ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne ai Jidda, rayuwa na tafiya a hankali, komai yana zuwa mataki-mataki kamar mafarki."""

"""Gaskiya ne, Allah ya cigaba da dafa mana a cikin lamarin mu."""

"""Amin ya rabbi. Ramadan mai zuwa a wannan gidan zaki tashe ni sallar tahajjud"" ya faWa yana ΄ar dariya yana kallon ta. Murmushi ta yi ta ce, ""eh mana, a gidan nan zaka ce ai ba kabarin mu Waya ba"" ta faWa cikin kwaikwayon yadda ya yi maganar wancan lokacin. Tare suka yi murmushi ganin ya saki rai ba kamar Wazu ba sai ta ji daWi dan itama tana so ya shirya da familynsa."

"Omar ya ce, ""taso mu je ki yi bacci ki huta, ni na san kin gaji sosai."" Nayla ta mi™e bayan ya tashi ta ce, ""wallahi na gaji kam, sai ka taimaka min da tausa."""

"""An gama"" ya faWa yana ri™r hannunta suka kwanta."

"Watan ramadan za a shiga, yana so su je umrah amma kuma saboda cikin Nayla ya tsufa dole ya ha™ura amma ya biyawa Didi da mijinta da Marmerh su zasu je. Ko da ya faWawa Nayla ta ce hakan ya yi sosai ya ce mata in sha Allah a shekarar sau uku Didi zata je Saudia har aikin hajji."

"Cigaba ake ta samu a fannin kasuwanci, dan zuwa lokacin inda aka mayar dashi kamar company ana aikin"

"takalman an ™ara girmansa har babban office Omar yake dashi a ciki mai kyau na saukar Saki. Yanzu ya ma daina yin aikin gabaWaya yara ne suke yi, tunda an zamanantar da abin injina ne suke yin komai sai dai abinda ba za a rasa ba."

"A cikin azumin Nayla tana video call da Didi ya shigo, bayan ta kashe ta kalle shi zata yi magana sai ya ce,"

"""Yaushe ne aka ce haihuwarki?."" Nayla ta ce, ""ko yau zan iya haihuwa, a yadda aka ce."" ""Mace suka ce ko?."""

"""Eh."""

"""In kika haifi mace wanne suna zaki saka mata?."" Ta kalle shi ta ce, ""zaka saka mata dai ko?."" Ya ce, ""to wanne ki ke so?."" Nayla ta ce, ""Duk wanda ka ke so, ni bani da zaSi."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""a'a, sai kin faWa."" Nayla ta yi murmushi ta ce, ""Sunan Didi, tunda Didi ta haifa mana Marmerh sai mu haifi mai sunanta."" Ya kalle ta ya yi murmushin jin daWi a zuciyarsa ya ce, ""Allah yana gani in mallakar da ki ka yi min har abinda yake zuciyata ki ka fara gani."" Dariya ta yi ta ce, ""to waye ya sani?."" Ya ce, ""Daman ina so na ji ra'ayinki ne amma daman ni sunanta nake so na saka, Ban sani ba ko kina son saka sunan mahaifiyarki shiyasa na baki dama."""

"Nayla ta ce, ""ni bani da wannan ra'ayin gaskiya, ban sani ba ko nan gaba zan saka."" Ya kalle ta yana taSe ya ce, ""kin cika iyayi ne ai."" Ta yi dariya ta ce, ""na ji, duk da ban kai ka ba."" A washe garin ranar da yamma gab da za a sha ruwa Nayla ta haifi kyakykyawar ΄arta mace a asibitin da take zuwa ganin likita.KRB3P096"

Nana haleema.

