You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamar a'a bata sani ba..... "Ina kaunarta fiye da kai'na, komai nata birgeni
yake yi, amma ta ci saurin yin fushi, kuma ita tana kaunata over, before ki zo ita
take bani abinci a baki fa, na yi missing na wannan moment ɗin, bari in je in bata
hakuri daren yau ta ciyar da ni abinci a baki".

Faɗaɗa murmushin dake saman face ɗinta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Gaskiya
kam ka je ka lallaɓa mana ita ta zo mu ci abincin dare a tare, nima ina missing
ɗinta sosai". ...... Jinjina kansa ya yi tare da manna mata sumbata a gefen
kumatunta, kara faɗaɗa murmushin ta yi tana kai hannu ta ɗan shafi gefen nasa
kumatun. Saketa ya yi tare da fara tafiya baya baya yana kallanta, ganin irin
tafiyar da yake yi ta cikin mirror yasa ta juyo dan ta gansa da kyau. Tana jiyowa
suka haɗa ido, kashe mata ido ɗaya ya yi yana cigaba da sakin cool murmushi har ya
kai jikin kofa. Kamar dai kullum, sumbata ta manna a hannunta ta hura mashi, ajiyar
zuciya ya sauke haɗe da juyawa ya cire password na kofar ya fita. Tana ta murmushi
bata zare kallanta daga kansa ba har sai da ya kurewa ganinta. Ajiyar zuciya ta
sauke tare da raba jikinta da jikin mirror, cikin natsuwa ta taka ta nufo waje ita
ma.

Kai tsaye master room na Black Tiger ta nufa, tana tafiya tana tinanin a wani irin
yanayi zata same shi?. Tana zuwa ta buɗe kofan without any scare and any excuse ta
afaka cikin ɗakin.

Tsaye yake a tsakiyar ɗakin ɗaure da towel a waist ɗinsa, da alama daga wanka ya
fito, dan ga dark black curly hairnsa nan yana ɗigar da ruwa, hannunsa rike da wani
ɗan ƙaramin towel yana goge kyakkyawan gashin kan nasa. Da yake ta kudurta a ranta
kome zai faru babu gudu babu ja da baya sai ta daure bata juya ta gudu ba, kada ku
manta ta taɓa ganinsa a yanayin da ya fi haka, a farkon ganinta da shi da ɗan
ƙaramin short ta gansa, gara yau towel ɗin tana da ɗan tsawo ta kai mashi har zuwa
gwiwa.

Tun daga kan tafukan kafafunsa ta fara kallansa har izuwa sama, ita kanta ta
shaida he's so sexy, handsome and cute, yanayin jikinsa sai yasa ka fola..... Tana
sauke kallanta a kan face ɗinsa sai taga shi ma ita yake kallo, dan fa ba karya ta
yi kyau cikin shigarta. Suna haɗa idanu ya yi gaggawar kawar da nasa kallan yana
ɗaure fuska, ta fahimci sam sam baya san ta kama shi yana kallanta, dan haka sai ta
yanke shawarar zata rinƙa dannewa ba zata bari ya san ta san yana kallanta ba.

Kai Black Tiger da Sweetie duniya, wato babu maganin Black Tiger sai Sweetie, a
gana mata azaba amma kuma yana jin daɗin kallanta, musamman idan tana tare da
Ronnie tana sakin cute smile ɗin nan nata mai narkar da zuciya.

Cikin dauriya da natsuwa ta tako ta nufo in da yake, bai yi kamar yasan tana zuwa
ba, ya cigaba da yin abin da yake yi. A dab gabansa ta tsaya, hannu ta kai ta karɓi
ƙaramin towel dake hannunsa, zuciyarta na harbawa da sauri sauri, ta yi ƙasa da
murya cikin siga mai jan hankali da salo ta ce. "Dama ni nasan kai adali ne, kai
ɗin mai tausayi ne, kai ɗin jarumi ne, kai ɗin mutum ne da dik in da ake neman
cikakken namiji ka kai nan har ma ka wuce, ba zan taɓa mantawa da alkhairinka na
yafewa mutanen birnin nan ba, tabbaa yadda kake da balai'n kyau zuciyarka ma haka
take". Ta ɗan dakata da yin maganar tare da kai kallanta a kan face ɗinsa, sannan
ta fara goge mashi Lion chest ɗinsa da towel ɗin.

