You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna zargin mahaifiyarsa Maryam da aikata
abin da bai dace ba. Amma Allah ya kare Maryam da Annabi Isa ta hanyar da ya sa
Annabi Isa ya yi magana tun yana jariri, cikin Surat Maryam shafi na 19 daga aya ta
29 zuwa 34. Wannan mu'ujiza ta tabbatar da tsarkin mahaifiyarsa da cewa shi annabi
ne daga Allah".

"Wasu daga cikin Bani Isra’ila sun karɓi saƙonsa saboda sunga mu'ujizarsa da
kyawawan halayensa. Amma yawancin shugabannin addini da manyan masu mulki a lokacin
sun tsangwame shi saboda ya ƙalubalanci mulkinsu da karairayinsu, so sai suka yi
ƙoƙarin karyata shi a idan duniya, suna ƙara yaɗa jita-jita kan asalinsa (ba tare
da uba ba), wanda ya kasance babban kalubale ga rayuwarsa a cikin al’umma".

"Duk da tsangwama, Annabi Isa ya kasance mai rahama, tawali’u, da juriya. Ya yi
wa mutane wa'azi, ya warkar da cututtuka, ya kawo zaman lafiya, kuma ya ci gaba da
kira ga bauta ga Allah Shi kaɗai, ya jure ya kuma cije".

"So a takaice Annabi Isa ya fuskanci tsangwama sosai daga shugabannin addini na
Yahudawa, waɗanda suka yi ƙoƙarin halaka saƙonsa saboda yana yi musu tsawa kan
zaluncinsu!. Amma talakawa, marasa galihu, da masu buƙatar taimako sun karɓe shi,
suna girmama saƙonsa na tausayi da gaskiya, a iya nan zaku iya gane cewa Allah
Ubangijin talikai shi ne Allah na gaskiya, dan shi ne mai jin ƙan bayinsa, ya
umarci annabi isa da ya wanzar da adalci, ya daraja kaskantattun bayin da aka
kaskantar, waye zai yi maku wannan idan ba mahaliccinmu na gaskiya ba? Ko malamanku
sun taɓa kwatanta maku irin hakan ne?".

Ta jefa masu tambaya tare da tsayar da idanunta a kan Ronnie ta kuma dakata da yin
magana tana jiran su bata amsa.

Dik cikinsu babu wanda ya iya buɗe baki ya yi magana, dik ta sare masu gwiwa ta
kuma sanya sun ji zuƙatansu ya fara karaya da addinin Kiristanci, sun ji sun
kwaɗaitu da san Allah da take ambata mai adalci da kuma jin kan bayinsa, ga
tausayawa marasa gata, tabbas zuƙatansu sun ji tausayin hakan matuƙa, sai dai da
kamar wuya Black Tiger ya bar hakan ta cigaba da yin tasiri a zuƙatansu, saboda
kada ku manta jinin kiyayya haɗe da yakar addinin musulunci yake gudana a cikin
jikinsa, burin babansa kenan kafin ya bar duniya, kada ku manta babansa ya kaddamar
da Duniyar shaiɗanu, kunga kuwa raya Musulunci a cikin Black world abu ne wanda
yiwuwarsa tana da matuƙar wahala!!.

Floris baki ya mutu, ta rasa abin faɗe, saboda ta ji tsagwaran gaskiya.

"Ronnie ku bani amsata, shin a cikin malamanku akwai wanda yake faɗa maku da
kuji tausayin na kasa da ku? Ku kyautatawa marasa shi, ku taimakawa gajiyayyu
marasa karfi, ku jikan mata da yara?! Akwai waɗan da suke gaya maku hakan?".

A karo na biyu bai amsa mata ba, binta da kallo kawai yake yi dan yasan ba'a
taɓa gaya masu hakan ba, sai dai tongue nasa ta mashi nauyi ta yadda ya kasa amsa
mata. Idanunsa sun yi jajir kamar wuta, kamar ba lafiya ba.

Ganin haka yasa Sweetie ta kawar da tambayar da cewa. "Akwai wani tambaya da kuke
san sake yi mun dan tabbatar da gaskiya?".