"Nayla ta sha wahala wajan haihuwa, hakan ya saka aka yi mata allurar bacci dan ta huta. Omar ya kasa"

"nutsuwa sai kai kawo ya ke yi, gashi ya kasa kiran kowa, bai ma san wanda zai yiwa wayar ba. Omar a asibiti ya sha ruwa, shi dai ya san da aka yi kira ya sha ruwa kawai, bayan nan ya kasa komai. Šakin da Nayla take bacci ya shiga yana kallon ta tana kwance tana bacci, ga babyn ta na kwance a kan baby bed idanunta a buWe tana ta mutsu-mutsu."

"Zubawa Babyn ido ya yi yana kallonta, wai ΄arsa ce wacce ya haifa shima, in ban da Allah waye zai maka haka?. Kamar yadda ya ji ™aunar Marmerh lokaci Waya tana shiga zuciyarsa haka yake jin ™aunarta na ratsa zuciyarsa. Yana so ya dau™e ta amma yana jin tsoro kar ta faWi, sai ya du™a ya shafa fuskarta tare da sumbatarta. Murmushi ya yi yana kallon ta ko ™iftawa idanunsa basa yi saboda ™aunar yarinyar da yake ji a zuciyarsa. Farin ciki yake ji shima yanzu ya zama uba, soyayyarta da ™aunarta ratsa zuciyarsa take yi sosai."

"""Rouhii!."" Nayla ta furta a hankali dan tunda ya shigo ta farka tana kallonsa yana kallon Babyn yana shafata."

"Juyowa ya yi ya kalle ta yaga murmushi take yi, sai dai ta rame a fuskarta, kuma kana kallon ta zaka san bata da lafiya."

"A hankali ya taka zuwa inda take kwance, yana zuwa ta mi™e zaune, yana daga tsaye ya rungume ta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Kuka take yi a hankali, ya zauna yana mayar da kanta ™irjinsa cikin sanyin murya da rauni ta ce, ""Rouhii haihuwa da wahala, Allah ya ji™an iyayenmu Rouhii, Allah ya saka musu da alkhairi."" Bayan ta yake shafawa a hankali bai ce komai ba, dan likitar da ta karSi haihuwar ta faWa masa ta sha wahala sosai."

"Ji yake shima kamar ya zubar da hawaye, ga farin cikin samun Wiya ga kuma tausayin abar ™aunarsa. Tana jikinsa a kwance yana shafa bayanta tana sauke numfashi, ya sumbaci goshinta ya mayar da ido ya lumshe bai ce komai ba itama bata sake magana ba. ˜ofar Wakin aka Wan yi knocking, bai sake ta ba ya juyo yana kallin ™ ofar midwife ta shigo da sallama ta ce, ""Sannu Maman Baby."""

"Nayla ta goge idanunta ta ce, ""Yauwa sister"""

"""Ya jikin na ki?."" ""Da sau™i."""

"""Me ki ke ji yanzu?."" ""Ciwon kai."""

"Ta ce, ""zan ga bp Winki."" Omar ya bata waje ta auna bp Nayla sannan ta ce, ""Bp ki ya hau shine silar ciwon kan, anya baccin nan ya ishe ki?."" Nayla ta ce, ""nayi bacci iya yadda zan iya."""

"""Okay ya kamata ki sake yin bacci kam, yanzu ki ci abinci zuwa anjima sai ki kwanta ki huta. Zan faWawa Dr abinda yace zan sanar dake."" Nayla ta Waga kai ta fita ya dawo kusa da ita ya ri™e hannunta."

"Nayla ta kalle shi a raunane ta ce, ""Wai jinina ya™i sauka."" Ya kalle ta yana shafa fuskarta a hankali, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, ""zai sauka in sha Allah."" Shiru tayi bata ce komai ba, ya Wago fuskarta yana kallon idanunta, ya ri™e fuskarta da hannayensa, ta Wan lumshe ido ta ce, ""Rouhi hannunka sanyi"" ta faWa tana ri™e hannun nasa tana shafa shi a fuskarta."

