ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na farko da ya fara amfani dashi a gidan nan. "

"Didi ta yi dariya bata ce komai ba suka fito tare Nayla ta fito tana dubawa ko zata su Bashir. Sai kuwa taga Tk,"

ya buWe mata gate Win ta fita da motar suka fita.

"Sun sha yawo da Didi har bayan sallar i sha basa nan, haka ya yi mata daWi sosai ko babu komai ta rage kewa."

"Sai da suka yi sallar i sha a gidan ΄an uwa sannan suka taho dan Abdulhamid yana ™ofar gidan Omar yana jiranta. Nayla tayi mamakin dangin su Omar, mutane masu kirki da karamci, gasu duk masu arzu™i dan babu gidan da suka je wanda za a ce gidan talakwa ne, sai dai manya gidaje da madaidaita. A ™ofar gidan suka yi"

"sallama da Didi da al™awarin zata je gidan Didi, Didi bata shiga gidan ba ta shiga motar mijinta suka wuce."

"Nayla kuma a waje ta ajjiye motarta, dan ba ita take shiga da ita ba su Bashir ne. Babu wanda ta gani a cikin su"

hakan ya saka ta shiga ta bar motar a wajen dan ta san zasu zo su shigar mata da ita in suka zo.

"Babu jimawa sosai ya shigo, bai kalle ta ba key Win motar ya Wauka ya fita ba jimawa sai ga shi ya kawo mata ta ajjiye. Yanayin fuskarsa ma baza ta bata damar yin magana ba, ko kallonta bai yi ba, a ransa kuwa haushinta yake ji tana take fita tana kaiwa dare ba tare da ya san inda take zuwa ba. Shi kuma bashi da lokacin da zai tambayeta da ya ji da izininwa take fita, sanin bazai iya tambaya ba ya saka ya share ta kawai ya shiga ciki."

Haka zaman na su ya cigaba da tafiya har hutun sallah ya ™are ta koma aiki kamar ko yaushe tun safe sai yamma. A haka ta fara azumin sitta shawwal kamar yadda ta saba kafin wata ya yi nisa take farawa. Su Hajja suna gab da dawowa dan Salma ta sanar da ita a satin zasu dawo haka su Abiy ma.

"Ranar laraba da yamma ta dawo daga aiki tana zaune tana danna waya taga kiran Twiny ya shigo, abin ya bata"

mamaki tana tambayar kanta kenan ta dawo nigeria ko labari. Da zumuWi ta Wauka a nan take sanar da ita ai tana ™ofar gidanta. Da sauri Nayla ta mi™e ta je ta buWe mata tun daga nan suka rungume juna cikin farin ciki suka shiga ciki.

"Jidda ta kalli Nayla tace,  Ma sha Allah, matar Omar kin yi kyau kuma duk da har yanzu da wannan shegiyar"

"ramar, Amma wallahi kin fes dake. Nayla ta ce,  Aiki ne fa yake saka ni ramar nan, ga aikin gidan nan yayi min yawa sosai. So nake su Hajja su dawo a kawo min maid Win da zata dinga taimaka min, in yaso ko gidan Hajja sai ta dinga zuwa tana kwana. "

 To ke aikin gidan naki ai sai yamma tunda da safe kin fita.

" Daman sai dai ta dinga zuwa da yamma. Jidda ta ce,  Amma duk da haka kin yi kyau, na ji daWi da ki ka"

"cire damuwa ki ka karSi ™addara. Nayla tayi murmushi ta ce,  Hakan ya zama kamar dole ai Twiny. Ya ki ka baro su Mama? Kowa Lafiya?. "

" Lafiya kowa ya ke, su ma jibi zasu dawo in sha Allah. "

 Allah ya dawo dasu Lafiya.