Jinjina mata kai Ronnie ya yi, da kyar ya iya furta.
"A cikin malamullah ɗinku (Alqur'ani mai girma) a wace sura da wace aya ce
Allah ya umarci annabi Isa da ya yi magana a lokacin da yake jariri? And a wace aya
da wace surace Allah ya umarci mahaifiyarsa Maryam da ta yi azumin magana?".


Nisawa Sweetie ta yi kafin ta ce. "A cikin Al-Qur’ani Mai Girma, Allah ya yi bayani
kan waɗannan abubuwan biyu a Surat Maryam, inda aka kawo lamarin Annabi Isa (A.S.)
da mahaifiyarsa, Maryam a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya na 29 zuwa na 33".

"Lokacin da Nana Maryamu ta haifi Annabi Isa, ta damu sosai game da abin da mutane
za su ce game da ita. Sai Allah ya umarce ta da ta yi azumin magana (wato ta yi
shiru kuma kada ta ce komai ga mutane), domin Annabi Isa zai yi magana da kansa don
ya bayyana gaskiya. Wannan umarni yana cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya na 26".

"Lokacin da ta dawo cikin mutane da jariri goye a bayanta, sai suka fara
zarginta suna ƙoƙarin cin mutuncinta a kan ina ta samu yaro? A lokacin sai ta nuna
masu shi goye a bayanta ba tare da ta yi magana ba, har sun fara yi mata izgili da
iyashege suna dariya a kan ta ya za'ayi su yi magana da jariri?!".

"Kwatsam ba zato ba tsammani cikin umarnin Allah Annabi Isa ya buɗi baki a in da ya
ce. Lalle ni bawan Allah ne, Allah ya ba ni Littafi, kuma Ya sanya ni matsayin
Annab, ya albarkace ni, kuma Ya yi wasiyya da ni game da salla da zakka matuƙar ina
da rai, kuma ni mai kirki ga uwata ne, bai sanya ni mai girman kai ba, ni annabi ne
ba kamar yadda kuke tunani ba, aminci ya tabbata a gare ni a ranar da aka haife ni,
da ranar da zan bar duniya, da ranar da zan tashi da rai".
(Fassara maku ayar fa na yi dan ku ji me annabi Isa ya faɗa time da ya yi magana a
jaririnsa.)

"Ina san wanna Alqur'ani dan na duba wanna aya da kuma sura da kika faɗa".
Cewar Ronnie kenan.

"Tabbas in na bar wannan gari na koma forest zaka zamu Alqur'ani a wajena, yanzu
dai babu yana wajen Pretty".

Floris ce ta katsesu da cewa. "Beb ka yarda da abin da ta faɗa kenan?".

Dawo da kallonsa a kan Floris ya yi. "Ina ji a rai'na dik abin da ta faɗa gaskiya
ne, amma ba zan yarda da hakan ba har sai na ga hujoji a zahiri ba a faɗe a baki
ba, dan haka zan nemi Alqur'ani dan na karanta na tabbatar!".

A hanzarce Sweetie ta karɓi zancen da cewa. "Tabbas zan baka hujjoji a zahiri da
zarar na bar nan".

Jinjina mata kai ya yi tare da miƙewa ya nufi hanyar shiga toilet.
"Yau muna da gagarumin party a empeir ɗin nan na fidda gwanar kyau, Sweetie
ki shirya, yakamata ki shiga cikin wanna gasa fa nasan zaki fi kowa, zaki samu
kyauta babba daga wajen yaya". Cewar Ronnie dake nufar toilet.

Jinjina kai Sweetie ta yi, a ranta ta kudurta cewa tabbas zata biyewa mutanen
birnin nan dan ta rinjayesu izuwa addininta, dan haka zata rinƙa shiga cikinsu,
zata bi al'adunsu dik dan ta yi masu mage mai kwamciyar ɗaukar rai, a cikin
zuciyart ta furta.

"Ya Allah kasa kafin na bar garin nan ko da rabinsu ne na samu su musulunta, Allah
ka tayani ka taimaka mun ka dafa mun".