Mutuwar tsaye ya yi yana tinanin shi kuma a yaushe ya yi wa mutanen birnin nan
afuwa da har take yi mashi irin wannan yabo? Sai dai kuma yabonta a garesa ta ratsa
zuciyarsa, ya ji daɗin hakan sosai, sai ya ji dama ta cigaba da yi kada ta
dakata...... Batu na gaskiya yabo tana karya zuciyar koma wani irin mutum ne, ki
gwada ware rana guda ki yi yabo da zafafan kalamai ga wanda yake kusa dake kiga
yadda zai shiga cikin farinciki a wannan lokaci, gaskiya ne abin da hankali bai
bayar ba rashinsa ba zai bayar ba, abin da kwamciyar hankali bai bayar ba rashinsa
ba zai bayar ba.

Haƙiƙa Sweetie ta fahimci yabon da ta yi mashi ya yi tasiri a cikin zuciyarsa, dan
har da sauke ajiyar zuciya ya yi, kuma ta ji hakan, dan haka ta shiga farinciki ita
ma.

"Kana da kyau sosai our big bro, haka zalika zuciyarka ma mai kyau ce
tsarkakekkiya". Yadda take magana cikin salo mai ɗaukar hankali yasa bai san
lokacin da ya amsa mata da. "Amma kuma jiya kin ce zuciyata bata da kyau
ai?"....... Kam bala'i ashe kalamanta na jiya sun shiga kunnuwansa, magana da ta yi
mashi a tsawatance yasa ya ji ba zai iya ragawa kowa ba, da ace jiya ta yi mashi
magana yadda ta yi mashi yau da tabbas za'a samu rangwame, sai dai kash, ta fusata
ita ma, tabbas magana cikin natsuwa yana iya canza komai.

"Jiya ai ɓacin rai ne yasa na yi maka magana a haka, amma tabbas kai mutum ne
mai farar zuciya". Ta kai karshen maganar tare da ɗaura mashi ɗan towel ɗin nasa a
saman shoulder ɗinsa, sannan ta juya da nufin ta matsa daga gabansa, ta koma saman
sofa ta zauna ta jirasa yasa kaya ya fito ta kara yi mashi godiya, bata san karya
Ronnie ya sharara mata ba.

Tana juyawa ɗan ruwa ruwan da ya zuba a wajen daga gashin kansa yasa ta zame,
baya baya ta yi ta faɗa jikinsa, buga kanta da kirjinsa ta yi a in da ta tsuke
fuska kamar zata yi kuka. Tana ƙoƙarin yin ƙasa daga jikin nasa yasa hannu ɗaya ya
tallabota tare da juyota garesa, face ɗinta ya zubawa idanu yana kallan yadda ta
datse nata idanun tana jiran ta ji ta isa ƙasa. Yau yabon da ta yi mashi ne ya
sanyaya mashi rai har yasa ya ceceta bai bari ta kai ƙasa ba, dama ransa tun jiya a
ɓace na juya mashi baya da mutanensa suka yi.

Kurawa juna ido suka yi gabaɗaya kamar sun mance a wani duniya suke, sun shagala da
kallan juna gangar jikinta ya gaza iya jurar tsawuyar da ta yi ɗin, dan kusan a
iska take, bayan wuyarta ya tallabota da hannunsa. Kerma kafafunta suka fara yi a
in da ta yi ƙoƙarin zubawa ƙasa, cikin zafa ya fisgota mai gabaɗaya ta tafi ta faɗa
saman lion chest ɗinsa, yasa hannunsa ɗaya ya tallabi tsakiyar bayanta. Like wow,
abin da bata taɓa expecting zai yi mata ba, wai ya taimaketa, bata taɓa zata ba,
sai ga shi ya yi hakaɗin sanadiyyar daɗaɗan lafuzanta a kansa, abin fa ya yi mashi
daɗi ne sosai, sai dai shi ba'a gane farincikinsa ko bakincinsa shiyasa bata wani
gane sosai ba.

Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman lion chest ɗin nasa ta gefe, dan dikkanta bata
gama cike rabin faɗin kirjinsa ba, ƴar karama a gabansa. So sai ta ɗaura hannunta a
gefen chest ɗin nata, a hankali ta ɗago da kanta dan ta kalli face ɗinsa, ya kura
mata idanu yana yi mata kallan kurillah. Habawa sarkafewa idanunsu ya yi cikin na
juna kamar ɗazun. Sun ɗan jima a haka kafin ya yi gaggawar kawar da kallansa a
kanta tare da saketa, kamar wani mara gaskiya ya juya da sauri ya nufi clothes set
ɗinsa. Bin bayansa da kallo ta yi har ya shige cikin wajen, ajiyar zuciya ta sauke,
cikin natsuwa ta taka ta isa gaban sofars ɗinsa, saman ɗaya ta zauna, tsabar laushi
har lumewa da ita ya yi, tagumi ta ɗan yi tare da afkawa duniyar tinani, faɗi take
yi a ranta ta fara yin nasara, ji take yi sun kusa canza zuciyarsa, amma ita dik a
tinaninta yafewa mutanen birnin da Ronnie ya ce mata ya yi ne take ganin sun fara
nasara ba. Uhm akwai sauran aiki a gabanki Sweetie, dan wannan mai black heart ɗin
kam bai ji komai a ransa ba.

Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress
ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya,
dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai
kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu..................

Dama a karshen littafin nan na yi maku alkawarin baku wasu addu'oi na mallakar
zuciya ko? Da na yi niyya sai a kashen littafin, amma duba da ramadan ya gabato, a
cikin Ramadan ma buƙata zata fi saurin biya yasa nace bari na baku the most
important ɗin, ku yi shi a cikin watar Ramadan, ki yi shi da kyakkyawar niyya, ina
uwa da ɗanta yake zinace zinace, yake yawace yawacen banza bin abokan banza da
shaye shaye? Ina mata masu shan wahalar namiji? To dik dai ku matso, ku yi shi da
tsarkakakken niyya sosai

Da farko dai zaki yi. Astaghfirullaha Rabbi min kulli zambin wa atubu ilayh kafa
ɗari dai'dai, sannan ki yi salati ga annabi kafa goma. Amma fa sai kin yi alwala,
zaki iya farawa karfe sha biyu na dare, za kuma ki iya farawa karfe 2 na dare, idan
kin yi alwala kika yi sallah raka'a biyu, sai ki zauna, ki gabatar da abin da na
faɗa a farko, sannan ki yi salati, ga salatin ma a rubuce ga waɗan da basu iya ba.
Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallayta ala Ibrahima wa
ala ali Ibrahima innaka Hamidum Majid. Bayan kin yi wannan sai ki gyara zama sosai
a kan dadduma, ki ɗaga hannayenki sama ki fara addu'ar kamar haka.

