You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi magana da mutum yana
waje ko yaki ko ya so sai ya so bawan Allahn nan ya cigaba da yin magana kada ya
dakata, cikin wani irin sigar soyayya mai sanyi da tafiya da imani ya yi ta.

"Amma ai ban gaji da kallonka ba". Tamkar zata yi kuka ta faɗa........ "Nifa naki
ne, mu je ki koma ciki sai gobe mu sake kallan juna". Ya kai karshen maganar tare
da miƙewa rike da hannunta. "To amma zamu yi video call idan na koma bedroom
ɗina?". Kai ya jinjina mata, sannan ta miƙe tsaye, jan hannunta ya yi suka nufi
kofar fita, da kyar yake iya ɗaga ƙafafunsa, dan dik ta saukar mashi da wani irin
kasala na musamman. A bakin door ɗin ya saki hannunta ya buɗe kofar, sai da ya leƙo
waje ya tabbatar da babu kowa, sannan ya ce ta zo su tafi. Cikin natsuwa ta fito,
janyo kofar ya yi tare da jan hannunta suka nufi hanyar komawa.

Suna tafiya suna hira gwanin birgewa, tana faɗa mashi cewa lallai yau har waye
wan gari suna video call, shi ma da giyar soyayya na ɗebansa ya ce mata sallar
asuba ne kawai zai sa su yi sallama. Allah sarki soyayya. Sai daɗi take ji har suka
isa kusa da door ɗin da zai sadata da cikin gida, sun kuwa yi sa'a basu ci karo da
kowa ba. A bayan wasu dogayen flowers dake wajen ya tsaya tare da juyowa suna
fuskantar juna, daga in da suke suna iya kallan kofar shiga cikin gida, sannan
akwai hasken bulb dake wajen Flowers ɗin da suke haskota, sai dai a in da suke ɗin
ba haske sosai bane, hasken kaɗan ne yake riskarsu. Zubawa kyakkyawan face ɗinta
idanu ya yi. "I will going to miss you my Hoonaira". Ya faɗa can ƙasa ƙasa.

Jingina da jikin bangon dake ɗan gefe kaɗan ta yi, sannan ta ɗan ɗago kanta kaɗan
dan ta samu damar ganin face ɗinsa, kunga ya fita tsawo nesa ba kusa ba, cike da
salo mai jan hankalin da yakamata ace ta bari sai bayan auren nasu ya rinƙa yi
mashi irin wannan salo ta ce. "My Hero zan fi kewarka sosai fa". Wani irin kafiya
ya ji ta soki zuciyarsa, ta kara birkita mashi lissafi.
"Rabuwa da kai tamkar za'a rabani da numfashi nane, ina jin zan bar iska da
haskena a nan in shiga cikin gida, na tabbata babu wata light da zata iya haska mun
bedroom ɗina, dan na baro light nawa a nan, bana san komawa ciki my Hero, zan ji
tamkar a ƙarƙashin ƙasa nike".

Tin da ta fara magana idanunsa a kan ɗan bakinta har ta dire aya, sam kunnuwansa
basu saurari kalamanta ba, hankalinsa ya yi nisa sosai. Ai tana dire aya ta rufe
baki ya tsinci kansa da matsawa dab da ita, a hankali ya matso da face ɗinsa dab da
tata, tana tsaye tana kallansa bata ce mashi ko uppan ba, soyayyarsa ya rufe mata
ido, hankalinta ya yi nisa a kallan face ɗinsa..... "My Hoonaira, can I have a one
kiss?". Ya faɗa murya can ciki ciki a dishashe kuma, yana jin faɗuwar gaba sosai,
tamkar zai rasata ne haka yake ji.

Ita kuwa da yake sonsa ya rufe mata ido sai bata san lokacin da ta ce mashi.
"Whyn't". Ba. Haba aikuwa wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa, slowly ya haɗe
face ɗinsa da tata, kirjinsa na harbawa da karfi karfi sosai ya sanya hannunsa ɗaya
a saman waist ɗinta, ɗayan hannun nasa kuma ya ɗaura a saman bayan wuyanta, cike da
tsantsar kaunarta ya haɗe bakinsu waje guda.

