ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayanta ta dauka ta danna sai kawai ta shiga dial calls nata batada wani me kiranta banda Baba sai Ni ima ko yan aikinsu ba waya take dasu ba saita kama, dan fuzar da iska tayi tana shiga contact list she is just craving tasami wanda zasuyi hiran soyayya dashi like kowace"

"yammata wanda zai kira yaji muryanta yamata goodnight kafin tai bacci, watsapp ta shiga tashiga account na Ni ima tasan ta kwanta yanzu,"

"dan runtse idanu tayi ta ijiye wayan tajuya tareda kifa kanta a filo wlh wlh tanason aure, tana mugun so itama tai aure taje gidan mijinta tabar gidan mahaifinta but batada mijin, yazatayi shi wannan Kabir din baimata ba at all bazatama taba zama dashi ba, ahankali tace  Ya Allah kabani mijina nima, Ya Allah banso nakoma gareka banyi aure ba, nima inaso nai aure kaman kowace diya mace ta sauke ijiyan zuciya"

ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

"Koda ta farka da asuba taga miss calls na Kabiru Musa yafi sau goma,"

"wanka tayi tai brush dan yau akwai office, salla tayi tana zaune kan dadduma tayi azkar nata da karatun Qur ani har zuwa seven sannan ta tashi ta linke komi tazo gaban mirror tayi morning routine nata na skincare yau yawanci uniform sawa suke last Thursday of the month sabida suna meeting da ake kira da Intelligent Briefing, wanda harda chef of staff da manya manyan mutane na kasa dai, tundaga kan yan military da other security personnel, zama tayi tana kallon kayan makeup na gaban madubin Baba pressure her so much da yanzu gani take kaman ita mummuna ce batada kyau maybe saisa babu mai nemanta, hannunta tamika ahankali tadauki powder zata shafa a fuskanta saikuma ta ijiye, makeup bashine zaisa a sota ba, and abin will look somehow dan bata sabayi taje wajen aikiba, murya chan ciki tace  Ya Allah kasa wani yace yana sona, na burge wani awajen meeting din tadanyi murmushin kunya tadauki kwalli tasaka tasa lipgloss dayama lips nata kyau yafito baby pink yir abinshi, tawuce ta bude sip tana ciro uniform nata, singlet tafara sawa fari kafin tasaka rigan police din mai dogon hannu, daman akwai skin tight short one black datasa tazauna ta saka safa sannan tadauki dogon wandon uniform din tasa tayi zanzaro da rigan ciki tadauki bakin belt nasu ta saka kayan sun mata kyau bana wasaba, wandon nada fadi bai wani nunata sosai ba, bakin veil tadauka tai rolling akanta ta tura gyalen cikin riganta sannan tasake maida boturan rigan, tadauki boot nata tasaka baki dake shinning yaji shoe polish."

Komawa wajen madubi tayi ta feffesa turaruka sannan takara kallon kanta a madubi takoma baya tace  Hawwa kinyi kyau sannan tadauki handbag dinta ta tarkata yan tarkacen ta cikinsu tafito tarufe kofan dakinta tayi hanyan waje Baba na zaune a kofar gida yabita da kallo dukawa tayi tace  ina kwana Baba anatse yace  kintashi lpy ya hannunki ? Smiling tayi tace  dasauki  Alhaji Kabiru yace yanata kiranki baki dagawa mesa baki daga wayanshi ? Dauke kanta tayi tafara kokarin mikewa tace  bansan shi bane shiru Baba yayi yana kallonta saikuma yahade rai yace  idanba kinaso nayi mummunan sabamiki ba makesure kin kirashi sannan kidawo dawuri dan zaizo anjima da yamma ya ganki murya ciki ciki tace  to tawuce tadan

dudduba motanta tayi warming sannan taja motar tabar unguwan.

