ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce, ""To ka ga ba™i ake ta yi shiyasa, yanzu ma motsin ka na ji nace ko mijina ya ci abinci?."""

"""Wa nake dashi da zai bani?."""

"""Baka ci ba kenan?."""

"""Ban ci ba."" Nayla ta ce, ""to bara na nemo maka."" Ya dakatar da ita ya ce, ""Wasa nake yi, har falon nan Mama ta saka aka kawo min abinci, na zama Wan gatanta, bata barina da yunwa."""

"Murmushi ta yi ta ce, ""Na ji daWin haka."" Ya zuba mata ido ya ce, ""Wai ba a gama jegon ba?."" ""Tab ai sai nan da kwana arba'in."""

"""Ko kuma sai an tashi duniya ba"" ya faWa cikin ba™ar magana yana harararta. Nayla tayi dariya kaWan tace, ""Allah da gaske nake."""

"""Kedai ayi shiru kawai, amma wallahi baza ki kwana arba'in ba."" ""Harda wallahi?."""

"""Kuma kin san bana rantsuwar banza ba."" Ta yi dariya ta ce, ""Wazu an kaiwa Hajja Musliha."""

"Ya yi murmushi mai sauti yana girgiza kai ya ce, ""ai gwara da aka kai mata ita."""

"""Murmushin na meye?."" ""Na Hajja ne."""

"""Da ta baka aurena?."""

"Omar ya sake yin ΄ar dariya ya ce, ""da aka bani auren ki a gidanta."" Nayla ta murmusa ta ce, ""tijarar da ka yi a gidan fa?."" Ya shafa fuskarsa yana tuna lokacin, ya sake yin murmushi ya ce, ""ta rashin sani ne, ai ban san haka sirrin yake ba, ban san haka abun yake da Wankaren za™i ba."" Nayla ta sake yin murmushi ta ce, ""baka da kunya."""

"Ya Wan sunkuyar da kai tare da Wago ido ya kalle ta ya ce, ""itama mai jin kunyar tayi ciki ta haihu, kuma ba a ruwa tasha cikin ba."" Nayla ta sake yin murmushi ta kwantar da kanta a kafaWarsa ta ce,""Yaushe Didi zata dawo ne?."""

"""Har sai an yi suna."""

"""Kai amma ban jiwa Didi daWi ba."" Murmushi ya yi akwai suka cigaba da hira."

"Haka aka cigaba da karSar ba™i ΄an barka, dangin babansu Omar duk sun zo kuma suna haWuwa babu wanda yake nunawa wani abu, sai yaga dama na zai kula su, hakan ya saka gobe ma wasu suke zuwa. "

"angaren su Umma Saroot kusan a gidan take yini kullum tunda itace bata da aure a cikin su, ko yaushe kusan"

"tana nan tana bawa Nayla irin ta ta kulawar ta mutanen Chad, musamman Sangaren turaren wuta da humra da gyaran jiki."

"Ranar suna aka raWawa yarinya suna Aisha ake yi mata la™abi da Musliha. Shanu uku aka yanka na ranar suna, aka yi decoration a harabar gidan dan gidan babba ne no need a fita event center, aka Wauko masu hoto da masu video da masu kiWan ™warya. Abinci kuwa ba a magana, dan komai da komai leemars_delicious ce tayi, kowa sai yabawa yake yi saboda daWin abincin."

"Taro aka yi gagarumi, tun daga farkon gidan banner hoton Musliha ne har ™arshe, a cikin wani gado na glass aka saka ta duk wanda ya zo ya ganta a ciki ba a Waukarta tana ciki tana bacci. Kafin a fara taron Nayla ta takura masa akan za a yi musu hoto da video, ya nuna baya so ta dage da magiya har ya amince, aka kira mai hoto da videographer aka yi musu a cikin gida shida ita da Musliha kafin a fara taro."

"Kafin a gama taro tuni hotuna sun yaWu a duniya, masu hoton wajan da masu video suna ta Worawa a duniya ana saka c.e.o exclusive footwear with his wife on their daughter's naming. Mutanen suna ta tofa albarkacin bakinsu, musamman yanayin kyaun da suke dashi sun dace da junan su sosai."

