You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita ta fara ƙoƙarin bawa
Jaish hakuri muryarta na sarkewa. Ina ai bai saurareta ba, dan ransa ya ɓaci sosai
shi ma, hannu yasa ya tureta gefe da karfi ta tafi zata kifa.

Kamar walkiya haka Hoorain ya tareta ta faɗa jikinsa, hakan ba ƙaramin kara kona
ran Jaish ya yi ba, zuciyarsa ce ta ƙara fusata, gadan gadan ya nufesu, yana zuwa
ya sanya hannu ya damki wuyar Auta zai sake tureta gefe guda.

Kankame Hoorain ta yi tana faɗin. "Yah Jaish dan Allah ka yi hakuri ka rabu da shi,
wlh bashi da laifi......"

Bata ƙarisa maganar ba Jaish ya saukar mata wani marin a gefen ƙuncinta, abin da
bai taɓa yi ba bai kuma taɓa sa ran zai yi ba a rayuwarsa sai ga shi yau ya yi, ko
a mafarki bai taɓa zatan akwai wata rana da zata zo ya ɗaura hannunsa a jikin Auta
ba, sai ga shi yau ɓacin rai yasa ya yi hakan.

Haba ai yana sauke mata wannan marin ran maza ta ɓaci, a miliyan Hoorain ya kai
hannu ya danki wuyar Jaish, sai wani irin huci yake yi yana furzar da wani irin
numfashi mai tsananin zafi daga bakinsa.

Yana damkar wuyar Jaish sai da King ya miƙe tsaye, gabaɗaya waɗan da suke cikin
fada sun yi wani irin zaro idanu tamkar idanunsu zasu faɗi ƙasa, commander Zafar
yau sai da hantar cikinsa ta ƙaɗa, mayaki da capkar wuyar Prince da kansa, tashin
hankali, lallai yau akwai bala'i.

Warriors dake cikin fada gabaɗaya suka zari takubansu suka yi kan Hoorain, da karfi
shi ma ya zaro takobinsa da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma ya shake Jaish da shi.
Mamaki ya hana Jaish motsawa.

Ɗaga takobinsa Hoorain ya yi ya sauketa a in da ja layi a floor na fada, cikin
kakkausar murya yana huci ya ce. "Dik wanda ya matso kusa da ni sai na datse kansa
na rantse!!!".

Tashin hankali, da yake dikkan warriors sun san halinsa sun kuma san fin haka zai
aikata idan ransa ya ɓaci, sai dikkansu suka ja suka tsaya tamkar an sassaƙasu.

Ido cikin ido Hoorain ya kalli Jaish, cikin kakkausar ya ce. "Dik ranar da ka sake
ɗaura hannunka a jikinta, na ratse sai na datse hannunka, ba kai ba dik wanda ya
sake taɓata tabbas zai iya rasa ransa, ni ka dakeni iya dukan da zaka yi mun, ai ni
na yi maka laifi, ita kuma me ta yi maka? Meyasa zaka taɓata?".

Yadda kuka san babu Jaish a cikin fada, tamkar ba shi Hoorain ya shakewa wuya ba,
idanunsa sun yi jajir kamar wuta, mamaki yana shi ya gwada kwanji da Hoorain ɗin
ma.

"Hoorain kana da hankali kuwa? Kasan kuskuren da kake san tabkawa kuwa? Ka manta a
ina kake ne? Kasan bala'in da kake san jefa kanka a ciki kuwa?". Cewar commander,
cike da tsananin tashin ya yi maganar.

Ɓacin rai dai shi yasa idanun Hoorain suka rufe, baya ji kuma baya gani, a yadda
yake ji yanzun nan ko King ya zama shamaki a tsakaninsa da ita ko kuma ya taɓa
lafiyarta to fa zai iya kawar da shi. Tashin hankali!!.

"Umarni nike baka da ka gefar da takobinka kasa kuma ka zube ƙasa a saman gwiwonka
ka bawa Prince hakuri". Cewar commander Zafar again, yana magana tamkar ya manta
wanene Hoorain, ya manta ya ɗan nasa yake idan ya fusata.

