You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shassha mana kamshi ana wani ɗaɗɗaure mana fuska.

(Kambalai kun san me na tina? Yadda haɗuwar Pretty and Heleena zai kasance, ga
Sareena a gefe, yadda Heleena ke mutuwar son Smart anya akwai zaman lafiya kuwa? Ga
shi su turawa mata ɗaya suke yi, idan Heleena ta san ya yi aure shikenan tasan ba
zai kara wata mata ba sai dai idan kashe Pretty zata yi sai ya aureta, akwai
badakala! Pretty dake son Kamran kuma shi aka bata ya kuke ganin wannan bidir zai
faru idan tasan ita matar wani ba Kamran bane?!)

A gefe guda kuwa Zee ce zaune a main parlour na ƙasa a party ɗin Aunty MieMie, tana
shirye cikin abaya mai shegen kyau launin dark purple, ta yafa mayafin a kanta, ta
yi matuƙar kyau sosai. Tana zaune saman kujera mai zaman mutum uku, shi kuma Dr
yana zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu suna fuskantar juna. Sanye yake da
ƙananan kaya masu kyau da tsada. Zee tana rike da baby Ahmad yaro mai wayo kuma bai
lafiya, yana girma yana ƙara kyau kamanninsa da familyn Akka yana ta kara bayyana!
Ya fi kama da uncle Jahiz sosai, sai dai banbanci yanayin zanen face ɗin baby Ahmad
sak Korean face ne, kazalika yanayin haskensa, ya fisu haske nesa ba kusa ba!.

Ta yi ƙasa da kanta tana jin kunyarsa, sai zuba mata love word yake yi babu kama
hannun yaro, Zee ta faɗa dayawa fa!!.

A gefe guda kuwa, Mahreen ce rike da wayar Momma suna waya da guyson, ya ci sa'a
yau momma ce ta bata wayar shiyasa ta karɓa, ba dan haka ba ta ce ta wuce class
ɗinsa, kai Mahreen duniya, wai ta wuce class dinsa, ai Aunty Chuchu ta ce mata ai
ita matar manya ce ba ta yara ba, to ita a tinaninta manyan a shekaru ake nufi,
bata san Chuchu tana magana ne a kan babban gida ba, shiyasa ta ce ta wuce yara sai
manyan kai, manyan kai a fagen kuɗi ake magana!! Kuɗi kuwa kowa ya san guyson
akwaisu ba'a magana!.

Sai shirme take zuba mashi shi dai ko kaɗan bai damu ba, sai murmushi yake yi yana
kwance a saman bed ɗinsa yana fuskantar celling, ya baro Auta and Leesharh a
bedroom ɗinsu suna a tare.

A gefe guda kuwa hira sosai Aunty MieMie da Khadijah suke yi, Aunty MieMie tana san
yi mata wayo ta faɗa mata wanenen daddyn Ahmad, dan tana zargin uncle Jahiz ɗinsu,
amma Khadijah ta ce mata bashi bane, shi ne nan take son nuna mata fifikon shekaru
ta yi mata wayau!.

A can gefe kuwa, gabaɗaya manyan cikin fada sun hallara sakamakon diran wani bako
sabon fuska da basu sani ba, da alama matafiyi ne da hanya ta biyo da shi ta nan,
dik a jigate yake yi, daga ganinsa ya sha wahala, magana yake yi da harshen da basa
ji, kun san nace maku Kamran yana da yare wanda suke magana da shi da Mammarsa, to
da shi ya yi ƙoƙarin yi masu magana da Fada, ko kaɗan bai yi turanci ba, dan ya
manta yaushe rabonsa da turanci, tun rabuwarsa da su Pretty tsawon almost 2 years
yanzu ake magana, ya sha bakar wahala a wajen neman su Pretty, shi yanzu ma ba
babansa yake nema ba, Pretty yake nema, dan ya nemi babansa har ya gaji bai iya
sanin in da yake ba, dama kuma mammarsa tasan ba zai taɓa iya ganewa ba, shiyasa ta
yi mashi ɓaddakama, dan tasan idan ya doshi in da babansa yake, to fa ba shakka ko
shi Kamran ɗin bai gane ba babansa ya gane ɗansa, ita kuma ba zata so hakan ba, dan
bata shirya rasa shi ba, bai san tarihin babansa bane shiyasa ya nemi zuwa in da
yake, matsa mata da ya yi yaki cin abinci zai kashe kanshi a banza yasa ta yarda ya
je, amma ba wai dan ya haɗu da baban nasa, kawai dai ta rabu da shi lafiya. MAMMA
FA TA IYA MUGUNTA YASEEN!!.

