ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita tsaye ya yi ya kalli kayan jikita, Riga da wando ne dogaye a jikinta na bacci ya yi tsaki ya ce,  gabaWaya kayan ki na banza ne baki da kayan kirki a rayuwarki. Yafa mayafin mu je ya faWa yana yafa mata mayafin."

"Jiri take yi hakan ya saka ya ri™eta suka fito, kasancewar akwai motar da yake amfani da ita ta haya a gidan. Asibiti suka tafi aka karSe ta ganin yanayin ta babu daWi, aka kwantar da ita aka fara yi mata abinda ya kamata. Yana zaune a inda aka tanada domin jira, likitan ya fito ya bishi office ya zauna ya ce,  Narma Sagir. Yadda likitan ya furta Sagir Win ya bawa Ashraf dariya ya murmusa ya ce,  yeah. "

 She s is your friance?.

" No. Dr ya kalle shi ya ce,  Your mistress?. Ashraf ya ce,  she s my wife ya faWa yana kawar da kai dan bai san me za a ce masa ba."

" She s pregnant. Ashraf ya wara idanu waje ya ce,  what? Ciki wata nawa kuma?. Likitan bai fahimta"

"ba kasancewar ba hausa yake ji ba. Ashraf ya dafe kai ya ce,  How many weeks?. "

" Three weeks. Ashraf yaja tsaki cikin takaici da ba™in ciki ya ce,  I m not ready to be a father, so abort the baby. "

 Are you sure you re not ready for that?.

" Yes I m sure. And even my wife she s not ready for that. Likitan ya ce,  okay. Sign here ya faWa yana bashi wata takarda shi kuma ya saka hannu babu Sata lokaci."

"Tashi likitan ya yi ya fita Ashraf ya ce,  ni ban shiryawa haihuwa ba, tana haihuwa zata daina burge ni ni kuma"

"ban shiryawa hakan ba. Tashi ya yi ya biyo bayan sa zuwa inda Narman take, zuwa lokacin an yi mata allurar zubar da ciki, a gabansa cikin ya fara fita Narma na juya kai saboda ciwo su kuma nurses Win suna ta yi mata sannu har cikin ya fita. Cikin lokaci kaWan aka gama gyarata aka yi mata komai yadda ya kamata ta yi bacci."

"Bata jima tana baccin ba ta farka tana kallonsa, Wan ciwo take ji kaWan a mararta, sai nauyin da kanta ya yi mata, bayan wannan babu abinda take ji a jikinta. HaWa ido suka yi ya ce,  Barka da tashi. Narma ta kawar da kai tana sauke ajiyar zuciya. Nurse ce ta shigo tana tambayar ta abinda yake damunta a nan ta fahimci an zubar mata da ciki ne."

"Bayan fitar nurse Win ta kalli Ashraf murya na rawa ta ce,  you have aborted my baby Ashraf?. Ashraf ya ce,"

" yes, saboda bamu shiryawa zama iyaye a yanzu ba, shiyasa na saka a zubar na san kema baza ki so haihuwa a yanzu ba. Narma ta ce,  ka yi shawara da ni?. "

" Ai ba sai na yi shawara da ke zan yanke hukunci. Na ga dai Wan nan nawa ne ko? Ni na yi silar samun sa kuma na ce bana so, meye na ki?. "

"Narma bata iya magana ba sai kallonsa da take yi cikin rashin sanin abinda zata yi. Ashraf ya ce,  Ban shiryawa"

"zama uba ba a yanzu sai zuwa wani lokaci, bani bu™atar na yi shawara dake wajan zubarwa ko barin sa ya rayu. "

" Amma ai a jikina yake, kuma ni ce zan ji ciwo a lokacin da za a yi aborting ko?. "

" Yanzu wanne ciwo ki ke ji? Abortion ki ka yi a Texas ba a nigeria ba, na tabbatar bakya jin ko wanne ciwo yanzu saboda sun cigaba wajan kawar da ciwo. So kar ki damu. "

"Narma ta ce,  na gaji da zama da kai, ha™urin da nake yi saboda wani dalili nawa ya ™are, zama na a Texas ya"