Guyson ne ya matsa ya riko hannun Auta domin ta bar wajen kada wani abin
ya sake samunta. Sai dai ina, fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, kuka
sosai ta ke yi.

Kai jama'a wato akwai tashin hankali a Kingdom of power, HOORAIN YA SHAKE JAISH
SABODA AUTA! BABBAR MAGANA, WANI IRIN HUKUNCIN KUKE TINANIN HOORAIN ZAI IYA
FUSKANTA? NA FARKO ANA ZARGINSA DA SACE GIMBIYA, NA BIYU YA SUMAR DA UNCLE TAHEER,
NA UKU YA TAƁA JIKIN GIMBIYA HAR YA RUNGUMETA, NA HUƊU UWA UBA YA SHAKE WUYAN
PRINCE JAISH DA KANSA, ME KUKE TINANIN ZAI IYA FARUWA NE WAI?.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Guyson ne ya matsa ya riko hannun Auta domin ta bar wajen kada wani abin ya sake
samunta. Sai dai ina, fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, kuka sosai ta
ke yi.

Shi kuwa Hoorain cigaba da daka masu warning ya yi a kan taɓa Zunaira, ɓacin
rai ta yi ɓacin rai........ Da sauri Auta ta matsa kusa da Hoorain, dan taga kamar
bashi da niyar sakar mata Yah Jaish ɗinta, shi kuma Jaish ɗin yana tsaye tamkar
wadda aka sassaƙa, to ta ji tsoron kada Jaish ya mutu dan taga idanunsa kamar wuta.

Kusa da Hoorain ta isa, ɗan hannunta ta kai saman nasa tana ja tana faɗin. "My Hero
ka sake shi mana, Yah Jaish ɗina ne fa, please ka sake shi, kada ka illama mun
shi". Tana magana voice ɗinta baya fita sosai, muryarta ya dashe sosai saboda kuka.
Hoorain da ya yi nisa sam baya jin kira, ko kaɗan bai ji kalamanta ba, sai ma
ƙara shake Jaish da ya yi. Uncle Jahiz ne ya sauko kasan stage ɗin, da sauri ya
matsa in da suke, dan hankalinsa ya tashi sosai na ganin jinin dake zuba daga cikin
Auta wanda ba kowa ne ya lura da shi ba, har ta fara ganin jiri jiri saboda ta rasa
jini sosai.

Yana zuwa ya ɗauketa cak ta baya ya nufi hanyar fita da ita. Ihu ta fara zunduma da
voice ɗinta da baya fita sosai, sam bai saurara mata ba sai da ya fice da ita, bai
kuma zame ko'ina da ita ba sai parking space, pretty ta bi bayansu, cikin motarsa
ya sanyata, da kansa ya kunna motar, da gudu ya figeta suka nufi hospital na
kingdom ɗin.

Hannu Jaish yasa ya damki hannun Hoorain ɗin, da karfi ya ɓanɓarota daga wuyarsa,
Hoorain sam bai yi ƙoƙarin hanasa ba, saboda dama shi idan da shi zasu daka ba zai
tanka ba, saboda sun kai su dakesa ɗin ne, amma su taɓa gimbiyarsa flowers
zuciyatsa kam wlh ba zai bari ba.

Dan haka yana ganin Jaish ya ɓanbare hannunsa daga wuyarsa, cikin fusata sosai
Jaish ya kai mashi wani duka mai firgitarwa a kumatu har sai da ya yi tangal tangal
kamar zai faɗi ƙasa, amma ya yi ta maza wajen rike jikinsa ya tsaya cak.

Uncle Abbas ne ya yi saurin tasowa ya matso ya rike Jaish ɗin, dan idan ya
barsu abin ba zai yi kyan gani ba. Commander Zafar gwanin ban tausayi, har idanunsa
sun ciko da kwallah dik jaruntar nan tasa, kowa yana da rauninsa, tabbas ba shakka
Hoorain shi ne raunin commander Zafar.

Jan hannun Jaish uncle Abbas ya yi suka nufi kofar fita fada ta kofar shiga cikin
gida. Da karfi Jaish ya kwace hannunsa daga hannun uncle Abbas, ransa in ya kai
miliyan to ya ɓaci, har kamar Hoorain ne zai rike mashi wuya? Lallai yau bai ga mai
iya dakatar da shi ba daga yi wa Hoorain illah ba!!.

