You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai kyau da ɗaukar hankali take, ta zama big girl mai
class yar gayu.

Sai dai har yau har gobe tana kukan sauyawar da Jaish ya yi, ya tashi daga hammanta
izuwa Jaish, kuma kullun idan ta gansa bata gajiya da yi mashi magana, ko ya amsa
ko karya amsa sai ta yi mashi.

Kai tsaye part na mama ta nufa dan ta je wajen Zee, yanzu sun fara sabo da su
Zee, kuma Zee tana koya mata karatu bata da matsala, rike take da takardanta ma a
yanzu, ta yi jagwalgwalan rubutunta kamar tafiyar tsutsa shi ne zata kaiwa Zee ta
duba mata.

Har zata shiga part ɗin mama sai ta kalli kofar part dake fuskantar nasu mama ɗin a
buɗe. Mamaki ne ya ɗan kamana ganin cewa bata taɓa kallan kofar a buɗe ba, da sauri
ta dakata daga shiga side ɗin mama, babu ko tsoro a ranta, bata san bedrooms ɗin su
waye a wajen ba kawai ta nufa abinta, tana tafiya babu ɗar ɗar bare waige waige.
Kai tsaye ta shige ciki.

Babu ko sallama ta afaka masu cikin parlournsu. Suna zuane a saman sofa suna aikin
latsan waya, Obaid ya tada kai da cinyar Omaid yana video call da Sharifat, shi
kuma Omaid yana waya da ɗaya daga cikin class mate ɗinsu, su da basa murmushi
saboda muguntar da ta yi masu yawa sai ga Omaid yana ɗan murmusawa alamar waya ta
yi daɗi kenan.

Shirye suke cikin sleeping dress ɗinsu iri ɗaya, kayan ya yi matikar yi masu kyau,
Omaid ya tara gashinsa ta yi tsawo, shi kuma Obaid ya yanke arab hairn nasa, ya yi
irin askin guyson, kuma ya yi kyau, ga shi dikkansu sun yi gyaran fuska, ƴaƴan
momma fa ɗaukar wanka a jininsu yake, wlh dik kalar wankan da suka ɗauka kyau suke
yi wa wankan.

Ganin mutum a tsakiyar parlon nasu yasa Obaid sarkin zafa ya miƙe zaune yana binta
da kallo tare da katse call da yake yi, shi kuma Omaid kallan wutsiyar ido ya bita
da shi suna mamakin zubin halittarta, a cewarsu ta yi siririya sosai.

"Who are you?". Omaid ya faɗa ba tare da ya kalli in da take tsaye ba, kallan gefe
ya bita da shi.
To ita dai ba jin turanci take yi ba, dan haka bata san me suka faɗa ba, da
ɗan gara ma larabci ne yanzu ta iya dik da ba wani mai zurfi sosai ba, amma zata
iya maganar minti uku cikakke da kai da larabci, abin da yasa kuma ta yi saurin
iyawa saboda zamanta da su mama Haulat, babu wani yare da zasu iya magana da juna
dole sai larabci, hakan yasa ta yi saurin iyawa.
So bata san me suka faɗa ba, sai bata amsa su ba, ta tsaya shiru tana binsu
da kallo, taga zubin halittar Jaish a tattare da su, kun san tun da suka zo basu
haɗu da ita ba.

Obaid sarkin zafa ne ya daka mata tsawa cikin harshen larabci. "Zaki faɗa mana
wacecce ke da abin da ya kawoki part ɗinmu ne ko sai na tashi na kakkaryaki?". Yana
magana yana kara ɗaure fuska.

Sarai ta ji wannan magana da ya faɗa, kun san bata barin ko ta kwana, jin zai
daketa da ya faɗa yasa ta sanya hannu ta rike waist ɗinta da kyau, kallan up and
down ta bisu da shi kafin cikin tsiwa ta ce.

"Tun da kai ka halicceni ba sai ka dakeni in gani ba! Kana tinanin ma barinka
zan yi ka taɓa ni ne? Wlh baka isa ba, ramawa zan yi". Tana jajjagen masifar tata
kuma tana kallon kofar fita, ta gama yin ready kis take jira ta yanka waje a
miliyan.