"Omar bai gani ba sai bayan an tashi daga taron kowa ya watse sai ΄an uwanta. Ran maxa ya Saci, aljanun tijararsa da rashin mutunci suka motsa. Nayla tana zaune kawai ta ganshi a falon ta, kafin ta buWe baki ya nuna mata wayarsa ya ce, ""meye wannan?."" Nayla ta kalli wayar ta ga hotonsu ne, ta kalle shi zata yi magana ya ce, ""da izninki aka yi posting kenan?."" Nayla ta girgiza kai ta ce, ""A'a ban sani ba, kawai sun yi ne saboda aikin su ne."""

"""Oh aikin su ne Wora matan mutane ba tare da izni ba? Aikin su ne dan sun yi maka hoto sai sun yaWa a duniya?."""

"Ganin ya fusata ya fara faWa sai tayi ™asa da murya ta ce, ""suna yi ne saboda advert, amma. """

"""Amma me!? Da hoton naki da na ΄ata za a yi advert Win Jidda!?."" Tayi ajiyar zuciya jin yadda ya fara yi mata halin, tsawar da ya yi mata har tsakiyar kanta, bata so maganar ta yi nisa sai ta ce, ""ka yi ha™uri."""

"Ya girgiza kai cikin fushi ya ce, ""Dole ki ce na yi ha™uri ai, dole ki bani ha™uri tunda sun riga sun yi, blog sama da goma sun yi reposting dole ki bani ha™uri Jidda."" Nayla ta kalle shi da damuwa ta ce, ""ban san zasu yi ba, da nace kar a yi."""

"""Yanzu ma ki saka su goge, yanzu ba anjima ba su goge hoto da video, ai ba da iznina suka yi posting ba. Ni ba"

"shashasha bane da zan bar hotunan ku a duniya suna yawo da sunan wayewa ba, bana ra'ayi, daman ni ba wayayye bane, dan haka bazan yi aikin wayayyu ba. Bana so a cire yanzun nan, in ba haka ba wallahi zan yi ™ ararsu!. Ai ba ni na ce su saka ba, kema ba ke kika ce su saka ba. In ba su goge ba kotu ce zata raba mu!."" Jin yadda yake yi mata faWa sosai harda zancen zai yi ™ararsu sai tayi sanyi dan ta san laifinta ne, da ta ce kar ayi posting da ba a yi ba. A sanyaye ta ce, ""To zan ce musu."" Ko kallon ta bai sake yi ba yana fita cikin ™unar zuci."

"Salma da take zaune ita da Jidda dan sun fito lokacin da ya fara faWan, Nayla ta kalle su da damuwa ta ce, ""Yanzu ta ina za a fara goge hotunan don Allah?."""

"""Kema laifin ki ne Twiny, kin san halin mijinki da sai ki ce kar su yi posting."" Nayla ta kalli Jidda ta ce, ""Wallahi"

"mantawa nayi Twiny, ban Wauka abin nasa zai zo da haka ba."""

"Salma ta ce, ""ki kira su ki ce su goge."" Nayla ta ce, ""kin san adadin mutanen da suka yi reposting kuwa? Kuma"

"ni tsorona ΄an TikTok wallahi, gwara ΄an Ig zasu iya gogewa, amma ΄an tiktok sai a hankali."" Jidda ta ce, ""haka zaki yi musu magana tunda baya so, sannan sai ki je ki bashi ha™uri."" Nayla ta girgiza kai ta ce, ""Hmmm"

"Twiny ke baki san shi ba ne, amma Salma ta san waye shi ai. Wallahi in ransa ya Saci wanda ku ka sani a baya yake komawa, baya Waga min ™afa ko kaWan."""

"Salma ta yi dariya ta ce, ""Tiger yana dawowa kenan. Amma ki je dai ki bashi ha™uri, Yayanki ma in ni ce aka yi posting pics Wina na shiga uku, ba ya ™aunar posting a social media da hotunana, wai ba tallata yake yi ba."" Jidda ta ce, ""Nima dai bana so wallahi, ban Wauki nuna hotuna na da mijina da sunan wayewa ba sam."" Salma ta ce, ""mu dai zamu wuce, ki je ku ™arke da Tiger lafiya, Allah ya sa kar ya yi kaca-kaca da naman jikinki. Jidda mu je"" ta faWa suna fita suka bar Nayla da ajiyar zuciya.KRB3P098"

Nana haleema

"A zaune ta same shi a falo ya rufe ido, ko da ya ji shigowarta bai buWe ba daman ta san bazai buWe ba, ta zauna a gefensa ta ce, ""Rouhi ka yi ha™uri, nayi mata magana zata goge yanzu in sha Allah."" Bai buWe ido ba ya yi mata banza, zata sake yin magana aka kira shi a waya."