" Amin. Mama ta ce nan zata fara zuwa ta ga ya yanayin ki yake, Tunda akace an kawo miki harin nan shikenan hankalinta ya kasa kwnaciya, ta ce ko a Abuja suka sauka sai ta siyi ticket ta zo Kano daga na ta wuce a mota "

"Nayla ta ce,  Allah sarki uwa ta gari, Allah ya dawo dasu Lafiya. Ta amsa da amin tana fito mata da tsaraba"

"Nayla ta ce,  KFC muka yi dake ko Albaik?. Jidda taja tsaki ta ce,  kawai sai na rasa abinda zan kawo miki sai kaza? Kawai ki saka ni dakon kaza? To ban shiryawa haakan ba. Nidai babu abinda na siyo, naga Salma dai ta ce zata siya miki ita Yaya J. "

"Nayla tayi dariya ta ce,  Ke da baki siyo ba ai kin huta. "

" To haka kawai na rasa me zan siyo miki sai fried chicken dan lalacewa? Ba ga KFC Win nan a nigeria ba, mu je ki siya mana. "

" Dallah can, tunda dai baki siyo ba kin kyauta. Zaki haWa KFC Win nigeria da ta can ne?. "

"Jidda tayi mata banza ta mi™a mata ledar ta karSa tana fito abin ciki. Abaya ce rantsatstsiya mai shegen kyau da tsada kalar ba™a, sai wani oil perfume a kwalba mai Wan girma, sai cross slippers, sai kuma misk tahara a babbar tasa. Nayla ta ce,  Kai Twiny wannan abayar ta yi kyau sosai wallahi. Jidda ta ce,  ga kuma turare nan ba, wannan turaren duk ranar da zaki amarce zaki shafa, wannan taurin kan da Tiger yake ji dashi ko lion ne shi duk sai ya sauke shi wallahi. Nayla ta ™yal™yale da dariya mai sauti ta ce,  au ashe ma ranar zata zo kenan?. "

"Jidda ta harareta cikin jin haushi ta ce,  nufin ki a haka zaki ™are kenan?. Nayla tana dariya ta ce,  ni dai bana wannan tunanin Twiny, ni na san da wa nake tare. "

" Ko waye shi sai dain bamu so kama shi ba wallahi, shi Win banza Jidda ta faWa cike da jin haushi. Nayla dai"

"dariya take yi ta buWe misk Win ta ce,  Kamar kin san nawa na barshi a Kaduna, bani dashi a na ko kaWan. Kuma na manta shaf ban siya ba wallahi. Ke dai Allah ya barki da baby, ya fito mana da unborn lafiya. "

"Ta amsa da amin Nayla ta buWe turaren ta ce,  Akwai ™hamshi kam sosai wallahi. "

" Yana da daWi gaskiya, shiyasa bana sakawa na fita nima a gida nake amfani dashi. Nayla ta ce,  mu kam gwara mu shafa mu fita Win, a nan Win amfanin uban me zai min?. Jidda ta ce,  kedai Allah ya ba mu lafiya. Suka yi dariya a tare suka cigaba da hira har aka yi i sha sannan Jidda ta wuce gida."

"Ranar juma a su Abiy suka dawo, kamar yadda Mama ta ce Kano Win ta shigo ita da Yaya J. Sai da daddare"

"suka zo gidan Nayla. Da zumuWi ta buWe ™ofar ta rungume Mama tana murna. A falo suka zauna Mama ta bita da kallo bayan sun gaisa ta ce,  Nayla babu wata damuwa dai ko?. "

"Nayla ta ce,  Babu komai Mama. Mama ta ce,  kar fa ki Soye min damuwarki, in kina ganin baza ki iya fa"

"Wa min a gaban Jawad ba sai ya bamu waje. Nayla ta yi dariya tana kallon Yaya J ta ce,  babu komai Mama, in akwai zan faWa miki. "

"Mama ba haka ta so ji ba, bata so ta ji ta ce lafiya lau ko babu komai, damuwa ko tashin hankali kawai take da"

"bu™atar ji daga bakin Nayla. Jin abinda Nayla take faWa sai ta sharebata nuna mata ba ta bata tsarabar da ta siyo mata. Jawad ma ya bata tsaraba harda McDonald fried chicken Win da suka yi da ita, ai kam ta ji daWi sosai sai muryar take yi ta ga babarta da yayanta. Bayan fitar Jawad yana jiran Mama a mota Mama ta kalle ta ta ce,  Nayla zo nan. "

"Nayla ta dawo kusa da ita ta zauna ta ri™e hannunta ta ce,  Kin tabbatar dai babu matsala?. Nayla ta ce,"

 babu Mama.