"™are. Wayata da ka Wauke da passport Wina dole ka dawo min dasu na bar ™asar nan. Wajan iyayena zan koma, dole a raba auren nan, bana son sa ko kaWan. "

" Za a raba auren da zarar na kammala abinda nake yi dake, har yanzu ban gama morar ki ba shiyasa bazan"

"bari ki yi ciki ba. Akan me zan bar ki ki yo ciki? Kina yin ciki zai canja min halittar da nake matu™ar sha awa a tare dake, ni kuma bana so abinda yake burge ni a jikinki ya gushe. "

"Narma ta kawar da kai hawaye na sakko mata ta goge ta ce,  Duk su Dad ne suka jawo min wannan damuwar,"

"da sun bar ni da wanda nake so duk da ba haka ba. Ina son Faruk, Ina son Faruk! Ta furta a hankali tana kallon wani waje daban.  Shi Wan daban yana sonki ne?. "

" Yana sona, na tabbatar bazai yi abinda zai cutar dani ba. Zan bani dukkan farin ciki, zai bani abinda nake so bazai sani ni kuka kamar kai ba. "

"Ya yi murmushi ya ce,  Kina da tabbacin shima son gaskiya yake yi miki? Kina da tabbas akan yana jin sonki a"

"zuciyarsa?. Kallon sa tayi da mamakin kalamansa, ya Wage kafaWa ya ce,  eh mana, ai ke kafin ki fahimci wanda yake sonki tsakani da Allah zaki jima wallahi, saboda da yawan mu duk sha awar ki muke yi ba so ba. "

 Me ka ke nufi?.

" Abinda nake nufi a bayyane yake, nima da farko na Wauka Ina sonki ne sai bayan na mallakeki na fahimci ba so ba ne. Daga lokacin na fahimci wani abu da yake a tare dake ne yake burge ni ba zuciyarki ba ya faWa yana mi™ewa tsaye tare da kallon ta ya ce,  tunda dai kin samu lafiya zan je na same su si yi discharging na ki su ha Wa miki drugs mu wuce gida, bazan iya zama a nan har gari ya waye ba, kar ki manta zan dau™i azumi ya faWa yana fita daga Wakin ya barta tana kallonsa zuciyarta a cushe babu daWi kwata-kwata."

*Abuja.*

" Ni fa shirun nan Narma yana saka ni damuwa, ya kamata a san abinda za ayi gaskiya Mum ta faWa tana"

"kallon Dad da yake zaune shima. Najwa ta ce,  gaskiya Mum shirun ya yi yawa, ko a waya ba a samun ta sai dai in ka kira shi. Wanne irin zaman lafiya ne wannan da zai saka ta daina amfani da waya? Kowa ya san Yaya da social media, kwana biyu har cigiyarta ake yi saboda tashin ganin update Winta. "

"Mum ta kalli Dad ta ce,  Ka ji ai, ya kamata a san abinda ya kamata ayi gaskiya. Ni na gaji da shirun nan ban"

amince lafiya lau suke ba wallahi. Zan sake komawa domin na gano halin da take ciki.

"Dad ya ce,  ni kaina shirun nan ya dame ni, Narma babu waya, babu social media ai kamar babu rayuwarta ne."

"Gaskiya akwai abinda yake faruwa. Mum ta ce,  bara na kira shi, su na san yanzu dare ne sosai ta faWa tana Waukar waya ta kira wayar Ashraf."

"Ashraf ya Wauka daga can Sangaren ya ce,  Mum barka dai. Mum ta ce,  Barka Ashraf, ina Daughter"

"take?. Ashraf ya ce,  Bacci take yi, bata jin daWi ne muka je asibiti aka bata magani. Amma yanzu bacci take yi. "

"Mum ta ce,  me yake damunta haka?. "

" babu komai, ciwon kai ne.  Ina wayarta?. "

 Cewa take yi bata bu™atar amfani da waya shiyasa kwana biyu gabaWaya ba a jinta. Ta ajjiye wayar gabaWaya ta daina amfani da ita kwata-kwata.

" In ta farka ka tabbatar ka kira ni ka haWa ni da ita, bazai yu ta ajjiye waya a daina jin ta gabaWaya ba. Ka kira"

ni video call in ta farka.