Kun san Obaid dama shi baya da hakuri ko kaɗan, aikuwa ransa ya
gama ɓaci, a gabaɗaya kingdom of power babu wanda yake yi masu nasiha cikin ruwan
sanyi ma ya zauna lafiya sai Jaish bayan Momma, amma saboda tsabar aljanun kanta na
guguwar bishiyar kuka ce zata tsaya a tsakiyar parlournsu, su tambayi meya kawota
har ta ce zata faɗa masu magana, wlh yau sai dai wata ba ita ba koma ƴar uban
wanene ne.

Sai huci yake yi ya miƙe tsaye, Omaid ne ya yi saurin rike hannunsa
yana faɗin. "Kai mezaka yi mata?". A fusace ya amsa da. "Mekake tinanin zan yi
mata? Ni ka sakeni dan Allah hai".

"Obaid kana tinanin in ka taɓa wannan tsinken tsintsiyar zata rayu ne? Ka
rabu da ita kada ka je ka yi kisan kai, ka ganta fa kamar sandar mopa...........".

Ana ƙoƙarin bashi hakuri a taushesa amma yarinyar nan tun Omaid bai gama
rufa baki ba ta cafke zancen da cewa. "Tun da dik cikinku babu ɗan iskan da ya yi
mun halitta sai ku rufe babin batun halittata, da kake ce mun sanda kai ya kake? Da
shegen idanunka manya manya kamar na shaiɗan"......... Kai jama'a ko a ina Mahreen
ta taɓa ganin shaiɗan har tasan idanunsa manya ne? Omaid kai ma ka shiga layin
littafin Mahreen.

Ai sake Obaid Omaid ya yi, wato ya je ya lallasata kenan tin da ita bata
san mutunci ba. Tana tsaye ya nufota cikin zafa, sai da ta bari ya kusanta sai ta
yanka waje a miliyan. Ai da gudu ya rufa mata baya, shi kuma Omaid ya cigaba da yin
wayarsa abinsa.

Kai tsaye part ɗin momma ta nufa da gudun gaske. Tana sanyo kai suka ci karo da
guyson da ya fito daga bedroom ɗin momma zai koma nasa dare ta yi. Karo suna yi a
in da ya ɗan yi baya yana dafe goshinsa da ta bugesa.

Ita kuwa da yake tasan abin da ta tsokano sai bata tsaya ba, a guje ta raɓa gefensa
zata wuce, da sauri ya riko hannunta, cikin natsuwa ya ce. "Lafiya kike gudu haka a
cikin daren nan?".
Ƙoƙarin kwace hannunta ta yi dan ta ruga da gudun ta karisa ciki.

Shi kuma bai gama rufe baki ba sai ga Obaid ya iso wajen da gudu. Da karfi ya sanya
hannu zai fisgota daga rikon da guyson ya yi mata yana wani huci. A hanzarce guyson
ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Ku dakata mana, lafiya Obaid ka biyota? Me ta yi
maka?".

Har lokacin ƙoƙarin kwace kanta take yi ta gudu. Ɗaure fuska sosai Obaid ya yi,
cikin ɓacin rai ya zayyana mashi dik abin da ya faru, daga karshe ya ce wlh idan
bai karyata pieces ba ba zai iya yin barci ba yau. Dik da guyson yana rike da ita
yana ƙoƙarin kashe wutar da ta kunna bakinta bai rufu ba, dan kuwa tana jin Obaid
ya ce sai ya karyata cikin tsiwa ta ce.

"Ka karyani tun da ni itace ce, da wani shegen ido kamar na shaiɗan na faɗa na
kara faɗa".
Me guyson zai yi idan ba murmushi ba, shi ya rasa wace iriyar yarinyace, ji fa,
ana ƙoƙarin kashe wuta tana kara kunna wani.

A fusace Obaid ya matsota yana faɗin. "Yah Omar dan Allah ka kyaleni in karya
yarinyar nan".
"Dakata dakata Obaid, wai baka ga mace bace? Me zaka daka a wajen? Su mata ai
babu gurbin duka a jikinsu ko?...........".