 Kina so ki ce ya karSe ki matsayin matar sa? Har ha™™in da yake kansa na aure yana sauke miki ko ya ya?.

"Nayla sai ta ji maganar ta yi mata nauyi sosai, ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Mama ta ce, ba kunya zaki"

"ji ba, faWa min zaki yi, ai ba ajiya aka kawo masa ke ba. Nayla a sanyaye ta ce,  Mama ki yarda babu wata damuwa. "

" Baki amsa min ba ai, yana sauke miki ha™™in ki da yake kansa?. A ta™aice ma ke da shi kun zama mata da mijin na gaske?. Nayla ta rasa abinda zata ce, ta rasa wacce amsa zata bawa Mama dan wallahi kunya take ji. Baza ta iya ce mata eh ba dan ta san ™arya take yi, sannan bazata iya cewa a a ba saboda kunyar da take ji."

"Mama ta ce,  bai faru ba, Ina kallon idanunki na san bai faru ba, kuma ki ce min babu matsala Nayla? Gaskiya"

"zan samu Abiy a raba auren nan kawai. Nayla a sanyaye ta ce,  A a Mama, Abiy har yanzu yana fushi dani, ki bari a kwana biyu ba yanzu ba. "

"Mama daman abinda so kenan sai ta ce,  ai shikenan. Allah ya kyauta, ki cigaba da ha™uri komai zai wuce.  Mama ki gaishe da Abiy, Na yi kewar sa sosai, har yanzu bai bani umarnin zuwa Kaduna ba ko?."

 Bai bayar ba Nayla.

" Ki gaishe shi. Bara na kawo sa™o ki kai masa Mama ta faWa tana shigowa ciki da sauri amma ta bita da kallo tana taSe baki. Ba jimawa fito ta bawa Mama sa™on ta karSa tana cewa,  Abiy Wan gatan Nayla, ya gode sosai. Tare suka fito har mota ta raka Mama sannan ta koma ciki zuciyarta cike da kawar ΄an gidan su."

Abiy yana zaune ranar asabar da safe shida Jawad suna duba littafi wanda suke rubuta duk abinda ya shafi

"kasuwancin su musmaman wanda suka bawa kaya. Mama ce ta shigo da sallama hannunta Wauke da abinda Nayla ta bata ta ™araso ta zauna ta ce,  barkan ku da aiki. Suka amsa kafin Mama ta ce,  Abiy ga sa™o jiya Nayla ta ce na baka ta faWa tana ajjiye masa."

"BuWewa ya yi ya yi karo da ™ananun cincin irin wanda yake so har take yi masa da tana gidan. Murmushi ya yi yana kallon cincin Win cikin kewarta ya ce,  na gode ya faWa yana rufewa ya cigaba da abinda yake yi."

"Mama ta sauke numfashi ta ce,  Abiy haka za a bar Nayla a cikin wannan yanayin da take ciki? Wata biyu da"

"kenan da tarewar ta amma babu cigaba tana nan a rame har yanzu. Dan tana sonsa ai ba hakan yana nufin zamu ™yaleta a halaka ba. Jawad ya kalli Mama jin abinda ta ce, dan shi kam bai ga alamun damuwa a tare da ita ba."

"Abiy ya yi shiru bai ce komai ba Mama ta ce,  Duk da ta Soye min damuwarta ta ce babu komai amma ni uwa"

"ce zan iya fahimtar damuwarta ta ko wacce fuska. Nayla tana cikin damuwa, mijin nan nata bai Wauke ta a bakin komai ba, itace take dakon sonsa na wahala wanda bazai amfane ta ba. Yarinya gabaWaya tayi ™ashin wuya, ba dan da kayan abinci aka kaita ba da ina jin ko abinci bazai dinga bata ba. Jawad da mamaki ya ce, Mama azumi fa aka gama, ga azumi ga aiki ai dole ta rame. "

"Mama ta kalle shi ta ce,  tun kafin azumin ai a rame ta ke, tunda ya shigo rayuwarta shikenan komai ya lalace,"

farin cikin gidan nan gabaWaya ya tarwatse. Ni na gaji kawai a raba auren nan.

