ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsoro take ji ina mai ciki ina gyaran jiki? kar a je a zubar da shi."

"Bayan ta gama kwalliyar ne Mama take cewa, ""Nayla Omar zai dawo kin sha ™unshi da gyaran kai ga gyaran jiki, yanzu dai kina da ciki komai a hankali ake binsa, in ba haka ba tsaf za a zubar dashi."" Nayla sai taji kunya sosai bata iya kallon Mama ba ita kuma ta fita ta ™yaaleta."

"Omar kuwa a Abuja ya sauka kamar yadda ya tafi ta Abuja, yana zaune a airport yana jiran jirgin da zai"

"kawo shi Kano ya zo. Yana zaune cikin manyan kaya na yadi coffee colour, kansa babu hula sai gashinsa da ya kwanta, ya Wora ™afa kan Waya yana danna waya ga trolly bag Winsa a gefe. In ka kalle shi sai ka sake kallo saboda yadda ya kame ya yi kyau, ya zama irin rich handsome guys Win nan."

"""Faruk!."" Ya ji an faWa daga bayansa, ya tsaya cak da abinda yake yi dan a kaf duniya ya san wacece ta taSa kiransa da wannan suna, kuma tana faWa fuskarsa ta zo idanunsa dan ya san itace Win. Ya maze bai motsa ba"

"kamar ba shi ta kira ba, sai ta ce, ""Omar!."" A hankali ya Wago ido ya kalli idanunta. Narma ta ja doguwar ajiyar zuciya, fuskarta ta nuna yanayin da zuciyarta take ciki, hawaye suka ciko idanunta ta ce, ""Safna na faWa miki Faruk Wina ne, kalle shi ki ga."""

Safna da take tsaye a bayanta ta kalli Omar da ya mayar da kai ya cigaba da abinda yake yi kamar bai ga

"Narma ba, ta Wan yi tsaki ta ri™e Narma ta ce, ""Narma please! haba meyasa ki ke ™o™arin haukacewa ne? Kin ga wani a waya kin ce shine, yanzu kin ga wannan ma kin ce shine, maza nawa ne zasu koma miki Faruk Win?."" Narma a sanyaye ta ce, ""Kalle shi ki gani, shine wanda na ce miki, shine a cikin wayar kuma shine Faruk Win.."" ta dawo da kallon ta gare shi ta ce, ""Faruk baka gane ni ba? Narma ce fa."""

"Sarai Omar ya ganeta kawai bashi da lokacin dai zai kulata ne, a ganinsa in ya yi mata magana kamar ya ci"

"amanar matarsa ne, amma wani Sangare na zuciyarsa ya ji tausayinta sosai, musamman kalaman ™awarta. Tausayinta ya ratsa zuciyarsa, jin yadda muryarta take rawa kamar ba ita ba ya dake shi."

"Safna ta kalli Omar ta ce, ""ka yi ha™uri, wani saurayinta ne da mahaukacin so, duk wanda ta gani sai ta ce shine, ka yi ha™uri please"" ta kalli Narma ta ce, ""Narma mu je"" ta faWa tana jan hannunta."

"Narma ta turje ta ce, ""Babu inda zan je, shine wanda nake nema kuma shi na gani yanzu"" ta dawo kusa da"

"Omar ta ce, ""Baka gane ni ba? Faruk say something please, ka yi magana kafin zuciyata ta buga. Na jima ina neman ka, na jima ina so na ganka, Faruk please!"" Ta faWa tana haWe hannayenta tare da zubewa a wajan."

"Omar ya rasa abinda zai yi, tausayinta yake ji sosai, ya san zafin so, ya san ya ake jin soyayya shiyasa yake jin"

"tausayinta yana yin tasiri a zuciyarsa. Musamman yadda take kuka ta kuma zube a gabansa ga mutane da suke ya wucewa tunda rana ce kuma waje ne na kowa da kowa. In ya nuna ya gane ta me zai ce mata?, bai san mai zai furta mata ba gwara ya yi shiru. In kuma ya nuna bai gane ta ba ya kyauta mata kuwa?. Omar ya rasa me zai yi mata, a hankali ya kalle ta suka haWa ido, yadda idanunta suka red, jijiyoyin kanta suka tashi ya sake karya masa zuciya, ya Wauke kai daga kallon ta ya ce, ""Kina ji, ba wanda ki ke nema bane"" ya faWa yana mi™ewa tsaye ya ri™e trolly bag Winsa zai bar wajan."

