ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma harda Ammi, dukansu biyun basu yarda da itaba, just for peace Baba yadena kukan nan zata yarda tai shiru amman tai alkawari saita nunama su Baba waye Khaleel she will bring evidence and everything dan kome za ayi ayi she will never ever accept yaron Pops din nan amatsayin mijinta ba!.  Hawwa kinji abinda muke fada miki? Kallon Ammi tayi fuskanta ta share tass da bayan hannu ta kalli Baba tareda kakalo murmushin dole tace  naji shikenan na yarda babu komi wani kayataccen murmushi Baba yayi yana share fuskanshi sai kawai ya rungumeta kaman zai cinyeta yace  nagode Hawwa, banso na tursasaki kiyi abu, nagode dakika yarda sakinta yayi yace  cikin kudin sadakin nawa kike bukata nabaki inaso naba Ammin ki sauran asayo miki kome kikeso Ibrahim yace sati uku on 24th ne taron biki wani abu Hawwa taji ya tsayamata awuya amman dai ta gyadamusu kai Baba yace  zamu fara shirin biki wannan gwal din kuma nida Aminu zamuje banki gobe mu boyemiki, yanzu gayamin nawa kikeso a kudin? Ahankali tace  banson komi Baba kuyi abinda yadace inada dan kudi ai ni Baba"

yace  to shikenan zan dauki ko miliyan goma ne nasai miki filaye

kisami kaddara sauran kudin ayi kayan aure dasu da gara Ammi tace

 zanje Zaria jibi nadan shiryo nadawo saimu fara shirye shirye bakama hannun yaro afito da anko sabida kowa yasami dinki tunda lokaci ya kuro Hawwa kawai tai shiru tana kallon Baba da Ammi dake planning sosai zuciyanta na kuna tana durama Khaleel ashar kirjinta na radadi kaman zata kama da wuta cus tasan auren is nothing but a

game.

Har tai bacci tabarsu awajen planning bikinta Ammi da Baba suke wlh

"ko Baba ne amaryan sai haka. wuraren 3 na dare ta farka tareda taba wayanta tadan haska Ramla ne ke kusada ita tana bacci, sai Ammi a bakin gadon ta dayan edge din, kankame jikinta Hawwa tayi abin yataso mata what is wrong with her? She s on MP fa though tagama da asuban nan zatai wanka tafara salla, haushin kanta ta shiga ji sabida tunawa da yanda Ni ima use this feelings against her, iska ta fuzar ahankali ta zame ta sauka kasa sai kawai ta sulale ta kwanta akasan tiles din dakeda sanyi, kusan 20mins tana ahaka kafin yasoma lafawa bacci ya kwasheta anan wajen, cikin bacci taji ana kiran sunanta da sauri tabude ido Ammi ce ta kunna wutan dakin tace  badai Ramla ta turoki kika fado kasa ba? Danne kunyan datakeji tayi tace  Ammi nakan fado kasa haka wani zubin Ammi tace  ahh lallai sannu iyayen bacci mara kan gado, idan zaki wanka yanzu nasa ruwa a wuta bayau zaki fara salla ba? Gyadama Ammi kai tayi ta tashi tana cire kaya Ammi tahau dadduma ta kabbarta salla wucewa tayi tafice Ammi tajuyo wlh tunda ta farka Ammi ta farka sabida ijiyan zuciyan dataketa saukewa abinda yatasheta kenan, saikuma sauka datayi kasa aranta Ammi"

tace  kodai tama Baba magana ne ayi bikin next week akaita kawai .

Dawowa dakin tayi tazauna gaban madubi tana kallon kanta dayayi tsufa

"ahankali tace  anjima zanje saloon tuna zancen Baba ya auramata Khaleel sai kawai taji ranta yabaci kwafa tayi she has plan she will show Baba waye Khaleel she will get evidence, saita nunama yaron nan ita ba kalan sauran matan daya saba aure bane, she don t want him so bazata taba zaman auren nan ba, 3weeks is morethan enough for her to show Baba evidence kan waye Khaleel even if it means nemo all matan"

daya aura adah.