Tsawon shekaru biyu yaro na shan azaba yana wantagaririya a hanya, har ALLAH ya
jefosa kingdom of power.

Idanun King a kansa babu ko kyaftawa, gani yake kamar ya gane wannan fuska dik da
cewa ya canza, ya rame saboda wahala, ya yi duhu, amma kamanninsa ya dawo, dik
askin da mammarsa ta yi mashi gashi ya sake fitowa fiye da na da a wajen, so
kamanninsa sun bayyana.

"Sarkin gida ku ɗaukesa zuwa ɓangaren baki, ya ci abinci ya huta zuwa gobe sai
mu san me ya kawo shi". Cewar King da tin da ya fara maganar har ya dire aya bai
zare kallansa daga kan Kamran ba. "Commander kasa a kula da shi sosai zuwa gobe".
Ya sake faɗa still kallansa a kan KAMRAN sosai, har mamakin irin kallon da King
yake yi mashi KAMRAN ɗin ya yi, sai dai kuma!.

Uhm my people's abin da baku sani ba a nan shi ne, da Kamran da Hoorain uwarsu
ɗaya, Hoorain mahaifiyarsa ya taimaka a daji lokacin da ya je neman su Auta ba tare
da ya sani ba, kuma babu wanda ya san KAMRAN da HOORAIN uwarsu ɗaya, harta
commander bai sani ba, saboda KAMRAN a forest aka haifesa, da cikinsa ta shiga
dajin, KAI MY PEOPLE'S YADDA KUKE TINANI FA BA HAKA STORYN YAKE BA, KU JIRA
BAYYANAR GASKIYA KAWAI, DAN DIK YADDA ZAKU YI TINANI WLH IDAN BA NI NA WARWARE MAKU
BA BA ZAKU TAƁA GANO BAKIN ZAREN BA, DAN A DABAYBAYE KUKE, KU DAI KAWAI KU JIRA,
LOKACIN BAYYANAR GASKIYA TA YI AI, YANZU ZA'AYI TA ZAƘULOSU ONE AFTER THE OTHER! BA
DAI KAMRAN YA BAYYANA BA? TO KU JIRA AKWAI BABBAR CAKWAKIYA, WAI KUN ƊAUKA A BANZA
NIKE TA CE MAKU AKWAI BABBAR CAKWAKIYAR NAN NE? UHM NA CE UHM, ABIN SAI SHIRU
KAWAI, KANKU ZAI ƊAUKI CAJI OVER.

Kamannin Hoorain King yake gani a tattare da fuskar Kamran shiyasa ya kura mashi
ido yana ta kallonsa, da farko ma ya ɗauka Hoorain ɗin ne, shiyasa ya shiga ruɗani,
sai da ya dawo hayyacinsa sosai ya iya gane cewa Hoorain ya fi Kamran haske nesa ba
kusa ba, sannan Hoorain ya fisa kyau nesa ba kusa ba, Hoorain ya fisa tsawo. Dik
cikin fada babu wanda ya lura da kamannin Hoorain a furkar wannan bako face King,
shi kaɗai ya lura da wannan, da yake ma ba ganin face ɗin Hoorain ɗin suke yi ba,
akwai waɗan da ma basu san shi a zahirance ba!

Miƙewa sarkin gida ya yi tare da cewa ya nufi in da bakon nasu yake durkushe a
saman gwiwowinsa, dik ya galabaita sosai, umarni ya bawa warriors guda biyu da suka
shigo da shi a kan su ɗaukesa zuwa ɓangaren baki matafiya. Basu ɓata lokacin wajen
ɗaukarsa zuwa can ba, commander ya miƙe ya bi bayansu. Har yau har gobe commander
yana kallan Hoorain a idanunsa, cutar bata sake shi ba.