"Ashraf ya ce,  To Mum in sha Allah. Daga nan ta yanke wayar ta kalli Dad ta ce,  gabaWaya hankalina ya"

"kasa kwanciya da wannan Ashraf Win, Ina ganin kamar akwai abinda yake yi mata shiyasa ko yaushe in aka kira sai ya dinga kawo excuse. Anya bazan tura Najwa zuwa can?. Dad ya ce,  ki jira ayi waya da ita Win, in akwai damuwa sai a tura ta, in babu kuma shikenan. "

"Mum bata ce komai ba Dad ya ce,  Na san Ashraf bazai yi abinda zai cutar da ita ba, yana sonta kuma yana ™ aunarta sosai, kuma yana da ilimi ya san abinda ya kamata ace ya yi. Mum ta taSe baki ta ce,  ashe wannan Wan daban ya yi aure, Wazu nake gani a social media wai an kaiwa matarsa hari har cikin gida. Dad shima taS e bakin ya yi ya ce,  na gani nima, ai ba abin mamaki bane ko kashe matar tasa aka ce anyi, Mahaifin da bai san darajar kansa da ΄a΄ansa bane zai bawa wannan mahaukacin auren ΄arsa. "

"Mum ta ce,  da mun biye ta haukan Narma da yanzu itace a wannan hali. Allah ka tsare faruwar hakan ko a"

"mafarki. Dad ne akwai ya amsa da amin ban da Najwa da ta san da gaske Yayarta tana son sasai, ta tabbatar har gobe tana ™aunar kasancewa dashi da zuciyarta."

******

"Nayla haka ta cigaba da rayuwa a gidan mijinta Omar, magana bata shiga tsakani su har gwara yanzu, in ta"

"gaishe shi ko ta yi masa barka da shan ruwa yana amsawa, amma kafin ta ganshi Win ma ana jimawa sai dai ta ji motsinsa kawai."

"angaren business ana ta kai takalma Kaduna, ana siyarwa ana kuma bada kuWi kamar yadda Nayla ta tsara, ita da Bashir suke yi ba tare da ya san ma ana yi ba har lokacin. Haka ma aikatan su na wajen aiki suna siya sosai daga hannunta shima ba tare da san ana yi ba. Kasancewar ™aramar sallah ta gabato mutanen Kano kwasar takalma kawai suke yi, abinka da ΄an Kano basu iya yayin abu ba, siyan takalman ake yi domin sallar bana wankan su za a yi."

"Daren ashirin da bakwai ga watan ramadan yana zaune yana addu a wannan dare mai matu™ar falala da lada da kuma amsa addu a, addu a yake yi sosai domin shigarsa islamiyya da yake karatu online ta ™ara masa sani akan abubuwan da bai sani ba a baya. Ya ™ara ilimi ya kuma san addu o i da yawa da matakan amsa addu "

"a. Yana zaune yana jerawa Allah bu™atarsa sai yake jiyo kamar sautin kuka daga falon. Katse addu ar ya yi ya taso ya fito ya shiga ™aramin falon da take zama ko yaushe dan ganin lafiya take kuka. Itace Win kuwa take kuka amma cikin addu a, ta yi sujjada tana kuka mai ratsa zuciya babu wanda ya san abinda take faWawa wanda ya haliccita sai shi kawai."

"Wani irin rauni Omar yaji wanda bai taSa jin sa ba a rayuwarsa, lokaci Waya zuciyarsa ta shiga bugawa da ™arfi ba tare da ya san dalilin da ya kawo hakan ba. Ya bita da kallo cikin wani yanayi da bai san meye ba, shi dai ya san ya tsaya yana kallon ta amma bazai ce ga dalilin kallon ba. Ba a bayyane take addu ar ba dan haka bazai ce ga abinda take cewa ba, shidai yana jiyo shashshe™ar kukanta. GabaWaya sai ya rasa kuzarinsa ya kasa daina kallonta, gashi dai ba fuskarta yake gani ba amma ya kasa Wauke ido daga kanta."