Ko kaɗan bata yi ƙoƙarin taka mashi birki ba, sai ma hannunta ɗaya da ta ɗaura a
saman faffaɗar kirjinsa, ta ɗaura ɗayan kuma a saman bayansa. Hot kiss ya shiga
bata cikin salon da bai san ta ya aka yi ya iya bama, ita ma mayar mashi da martani
ta shiga yi cikin salon soyaya mai kara narka zuciya, ai bai san lokacin da ya
janyo waist ɗinta ta tafi gabaɗaya ta faɗa saman kirjin nasa ba, macewa suka yi da
kissing na juna babu kakkautawa. Woooooo yau Hoonaira ta bawa heronta abin da ba
zai taɓa mantawa ba, gabaɗaya ya fita a hayyacinsa, ya ƙanƙameta sosai sai juya
tongue ɗinsa a cikin bakinta yake yi, abin mamaki, ko waye ya koya mashi kiss cikin
salo har haka kuma? Shi da yake so silent bai san komai ba!.
Sai da ya sha lips ɗinta son ransa, ya gama yin musayan yawun bakinsu, sannan
ya saketa yana wani irin numfashin da kana ji kasan yana a cikin tsananin buƙata,
ƙasa iya yi mata magana ya yi, idanunsa a ƙasa ya yi mata nuni da kofar shiga cikin
gida, alamar ta tafi da sauri tin kan shaiɗan ya cigalaba mai gabaɗaya a kansu
wajen sanya shi ya aikata fiye da abin da ya yi. Ita kanta gabaɗaya jikinta tamkar
an zare mata laka, bata da karfi ko kaɗan, da kyar ya iya jan kafafunta ta nufi
cikin gida, ko sau ɗaya bata waiwayosa ba, shi kuwa, tana tafiya ya ɗago idanunsa
ya tsareta da kallo har ta shiga ciki, lokacin da ta turo kofar nan sai ya ji
tamkar kofar zuciyarsa ta datse, gabaɗaya sai ya ji tamkar an jefasa cikin kunci da
matsi, da kyar ya juya ya nufi bedroom ɗinsa. Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinsa ya
fara juyi dan samawa kansa sassaucin abin da yake ji.

Ita kuwa kai tsaye bedroom na Momma ta nufa, sai dai ko da ta je babu kowa, hakan
yasa ta fito ya nufi wajen King, har zata shiga sai kuma ta fasa ta koma bedroom
ɗinta. A lokacin Pretty ta jima da yin barci abinta. Saman bed ta haye tare da
ɗauko wayarta, lokaci guda ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, gabaɗaya abin da ya faru a
tsakaninta da shi ne ya dawo mata cikin kwakwalwarta, lumshe idanunta ta yi tana
tariyo yadda ta ji tausasan lips ɗinsa wanda ta san babu wata mace da ta taɓa
ɗanɗanawa sai ita, dama kuma mallakinta ne, shi da ko face ɗinsa ba a gani yaushe
wata zata samu damar ɗanɗanar lips ɗinsa? Ai ba wannan magana, ita ce first and
last in ji zuciyarta. Lokaci guda ta saki cool murmushi, bargon sanyin ne ya
lulluɓe zuciyarta. Wayarta ta janyo tare da danna mashi kira. A daidai lokacin da
kiran ya shigo yana juyi a saman bed ɗinsa, dik yagama birkicewa ya fita a
hayyacinsa.

Wayar ta yi kara har ta katse bai ɗaga ba, sake kira ta yi, a karo na biyu ma bai
iya yin picking ba, sai a karo na uku ne ya miƙa hannunsa da kyar ya ɗauki wayar,
ba tare da duba mai kiran ba kawai ya yi picking, manna wayar a kunnesan ya yi ya
ƙasa iya yin magana. Daga can ɓangare ta saka mashi shagwaɓa tana faɗin. "My Hero
shi ne kaki picking da wuri?". Wani irin zoki bananarsa ta kara yi mashi ma jin
sautin muryarta, da kyar ya iya amsa mata da. "Am sorry my Hoonaira".

Zare eyeballs ɗinta ta yi kafin ta ce. "Ya naji voice ɗinka a haka? Ko dai ka
fara barci ne?". Ɗan datse idanunsa ya yi tare da girgiza kai irin wanda yake cikin
tsananin azabar nan, ya ɗan datse lips ɗinsa na kasa da hakwaransa, bai iya ce da
ita komai ba. Jin shiru yasa ta sake maimaita tambayar tata, a zatanta barci yake
yi.