Guyson bai gama rufe baki ba ta capki zancen da cewa. "Kai kana tinanin kana da
karfin dukana ne da kake wani tadada jijiyoyin wuya? Wlh ni na ci dubu sai ceto,
kuma kai ma ka sakeni tun da baka da wani karfi mai kukan ciwo kawai". A karshen
maganar tata da guyson take yi, wai bashi da karfin tare mata faɗa tin da yana
kukan ciwo, larabcin nata ne a karkace.

Sarai Guyson ya fahimci kalamanta, ya fahimci zaginsa ta yi, amma da yake shi
ɗin damone sarkin hakuri, sai ya yi kamar bai ji ba, yasan idan ya barta da Obaid
wlh ko momma ba iya kashe wannan wuta zata yi ba, dan ko an bashi hakuri ya tafi
sai ya sakar mata kunama ko kwari, basa yafiya ai, dan haka solution kawai ya kashe
wutar a nan mai gabaɗaya.

Capka Obaid ya kai mata da karfi zai shaki wuyarta Guyson ya yi saurin janyeta da
karfi sai ta tafi ta faɗa saman kirjinsa, a hanzarce ya ce. "Obaid ka kyaleta mu yi
magana mana".

"Ni Yah Omar ka barni in take bakin yarinyar nan sai hakwaranta sun cire
gabaɗaya". "Aa Obaid, ba za'ayi haka ba, ka bari za ta baka hakuri..........". Bai
kamala kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon turesa da karfi da ta yi har ya
yi baya kamar zai faɗi. Cikin tsiwa ta ce. "Kai ɗan iska ne ashe? Allah ya isa da
ka rungume ni". Tana magana tana galla mashi harara.

A zabure Obaid ya nufeta yana dunkule hannunsa ɗaya zai kai mata duka a baki,
damo sarkin hakuri bai gaji ba ya sake shiga tsakaninsu, bai damu da kalamanta ba,
dan yasan yarinya ce, kuma girman kauye ce, fin haka ma zata aikata, kuma shi wlh
burgesa take yi sosai, yana san mace mai confidence kamar Aunty MieMiensu, hakan
yasa in dai ya shigo bai ganta a wajen momma ba sai ya tambayi ina take, tun da
suka sha gyara suka fito a ƴan gayu take burgesa take kuma yi mashi kyau, shiyasa
ya zage ya tsaya rabata faɗa da Obaid.

Ran Obaid ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dan haka sai ya sakar mata kunama guda
biyu. Tana ganinsu ta zunduma ihu tare da daka sufa ta ƙanƙame guyson, kamar ba
yanzu ta turesa tana kiransa da ɗan iska dan ya janyeta daga capkar Obaid ba, sai
ga shi yanzu da kanta ta rungume shi tana ihu kamar zata tashi gidan da kuka, tana
faɗin ya taimaka mata.

A lokacin momma ta tafi wajen King ta je ta rarrashesa ko zai sauko, so bata
nan. Part na su Jaish kuma ba kusa da na momma yake ba shiyasa basu ji ihunta ba.

Da gudu Omaid ya iso wajen dan ya ji ihun, a tunaninsa lallasata Obaid yake yi yasa
take kuka haka, so gudun kada ya kasheta yasa ya biyo bayansu da gudu.

Riketa sosai guyson ya yi yana ƙoƙarin kare mata kunamar. Obaid yana tsaye yana
kallansu, a tinaninsa kunamar ba zata yi wa guyson komai ba tun da Mahreen ya
sakarwa, sai dai bai ankara ba sai gani ya yi ɗaya ya sakewa guyson harbi a kafa,
dai'dai lokacin kuma Omaid ya iso ɗin.

