ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

him and please him, in sha Allah bazata tabayin abinda zaisa yasaketa ba, In Allah ya yarda ta shigo kenan, ta yunkura ta dafa bango ahankali tana tashi daga kasa, da kyar tabude kofa tafito daga dakin, Mommy ta hango zaune nan falon sama tai shiga na alfarma tana wani mahaukacin kamshi ga jarida a hannunta tana budewa tana sipping tea, da sauri ta gyara riganta Mommy ta kalli PA ta dake tsaye gefenta batare datai magana ba hakan yasa tazo da sauri da taimakonta suka karasa inda Mom take zaune, har shakkan Mom take sabida yanda kana ganin matan kasan ba kanwan lasa bace, ahankali tace  good morning Ma awulakance Momy tace  take her away tai wanka tai breakfast anjima tafito wajen shakatawa damu PA"

tace  yes Ma

"Ficewa sukayi, yarinyar na ganin ikon Allah, haka masu kudi ke rayuwa,"

"kaman irin she s just robot din dansu din nan, Momy tadan jima awajen sannan ta mike tsaye tai murmushi ta tashi tawuce tafita daga dakin."

"Wuraren karfe 3:00 na rana ya bude idanunshi kanshi na bugawa, da"

"kyar yatashi yazauna yana yatsine fuska chan yadauki wayanshi yashiga camera yafara hoto ba riga ajikinsa, he looks super hot da idanunshi dake nuna yanzu yatashi daga bacci, lips dinshi sun kara pink sosai dan idan yadansha abubuwa haka suke kara pink yir ba baki ba, shi kanshi yasan yanada kyau, yadaura hoton a IG story sannan ya ijiye wayan yasauka daga gadon yanabin boxer nashi da abubuwanshi da kallo dake kada yafada bayi, wanka yayi yafito yashiga closet nashi ya chanza kaya ya shimfida dadduma anan yayi salloli tundaga na asuba sannan yatashi sabida ciwon kai na hangover yasa yau baiyi training ba, flip flops fari yasaka yashiga saukowa kasa yana dandanna wayanshi looking relaxed and happy, sauka kasa yayi yafita daga dakin"

"sai gaidashi ake wanda yayima ke bata baki dan hankalinsa nakan wayan,"

"yana fitowa yan aiki suka shiga dan gyarawa, yataho ta wajajen falon"

"Momy daya gani tareda Noor dake ta bayanta akujera tana rawa saikuma ga wata yarinya tana sanye da hadaddiyar atampa mai kyau zaune looking uncomfortable but still okay, jin kamshin turarensa yasa Noor tazo da gudu tace  Dadyyyyyyy, My Daddy da gudu tai wajenshi tai tsalle ya dauketa yana mata kiss a kumatu yace  my princess dasauri tace  Dady kaga Momy tahanani zuwa wajenka ko dasauri yace  don t mind your old grandma din nan Noor ta kwashe da dariya tana jin dadi, Momy tace  zakici gidanku fitsararriya zuwa yayi ya zauna kusada Momy dake musu murmushi tace  akawomai abinci ? yatsine fuska yayi yadan shafa kai yace  Coffee first Mom banjin yunwa sosai yarinyar ke kallonshi har abin yasa yaji ajikinsa ana kallonsa yadan dago karaf suka hada idanu dasauri tace  barka da tashi ina yini hade giran sama dana kasa yayi sannan yakalli Mommy"

da zuciya daya yace  who is she Mom?

Dan murmushi Momy tayi daidai an kawo tray abinci tadauki Coffee

"tamikamai ya karba Momy tace  she s Minal, she s among mata hudun da aka aurama jiya, she s the one you shared night with tabe baki yayi yakai coffee baki yayi sipping kadan he knew he spend the night with wata jiya but wlh baisan wacece ba, yarinyar dake zaune gwanin ban tausayi duk taji wani iri, wannan wani kalan family ne da she doesn t even know how to describe them, ko kadan basusan darajan dan Adam ba, tea yasake sipping yace  Momy can she excuse us dasauri Momy tace  tashi kifita takalli PA tace  take her back to her room yes Ma ta amsa tai wajen yarinyar tace  tashi muje gyadamata kai Minal tayi tana kara satan kallon Khaleel dake sipping tea yana kallon wayanshi yana dan murmushi suka fice, Momy ta shafamai kumatu cikeda so tace  Khaleel are you happy? Gyadamata kai yayi hankalinsa nakan wayansa, anatse Momy tace  to"

"Alhamdulillah ijiye wayan yayi Noor tace  Dady I want your coffee murmushi yayi yace  is hot Princess yadebo a spoon kadan yakai bakinta tasha tana tabe baki tana sha, Momy kuma tana kallon yanda"