"Ya buWe ido ya kalli mai kiran ya ga Farid China da haka ya yi saving, ya Wan yi tsaki sannan ya Wauka ya saka a a speaker. Daga can Sangaren ya ce, ""Omar ashe yau ake sunan babyn ka shine babu labari? Yanzu na gani a tiktok, gaskiya matarka she is so cute wallahi, kun dace, damn....."" ™it ya kashe wayar ya cillar da ita akan kujera."

"Nayla ta sake tsorata dan ta san an kuma tsokano shi, in bai yi niyar magana ba ma yanzu ta san sai ya yi. Ya"

"kalle ta bayan ya tashi zaune sosai ya ce, ""Hankalinki ya kwanta ko? Hankalinki ya kwanta kin ji daWi a zuciyarki an ga hotonki an ce kina da kyau, sai ki je ki siyi abin sadaka ki rabawa yara."" Nayla ta kalle shi a raunane zata yi magana ya Waga mata hannu ya ce, ""kar ki ce min komai, ban ce ki yi min magana ba. Ba hakan ki ke so ba? In ba hakan ki ke so ba meyasa ki ka aikata!?."""

"Ta sunkuyar da kai tayi shiru dan bata ™aunar wannan faWan na sa, faWa ne wanda bashi da full stop in ya fara, bai san kara ba kuma baya Waga mata ™afa."

"Omar ya cigaba ya ce, ""iya ™afarki ce ta fita a duniya nace miki bana so aka daina, amma da yake kina so a ga fuskarki sai kika ™ir™iro da za ayi hotuna. Na ce bazan yi ba, ki ka yi min magiya na tsaya aka yi saboda tarihi kamar yadda kika ce, amma sai ki ka bada dama aka yaWa min hotunan matata a duniya. Ke kin san me nake ji kuwa? Kin san lokacin da na ga ™afarki ana yabonta a duniya me naji?. Ji nayi zan iya aikata komai a lokacin, zuciyata tana bugawa, gangar jikina tana rawa matu™a saboda kawai an yabi ™afarki. Yau fuskarki da surarki ake yabo..."" ya faWa yana watsa hannayensa cikin tsananin kishi da Sacin rai."

"""Har wanWanda ba sa jin hausa abokan kasuwancina sun kira ni suna cewa sun ga matata. Hankalinki ya kwanta an ganki ko Nayla!? To ta shi ki tashi ki bani waje!."" Nayla ta kalle shi da sauri jin da sunan da ya kirata, zata iya irga sau nawa ya kira ta da Nayla, dan baya faWa kwata-kwata. Kuma ta san baya taSa ce mata Nayla sai in ta Sata masa rai, a lokacin ne yake mantawa da Jidda ko Ashiq ya kirata da sunanta."

"A raunane ta ce, ""wallahi Rouhi ban ce ayi posting ba, na san laifina ne da ban yi magana na ce kar ayi ba,"

"amma ban san zasu yi ba."""

"Kamar zai dake ta ya yo kanta da faWa a hargitse ya ce, ""Amma kin san babu ta yadda za a yi ayi mana hoto nida ke ace baza a yi posting ba ko!? Likers suke nema, kuma matu™ar aka Woraki dole a samu likers har da comments. Meyasa baki wannan tunanin ba!?"" Ya faWa a fusace yana zare mata idanu waje."

"Sak ya koma mata Tiger, kallon Tiger take masa lokacin da ya Wora mata wu™a a wuyanta yana zare mata ido, kallon tiger take masa wanda ta ganshi da jini kaca-kaca a jikinsa. Jikinta ya yi sanyi sosai, a hankali ta sake cewa, ""na yi kuskure ka yi ha™uri, amma yanzu na yi mata magana zata goge in sha Allah."" Ya kalle ta cikin hararar da ta saka ta yin shiru, ya yi ™wafa tare da jan tsaki ya girgiza kai bai ce komai ba."

"Nayla ta duba wayarta ta nuna masa ta ce, ""ka gani har ta goge ma."" Ya Harare ta da jajayen idanunsa ya"

"ce, ""Ko ki matsar da wayar nan daga kusa dani ko na fasata, kuma wallahi in na fasa bazan siyi wata ba, kema kuma baza ki siya ba, na kuma ce wallahi."" Nayla ta janye wayar ta ajjiye a gefenta, ya bita da kallon up and down ya ce, ""Dan ta goge mutane nawa ne suke dashi? Mutane nawa ne suka saka su ma? Ko duk zaki bi su ki ce su goge ne?."""