Shi kuwa uncle Abbas sam baya san abin ta wuce haka, fatan abin ya tsaya a haka
kawai yake yi. Gadan gadan cikin zafa ya nufi Hoorain ɗin again.

Ni da ku dik mun san a nan dai Hoorain ya tabka babban kuskure, ai ko zai shaki
kowa banda Jaish dake matsayin yaya ga Zunaira, amma dai soyayya ce ta rufe mashi
idanu, kuma idan kuka kwantanta abin da kanku zaku ga shi ma Jaish bashi da laifi,
dan kowani yaya na gari zai tsayawa kanwarsa ce a koma inane, kuma shi dai Jaish ba
soyayya yake yi ba bare muce yasan zafin da masoya suke ji, dikkansu dai cikin
rashin sani suke, amma dai abin bai yi daɗi ba gaskiya.

Cikin zafa ya nufi sauka kan stage ɗin ya ƙarisa gaban Hoorain sai ji ya
ji an rike hannunsa ta baya, cikin zafa ya juya dan yaga wanenen?. Yana juyawa suka
yi ido huɗu da Aunty MieMie, ƙara ɗaure fuska sosai ya yi yana wani huci yana san
kwace hannunsa, shi kuwa Hoorain yana tsaye a kan kafafunsa ya sunkuyar da kansa
ƙasa zuciyarsa tamkar zata yi bindiga.

Cikin dakiya King ya ce. "Abbas kama shi ku tafi".......... Matsawa uncle Abbas ya
yi yana riƙosa suka tafi, ba dan King ba da bai ga abin da zai sa yau ya kyale
Hoorain ba.

Kallan Aunty MieMie King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan commander Zafar,
tsab King ya gama fahimtar soyayya ce take a tsakanin Hoorain da Zunaira, wannan
bakincikin ita ta hana shi yin magana, dan ya fahimci Zunaira tana san Hoorain
sosai, shi kuwa ko mutuwa zasu yi bai ga dalilin da zai sa ya bawa Hoorain Zunaira
ba, dan bai shirya ganin yarsa a matsayin karamar bazawara ba, kowa dai yasan
mayaƙa rayuwarsu babu tabbas, a kowani lokaci suna iya mutuwa, kuma ko da King ya
ƴanta Hoorain ɗin ya zama ɗan ahali ba zai taɓa zama mai ƴanci da rayuwarsa ba,
saboda ya riga ya tarawa kansa tarin makiyan da ba zai iya faɗa dasu domin ƙwatar
kansa ba, dik in da ya je masu san ɗaukar fansa a kansa suna kewaye da shi, dan
haka shi King yasan me matsalar, dole kuma ya dakatar da wannan soyayya cikin sauri
tin kan abin ya yi nisa ya fi karfinsu.

Hmmm King a ganinsa soyayyarsu bata yi nisa ba kenan, my people's mu gaya
mashi wannan soyayya ta fi shekaru 8 ne ko dai mu barshi su masoyan su nuna mashi
karfin soyayyar dake zuƙatansu?.

Tsit fada ya yi kowa idanunsa a kan King, jiran word ɗinsa kawai suke yi, saboda
babu wanda ya isa ya yi magana idan ba ya yanke abin da ya dace a kan wannan case
ɗin ba.

Commander dai ji ya yi ƙafafunsa sun gaza ɗaukarsa, hakan yasa ya koma saman sofa
ya zauna tare da sunkuyar da kansa ƙasa, domin shima ya rigada ya gane Hoorain ya
fahimtar da Zunaira abin da yake ransa, idan baku manta ba dama commander yana hana
shi kusantar Auta, ashe dik irin wannan yake gudun mashi, so yanzu ya fahimci
soyayya suke yi da Auta, kuma ya fahimci King Zuhair ma ya fahimci hakan, Allah
sarki yasan ko mutuwa Hoorain yake yi ba za'a taɓa bashi auren Auta ba, saboda ba
kowa ma yake yarda ya bawa mayaƙa yayansa ya aura ba bare ita da take matsayin
gimbiya, tab ai abune wanda sai in Allah ya ƙaddara akwai aure a tsakaninsu ne
Allah zai kawo sanadi, amma kam akwai matsala.