Allahumma aslih zawji ( sai ki ambaci sunansa, wato suna da kike yiwa ɗin kenan)
waj’alhu min as salihin, waj’alhubniyyatahu nafi’atan lid duniya wa akhirati. Da
kyakkyawar niya fa, ki sanya a ranki tamkar Allah ya gama biya maki buƙata, ki ji
cewa bayan Allah babu wanda zai yi maki. Sai Rabbana hablana min azwajina wa
dhurriyyatina qurrata aƴunin waj’alna lil-muttaqina imama. Wannan addu'a tana da
mahimmanci kowace uwa ta kasance tana yi, yana cikin Suratul Furqan. Sai Allahumma
inni as’aluka an tahdi zawji ila sabilika al-mustaqim, wa an tub’idahu ‘an ma
yughzibuka, wa an taj’alahu min ahlil taqwa wal istiqama. Wannan addu'oi masu
tsadar gaske ne, idan kika yi sho da tawali'u zaki sha mamaki, zaki gode mun kamar
babu gobe. Sai Allahumma inni a’udhu bika min jahdi al bala’ wa su’il qadha’ wa
shamatati al a’da’, wa min kulli sharrin dhahirihi wa batinihi. Wannan addu'a tana
matuƙar kariya daga dik wata sharri na abin halitta, wannan ba dan miji ko wani
zaki yi ba, kanki zaki yi wa dan Allah ya kareki, amma zaki iya yiwa kowa yaki dan
ya shiga kariya, wlh wlh wlh addu'a ce mai karfin gaske. Tsarin yin wannan addu'oi
dama kwanaki 40 zaki ɗauka kina yinsu cikin dare bayan kin yi sallah raka'a biyu,
kinga ga Ramadan ya zo, zali samu saukin tashi ki yisu, sai ma buƙatunki sun fi
biya, shiyasa na baku a yanzu dan ku yi da ramadan, saura sai mun haɗu a karshen
littafin, saura wata budurwa ta je ta yi wa sarauyinta ta zo ba aurensa zata yi ba,
wlh babu ruwana, ya Allah dik wanda ba da kyakkyawar niya zata yi wannan addu'oi ba
Allah kada ka amsa mata, dan ba da ni za'a cutar da wata ko wani ba!!.

Yauwa ina da wata ƴar rokan alfarma a gareku my people's, kunga dai azumi ya zo,
Please a taimaka a sakani a addu'a, wlh addu'a in dai ta alkhairi ce a gareni
kowacce iriya ce ina so, please my people's, ina kannena da suke gida, ƴan yaran
nan da basu wuce 10 ya yi ƙasa ba, please a sanyasu su yi wa princess taku ta amana
addu'a, kun san addu'ar yara da karɓuwa yake, to a taimaka a mun wannan alfarma,
dik wadda ta je ta hajju ta jefani cikin addu'arta, ina godiya Allah ya bar kauna 💘
🔥 💘 🤍 much love my people's, sai mun haɗe gobe.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬

48


Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa,
yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai
lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen
kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu kyawawan robbot ne gungu guda da a kallah zasu
kai su 8, gabaɗayansu kowanne ɗauke yake da katan tray mai shake da kayan abinci
kala kala, ga wasu irin abin rufe abinci wato food cover masu shegen kyau da tsada
launin golden suna ɗaukar idanu aka rufe abincin da su, kai tin daga kan masu ɗauko
abincin zaka fahimci robbot ne na musamman da zasu kaiwa mutum na musamman abinci,
harta tafiyar da suke yi cikin tsari suke yinsa, a tare suke ɗaga kafafu su sauke.

Ai zuba masu idanu Sweetie ta yi tana kallan yadda suke taku gwanin birgewa, kai
tsaye suka nufi can wani ɓangare na ɗakin, kun san ɗakin da shegen girma yake,
wajen da yake cin abincin zaka yi zatan ba'a ɗakin yake ba saboda girmansa. Sweetie
bata kara tsurewa ba har sai da suka yaye white curtains dake wajen, ai wani irin
zaro idanu ta yi tana kallan tsaruwar dining room ɗin, kun san a baya Black Tiger
baya fita, hakan yasa yake da haɗaɗɗen dining room a cikin bedroom ɗinsa bayan na
parlournsa. Sweetie ta sha madarar mamakin ganin set na table ɗin dake ciki,
haɗaɗɗun chairs har guda 24 ne a wajen, ko shi da waye yake zaman cin abinci yawan
chairs har haka? Ta jefawa kanta tambaya, my people's dining room ɗin nan ya haɗu,
ga wasu decorations masu ɗaukar hankali, manya manyan flowers da kayan more rayuwa,
sai dai kuma kusan dik da ɗanyan gold aka yi su, yo Black Tiger da WC ɗinsa ma na
gold ne me ba zaku gani na gold ba?..... Shi dai wannan sarki wlh sai shirin Allah.