Šagowa ta yi daga sujjadar ta kifa kanta akan hannayenta tana cigaba da kuka. Da™yar ya iya jan ™afarsa ya koma ya zauna akan sallayar ya cigaba da ta sa addu ar cikin rauni. Ba tare da ya sani ba ya tsinci kansa yana ro™on Allah ya yaye mata duk abinda yake damunta ya bata abinda take so.

"Lokacin sahur ne ya yi gashi ya manta bai shigo da fruits ba kamar yadda ya saba sha, hakan ya saka shi ya taso"

ya fito ya kalli inda take taga tana shan ruwa. Tambayar kansa yake yi ita bata sahur ne? Bai taSa ganin ta tana

cin abu ba sai dai ya ga tana shan ruwa. Bai tambayeta ba ya sha kawai ya koma ba tare da ya ce mata komai

ba.

"Washe gari da safe da ™arfin guiwa ta tafi aiki, ji take kamar Allah ya amsa mata dukkan addu arta, ji take komai ya wanke daga zuciyarta kamar ta samu duk abinda ta tambayi mahaliccinta a daren jiya. ˜arfin guiwa take ji da karsashi tun a daren jiya, shiyasa ta saka a ranta komai ya zo ™arshe."

"Tunda ta fita take bada sadaka cikin fariin ciki har ™arasa wajan aiki. Da wuri ta gudo daga wajan aiki ta wuce saloon a inda suke zuwa ita da Salma in tazo Kano. Gyara mata kai akayi da gyaran ™afa harda facial, ta bar wajan da niyar zata dawo washe gari ayi mata black henna."

"Maimakon tayi gida kawai sai ta wuce gidan Abba, ta san duk shekara yana haWa shan ruwa ranar ashirin da bakwai ga wata. Bata taSa zuwa ba, yawanci ko yaushe tana Kaduna ko tana Saudia shiyasa wannan karon tayi ™udurin zuwa tunda tana Kano. Kowa da ya ganta ya yi farin ciki musamman yadda take walwala tana ta tsokanar mutane ana dariya. Da ita aka sha ruwa dan su Mama Sa adatu duk suna wajan har Abbas."

"Da farko ta Wan ji babu daWi ganin Abbas, amma sakewar da ya yi yana janta da hira sai ta manta ta saki jiki aka sha ruwa tare. Bayan an gama aka zauna ana ta hira cikin zumunci ana tsokanar juna kafin lokacin i sha ya yi a haWu ayi sallah gabaWaya har tarawee tare aka yi."

"Bayan an idar ne Abba ya kalle ta ya ce,  Hauwa Ina fatan baki da damuwa ko?. Nayla tayi murmushi ta ce,"

" babu komai Abba, babu abinda yake damuna.  Ko a gidan auren na ki babu matsala?.  Babu komai Abba. "

" Haka ake so, Allah ya Worar da zaman lafiya a tsakani. Ta amsa da amin aka cigaba da hira."

"Ta shi tayi ta ce,  dare yayi har tara tayi, bara na wuce. Abba ya kalle ta ya ce,  Zaki iya tafiya ke kaWai ko"

"na haWa ki da driver in yaso ya hawo keke napep ya dawo?. Nayla tayi dariyata ce,  zan iya Abba, ai garin da jama a sosai tunda azumi ne. Abbas cikin tsokana ya ce,  in fa baza ki iya ba ki faWa, na san ki da shegen tsoro. Dariya ta yi sosai ta ce,  Nayla Kaduna kenan Ya Ab, Naylan Kano ai bata da tsoro. "

"Wata daga cikin cousins Winta ™anwar Abbas wacce suke kira Ummimi ta ce,  saboda Naylan Kano tana auren Tiger ko?. Kallon ta Nayla tayi kafin Nayla tayi magana ta kuma cewa,  Eh mana, matar Wan daba ai babu ita babu jin tsoro, ke da har gida aka shiga aka kusa kashe ki kuma kika cigaba da zama lafiya, kema ai kin zama jan wuya matar Tiger"

"Sai fara ar fuskar Nayla ta gushe gabaWaya saboda rashin jin daWin maganar, ta san gaskiya ta faWa amma bata"

"ji daWin abinda ta ce ba ko kaWan. Abbas ganin ta canja alamun rashin jin daWi sai ya kalli Ummimu ya ce,  Zama matar Wan daban ma matsayi ai ne, wata ta zama mana in ta isa, ko ba haka bane Nayla?. Murmushi tayi ganin tayi murmushi sai ya ce,  mu je na raka ki mota ki wuce gida dare yana yi. Sallama ta yiwa su Abba tana ji suna yiwa Ummimi faWa."