Good 10 mins King ya ɗauka shiru yana binsu da kallo kafin ya ɗan yi gyaran murya,
with sharp voice ya fara magana kamar haka.

"I think ka fahimci abin da na fahimta a tsakanin yaran nan ko Zafar?".
Dum dum commander ya ji kirjinsa ta buga, dan ya fahimci in da King ya dosa. Da
kyar ya iya jinjina kai cikin girmamawa ya amsa da ya fahimta.

"Ba sai na faɗa maka hukuncin da ya dace da Hoorain ba, ka fi kowa sani tin da
tare da kai aka kafa waɗan nan dokoki da hukunce hukuncen, dan haka ina mai baka
umarnin da ka hukunta shi yadda yakamata, daga karshe ka datse alakar dake
tsakaninsa da Zunaira bana san sake yin magana a kan hakan!!".

Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, haba King, wani irin zalinci ne wanna? Ta ya
za'ayi kace uba ya hukunta ɗansa bayan kasan hukuncin yana da tsauri da tsanani
sosai? Wannan babban zalinci ne wlh.

Tamkar commander zai yi kuka, idanunsa sun tsananta ja sosai, kansa a ƙasa cikin
girmamawa ya ce. "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, dan girman Allah ina
neman alfarman da abawa wani daga cikin mayaka damar su hukunta Hoorain, ba zan iya
hukunta shi ba".

Wlh dik taurin zuciyar Aunty MieMie na jinin Modarawa sai da ta ji zuciyarta ya
karaya a wannan gaɓa, saboda abin da ciwo ace uba ya hukunta ɗansa hukunci mai
azabtarwa, kuma dole ya yi yadda hukuncin take a rubuce idan ba haka ba dikka a
azabtar da su, innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil,
wannan abin akwai taɓa zuciya.

"Amma dai kasan bana magana biyu ko Zafar?". Cewar King. A tinanin King fa idan
ya sanya commander ya hukunta Hoorain to tabbas Zunaira zata fita a ransu
gabaɗayansu, dan uba da ɗa ba wasa ba, shiyasa ya yi masu irin hakan, burinsa kawai
ya yanke alakar Hoorain da Auta. Hmmm akwai matsala.

Shiru commander ya sunkuyar da kansa yana jin wani irin raɗaɗɗi na ratsa zuciyarsa,
haƙiƙa bai taɓa yin danasanin zamansa da su King ba sai yau, ya ji da ace shi ba
musulmi bane bai san girman Allah ba da babu abin da zai hana ya kashe kansa a kan
ya yi wa Hoorain wannan hukunci, amma bashi da zaɓin da ya wuce ya yi mashi ɗin,
dan haka sai ya miƙe jikinsa na kermar tashin hankali. Da kyar ya iya taka
kafafunsa ya isa in da Hoorain yake tsaye. Guyson ne ya juya da sauri ya bi bayan
uncle Abbas da ya fita da Jaish, dan kun san guyson akwai tausayi, ya ji bashi da
kwarin zuciyar kallan commander Zafar a halin da yake ciki.

Aunty MieMie ce ta yi saurin juyowa ga King da nufin ta taushesa ta bashi
hakuri wani ya hukunta Hoorain ba mahaifinsa ba. Sai dai tana ƙoƙarin buɗe baki
King ya ɗaga mata hannu fuskar nan tasa babu alamar wasa, ya ɗaureta tamau kamar
hadari, ya ɗaga mata hannu alamar ta yi mashi shiru.

Zuciyoyi dayawa sun karaya a cikin fada, dayawan jama'ar dake ciki sai da
idanunsu ya tara ruwa mai ɗumi, dik mai imani sai ya tausayawa commander idan ya
gansa.

Riko hannun Hoorain ya yi, jansa ya yi suka juya suka nufi hanyar fita, da kyar
yake jan kafafunsa saboda rashin kwarin jiki.

Da kallo kowa ya bisu, warriors dake cikin fada kuwa daɗi suke yi suna faɗin Allah
ya kama commander yau, ba ya iya hukunta ƴaƴan mutane ba, to yau abin ya juyo ta
kansu ai shikenan shi ma ya ɗanɗani yadda iyaye suke ji a lokacin da yake azabtar
masu da ƴaƴa.