"Yadda ya kafe ta da ido shine ya saka ta sauke ido ™asa bata ce komai ba. Yaja dogon tsaki ya ce, ""Kawai kin riga kin cuce ni, kin yi min abinda bana ra'ayi kuma bana so. Duniya gabaWaya a kan hotonki take magana, ni ba banza ba ne da zan ji alfahari dan wani ya yabi matata ba......"" ya Wauke ido daga kanta, kafin ya sake kallon ta ta ce, Ki ta shi ki bani waje na ce ko!?."""

"Nayla zata yi magana cikin tsawa ya ce, ""in kika yi min magana sai na fasa miki baki, ki bar wajan nan ko na"

"nuna miki asalin waye ni!."" A hankali ta mi™e ta bar falon bata ce komai ba, ya yi tsaki ya Wauki wayarsa ya shiga TikTok, bai yi seconds biyar yana scrolling ba ya yi karo da video sa shida Nayla da kuma Musliha."

"Kishi da haushi suka sake kama shi ya furzar da iska ya cillar da wayar. A haka ya kwanta cikin takaici da Sacin rai, in dai zai farka sai ya duba wayarsa, amma baya jimawa yana scrolling zai ga ga abinda baya so, ™arshe kashe wayar ya yi cikin ba™in ciki da takaici."

"Cikin wanda suka ga video Nayla da Omar harda Narma, Narma ta ruWe ta saka hotunan a gaba tana kuka. Dad da yake zaune a kusa da ita ya ri™e hannunta ya ce, ""Haba Narma meye haka kuma? Baki yarda da abinda nace miki bane ba wai?."""

"Narma ta ce, ""Dad kalli matar shi, kalli yadda yake farin ciki kana gani ka san yana sonta. Dad ni ce baya so, Dad"

"bazai aure ni ba, shikenan mutuwa zan yi."" Ta faWa cikin kuka mai tsanani. Mum ta kalle ta cikin tausayi ta dafata ta tace, ""ki yi ha™uri Daughter, kin ga saboda ke mu ka zo Kano dan a same shi a yi magana, in kina wannan kukan sai ki saka mu ga kamar har yanzu kina ganin bamu kyauta miki ba."""

"Dad ya ri™e hannunta ya ce, ""Zan je na same shi da kaina nayi masa magana, na tabbatar zai amince ya aure ki tunda yana sonki yana ™aunarki, na tabbatar zai amince ya aure ki in sha Allah, so don't be nervous."" Ta kwantar da kanta a kan kafaWar Dad ta ce, ""Dad da gaske zai amince?."" Dad ya ce, ""zai amince ya aureki, I promise you zan san yadda zanyi ya amince ya aure ki daughter. Kar ki damu ki kwantar da hankalinki."""

Ta goge idanunta tana cigaba da kallon hoton Nayla da Omar zuciyarta na bugawa sosai. Hankalinta ya gama

tashi gani take yi bazai amince ya aure ta ba tunda yana da matarsa mai kyau gashi har ta haihu.

"Washe gari da safe Dad da Mum suna zaune suna breakfast Narma ta fito taja kujerar dining ta zauna,"

"Dad ya kalle ta kafin ya yi magana ta ce, ""Morning Dad."" Dad ya ce, ""Ya ki ka tashi Daughter?."""

"""Fine"" ta faWa tana haWa tea tana sha bata sake cewa komai ba. Dad ya ce, ""nayi waya an tabbatar min da yanzu yana office, in na fita zan je na haWu dashi."""

"Narma ta Waga kai kawai bata ce komai ba. Mum ta ce, ""ki kwantar da hankalinki dear, komai zai zama daidai."" Kai ta Waga bata ce komai ba ta mi™e da mug Win hannunta ta hau sama."

"Mum ta kalle shi a raunane ta ce, ""Dear anya yaron nan zai amince da auren Narma?."""

"""Zai amince in sha Allah, kar ka damu in sha Allah zai amince. In bai amince ba ya zamu yi da Narma? Ai sai ta samu heart attack."" Mum ta yi tagumi ta ce, ""wallahi na damu sosai, bana son wani abu ya samu Narma wallahi."""

