ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jinsa!."

Babban abinda yake Waure masa kai shine in dai son Nayla yake yi ita Narma me ya yi mata a baya? Sonta ya yi

ko tausayinta yaji ko kuma meye bai sani ba.

"Hankalinsa ya gama kaiwa ™arshe wajan tashi, ya tsayar da tunaninsa waje Waya ya kuma yarda da gaske dai Nayla yake so ba wai da wasa ba. Abin ka ga soyayyar farko, in yana tunaninta jikinsa har karkarwa yake yi saboda azabar da zuciyarsa take yi masa, fatar jikinsa har Waukar zafi take yi saboda yanayin da zuciyarsa take ciki. Nauyi ™irjinsa yake yi masa sosai, har ya kai ya kawo in ya motsa yana jin zafi a ™asan zuciyarsa. In ya yi tari sai ya ji numfashinsa yana neman tsayawa cak, sai ya ja numfashi da ™arfi sannan yake samun sassaucin nauyin da yake yi."

"Ranar asabar bayan sallar azhar ya kasa jurewa, ya rasa ya zai yi ya kasa cin abinci tun safe. Ya haWa tea amma ya kasa sha ruwa kawai yake zubawa cikinsa. Ya kasa cin komai, baya sha'awar cin komai balle ya nema ya zuba a cikinsa, duniyar yake ji ta yi masa zafi tana juya masa. Nayla kaWai yake so ya gani, itace abincin da idanunsa da zuciyarsa take marari, muryarta yake so ya ji ta furta sunan da ta saba faWa masa. Ya tabbatar da ya ji wannan suna daga bakinta duk abinda yake ji a zuciyarsa zai daina ji. Ganin yana neman kashe kansa da tunani sai ya kira Didi a waya dan tunda tazo basu sake magana ba, tana Wauka kafin su gaisa ya ce, ""Didi meye abu na gaba?."""

"Didi ta ce, ""Ya naji magnarka haka, Omar ko ka je asibiti a duba ka?."""

"""Didi gab nake da zaucewa wallahi, tafasa jinina ake yi kullum"" ya faWa a sanyaye."" Didi ta ce, ""Allah ya kawo mafita Omar."""

"""Ina tambayarki, meye abu na gaba?."" ""kamar me kenan?."""

"""A ina zan sameta?."" ""Ita wa kenan?."""

"""matata!"" Ya faWa kansa tsaye ba tare da wani tunani ba."

"Didi ta yi dariya mai sauti ta ce, ""ban gane abu na gaba ba."" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, ""Me aka ce zan yi?."""

"Didi ta ce, ""akan dawowarta?."" ""Uhum."""

"""Gidan iyayenta zaka je."""

"""Ina ne gidan? Ki tura min address Win gidan zan je."""

"Didi ta ce, ""Da gaske ka ke?."" Omar ya ce, ""kin san ba wasa nake yi ba ai, zan je ina bu™atarta tare dani. Na yarda da duk abinda ki ka faWa, da gaske ina matu™ar sonta Didi, Ina yi mata son da bana yiwa kaina. Didi ko abinci na kasa ci, kamar ana gasa zuciyata haka nake ji. Kullum da zazzaSi nake kwana, damuwa ta yi min yawa, zuciyata ta kasa jure wannan yanayin. In na sake na kai gobe ban ganta ba wallahi zaki iya zuwa ki Wauki gawata, ni kaWai na san yanayin da nake ciki Didi, na kasa jurewa!"" Ya faWa a hankali kamar zai yi kuka."

"Didi ta yi ajiyar zuciya cikin farin ciki tace, ""Alhamdu lillah! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana,"

"ko yau Allah ya Wauki raina ya cika min burina. Omar yana son Nayla, Allah na gode maka."" Shiru ya yi bai ce komai ba Didi ta ce, ""Yaushe hakan ya faru? Yaushe ka fara jinta a zuciyarka?."""

"Omar ya yi ajiyar zuciya shima ya ce, ""Ban sani ba Didi, ni kaina bazan ce ba. Abinda na sani kawai soyayyarta"

"ba yanzu bace, Didi ta jima a raina, ban fahimta bane sai yanzu. Wallahi Didi ina sonta, ina ™aunarta sosai."" Didi cikin zumuWi ta ce, ""To yanzu yaushe zaka je?."""