Glass wall ne wajen, haka zalika glass door ne, tura kofar suka yi suka shiga
ciki, shi kansa table ɗin abin kallo ne, ya tsaru matiƙa, samansa suka hau shirya
mashi abinci kamar yadda suka saba. Suna kammala shirya komai suka kunna ligh
launika daban daban dake wajen bayan sun kashe white light ɗin, take wajen ya ɗauki
wani irin launi mai ɗaukar hankali, sai ma da suka kunna kenduran dake saman table
ɗin, ya ilahi ya lilliahi, haɗuwa iya haɗuwa. Sweetie kam dai sumar zaune ta yi,
sai taga tamkar ba a duniya wannan dining room ɗin yake ba.

Fitowa suka yi su 7 sun bar ɗaya a ciki, suka nufi waje ba tare da sun yi komai
ƙanƙantar magana ba, da kallo Sweetie ta bisu tana mamakinsu, ita dai yau taga abin
da ya goge mata hadda, tambayar kanta ma take yi ashe Black Tiger yana cin abinci?
Abin like wow, ya ƙayatar.

Shi kuwa gaban mirror ya wuce, wasu document ya ɗauka yasa hannu, takardu ne na
katafaren ginin da za'ayi mashi a cikin empeir ɗin, tamkar fadar sarki ne shi ma,
tsarin ginin ya fi wanda yake ciki komai da komai, sai dai ya ce da zallar gold
za'ayi mashi ginin, dan yana san zarce kowani sarki a mulkinsa.

Ni kam na ce mu da mun san tarihin sarkin romawa da su habashawa, a zamanin da
manyan sarakunan da suka yi gidan ɗan yar gold a tarihi ma ai suna dayawa, amma yau
ina suke? Sun koma ga Allah, to a zamanin nan ma mun samu King Black Tiger, ginin
ɗan ƴar gold za'a zuba mashi, my people's yake kuke ayyana wannan gini a ranku?
Ɗanyar gold fa? Tab Black Tiger zai tashi hankalin duniya, ai dole ne ma kowani
sarki zai so kwace birnin daga hannunsa, ko dan tarin arzikin da Allah ya basu, aww
ace fadarsa da komai na gold, dole hankalin duniya ya tashi, ga katafaren filin
saukar jirginsa a saman ginin gabaɗaya, ginin dai ya tsaru matuƙa, a zamanin yanzu
banda sarakuna da suka shuɗe kafin zuwan manzan Allah (SAW) a zamanin yanzu shi ne
mutum na farko da zai yi irin wannan gini, abin dai ba'a cewa komai.

(Ni kuma na ce ya kuke tunani idan ya kammala wannan gini Sweetie ta zama Queen a
ciki? Ronnie ya zama Prince? Su dake a fada su ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya suna
zartar da hukunci irin na addinin musulunci, ya kuke ganin haɗuwar wannan sabon
empire ɗin nasa zata kasance da waɗan nan taurari guda biyun a cikinta?.🤔)

Sai dai har yanzu bai sakawa sabuwar empire ɗin suna ba, ya ce dai su fara kaddamar
da ginin sai an kammala zai faɗi sunanta a rubuta a farkon shiga.... Amma kuna
tunanin wani irin suna zai bawa empeir ɗin nan?.

Yana kammala sa hannu a kan document ɗin, sai ya sanya hannu a kan wata takardar da
ya umarci a biya dik mutanen birnin asarar dukiyar da aka yi masu a sanadin wannan
yaki, waɗan da basu bijire mashi ba kuma suka rasa nasu a biyasu diyya na makuɗan
kuɗaɗe masu zafi, sannan ya cike wasu takardu na sabbin ma'aikatan da yake san
buɗewa na sarrafa abinci da abin sha wanda kowani ma'aikata ɗaya zai iya ɗaukar
ma'aikata sama da 500, kunga ya ragewa mata zaman banza, kuma fa shi a ƙaidarsa
maza basa aiki sai dai su tafi bakin daga, mata ke yi mashi aiki a dikka
ma'aikatunsa domin su samu abin dogaro da kai tun da basu da maza da zasu wani
ɗauki nauyinsu........ Yaseen Black Tiger shegen kwaro ne, wai yanzu kun yarda da
batun Sweetie da ta ce tana da yakinin akwai abin da ya canza zuciyarsa daga fara
zuwa baka? Kun yarda wani lokaci mutumin kirki ne shi, wani lokaci kuma bakin
shaiɗani, sai ka rasa gane ina ne takamaiman alkiblarsa wlh, wani lokaci dai ga shi
mutum, wani lokaci kuma kai bashi da kyan gani fagen mugunta.