Da kyar ya iya sake lips ɗinsa ya amsa mata da e barci ya fara yi. "To mu bar wayar
sai da safe ko?". Ta jefa mashi tambayar, ko kaɗan bai iya sanin amsar da bakinsa
ya bata ba, daga haka ya saki wayar ta cigaba da juyinsa dan nemawa kansa sassauci.
Ita ma cire wayar ta yi daga kunnenta tare da katse kiran, dan yadda ta ji ya ce
sai da safen ya yi mata kama da wanda barci ta rigada ta ci karfinsa, so bata tsaya
neman kiss na good night ba, gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike da tinanin kiss
da ya bata. Saboda gajiyar hanya yasa tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba
da ita. Tana yin barci bai fi da minti biyu ba sai ga guyson ya shigo cikin bedroom
ɗin ya zo nemanta...... Ganin tana barci ya sa ya matsa dab da ita, addu'oi ya tofa
mata kafin ya fice abinsa.

A ɓangaren Smart kuwa, yana barin bedroom na King ya wuce nasa, a gurguje ya yi
wanka ya yi shirin kwanciya, rufe kofarsa da key ya yi ma saboda kada su zo su
damesa, dan ya san Jaish zai zo, kuma yana kan tsini za'a iya samun matsala. Kuwa
hasashensa gaskiya ce, dan kuwa Jaish ya zo nemansa, sai dai da ya ji kofar a rufe
sai ya juya ya koma bedroom ɗinsa cike da damuwar menene yake damun ɗan uwan nasa.
A daren wannan rana dai kusan rabin family ba barcin daɗi suka yi ba, cike da kunci
da bakinciki wasu daga cikinsu suka kwana, har shi kansa King zuciyarsa tamkar zata
fashe haka ya kwana. Momma ma dai hakan ce, Jaish cike da damuwa da tinanin san
sanin abin da yake faruwa ya kwana, haka shi ma Jawad, abin dai sai shiru.

Washegari da safe, misalin karfe bakwai na safe, kiran gaggawa King ya aikawa da
kowani members na family da ya hallara a cikin main parlournsa, aikuwa basu ɓata
lokaci ba wajen hallara gabaɗayansu except Smart da kwata kwata ya ce ba zai sake
taka kafafunsa a in da daddynsa yake ba har sai ya canza magana, kada ku manta kuma
momma ta yi zazzafar magana a kan kada ya sake saka baki a kan bikin Auta, shiyasa
ya yi banza da kiran daddyn nasa, ya ga massage ɗin kuma, yana kwance saman bed
ɗinsa, wani ɓangare na zuciyarsa yana ta tinanin Pretty, dan da safe war haka a
France tana ɗakinsa ne tana damunsa da zata sha tea ya je ya bata, yau dik sai ya
ji babu daɗi da bata zo ta damesa ba, a ɗayan ɓangaren zuciyar tasa kuwa, bakinciki
ne tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu!!.

Gabaɗaya family sun haɗe a main parlour, har da su Mammie, kowa ya natsu tsit yana
jiran fara maganar King, Sarina burinta kawai taga Smart ya shigo cikin parlourn,
dan a yunwace take da san kallansa. Fanan sai satar kallan Jaish da ya yi ƙasa da
kansa yana tinanin zuwa ya duba Smart take yi, Khadijah and Zee suna part na Aunty
MieMie. While ita kuma Aunty MieMie ɗin tana nan a wajen meeting da za'ayi. Gyaran
murya King ya ɗan yi wanda ya janyo hankalin gabaɗayansu a kansa, natsuwa suka yi
tsit dan sauraran abin da zai faɗa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kalli Jawad da
Jaish ya fara magana a natse cikin bada umarni.
"Bakin Dubai sun sauka, ku shirya motocin zuwa tarbarsu a airport cikin
ƙanƙanin lokaci". Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan Auta dake zaune kusa da
Chuchu ta kwanto jininta, dama ba komai yasa ya tattara ƴaƴan nasa dikka ba face
yana san ne ya nuna masu cewa lallai ya isa da kowannensu, da alama kalaman Smart
na cewa watarana zasu bijirewa maganarsa ta tsaya mashi a rai, shiyasa yake san
kara nuna masu shi mai iko ne da su.
"Zunaira!". Ya ambaci sunanta. Da sauri ta ɗago daga jikin Chuchu, cike da
respect ta amsa da na'am dad. "Anjuma by 2 za'a ɗaura aurenki da yayanki
Abdussalam, shi ne taran jama'ar da kika gani a gidan nan, abin ya zo cikin gaggawa
ne, dan haka ki shirya". Ya kai karshen maganar tare da juyo da kallonsa a kan su
Momma. Da farko ya ce ba za'a faɗawa Auta ɗin ba sai an ɗaura auren, amma da Smart
ya yi mashi waɗan can kalaman sai ya ce bari ya sanar da ita ya gwada masu shi ke
da iko da su, kun gane irin abin ai?!!.