"""In anjima, amma ina so mu je tare dake, Ina jin nauyin mutanen nan sosai, ban taSa jin nauyin mutum kamar yadda nake jin nauyinsu suda mahaifinta ba, lokacin da mu ka je Kaduna kasa magana nayi saboda girmansa da naji a idona da zuciyata."""

"Didi ta ce, ""bazan je ba, kai kaWai zaka yi faWan ka, in har da gaske kana sonta kai kaWai zaka je ka dawo da ita. Amma ka kwana da sanin babu lallai ta dawo a zuwan farko."""

"Omar ya Wan murmusa ya ce, ""Hmmm Didi kenan. A yadda nake ji a zuciyata ko da za a shekara bata dawo ba indai zata dawo zan iya jira."" Didi ta yi murmushi ta ce, ""Gaskiya ne Omar, Allah ya tabbatar da alkhairi ya daidaita ku."""

"""Amin Didi. Ki tura min address Win."""

"""An gama angon Nayla."" Murmushinsa ta ji mai matu™ar sauti kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce, ""Kin san an kawo min motar da na siya? Kwanan ta huWu kenan, da yake bana cikin nutsuwa ban ma ganta ba sai jiya da daddare."""

"Didi ta ce, ""ma sha Allah Omar! Allah ya sanya alkhairi. Wallahi shigowar Nayla rayuwarka alkhairi ne, daga"

"lokacin da ta je Saudia na ce ta yi maka addu'a daga lokacin Narma ta shigo rayuwarka. Shigowar Narma rayuwarka kamar farkar da kai daga dogon baccin da ka ke yi ne."""

"Murmushi ya sake yi ya ce, ""Didi!."""

"""Na'am angon Nayla."" Murmushi ya sake yi wanda ya nuna mata ya ji daWin sunan har cikin zuciyarsa ya ce, ""ina jin daWi in kika faWi sunan nan, amma yanzu dai ki faWa min inda zan je kin san bana son Sata lokaci."""

"Didi ta yi dariya ta ce, ""To yanzu kuwa."""

"""Basai na siyi komai ba?."""

"""Zaka iya siya mana, koda kayan marmari ne zaka iya siya ka kai musu duk girmamawa ce."""

"""To"" ya amsa a ta™aice. Kwatancen gidan Daddy tayi masa ya yanke wayar da niyar in an idar da sallar la'asar zai je ya samu Daddy dan ya dawo da matarsa."

Omar zai je bikon Nayla KRB3P035

Arewabooks@nanahaleema11.

"Omar cikin ™arfin guiwa da karsashi ya shirya cikin manyan kaya, ya saka shadda kalar golden mai kyau sai W aukar ido take yi, sabuwa ce dal bai taSa sakata ba, tana cikin wanda ya Winka gab da Nayla zata tafi dan shi mutum ne mai son Winka suttura. Bayan ya kammala shiryawa ya saka hula ya tsaya yana kallon kansa."

"Samun kansa ya yi da murmushi cikin mamaki wai shine yake wannan zumuWi akan wata mace, tabbas ya amince da maganar Didi ba son Narma ya yi ba, dan a cikin kashi goma na abinda yake ji yanzu ko kashi Waya bai ji ba a lokaci Narma. Wayarsa ce tayi ™ara ya san bazai wuce Didi ba yana dubawa yaga itace ya Wauka ya saka a kunne."

"Da to kawai ya amsa sai ya kashe sai ga video call Win Didi ya shigo. Šauka yayi daga can Sangaren Didi ta ce, ""kai ma sha Allah angon Nayla, gaskiya ka yi kyau sosai, daman Ina ta fargabar kar ka ce zaka je da ™ananun kaya shiyasa na kira ka."""

"Murmushi ya yi mai sauti ya ce, ""Haba Didi! ya za a yi na saka ™ananun kaya?."" ""Ai na san hali ne."""

"""Lokacin da bana so kenan, yanzu kuwa ai ina so."" Didi tayi dariya ta ce, ""Gaskiya ne Omar. Ka yi kyau wallahi, Allah ya dawo da kai Lafiya."

"Duk abinda ya faru ina jiran labari, Kuma don Allah kar ka je ka ce zaka zauna akan kujera ka yi Warea-Ware, gidan sirikan ka ne dai."""

"Fuska a sake ya ce, ""To Didi. Baki zo kin ga motar ba."" Didi ta ce, ""kai zaka kawo min ai, kai kuma yanzu"

"hankalin ka baya jikinka, ka gama da dawo mana da Nayla in ya so komai ya biyo baya."" Murmushi ya sake yi ya ce, ""yaushe zaki haihu ne?."" Didi ta ce, ""na kusa, ka cigaba da yi min addu'a Allah ya sauke ni Wafiya."""