"Hannunsa ta ri™e da sauri ta ce, ""Wallahi kaine, Muryarka ta tabbatar min da kaine. Ko a cikin mutanen da ban san adadinsu ba in na ganka na san kaine, ko maganar ka na ji na san kaine Faruk. Me nayi maka ka ke ™o™arin yi min wannan hukuncin? Meyasa ka ke ™o™arin wula™anta zuciyar da ta gama narkewa a soyayyar ka? Meyasa ka ke ™o™arin cutar da zuciyar da ta jima da cutuwa akan soyayyar ka?. Please Faruk, ka tausaya min kafin na rasa hankalina a kan ka."""

"Omar ya tsaya cak yana jinta, jikinsa ya yi sanyi sosai ya kasa motsawa. Ajiyar zuciya ya yi ya zame hannunsa"

"daga ri™on da ta yi masa, bai ce komai ba zai wuce ta. Sake tsayawa a gabansa tayi tana kallon fuskarsa gabanta yana faWuwa, kallon fuskarta ya yi suka sake haWa ido, ya Wauke kai ganin yadda hawaye yake a kwance akan fuskarta idanunta sun sake yin ja. Hannayenta ta haWe waje Waya cikin wani yanayi na kewa da soyayya ta ce, ""Please Faruk, allow me to hug you!."" Jin abinda ta ce a lokacin ya janye ido daga kanta, tausayinta ya kama ratsa zuciyarsa, baya so raunin da yaji ya bayyana akan fuskarsa."

"Ya sake raSata zai wuce ta ce, ""ina sonka, ina so na aure ka. Faruk a yanzu babu wanda ya isa ya raba ni da kai."" Baice komai ba ya wuce ta dan in ya cigaba da tsayawa zata karya masa zuciya shi kuma ba haka yake so ba."

"Narma zata bi shi Safna ta ri™e ta cikin masifa ta ce, ""Haba don Allah Narma, kawai daga ganin mutum sai ki ce shine wanda ki ke nema? Wannan ya yi miki kama da Omar Win Kano ne? Ko kuma nan Kano ne da zaki ce ai shine?. A Abuja ki ke, a Abuja ma a cikin airport, wanda ki ke magana a kai me zai kawo shi airport?. Ki dawo hankalin ki Narma, ki daina yi mana shirme, kina gani ana ta kallon mu kamar wasu cartoon. Ni da na sani ma ban ce ki rako ni ba"" ta faWa tana jan hannunta da ™arfi suka bar wajan. Ita kuwa Narma tunanin ta yana ga Faruk Winta, duk abinda ya yi mata da abinda ya ce bata damu ba, burinta ya cika ta ganshi ta kuma"

"tabbatar shine. Saura burinta na aurensa, dan a wannan lokacin bazata Waga ™afa ba."

"Omar kuwa a haka ya shiga jirgi duk sai ya ji ta sake bashi tausayi sosai, jikinsa ya yi sanyi har yana tuna yadda"

"take kuka. Bai bari tausayin ya yi tasiri a zuciyarsa ba, ya watsar da tunanin ya jawo tunanin matarsa yana tuna irin yanyin da zai same ta in ya koma gida.KRB3P085"

Nana haleema.

"A Kano suka sauka ya kira Bashir yazo ya Wauke shi suka tafi. Sai da suka fara zuwa gidan Didi kamar wancan lokacin dan zuwa lokacin yamma tayi sannan suka wuce gida. A gaggauce ya shiga saboda bai yi sallar la'asar ba ga magriba ta gabato, kai tsaye ya shiga Waki da niyar yin alwala amma sai ya tsaya yana kallon W akin."

"Decor aka yi masa mai matu™ar kyau da Waukar hankali, an rubuta welcome back Rouhi da flowers masu kyau da ™hamshi. Murmushi ya yi ya kalli table Win da yake Wakin ya ga harda cake ya girgiza kai ya ce, ""ko kina ina? Na ga cake ban ganta ba."""

"A hankali ta fito daga bayan labule ya bita da kallon ™urilla ganin ta canja masa gabaWaya, ta sake haske ga wata cikar jiki da ta sake yi na musamman. Nayla ta tako tana murmushi tana kallonsa. Murya a raunane ya ce, ""rowar ganin ki ki ke yi min in na dawo ko? Wancan lokacin ma Suya ki ka yi."""