Sosai Floris ta ji rashin daɗin cewa da Ronnie ya yi Sweetie ta shirya ta shiga
cikin gasarsu da suke yi dik karshen sati, dan tasan Sweetie ta fita kyau nesa ba
kusa ba, so tasan zata bugeta ta cinye mata number na farko da take zuwa, sai ta ji
ta kara jin haushin Sweetie, dama can akwai sauran haushinta na zagin malamansu da
ta yi, sai ya karu mata.

Ita kuwa Sweetie raba jikinta da jikin bangon ta yi ba tare da ta sake bi ta
kan Floris ba ta nufi hanyar fita faga cikin ɗakin.

"Ina zaki je?". Ronnie ne ya jefa mata tambayar.

Da sauri ta juyo haɗe da kai kallonta in da yake, yana tsaye a bakin kofar
toilet ta waje, ya harɗe hannaye a saman kirjinsa.

"Zan je wani ɗakin ne na yi amfani da toilet ɗin, lokacin sallar mangariba ta
wuce".

Da hannu ya nuna mata hanyar cikin toilet ɗinsa.
"Zo ki yi amfani da wanna, daga nan ki yi wanka, Floris je ki kawo mata ɗaya
daga cikin irin kayan da kuke sakawa dan yin gasa, mai kyau zaki kawo mata
fa".............. Ya yi maganar ne idanunsa a kan Sweetie.

Ba musu ta dawo ta nufi toilet ɗin nasa, yanzu ba zata yi gardama da su ba, dan ta
ɗaura ɗamarar musuluntar da su dikka birnin da izinin Allah, dan haka ta shirya
tsab wajen shiga cikinsu sosai dan ta san takamaiman ina ma suka dosa tukun nan.

Sai da ta iso dab da shi sanna ya bata hanya ta shige ciki, shi kuma ya wuce ya
nufi waje yana faɗawa Floris ta zo su je bari ya je wajen ƴaƴansa ya duba irin
kyautar da aka tanadawa waɗan da zasu zo daga na ɗaya zuwa na goma, ita kuma ta
wuce room ɗinta ta shirya ta kawowa Sweetie kaya sanna ta taimaka mata wajen
shiryawa.

Da okey ta amsa mashi a fili, amma a cikin zuciyarta ta kudurci niyar shiryawa
Sweetie mugunta ta yadda ba zata taɓa cin wanna gasa ba, har da shirya irin
kwalliyar muguntar da zata yi mata, ga shi Ronnie idan ya fita yanzu sai dai su
haɗu a wajen wasa kawai, so ba zai samu damar ganinsu ba bare idan Floris ta yi
mata ba daidai ba ya ce ta gyara mata, sai a cikin mutane zasu haɗu.

Hakan ne ma ya bawa Floris kwarin gwiwar cewa zata ɓata mata fuska ta dishashar
mata da kyanta.

Alwala Sweetie baiwar Allah ta ɗauro ta zo kamar yadda ta saba ta gabatar da
sallar mangariba, tana idarwa lokacin sallar isha ta yi, hakan yasa ta miƙe ta
gabatar da shi.

Sanna ta shiga cikin toilet ta yi wanka, tana fitowa ta isko Floris zaune a saman
bed ta tsantsara kwalliya kamar wata amarya, tana shirye cikin wani doguwar riga
mai kama da weeding gown, ta yi masifar kyau sosai, kwalliyar ya karɓeta matuƙa.

Sweetie baiwar Allah har da yaba kyalliyar tata ta yi, cikin sanyin murya ta ce.
Floris kin yi matuƙar kyau sosai".

Tsabar haushi kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta tina im bata amsa ba Sweetie zata
fahimci ta shirya mata wani muguntar ne, dan haka sai ta amsa da thank u. Kawai.

A kusa da ita Sweetie ta zauna tana bin kayan jikinta da kallo, irin kayan ƴaƴan
sarakuna ne, shigensu wannan sadauki mai taimaka masu a forest ɗin yake kawo masu
ita da Pretty suna amfani da shi!.

