ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace  Mommy mezan zuba miki ko kinason wani abu daban na dafa miki  ? Atare duka kawayen Mom sukace  wowwww Hajiya Zee we want daughter in law like this oo dan murmushi kadan Mom tayi tace  samin moimoi da sauce Hawwa tadau plate mai kyau tasama Mom da nama ta ijiye gabanta tasamata spoon tace  Mommy zakici fruits na yanka miki naga kinason avocado harda shi sosai Mom ke kallon Hawwa saikuma tace  give me small sama Mom tayi sannan tabar wajen sai kawai ta shiga kitchen ta zauna kan kujera dake island din batasan wani daki zata shiga ba"

Kawayen suna fara yaban abincin Hawwa Mom ba yanda zatayi tana kai moimoi bakinta Ya Allah! Saida taji kunnenta yayi motsi sabida dadi this girl can cook like this? She has chef oo but akwai wani homely

and love taste da abincin Hawwa kedashi tass ta cinye ta kara saida

tac1 moimoi uku kawayenta sunci sukai nak Hajiya Hajara tace  Hajiya Zeenatu anya bazan kawo matar d ana Muhammadu tazo wajen matar danki ta koyi girki ba kuwa? Kinga har cooking school na sata but duk abanxa gaskiya matar danki ta iya girki wat! Please can I package this kofta naje dashi gida with this fresh juice murmushi sosai Mom tayi tace  sure sure haba sunci abinci sosai Mom was just feeling herself suka dawo falo suna hira saiga Hawwa tafito rike da tray na Bowl of ice cream da brownie Hajiya Shema tace  anya kinaso mu koma gidanmu kuwa Hajiya Zeenatu diyarki ta karyamin wait loss see standard dessert ice cream da brownie suka daddauka Hawwa taja stool ta ijiye gaban Mommy tawuce kitchen Mom ta kalli kawayenta tace ina zuwa

Kitchen tabiyo Hawwa tana rufe kofa dasauri Hawwa ta juyo cikeda masifa Mom tace  so kike ace na maida matar d ana yar aiki na? Kan Hawwa na kasa Mom tadan dafa goshinta tace  wat are you still doing in my side eh? Wuce kitafi nagaji da ganinki wlh Mom tana

maganan tafito tana murmushi.



EPISODE

Kofan kitchen Hawwa tayi tayi alwala anan pampo baya tashigo tafito

"tashiga dakin masu aiki tayi salla aciki tanaji kawayen Momy na tambayanta Mom na cewa ta kwanta taji sunce agaisheta please, tana nan cikin dakin kusan 10min saiga PA tazo dakin tace  Madam tace nakiraki tashi Hawwa tayi tafito kanta akasa Mom ta kalleta so take tarufeta da masifa but saitaji kuma takasa ba yabo ba fallasa tace  kinci abinci? Girgiza mata kai Hawwa tayi, cikeda masifa Mom tace  wuce kije kidiba kibarmin flat dina kitafi naki batai musu ba saitaje dinning din dahar an gyara tadauki karamin plate ta debi abinci kadan tasa spoon ta zauna takai bakinta wlh takasa ci, damuwa yamata yawa da bata iyacin abinci Mom takai kusan 3min tana kallonta, tadan sauke ijiyan zuciya tace  jiranki nake ki cinye abincin nan"

"kitashi ki bar bargarena dasauri tashiga cusama kanta abincin, sai"

kawai ta kware tafara tari dasauri Mom tace  give her water PA

"wucewa wajen PA tayi da sauri tasama Hawwa ruwa a cup tabata da sauri ta karba tasha Mom duktana kallonta, ita kawai tabarmata flat cus bamataso ganinta tazo tafara tausayinta danta farajin wani iri iri game da yarinyar itakuma tasan batason Hawwa ta tsaneta sabida abinda tama danta, ijiye cup din Hawwa tayi ta karasa dannama kanta abincin sannan tadauki plate din Mom tace  bama PA na plate din zatakai kitchen wuce kitafi ahankali Hawwa tabata ta taho tana tafiya kaman bataso tawuce kofa Mom na hararanta saikuma ta tsaya wajen kofan tadan juyo ta kalli Mom dasauri Mom tadauke kai tana tabe baki hakan yasa Hawwa tabude kofan tafita daidai Motan Noor na shigowa gidan tadawo daga school tun kafin ayi parking tafara ihu Hawwa ta tsaya Noor tafito ana parking tazo da gudun bala i kaman tai shekara bataga Hawwa ba tace  Mommy FAA Hawwa tabude mata hannu tawani rungumeta kawai Mom tabude kofa tace  saken mini yarinya, Princess come here sakin Noor Hawwa tayi Mom ta dauketa suka wuce ciki Noor nama Hawwa bye, Hawwa tawuce flat nata ahankali zuciyanta ba dadi."