"""In sha Allah."" Didi ta ce, ""ka je ka dawo."" Yanke wayar ya yi ya fito daga Wakin yana kallon falon."

"Zuciyarsa ya ji tana bugawa sosai ya dafe saitin zuciyarsa yana jan numfashi, bai san me zai tarar ba in yaje"

"shiyasa yake fargaba. A bayyane ya ce, ""Allah ka bani ikon iya sarrafa kaina koda wani abun zai Sata min rai."" Ya furzar da iska ya fito yana kallon sabuwar motarsa da take ajjiye. Motar mai kyau ce Sa™a wuluk zubin matasa ΄an kwalliya kamarsa sai Waukar ido take yi."

Tunani yake ya je a motar ko kuma ya kira Bashir ya kai shi a machine?. Katse tunanin ya yi ya kira Tk ya ce yazo

"gate Win gidan. Ba jimawa yazo yana ganin Boss Win na su sai ya yi murmushi ya ce, ""Allah ya biya Damisa, irin wannan kyau haka, gaskiya ka yi kyau sosai."""

Murmushi yaga ya yi amma bai ce masa komai ba. Tk ya yi mamaki sosai dan kwana biyu ko fuska baya saki

"balle murmushi, lallai yana cikin tsananin farin ciki sosai. Motar ya buWe ya kalli Tk ya ce, ""BuWe min gate Win."" Tk ya buWe gate shi kuma ya fita da motar bayan ya bawa Tk key Win gidan dan ya kulle, Tk bayan ya kulle ya dawo masa dashi sannan ya ja motar da bismillah ya bar unguwar."

Kasancewar ranar babu aiki Nayla suna gidan Daddy ita da Salma da Ummimi. Ta ware sosai tana harkokinta

"duk da akwai abinda yake damunta daga zuciya amma bata bari ya yi tasiri, musamman da aka Wauki wannan lokacin Omar bai zo ba sai ta sake ™o™arin kawar da tunaninsa dan ta san bazai zo ba. Daman ta san ko number ta bashi da ita balle ta yi tunanin in bai zo ba zai yi mata waya, wannan ya saka ta daure ta danne zuciyarta ta cigaba da addu'a tana shiga cikin ΄an uwa ana hira da ita."

Suna zaune a falon Daddy har da Daddyn kasancewar ranar asabar ce yana gida. Hira kawai suke yi tana cikin

"su tana dariya, Mummyn su Salma tana basu labarin ™uruciyar baban yayan su Salma wanda ya kasance mai tsare gida baya son raini."

"Abba ne ya yi sallama ya shigo falon yana cewa, ""Nayla tun daga bakin ™ofa nake jin muryarki."" Dariya tayi a tare suka ce, ""Abba sannu da zuwa."" Ya amsa suka gaisa gabaWaya."

"Abba ya kalli Daddy ya ce, ""na je gidan Hajja sai take shaida min kwana biyu baka da lafiya, shine na shigo mu"

"gaisa."" Daddy ya ce, ""Hajiya Hajja kenan, mura ce fa kawai take damuna, amma kowa sai da tace masa bani da lafiya.Yanzu Sa'adatu ma ta shiga ciki."" Abba ya ce, ""Ai mura ciwo ce babba Yaya."" Ya kalli Nayla da take yiwa Salma raWa a kunne ya ce, ""Nayla kina da aure fa, meyasa ki ke yawo ne haka? Jiya ma na ga motarki a kan titin maiguuri road, ki daina yawo ba tare da izinin mijinki ba, har yanzu da aure a kanki."""

"Nayla ta tsayar da dariyar da take yi ta sunkuyar da kai ta ce, ""Abba gidan Twiny na je jiya."" Abba ya ce, ""amma"

"a satin nan kin je gidana ai, sannan ga aiki da kike fita kullum, yau kuma ga ki a gidan nan, gobe kuma ki ce kin tafi gidan Khabir. Matar aure ce ke ki daina biyewa su Salma."" Nayla ta ce, ""To Abba."""

"Daddy ya kalli Salma ya ce, ""ke wai Salma me yake fito dake kina barin Hajja ita kaWai ne?."" Salma ta ce, ""Daddy duba ka nazo yi fa."""