Su hajiya Sweetie manyan ƙasa, girma ya fara zuwa ƴan kirgan danginta sun girma
kamar na Auta Zunaira, hakan yasa yanzu take ɓoyesu, kamar dai yanzu yadda ta wani
ɗaura towel ɗin Ronnie daga saman kirjinta, ita ma Floris dik da take krista bata
taɓa yarda ta fito wanka kirji a buɗe, tana rufe kayanta, Floris ta fi Sweetie
shekaru, amma Sweetie ta fita cikar halitta, dan tula tulanta ɗaya ya yi kusan
biyun na Floris a girma.

In short kwalliya Floris ta tsarawa Sweetie kamar wata ta Allah, kamar dai da gaske
take tare da ita, alhalin a karkashin zuciyarta ba haka bane, hasada take da kyan
da Allah ya yi wa Sweetie da kuma iliminta, Floris an fara hasada da kishi.

Wajen da za'a gabatar da gasa ya cika makil, jama'a suna zazzaune cikin hall
ɗin, ƴan matan da zasu shiga wannan gasa suna killace cikin ƙayatatcen ɗaki, dama
haka suke yi, sai sun gama haɗuwa a cikin wannan ɗakin sanna sai su fito izuwa
saman stage na hall ɗin dan bayyanawa duniya irin kyansu da surar jikinsu.

Dikkanninsu matasan ƴan'mata ne da babu wacce ta wuci 18 years a cikinsu, sai dai
dikkansu daga 15 years suke, babu wanda take kasa da 15 sai Sweetie da zata shiga
gasan a yanzu.

Kafataninsu kayan jikinsu irin kayan nan ne da ake cewa aunty tsirara, sun ɗame
jikinsu dan fito da surar da Allah ya yi masu, idan ba ku manta ba a baya na gaya
maku ƴan'matan birnin suna da sura mai matuƙar kyau da ɗaukar hankalin dik mai
kallonsu, to hakance.

Sun yi kyau sun kuma saki gashi har baya, kowacce ji da kanta take yi, tana ganin
tafi kowa kyau, anyi fente fenten kwalliya kam har an gaji, ga wani uban high heels
a kafafunsu, wasu daga cikin sai taunar chewing gum suke yi suna yi wa junansu
kallon ƙaskanci da matsayin basu kai ba.

Ronnie yana tare da Oxil a saman kujera suna hira a kan yadda gasan zai kasance
da kuma wadda zata yi nasara.

Oxil dai ya ce Floris ce zata yi nasara dan yasan a kullum ita take bige kowa ta zo
ta farko, saboda ko kayan da take sanyawa a jikinta ya take na sauran ƴanmatan kyau
da tsada, bare a zo kan kwalliyarta, abin ba'a magana, hakan yasa take zuwa ta
ɗaya.

Angama kimtsa komai ƴan'mata kawai ake jira su iso. Ga shi Floris ɓatawa Sweetie
fuska, me kuke tunanin zai faru a wanna fasa? Ronnie zai yarda da hakan ko yaya?.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




A dab zasu shiga hall ɗin Sweetie ta tsaya bata shiga ba. Floris ta tambayeta
dalili, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.

"Kunyar shiga da irin wannan kaya nike ji Floris".

Binta da kallo Floris ta yi, nan take wani kululun bakinciki ya tokare mata
maƙoshi, kamar zata haɗiyi zuciya, saboda tafa zaɓo kayan da bashi da kyau sosai ne
ta bata, amma kuma sai ta yi bala'in yi wa kayan kyau, saboda tana da round butt,
yadda kuka san ita ta yi wa kanta halitta.
Floris bata san cewa ba kaya ne yake yi wa Sweetie kyau ba, yanayin shape ɗin jikin
Sweetie yake yi wa kaya kyau, in kina da kyau sai kaya ya zauna maki.

"Gaskiya Sweetie bai kamata ki shiga ba tin da kince addininku ya yi hani da
fidda tsiraici, kinga wannan riga kuma ta kamaki sosai". Cewar Floris. Cike da
hasada ta yi maganar.