"Tana zama taji ana sake bude gate dasauri ta daga labule ganin motan Khaleel ne sai kawai tawuce wajen kofa tabude kofan tafito tundaga mota Khaleel yake kallon Hawwa da tsabagen sauri bama ta yafa gyalenta tarufe kirjinta ba, kawai akanta gyalen yake, kirjinta duka abude kana ganin tundaga wuyanta har kasa tana tahowa dasauri, yashiga bin compound din da kallo ga few security nasu maza gashi atampan yamata kyau, dinkin yakamata, abu yaji ya tsayamai a wuya dasauri yarike, Salman na parking yafito batare daya jira an budemai kofan ba zai wuce, daidai Hawwa tasha gabanshi looking very emotional kawai tai hugging nashi chak Khaleel ya tsaya! Hawwa ta manna kirjinta a kirjinshi sosai ta manna fuskanta awuyanshi tace  Husbyyyyy please talk to me dan Allah, dan Allah cikin kakkausan murya Khaleel yakasa tureta yace  I will count three idan baki fita daga jikina ba saina fitar dake na yardaki I don t care muna outside! Wani iri kirjin Hawwa yayi jin upon all the boobs data manna mai a jiki did not work another kuka kawai taji yana taso mata, ahankali Khaleel yace  one! Two! Thr& .. fita daga jikinshi tayi da sauri tana komawa baya wlh wani tsoron Khaleel take! Baki tabude zatai magana tana sheshekan kuka Khaleel yawani daka mata tsawa.  I said go back to your room! Harwani gudu baya Hawwa tayi tana"

kallonshi sabida tsoro saikuma tajuya dasauri takoma side dinta

kirjin Khaleel na tafarfasa ganin yanda tabar kirjinta awaje ga maza

"a compound nasu tako ina mtsswww yajuyo yakalli Salamn da kanshi ke kasa yace  all of this security I don t want them here anymore su dinga tsayawa a second gate, I don t want men here that includes you unless na bukaci wani abu or i want to see someone dasauri Salman yace  yes Sir Khaleel yawuce flat nasu ranshi duk abace fuuu yashiga ciki Noor tazo da gudu tawani rungumeshi tace  Dady daukanta yayi yace  my princess have you eaten? I m taking you to islamiyya by 4 dasauri Mom tace  islamiyya kuma Khaleel? Batai karama da yawa ba she s just 4 fa kasan islamiyun nan dukan yara suke fa babu joy akan muryanshi yace  idan she s not too to start school she s not too small to start islamiyya, babu wanda zai dakanmin yarinya, princess kinason Islamiya? Dasauri Noor tace  yes even Mommy FAA once said zata tell Dady na yasani a islamiyya so I love islamiyya mommy ta harari Noor, Khaleel yadan kwanta akan kujera Mom tace muje kaci abinci girgiza mata kai yayi ahankali, cikeda damuwa sosai yace  Noor come here dasauri yarinyar tazo tanamai murmushi daukanta yayi yasa akirjinshi yarinyar ta kwanta ajikinshi lamooo murya chan kasa yace  Dady loves Noor so much murmushi tamai tace  Noor loves Dady too alot, and I love Momy FAA shiru Khaleel yayi wlh he s missing matarshi sosai kaman zai zare yana rikeda ita har saida Mom tace  saketa taje taci abinci Leely wucewa sukayi itada Mom sukaje dinning Mom na feeding nata, he s very very angry with Hawwa but he s missing her, he can t eat properly, ba daman ya zauna Tuna n1n ta ya addabeshi, this few days fight from dai ranan dayaje party nan feels like kaman yayi 100yrs suna fada, he s so lonely, he s so horny! He lost his sanity, but yama kanshi alkawarin nan kozai mutu bazai nemeta ba. Yana wajajen har lokacin as1r yatashi yatafi mosque yana dawowa yaga Noor zaune tasa hijabi murmushi yayi yakama hannunta yace  muje tabishi suka fice."

Wani babban makarantan islamiyya yakai Noor da kanshi na yaran yan gayu yabiya mata islamiyya da haddansu da akeyi Saturdays and Sundays 8-6 na yamma sannan yabarota awajen suka dawo gida driver ta will

bring her by 6.