Sai da ya kammala abin da yake yi tsab sannan ya nufi dining room ɗin nasa, da
alama ya mance da ita a cikin bedroom ɗin. Wani robbot na tsaye a wajen yana jiran
ya kariso ya yi serving ɗinsa. Sai da ta bari ya shiga room ɗin ta miƙe ta bi
bayansa tana kara jinjinawa girman arzikin da Allah ya bawa birnin nan. Ba tare da
neman izininsa ba ta shiga cikin room ɗin, wannan robbot na ƙoƙarin zuba mashi
abinci ta yi gaggawar dakatar da shi tare da cewa. "Zan yi serving ɗinsa kada ka
damu".

To kun san abubuwan nasa idan ya rigada ya basu umarni kawai zasu aikata abin da ya
ce ne, dan haka wannan robbot ya riga ya karɓi umarnin yin serving ɗinsa, sai ya
hanata ya cigaba da yin aikinsa, ba ta isa jayayya da Robbot ba, dan idan ta yi ma
ita ce zata sha wahala shi babu ruwansa, dan haka sai ta ja chair dake kusa da shi
ta zauna tana kallan face ɗinsa, ya ɗaure fuskar nan tamau yana tinanin gina
katafaren football stadium saboda Ronnie, kun san yana sha'awar wasannin.

Kammala zuba mashi abin da ya buƙata wannan robbot ɗin ya yi tare da matsar
mashi da plate ɗin gabansa. Chopping stick ya ɗauko guda biyu, zubawa abincin idanu
Sweetie ta yi tana mamakin wannan wani irin abinci ne? Bata taɓa gani ba, a hankali
ta fara bin sauran cimar da kallo, dik launikan abinci ne da bata san ma da me ake
yinsu ba, ga wasu dai kamar nikakkun nama da kwai, wasu kuma kamar damammen
shinkafa da yoghurt, abubuwa dai kala kala, baki ta taɓe tana jin ko kasheta za'ayi
ba zata iya cin abincin Black Tiger ba, gara ma nasu Ronnie wanda ta sani ne.
Abin da bata sani ba anan shi ne, ta sha cin irin wannan abinci a hannun Kamran,
kun san a lokacin bata gani shiyasa bata san irin abincin da yake bata tana ci ba,
wlh babu wani banbanci tsakanin cimar mammar Kamran da na Black Tiger, dik irin
ɗaya ne, sai dai nata local ne na talakawa, nasa kuma na manyan kai, amma dik iri
ɗaya ne, amma har da cewa sun yi mata wani irin ba zata iya ci ba, bayan su ta ci
ta girma har ta ƙosa ta yi kumatun da in ta yi murmushi suke birge big bro, eh
manaaaaaaaaaaaa.😅

Ɗibar abincin ya yi da chopping stick, abincin wani ball ball haka ash colar, yana
ƙoƙarin kaiwa ɗan bakisna cool voice ɗinta ya daki dodan kunnnesa in da take cewa.
"Ka yi bismillah kafin ka ci". Ta yi maganar tana kallansa. Tamkar bai jita ba,
kamar bai san da halittarta a wajen ba ya cigaba da ƙoƙarin sanya abincin a
bakinsa. Cike da tsoro a gaggauce ta kai hannu ta rike hannunsa, kirjinta na bugawa
da karfi ta ce. "Please say Bismillah before you eat.........".

Bata gama rufe baki ba robbot dake tsaye ya yi gaggawar kai hannu ya damki wuyarta
ta baya tare da capke hannunta da ta rike hannun Black Tiger, dan dolenta ta saki
hannun big bro, da hannu ɗaya wannan robbot ya ɗagata daga saman chair ɗin, kai
tsaye ya yi wurgi da ita izuwa saman wani kyakkyawan sofa two seater dake wajen
wanda an ajiye shi ne dan ɗan hutawa idan ka kammala cin abinci, dama ana san idan
ka ci abinci ka ɗan miƙe kafafunka ka huta ko da na 30 mins ne, a nan ne abincin
zai shiga cikinka da kyau.