Shiru Sweetie ta yi, sai ta ji kamar da gaske Floris ta gaya mata gaskiya
ne, ta yi mata nasiha kanan, wani irin sanyi ta ji a ranta, sai taga kamar da gaske
Floris take yi, kamar santa take yi, bata san ba haka bane.

"Tom shikenan Floris, zan koma ciki ni kam".

Tsabar farinciki ta kasa shanyewa har sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya,
buƙata ta biya.

"To ki koma kam zai fi". Ta faɗa fuska ba yabo ba fallasa ba kamar yadda ta
ɗaure face ɗin nata ɗazun ba!.

Juyawa Sweetie ta yi ta nufi hanyar komawa cikin gida, ita kuma Floris ta yi maza
ta shige cikin room na hall ɗin, wai dan ma kada Sweetie ta canza shawara ta ce
zata shiga ciki, shi ne ta yi saurin wucewa ciki ta yadda ko ta juyo ba za ta ganta
ba.


"Ina kuma zaki je?". Daga bayanta ta ji wannan tambayar.

Juyowar da zata yi gabaɗaya komai na face ɗinta ya canza, kwalliyar mugunta da
Floris ta yi mata maras kyau ɗin nan, dik kafin ta juyo ga Ronnie kwalliyar ya goge
izuwa wani tsantsararren kwalliya na ban mamaki, ta yi balai'n haɗuwa, har da wani
gashi dogo guda biyu ya bayyana a gaban goshinta wanda aka naɗa mata shi kamal
indomie.

Ta yi masifar kyau wanda sai da ta sanya Ronnie zaro idanu, cikin second ɗaya
magic ya canza mata kamannin kwalliyar face ɗinta.

Da yake ba ganin kanta a mirror take yi ba, sai ta ɗan sakarwa Ronnie murmushi
wanda ya kara haukata ƙwaƙwalensa, dimples ɗinta dik suka lotsa.

Kamar wanda ya ga abinci Ronnie bai san time da ya haɗiyi yawu ba, ya kasa sake ce
ko uppan.

"Ciki zan koma" ta bashi amsa tana kara faɗaɗa murmushinta.

Hannu kawai ya iya buɗe mata ba tare da ya yi magana ba. Tsaresa da ido ta yi tana
kallan irin shigar jikinsa, ya yi kyau matuƙa shi ma, sai dai ya yi aske gera, ya
raba gashin gerarsa har kashi uku, hakan ta yi mashi kyau kam matuƙa, sai dai a
addinin musulunci Allah ya tsinewa masu haske gashin gyara da masu kankare hakwara
su yi wishirya.

So hakan yasa Sweetie ta ɗan ji ranta ya sosu, meyasa zai rinƙa aske gerarsa haka?
Ga ɗan kunne a kunne har saman kunnensa, bayan haka ga sarkoki a wuya kamar wani
mace, har da wani ɗan pil a gefen bakinsa, sun yi mashi kyau kam over, sai dai
Allah ya haramta, dole ta san yadda zata gaya mashi ya rabu da sakasu.

Kamar ba zata je in da yake ba, amma ganin irin shigarsa yasa ta ji yana da kyau
ta je garesa dan ta shiga jikinsa sosai ta samu ya fita daga wanna irin rayuwa. Dan
haka sai ta nufesa da sauri.
Tana isa garesa ya rikota ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, ita ma bata
zare jikin nata daga nasa ba, sai ta rungume shi da kyau tana ɗan murmushi.

"Kinga yadda kika yi kyau kuwa?". Ya faɗa kamar mai raɗa.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba.

"Kin yi kyau sosai da sosai, zo mu je an kusa fara gasar".

Kamar zata ce mashi ba zata je ba, sai tunani ya faɗo mata a kan tana san fa ta
rinjayesu su musulunta, dan haka dole ta yi aiki tukuru, dole zata ɗan kawar da
idanunta a kan wasu abubuwan ta shiga jikinsu sosai.

Dan haka sai ta aminta suka shige ciki a tare.