Tsabar mugutan irin na King kuma ya ce ba za'a kaisa hospital ba, dan idan suka
tsaya mashi cutar ta sake shi, ya gane da gaske Hoorain ya mutu to tabbas zai yi
masu bore, zai dai'na kare rayukansu da dukiyarsu, shiyasa ya ce a rabu da shi ya
cigaba da imagine ɗin har abada!.

My people's me kuke tinanin zai faru ne wai? Uhm true colorn King yana ta kara
bayyana, ta bakinku ƴan special grp ko dai a kan King RAWANIN ZALINCI take ne? To
ku je dai zuwa, gaskiya tana ta bayyana tana zaƙulo kanta!!. In da one tambaya!
Meyasa Mammar KAMRAN ta ce idan ya kusanci babansa tamkar ya kusanci mutuwarsa ne?
Meyasa ta ce wajen babansa ba in da zai je bane?.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬


62

Momma gabaɗaya kanta ya shiga ruɗani, tinani a kan mahaifiyar Hoorain ya sakota a
gaba sosai, dik tinanin da ta yi sai result ɗin ya bata cewa Hoorain ɗan King ne,
dik yadda zata yi wannan amsa yake fito mata, gabaɗaya kanta ya ɗauki zafi matuƙa,
jikinta har zafi ya yi saboda wannan tinani da damuwa game da tashin hankali!.

Da yake tana da alkunya ita, sai ta ji ba zata iya faɗawa Smart abin da mahaifinsu
ya aikata a baya ba, dik da cewa ta san yasan sarakuna wannan al'adarsu ce, so ba
wani abin bane a wajensu, amma ta ji nauyin hakan matuƙa. Bata ma san Smart kam ya
fita sanin komai ba!!.

Ita kuwa Mama sai ƙoƙarin banƙaɗo dalilin da zai sa ace Smart ba ɗan King bane take
yi, dik ta damu kanta, ba yadda za'ayi ta ci burin ɗanta Ramish ya gaji karagar
mulki za'a wani ce mata ga wani ɗan da zai gaji ubansa ba nata ɗan ba, gaskiya ba
zata yarda ba!. Rashin sani ya fi dare duhu, Allah sarki har ta ban tausayi, ya
zata ji a lokacin da za'a ce mata Ramish ba mallakinta bane?!!.

Mummyn Chuchu dai yanzu ta cire rai da mulki baiwar Allah, da farko tana sa rai,
amma yanzu tin da bayan Ramish ga Smart shikenan sai ta hakura ta fawwalawa Allah
lamuranta.

UNCLE ABBAS PART. Bakaramar rikici ake bugawa a tsakanin Mammie da Aliyah ba, dik
kuma rikicin a kan King Zuhair ne, sun yi sunyi tsafinsu ya gagara kama shi, Aliyah
ta yawace bokaye daban daban amma kowannensu amsa ɗaya yake bata shi King Zuhair ya
fi karfinsu, ba zai tsafu ba, bama King kawai ba, ƴaƴansa gabaɗaya nan gani nan
bari ɗumaman mayya, shiyasa kuka ga da suka yi niyyar tsoratar da guyson ya zage
aljanar tas, to jinin Zuhair sun fi karfin wani sihiri ya taɓasu, shiyasa suka kasa
cusawa Smart soyayya Sareena, saboda ya fi karfinsu.

A yanzu kwakkwaran shiri suke shiryawa mai zafin gaske wanda suka ɗaukarwa Queen
Zarina alkawarin zasu salwantar da jinin mutum ɗaya daga cikin ƴaƴansu ko ƴan uwa
domin ta yi masu bakin sihiri a kan jinin King Zuhair, to dama kun san ZARINA tana
kullace da kingdom of power, aikuwa ta yi gaggawar aminta da wannan shiri, ta kuma
rattaɓa alkawarin zata yi masu aiki, yanzu Mammie tana cikin zulumi da damuwa
matuƙa a kan waye zata sadaukar da jininsa ga Zarina? Ba zata iya bada jinin
Sareena ba, saboda sheɗancinsu ɗaya, Sareena tana bin abin da take so, kuma ƴaƴa
biyu gareta, yanzu dole ta sadaukar da jinin Fanan muddin tana son cikar burinta!!!
Uhm ana tashin hankali ba kaɗan ba a Kingdom ɗin nan.