"Nayla kuwa tana shiga mota suka rabu da Abbas bayan sun yi sallama da al™awarin zai kawo mata ziyara ta wuce gida. Tana zuwa ™ofar gidan ta tarar da yaran sa su uku a tsaye suna ta waige-waige kamar masu neman wani abun. Ta tsayar da motar dan yanzu sune suke shigar mata da ita gidan, ko basa nan a waje take barin motar da sun zo zasu shigo su karSi key su shigo da motar gidan."

"Nayla ta fito daga motar bayan ta Wauko jakarta da wayarta da snacks Win da ta taho dashi daga gidan Abba. Bash ne ya ™araso wajan ta ya ce, Antyn mu ina kika shiga tun Wazu muna neman ki? GabaWaya hankalin mu ya tashi, na kira ki sau babu adadi ban same ki ba. Hankalin Damisa ya tashi sai faWa yake yi. "

"Nayla da mamaki ta ce,  na je gidan Yayan Mamana ne, a can na yi iftar. "

" Amma antyn mu da sai da kin sanar dashi ko a waya ne, ya tayar da hankalin kowa, ya ce in ba a nemo ki ba akan mu zai wuce. Nayla mamaki ya cika zuciyarta jin wai ya tayar da hankali, kafin ta yi magana Tk ya ce,  kuma an kiran ki bakya Wauka. "

"Nayla ta ce, Ina can cikin ΄an uwa wayar ma tana cikin jakata har yanzu ban Wauko ba. Tk ya ce, Gaskiya Antyn mu kin Waga mana hankali, kin san Boss ya tara ma™iya da yawa tsaf wani zai cutar take, don Allah ki daina nisa haka babu sanarwa. Nayla tayi murmushi ta ce,  to ku yi ha™uri, in sha Allah baza a sake ba. "

"Goje ya ce,  dole mu karSi ha™urin ki Antyn mu, kawo key Win. Ba musu ta bashi ta ce,  Na gode. Daga haka ta shiga cikin gidan tana mamakin meyasa ya tayar da hankalinsa dan bata dawo ba?."

"Tana shiga falon dashi suka haWa ido, sai ya Wauke kai kamar bai ganta ba amma ya amsa sallamar da tayi. Nayla ta ™arasa nesa dashi ta kalle shi ta ce,  an sha ruwa lafiya?. Banza ya yi mata bai amsa ba. Da yake ta saba kwana biyu yana amsawa sai ta sake kallonsa taga ya wani basar kamar basarake, daman marocon jallabiyya ce a jikinsa mai zubin al™yabba, ya hakimce ya Wora ™afa kan Waya sai ya koma tamkar yarima. Nayla ta ce,  na biya gida Abba ne a can muka sha ruwa gabaWayan mu shiyasa ban dawo ba. "

"A ™ufule ya kalle ta ya ce,  Wani ya damu da zuwan ki da dawowarki ne? Kin ji na ce ina kika je?. Samun kanta ta yi da yin murmushi jin abinda ya ce ta ce,  A a, sanin baka damu ba shiyasa ma ban faWa maka zan je tana faWa ta bar wajan da sauri kar ya make ta, dan yanayin da yayi magana ya nuna mata kamar ba a daidai yake ba."

"Tsaki ya yi cike da jin haushi, ya rasa meyasa ya damu da rashin dawowarta da wuri har haka, gabaWaya ya bi ya Waga hankalinsa sai ka ce Didi ce ta Sata. Tsaki ya sake yi ya kalli inda ta bi, ya sauke numfashi tunawa da ta dawo kuma lafiya lau take babu abinda ya same ta. Ido ya lumshe ya buWe ya tuna murmushin da tayi kafin ta bashi amsa. Gashin kansa ya shafa ya sake yin tsaki ya mi™e ya bar falon."