"""Saboda ita zan je na same shi amma bayan haka ke kin san bazan je ba, amma zan je saboda mu san abinda"

"zai faru, Na san bazai ™i amincewa ba tunda yana sonta. Kuma a matsayin da yake dashi yanzu abin alfaharinsa ne ace yana da inlaw kamar ni."" Mum ta girgiza kai ta ce, ""to ba dole ma ya amince ba, ai dole ya amince ya aureta ko baya so."" Shiru ya yi ya girgiza kai bai ce komai ba ya mi™e ya fita."

Omar da safe koda ya tashi shiryawa ya yi ya fito falo ya tarar an ajjiye masa kayan breakfast. Zama ya

"yi yana ci, a lokacin Nayla ta shigo da sallama hannunta Wauke da Musliha. Sallamar ya amsa ya kalle ta ya watsar kamar bai ganta ba, ya mi™a mata hannu alamun ta bashi ΄arsa. Ba musu ta bashi Musliha, sai ya yi murmushi yana kallonta domin kuwa Allah ya zuba baiwar kyau a fuskar Musliha. Nayla ta ce, ""Ina kwana."""

"Kallonta ya yi ya Wauke kai a da™ile ya ce, ""Lafiya."" Daga nan ya yi shiru bai ce komai ba. Nayla ta ce, ""YaMar har yanzu fushi ka ke yi?."" Bai kula ta ba ya gama abinda yake yi, ya sumbaci goshin Musliha ya mi™e tsaye ya zo inda take ya ajjiye mata ita a jikita, ya kalle ta suka haWa ido na wani lokaci kafin ya janye idonsa ya Wauki key na mota ya sauka daga saman."

"Ajiyar zuciya ta yi tana binsa da kallo ta ce, ""na shiga uku kuma fa ai, shi bai san ayi abu ya wuce ba, yayi ta"

"fushi kenan kamar tsohon arne. Zai yi ya gama ya dawo ya same ni."" Tashi ta yi ta shiga nata falon dan bata san abinda zata yi masa ba kuma."

"Omar ko da yaje a haWaWWen sabo office Winsa na karSar manyan ba™i ya zauna, office Win yana da girma sosai, Wauke da kujeru set Waya masu kyau da kuma kujeru na zaman office. Da awards da ya samu a jere akan wani dogon table, ga hotonsa da manyan mutanen nigeria da wajenta."

"Babu abinda babu a office Win, tv, dispenser, fridge, kettle ta dafa tea, microwive da komai na amfani akwai. Buga ™ofar aka yi ya ce a shigo, aka shigo da sallama ya kalli yaronsa alamun ™arin bayani ya ce, ""Boss akwai wani babban mutum da ya zo nemanka."" Omar ya Wan yi jim kafin ya ce, ""Waye?."""

"""Kamar Wan siyasa ne."""

"""Ya jira ni ina zuwa, ina wani aiki yanzu."" Yarom ya amsa ya fita."

"Ya samu Sen a zaune ya ce, ""Boss ya ce ka jira shi yana zuwa."" Da mamaki yake kallon yaron ya ce, ""ka faWa waye ya zo nemansa?."""

"""na sanka ne da zan faWa masa waye?."" ""Ka koma ka ce masa Sen Sagir ne yazo."""

"""Umarninsa nake bi ba naka ba, in kai shugaban ™asa ne ba sanata ba abinda yace shi zan yi"" ya faWa yana wucewa ya bashi waje. Sen cike da ™unar rai ya bi yaron da kallo, sai yanzu yake dana sanin rashin tahowa da escort, da tare suke dasu babu abinda zai hana bai saka an yiwa yaron dukan tsiya ba."

"Sen ya gama zuwa wuya, sama da mintina talatin yana jiran Omar bai ce ya shigo ba. Sai wuci yake shi"

"kaWai yana ™wafa, Allah ya taimaka wajan ba public waje bane da ya shiga uku da jin kunya. Narma kaWai yake hange a idanunsa, in ba dan haka ba da yanzu ya saka an tashi wajan, amma ita yake tunawa shiyasa yake yin sanyi. Bashir ne ya zo wucewa ya ga babban mutum kamar Sen yana jiran Boss Winsu. Ya bishi da kallon mamaki, bai yi magana ba ya shiga wajan Omar. A tsaye ya samu Omar yana Waukar wayarsa da key da alama fita zai yi. Bash ya ce, ""Tiger kana da ba™o a waje."""