Sareena kuwa tana can har da zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda uncle Abbas ya faɗa
mata cewa ya bada aurenta ga Smart, sai murna take yi, har da wani cewa yanzu
lokacin cin uban dik wanda ta gani a part ɗinsa ne, dan shi ɗin mallakinta ne ita
kaɗai, sai tsantsara kwalliya take yi zata je wajensa, wai fa ba shi zai zo hira
ba, ita zata je wajensa, dik da a tsorace take da shi, amma tana da kwarin gwiwa a
kan yakininta, ta yi imanin ba'a jin daɗi sai an sha wahala, kuma ta yi imanin
yanzu babu abin da zai yi mata tin da har ya karɓi aurenta hakan na nufin yana
sonta, bata san cewa shi bai ma san wainar da ake toyawa ba!!.

Shi kuwa Kamran an kaisa part na baki, commander ya sanya tsaro a kansa sosai,
sannan anbashi kulawa a matsayinsa na bakonsu, sun bashi abinci mai rai da lafiya,
sun kuma tsaya mashi ya yi wanka ya canza tamkar ba shi ba, ya fito a ainahin yaron
mammarsa, babu abin da yake ransa face tinanin Pretty, baya tinanin mammarsa kamar
yadda yake tinaninta, saboda yasan mammarsa mace ce da zata iya tsayawa kanta a
kowani hali, jaruma ce kuma sadaukiya, so Pretty kuma macece mai rauni da bata san
kanta ba bare har ta san me duniya yake ciki, tinanin twins ne kawai a ransa,
tsawon waɗan nan shekaru biyun bai taɓa yin minti biyu ba tare da ya tuna amanarsa
kuma twin's ɗinsa ba, suna ransa tamkar yadda yake a ran Sweetie, kunga kullum tana
tinaninsa, amma Pretty ko maganarsa bata yi, ko da yake ita yarinya ce da ba zaka
taɓa iya gane cikinta ba, bata magana bare kasan ina ta dosa, waya sani ko tana
tunasa bayyanawa ne kawai bata yi!

My people's, KAMRAN team, ina mai baku hakuri a kan abin da ya faru, kun san bana
yin abu haka kawai sai da kwakkwarar dalili, na san kun ji zafin auren Pretty da
Smart, amma nasan idan kuka ji dalilina da kanku zaku jinjina mun, tafiyar yanzu ta
fara, kada ku manta yanzu muka gota tsakiya kaɗan, ina da dalilina mai karfi na yin
hakan, amma kun kusa ji soon!! Ku yi wa KAMRAN fatan samun wacce zata kasance
alkhairi a garesa, ba son rai'na bane nike raba masoyan nan, dalili yake sanyawa!!
Amma kada ku damu a karshen page ɗin nan zan faranta rayukanku!......🙌💘

*CROWN OF JUSTICE*🔥🔥

Katafaren government house na ƙasar, zaune dattijo MUZAFFAR yake a saman wani
dandatsetse kuma lallausan kushin mai bala'in tsada a cikin katafaren parlournsa,
yana rike da wani littafin mai suna The Franklin scandal yana karantawa, yana cikin
shigar manya-manyan malaman larabawa masu kima da mutumci, fuskarsa sanye da farar
glass, ya sha rawani mai bala'in kyau na manyan malamai, farin balarabe ne tas
wanda da ka gansa kasan mutumci da kima game da kyau haɗe da dukiya sun yi mubaya'a
a wannan waje. Daga bakin kofa wasu zaƙwaƙuran securitys ne ke gadinsa, ya natsa
cikin karatun da yake yi sai ji ya yi an yi mashi sallama.

