kuma Allah ya
taimaketa babu wani jijiya da ciwon ya taɓa.

Tana ganin Ronnie ta yi saurin miƙewa zaune, dama shi take dakon jira tsawon
kwanaki, tun da ta farfaɗo bata ga kowa a ɗakin ba, dan Black Tiger ya daina zuwa
tin da yaga ta farka.

Ta rasa ina zata sa ranta, ta kwana ta wuni tinanin ina Ronnie yake, bata tinanin a
in da take kamar yadda take tinanin a ina Ronnie yake. Shi ne yasa tana ganinsa ta
yi gaggawar miƙewa zaune, shi ma da sauri ya ƙarisa cikin ɗakin.

Yau satinsa biyu da musulta amma ko sallah bai taɓa yi ba, dan bai san yadda ake yi
ba, ita da zata koya mashi gata a kwance bai ma san ina take ba sai yau. Dan haka
yasa bai yi ba sam sam, kuma a ƙagare yake da ta koya mashi ya yi ɗin, dan addinin
ta ratsa zuciyarsa sosai.

Tsabar farinciki yana zuwa saman bed ɗin ya haye, cike da farinciki ya fara yi mata
sannu yana kara bata hakuri, zuciya a karaye ya ce. "Sweetie yaya yafi karfinmu, ba
zamu iya da shi ba, kawai ki barshi mu hakura". Ya yi maganar tare da riko hannunta
yana murnar bata mutu ba.

Kai ta girgiza mashi, cike da kwarin gwiwa ta ce. "Bai fi karfinmu ba, kuma bai
isa ya fi karfinmu ba, saboda mu Allah muka rike, da izinin Allah zamu canza
yayanka, babu gudu ba ja da baya sai ya musulunta, dik azabtarwa da zai yi mana
matuƙar ina numfashi ba zan janye kudurina ba".

Zaro idanun Ronnie ya yi sosai, cike da tsoro ay ce. "Sweetie kin ga abin da ya
faru dake? Baki tsoron idan ya zo da ƙarar kwana ki rasa ranki?".

Ko a jikinta ta ce. "Tabbas idan na mutu a wannan hanya sai na fi kowa
farinciki, a kan jahadi na mutu, a kan haryar isar da saƙon Allah da hidimtawa
addini na mutu, dik wanda ya mutu a kan wannan hanyar ya yi shahada Ronnie, dik
kuma wanda ya yi shahada makomarsa aljanna ce, dan haka babu gudu ba ja da baya, a
da ina tsora ce da hakan, amma yanzun na kara samun kwarin gwiwar zan iya".

Sosai ya yi mamakin jin kalamanta, ya san da farko a tsorace take, to yanzu menene
ya bata confidence har haka?.

"Kana mamakin menene ya kara mun kwarin gwiwa kenan ko?". Ta jefa mashi tambayar
ne ganin cewa ya afka duniyar tinani.

Kai ya gyaɗa mata alamar e abin da yake tinani kenan. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce.
"Ba komai ne ya kara mun kwarin gwiwa ba face wasu abubuwa da na gano dangane da
yayanka".

Like wow ya zaro idanu, a ƙagare ya ce. "Wani irin abubuwa kenan?". Ɗan girgiza kai
kaɗan ta yi alamar ba zai gane ba kenan, sannan ta ce.
"Ba lallai ka fahimta ba, amma dai na gano cewa yayanka yana da bala'in saurin
fusata, na biyu kuma baya saurin sauka idan ya yi fushi, na uku kuma tabbas bayan
zuciyarsa fara ce, gaban ce aka dabaibayeta da bakar fenti, tabbas idan muka yi
galaba a kansa mutane dayawa zasu ji daɗi su huta, ina da yakinin akwai abin da ya
rikiɗar da shi izuwa bakin mugu....."

Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Ai na faɗa maki tsananin kaunar mulki ya rikeɗar
da yaya izuwa mugu".

Kai ta girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ɗaura da cewa. "Ba tsananin kaunar mulki
bane ta rikiɗar da shi, akwai abin da ya saɓa, tabbas yana san mulki, amma bayanta
akwai abu mai karfi da ya rikiɗar da shi, tabbas zan gano ko menene nan na da
jimawa ba dan saukaka aikin mu". Babbar magana, amma me kuke ganin ya rikiɗar da
Black Tiger izuwa azzalumi idan ba giyar kaunar mulki ba?.

"Sweetie zaki iya kuwa?". A tsorace ya jefa mata tambayar.

"In Sha Allah zan iya, samun kwarin haske da na yi a kansa ba ƙaramin taimaka mun
zai yi ba, kaga yanzu zan san ta yadda zan gudanar da aikina a kusa da shi, zan san
ta yadda zan guji ɓacin ransa da zai iya sakawa ya cutar da ni, sannan zan koyi
yadda zan sarrafa ɓacin ransa a dik lokacin da Black heart ɗinsa zata motsa, yanzu
ka koya mun yadda zan yi amfani da magic ɗina, dan shi ma zai taimaka mun wajen
ganin na sarrafa Black heart na yayanka".

Shi kansa a yanzu ya samu kwarin gwiwa jin kalamanta, ya ji kuma kamar

Please Login or Register in order to submit comment