"""To ki yi gaggawa ki gama ki koma gida."" Abba ya ce, ""Ku shiga ciki Salma."" Duk gabaWaya suka tashi daga main falo suka shiga ciki gidan."

"Bayan fitar su Abba ya kalli Daddy ya ce, ""har yanzu mijin Hauwa bai yi magana ba? Ni fa na gaji da jira wallahi,"

"kawai a raba auren nan kowa ya huta."" Daddy ya ce, ""Bai zo ba Ali, abinda yasa bana so ayi gaggawa saboda Nayla tana son mijinta har yanzu, babarta Sa'adatu ta ce tana son mijinta wani dalili ne ya saka take cewa a raba auren."" Abba ya ce, ""Zancen banza kenan, meye amfanin soyayyar da take masa ana irin wannan abum?."" Daddy ya ce, ""mu bi komai a hankali Ali."""

"""Assalamu alaikum, Alhaji barka da yamma"" aka faWa daga bakin ™ofar falon. Daddy ya ce, ""Wa'alaika Salam, Aminu shigo mana."" Aminu ya shigo ya dur™usa ya ce, ""Alhaji ba™o ka yi, ya ce don Allah nazo na sanar da kai."""

"Daddy da mamaki ya ce, ""Ba™o kuma? Yana Ina?."""

"""Yana waje dan bai shigo gidan nan ba."" Daddy ya ce, ""ya sunansa?."" Aminu ya ce, ""ya ce sunan shi Omar, wani saurayi haka fari kyakykyawa."""

"Daddy ya kalli Abba dan tashin farko Omar Win Nayla ne ya zo zuciyarsa, ya kalli Aminu ya ce, ""jeka ka shigo dashi, ka rako shi har falon nan."" Aminu ya amsa ya fita da sauri. Daddy ya kalli Abba ya ce, ""ka ga abinda nake faWa maka, mu bi komai a sannu gashi ya kawo kansa."" Abba ya ce, ""gwara da Allah ya sa ina nan, dan na san halin ka baza ka buWe masa wuta yadda ya kamata ba, tunda ya same ni kuwa ya haWu da daidai shi."" Daddy ya yi murmushi a lokacin Aminu ya yi sallama suka shigo."

"Omar akan carpet ya zauna kamar yadda Didi tayi masa nasiha, Aminu da ya rako shi ya fita ya barsu su uku a"

"zaune. Daddy ya kalli Omar da fara'a ya ce, ""Malam Omar barka da zuwa."" Omar kuwa tunda ya shigo falon nauyi da girmansu ya gama mamaye masa zuciya, ya rasa abinda zai yi balle ya iya magana. Da™yar ya iya furta, ""Barkan ku da yamma."" Daddy ya mi™a masa hannu ya ce, ""bismillah ,mu gaisa."" Hannu ya bayar kamar yadda Daddy Win ya mi™o masa hannu, suka gaisa harda Abba da yake ta kallonsa dan gani yake Omar ya canja masa."

"Daddy ya ce, ""Ya aiki ya kuma Yayarka?."" Omar ya ce, ""Alhamdu lillah."""

"""Ma sha Allah haka ake so."" Omar ya yi shiru ya rasa ta inda zai fara, shi fa wallahi bai san ta inda zai fara bai ma san me zai ce ba, sunan da zai yi amfani dashi wajen kiran Daddyn ma bai sani ba hakan ya saka shi yin shiru."

"Abba ya kalle shi ya yi murmushi ya ce, ""Malam Omar ka yi shiru baka ce komai ba."" Omar ya Wan sauke numfashi ya ce, ""Alhaji ayi ha™uri da abinda ya faru."" Daddy ya yi murmushi ya ce, ""Omar ai mu ba laifi aka yi mana ba, Nayla ta dawo ta ce ita ba faWa ku ka yi ba kawai tana so ka saketa ne ta gaji da zaman auren."""

"Omar ya lumshe ido ya tsani kalmar sakin nan da ake faWa, in dai za a ambaceta sai yaji kamar an soka masa mashi a zuciyarsa. Ya buWe ido ya ce, ""laifina ne duk abinda ya faru."" Abba ya ce, ""yanzu kana nufin kazo a baka ita a karo na biyu kenan?."" Omar ya Waga kai alamun eh kana ya ce, ""abinda nake nufi kenan."" Daddy ya ce, ""Omar bamu san abinda ya saka Nayla ta ce haka ba, baza mu yi gaggawar cewa zata dawo wajanka ba dan wata™ila tana da dalilin da baza ta iya faWa mana meye shi ba."""