Cikin sanyin murya ya amsa, murya mai cike da dattaku da kima. Wani security ne ya
shigo cikin parlourn, with full respect ya ce. "Sir Prince Rishan ne yake neman
iso"....... Gyara zamansa cikin natsuwa dattijo ya yi kafin ya ce. "Ka ce ya
shigo"....... Sara mashi securityn ya yi alamar girmamawa kafin ya juya ya nufi
waje. Yana fita bai fi five seconds ba sai ga Prince Rishan ya shigo cikin shigarsa
ta alfarma irin ta ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji da su. Zuba mashi idanun
dattijo ya yi yana kallonsa har ya kariso, a saman kushin da yake zaune ya zauna,
amma kafin ya zauna sai da ya duka kasa, dik wata sarauta ya ajiyeta a gefe ya
tsugunna a gaban dattijo ya kwashi gaisuwa. Hannu dattijo yasa ya shafi lallusan
gashin kansa kafin ya amsa gaisuwar.

Kusa da shi ya zauna, kallo ɗaya dattijo ya yi mashi ya gane cike yake da damuwa,
dan haka sai ya rufe littafin dake hannunsa ya ajiye a gafe, sannan ya juyo da
hankalinsa game da natsuwarsa a kan Prince Rishan. A natse ya ce. "My son akwai
wata damuwa ne?".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Papa akwai damuwa sosai ma, amma papa please meyasa
baka san faɗa mun gaskiyar lamari a kan waɗan nan mutane biyu?". (Ude and Zarina
yake magana) Dogon ajiyar zuciya Papa ya sauke kafin ya ce. "Rishan tono gaskiyar
babu abin da zai kareka face bakinciki, koma menene ya rigada ya wuce, ka bar
maganar, yanzu ina Rishma?".

Ciki ciki ya amsa da tana gida, da alama ransa bai so amsar Papa ba sam. Wai menene
gaskiyar da Rishan yake son sani?. Batu ne a kan mutuwar babansa wanda yake zargin
kashe shi aka yi, dan shi bai samu damar ganin gawarsa ba, a lokacin da abin ya
faru baya nan, kuma zarginsa gaskiya ya ce, dan familyn Thomas ne suka kashe shi,
wato familyn Zarina kenan, ita ta yi poisoning na King Ranveer da hannunta, poison
ɗin kuma daga hannun mahaifinta Thomas ya fito, so ita ta kashe sirikin nata, domin
kawai Ude ya karɓi mulki ita kuma ta kwace, burinta kuwa ya cika, sai dai ta bar
baya da kura, domin kuwa Papa ya san komai, ta so rufe mashi baki amma abin ya ci
tura, shi kuma Papa yanzu abin da yasa baya son bayyana gaskiya saboda Rishan shi
kaɗai ne, ba zai iya yaki da su ba, zasu cutar da shi ne kawai, dik da suna bala'in
shakkarsa da tsoronsa, amma aka ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, Papa yana ganin
kamar zasu iya cutar da Rishan and Rishma, shiyasa ya ki faɗa masu gaskiya, har yau
Rishan ya gagara samu natsuwa, zuciyarsa tana faɗa mashi lallai dole ya nemo waɗan
da suka kashe babansa. Kun san meyasa na baku wannan tarihi? Saboda a gaba kaɗan
zaku tsinci kanku a alaƙa da wannan tarihi, bana son ina gaba in dawo baya shiyasa
na faɗa maku a nan kawai, dan a gaba ba ɗauko tarihin daga farko za'ayi ba, za'a
ɗaura ne daga kan in da Rishan ya tsaya!.

And Papa yana zargin da sa hannun Ude a kashe King Ranveer, saboda bai yarda Zarina
kawai ta kaddamar da wannan aikin ba!. Lallaɓa Rishan Papa ya rinƙa yi har ya
hakura ya daure ya sake suka sha hira da Papa ya mance da batun su Zarina, sai dai
a karshe da ya tashi tafiya ya ce da Papa. "Papa zan kashe Ude tin da yaki komawa
musulunci, kuma kasan hukuncin wanda ya yi ridda!". Ya kai karshen maganar tare da
juyawa zai fita.

Miƙewa tsaye Papa ya yi, sai da ya gyara alkyabbar jikinsa, sannan ya gyara glass
ɗinsa kafin ya ce. "Kada ka yi saurin yanke hukunci Rishan, ka kara mashi lokaci
zuwa nan da ko ƴan watanni ne, idan babu haske sai mu san hukuncin da zamu yi
mashi, koba komai yayanku ne".