Wani simple riga da skirt tasaka tadauki dadduma ya shimfida itama

"tai salla suka idar ta gaida Ammi, Ammi tace  yajikin? Ahankali"

"tace  lpy lau murmushi tamata  zanje zaria nataho damai gyaran jiki, dakin chan da akasa tarkace Baba yace yau duk zaisa afitar dasu a gyara tsaf anan za a dinga tara abubuwan ki da za a siyo mai gyaran ta sauka anan, saikuma inaso ki gayamin wani kalan kayan kitchen kikeso? "

"Ita abinma dariya yadan bata sai kawai ta tashi tace  duk wanda kika saya Ammi, bari nai aikin office yau zani saloon gobe nakeso nakoma aiki Ammi tabita da kallo tace  okay "

"Wuraren 11 Baba yashigo yana kwalamata kira tana cikin shiryawa itada Ramla datace zata bita dasauri ta taho kofa, wani key mai kyau na benz yace  gashi mijinki ya aiko miki da motansa wai kidinga hawa naki har yanzu ba a gama gyarawa ba tai condemn key tadan harara kadan tace  da keke zamu ai Baba ba nisa saloon din sarai yasan halin yarsa watsamata mugun kallo yayi yace  mijinki yabada umarni kihau tasa motar ke kice keke zaki hau? Hawwa kinsan hukuncin wacce batama mijinta biyayya tarbiyan dana miki kenan? Wlh zan cimiki mutunci fa Kaman zata kurma ihu ta hadiye abu awuya tasa hannu ta amsa tace  yakuri murmushi Baba yamata yace  ko Kefa yar albarka"

"yanada kyau mata tadinga bin umarnin miji tafi ganin haske arayuwanta komawa ciki Hawwa tayi ta zauna turus akan gado ranta dukya baci Ammi tace  uwarfada tashi kuwuce kutafi kafin na sabamiki mikewa tayi ahankali tadauki black veil na abaya dake jikinta dogo mai kyau ta daura aka tadauki wayanta da handbag Ramla ta fesa turare sannan suka fito, motar na kofar gida wata mahaukaciyan 2024 Benz ce grey, ga ledojin duk ajikin car seats din daga gani kasan sabuwa ce motar har kyalli take, Baba yace  kunfito wuce kutafi sake hadiye abu tayi awuyanta tawuce Ramla tabita taje zata bude motan tasake tsayawa"

"turus tadan kalli Baba ganin ita yake kallo yasa ahankali tabude motan ta shiga ahankali kaman bataso ta zauna Ramla ka tashigo tace  wowwww Ya Hawwa sabuwar mota ce kal wlh Ya Ibrahim naji dake mugun kallon da Hawwa tamata yasa taja bakinta tai gum, ganin taki tada motar yasa Baba yadaga murya yace  kuna jiran wani ne? Ko injin ya mutu ne azo aturaku ? Ahankali Hawwa ta tadamotan kaman bataso sannan taja motan ahankali sukabar anguwan motan dadi Ya Allah! Wato better thing money kill am, steering wheel din kaman oil sabida yanda yake juyuwa ta dadi ba irin nataba da kaman tana dambe ba, wayanta ne"

yashiga ringing tahau kan hanya batare tadauka idanunta kan hanya

takai wayan takai kunnenta batare data kallaba cikin murya mai dadi

"tace  hello strictly taji muryanshi that sounds kaman yanzu yake farkawa daga bacci yace  da permission din waye kika fita? Dawani irin sauri Hawwa tazare wayan daga kunnenta number ne kuma Truecaller ta bai fadamata waye ba kashe wayan tayi taidan tsaki ta ijiye Ramla ta kalleta ringing wayan yashiga yi taki kallon wayan ma Ramla tace  Ya Hawwa ana kiranki ahankali tace  share har sukakai saloon din kiranta yake, kashema wayan tayi daga baya gabaki daya suka shiga saloon din batason tai kitso kar kanta yayi ciwo kawai tsifa da wanke kan da blow drying shiko aka mata cikin 1hour aka gama tabiya kudi suka fito Khaleel tagani zaune kan bonnet na motanta yadaura kafa daya kan daya dagashi sai short na rick owens nude more like milk, da armani polo mai kyau maroon ga pcap akanshi milk shima dayamai kyau crocs ne akafanshi duk wanda zaiga Khaleel saiya juyo yakara kallonshi cus baimayi kama da Nigerians ba kaman irin black black American people din nan ma har yanda yake dressing, Ramla ta washe baki ganinshi tama wuce Ya Hawwa ta taho wajenshi da gudu tace  Ya Ibrahim ina yini kazo murmushi kadan yamata yace  Hi Ramla kema kinyi saloon da wanchan yarinyar nan ne ? Yanuna Hawwa dake tahowa sarai tajishi takuma shaka but ta daure sabida Ramla, akunyace Ramla tace  ni yau kwanan kitsona uku saisa banyiba, Ya Hawwa na rako kawai zuwa wajen Hawwa tayi azuciye zata wucesu tabude mota karaf taji an rike mata hannu kafin tai magana kawai Khaleel ya fizgota jikinshi da shegen zafin nama, kafin tasake magana taji hannunshi cikin nata ya karbe key motan ya wurgama Salman ya chabe yace  take"