Noor ke tayashi shan coffee tana tabe fuska tana sha still tace  kai wannan yarinya da kwadayi gwalo tama Momy tace  I will call my Fairy Angel Anty to catch you dan dariya Mom tayi da sauri Noor ta

sauka daga jikin Khaleel tace  Dady ai Fairy Angel Anty nada karfi

"ko, Grandma kinga the bad man wanted to hit my Dady, shine FAA ta"

"pushing My Dady and hit the bad guy with leg like this ta shiga gwadawa Khaleel yayi shiru yana kallon Noor kaman mai tuna wani abu, Momy tace  oh ni Noor menene kuma FAA ? Dasauri tai tsalle tace  Fairy Angel Anty Grandma tashi Khaleel yayi yace  Noor stay with grandma zan fita da sauri takama hannunshi kaman zatai kuka tace  Dad zaka kaini gidansu Lulu nima ? Dan tsayawa yayi yay jimmm yana kallonta dan baiso tamai fita kuka, ashagwabe tace  Dadyyyyy dasauri ya tsugunna yace  okay but that s gonna be tomorrow or next, I have somewhere to be now, is that okay Princess? Good gurl gyadamai kai tayi ya manna mata kiss sannan yatashi yayi kofa ana budemai Momy tace  have fun Khaleely ficewa yayi zuwa wajen wata Rolls Royce fara aka budemai ya shiga baya aka maida kofan aka rufe driver yaja motan security nashi daya agaba daya abaya suka fice sai"

motocin mopol daya agaba daya a bayansu tasa a tsakiya.

EPISODE 15

Tunda tai wanka tadawo daki tai salla batabar kan dadduma ba haka

bacci yayi awon gaba da ita.

**

Around 4 cikin bacci ta shiga juyi agado tanadan kankame filon dake

"gadon saikuma chan afirgice ta tashi zaune cikin muryan da baya fita da kyau sabida bacci tace  hasbunallahu wa ni imal wakeel wayanta ta shiga tattaba gadon tana nema chan ta juyoshi da sauri ta dauka ta kunna flash dakin yayi haske ta ijiye wayan akan gadon sannan takama cikinta tarike tana kankame idanu, kusan 3minutes tayi ahaka sannan ta dago filo ta dauka ta daura kan cikinta tarike saikuma ta kwanta da kyar tana kallon silin dakin chan kuma saita mirgina tahau kan filon tana kulle idanunta tana sauke ijiyan zuciya saikuma takara tashi zaune da rarrafe ta sauka daga kan gadon ta duka tana kife kanta akan gado chan tasake tashi tana layi tashiga tafiya atsakar dakin kafin tasake dawowa tahau gadon ta kwanta akan filo ta mika hannunta tadauki wayanta kiran Samsung S20 Ultra tabude number datai saving da best ta shiga kira wayan na gab da katsewa aka daga cikin"

muryan bacci Ni ima tace  Best ahankali cikin muryan da baya fita

"sosai Hawwa tace  Best na shiga uku, yauma yadawomin abin ke"

"kadaine? Da sauri Ni ima ta kalli Aliyu dake bacci a gefenta saita tashi da sauri tawuce tafita daga dakin tana maida kofa tarufe tawuce falo ta zauna batare data kunna wuta ba tace  gani nan nashigo falo, don t worry Baban Yaseer na bacci, Best this week alone this is the 2nd time da sha awa ke tadaki daga bacci, ina maganin dana baki ?"

"Kaman zatai kuka tai wahalallen tsuki tace  na shanye ahankali har wani fiffizgewa jikin Hawwa keyi tsigan jikinta na tashi tace  mezanyi yadena Best? Cikina har ciwo yakemin dasauri Ni ima tace  sannu kinji Best shan kanwa is not good for mata dasu lemon tsami, just ki daure kije ki watsa ruwa mai sanyi sosai zaki warware kinji, Allah yakawo miki miji duk ki huta da wahalan nan, jeki watsa ruwan sanyi ahankali Hawwa tace  okay ta katse wayan, zare wayan Ni ima tayi daga kunne daidai nan ana kunna wutan falon da sauri tajuyo hada idanu tayi da Aliyu dagashi sai gajeren wando yana kallonta cikin idanu da dan damuwa kan fuskanshi yace  what is wrong with Hawwa? Dan kallon mijin nata Ni ima tayi saikuma ta tashi daga kan kujeran ahankali ta taho wajen dayake da dan sanyin jiki tace  just girls problem ne Husby sorry na tadaka daga bacci muje mu kwanta tai maganan zata wuceshi ta shiga bedroom nasu taji ya damki hannun bata ankara ba taji ya fizgota da karfi zuwa gabanshi har saida wayanta yafadi akasa ya daka mata tsawan gaske kaman ba Baban Yaseer ba yace  tell me meke damun Hawwa? Ayanda Ni ima ta firgita batasan sanda bakinta yace  sha& & ..sh& .sha awa ne Husby, Uhmm daman ina bata magani so yakare shine yau take wahala dan lumshe idanu Baban Yaseer yayi yadan sauke ijiyan zuciya, adan rude Ni ima tace  what s wrong Baby ko bakada lafiya ne? Takai hannunta zata taba wuyanshi hannunta yakama batare daya bari ta tabashi ba kawai ya jata ciki zuwa gado rikice mata yayi saida aka fara kiran salla ya barta ya sauka yawuce bayi tabishi da kallo kaman akwai abinda ke damun Aliyu har yau takasa ganewa, tashi tayi tana kallon wayanta dayake kasa chan sai gashi yafito wayan nata ya kalla dake kasa karasawa wajen yayi yaduka yasa hannu yadauki wayan yaduba ganin wayan is fine yasa yamike yataho wajen gadon datake tsaye yamika mata wayan tareda mata murmushi yace  tashi kije kiyi wanka kiyi salla, anjima sai muje mu gaidata ko tareda su Yaseer ?"