"Peckimg Winta ya yi a goshi yana kallon idanunta da suka yi kama da na marasa lafiya. Ya gyara mata hular kanta ya ce, ""ki kwantar da hankalin ki, zai sauka."" Ta Waga kai alamun to, ya sake pecking Winta a kumatu yana kallon ta. Tashi ya yi ya jawo gadon babyn ya kalli Nayla da take kallon Babyn ya ce, ""Kin ga kyautar da Allah ya yi mana ko Ashiq?."""

"Nayla a raunane ta ce, ""A lokacin da baby take gab da fitowa daga jikina, na rasa hankalina Rouhi, ina jin kamar"

"na mutu kamar ina da rai, na kasa gane a raye nake ko kuma a mace. Ciwon haihuwa ciwo ne wanda duk mai kwatance bazai iya kwatanta shi ba Rouhi"" ta Wora hannunta akan fuskar babyn ta ce, ""Amma lokacin da ta fito aka zaro ta aka Wora min ita a ™irjina, sai na ji wani farin ciki, na ji soyayyarta na mamaye ko ina na jikina. Rouhi ba a banza uwa take son abinda ta haifa ba, ita kaWai ta san ta yadda ta same shi. Wallahi na daina ganin laifin son da mahaifiya take yiwa ΄a΄anta, ko bata yi niyar nuna soyayyar ba sai ta nuna"" ta faWa hawaye na gangaro mata tunawa da mahaifiyarta."

"Ta dawo da hannunta fuskarsa tana shafawa a hankali ta ce, ""Nayla ce ta haihu yau YaMar, ina ganin abin"

"kamar a mafarki, gani nake kamar zan farka na ganni a gidan Abiyna. Ina ma mahifaiyata tana da rai da na"

"ninka biyayyar da nake yi mata sau babu adadi, domin yau na WanWana abinda ta ji a lokacin da ta haife ni."" Hannunta da yake fuskarsa ya ri™e ya sumbaci hannun, ya shafa fuskarta yana share mata hawaye ya ce, ""Allah ya ji™ansu yasa suna aljanna."""

"""Amin Rouhi, amin ya rabbi."""

"""Ki gode Allah da ya yi nufin kina daga cikin wanda ya yiwa ni'imar haihuwa Ashiq, ki gode masa."" Nayla ta ce,"

"""Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!!."" Murmushi ya yi ya ce, ""Na rasa da wacce kalma zan yi amfani na nuna miki farin cikin da nake ciki a yanzu. Kallo Waya na yiwa ΄armu soyayyarta ta gama mamaye ko ina a zuciyata, nima ji nake kamar a mafarki wai ni Omar ne yau nake da ΄ar da dole a gaban sunanta a saka Omar. Abin mamaki yake bani, amma in na tuna ikon Allah sai na ji sanyi a zuciyata. Tunda Allah ya bani ke nake ganin canji da yawa a cikin rayuwata, yau ni kika haifawa wannan kyakykyawar yarinya a matsayin ΄ata. Na gode Ashiq!."""

"Murmushi tayi ta shafa kansa, ta lumshe ido ta buWe taga ita dai yake kallo ta ce, ""Ni ai ko ban ce ba ka san ina sonka, na kusa mutuwa saboda haihuwar ΄arka"" ta faWa tana mayar da fuskarta kalar tausayi. Dariya suka yi a hankali shida ita ya kalli Babyn ya ce, ""ina so na Wauke ta ina tsoron kar ta faWi."""

"Nayla ta mi™a hannu ta Waukota ta ri™eta a ™irjinta tana kallon ta kafin ta kalle shi ta sake kallon ta ta ce, ""Tabarakallah ma sha Allah! ³ar tamu ta Wauko suffar kamannin mahaifinta, gata nan kyakykyawa kamar babanta. Allah ya sa kar kamanninta su canja, so nake ta zauna da kamannin YaMar Wina."" Ya yi murmushin farin cikin da yake ji yama ratsa zuciyarsa."