"""Sannu da dawowa Rouhii!"" Ta faWa tana shiga jikinsa ya sanya hannu ya rufe ta a jikinsa ya yi ajiyar zuciya mai ™arfi kana ya ce, ""Don Allah indan kina yi min addu'a akan Allah ya sa na ™ara sonki ki daina, Ashiq son da nake miki yana neman fin ™arfin tunanina. Kullum soyayyar ki ™aruwa take a zuciyata, shiyasa nake neman alfarma in kina addu'a ki daina kar ta zauce"" ya furta a hankali yana ri™e da ita a jikinsa ita kuma tana hasahen yanayin da zai kasance in ya san tana da ciki."

"""Rouhi I missed you."""

"""Likewise Ashiq."" Bata Wago ta kalle shi kamar ko yaushe ba, amma yana bata mamaki in ta faWi abu ya bata amsa bayan ya ce shi bai iya ba, gashi in zata kwana tana tambaya akai bazai bata amsa ba."

"Sun jima a haka kafin ya Wago ta ya yi mata peck a goshi ya ce, ""ban yi sallar la'asar ba Ashiq."" ""Na haWa maka ruwa yana nan yana jiranka."""

"""Na gode Masoyiya"" Abinda ya ce kenan ya shiga bai saurare ta sai ta taya shi ba saboda sallah."

"Tana zaune a falo ya fito dan lokacin har an yi magrib, ya zauna a kusa da ita ya kalle ta ya ce, ""Ni na ga"

"kin rame, rashin lafiyar da ki ka yi ne ya jawo haka?"" Ya faWa yana saka hannunsa a wuyanta yana shafa ™ashin da ya gani. Nayla ta kalle ta shi tana ganin kamar ana canja mata shi, ya ™ara haske sosai fuskarsa ta canja ya yi wani irin kyau mai Waukar hankali."

"A hankali ta ce, ""Mijina baya nan ba dole na rame ba? Ni wai wannan kyaun da ka ke ™arawa na meye?."" Yana kallon ta ya ce, ""Na kewar ki ne."""

"""Shine zai ka ™ara kyau kuma?"" Ta faWa tana kallonsa da shagwaSa."

"""Eh mana, tunda bakya ganina ai dole ki ga na yi kyau. Ina tambayar ki baki bani amsa, ya naga kin rame?."""

"Nayla ta ce, ""Tunanin ka ne wallahi."" Ya zuba mata ido bayan ya ri™o hannunta ya ce, ""Tunani ki ka saka har haka Jidda?."""

"""Ni kaWai na san yadda na yi kewarka Rouhi"" ta faWa tana kwanciya a jikinsa ya ce, ""Bana tunanin kina jin abinda nake ji."" Zame jikinta tayi ta ce, ""abinci Rouhi."" Bai musa ba ta kawo masa suka ci tare suka yi sallar i'sha tare. Šakinta shiga ta Wauko cake Win da ta yi da kanta ta yanka ta bashi ya ci itama ya bata yana cewa, ""kina ta zirga-zirga ko?."""

"Nayla ta ce, ""da kaina na yi fa, ko decor Win ma da kaina nayi, kayan na siya kawai. Ya za ayi na bari masu decoration su shigar min Wakin mijina?."" Kallon ta ya yi yana Wan taSe baki ya ce, ""uhum ka ga mai miji."" Dariya ta yi ta saka sauran cake Win a fridge ta dawo ta zauna a kusa dashi. Shi kuma baya son zaman da take yi a inda yake, yanayin shigar jikinta da ™hamshin ta haukata shi yake yi, gashi daman kwaWayinta ya dawo, kuma bai manta da yanayin da ya barta ba, baya son yin abinda zai takura ta shiyasa yake kamewa amma ta kasa ganewa."

"A jikinsa ta kwanta ya yi shiru bai ce mata komai ba, jin shirun yayi yawa sai ta Wago tana kallonsa, zai yi magana ta hana shi maganar ta hanyar fara kissing Winsa, ya mayar da ido ya rufe yana jin abinda take yi masa amma ya kasa bata haWin kai, baya so sai ya birkice kuma ta janye jikinta. Nayla a zuciyarta take jin zata iya a wannan lokacin baza ta bashi kunya, amma shirun da ya yi mata baya taya ta sai ta sare, duk ™arfin guiwar da take ji dashi ya gusshe, ta kalle shi ta ga idanunsa a rufe suke. Ajiyar zuciya ta yi kamar yadda ya yi, ta mi™e ta bar jikinsa hankali ta shiga ciki."