"Ku shirya mana motoci zuwa hospital duba Zunaira, sannan ku ɗauki Taheer ma zuwa
hospital". Shi ne abin da King ya faɗa kafin ya koma saman kujerarsa ya zauna yana
jin wani irin kuna a ransa, wai Hoorain da Zunaira suna soyayya, wannan abin ya
kona mashi rai matuƙa, har ji ya yi kansa na sara mashi.

Dik wannan abin da yake faruwa a cikin gida babu wanda yake da labari sai Mammien
su Sarina and mama da suke da c.i.d, kun san suna da masu saka masu ido a lamarin
fada, so har sun samu information a kan abin da yake faruwa.

JAISH kuwa kai tsaye part ɗinsa uncle Abbas ya wuce da shi, sai huci yake
yi, wlh ba dan King ba yau bai ga abin da zai hana shi yi wa Hoorain dukan mutuwa
ba. Tab yadda Jaish fusata haka kuna tunanin ko mutuwa Hoorain yake yi zai yarda ya
bashi auren Auta kuwa? Hmmm akwai dai matsala.

A bakin bed uncle Abbas ya zaunar da shi yana tausan shi a kan ya yi hakuri.
Hannu ya ɗaga tare da cewa uncle Abbas. "Second dad it is okey, zaka iya tafiya
babu komai". Yadda ya yi maganar yana fitar da huci mai zafi zaka iya fahimtar har
yanzu bai huce ba.

Kin matsawa daga kusa da shi uncle Abbas ya yi, dan ya fahimci komai zai iya faruwa
idan ya tafi ya bar shi a haka. Dan haka sai ya zauna tare da shi ya cigaba da
rareashinsa.

Shi kuwa guyson part ɗin momma ya wuce kai tsaye dan ya faɗa mata abin da yake
faruwa, zuciyarsa ba zata iya ɗaukar hukuncin da King ya yankewa commander Zafar
and Hoorain ba, abin akwai ciwo sosai, hukuncin ya yi masu tsauri sosai, ace uba ya
kai ɗansa ɗakin duhu dan hukunta shi, bayan ya gama hukunta shi da kansa kuma zai
jefa shi a gidan yarin masarautar tare da horo mai tsanani bayan na ɗakin duhu, wlh
commander ba zai iya ɗaukar wannan musifar ba, dole su momma su saka baki ko za'a
samu sassauci.

Yana ƙoƙarin shiga part ɗin momma ciwonsa ta tashi, wani irin azabbabben murɗa
mashi da cikinsa ta yi ne yasa ya dafeta da karfi yana sakin ihu mai ɗan sauti
kaɗan. Wani irin numfashi ya fara fitarwa da zafi zafi yana kara dafe jikin bango,
a hankali ya fara jujjuyawa ko zai ga wani a kusa ya taimaka mashi, dan ko motsawa
ba zai iya yi ba.
Dai'dai lokacin Mahnoor ta fito daga part ɗin Jaish cikin shiga ta girma wato ta
matar Prince wanda mama Haulat ce ta ƙawata mata shigar, so zasu je gaishe da Akka
ce ita da Chuchu, shi ne ta ce bari dai ta fara duba momma kafin su je wajen
tsohuwa.

Chuchu na can suna sallama da Yah Jawad zai tafi office, sai aikin rungume juna
suke yi kamar ba gobe.

Ganinsa ya dafe bango yana hawaye yasa Mahnoor ta yi saurin nufarsa tana
tambayarsa lafiya kuwa?. Riƙo hannunta ya yi ya kasa yin magana, da hannu ya nuna
mata part ɗin monma a kan ta taimaka mashi su je can.

Daddagewa ta yi tasa karfinta dikka zata taimaka mashi, gabaɗaya ya sake mata
nauyin jikinsa saura kaɗan su zube ƙasa, da kyar ta iya kamewa ta iya ɗaukar
nauyinsa, sai kuka yake yi sosai yana cigaba da dafe cikinsa da hannu ɗaya.

