ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

""idon nan naka ka daina buWe su, wani iri nake ji wallahi."""

"""FaWa min me ki ke ji."" Bata ce komai ba ya canja salon maganar ya hanata magana ya karkata zuwa wani fage daban. Nayla ta ce, ""YaMar!"""

"""Shiii!"" Abinda ya furta kenan dole ta yi shiru ta sakar masa amma ta gaji matu™a."

"Har azahar suna tare ya hanata motsi, abinci ma order ya yi musu a wajan leemars_delicious, rider ya kawo"

musu ya je ya karSa ya dawo.

"A Waki suka ci abincin tana jikinsa baya so ta motsa ko ina sai tare dashi. A lokacin ne ya fara bata labarin abubuwan da suka faru a China da wanda ya haWu dasu da abinda ya siyo da sauran su. Jakar da ya dawo da ita ya buWe ya Wauko mata doguwar riga mi™a mata ta karSa tana dubawa. Kallon sa ta yi shi kuma ba ita yake kallo ba kaya yake fitowa dasu, rigar ta yi kyau sosai amma bata da maraba da babu komai a jikinka, kuma doguwa amma ta banza ce. Ta girgiza kai ta ajjiye tana ayyana yana so ya mayar da ita ΄ar iska ne kawai."

"Duk tsarabar da ya siyo mata irin kayan ne, sai wani turare mai bala'in ™hamshi da ya ajjiye mata ya ce, ""turaren ya yi min daWi shiyasa na siyo miki, ina so na ji ™hamshinsa a jikinki kawai."""

"Wani bangle ya Wauko a cikin cover sa ya ri™e hannunta ya Wura mata yana murmushi, ya kalle ta yaga sai murmushi take yi da alama abin ya burgeta ta ce, ""YaMar ya yi min kyau sosai."""

"""Hannun ki ya yi masa kyau dai, wane shi da zai miki kyau?."" Murmushi ya yi tana kallon kuWin da ya siya a jiki, ta kalle shi suka haWa ido ta ce, ""YaMar da tsada sosai fa."""

"""Ni a wajena ya yi arha na baki kyautarsa, ya yi min kyau ne kawai shiyasa na siya miki. Amma bai kai matsayin"

"abinda zan yi miki kyauta dashi ba."" Murmushi ta yi ta kwanta a jikinsa ta ce, ""Kaf matan duniya bana tunanin akwai wacce ta kai ni sa'ar miji mai sonta."""

"""Ki faWa da babbar murya, mijinki na matu™ar ™aunarki, ya yarda ya rasa komai ya mallakeki ke kaWan ki. In na ce ga adadin son da nake miki ™arya nake yi Jidda!"" Ya faWa yana shafa fuskarta yana cigaba da duba kayan."

"Toys ta gani ta san kayan Marmerh ne, tayi murmushi tana kallon kayan dan sun yi kyau sosai. Ya ce, ""wannan"

"na Didi ne."" Ta kalle shi ta ce, ""ban ga naka ba."" Ya kalle ta ya ce, ""in na yi miki, na yiwa Didi, na yiwa Marmerh bana da bu™atar siyawa kaina komai."" Murmushi ta yi tana kallonsa ya ce, ""iya suit Win da na dawo ita ita kaWai na siya kawai, sai wasu guda biyu."""

"Nayla ta ce, ""Allah ya ™ara maka arzu™i mai amfani Rouhii, Allah ya cigaba da kulawa da rayuwarka."" Ya kalle ta ya amsa da amin yana murmushi yana cigaba da bata labarin abubuwan da suka faru a can."

"Da daddare suka je gidan Didi aka kai mata tsarabar ta ita da Marmerh, a can suka zauna har goma na"

"dare sannan suka dawo gida. Wayarsa tana hannunta ta ji shigowar message wayar tayi haske, ta kalla ta ga number ce sannan ga abinda aka rubuta nan tana iya gani ta notification."

"Gabanta ya faWi ganin kalaman soyayya da na ban ha™uri, da hanzari ta danna message Win ya buWe a nan ta ga messages Win da yawa alamun ba yau aka fara ba. Bi ta dinga yi tana karantawa tunda kaWan-kaWan ake rubutowa har ta zo kan wanda aka turo a lokacin."

"A lokacin Omar ya shiga Wakin, ya bita da kallo ganin yanayin ta ya canja ga kuma wayarsa a hannunta, ya kalle ta ya ce, ""Ya dai?."" Ta kalle shi ta ce, ""Yaushe ta fara yi maka messesges babu labari?. Ya kalle ta da mamaki ya ce, ""Wacece?."""

"""Narma!."" Ya Wan yi jimmm alamun mai tunani kafin ya ce, ""Wacece ma haka?."" Ta zuba masa ido jin yana raina mata hankali ta ce, ""budurwar ka."""