Tin da ta ɗaura kafafunta a cikin wajen idanun mutane suke a kanta, kallonta kowa
yake yi babu kyaftawa, hakan ya ɗan sosa ran Ronnie, amma ya daure.

Floris ta kara jin haushinta sosai, dan tana ganin kamar Ronnie ne ya je ya gyara
mata face ɗin nata a cikin room ɗinsa, sai ta kara jin wani irin kululun bakinciki
ya tokare mata maƙoshinta, kamar ta shake Sweetie, amma ta girgiza sosai na ganin
wanna halitta ƙayataccen kwalliyar, babu wata mace da ta taɓa yin irin wannan
kwalliya a cikin birnin, zallar madarar kyau, ga yanayin gashin kanta dik cikin
birnin babu mai irinsa, ita kaɗai ce mai irinsa.

Amma kuma da Ronnie ya kawo mata Sweetie ɗin kusa da ita, sai ta ƙaƙalo murmushin
dole ta yi mashi tsabar iya makirci da munafurci.

Bai kawo komai a ransa ba ya haɗasu ya koma wajen zamansa.

Zubawa takalmar kafar Sweetie idanu ta yi tana kallon yadda suka ci uban nata a
kyau, bata taɓa kallon irinsu ba, da duwatsun lu'ulu'u aka kawata kwalliyarsa,
hakan yasa ya kara rinjayar jama'a dayawa wajen kai kallonsu a kan takalmar.

A tunanin Floris Ronnie ne ya ɗauko mata takalmar daga ɗakin Black Tiger, amma kuma
ba haka bane, dan shi kansa Ronnie bai san da takalmar ba, ruhohin tsafinta suka
canza mata komai!.

Dik fa abin da suke yi kada ku manta Black Tiger yana jinsu kuma yana ganinsu,
sai dai this time bai wani mayar da hankali sosai a kansu ba, ya mayar da
hankalinsa ne a kan katafaren ginin companyn motocinsa da ake yi, wato BLACK TIGER
SUPER AUTO MOTORS, yana san su zama na ɗaya a duniya wajen kyara motoci waɗan da su
suka fara kawo irin style ɗin, yana san su tashi kan duniya ne sosai.

So ya fi kayar da hankalinsa a kan ginin da kusan rabin aikin Robbot ne suke
yinsa ba ƴan adam na, hakan yasa aikin yake kara sauri yake kuma tafiya yadda ya
kamata, ga shi girman companyn gidan sama ne mai hawa goma, Robbot sun taka
muhimmiyar rawa sosai wajen rage samu mace mace mutane a kan wanna gini, su suke
hawa sama ƙololuwa su yi aiki, kunsan a gini irin haka laburas and engineers suna
rasa rayukansu wajen faɗowa kasa daga sama idan aka samu akasi, so yanzu Robbot ke
hawa sama wanda su idan ma suka faɗo sai dai su tashi su karkaɗe jiki su kara gaba
abinsu, babu abin da zai same su!.

So yanzu an samu sauki sosai wannan fasaha ta Black Tiger wajen amfani da Robbot
sosai a aikin da ƴan adam suke yi ya yi matuƙar birgewa, saboda ya taimakawa mutane
matuƙa. Yanzu hankalinsa baya a kansu sosai.

Ko ban faɗa ba nasan kunsan dik faɗin birnin Black world babu wanda za'a samu ta
iya doke Sweetie a kyau, dan faɗe ma ɓatawa ne, kun san in ta shiga fili dole mata
su matsa mata, hakan ma yasa Floris ta kullah mata tuggun ta hanata shiga wajen,
amma ina hakarta bai cinma ruwa ba.

Sweetie ta yi gasa kuma ta ci na ɗaya, Angela ta zo na biyu, sai Floris ta uku, ba
komai yasa Angel ta zo na biyu ba kuma face alhakin Sweetie ne ya kama Floris, ta
mata mugunta reshe ya juye da mujiya, ita da take zuwa na ɗaya kullum yau ta kare a
na uku.