"Gyadamai kai tayi asanyayye tasa hannu ta karba wayan, hannunshi"

yakai yashafa kumatunta ahankali yace  Ni ima kallonshi tayi

asanyaye daukanta yayi yay gaban bayi da ita ya sauketa yace  go and

shower shikuma yajuya ya shirya yasa jallabiya yafice.

Hawwa na fitowa daga bayi taci karo dawata wata mata da tadan

"manyanta rike da buta a hannu ga asuwaki a bakinta tsaye dab da bayin tana mata wani kalan kallo dasauri Hawwa ta dauke kanta cikeda dan kunya dajin nauyi danta daura towel akanta tace  ina kwana Umma mugun kallo Umma ta watsamata ta juya ta tofar da ruwan asuwakin bakinta a wajen tace  anje anyi abinda aka sabayi tohh Allah kyauta tir da wannan hali dudda Hawwa tajita bata bata amsaba tawuce dakinta ta shiga da basket din sabulunta da soso dakin ta ijiye taje gaban mirror taja dan stool ta zauna tana kallon kanta dake daure da dankwali da duk ya jike zare dankwalin tayi ta ijiye gashin kanta ya zubo sannan tadauki abubuwan face nata tafara shafawa kafin ta shafa cream ajikinta ta feffesa turare sannan tawuce tabude sip tadauki wani simple gown tasaka lokacin an fara kiraye kirayen salla, shanya zanin da towel data cire tayi a kofa sannan tasa hijabi tahau kan"

dadduma.

Tana kan dadduman nan har gari yawaye sannan ta tashi tazauna tana

"duba hannunta da har yasoma warkewa tai shiru she s just happy yau bazata aiki ba DIG yabasu off taga message din a group dinsu na watsapp, kwanciya tayi agadon tadauki wayanta ta danna tana kallon hoton dake jikin screen dinta da wata yarinya ce dake kama da ita ahankali tace  I miss you Mims tashi tayi tafara gyara dakinta da babu datti tafito da sharan waje sannan tafara share tsakar gidan lekowa daga kitchen Umma tayi ganin itane yasa taja tsaki takoma cikin kitchen din abinta."

"Tana cikin sharan Baba yashigo gidan da sallama using crutches dinshi dukawa tayi gabanshi tace  ina kwana Baba binta yayi da kallo kaman mai nazarin wani abu sai chan yace  kin tashi lafiya, yau babu aikin naki ne ? Kanta na kasa tace  ance muhuta yau sabida operation damukayi shiru yasakeyi kawai kallonta yake chan yace  muga hannun ahankali ta dago kanta for the first time ta kalleshi da dan masifa Baba yace  kina kallona Baban Yaseer ya sanar dani kinji ciwo a hannu wajen aiki, tashi ki nunamin in gani ahankali ta"

"mike tsaye daidai lokacin Umma na lekowa daga cikin kitchen tahaderai,"

dan jan hannun dogon riganta tayi tanunamai ciwon wanda yake small

"cut, matse crutches nasa Baba yayi a hammata yakai hannunshi ahankali yakamata hannunta dan boyayyen ijiyan zuciya Hawwa ta sauke rabon da Baba yarike hannunta tun tana secondary school, kallon fuskanshi take, cikeda so dan damuwa Baba yace  bakince ke a office ko a mota kike aiki ba meyakai har kikaji ciwo haka iyye? Idan wani abu yasameki fa iyye Hawwa ? Baba yayi maganan yana dago kanshi yana kallon fuskanta, maida kanta kasa tayi batai magana ba, ahankali yasa hannunshi yadawo da hannun riganta yarufe yace  ai shikenan, Allah baki lafiya, zansaka Auwallu ya karbo mini maganan hausa saiki shafa awajen kinji ko ? Ahankali tace  to Baba nagode sakin hannunta yayi yace"

" gama sharan kizo falo muyi kari tare ahankali tace  toh yawuce ciki itakuma Umma takoma kitchen rai abace

Please Login or Register in order to submit comment