Wani irin zaro ido da Auta ta yi, tsabar rikicewa da shiga tashin hankali bata san
lokacin da ta zamo daga saman sofa ta zube gwiwowinta a kasa ba, a kiɗime ta fara
faɗin. "Dad Hoorain fa? Shi fa nike so dad, wlh Yah Abdussalam yayana ne kawai,
Momma ki faɗawa dad, Akka please ki faɗawa dad cewa Yah Abdussalam yayana ne kawai,
small dad ka faɗawa dad ina san Hoorain ka ji?". Cike da tashin hankali take
sambatun, ba komai ya girgizata har yasa ta fita hayyacinta ba face tasan King
magana ɗaya yake yi, yanzu ya rigada ya yi kenan, wannan abin yasa ta kusa zaucewa,
surutu kawai take yi ba tare da tasan me yake faɗe ba!.

Wani irin tsawa da King ya daka mata a kan ta natsun masa ne yasa bata san lokacin
da ta zabura ta miƙe ta faɗa jikin guyson tare da kankame shi gam ba. Cikin
kakkausar murya King ya ce. "Na rigada na gama magana, ƴan awanni kaɗan suka yi
saura!!".

Dik cikin parlourn nan babu wanda bai razana da ganin yadda King ya ɗauki zafi
sosai ba! Dayawa daga cikinsu sun tausayawa Auta, mussamman ma Chuchu da tini
hawaye sun gama jiƙe mata fuska, ita ma Fanan hawaye ya jiƙe eyelashes ɗinta
sharkaf saura su zubo, Aneesa ma dai idanunta sun yi jajir alamar ta tausayawa
sister tata.

Cikin kiɗimawa Auta ta fara faɗin. "Daddy mutuwa zan yi idan har ka aura mun Yah
Abdussalam, wlh nasan zan mutu ne kawai, Yah Omar ka faɗawa daddy zan mutu". Ta
faɗa cikin wani irin murya mai tsananin rauni dake taɓa zuciya. Miƙewa tsaye King
ya yi, dik jikunnan dayawa daga cikinsu ya mutu, mussamman ma uncle Jahiz da yake
ganin kamar suna da ƴancin yin abin da suka ga dama, kun san shi ma renon masu
jajayen kunnuwa ne, so sai yake ganin kamar King ya tauye mata hakkinta ne. King
kuwa ya fusata sosai, sai yake ganin ja in ja da shi da Auta ta fara yin nan kamar
zancen Smart ne ya fara tabbata, nan fa hankalinsa ya yi mummunar tashi!.

"Hoorain kike so ba?". King ya faɗa murya ƙasa ƙasa. Da sauri ta fara gyaɗa
mashi kai alamar e shi take so, take su momma suka fara jin daɗi har da sauke
ajiyar zuciya, dan suna ganin kamar zai aminta da batun ne.......... "Tabbas ba zan
hanaki aurensa ba, tin da shi kike so to bismilla gaki ga shi". Wani irin daɗi da
ta ji har bata san lokacin da ta zabura ta raba jikinta da na guyson ba, sai dai
kalaman King na karshe sun sa ta ji tamkar duniya ya tsaya mata cak, gabaɗaya brain
ɗinta ya dai'na iya tariyo mata komai, cak ta yi na wucin gadin..