"Shima tashi ya yi ya shiga Waki ya zauna ya dafe kai da hannunsa. Bai san me zai yi mata ba, bbai san ya take so ya yi ba, indai za a cigaba da kasancewa a haka tabbas akwai babbar matsala. Ba jimawa Nayla ta dawo ta sake zama a kusa dashi, bata yi ™asa a guiwa ba ya cigaba da abinda zai faranta masa rai. Tun yana daurewa har ya kasa ya fara taya ta amma zuciyarsa na ji tsoron guduwarta. Nayla kuwa kuka take yi amma haka take daurewa ko zata iya amma ta kasa jikinta ya fara rawa tana jin numfashinta kamar zai Wauke."

"Ganin yanayin da ta shiga sai ya ™yaleta ya tashi ya fita daga Wakin gabaWaya. Kuka sosai Nayla ta yi na rashin mafita, dan ita haushin cikin take ji da ya sakata a wannan yanayin da take cutar kanta da mijinta. Tunawa take yi rabon ta da shi har ta manta, Allah kaWai ya san halin da yake ciki dan ta san halinsa a wannan Sangaren."

"A falon bacci ya Wauke shi ita kuma a Waki tayi bacci, ta riga shi tashi tana fitowa yana tashi ta kalle shi ta ce, ""ina kwana."" Kallon ta ya yi ya ce, ""Kin tashi lafiya."""

"""Lafiya lau."" Daga haka ta shiga ciki ta yi wanka, ta fito ta dafa tea daman tana da bread ga kuma cake Win jiya ta dawo falon ta tarar ya dawo ya zauna da alama shima ya yi wanka."

"Ajjiyewa tayi a gabansa, ya Wauki tea Win yana sha. Ya share abinda ya faru a ransa ya fara bata labarin abubuwan da suka faru a China da nasarorin da aka samu da wanda za a samu nan gaba. Itama ta sake dashi suna ta hira kamar komai bai faru ba, amma ta san sai an zo Sangren zai nuna mata kuskurenta. Ta inda yake burgeta kenan, laifin Sangare Waya baya shafar zamansu, zai ware a inda take masa laifi ya hukunta amma ba a komai ba. In dai kuwa ya birkice mata to tabbas ta Sata masa rai sosai."

"Nayla bayan ta shanye tea ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""Rouhii!."" Ya kalle ta alamun yana jiran ™arin bayani dan bazai amsa ba. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""Abinda yake faruwa wallahi bana sane nake yi, ka yi ha™uri."""

"Bai tanka ba daman ta yi tunanin haka, sai ta dawo kusa dashi ta ce, ""baka ha™ura ba?."" Nan ma ya yi mata banza bai ce komai ba ta ce, ""Ajiyarka da na karSa ce ta kawo wannan saSanin."" Nan ma ya yi mata banza dan ko kusa bai kawo ciki take nufi ba. Ta Wago da kansa tana kallonsa ta ce, ""Rouhii!."" Yana kallon idonta ya ce, ""Jidda na ce miki kin yi min laifi ne?."" Ta girgiza kai ta ce, ""baka ce ba, amma ni na san ina yin abinda baka so wallahi."""

"Shiru ya yi bai ce mata komai ba ta ce, ""Rouhi ajiyar da ka ke cewa yaushe zan karSa ita na karSa fa."" Da sauri ya kalle ta sai ta kawar da kai gefe, ta ri™e hannunsa ta Wora shi akan cikinta ta ce, ""Da gaske Rouhi, da gaske nake shine silar canjawata"" ta faWa tana fashewa da kuka."

"Shi ta rikita shi ya kasa gane me take nufi, ta Wora hannusa akan cikinta ta kuma saka kuka sai ya kasa"

"gane abinda take so ta ce. Ya ce, ""Jidda meye na kukan? Ki faWa min meye a cikin na ki?."" Ta kalle shi ta goge idanunta ta ce, ""Ka tambayi Didi."" Bai yi ™asa a guiwa ba ya kira Didi kai tsaye ya saka a speaker, tana Wauka ko gaisawa basu yi ba ya ce, ""Meye a cikin Jidda? Ta saka ni a gaba tana kuka, wanne ciwon ne a ciki?."""

"Didi ta yi dariya ta ce, ""ita bata faWa maka ba?."" ""Inda ta faWa ai bazan kira ki ba."""

"""ciki ne da ita Omar."" Omar ya wara ido ya ce, ""bana son wannan wasan da ki ke min Didi."""