"Abiy ya sauke numfashi ya kalle ta ya ce, Zeenatu meyasa baki taSa faWar alkhairi akan auren nan na Nayla ba?"

"Ko yaushe cikin kushewa ki ke bayan ke kika bata goyan bayan aurensa?. Gaban Mama ya faWi ta kalli Abiy da yake kallonta ta ce,  bana faWar alkhairi fa ka ce?. "

" Eh haka na ce. In aka ga Sarna shiru ake yi ba yaWata ake zuwa a yi ba, a matsayin ki na uwa a gareta sai ki cigaba da yi mata addu a tunda kin shaida tana son mijinta. Ni kar ki sake samu na da irin wannan batun, bana so. "

"Mama ta ce,  Yanzu inda mahaifiyarta ce ai baza ka ce mata haka. Kullum da tunanin Nayla nake kwana nake"

"tashi, kullum tunanina ya take me yake faruwa da ita wacce irin rayuwa take yi a gidan. Damuwa da ita ne ya saka make yawan maganarta ba dan bana faWar alkhairi akan aurenta ba. Ka bashi auren ta ba tare da ko sisi ba, ta tare ka ce kar ta zo maka gida sai ka neme ta, ka san yadda Nayla take da ™ulafucin ™aunarka ko iya wannan bazai saka ta rama ba?. Ga shi bata da wani matsayi a wajan mijin nata, ya jingine ta a gefe kamar ba matar sunna ba. Ni bazan iya jure ganin Nayla a wannan hali ba gaskiya, sai dai ka ce bana faWar alkhairi amma bazan iya ba tana faWa ta tashi ta fita daga falon."

"Abiy ya kalli Jawad ya ce,  kai ka ga alamun wani abu a tare da Nayla?. "

" Wallahi Abiy ban gani ba, rayuwarta ke yi da walwala kamar tana cikin gidan nan. Inda tana da damuwa ko a fuska za a gani, damuwar ta bai wuce har yanzu kana fushi da ita ba. Abiy ya ce, magana ta ™are, cigaba da lissafin. Suka cigaba da abinda suke yi."

"Mama da ta koma Waki ita kanta ta kasa nutsuwa, ba haka taso ta ga Nayla ba, taso ta ganta cikin damuwa sosai amma sai ta ga akasin haka. Taso ta je ta ga Omar ya yi mata dukan tsiya sai taga babu alamun koda cizon sauro a jikinta balle alamun duka, taso ta je ta ga fuskarta a kumubure, fatar jikinta a yayyake amma sai ta ga kyau da ™yalli ma fatar take yi. Gashi yanzu Abiy ya fara zargin bata faWar alkhairi, tunda ya fara faWar hakan kenan ya karSi auren na su hannu biyu. Ba yanzu take so ya amince da auren ba, ko da zai amince tafin so sai Nayla tasha ba™ar wahala a hannun Omar, amma yanzu tun ba a je ko ina ba ya fara faWar haka dole ta"

damu. Zagaye take yi tana tunanin ya zama dole ta samo mafitar da Nayla zata sha wahala sannan Abiy ya sake

"tsanar auren, sai ta yi hakan burinta zai cika, a yanzu abinda yake faruwa ba shi take so ba."

Mum da Dad da Najwa sun dira Texas saboda yadda hankalin su ya kasa kwanciya a kan Narma. Sun je estate

"Win da suka san suna nan amma basa gidan. Hankalin Mum ya sake tashi da™yar Dad ya lallaSa suka koma inda suka sauka. Bayan sun koma Mum cike da damuwa ta kalli Dad ta ce,  ni wallahi jikina yana bani wani abun ya samu Narma, ka kira Ashraf Win mu ji suna ina. "

"Dad bai musa ba ya kira Ashraf whatsApp call, Ashraf bai fahimci Dad yana America ba tunda whatsApp call ne"

"ya saka shi ya Wauki wayar. Yana Wauka Dad ya ce,  Ashraf kuna ina ne? Ga mu a estate Win da ku ke amma gidan babu kowa. ˜irjin Ashraf ya buga ya kalli Narma da take kallon sa ya ce,  Eh Dad, mun canja estate ne. "

 Turo min location Win yanzu.  Okay Dad ya faWa yana yanke wayar.