"Tin da Hoonaira kika zaɓa tashi ki je garesa, amma kuma ki shafeni a babin
rayuwarki, ki cireni daga matsayin mahaifinki, ki kaddara baki taɓa sanina ba, nima
na cireki daga jerin ƴaƴana, ki nemi wani uban, Obaid shi ne ɗan Auta na a yanzu,
Zunaira ta mutu a rayuwata!!". Su ne kalaman da suka gigita ƙwaƙwalwar dik wanda
yake cikin parlourn, dan kuwa babu wanda ya taɓa tinanin King zai tsani Hoorain har
haka, ita kam Akka ko a jikinta, dan ita ce ma ta kara takawa King birki a kan
batun, bai yanke hukunci ba sai da suka yi zama da ita da uncle Abbas, a nan ne fa
ta ce wlh ba zata taɓa yarda Zunaira ta auri warrior ba, dan haka bata aminta ba,
wannan dalilin yasa shi ma King ya kara tsananta a kan hukuncinsa. Amma my people's
baku ganin kamar irin wanna tsana da King ya yi wa Hoorain akwai wata dalili mai
karfi a ƙasa kuwa? Anya iya kasamcewarsa warrior ne yasa ya yi mashi mummunar tsana
haka? Kai ina zargin da wata ƙullalliya a ƙasa.

(Ni dai a nawa tinanin fa to kada ku ɗauka gaske ne, a nawa hasashen na ce
Allah yasa ba shi ne uban Hoorain ɗin ba😅 dan kun san sarakuna suna iya tarewa da
kuyangunsu, matar commander Zafar kuma kuyangarsu ce, balai'n can, wannan fa
hasashena ne, dan ina ganin akwai dalili kai karfi na tsanar wanna haɗi da King ya
yi, amma ku kai dubanku kan yadda Hoorain tun tasowarsa fuskarsa a rufe bata
bayyana ga kowa ba zaku gane dalilin hasashena!! Me dalili rufe fuskar? Meyasa King
bai damu da ya buɗe fuskarsa ba? Kai akwai fa bala'i!!! Amma mu je zuwa bayan
bikin!!! King fa hege ne😅😅😅 ba dai ruwana na yi shiru sirikina ne kada ya hana
aurenmu da guyson nima in shiga uku!!🥱)

Ai tsabar tashin hankali Jaish da Jawad basu san time da suka miƙe tsaye a tare ba,
uncle Jahiz uncle Abbas uncle Taheer suma a tare suka miƙe, kalaman King ya
gigitasu. Momma kam ta kasa motsawa daga in da take, guyson ma dai ya kasa motsawar
ne, dan ya ji abin da ya girmawa shekarunsa. Dik rashin kunyar Omaid and Obaid sai
da suka ji zuciyarsu ta raunata a yau, Aunty MieMie tamkar wadda ruwa ya cinyeta.

Cike da tsananin tashin hankali da kiɗima Auta ta zabura ta diro ƙasa, ai tsabar
ruɗu bata san lokacin da ta isa gaban King ba. Tana kuka tamkar ranta zai fita ta
riko alkyabbarsa, muryarta da kyar yake fita ta fara faɗin. "Na shaga uku na boni
na lallace, wlh daddy bana san Hoorain, ka fiye mun kowa da komai a rayuwata, kai
ne sanadiyar zuwata duniya da har na san daɗi da rashinsa, ka yafe mun daddy, wlh
ba zan sake yin maganar kowa ba sai na Yah Abdussalam, shi ne zaɓinka kuma zaɓina,
na karɓesa hannu bibbiyu ina mai biyayya, daddy tin da nike da kai ko magana cikin
ɗaga murya baka taɓa yi mun ba, amma a dalilin wannan magana har marina ka yi,
tabbas ko zan rasa rai'na ba zan sake kaucewa maganarka ba, dan Allah ka yi hakuri
ka yafe mun, wanenen Hoorain? Ban san shi ba daddy, momma ku faɗawa daddy ko zan
mutu na yarda zan zauna da Yah Abdussalam, Mummy, mama, Yah Jaish, Yah Jawad, Aunty
MieMie, daddy, small dad, Yah Omar, Yah Omaid ku faɗawa dad ba zan sake ba, ya
janye kalamansa a kai'na, na shiga uku na lallace yau!.........". Da kyar ta iya
kai karshen maganar, a wannan gaɓa kusan dikkansu idanunsu sai da ya ciko da
kwallah. Guyson, Chuchu da Aneesa kam hawaye sharɓa sharɓa. Jawad yana san zuwa ya
ɗagota, amma kuma bai isa ba, saboda tsarin gidan sarauta, in har ba King ne ya
basu umarni ba to fa ko mutuwa take yi a wajen haka zasu daure su bita da ido.