Azaban zafi yasa ya yi gaggawar saketa tare da tsugunnawa ƙasa yana ƙoƙarin riko
kafar nasa. Ita kuwa yana saketa ta yanka a miliyan sai bedroom na momma.
Kusan a tare Omaid and Obaid ɗin suka zube gwiwowinsu a gaban guyson ɗin
tare da kai hannunsu a kan kafar nasa, hankalinsu ne ya yi mummunar tashi, ga shi
Jaish and Omerish suna gida, yau sun shiga uku, sun san idan brothers ɗin nasu suka
samu labarin kunama suka saki ya cutar da guyson yau ba mai karɓarsu, dama Jaish ya
jima da hanasu sake kunamar nan, amma basu dai'na ba.

Hankalinsu a tashe Obaid ya fara bawa guyson hakuri kamar zai yi kuka, Omaid
kuma miƙewa ya yi tare da zura wayarsa a aljihun wandon sleeping dress ɗin jikinsa,
sannan ya tattare karfinsa dikka ya ɗauki guyson cak, sai sorry suke ce mashi, kai
tsaye cikin bedroom ɗin momma suka wuce da shi, tuni fuskarsa ta wanke da hawaye,
rago a ciwo ba. Sosai yake kuka ga harbin kunama da balai'n zafi.

Abin mamaki, ko da suka shigo bedroom ɗin momma basu ga Mahreen ba, kuma tabbas nan
ta shigo, sai dai ɓuya ta yi a wani wajen dan kada Obaid ya biyota ya kamata, ita
bata wani damu da kunamar ya harbi guyson ba, ita dai ba ta samu ta tsira ba ai
shikenan kuma.

Saman bed suka kwantar da guyson, a gaggauce Omaid ya fara ƙoƙarin cire mashi dafin
kunamar, shi kuma Obaid ya ɗaura kan guyson ɗin a saman cinyarsa ya hau rarrashinsa
yana goge mashi hawaye yana kara bashi hakuri da ya yafe mashi. Hankalinsu a
tsananin tashe matuƙa.

Wlh Mahreen sai shirin Allah, haka kawai ta ja bawan Allah ya samu tsarabar
harbin kunama, har wajen ya kumbura sosai, ita kuma ta gudu abinta, wlh idan aka
bar Mahreen da su Obaid su kaɗai sun isa su tada kingdom ɗin nan, zasu tada
zazzafar yaki wlh.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

SARINA.

Tana shiga parlon Jaish ta zare alkyabbar jikinta ta ajiye saman sofa, wai dan
Smart ya kwaɗaitu da kyakkyawar surar jikinta...................... Yarinya, wai mu
faɗa mata daga cikin masu jajayen kunnuwa masu yawo kusan tsirara ya fito ne ko dai
mu yi shiru?.
Zuciyarta na shakkar tinkarar bedroom ɗin, amma burin da take da shi a kansa ya
fi wannan yawa, san nan Mammienta ta kara mata kwarin gwiwa tare da ce mata yana
shakar wannan kamshin perfume ɗin shikenan ba zai iya yi mata musu ba, dan haka sai
ta ji ta kara samun kwarin gwiwar tinkarar bedroom ɗin tun da babu abin da zai yi
mata.

A maimakon ta yi mashi sallama irin ta addinin musulunci ma sai ta wani kashe
murya ta ce. Excuse me. Bata jira umarni ba ta turo kofar kawai ta shiga, tana ta
faman yauki kamar hawainiya.

Tana sanya kanta cikin ɗakin ta ja birki a bakin kofar ta tsaya, lokaci guda
cup ɗin hannunta ya suɓuce ya faɗi kasa ya tarwatse, gabaɗaya cappuccinon ya malale
a ƙasa. A miliyan ta zaro idanunta gabaɗaya waje, tamkar zasu faɗo ƙasa, cikin wani
irin karuwin murya ta ce. "Wow, handsome, gorgeous and sexy guy with sexy body".
Babbar magana!!!.

Ba komai yasata yin wannan zabura da sambatun ba face Smart, kyakkyawa kuma
kakkarfar surar jikinsa ya ruɗar da ita, ya fito daga wanka kenan yana sanye da
bathrobe na Jaish a jikinsa, so bathrobe ɗin ta yi mashi gajere dan ya fi Jaish
tsawo, bata gama rufe mashi cinyoyinsa ba, kun san mutumin da balai'n kyau, ga arab
hairnsa a jike yana ɗigan ruwa, sajensa ta kara kwanciya luf, fuskarsa ta kara
haske sosai, hakan yasa ya tashi kanta matuƙa.