"Omar ya sauke numfashi kaWan ya ce, ""laifina ne kamar yadda na faWa, ni ba mutum ne mai ™arya ba zan sanar daku gaskiyar abinda ya faru. Da farko ban karSi aurenta ba gaskiya, a ranar da aka sanar dani in zaku tuna na furta bana so kafin yayata ta ce zamuyi magana a keSance, itace tayi min dole har na amince da auren amma ba dan ina so ba. Itace ta yi min dole ta saka nayi mata al™awarin bazan taSa rabuwa da ita ba koda mahaifinta ne zai kira ni ya ce na rabu da ita, hatta zama a gidan da nake yi Didi ce tayi min dole ba dan ina so ba. Ina da wahalar sabo, shiyasa abubuwa suka dinga faruwa har ta kai ga ta kasa jurewa ta ce zata dawo."""

"Abba ya ce, ""kace da gaskiyarta gwara ayi sakin a huta, meye amfanin zama da wanda baya sonka bai karSi aurenka ba?. Har gwara ace itace take zaune da kai bata sonka da ace kaine baka sonta, ka ga zaman da ku ka yi zaman cutuwa ne da Sacin rai da kuma ba™in ciki."" Daddy ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, ""gaskiya ne, tunda har abin ya zama haka yanzu ka rubuta mata takardar sakin kawai zai fi alkhairi."""

"Omar ya Soye ruWaninsa ya nutsu sosai ya ce, ""A'a Alhaji, bana tunanin ko duniya zata taru ta ce na saketa zan iya sakinta, ko meye zai faru a yanzu sai dai ya faru amma wallahil azim bazan iya rabuwa da ita ba. A yau na zo da kaina da cikin umarnin kaina ba dan umarnin yayata ba, na ji a raina in ban bata dawo gidana ba bazan sake yin farin ciki ba a duniya. Alhaji da gaske nake wannan zuwan na kaina ne ba na umarni ko dole ba, a shirye nake na zauna da ita zama na har abada. Na san mahimmacin da take dashi a rayuwata, a baya ma ban gama fahimta ba shiyasa har hakan ya faru, amma a yanzu na gane mahimmacin da take dashi a rayuwata bazan iya rabuwa da ita ba. Ina sonta, ina ™aunar zama da ita har abada."""

"Daddy ya yi murmushi domin kalaman Omar sun burge shi sosai, kai tsaye yake magana babu ruwansa da wani"

"kara ko kunyar surukai. Daddy ya ce, ""in na fahimce ka yanzu ka amince da auren, sannan zaka zauna da ita a matsayin matarka?."""

"Omar ya girgiza kai ya ce, ""haka ne."" Abba ya ce, ""kuma ba umarnin ta sake baka ba kuwa? Anya ba dole aka"

"sake yi ba?."""

"Omar ya yi murmushi ya ce, ""ko Waya, itama ta san ta gama yi min dole a duniya. Da kaina nazo kuma saboda son raina ba dan ita ba, nakasa jurewa ne kawai, duk yadda na so na jure rashinta na kasa, duk yadda naso na ™aryata kaina akan ina ™aunata na kasa. In da dole tayi min da tare zamu zo da ita, kuma baza ta taSa bari nayi magana ba, kafin nayi magana Waya tayi goma saboda tsoron kar na furta abinda bata so. Kamar yadda na ce ni ba mutum ne mai Soye gaskiya ya faWi ™arya ba, wallahil azim da ace bana ra'ayi labarina ma baza a sake ji ba balle har nazo da kaina. Wallahil azim ina sonta, babu halittar da nake so a duniya kamar yadda nake sonta."""

"Abba ya yi murmushi mai sauti cikin jin daWin kalaman Omar ya ce, ""Haka ne Malam Omar, na amince da gaske yanzu kana son Nayla ba dole aka yi maka ba. Amma kamar yadda aka baka dama a wancan lokacin aka zauna dakai aka tambayeka ra'ayinka akan auren itama za a bata dama, a lokacin baya ba a tambayeta ba saboda muna ganin kaine ba a kyautawa ba an baka aureta ba tare da ka sani ba. Itama zamu bata dama kamar kai, in tana ganin zata iya cigaba da zama da kai shikenan, in baza ta cigaba da zama da kai ba Omar babu wanda zai yi mata dole, sai dai mu ce ka yi ha™uri.""KRB3P036"