"""Assalamu alaikum!"" Aka faWa daga bakin ™ofa suka amsa aka shigo. Dr ne ya shigo ya ™araso ciki ya mi™awa Omar hannu suka gaisa ya ce, ""An samu ™aruwa, Allah ya raya."" Ya amsa da amin ya kalli Nayla ya ce, ""Madam ya jiki? Nurse ta ce har yanzu bp ki bai sauka ba, da alama a asibiti zaki yi bikin sallah."" Nayla ta ce, ""Kaina na ciwo har yanzu."""

"""Saboda jinin naki da bai sauka ba ne, hutu ya kamata ki samu ban da hayaniya, ki yi bacci sosai."""

"Nayla ta ce, ""To."""

"""Amma akwai maganin da za a baki shima zai taimaka miki in sha Allah, sannan ki ci abinci mai ™arin jini."" ""Na gode"" ta furta tana kallon ΄arta. Daga nan ya fita daga Wakin."

"Omar ya ce, ""Na sanar da Abiy, amma bani da number Mama da na faWa mata"" ya faWa yana kallon ta tunawa da kalamanta na kwanakin baya. Nayla bata kalle shi ba ta ce, ""bani wayar na kirata."" Nayla ta karSi wayarsa ta saka number Mama Sa'adatu ta sanar da ita. Ta saka number Twiny dan ta haddace ta faWa mata, Salma kuwa ta san tunda Abiy ya sani zai faWawa Jawad, Jawad kuma zai faWa mata."

"Nayla ta kalle shi bayan ta gama wayar ta ce, ""Ka kuwa sha ruwa? Na ji ana zancen gobe sallah."" Ya kalle ta ya"

"ce, ""na sha ruwa mana Ashiq, amma bayan shi na kasa cin komai."" Ta kalle shi a Wan firgice ta ce, ""baka ci abinci ba? Rouhi azumi fa ka yi."""

"Ya zuba mata idanu yana yawo da ™wayar idanunsa a kanta ya ce, ""Kina kwance zan iya cin wani abu? Wallahi na manta azumi nake yi sai da naga ana ta shan ruwa sannan na tuna ashe na yi azumi. Bani da nutsuwa Ashiq, sai da ki ka farka sannan hankalina ya kwanta."" Ajiyar zuciya ta yi ta ce, ""to yanzu ka je ka ci abinci."""

"""A Ina?."" Sai ta kalle shi ta yi ajiyar zuciya tunawa da bashi da kowa tunda Didi bata nan, Nayla ta ce, ""to tea ka"

"haWa mana ai ka iya, don Allah kar ka zauna da yunwa ka ga babu lallai mu tafi gida yau tunda sun ce bp na bai sauka ba."" Omar ya yi ajiyar zuciya yana kallon ta ko kifta ido baya yi amma bai ce komai ba."

"""Rouhii."""

"""Ashiq."""

"""Ka je ka ci abinci, ni na samu sau™i."""

"""Zan ci, amma sai kin nutsu yanzu ki ka gama kuka fa."" ""Ai na daina, kuma na tabbatar yanzu Mama zata zo."""

"""To ki jira ta zo sai na je, bani Yayata na Wauketa"" ya faWa yana mi™a mata hannu alamun ta bashi babyn. Bashi ita ta yi ya ri™eta yana kallon fuskar yarinyar, zuciyarsa sai ta karye ya ji rauni yana mamaye sa, sai ya ji ina ma shima mahaifiyarsa tana da rai, da yau ta ga abinda Omar Winta ya haifa da zata yi farin ciki sosai."

"Ajiyar zuciya ta ga ya yi ya kalle ta ya ce, ""Da wanne suna zaki kirata? Ko Aisha Winta zaki ce?."" Ta girgiza kai ta ce, ""Sunan Didin zan faWa kai tsaye babu girmamawa? A'a bazan iya ba. Zan kirata da Musliha."""