Anya a jikokin Akka a mata ba Sarina bace ta yi gadon abar kuwa? Jarabar yarinyar
nan dayawa yake.

Yana tsaye a gaban mirror yana shiryawa, Auta tana kwance a saman bed ɗinsa ta yi
barci, shi kuma guyson ya tafi wajen momma tun ɗazun.

A hankali ya ɗago idanunsa ta cikin mirror ya yi mata kallo guda ya kawar da
kallonsa, cigaba da abin da yake yi ya yi tamkar bai san da halittarta a wajen ba.
Ganin hakan yasa zuciyarta ta saƙa mata ai ta matsa kusa da shi ya samu damar
shakar kamshin perfume ɗin nata kafin ta cigaba da santin kyan jikinsa, har tinani
take yi a ranta gata kwance a saman lion chest ɗinsa tana wasa da ɓul ɓul ɗin
breast ɗinsa saboda jarababbiya ce ta karshe yarinyar nan.

Ta manta ma da batun ta ɓarnatar mashi da cappuccino, ta ɓata mashi ɗaki dan
jaraba amma dik bata bi ta kai ba, cikin yanga ta fara taku tana jin faduwar gaba,
amma haka ta daure ta isa gabansa.

A kusa da shi ta tsaya na ƴan sakanni, sai da zuciyarta ta tabbatar mata da ya
shaki kamshin perfume ɗin, sannan ta kara matsawa kusa da shi, Sarina bata tsoro
kuma bata da hankali my people's, ko da yake Mammienta ce ta ce mata in dai ya
shaki kamshin shikenan ta yi mashi dik abin da take so bashi da bakin yin magana
sai abin da ta ce kawai.

Dan haka tana ganin alamar ya shaka ta matsa dab da shi, yana ƙoƙarin zuba lotion
a hannunsa dan ya shafa a jikinsa kawai sai ganin hannunta ya yi ta rike robar man,
a tinaninta zai ɗago ya kalleta ne dan ta rike robar, sai taga akasin haka, bata
san shi daban yake da kowa ba, ba komai yake ɓata idanunsa dan kalla ba.

"Yah Omerish ni yakamata in zuba maka man ka shafa ai, idan kana so ma ni zan
iya shafa maka ai, tin da kai nawa ne". Cikin salon kirsa da kisisina ta yi maganar
tana wani make murya kamar akuya mai jego.

Shiru bai yi kamar yasan da wata halitta a wajen ba, a ransa yana tinanin wai a
cikin kannensa ne a ka samu fitsararriya mara kunya har haka? To me aikin Jaish
kenan da bai gyarawa shegiya zama ba? Dama su Jaish haka kenan suka saki gidan kowa
yana yin abin da ya ga dama basa cin kaniyarsu su gyara masu zama? Lallai da sake,
dole ya sako tarbiya kuwa, dan ba zai ɗauki wannan iskanci ba, me banbancin kannen
nasa da Heleena da ya ɗaurawa karar tsana kenan? Ai basu da wani banbanci, ya
gyarawa Heleena da ba abin da suka haɗasu ma zama bare kannensa?

Kunsan da farko ita ma Heleena ta so ta kawo mashi iskanci ta rinƙa taɓa jikinsa,
watarana kawai ya ware rana ɗaya ya ci uban hegiya daga lokacin ta haɗa malaman
jikinta ta natsu, shiyasa kuka ga tana tsoronsa kamar ta mutu, bugu ta ci a
hannunsa.

Yana tsaka da tinani unexpect ya ji saukar hannunta a saman hannunsa da yake rike
da robar tana faɗin. "Yah Omerish bari ma kawai in murza maka man da kai'na".
Tashin hankali, lallai Sarina ta wuce yadda ake tinani.