Bata san ba'a kusantar Black Tiger ba idan ma'aikatansa suna nan kusa, yanzu mutum
zai bakunci lahira, ita ta samu har ta zauna a kusa da shi shi ne zata kama
hannunsa, a tinanin robbot ɗin riko hannunsa da ta yi ta hana shi cin abinci cutar
da shi zata yi shiyasa ya yi mata abin da ya yi mata. Kai tsaye ya nufi kanta domin
ya zartar da hukuncin da suke yiwa dik wanda ya kusanci Black Tiger. Wuyarta ya
rike tare da sanya ɗayan hannunsa zai ɓalle mata makogoron wuya shikenan ya
kasheta, yana ƙoƙarin yin hakan Black Tiger ya dakatar da shi tare da ce mashi ya
barta ya koma bakin aikinsa, daga haka ya cigaba da cin abincinsa babu wani
bismilla da ya yi. Ita kuwa ta sha shakar robbot sai da ta ji kamshin mutuwa, ta
zaro ido tana numfashi sama sama.

Shi kuwa Black Tiger a cewarsa ya sa a barta ne saboda ba zai iya ɗaukar haukar da
Ronnie zai yi mashi ba, kun san yasan Floris ta mutu ai? To ace Sweetie ma ta mutu,
ai wlh Ronnie zai yi mashi hauka mai zigidir mai lasisi, yanzu ma bai san taya zai
iya shawo kansa ba idan ya gane Floris ta mutu, saboda har ga Allah Ronnie yana
kaunar Floris fiye da tinaninku, akwai soyayyarta ma a kasar zuciyarsa wanda bai
san da ita ba, kun ga kuwa babu zaman lafiya idan ya gano meke faruwa, ina ga wlh
irin hukuncin da zai yi wa master kare ba zai shinshina ba.

Tana ƙoƙarin miƙewa zaune domin ta samu damar shaƙar numfashi da kyau sai ga
Ronnie ya shigo wajen, ko excuse babu, hankalinsa a tashe ya ce. "Big bro please ka
tayani neman Floris, dik in da nike zatan zan ganta a cikin empeir ɗin nan babu
ita, na tambayi Angela ta ce mun tun shekaran jiya bata kara ganinta ba". Cikin
ruɗu yake maganar, har word ɗinsa suna harhaɗewa.

Miƙewa tsaye Sweetie ta yi, take ta ji faɗuwar gaba, a kiɗime ta ce. "Ina ta shiga
to? Karfa ace wani abin ya sameta a wajen yakin da aka yi....... ". Cikin zafa
Ronnie ya katseta da cewa. "No lovely sis, babu abin da ya sameta, nasan dai fushi
take yi da ni shiyasa kila take san bani wahala ta ɓuya, kila ma ta gudu wajen
parents ɗinta ne"..... Shi kansa faɗuwar gaban nan yake ji, amma yana ƙoƙarin dole
dole sai ya karyata zuciyarsa a kan wani abin ya sameta.

Shiru Sweetie ta ɗan yi kamar mai tinanin wani abin, can kuma sai ta ce. "Muje
wajen parents ɗin nata mana mu dubata". .... A gaggauce ya amsa da. "Good idea,
lest go". Ya faɗa tare da juyawa da sauri. Cikin kakkausar murya Black Tiger ya
dakatar da shi ta hanyar ce mashi kada ya kuskura ya fita bedroom ɗin nan nasa a
wannan daren. Turus Ronnie ya tsaya, lokaci guda zuciyarsa ta tilasta mashi dole ya
yarda wani abin ya sameta, dan Black Tiger bai taɓa hana shi yin komai ba idan ya
sa a gaba, tun da kuwa ya hanasa zuwa nemanta dole akwai abin da ya saɓa, to me
kenan? Tashin hankali da fargabarsa

Please Login or Register in order to submit comment