"Nayla kuwa da fara a ta shiga ciki tana tuna abinda Bash ya ce mata akan Waga musu hankalin da Omar ya yi,"

"dariya tayi tunawa da ya ce in basu nemo ta ba akan su zai huce. A bayyane ta ce,  kenan dai ya damu dani har haka? tayi juyi a kan gado ta girgiza kai ta ce,  tunda har ka damu haka wallahi sai na saka ka magantu da kan ka, Allah ya kaimu bayan sallah ta faWa da fara a tana cigaba da murmushi."

"Sai a wannan ta Wauko wayarta daga jaka, a lokacin kiran Didi ya shigo ta Wauka ta saka a kunne Didi ta ce,  Ya Allah! Nayla ina kika shiga Ina ta kira bakya Wauka? Omar gabaWaya ya Waga min hankali, wai baki dawo ba shi bai san inda kika tafi ba. "

"Wani daWi ya sake mamaye zuciyar Nayla ta ce,  Didi ina gidan Abba fa, a can na sha ruwa gabaWaya har su"

Mama da ΄an gidan Baba.  Amma bai sani ba ko?.

" Eh bai san zan je ba, daga wajan aiki na wuce.  Amma da kin sani koda a waya kin sanar dashi. "

" Didi shine fa ya ce duk inda zan je bai dame shi ba, cewa yayi naje lahira ma ai ba a kansa nake ba, shiyasa na yi tafiyata ta ™arasa faWa da shagwaSa harda turo baki. Didi tayi dariya ta ce, ai kam ya dame shi wallahi, sai cewa ya yi yanzu wani abun yana samun ki zan fara yi masa faWa ina cewa baya kula dake shiyasa ya ke so ya san inda kika tafi. "

"Nayla tayi dariya ta ce,  To yanzu ma da na dawo ina faWa masa inda naje ko kallon kirki ban ishe shi ba, da ya"

"gama shan ™hamshi sai cemin ya yi ya damu da inda naje ne. Didi tayi dariya sosai ta ce, ban taSa ganin W an rainin hankali kamar Omar ba, amma zamu kama shi hannu biyu. Nayla ta yi murmushi ta ce,  Didi bara na yi wanka na gaji. Daga nan suka yi sallama ta fito ta dafa ruwan zafi a kettel ta shiga dashi banWaki ta yi wanka cikin karsashi da farin ciki."

"Bayan ta shirya ta fito sanye da hijjabi ta Wauki ruwa a falo yana zaune a falon yana duba wani littafi. Tv a kunne take, ta tabbatar ba shi ya kunna ba sai dai in tun safe take a kunne dan ta kunna da safe kafin ta fita, kuma da ta dawo bata lura da tv ba. ˜arasowa tayi zata kashe aka fara tallan company sa da ta bayar a tashar. Kallon sa tayi sai ta ga ya Wago ido yana kallon tv fuskarsa cike da mamaki mai yawan gaske. Tsayar da idanunsa yayi cak ganin komai ana haskawa harda number wayarsa a cikin numbers Win da aka bayar."

"Waya ya Wauka ya kira Bash yana Wauka ya ce,  Zo abinda ya furta kenan ya yanke wayar yana sake kallon"

"tv Win. Lokacin an gama tallan Nayla ta kashe tv a sanyaye ta san shikenan asirin ta ya tonu, fata take Allah ya raba su lafiya kar ya yi mata wani abun. A hankali ta bar wajan ta shiga kitchen ta ji an buWe ™ofa alamun Bashir ya shigo."

" Yaushe aka bada talla a wannan tashar? Ya faWa tana nuna tv, Bash ya kalli ya ga tv a kashe take ya sake"

"kallon Boss Win nasu da yake kallon sa. Bash ya gane abinda yake nufi hakan ya saka ya ce,  Tiger ai tun farkon watan nan aka bayar. Ya zuba masa idanu yana binsa da kallon mamaki ya ce,  da izinin wa? Kuma waye ya ce ayi?.

Please Login or Register in order to submit comment