"Ya Waga gira sama ya ce, ""Meye kuma Musliha? Bazan yarda a sakawa ΄ata sunan wata dabbar ba."" Murmushi ta yi ta kalle shi ta ce, ""ba sunan dabba bane Rouhi. Musliha yana nufin Righteous, good doer, reformer. Sunan larabawa ne irin ku."" TaSe baki ya yi ya ce, ""Ni dai Didi zan ce, babu wani Musliha da zan ce."""

"Ta yi murmushi kaWan kawai bata ce komai ba dan kanta nauyi yake mata. Ganin ta yi shiru sai ya kalle ta ya ga ta Wan kawar da kai gefe ya ce, ""Ashiq ya dai?."" Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ta ce, ""kaina ne ya yi nauyi sosai Rouhi, har bana son motsawa."""

"""Subahanallah! To sun ce ki ci abinci ai, kuma baki ci ba, Wauketa a hannuna na samo miki abinci...Ko kuma barta bara na ajjiye ta da kaina, ki yi addu'a kar na yar miki da ita."""

"Murmushi ta yi kawai bata ce komai, ya ajjiye ta akan gadon ya kalle ta ya ce, ""itama yunwa take ji Ashiq."""

"Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Matsowa ya yi ya dafa kanta, cikin tausayawa ya ce, ""Sannu Jidda, bara na samo miki abinda zaki ci."" Zai motsa ta ri™e hannunsa ta ce, ""ina zaka je? Kaima baka ci komai ba."" ""Kin fi ni bu™atar cin abincin Jidda, haihuwa ki ka yi fa."""

"""Kaima azumi ka yi, gwara ni daman tun safe bana azumin, na kuma ci abinci, amma kai fa?."""

"""Sai kin samu lafiya zan nutsu Jidda, ki bari na samo miki, na san baza su rasa entry a wajan nan ba, Ina zuwa."" Ta sake ri™e shi tana langwaSewa ta ce, ""A'a Rouhi, in ka siyo ka fara ci ka ji?."""

"Saboda ya katse musun nata ya saka ya ce, ""To."" Knocking ™ofar aka yi, Mama Sa'adatu da Ummimi suka buWe ™ofar suka shigo. Nayla ta yi murmushi tana kallon su, Mama ta ™araso ta dafata ta ce, ""Sannu Nayla, shine baki faWa mana ba?"" Sai ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, ""Omar yanzu Nayla tana nan har haihu babu labari?."" Murmushi ya yi kaWan, cikin rashin sabo suka gaisa ta amsa ta ce, ""na Wauka in za a taho asibitin ni za a faWawa sai aka yi min Wanwaken zagaye? Yanzu ya jikin ta?."""

"Omar ya ce, ""kanta yana ciwo sosai, sun ce jininta bai sauka ba tana Sukatar hutu sosai, yanzu ma abinci aka ce taci."" Mama ta ce, ""to ai an taho da ruwan zafi, daman na san dole za a bu™aci ta sha koda tea ne"" ta kalli Ummimi da take gaban Babyn tana yi mata hoto ta ce, ""Ummimi ke ta ΄a kike yi ni ga tawa ΄ar bata jin daWi, haWo mata tea tasha sai ta shayar da ita. Mi™o min ita."" Mama ta faWa. Ummimi ta kawo mata babyn sannan ta haWa mata tea Win kamar yadda Mama ta ce ta bawa Nayla."

"Nayla ta ce, ""Mama shima ko iftar bai yi ba har yanzu, nace ya je yaci abinci ya™i."" Mama ta kalli Omar da yake duba waya ta ce, ""Omar baka ci abinci ba? Maganar ™arfe tara na dare ake yi fa yanzu?. Ummimi maza yi serving Winsa da abincin da na taho dashi, wannan ai ba daidai bane, in rashin abincin ya saka ka faWi fa?."""