"Ramla shopping then home Salam, I want to talk to my wife privately! Kawai ya kankame Hawwa ajikinshi yana turata baya kunya kawai yarufe Hawwa na masifa, ga Ramla data saki ido baki hanci tana kallon abinda Khaleel kemata, ga jama a, ga su securities dinshi, she had no"

"choice haka ya dinga turuwanmai har jikin motanshi yakaita yabude kofa yamata rumfa agabanta kaman zaiyi hugging nata yakalleta yace  get in zatai magana yace  i will kiss and touch you all over kikamin gardama! Runtse idanu Hawwa tayi ta tabbatar Ramla taji maganan wlh harsu Salman da kowama, kaman zata shige kasa, da kyar tabude idanunta Ramla tadan kalla dahar ta shige gaba abinta tana mata bye tana washe baki na murna da farinciki, da sauri kawai ta juya ta shige without saying a word, shima yashige yana rufo kofan"

motan yace  let s go Aharzuke Hawwa ta kalleshi tace  wai is

something wrong with you? How dare you touch me like that a public?

"Hannu yasa yazare pcap na kanshi yakalleta babu wasa kan fuskanshi yace  duk randa kika kara fita without kin sanar dani sai ranki yabaci I forgive this one but next one I won t tsayawa Hawwa tayi tana kallon ikon Allah abinma sai yasa tai dariyan takaici tace  ikon Rabbi! Auren da Baba yamin dakaine yasa kake wani takama kana feeling kaman u own me? Kallonta Khaleel yayi baice komiba hakan yasake pushing Hawwa to the wall, tace  guess wat nariga nama kaina alkawari before this 3weeks I will expose who you are to my family! I trust Baba da kanshi zai raba auren nan daya mana I will prove to them cewa you are nothing but a womanizer sai aure aure kaman ayu ga shaye shaye da party BfF din dujal, I m Hawwa! I can never settle for less! I want a man dayaci sunanshi man not yaro! I want a responsible man not Pops boy! I want a man that shoulder responsibilities not wanda ake shouldering responsibility shi! Ni da kai are two world apart trust me you need plenty years to get to world din danake, so forget kayi abin nan waishi daurin aure but Hawwa can never ever be yours wani juya idanu Khaleel yamata kaman zaiyi bacci yayi shiru chan yace  feel free! Do whatever you want!"

"Khaleel yariga ya sameki! Dudda kina chan world dinki but without stress na mika hannu na ciroki daga world din nakawoki my own world dakika tsana so much Kululuwa, matar dujal bff dasauri tawani yunkuro kaman zata dakeshi tace  nace kadaina kirana sunannan! Murmushi kadan yamata yace  to Yar Sanda! Wani irin runtse idanu tayi kaman zata dakeshi cus he s pushing her yayi murmushi kadan baice mata komi ba, afadace tace  ina zaka kaini? Ba hanyan gidanmu bane nan ba? Dan kanshi ya sosa yana kallonta kaman yanda take"

kallonshi murya chan ciki yace  we are going to hotel! Mummunan



gaban Hawwa yayi.EPISODE Gidan Mama Jin parking

"mota a kofar gida yasa Mama dake kokarin shanya zani a igiya tace  waye yazo duka duka ko awa daya cikakke Ni ima batayi da fita ba yo ko Aliyu ne ? Tana fadin haka tacire hannunta daga kan zanin datake kokarin shanyawa daga igiya tai wajen gate din nasu tana kokarin bude kofan aka turo Ni ima ke shigowa ga fararen uniform nata ajikinta sai abaya asama dayake abude, ga wani katon envelope a"

hannunta sai jaka da wayanta da car key a hannunta idanunta sunyi

"jajir ga ruwa ruwa ma kaman tai kuka, faduwa gaban Mama yayi rass"

"dasauri tace  lafiya naganki gida? Bayanzunan kika tafi aiki ba sai dare zaki dawo? Yanaga kaman kinyi kuka Meya faru ? Envelope din hannunta tadaura akan hannun Mama tawuce tazauna gaban dakalin dakinsu kawai tafashe da kuka mai ciwo da zafi, Mama ta kalleta saikuma hannunta yashiga rawa sosai ta bude envelope din da sauri ta zaro paper ciki ta yarda envelope din akasa ta iya karatu tadanyi makaranta bakinta har rawa yake tace  lICENCE REVOKED LETTER FRON NMCN takasa karanta surutun data gani sai kawai ta taho wajen Ni ima tace  ke meke faruwa fadamin bazan iya karatun nan ba tell me da kyar harshenta har karyewa yake tace  NMCN shine Nurses and midwifery council of Nigeria, sune suka aikomin da letter nan ta asibitin mu wai Leadway hospital sun turamusu video evidence of ni Nurse Ni ima nazo hospital ina threatening patient

Please Login or Register in order to submit comment