Sake mata robar ya yi ya zame hannunsa, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta
sauke, a tinaninta aikin Mammienta ya ci, ta samu kan Smart, sai ta wani ji bargo
mai sanyi ya lulluɓe zuciyarta. Kawo robar man kusa da ita ta yi, tana ƙoƙarin zuba
man a hannunta da nufin ta murza mashi a jikinsa tana wani fari da ido unexpect ta
ji lokaci guda ta dai'na gane komai, sai ta ji kamar bata duniya, irin mutum ya ji
komai ya tsaya mashi cak, shi kansa robar man dake hannunta sai ganinsa ta yi a can
tsakiyar ɗakin, wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta ta tafi ta zube ƙasa.

Ba komai ya ja mata hakan na face wani irin mari da Smart ya ɗauketa da shi, tass
kake ji, kunnuwanta gabaɗaya sun dai'na jin sautin komai.

Bai bari ta dawo cikin hayyacinta ba yasa kafa ya yi ball da ita sai da ta tafi
ta bugu da jikin bango. Daga nan ta ƙarisa dai'na gane komai gabaɗaya. Taku biyu ya
yi ya isa in da take, hannunta da ta sanya a saman nasa lokaci da ta karɓi robar
man ya take da kafarsa, ga shi in da ya taka ɗin ta wajen kashi ne, hakan yasa ta
ji wani irin azaba ya ziyarceta.

Da karfi ta kurma wani irin ihu mai sautin gaske, ɗauke kafarsa daga kan hannunta
ya yi ya take bakinta da take yi mashi ihu da kafar tasa, take bakin nata ya fashe
sai jini. Belt ya ɗauko daga dressing room na ɗakin, yadda kuka san wanda yake
jibgar katan gardin namiji haka ya fara saukar mata belt ɗin nan a jiki.

Ihu ta fara kurmawa mai sautin gaske, ko a jikinsa tamkar wanda aka saukarwa da
wahayin duka haka ya yi mata lilis har sai da ya ji zuciyarsa ta ɗan samu natsuwa,
sannan ya dakata da dukan nata, dik ya fashe mata jiki, ga shi ba kayan mutunci
bane a jikinta bare su ɗan saukaka mata zafin belt ɗin, ga belt ɗin da kauri, ta
zanu ba karya.

Ga shi Jaish baya part ɗin bare su ji ihunta su kawo mata agaji, yana can
hospital shi da Mahnoor, shiyasa Sarina ta daku babu wanda ya kawo kata agaji.
Ihunta ya tashi Auta daga barcin da ya ɗauketa. A tsorace ta miƙe zaune a saman bed
ɗin. Ganin zane Sarina yake yi yasa Auta ta fara ruwan hawaye.

Yau Sarina sai da ta kira ainahin sunan Mammiensu na yanka saboda jibgar da ta sha.
Bakin bed Smart ya koma ya zauna, cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa a kan ta
tashi ta zo gabansa. Ai tuni tsawansa yasa ta dawo cikin hayyacinta, dan muryarsa a
kaifafe take. Wai a haka ma Smart fa bai ɗauki zafi ba, ransa bai ɓaci ba, da ransa
ya ɓaci ai sai dai wata ba Sarina ba, ace a cikin kannensa a samu mai irin halinsu
Heleena kuma yana raye? Tab wlh dik sai ya gyara masu zama kafin ya bar kingdom of
power.

Sam ta kasa iya miƙewa da kafafunta, da jan jiki a kasa ta iso gabansa, sai kerma
jikinta yake yi, bakinta ya kumbura suntum saboda take ta da ya yi, gabaɗaya
singalalin hannunta sun yi ruɗu ruɗu da belt ɗin, abin ku da farar fata, tini
jikinta ya zama jajir kamar jan gauda.
A gabansa ta ƙariso tana kuka ƙasa kasa. Ko kallon in da take bai yi ba ya
umarceta da ta yi mashi kneel down ta ɗaga hannunta sama, daga nan har wayen gari
ba zata bar wajen ba, in kuma ta yi koda motsi ne sai ya kakkaryata, daga karshe ta
rufe mashi baki tsit baya san ya ji komai ƙanƙantar sauti ya fita daga gareta.