"Narma ta kalle shi bayan ya yanke wayar ta Wauke kai bata ce komai ba, ko murnar zuwan iyayen nata ma bata ji ba dan a ganin ta duk su suka saka ta a cikin wannan hali da take ciki. Da sun amince ta auri wanda take so duk da ba haka ba ai."

"Ashraf bai nuna ya wani damu sosai ya turawa Dad location Win inda suke. Ya juyo ya kalle ta ya ce,  Ko da su Dad sun zo babu wanda ya isa ya raba ni dake wallahi, sai na gama fanshe wahalar da ki ka bani kafin na rabu dake ki je ki auri Wan daba. Narma bata ce komai ba ta Wauke kai dan gabaWaya yanzu ta zama shiru-shiru, duk rashin kunyar nan da take ji da ita ta gudu."

"Kusan mintina ashirin da tura musu location Win aka fara danna door bell, Ashraf ya mi™e ya buWe suka fara haWa ido da Mum. Kallon da take yi masa ya saka ya Wauke kai daga kallon ta, Dad ya yi hugging Winsa ya ce,  Ashraf mun zo babu notice ko?. "

" Babu komai Dad, ku shigo. Shiga suka yi falon Narma na zaune a kan kujera ko motsawa ma bata yi ba."

"Mum ce ta kalle ta ta kalli Dad da shima ya kalleta ta ce,  Narma baki gan mu ba ne?. Kallon su tayi ta sake"

"Wauke kai bata ce komai ba. Dad ya wara idanu ya ce,  Narma me yake damunki? Kin yi rashin Lafiya ne?. A guje suka taho inda take kawai sai ta fashe da kuka."

"Dad ya zauna a gefen ta Mum ma haka, suka sakata a tsakiya suna tambayarta abinda ya same ta. Bata ce"

"komai ba kuka kawai take yi Mum ta kalli Ashafe ta ce,  Asharaf me yake damunta ne? Me ka ke yi mata da ta koma haka duk ta rame uhum?. Meyasa ko yaushe ba a samun ta a waya?. Ashraf ya ce,  Mum ta samu miscarriege ne fa. Dad da mamaki ya ce,  miscarriege! Yanzu Ashraf miscarriege ta samu baka kira ka sanar da mu ba? Meyasa ka Soye mana?. "

"Mum kallon Narma take yi ta ri™e hannunta ta ce,  yaushe hakan ya faru?. Ashraf ya ce,  Dad na so na sanar da ku itace ta ce bata so na faWa mu ku kar hankalin ku ya tashi. Dad ya kalle ta ya dafa kanta sai ya ce,  har yanzu jikinta da zafi sosai. "

"Narma cikin kuka ta ce,  Dad kun raba ni da Faruk Win, kun aura min wannan. Na tsane shi bana sonsa na gaji"

"da zama dashi. Kuma ba miscarriege na samu ba, he aborted my baby! Ta faWa tana hawaye."

"Mum a razane ta ce,  What! Abortion?. Narma ta ce,  Yes Mum, da kansa ya saka aka cire cikin ya ce he "

"s not ready to be a father shiyasa ya zubar da cikin. Ya mayar da ni s*x machine, always on it. Ya ™wace wayata, ya canja mana estate, ya canja password na ™ofa saboda kar na fita. Rayuwa nake kamar a prison, na"

gaji! ta faWa tana kwanciya a jikin Mum tana kuka.