Ya yi mata nauyi sosai, amma haka ta daddage ta tallabosa da kyar suka nufi part
ɗin momma. Allah ya taimaketa momma tana parlor zaune ita da Mahreen and Zee suna
hira, momma kenan, mai farar zuciya, ta haɗe ƴan'matan dikka ta rikesu abinta, babu
kyara ko kyama.

Suna shigowa cikin parlourn saura kaɗan su zube ƙasa gabaɗayansu, a hanzarce momma
ta miƙe ta taresu. Kuka ya kara sakawa mai sauti yana nunawa momma cikinsa babu
bakin yin magana. Wlh idan ciwon guyson ya tashi sai kun tausaya mashi, ba karamar
wahala yake sha ba...... WAI MENENE DALILIN WANNAN CIWO NA TSAWON SHEKARU HAKA?
AKWAI AYAR TAMBAYA GASKIYA, TO MUJE DAI ZUWA.

Gabaɗaya ya sakewa momma nauyinsa, saman sofa ta kwantar da shi tana tambayar
lafiya tana kallan Mahnoor. Cikin natsuwa Mahnoor ta ce ita ma bata san me ya same
shi ba, kawai ta gansa ne a bakin kofar shigo part ɗin.

Riko hannayensa momma ta yi tana tambayarsa meyake yi mashi ciwo. Cikin tsananin
ciwo da azaba ya fara nuna mata cikinsa yana kara tsananta kukansa.

Da yake momma tasan irin azaban da yake sha idan ciwon ya tashi sai hankalinta ya
tashi sosai. Wayarta ta ce Mahreen ta miƙa mata, dama wayar tana kusa da ita.

Ɗauko wayar ta yi ta miƙa mata tana kallan guyson ɗin.
"Ji fa, kato da shi ne yake yin kukan ciwo, Adda Mahnoor kalle shi fa, wannan
anyi wawa gaskiya". Tana magana tana harararsa. Ko kunyar idanun mommarsa bata ji
ba take yi mashi wannan iskancin.

Ɗan buge mata baki Mahnoor ta yi tana kallanta. Hannu ta ɗaura a saman bakin nata
ta hau murjesa tana faɗin. "To me na yi maki zaki buge mun baki?".

Momma dai hankalinta baya a kansu, ƙoƙarin kiran number Dr Raj kawai take yi. Ta
kuwa yi sa'a bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin ya bi bayan Ramish yana faɗa mashi
Leesharh tana da buƙatar karin jini idan ba haka ba zasu iya rasata, an gwada jinin
Bilal and shi Dr Raj ɗin dik jininsu bai yi irin nata ba, o negative take da shi,
ashe shiyasa take da shegen janircewa da taurin rai, jinin sojoji ke gareta.

Dr Raj ya yi iya yinsa a kan Ramish ya tsaya a gwada jininsa idan ya yi a sanya
mata ya ce ba zai bata jini ba, dan yana jin nau'in jinin nata yasan irin nasa ne,
bama sai an gwada shi ba, amma dai ya ce ba zai bayar ba, a sayi sabo a saka mata
ko kuma a nemo ƴan uwanta dik a in da suke su zo su bata, dan ta bada ranta ta
cecesa ba wai hakan yana nufin shi sai ya tsaya mata a kan komai ba, ya yi abin da
yakatama ya yi, shi yanzu ma ya fara zarginta ne, dan da ya zauna ya yi tinani
ƙwaƙwalwarsa ta basa dik yadda aka yi tana da masaniya game da komai, ashe banza
kwanaki ya saketa, ya yi kuskure, dik yadda aka yi ta san komai, wannan abin ya
baƙanta mashi da yasa ya ji ya tsani zuwa in da take.

Tun da ya sanya kafa ya bar ɗakin da ya cire mara bullet bai sake waiwayarta ba, Dr
Raj yake kula da ita karkashin umarnin Bilal, abin kuma da baku sani ba shi ne,
kamar Bilal ne yake kara tunzura Ramish a kan Leesharh, saboda Ramish ɗin ya ja
baya da ita. Amma shi Bilal abin da bai sani ba shi ne, Ramish yana amsa mashi dik
abin da ya faɗa mashi da fatar baki ne kawai, ba wai dan yana ɗaukar hakan a
matsayin gaskiya ba, in short da Bilal da Leesharh dikka yanzu suna a karkashin
sarrafawar Ramish ɗin ba tare da sun sani ba, dik yasa masu question mark, dik
bincike yake yi a kansu ta ƙarƙashin ƙasa domin ya gane gaskiyar abin da yake
faruwa.