"""Ba wasa bane Omar da gaske ne, in zaka tuna lokacin da na ce maka na rakata asibiti ai cikin aka tabbatar mana dashi, ta ce kar na faWa maka ne shiyasa na yi shiru."""

"Cikin ruWewa ya ce, ""Wai da gaske ki ke?."""

"""Wallahi da gaske nake Omar, kaima ka kusa zama uba."" ˜it ya kashe wayar ya cilla ta kan kujera ya zubawa Nayla ido yana kallonta ya rasa wanne irin farin ciki zai yi. Nayla ta goge idanunta ta ce, ""Likita ya ce duk abinda nake yi shine yake sakawa. Rouhi ina kewarka nima, amma ban san ina barin ka ba sai bayan na yi."""

"Shi ba ta wannan yake ba a lokacin, ya mi™e tsaye ya ri™e hannunta ta mi™e itama ya kalli cikinta ya kalle ta ya ce, ""yanzu da gaske kawai Wana a nan Jidda?"" Ya faWa yana Wora hannunsa akan cikinta. Nayla ta Waga kai alamun eh ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yana cewa, ""Alhamdu lillah, Allah na gode maka, ashe nima zan ga wannan rana Jidda?. Kina da ciki fa, cikina ne a jikinki, zaki haifi yaro ko yarinya. Jidda na kasa sarrafa farin cikin da nake ciki, na kasa ri™e kaina..."" ya faWa cikin ruWewa yana shafa bayanta."

"Šagota ya yi daga jikinsa ya Waga rigarta yana kallon cikin ya kalle ta ya ce, ""yanzu a nan akwai Wana?."" Sai ta yi dariya ta ce, ""Da gaske akwai."" Ya sumbaci cikin nata ya Wago yana ™are masa kallo kamar bai kallon wani abu, ya zube guiwarsa a ™asa ya sake yin kissing cikin tare da tsotsar fatar jikinta cikin tsananin farin ciki. Mi™ewa ya yi ya kalle ta ya rasa abinda zai ce mata. Kisses yake yi mata a ko ina, fuskarta wuyanta da duk inda ya yi masa. Ta lura ya kasa magana a ruWe yake, ya ri™e hannunta amma ya rasa abin faWa."

"""Jidda kin karSi ajiyata shine ban sani ba? Jidda meyasa baki faWa min ba?."" ""nima ban sani ba, sai lokacin da mu ka je asibiti da Didi akace na sati huWu ne."""

"""Ya Salam! Jidda yanzu ya kai sati biyar kenan ko shida? Jidda Wana yana cikin ki har wannan kwanaki ban sani ba, Meyasa baki faWa min ba?."""

"Nayla ta ce, ""ina so na baka mamaki, kuma ina so naga farin cikin da zaka yi, in kana can bazan gani ba."" Sake"

"mayar da ita jikinsa ya yi cikin tsananin farin ciki yana cewa, ""Na gode Jidda, na gode da ki ka karSi ajiyata Jidda. Na rasa me zance miki, na rasa me zan ce da zan nuna miki ina cikin farin ciki Jidda "" Lumshe ido Nayla tayi"

"cikin jin daWi, kafin ta ji ya ce, ""Yanzu me ke so?"" Ya faWa yana Wago ta daga jikinsa yana kallon ta fuskarsa ta kasa Soye abinda yake zuciyarsa."

"Ita Nayla tausayi ma ya bata, duk da kewar ta da yake ciki amma farin cikin samun ciki ya kore ta, ta san yana"

"cike da kewarta da kwaWayin kasancewa sa ita, amma maganar ciki ya kore wancam batu. A sanyaye ta ce, ""Babu komai Rouhi."" Ya girgiza kai ya ce, ""A'a ki faWa min, ki faWa min meye ki ke so Jidda zan kawo miki. Ki faWa min don Allah, kar ki ce babu komai, ki faWa ina jiranki."" Nayla ta ce, ""So nake ka yi ha™uri, ka daina fushi dani."""

"Ya zaunar da ita ya tsuguna gabanta ya ce, ""ki daina faWa ni bana fushi dake, in ma ina yi na daina duk abinda ya faru ai Wana ne silar faruwar shi. Shine yake wahalar min dake ni kuma na kasa fahimta, ki yi ha™uri kin ji? Ki bawa Wana ha™uri shima."" Nayla ta shafa fuskarsa ta ce, ""Ka nutsu Rouhi, cikin Wanka ne fa, ka nutsu don Allah, duk ka koma wani iri."""