"""Kin sake Satar dani, na san sunan Narma amma na manta wacece."" Zuba masa ido tayi tana binsa da kallon kana raina min hankali mai cike da tuhuma. Shi kuwa Omar tunani ya tafi kafin ya ce, ""ohhh wai ΄ar sanata? daman itace take damuna da message?."""

"Ran Nayla ya Saci jin yana mata wata tambaya ta rainin hankali ta ajjiye wayar ta ce, ""Ashe ka gane wacce nake nufi, in ma itace take maka messages Win ai ka sani."" Ganin zata fara kuka ya zo kusa da ita ya Wauki wayar yana duba messages Win ya yi tsaki ya ce, ""Ban taSa buWewa ba balle na san wacece, da ya shigo nake goge shi a notification shikenan."""

"Ta kalle shi hawaye cike a idonta ta ce, ""Har yanzu tana sonka daman?."""

"""Yanzu meye na kukan? Daga ganin messages sai ki fara kuka. uhum?."""

"""Kana ganin irin kalaman da take faWa maka, itace wacce ka fara so, zata dawo gare ka, zaka aureta, haka fa take cewa"" ta faWa kukan ta na yin ™arfi. Ya tsuguna a gabanta, ya jawo ta jikinsa yana shafa bayanta ya ce, ""ni ba dan kin karanta ba ban taSa bi ta kai ba, kuma mantawa nayi shiyasa ban faWa miki ana yi min messsge ba. Ki daina kukan nan shine bana so."""

"Nayla ta Wago ta kalle shi shima ita yake kallo ta ce, ""Don Allah kar ka bata amsa ko sau Waya, in ka kulata mutuwa zan yi."" Ya ri™e fuskarta ya ce, ""ki Wauka ban santa ba, ban ma taSa ganinta ba, kuma in na kula ta ai zaki gani, tunda wayata ko yaushe tana hannunki kuma babu inda na ce kar ki buWe a cikinta. Duk inda ki ke so ki shiga ki duba ki gani in na taSa yi mata magana, yadda zuciyata ta kasance mallakinki, gangar jikina ta zama ta ki, babu wani abu nawa da zai kasance sirri a gareki. In kina kokwanto ki Wauki wayar ki duba Jidda."""

"Ta koma jikinsa tana kuka ta ce, ""na yarda da kai, kawai ina kishi ne, zuciyata zafi take yi."""

"""Ki yi ha™uri"" ya furta a hankali a kunnenta yana shafa kanta zuwa bayan ta ya ce, ""ki yi shiru."""

"Kukan ta daina ta Wago ta Wauki wayar ta yi deleting messages Win duka ta jefa number a block, ta shiga whatsApp Winsa ta nemi number ta ga kuwa messages Win da aka yi dan bai ma taSa buWewa ba, ta yi blocking bayan ta goge su duka. Ajjiye wayar ta yi ta dafe kai tana ajiyar zuciya. Ya bita da kallo ya ce, ""hankalin ki ya kwanta?."" Ta Waga kai alamun eh kafin ta ce, ""in ta kira kar ka Wauka ka ji?."""

"Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce, ""To."" Zama ya yi kusa da ita ta kwantar da kanta a kafaWarsa ta ce, ""ina kishinka Rouhii, ina kishinka sosai. Kar ka kula ta don Allah, ka daina kulata ka ji!."" Murmushi ya yi bai ce komai ba, Allah na tuba banda rigima irin ta Nayla shi bai ga abin kishi da Narma ba, ita bata san in ya wuce waje baya dawo baya ba ne shiyasa."

"Cikin ™aramin lokaci aka cigaba da modernizing kayan Omar da kayansa da yayi order, kaya suka sake yin kyau sosai in aka saka a kwali aka baka baza ka ce made in nigeria bane, saboda komai yayi kamar kayan ™ asar waje. Tunda ta goge messages Win Narma bata sake gani ba, duk da bata bincika masa waya duk da ya bata damar hakan amma bata yi, kawai messages take dubawa taga zata gani amma babu sai hankalin ta ya kwanta."

"Cikin haka ta ga mail Win da aka turo masa, ta karanta jikinta na rawa ta mi™e tana jira ya fito daga wanka ta faWa masa, banWakin ta so shiga ta faWa masa amma sai ta fasa dan ta san bazai barta ta fito ba, sai ya gama lugwigwita mata jiki zai ™yaleta."

"Jikinta har rawa yake yi saboda murna tana jira ya fito, yana fitowa ta kwasa a guje ta Wafe shi ya ri™e ta ya ce, ""zaki faWi ki ji ciwo, lafiya?."" Sauka tayi daga jikinsa ta nuna masa ta ce, ""Mail aka yi maka, kalli kaga kamfanin sarrafa takalma na ™asar Chine su ne suke son ka basu lokaci su tattauna da kai. YaMar a kaf duniya babu ™ asar da ta fi ™asar China manufacturing shoes, sun nemi zama da kai duk yadda aka yi babban alkhairi ne."""