Waɗan can guy da suka harba a hall ɗin nan da Ramish ya je ya gansu sai da ya
razana matuƙa, domin kuwa ya sha ganin ɗayan guy ɗin a tare da Bilal several times,
and akwai hotunansu tare da Bilal a wayar Bilal ɗin, hakan yasa Ramish ya kara
tsananta zarginsa a kan Bilal matuƙa.

And kuma yaki bari Bilal yaga gawarwakin mutanen, hakan ma tana daga cikin aikinsa,
lokacin da zai je h-q duba mutanen Bilal ya so su tafi tare, amma sai ya ce a'a zai
je shi kaɗai, ashe kuwa gara da ya tafi shi kaɗai ɗin, dan yana ganin mutumin ya ce
ba zai bari Bilal ya fahimci komai ba, dan in da gaske Bilal yana da masaniya a kan
komai idan yasan wanda suka kashe mutuminsa ne to zai iya katsewa Ramish yunkurinsa
na gane suwaye suke da sa hannu a lamuran. Shiyasa ya canzawa kowa a gidan yanzu,
ya kuma dai'na bari suna samun damar haɗuwa da shi, yanzu haka tin safe Dr Raj yake
san haɗuwa da shi ya rokesa da ya taimaka ya bawa Leesharh jini amma ya gagara
samun damar ganinsa, kuma yana cikin gidan, ganinsa ne ya hanasu dama.

Sosai Bilal ya shiga damuwa a kan ɗauke mashi wuta da Ramish ya yi, yanzu haka tun
jiya bai samu damar haɗuwa da Ramish ɗin ba, ya yi ya yi su haɗu abin ya gagara.

A ɓangaren Ramish ɗin kuwa, wlh jinyar kansa yake yi sosai, domin kuwa dik wasu
bincike da zai yi mutanen da zai zarga suna da sa hannu a yunƙurin kashesa sai ya
gansu a tare da Bilal, duniya yau Ramish ya rasa me yake yi mashi daɗi, ya shiga
tashin hankali da kunci da bai taɓa shiga makamancinsa ba, tun daga jiya kirjinsa
take yi mashi wani irin azabbabben ciwo mai tsananin gaske har yau, haka yake
daurewa yana aiki.

Wani lokaci sai ya ji kamar ya dakatar da binciken nan domin fargabar abin da zai
iya cin karo da shi, yana tsananin fargabar abin da zai binciko, zuciyarsa tana
rawa a kan binciken nasa, sai ya ji kamar ya haƙura kawai, gara ya zauna da Bilal
ɗin a haka bai binciko gaskiya ba sai ya fi mashi, amma kuma yana san sanin gaskiya
ta wani fannin.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Cikin natsuwa Dr Raj ya yi picking call ɗin momma. Hankalinta a tashe ta fara
zayyana mashi ciwon guyson ya tashi, ai yana daga zaune bai san time da ya miƙe
tsaye ba, muryarsa a ɗan dishashe ya ce what.

A tinanin Dr ciwon Guyson zata ɗauki a kallah shekaru biyu ko uku kafin ta sake
tashi, amma sai suka ga akasin haka. A hankali ya koma ya zauna tare da haɗe
natsuwarsa waje guda, sannan ya ce momma ta yi gaggawan kiran likitoci da wuri so
zo, lokacin yi mashi aiki kuma bata yi ba, dan bayan shekara ɗaya ake yi mashi, so
da yin wancan aikin bai kai shekara ba yanzu, to me matsalar? Dr ya tambayi kansa.

"Bari in kira Jaish ko Jawad su yi gaggawar kiran Drs yanzun nan, idan Drs sun
iso sai mu yi waya dan su duba mun shi su ji menene matsalar kuma". Cewar Dr.
Jinjina kai momma ta yi tare da katse

Please Login or Register in order to submit comment