Ban da sambatunta da shesshekar kuka babu wani abin da zaku ji yana tashi a cikin
parlon, King yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa yana jinta, ƙoƙari yake yi ya
danni zuciyar Modarawar, dan fa ya hasala matuƙar. Ganin kukan nata ya yi yawa,
tamkar zata rasa ranta yasa Queen mother ta miƙe ta isa wajen, dan bayan Akka babu
wanda ya isa ya tsoma baki a cikin wanna case ɗin ba tare da izini ba. Hannu tasa
ta ɗago Zunaira, cike da sigar rarrashi ta ce. "Ya isa haka, shikenan ki yi
shiru"....... A birkice ta fara tattaɓa hannun Akka tana faɗin. "Akka dad bai yafe
mun ba, yaki ya yi mun magana, dan Allah Akka ki ce mashi kome yake so shi
zan". ......... Hannu Akka tasa ta rufe mata baki. "Ya isa haka, ya yafe maki, Ke
Rahilarh zo ki kamata ku je". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kan
Momma......... UHM KING A KAN YA NUNAWA SMART YANA DA IKO DA ƳAƳANSA ZAI KASHE
AUTA!! WLH SMART ƊAN DUNIYA NE, DA KALMA ƊAYA TAK YA TARWATSA ZUCIYAR KING YASA YA
KUSA ZAUCEWA!!

Ai tin bata gama rufe baki ba Jaish ya matsa ya ɗauketa cak, cikin sauri ya juya ya
fice da ita daga cikin parlon, sai yan zu ya fahimci ɓacin ran Smart, ashe abin da
yake faruwa kenan........ "Dikkanku ku tashi ku je". Cewar Akka kenan, ta ce da su
mummy su tafi. Ai a hanzarce dik suka miƙe suka fita, wannan ya zama izina ga su
Aneesa, dama abin da yasa King ya tarosu kenan, dan ya zama izini a garesu, sun
kuwa tsorata ba kaɗan ba, dan sai da suka zub da kwallah, dikkansu addu'a suke yi a
kan kada Allah ya ɗora masu san wani bare face zaɓin mahaifinsu.

Da kyar suka shawo kan King ya hakura, sannan ya wuce fada dan tarban manya manyan
baki, Abu Abdussalam da kansa ya tako har KINGDOM OF POWER ya zo wanna ɗaurin aure,
abokan Abdussalam tawaga guda suma sun iso yau, abubuwa dai babu kama hannun yaro.
Ita kuwa Auta tin da ta yi shiru ta dakata da wannan kuka ba wanda ya sake jin
bakinta ta furta wani abin, ta zama ganganji kawai, dan ainahin ruhinta yana tare
da Hoorain, Allah sarki yana can bai san me yake faruwa ba, da safe ya yi ta
kiranta almost 10 miss calls bata ɗaga ba, dik ya bi ya shiga damuwa, amma haka ya
yi shirinsa sosai, dan yau gidan ya kara cika, tsaro zai tsananta a kingdom ɗin, ga
kuma baƙi, dole ya shirya ya fita da wuri, amma ya so ya yi waya da ita dan ya bata
hakuri a kan abin da ya faru jiya, amma ba dama, haka ya shirya suka nufi
masallacin King dan tabbatar da tsaron rayuka, sai tsokanarsa su Ansar suke yi a
kan ya kara kiba, sai dai shi gabaɗaya tin da ya tashi baya cikin mood mai kyau,
sai ya ɗauki abin a matsayin ko halin da ya shiga daren jiya ne silar mutuwar
jikinsa, dan gaskiya bai taɓa shiga yanayi irin na jiyan nan ba, da ace lokacin da
yake juyin nan ta zo kansa tsab zai iya yi mata fyaɗe, dan gabaɗaya a out of
control yake!.