Parking motarta tayi tafito bayan tadauki duk abinda zata dauka

"tawuce ciki direct office din Hayatu tawuce knocking tayi tareda bude kofan yana cikin office din tareda Abraham duk suna sanye da uniform gani ta yasa Abraham yatashi da sauri yana murmushi yace  welcome back Miss Hawwa, how is your hand ? Smiling kadan tayi tace  fine ya jiki? Hope you guys are good ? Gyadamata kai dukansu sukayi saikuma tai shiru saikuma tajuya zata fita Hayatu yace  Miss Hawwa juyowa tayi ta kalleshi duk kallonta suke yace  kina bukatan wani abu ne? Dan shiru tayi kaman mai tunani sai kuma ta shigo office din da kyau tazo gabanshi ta tsaya tace  uhmm actually I kinda need your help dukanku biyun banda wanda zan tunkara sai ku Hayatu na kallonta yace  whatever you need we are here gyadamai kai Abraham yayi yace  yes Miss Hawwa cus bata taba zuwa da sunan tana neman su mata wani abuba, sakeyin jimm tayi sai chan tace  wani mutumi nakeso kudan tsoratamin shi ya rabu dani tasake shiru kaman maijin nauyin maganan dazata yi tace  arrhhhhh daga ta bangaren Babana yafito yanason ya aure ni and and& uhmm bana sonshi i just want him to leave me, so please can you scare him off ? Calmly Hayatu yace  we got you anatse Abraham yace  always! Give me his number ta track him dan murmushi tayi tabude wayanta tashiga kiramai number sannan tace  thank you guys tawuce tafito hankalinta ya kwanta office nata tashiga ta zauna tadan fara paper work, she needs to write detailed report na abinda yafaru a field takai office na DIG, karfe 10 suke shiga meeting din, 10 daidai akai knocking kofan office nata Abraham ne rike da two cup of coffee yashigo ciki ya ijiye daya agabanta yace  let s go mikewa tayi tadauki coffee din tace"

 thanks suka fito tare zuwa meeting din wanda 12 suke gamawa.

12:15 suka gama tafito DIG yace  meet me in my office gyadamai kai

tayi tace  yes sir tai discarding cup na coffee a trash na wajen

"tawuce Abraham yabita da kallo kawai yasan he doesn t stand a chance ne but Miss Hawwa na burgeshi, she will forever be his crush."

"Knocking kofan tayi aka bata izini ta shigo, DIG ne kadai a office"

din yana duba some files yasa glasses a idanu yace  yauwa Miss Hawwa saramai tayi tace  Sir ijiye file din yayi tareda zare glasses

dinsa yace  ease please sauke hannunta tayi yace  you solved that

case brilliantly Officer kudos dan murmushi kadan tayi tace  thank

"you Sir, you trained me after all murmushi yamata ba karya bane"

"yana alfahari da Hawwa in this task force yace  yanzuma I have another case for you kai tsaye tace  nakira su Hayatu ne Sir? Hannu ya girgixamata yace  no ke kadai sukai requesting for kallonshi tayi alamun bata gane meyake nufi ba, yace  I got a call from Excellency they can t find wani bodyguard nasu and they want you to look into it suna tunanin anyi kidnapping dinsa shima so they want you for the job kawai jitayi ranta yabaci gabanta kuma yafadi, tadai daure tana kallonshi batare datai magana ba, DIG yace  please kije and investigate, Hawwa bance kije kifara fada da yan gidanba, rayuwansu da namu ba dayaba, this people ba a Nigeria aka haifesu ba a kasan waje sukafi rayuwa so don t expect them to act like us, masu kudi basa tunani kaman yaku bayi irinmu, just do your work without interfering in affairs nasu, be professional about it and keep me posted, am I clear?  yes Sir Hawwa tafadi ranta ba dadi, hannu yakai aljihunshi yadan zaro kudi yan 1k kusan na 15k yace  gashi kisa fuel a car naki hannu tasa ta karba tace  thank you Sir kofa yanuna mata yace  zaki iya tafiya juyawa tayi tafice, babu yanda zatayi harkan police dama duk wani harka daya danganci hukuma ba ama Oga gardama koda yace ka fada cikin wuta ne dole you must obey, obey before complain yana daga cikin slogan nasu, office nata tawuce zama tayi kan kujera tareda dafekanta tadan fuzar da iska taja drawer tadauki wayanta da car key tamike tafito tawuce wajen motanta tabude tashiga taja tafita saida ko ta tsaya tasha fuel cus gidansu da nisa ahaka har takai gidan tsayar da motanta akayi security suka"

leko yace  Hello Miss wakike nema ? Anatse tace  DIG sent me here magana yashigayi awaya kusan 5min sannan yace  booth please booth tabude musu suka duba akai scanning motan sannan aka bude mata gate

"din da sauran gates din daidai tana shiga gidan kawai taji gabanta yafadi hakanan, wani arnen Lexus jeep tagani black a compound din tinted ga security awajen daidai yarufe back seat din yajuyo yanabin motan Hawwa da kallo, parking tayi itama tadan fuzar da iska tareda kashe motan ta kashe AC tadauki wayanta tana kokarin kiran DIG ta sanar dashi ta iso akai knocking glass na motan hakan yasa ta dagokai ganin security da uniform yasa ta sauke glass na window cikeda girmamawa yace  afternoon Ma am, Yallabai yace kishigo mota he will brief you aciki meeting gareshi and he s running late the thing is"

batasan Baban ne ko yaron ke nementa ba dudda tasan yawanci manyan

mutanen nan haka suke basuda time amman saita bisu yanzu haka?