"Omar ya Wan dafe kai ya ce, ""na manta, ka ce ya shigo"" sai ya kalli agogo ya ce, ""duk da dai sauri nake yi."" Bashir bai faWa masa waye ba ya Wauki abinda ya kawo shi wajan Omar Win ya fita.P099"

"Da sallama aka shigo ya Wago tare da amsawa idanunsa suka haWu da na Sen Sagir. Omar ya gyara zama yana kallonsa da matu™ar mamaki amma bai ce komai ba, ya ™araso ya zauna yana kallon Omar kamar yadda yake kallonsa, Hannu ya mi™awa Omar alamunsu gaisa, ba musu Omar ya bashi hannu suka gaisa. Yangance"

"Sen ya ce, ""Ya aiki? Ka barni ina jira for more than 40mints."" Omar ya ce, ""Alhamdu lillah Ban san da zuwan"

"ka ba, so dole zaka jira na gama abinda nake yi."" Sen ya yi ajiyar zuciya, bai bari maganar ta yi tasiri a ransa ba, Narma kaWai yake gani hakan ya saka ya ce, ""Tiger nazo tun daga Abuja kawai saboda na ganka."""

"Omar ya Wan taSe baki ya ce, ""zaSe ya kusa ko? Kamar saura ΄an kwanaki kaWan na ji ana cewa ko?."" Sen ya kalli Omar suka haWa ido sai Omar ya ce, ""Yanzu ba wancan tiger Win da ka sani ba bane, wannan Tigers Footwear ne. In ma kana neman wanda zasu yi maka aiki kamar yadda ka saba zaka iya zuwa bakin titi suna nan suna zaman jiran zuwanka, in maganar da ta kawo ka kenan ina da ba™in da zan yi"" Omar ya faWa yana cigaba da duba abinda yake gabansa."

"Sen ya daure ya ce, ""Ba wannan maganar ce ta kawo ni ba."""

"""Ina jinka, but don't waste my time, ina da ba™i suna jirana."""

"""Omar na zo ne akan batun Narma."" Da sauri Omar ya kalle shi kana ya ce, ""Driver take nema ne?."""

"Sen ya kalli Omar jin ba™ar magana yake faWa masa a fakaice, amma saboda Narma da halin da take ciki sai ya kawar da maganar Omar ya ce, ""Omar wannan ya wuce ya kamata ka manta komai ya wuce. Narma ta shiga damuwa a kanka, tana matu™ar sonka, in ta rasa ka zata shiga damuwa sosai. Please Omar ka amince ka karSi auren Narma, this the first time da nake ro™on wani a rayuwata, i beg you for that, ka amince ka auri Narma in ba haka ba zata iya samun matsala."""

"Omar ya zuba masa ido yana kallonsa cikin mamaki da al'ajabi, wato yanzu ya zama mutum kenan, tunda da ya"

"ce kallon dabba yake masa, ya ce ma gwara dabba akansa. Yanzu ya tashi daga jahili kenan ya dawo mai ilimi tunda gashi a zaune a cikin office Winsa yana kallonsa yana faWa masa ya auri ΄arsa, yanzu ya tashi daga wanda bai zai kaiwani mataki a rayuwarsa ba ya dawo mai matsayi a idon sanata. Soyayyar da ake i™irarin yayi asiri yanzu ta dawo ta gaskiya tunda gashi ana cewa ya aure ta. Omar ya dinga binsa da kallo yana tuna abinda ya faru a baya, hakan ya saka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. In ba dan ma yana so ya nuna masa banbancin da da yanzu shi ya isa ya iya haWa ido dashi?."

"Sen ba tare da jin nauyi ba ya ce, ""Gab take da kamuwa da heart attack Omar, ka amince da ita ka aureta zata"

"zama matarka ta biyu, dan ta zo a sencond wife Winka ba wani abun damuwa ba ne."""

"Omar ya girgiza kai cikin dubun mamaki, ya yi wani irin murmushi na rainin hankali ya kalle shi ya ce, ""Sen"

"Sagir Sani Shatima, yau kaine ka ke neman alfarma a wajan Omar? Ka manta waye Omar ne a wajanka?."""

"Sen ya ce, ""ka ji na ce komai ya wuce ai, ni dai burina ka amince ka auri Narma please

Please Login or Register in order to submit comment