In short a yau da misalin karfe biyu na rana dai'dai bayan saukowa daga sallar
azahar ne dubban jama'a suka shaida da ɗaure auren ABDUSSALAM OMAR BADEEN tare da
amaryarsa PRINCESS ZUNAIRA ZUHAIR ABDUL MALIK a kan sadaki na zallar zinari da ya
haura darajar 100 million, kowa ya shaida wannan ɗauri aure da aka yi da misali
karfe biyu dai'dai, jama'a sai murna suke yi, tabbas Momma ta yi murnar da ya
kasance ɗan yayanta Auta ta aura, amma tawani ɓangaren ta yi tsananin bakincikin da
ya kasance ƴarta bata samu zaɓin ranta ba. Ƴan uwa sai murna suke yi, yau King ya
yi kyaututtukan da bai taɓa yin makamantansu ba, uncle Abbas, Uncle Jahiz dik sun
yi tarin kyaututtukan da baki ba zai iya faɗarsu ba, duniya ta amsa da wannan biki,
jikokin the most powerful King Badeen sun mallaki juna, ƴan uwa sun yi matuƙar
murna ban da guyson da shi yasan komai. Shi kuwa Smart yana cikin bedroom tun da
Momma ta yi wannan furuci shikenan bai sake fita ko parlour ba, a cikin bedroom
ɗinsa yake sallah, tsawon sati ya ɗauka yana ƙoƙarin danne zuciyarsa a kan iyayen
nasa, shiyasa ma yaki fitowa, dan yasan idan har zuciyarsa bata kwanta ba ya fito
to fa zai iya tabka babban aiki, zaman sa lafiya ya zauna a ɗaki kada ya ja
zuciyarsa ta ɓatawa momma rai!.

Hidima ta kara tsauri, sai kai komo ake yi, manyan baki daga sassan duniya daban
daban sun halatta, harda manyan sarakuna daga Nigeria, masu mulki da sauransu,
almost good one week aka ɗauka anata shagulgula, ita dai Auta ta zama tamkar kurma,
bata uhm bata uhum-uhum, tazama abar tausayi, dik yadda aka jata haka take bi, taki
furta ko word ɗaya. Hoorain ya yi kiran duniyar nan har ya gaji, sai ya ce ko dai
shagalin biki ne ya yi mata yawa bari ya barta zuwa ɗan lokaci!!.

Yau za'ayi dinner, tin da su Aunty MieMie suka fara shiryata take zaune shiru bata
ce ko mai ba, Allah ne kaɗai yasan me yake a cikin zuciyarta.... Anyi aladun
larabawa daban daban wanda ya shafi girma da sarauta, anyi al'adar Henna Night wato
laylat al-henna. Wannan rana ce na farinciki inda ake taruwa dan sawa amarya
albarka, ana waka, rawa da annashuwa. Family mata da ƙawayen amarya ne ke halarta.
Ana yawan amfani da garwashi da turaren wuta, da wake-waken larabawa da duma-duma.
Sai dai dik Auta binsu kawai take yi, bata yi ko magana ba, da alama zuciyarta ya
rigada ya mutu, gangar jikinta ce kawai ta rage tana motsawa!.

Bayan Henna night sun yi Zafaf. Ana nuna dukiya ta amarya, riguna masu kyau, kayan
ado, turare, da kayan ɗaki masu ƙyalli. Wannan yakan zama wani biki daban, ana
gayyatar mutane su zo su kalla. Familyn King suna ajiye wa amarya and ango manyan
gift boxes masu shaƙe da zinari da lu'u-lu'u dan ɗaukaka amarya su nuna girma ta
family ɗinsu. Dik kafin dinner suka yi wannan fa. Bayan ankammala shi ranar
Saturday da daddare sun yi Gaisuwa da Karramawar Sarauta. Ana gudanar da gaisuwar
sarauta tare da masu manyan cikin gida, ƴan majalisar sarauta, da jakadu daga
ƙasashe daban-daban. Kamar yadda manyan sarakuna da shuwagabannin suka zo daga
Nigeria, to amarya da ango zasu je har fada su gaisa da su!. Su kuma zasu gabatar
da kyaututtuka daga sarkin garin, ministoci, da shugabanni zuwa ga amarya da ango.
Sai dai nan ma Auta

Please Login or Register in order to submit comment