"Motanta ta kalla hakan yasa security yace  you don t have to worry about motanki Ma am ko ina kike za a iya kawomiki kokuma adawo dake har nan kidauki motan ki wuce dan ijiyan zuciya ta sauke tace  okay hakanan she s feeling so uneasy, bude motan tayi security ya matsa gefe tadauki wayanta da jotter tanada pen makale a aljihu already ta maida kofan tarufe tamai key tasa key a aljihu, Salman sai kallonta yake baitaba ganin police mace da uniform yama kyau kaman itaba, she s damn beautiful, gashi tai rolling gyale akanta abinta sai tai kaman balarabiya, dan kallonshi tayi, cikeda good etiquette yanuna mata jeep nasu yace  after you Ma am gaba tayi yana biyeda ita har sukai wajen motan daidai takai wajen motan ta tsaya Salman yataho yasa hannu ya bude mata motan kamshi mai bala in dadi yafara mata sallama da sanyi kafin idanunta su sauka kan Khaleel dake zaune cikin motan yayi crossing legs yana sanye da Ralph Lauren polo custom fit oxford shirt white dayayi folding dogon hannun, as usual babu kusan botura 3 na gaban rigan bai makala ba kana iya ganin kirjinsa, yasaka AMI Paris logo track short brown, short din yau ma baikai knee ba adan cinya ya tsaya, kafafunshi sanye da slides na Yeezy brown suma ga kumbunan kafanshi farare tass agyare diddigenshi kaman kasha sabida yau fari tass yasha spa pampering, writs nashi daure da agogon nexus pro smart watch, yasaka Burberry brown shades dasuka mai shegen kyau yana zaune cikin motan comfortably yana rikeda wine glass da wine keciki yana kallonta kaman yau yafara ganinta, juyawa Hawwa tayi azafaffe bawasa ko nonsense kan fuskanta takalli Salma dake tsaye abayanta tace  mai gidan nazo gani ba dan masu gidan ba! Tajuyo ta kalli Khaleel tareda nunashi da hannu cikeda cin mutunci tace  Babansa nazo gani! Wow! Har kirjinsa Khaleel yaji sigan maganan"

Hawwan cus she stepped on his ego and pressed it sooo hard!



EPISODE

Zafi kirjinshi kemai sabida abinda ta fadamai tamugun rainashi

"yarinyar, wlh baitaba haduwa da any of this creatures data rainashi"

"ba like this girl in his 32yrs of life, but zaiyi maganinta, ko gezau"

"baiyiba balle yayi wani alamu na zaiyi magana, cikeda girmamawa Salman yace  Excellency bayanan but he specifically made it clear kiga Yallabai on his behalf da dan fushi kan muryanta tace  children like him manta sakon da aka basu suke ba Salman ba har sauran security dake wajen da shi kanshi Khaleel din saida suka kalli Hawwa, ta kirne fuska tajuya tace  I need to check in with my Boss tai maganan tana barin wajen motan tai chan gaba tana ciro wayanta tashiga kiran DIG ringing daya ya daga tace  Sir Excellency bayanan fa zan dawo dasauri yace  ohh na manta ban gayamiki ba Mr Khaleel will attend to you, ki tambayi Mr Khaleel za a kaiki wajensa kiyi magana dashi wayan na kunnenta tadan juyo takallo motan dataga Khaleel yajingina abinshi da mota kaman ma bacci yake da dan damuwa kan fuskanta tadan rage murya tace  Sir naga Khaleel din wai saidai na shiga motanshi cus meeting zashi he will update me on our way dasauri DIG yace  to kishiga mana, Senate president namu na bukatan service namu don t ruin my reputation, kishiga tsoro kike duk rashin jinsa he can t do nonsense with Nigeria asset, let s take the case quick I have to go ya katse wayan, zare wayan Hawwa tayi daga kunnenta tana kallon screen din gabaki daya zuciyanta bayamata dadi, ta tsaya awajen taki motsi Salman yataho yace  we are running late Miss juyowa tayi takalli Salman da idanunta dahar sun kada sabida bacin rai sai kawai tawuce fuu azuciye kaman zata tashi sama, kai tsaye ta shiga motan ta zauna akan kujeran dake facing na Khaleel, Salman yazo yarufe musu motan ya zaga ya shiga

Please Login or Register in order to submit comment