Idan ranta ya kai miliyan to ya ɓaci, zuciyarta ya sosu, tsabar kishi da kuka ta
bar wajen taron, bata ma tsaya an shigar da mark na kowa a Idanta ba, ta wuce ciki
da gudu.

Sai gobe da safe za'a bawa waɗan da suka ci gasar kyautarsu, hakan yasa Sweetie ta
ce da Ronnie zata je ta yi barci dan zata tashi ta yi sallar dare.

Sam bai so hakan ba, ya so ta tsaya su yi casun rawar da zasu yi, ya so koya mata
rawa, amma baya san shiga hakkinta, sai ya rakota har cikin room ɗinsa ya ce ta
kwanta a nan shi zai je wajen rawar, in suka gama rawa kuma ba lallai ya dawo ɗakin
ba, kila a ɗakin yayansa zai kwana.

Ko tsoro babu a tattare da ita ta amsa da to tare da wucewa ciki, yana tsaye har
sai da ta canza kayan jikinta izuwa kayan barcin Floris da ya kawo mata, dressing
room ɗinsa ta shiga ta canza kayan, sanna ta zo ta haye gado, da kansa ya rufeta da
bargo kafin ya juya ya fita.

A tunaninsa Floris tana wajen gasa, dan bai ga fitarta daga wajen ba, hankalinsa na
kan Sweetie, so bai san ta fice ba, hakan yasa ya koma can dan su yi rawa da ita.

Ita kuwa Sweetie Ronnie na tafiya ta miƙe zaune, dama ba wani barcin da take ji, so
take ta dawo dan ta zo ta yi masu bincike a cikin gidan.

Kamar wata ɓarauniya haka ta saɗaɗa ta fito waje ta hanyar sanya password na kofar
ta buɗe, ya gaya mata password ɗin yanzu.

Ko tsoro babu ga dare wajen karfe 12, ga kuma kanta ko ɗankwali babu, kuma tasan
akwai ababen ban tsoro a gidan, amma ko ɗar bata ji ba ta nufi part ɗin Black
Tiger.

Kunsan komai ilimin mutum in dai yaro ne to sai yarintar nan ta nuna, a shirmen
yarintarta wai tunani take yi Black Tiger ya yi barci, hakan yasa ta lallaɓa dan ta
je ta yi mashi bincike a part ɗinsa, Ronnie ya gaya mata akwai kofar sirri na fita
daga cikin Daular nan a saukake, amma kofar tana cikin part ɗin yayansa, shi kansa
bai san takamaiman in da kofar take ba, amma zai bincika masu, to shi ne ita uwar
ƴan rashin tsoro ta je dan ta fara bincikawa da kanta, bayan kuma Ronnie ya gaya
mata ta yi taka tsantsan kada ta sake shiga gonar yayansa, in ba haka ba zata rasa
ranta ne a banza, amma kunga yarinyar nan bata ɗauki zancensa a bakin komai ba, ta
yi fatali da komai ta yi biris.

Babban parlournsa ta shiga, babu komai sai daddaɗar kamshi dake tashi, ko'ina
very very clean, kamar sabbin kaya aka zuba.

Wucewa ta yi ta nufi ɗaya daga cikin bedroom dake cikin parlourn, ba ainahin
bedroom ɗinsa ba.

Babu wani ɗar ta gwada sanya password irin na ɗakin Ronnie, ga mamakinta sai gani
ta yi kofar ya buɗe, wato ba ina ga daga kan Sweetie karfin hali ya kare yarinyar
nan. Kila ma ba dai'dai tasaka password ɗin ba kawai an buɗe mata kofar ne dan a
shirya mata tarko, amma sam bata gane ba!.
Har da wani ɗan siririn munafikin sallama ta yi yadda kukasan ɗakin Pretty zata
shiga.

Tashin sense, ai tana shiga cikin ɗakin sai ganinta ta yi a wani irin kungurmin
forest, wata duniya daban, wanda ganinsa kawai zai iya sa mai karamar zuciya
zuciyar tasa ta buga ya mutu.

Ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba na ganin wanna kungurmin forest bakin kirin
mai cike

Please Login or Register in order to submit comment