"""Kyautar Wa fa Allah ya bani, ciki ne dake Jidda, dole na fita a nutsuwata."" Nayla ta ce, ""ka dai nutsu ka ji."" Ya zuba mata ido kawai yana kallonta yana jin sabuwar soyayyarta na shiga zuciyarsa. Ya ri™e hannunta ya ce, ""na rasa me zan ce miki, amma ina so ki san na gode, na gode, na tabbatar da ™aunarki a gare ni mai yawa ce ba"

"kaWan ba. Tunda har ki ka iya Waukar cikin Wana ban san wacce irin soyayya ki ke yi min ba. Na gode Ashiq, ina sonki, ina ™aunarki."""

"Murmushi ta yi ta ri™e hannunsa duka biyun ta ce,""nima na gode da ka zaSe ni ka mayar dani uwa a wajan W an da zamu haifa."" Murmushi yayi ya sake Waga rigarta yana shafa cikinta ya ce, ""ni yanzu me ki ke so ki ci? Akwai abinda ki ke so?."" Nayla ta ce, ""bana son komai, so nake ka zauna a tare dani na yi bacci a jikinka."" Da hanzari ya dawo kusa da ita ya zauna ya kwantar da ita a jikinsa ya ce, ""Koda maciji zai sare ni bazan motsa ba sai kin tashi, ki ji bacci na adadin awannin da ki ke so, ni mai gadin ki ne"" ya faWa yana sake kwantar da ita a jikinsa."

"Nayla murmushi take yi, duk yadda take hasashen yanayin da zai kasance abin ya wuce haka, ya kasa ce mata"

"komai jikinsa har rawa yake yi saboda murnar tana da ciki, lallai ta yarda da maganarsa da ya ce yana son yara dan yanzu ta tabbatar da hakan."

"Tun daga ranar Omar ya amsa sunan mai gadin Nayla, babu abinda yake barinta tayi shi yake yi mata da"

"kansa, baya so ya ga ta motsa saboda kar wani abun ya samu cikin ta gabaWaya hankalinsa na kan cikin duk ya rikice. angaren harkokinsa komai yana tafiya yadda ya kamata, an fara aiki an kuma tura da takalma China, an kuma samu kyakykyawan feedback akan hakan."

"Kamar ko yaushe suna zaune a falo yana matsa mata ™afa kamar wacce cikin ya tsufa ya ce, ""kina ji."" Ta kalle shi dan ta san labari ne ta ce, ""ina ji."""

"""Wani mail na samu tun farkon dawowa ta, sai ban mayar da hankali a kai ba saboda ban Wauka na gaske bane. Sai Wazu aka kira ni aka tabbatar min da na gaske ne, shi mutumin ma na ganshi ido da ido kuma na tabbatar da gaske Win shine."""

"Nayla ta ce, ""meye kenan?."" Ya kalle ta ya ce, ""Saboda nasarar da na samu, kuma ni ne na farko a Africa da"

"China suka fara aiki dashi shugaban ™asa ne yake son ganina, an bani appointment gobe monday in sha Allah zan je."" Nayla da hanzari ta ce, ""da gaske.?"""

"""Da gaske nake."" Nayla ta buWe ido sosai ta ce, ""Rouhi president fa...."" Ya Waga mata kai alamun eh, ta ce, ""Rouhiii wannan ai abin farin ciki ne, ni wallahi na rasa ma me zan ce."""

"""Kar ki yi farin ciki da ya yawa kar ya shafi abinda yake cikin ki, ki yi kaWan."" Ta harare shi ta ce, ""yanzu ba ta ni ka ke yi ba ko?."""

"""Ni na isa."" Nayla tayi dariya ganin yana murmushi shima ta ce, ""Rouhi zan bika Abujan."" Ya kalle ta ya ce, ""Da kina tunanin a nan zan bar kii? Ina zan iya zuwa na bar rai biyu a gida? Tare da ke zamu tafi."" Tayi murmushi ta ce, ""Yauwa Rouhina."" Murmushi ya yi ya ce, ""da safe zamu tafi, tashi mu je ki kwanta."" Bata musa ba ta tashi suka kwanta kamar ko yaushe babu komai a tsakaninsu sai dai baccin."

"Ranar ji tayi a zuciyarta ko me zai faru sai dai ya faru amma ta gaji da ganin mijinta a wani hali,

Please Login or Register in order to submit comment