"Omar ya ji wani irin banbara™wai, wai wata mace ce bayan Didi da Nayla da suka damu ya ci abinci har take cewa kar ya faWi. Sai yaji girman matar ya sake ™aruwa a idanunsa, dan bayan Didi ds Nayla bashi da mai damuwa dashi. A hankali ya ce, ""Babu komai, zan je gida yanzu."" Nayla cike da shagwaSa ta ce, ""Allah Mama in ya je ba ci zai yi ba, to waye ma zai masa girkin..? na san shi ya gaji ba yi zai yi ba, don Allah zauna ka ci ka ji!"" Ta faWa tana kallon sa kamar zata yi kuka."

"Mama ko a jikinta da yanayin da Nayla take yi masa magana ta kalle shi ta ce, ""babu inda zaka je ai, Ummimi ki"

"zuba masa har tea Win ya sha."" Omar ya kasa magana yana jin yadda take magana cikin bada umarni, to ya zai yi mata? Kamar babar matarsa take dole ya yi abinda ta ce. Ya kalli Ummimin ya ce, ""iya tea Win ma ya isa."""

"Tea Win ya karSa ya koma ya zauna daga can ™arshen Wakin ya zauna dan gaskiya bazai iya fita ya bar Nayla ba. Mama ta saka aka bawa Nayla dafaffen naman rago da aka shi da romo mai yaji kaWan ta ce ta ci. Ta kuwa ci Win amma ta fi shan ruwan, ta ajjiye bayan ta gama ta Wora mata Babyn a cinya ta ce, ""To bismillah, ki shayar da ita yunwa take ji itama."" Nayla kamar zata yi kuka ta kalli Omar da ya kalle ta, suna haWa ido yayi mata wata inkiya da ido yana sipping tea da yake hannunsa yana ™ifta idanunsa. Dariya ta kama Nayla, amma sai ta Wauke ido daga kansa ta kalli Mama ta ce, ""Mama ai ban iya ba."""

"Shigowar Jidda Wakin ya hana Mama magana, ta taho ta rungume Nayla ta Wauki Babyn tana kallonta ta ce, ""kin ci amanata."" Nayla ta ce, ""yi ha™uri."" Suka gaisa da Mama dan ita bata ma ga Omar ba dan yana can ™ arshe sai ka kula zaka ganshi dan Wakin yana da girma.KRB3P097"

Nana haleema

"Mama ce ta nunawa Nayla yadda zata shayar da ita, Nayla ta yi yadda tace sai zuba shagwaSa take yi ita zafi take ji, ita ta gaji waye-waye. Duk Waga idon da zata yi ta kalle shi sai sun haWa ido, da sun haWa ido kuma sabuwar inkiya zai yi mata wacce ita dashi kaWai suka san me hakan yake nufi. Mama bata ™yaleta ba sai da ta tabbatar yarinyar ta ™oshi sannan ta karSeta aka kwantar da ita. Jidda hoto ta dinga yiwa yarinyar ta tura family group Winsu."

"Omar bai jima ba sai ya fita, fitarsa Jidda ta gani dan bata san yana nan ba. Mama ta saka Nayla ta yi"

wanka ta saka doguwar riga wacce Mama ta taho mata da ita ta kwanta a kan gadon bacci ya sake Wauketa. Duk suka fito waje saboda ta samu ta yi baccin yadda ya kamata.

"Omar sai da ya koma ya ga kiran Didi WhatsApp call, ya yi murmushi ya kirata ta ke tambayar mai jego ya"

"ce ya barta asibiti. A gaggauce ya shirya shima, ya yi wanka ya canja kaya ya dawo asibitin dan bazai iya zaman gidan ba sam."