"Mum ta kalli Ashraf da yake zaune ya wani basar kamar ba laifinsa ake faWa ba, ta kalli Dad da yake kallon Ashraf Win shima cikin ™unar rai. Mum ta ce,  na faWa maka daman jikina yana bani Narma tana cikin matsala ka ce min ba haka ba. Kana ji ai yanzu, har zubar mata da ciki ya saka anyi, baiwa aka kawo masa ko kuma sonta ne baya yi?. "

"Dad ya kalli Ashraf cikin Sacin rai ya ce,  Ashraf duk abinda ta faWa kana aikatawa?. Asharaf cikin rashin"

"damuwa ya ce,  Dad har yaushe muka yi auren da za a ce an samu ciki? Ni ban shiryawa hakan ba shiyasa aka zubar da cikin. Kuma da take zancen na mayar da ita s*x machine, to dan me na aure ta?. "

"Mum ta buWe baki tana kallonsa jin da yadda yake magana, ta kalli Dad da shima shi yake kallo cikin tsananin takaici da mamaki. Dad ya ce,  Ashraf sakamakon ™aunar da na nuna maka kenan? Sakamakon yarda da amince maka da nayi na baka amanar ΄ata kenan? Yanzu abinda zaka saka min dashi kenan ko?. Ka ajjiye min yarinya kana wahalar da ita shine daidai a wajan ka?. Ashraf ya ce,  Dad ni ban wahalar da ita, itace take wahalar da rayuwarta. Kuma ko yaushe cikin yi min zancen wancan banzan Wan daban take yi, ta kalle ni ta ce ta tsane ni shi take so ba dole raina ya Saci ba. "

"Narma ta sake kallonsa ta ce,  na tsane ka, bana sonka Omar nake so. Kuma Allah ya isa virginity Wina, Allah"

ya isa babyna da ka zubar min. Ka jira sai na yi shari a da kai!.

"A firgice ya taso yazo inda take, ba zato ba tsammani suka ga ya tsinke ta da mari ya ce,  ko wacce irin shari "

"a zaki yi dani baki isa na sake ki ba, ban gama amfanar jikinki ba, ki bari duk sanda na gama sai na& . Marin da ya sauka a fuskarsa ya hana shi ™arasawa. Ya juyo ya kalli Dad da yake wuci cikin Sacin rai ya sake marinsa. Kafin ya dawo daidai Mum ma ta mare shi a Waya Sangaren cikin tsananin tasafar zuciya."

"Kallon su yake yi su duka biyun cikin mamakin da ya hana shi magana. Dad y ce,  Ashe baka da mutunci ban"

"sani ba? Ashe baka da tarbiyya?. A gabana ka ke Waga hannu ka mari Narma? Har kana cewa baka gama amfani da jikinta ba?. Ashraf ya ce,  Dad Narma itace mara tarbiyya ba ni ba, bata girmaman ni a matsayina na mijinta, shiyasa raina yake Saci ko yaushe. "

"Mum ta kalle shi da dan ita ta kasa magana, takaici da ba™in ciki sun yi mata yawan da ta kasa buWe bakinta tayi magana. Narma ta ce,  ba yau ya fara mari na ba Dad ya saba, ya mayar dani kamar slive Winsa ko yaushe abinda yake so yake yi. Dad ya ce,  Tunda abin naka haka ne ka sake ta yanzu, auren ya ™are gabaWaya ai babu dole. Ashraf ya kawar da kai gefe ya ce,  ni bazan iya sakin ta ba, kuma babu wanda zai saka na sake ta. "

"Mum zata yi magana Dad ya hana ta ya kalli Narma ya ce,  Ina passport Winki?. Narma ta ce,  yana wajan"

"shi. Ya kalle shi ya ce,  Wauko min passport Winta. Ashraf ya ce,  bazai yu na Wauko ba, haka kawai ku zo ku Wauke min mata ba, bazan iya Waukowa ba. "

"Dad ji yake kamar ya dinga dukan Ashraf har sai ya fitar masa da jini. Ya danne zuciyarsa ya ce,  Ashraf in baka"

"Wauko min passport Win nan ba sai nayi reporting Winka a ™asar nan bisa cin zarafin ΄ata da ka ke yi. Ya san Dad zai iya, kuma in hakan ya faru abin bazai yi kyau ba dan a ™asar America yake ba a nigeria ba, tsaf zasu W aure shi bayan tara da zasu saka ya biya. Hakan ya saka ya shiga ya Wauko ya mi™a masa har wayar Narma. Dad ya kalli Najwa da ta kasa magana ya ce,  Wauko abinda ki ka san nata ne ku zo mu

Please Login or Register in order to submit comment