Yau dai Sarina ta faɗa koma. Wayarsa ya ɗauko domin ya kira Jaish ya zo ya faɗa
mashi wanenen uban Sarina a cikin familynsu? Dan a cewarsa uban nata ma yana da
buƙatar a gyara mashi tarbiyarsa, dan bashi da tarbiya shi ma, saboda idan yana da
tarbiya a cewarsa da zai bawa Sarina tarbiya yadda yakamata, dan haka daga ita har
ubanta yau zai gyara masu zama, irinsu ne ke ɓatawa larabawa suna...... Tashin
hankali, lallai Smart ya dame su King ya iskancin, kam bala'i uncle Abbas zai bawa
tarbiya lallai akwai cakwakiya.

A lokacin da ya kira Jaish wayar tana cikin mota shi kuma yana cikin hospital ya je
kiran nurses, so bai yi picking ba. Jefar da wayar a gefensa ya yi tare da miƙewa
ya shiga dressing room domin ya shirya ya zo ya kwanta, sai lokacin da Jaish ya
kirasa zai iya sanin hukuncin da zai yi wa Sarina, dan yanzu wannan duka da kneel
down ɗin dik ba hununci bane, ta dai yi ne zuwa yasan ubanta sai ya san kalar
hukuncin da ya dace da su.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Da kyar Jaish ya iya driving suka isa hospital ɗin, ko da ya kashe motar sai da ya
ɗauko good 5 mins a zaune shiru ita kuma tana kwance a jikinsa, sannan ya buɗe
kofar motar a hankali, kafafunsa ya fara zurowa wajen da ita a jikinsa ya fito, da
hannunsa ɗaya ya tura kofar motar ya nufi hospital ɗin.

Har zai shiga sai ya lura da yanayin kayan jikinta, to kun san su da kishi ko da ba
matansu ba bare matansu, hakan yasa ya fasa shiga ya juyo da ita, cikin motar ya
mayar da ita tare da fita ya nufi cikin hospital ɗin shi kaɗai yana wani lumshe
idanu yana kame jikinsa wajen guda, da kyar ma yake tafiyar.

A dai'dai wannan lokacin ne call ɗin Smart ya shigo wayarsa, Mahnoor tana ganin
call ɗin har ya katse, shi kuwa nurses mata guda biyu ya je ya taho da su a kan su
zo su dubata a ciki.

Suna isa wajen motan babban Dr ya biyo bayansu yana kwala kiran sunan Prince Jaish,
dakatawa Jaish ya yi domin su gaisa, su kuma nurse ɗin ya ce su shiga su dubata a
ciki.

Gaisawa suka yi da Dr, cikin girmamawa dr ya ce meyasa bai kirasu a waya sun zo
gida sun dubata ba ya fito a cikin daren nan. Ɗan jinjina kai ya yi kafin ya ce
babu komai su tara next time, daga haka ya ce wa Dr ya je kawai.

So shi kansa Dr ya sansu da kishi, dan ko Auta ce bata da lafiya Jaish baya bari
namiji ya dubata sai dai bace, dan haka dik da Dr bai san wacece bace sai ya juya
ya koma ciki, a tinaninsa ma Auta ce. Dr na tafiya ya koma cikin mota ya zauna yana
jin tamkar ba shi ba, wani zazzafar abar ce ma take sake taso mashi, kamar ba
lafiya ba.

Shiru ya ɗan jingina kansa da jikin kujerar motar yana jin mararsa tana ɗan
murɗa mashi a hankali hankali, ba komai ya ja hakan ba kuma face jarabar tasa. Yana
jin nurses ɗin suka yi mata dik tambayoyin da yakamata kafin su fita su je su kawo
mata magungunan da suka dace, sannan suka yi masu sallama.

Kuɗi ya ɗebo a cikin motar tasa ya miƙa masu ba tare da yasan adadin da ya ɗeba ba.
Godiya suka yi mashi suka juya suka bar wajen. Tamkar jira yake yi su tafi, suna
barin wajen ya janyota jikinsa yana jan numfashi a hankali hankali. Ajiyar zuciya
ta sauke tare da saƙalo wuyarsa, can ƙasa ta ce. "Yah

Please Login or Register in order to submit comment