"Washe gari ranar sallah, ji yake ko sallar ma bazai iya zuwa ba, amma ganin Mama na kula da ita sosai sai ya je"

"ya dawo daga masallacin kai tsaye ya dawo asibitin. Da yake asibitin kuWi ne akwai ma'aikata suna ta aikinsu, ya shiga Wakin Nayla da sallama a nan yaga jama'a sun ™aru harda waWanda bai sani, abinda ya bashi mamaki ganin dangin mahaifiyarsa, ya bisu da kallo dan ya san aikin Didi ne. Gaisawa kawai suka yi ya fito ya zauna sai ga Mama Saroot da Mama Zainab sun fito suka kalle shi a raWaWe suka ce, ""Omar an samu ™aruwa, Aisha ce take sanar damu, Allah ya raya."""

"""Amin. An yi sallah lafiya?."" Mamaki ya hana su magana suka zubawa juna ido, da™yar Mama Zainab ta ce, ""Lafiya lau, Allah ya raya abinda aka samu, ance sunanta Aisha ko?."" Ya Waga kai Mama ta ce, ""Allah ya raya mana, yasa ta yi halin mai sunanta."" Ya amsa da amin sai suka samu ™arfin guiwar zama a asibitin dan suna tsoron kar ya yarfa su a gaban sirikai."

"Sai da aka kwana biyu a asibiti sannan aka bada sallama, da kansa ya ri™o hannun Nayla suka fito tana takasa a hankali Babyn na hannun Mama Sa'adatu, sai Mummy Maman su Salma. Mota suka shiga aka wuce gidan sa kai tsaye."

"Kai tsaye sama aka saka ta ta hau yadda baza ta sake sakkowa ba, duk wanda ya zo sai dai ya hau saman."

"Tana falon a zaune, bayan Mama ta saka ta yi wanka ta shirya cikin atamfa baza ka ce ita ta haihu ba. Nayla ta saka Jidda ta Wauko kayan Babyn ana Waurawa, baby beds da baby swing aka ajjiye a falon. A ranar su Mama suka zo daga Kaduna harda Abiy da Salma da kuma Jawad da su Jalila."

"Farin ciki a wajan Nayla sai da tayi kuka, ta ri™e Abiy dan bai taSa zuwa gidan ta ba sai yanzu. DaWi take ji da ta gashi a gidanta, ta saka aka yi musu hoto shida ita duk ta ruWe kamar bata taSa ganinsa ba. Bai jima ba ya tafi bayan ya bada kayan baby da kuma kayan ita kanta Naylan. Mama kuwa basu tafi ba sai dare, Salma ma sai dare sosai sannan suka tafi. Jalila kam ta ce kwana zata yi suna tare tana ri™e da Musliha tana yi mata hoto."

"Mama Sa'adatu bayan tafiyar Maman Kaduna ta kalli Nayla ta ce, ""Nayla zan koma gida yanzu, amma gobe da"

"safe zan dawo. Zan zauna har sai an yi suna daga nan Baba Hafsatu zata zo ku cigaba da zama har ki samu lafiya."" Nayla ta ce, ""To Mama."""

"""Ki kula sosai, ban da yawan zirga-zirga kin ga baki da lafiya kuma an miki Winki. Wai kin ™aru a wajan haihuwar ne har aka yi miki Winki?."" Nayla ta girgiza kai tana turo baki ta ce, ""A'a, kawai an yi min ne, cosmetics ne."" Mama ta ri™e haSa ta ce, ""Gaskiya ne ΄an daWi miji, kin kyauta."" Nayla ta yi murmushi Mama ta tafi aka barta da Jalila da Ummimi."

"Nayla falonsa ta shiga da Musliha a hannunta, ta same shi yana zaune a akan kujera yana duba waya, ganinta"

"sai ya ajjiye wayar ya yi ajiyar zuciya ya ce, ""Wai haka ake haihuwar a hana ka ganin matarka? Zo ki zauna"" ya faWa yana tashi tsaye ya karSi Musliha sannan ya zaunar da ita. Nayla

Please Login or Register in order to submit comment