"Omar ya Wago a hankali ya kalli Abba, ya sake sauke kansa ™asa yana maimaita kalmar sai dai mu ce ka yi ha™ uri, bai san ko duniya ce zata taru a kansa ba bazai saki Nayla bane shiyasa yake faWar haka. Ya yi ajiyar zuciya amma bai ce komai ba dan ™irjinsa bugawa yake yi in ya tuna su Win iyayenta ne. Daddy ganin yanayin da ya shiga sai ya murmushi ya ce, ""na amince a yanzu baza ka bar Nayla ta yi kuka ba Omar, tabbas a yanzu na amince a zuciyata Nayla tayi aure ta auri wanda yake ™aunarta. Amma kamar yadda ™anina Ali ya faWa maka za a bata dama kamar yadda aka baka, daman mahaifinta ne ya yanke hukunci a kwanakin baya shiyasa mu ka tambaye ka dan kaine ba a kyautawa ba, amma yanzu za mu tambayeta mu ji me zata ce."""

"Omar ya girgiza kai cikin rauni ya ce, ""To. Amma zamana da ita a wannan lokaci bazai taSa zama na cutarwar ba balle har ta kai ga dawowa gida ba, ko a baya ban taSa cutar da ita ba balle kuma yanzu da na san mahimmacinta. Sai ka rasa abu ka ke gane darajar da yake dashi da adadin ™aunarsa da ka ke yi masa, bazan sake bari hakan ta faru ba a yanzu ko a nan gaba."""

"Suka yi dariya tare Abba ya ce, ""Dakyau Omar! Haka nake son mutum mai faWar asalin abinda yake zuciyarsa, bana son mutum bai Soye gaskiya ya faWi ™arya dan farantawa wani rai. Tabbas ba dan na san iyayenka ba da sai na ce ni na haife ka."""

"Omar ya murmusa kaWan amma bai ce komai ba. Daddy ya ce, ""Tunda yanzu ka amince da auren naku za ka karSi shi hannu biyu, maganar gwajin jinin da mu kayi tun kwanakin baya yanzu muna da bu™arta shi gaskiya."" Omar ya sauke numfashi kaWan ya ce, ""in sha Allah za ayi."""

"""Kasancewar ka mai gaskiya na baka dama ka je duk inda ka ke so ayi maka ka kawo min, na san baza ka Soye min komai ba, dan na amince da kai Wari bisa Wari."" Omar ya sake yin murmushi, sosai yake jin girman mutanen a idanunsa, yadda suka karSe shi hannu biyu, suka sakar masa fuska lamarin ya yi masa daWi."

"Daddy ya ce, ""Naylan tana gidan nan, sun zo duba ni ita da Mamanta saboda na Wan yi fama da mura. Yanzu zan turo maka ita ku gaisa kafin gobe in Allah ya nuna mana mu zauna da ita mu tattauna dan mu ji ra'ayinta."""

"BuWe baki yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Abba da ya kula da hakan sai ya ce, ""kar ka damu Omar,"

"faWi abinda yake bakinka."" Omar ya ce, ""in da dama a tambayeta a yau.....don Allah"" ya ™arasa faWa murya a ™ asa. Daddy ya yi murmushi haka Abban ma, gabaWaya Omar Win ya canja musu ya koma wani daban kuma ya basu nishaWi matu™a."

"Daddy ya ce, ""ka kwantar da hankalinka, mu jira gobe in Allah ya kaimu."" Omar ya sauke kai ™asa bai ce komai ba amma ba haka ya so ba. Abba ya ce, ""ka kwantar da hankalinka kaji Omar, Ina bayanka nima a yanzu, zan taya ka ya™in dawo da Hauwa in sha Allah."" Murmushi ya sake yi amma bai kuma magana ba."

"Daddy ya Wauki waya ya saka a kunne ya ce, ""ki turo min Nayla parlour."" Babu jimawa Nayla ta shigo da sallama, bata lura da Omar ba amma gabanta ya faWi sosai ba tare da san dalili ba. Kusa da Daddy ta je ta ce, ""Daddy gani."" Daddy ya kalle ta ya ce, ""mijinki ne yazo, gashi a zaune ku gaisa"" ya faWa yana tashi tsaye, Abba ma ya tashi suka fita zuwa harabar gidan."

"Nayla tsam tayi a inda take zaune ™irjinta ya buga sosai, lumshe ido tayi domin kuwa sai yanzu ta sha™i ™ hamshin turarensa mai matu™ar sanyi da kashe mata

Please Login or Register in order to submit comment