EPISODE

Hawwa duk tana tsaye wajen window taga dawowan Khaleel yawuce side

"nasu, ahankali tasaki labule ta zauna, she s angry da kanta, she hates kanta, gawani mahaukacin son Khaleel datakeji da bata tabajin kalansa ada ba, like every single thing reminds her of him agidan nan nasu, tagumi tayi saikuma ta dauko Al Qur ani takaranta har isha i, ta tashi taje tayi wanka tafito ta shirya cikin wani short gown na bacci, tadauki wani vintage scarf blue ta daura dayamata wani shegen kyau, tazo tasake zama ita kadai, kawai rayuwa yamata zafi, duniya yamata zafi, wayan Ammi takira harya katse no answer, takira Baba shima yaki dauka kawai saita ijiye wayan hawaye suka gangaro mata daga idanu ta share da sauri, tashi tayi taje dakin Khaleel ta zauna tai shiru har shadaya tabuga tagumi sai kawai ta tashi tadawo dakinta wani navy blue hijab tadauka mai hula tasaka har kasa ta dauki wayanta kawai tasauko kasa tafito tawuce flat na Mommy, kaman barauniya tabude kofan gabanta na faduwa kar Mom takara kadota, luckily babu kowa a falon sai tv dake aiki ko ina a gyare tsaf tsaf, maida kofan tayi tarufe tashigo tana kallon ko ina wlh bama tasan inane dakin Noor ba, wani kalan gini ne ga sama ga kasa, ga bangare bangare, wajen kujera taje ahankali ta zauna tareda sauke ijiyan zuciya sanin akwai mutane anan sai taji hankalinta ya kwanta, ta kishingida a dogon kujera before kace me bacci yayi awon gaba da ita. Mommy na cikin video call da Excellency awaya wuraren 12 nadare akai knocking, daukan wayan tayi a hannu tace  common in bude kofa PA Mommy tayi tace  sorry to disturb you Ma Mom tace  No problem lafiya? Noor ta farka tana nemana ne? Dasauri PA tace  No Ma is"

about Mrs Hawwa dasauri Mom ta haderai tace  what about that girl ahankali PA tace  tana downstairs a falo tana bacci akan kujera cikeda masifa Mom ta juyo ta kalli Excellebcy awaya tace  you see

wat this girl is doing ko Alhaji haka yau tazo tadinga aiki salon ace ina wahalar da yar mutane mehaka wai? Dan murmushi Excellency yace

 common Zeenatu pity her mana yarinya tayi fada da mijinta yadawo

side naki bazata biyoshi ba taga ko zataci nasara akanshi wat if

"she s your daughter eh? Tunda they decided a side naki za ayi fadan itama yanda kika bar Khaleel yadawo wajenki itama ki bata daki tadawo nan, be just among your children Mom tace  bazata dawo flat dina ba akan wani dalili da tana zuwa ne? Murya chan kasa Excellency yace  Zeenahhhhhhh! Dan ijiyan zuciya ta sauke tace  okay okay ni naji tadan turo baki cikeda masifa tace  ina zuwa ijiye wayan tayi ta mike yafice daga dakin cikeda masifa PA na binta lift tashiga ta sauka kasa wlh da masifa tayi kan Hawwa but gannin ayanda Hawwa ke baccin awahale sai taji tabata tausayi idanunta duk sun kumbura sai kawai ta tsaya takama waist nata saikuma takalli PA tace  wake her up kibata daki daya PA tai patting chair wajen tana.  Mrs Khaleel! Mrs Khaleel& .. daidai Khaleel na fitowa daga side nashi cus ya kasa bacci ga bakin sha awa dake damunshi yaga Hawwa akan kujera tana bacci a wahale a zaune, baitaba tunanin zai ganta here around this time ba sai yadanyi slowing down, though baya kallon wajen but kunnenshi na wajen, PA tace  Madam Hawwa firgigit Hawwa tabude idanu takalleta saikuma taji kamshin turaren Khaleel dasauri ta juyo daidai Khaleel yakarasa saukowa daga side nashi sanye dawasu pajamas dark blue masu taushi, dawani kalan sauri kawai Hawwa takama hannun Mom tana kallon Khaleel dake tahowa, ko kunyan PA batajiba tana kallon Khaleel na tahowa tafashe ma Mom da kuka tace  Mommy dan Allah kiyakuri kisa ya saurareni, Mommy dan Allah kinji Mommy, Mommy dan girman Allah Khaleel kawai yawuce su abinshi yaje dinning ya zauna dan yunwa yahanashi bacci murya ciki ciki yace  Moma come and feed me dasauri Hawwa tasaki hannun Mom kawai tawuce wajen takai hannunta zata bude warmer wani kalan zabura Khaleel yayi kaman zai mata duka yace  wat are you doing here! Baya Hawwa tashigayi tsabagen firgita zata fadi karaf taji an riketa da sauri tajuyo Mom ce sai kawai takalli Khaleel ranta adan bace tace  mehaka wai? Da bana nan tafadi taji ciwo fa? Is okay to be angry but stop scaring her haba saikace zaka koma dodo takalli Hawwa tace  kema mekikeyi a side dina? Eh? Nace nagaji da ganinki wannan wani kalan bakin naci ne eh? Ohh ni Allah wani kalan yara kahadani dasu, wuce kitafi flat naki muryan Hawwa abala in sanyaye

Please Login or Register in order to submit comment