Kun san me my people's, wlh ba dan Rishan baya shiri da su Zarina baya taimaka masu
ba, tabbas da babu wanda zai iya cinsu da yaki, saboda shi ɗin namiji ne kuma
jarumi ne, tamkar yadda kingdom of power suke da commander Zafar, haka jarumtarsa
yake, tsab Rishan zai iya kayar da commander, saboda commander Zafar ya tsufa, shi
kuma sabon jini ne, amma Zarina saboda rashin wayo insert of ta kallaɓasa ya zama
mai tsaya masu wai take faɗa da shi, ko da yake shi ma ba zai yarda ba, dan ya
tsaneta tin kafin Ude ya aureta, tun yana yaro ya tsaneta sosai!.

Jinjina kai ya yi tare da cewa. "A kullum kai kake dakatar da ni Papa, kuma In Sha
Allah ba zan taɓa gajiya da bin umarninka ba". Ɗan kara sakin fuska Papa ya yi haɗe
da cewa. "ALLAH ya yi maka albarka Rishan, In Sha ALLAH kana cikin kariyar UBANGIJI
babu abin da zai sameka, sannan zaka kasance cikin farinciki, na gode kuma na yi
murna da har yau baka cireni a matsayin uba da ka ɗaukeni tin King Ranveer yana
raye ba, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, ka kula da Rishma sosai, ka tsaya da taka
tsantsan".

Amin ya amsa da shi tare da juyawa zai fita, har ya kai bakin kofa sai kuma ya
juyo, ya yi mamakin ganin yadda Papa yake yawan kallonsa a kullum idan ya zo zai
tafi. "Papa meyasa kake yawan cewa in kula da Rishma da kai'na?". Ya jefa tambayar
cike da sa ran zai samu amsar da yake so, dan abin na damunsa ta yadda ko a waya ya
kira Papa sai ya ce mashi ya tsananta kula sosai, abin ya fara ɗaure mashi kai.

Murmushi irin na manya Papa ya yi dik dan ya kwantar mashi da hankali kafin ya ce.
"Babu komai, kawai ina so ne in tabbatar da amanar da King Ranveer ya bani na rike
amanar sosai, dan haka ka kula, ba zan gaji da faɗa ba, dan amanace ku a gareni!!".
Shiru ya yi tare da juyawa ya cigaba da tafiya, ko kaɗan bai gamsu da amsar Papa
ba, ya dai yi shirun ne kawai, kuma hakance, Papa na ɓoye mashi gagarumin gaskiyar
da yakamata ace ya sani, amma Papa ya dubi abin ta wata fuska ta daban shiyasa ya
ɓoye!.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Bayan wani lokaci.

Zaune Auta take a saman bed ɗinta ta yi shiru tana tinanin rayuwa, wasa wasa yau ta
shafi almost 3 month ba tare da Hoorain ko jin sautin muryarsa ba, abin har ya fara
zame mata jiki, yanzu ta fara yarda da Hoorain baya duniya, Leesharh tana bedroom
ɗinta tana wanka, guyson ya koma kingdom of power saboda an buɗe school, dole ya
koma.

Ramish baya nan ya fita, a yanzu ya yi nasarar capke mutane kaso 60 cikin ɗari na
masu nikaf, sai dai dik wanda ya kama sun ki faɗa mashi wanenen mai turosu, ya
azabtar da su har ya gaji, amma sun ki faɗa, sun ce su haya killers ne, idan sun
karɓi contract ko kashesu za'ayi alkawari suke ɗauka basa taɓa tona asirin wanda ya
sanyasu aiki, sannan su idan suka karɓi aiki fa ko mutum me zai yi sai sun kashe
shi, ko duniya dikka zai basu idan sun karɓi aiki a kansa sai sun ƙaddamar.

Ba karamun ɓacin rai Ramish ya ji ba, ya sanar da Smart ga abin da yake faru, Smart
ya ce mashi kada ya damu ya kashesu gabaɗaya a rage mugun iri a cikin al'umma, kuma
idan ya kashesu kada ya sake saka hannunsa a neman wanda ya sakasu, ya bar mashi
aikin dan matsalar daga cikin gida ta samo asali, wanda ya sakasu yana cikin
kingdom of power, su kansu basu san ainahin wanda ya sakasu ba, dan haka ya bar
binciken shi zai kama koma wanenen a nan, saura kaɗan ya tattara dik wasu
hojjijinsa ya tinkaresu gadan gadan! Wannan ne ma dalilin zamansa a kingdom of
power bai koma Paris ba, shi ne kuka ga ya yi shiru kamar babu abin da yake yi, uhm
babban ɓarna yake yi masu ta karkashin kasa ba tare da sun sani ba,. BALA'IN CAN,
WANDA YA SANYASU KUMA YANA KINGDOM OF POWER?! HOW TO?! KUMA WHO?. UHM AKWAI ABUBUWA
FA!!.

Ba kara mun shocked Ramish ya ji ba a lokacin da ya ji abin da yayan nasa ya ce, ya
so ya faɗa mashi wani abin da zai kwantar mashi da hankali yasa ya ji sanyi a
ransa, amma ina sai ma kara mashi zafin da ya yi ta hanyar cewa kada ya kuskura ya
sake zuwa gidan King Badeen, dan baya son kowa ya zargi wani abin, sannan shi Smart
ɗin a zuwansa wancan karon da ya kawo Auta basu yi rabuwar daɗi da kakan nasa ba,
ya yi masu tas bai ragawa kowa ba, ya kuma ce masu in dai kannensa basu auri waɗan
da suke so ba to su ce shi ba jinin King Zuhair bane!!! Har da ce masu ya yi ya yi
masu alkawarin Zunaira zata rayu ne kawai da abin sonta, ba zata zauna da
Abdussalam ba! Sannan kuma Ramish ma yana da wacce yake so, kuma bare ce, yaga
wanda zai hanasu zama ma'aurata tun da su babu abin da suka iya sai son kai, to shi
kuma zai gwada masu a cikin Rahilarh ya haifu, ba su yi rabuwar daɗi ba dai, dan
King Badeen ya nuna kafewarsa a kan babu auren bare a cikin zuri'arsa, dik gida
zasu dawo su yi aure, har da cewa shi ma Smart ɗin ya dawo gida ya zaɓi mata! Shi
kuwa ya ce zai gwada masu shi ɗan yau ne. DA ALAMA SHIYASA YA AURI PRETTY DAN YA
GWADA MASU SHI MA YA AURI BARE, KAI SMART ƊAN DUNIYA NE WLH!!

Wannan dalilin yasa ya ce wa Ramish ɗin kada ya kuskura ya je gidan King Badeen,
dan yana zuwa zasu kama shi su yi mashi auren gida ne tin da Smart ya ce yana da
bare wacce yake so, sannan yasa Ramish ɗin ya cire sim ɗinsa ya ajiye a ƙasa, yanzu
yakin ya koma na cikin gida, bari a saita na cikin gida tukun nan, dama kun san
idan kana son yin gyara to ka faro daga cikin gida, a nan ne zaka iya cin nasara,
amma idan ka faro daga waje, kana gyara a cikin gida ana warware maka komai!.

To kun ji abin da ya faru a zuwan Smart gidan kakan nasu, a lokacin Momma tana
gidan uncle Rahab abin ya faru, da ta dawo baban nata bai sanar da ita ga abin da
yake faruwa ba, sai ya kira King Zuhair ya sanar mashi, nan King Zuhair yake sanar
da shi cewa shi ma Smart bai barsa ba, ya fi karfinsa, abin da yagadama kawai yaron
nan yake yi, nan fa ran King Badeen ya kara ɓaci ya kira uncle Muhammad wato daddyn
Smart na Paris, dan shi kaɗai kawai a duniya Smart yake jin maganarsa bayan Momma.

Sosai King Badeen ya yi wa uncle Muhammad faɗa a kan irin tarbiyar da ya bawa
Smart, yaro kwata kwata baya ganin girman manya, sannan baya da tsoro, dik wata
barazana a banza!. Hakuri uncle Muhammad

Please Login or Register in order to submit comment