"KarSar wayar ya yi ya kalle ta ya ce, ""kuma ba ΄an damfara bane?."""

"""Kalli ka gani mana, ba su bane. Ga stamp da logo nan sun turo maka in kana kokwanto a kai."" Murmushi ya yi ya rungume ta tsam ya ce, ""Alhamu lillah!."""

"""Allah mun gode maka, Yanzu yaushe zaku zauna dasu? Ka yi reply Win mail Win dan a san ka gani"" ta faWa jiki ta har rawa yake yi. Ya zaunar da ita ya ce, ""ki nutsu tukunna."""

"""Bazan nutsu ba YaMar, ka basu date da time da kuma venue kawai. Suna da agent a Nigeria kawai zuwa zasu"

"yi su haWu da kai."""

"Omar ya ce, ""To wacce rana ki ke ganin za a saka?."""

"""Friday, kaga yau tuesday ka basu friday saboda albarkar ranar. Don Allah ka yi reply dan su san ka gani."" Tsayawa ta yi ta ga yana typing kuma da turanci yake rubutun, ganin tana kallonsa sai ya kalle ta ya mi™a mata wayar ya ce, ""Na yi daidai?."" Ta Harare shi ta ce, ""raina min wayo kawai ka ke yi wallahi."""

"""Allah ki duba ki gani."" KarSa ta yi tana gan, babu abinda ta canja kawai ta tura."

"Messages Win na zuwa suka dawo da amsa yaushe zasu haWu, ko faWa masa bata yi ba ta basu date kafin ta kalle shi ta ce, ""A ina zamu zauna to? Wannan hotel Win da muka je ai yana da kyau, bara na rubuta sunansa."" Shi kallon ta kawai yake yi ganin kamar ma ta fishi farin ciki jikinta sai rawa yake yi."

Farin ciki yake ji a zuciyarsa ya samu macen da take son cigaban sa fiye da nata cigaban. Tana gama

"turawa ta kalle shi ta ga ya zuba mata ido yana kallo, sai ya yi murmushi ya ce, ""ke kaWai tal a duniya, daga ke ba ™ari."" Murmushi tayi ta shiga jikinsa da ko riga babu yana fara shafata ta mi™e, dan yanzu sam-sam bata son wannan ala™ar ta haWa su. Ko dan tana shan wahala a hannunsa wani lokacin ne oho."

"Ganin yana kallon ta sai ta ce, ""Didi zan faWawa."" Bai hanata ba ta kira Didi ta faWa mata komai. Didi ta dinga murna tana addu'a Nayla na biye mata. Shi kan ya rasa gane wacece tafi wata farin ciki a cikinsu, Nayla ko Didi?."

"Bayan ta gama murnar ta zauna ya kalle ta ya ce, ""Jidda!."" Ta kalle shi jin da yadda ya kira sunanta ta"

"san serious abu ne, ta ce, ""Na'am."""

"Ya kafa mata idanu ya ce, ""Meyasa yanzu bakya so na taSaki?."" Ta sunkuyar da kai a hankali ganin yana kallonta, gabaWaya sai muryar ta gushe akan fusksrta. A sanyaye ta ce, ""yaushe na ce bana so?."" Ya Wan taSe baki ya ce, ""Sai kin faWa min zan fahimci hakan?."" Ta kalle shi zata yi magana ya ce, ""yanzu ma gashi kin bar jikina ina fara taSa ki, bayan da ba haka ki ke ba, akwai abinda ya canja ne? Akwai abinda nake gaza yi miki ne yanzu?."""

"Nayla ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, ""A'a."""

"""To Meyasa?."" Ta Wan yi shiru cikin rashin sanin amsar da zata bashi ta ce, ""Babu komai, ka yi ha™uri bazan sake ba."" Ya Waga kai ya ce, ""Na yi ha™urin, amma in da damuwa ki faWa min kar ki cuci kanki."" Ta girgiza kai ta ce, ""Babu komai."""

"""Okay"" ya faWa yana tashi yana shiryawa."

"Ita kanta abin na damunta sosai, gashi tana tsananin kewar mijinta amma da ya fara taSata sai taji kamar za a rabata da numfashinta, komai ya tsaya mata cak har sai ta bar kusa dashi take jin daWi."

"Shima a nasa Sangaren tunanin da yake yi kenan, me ya gaza mata har take gudunsa haka? Me yake yi mata wanda bata so da zarar ya taSa ta sai ta zabura kamar wacce wutar lantarki ja ta?. Raini ne ko kuma son da yake nuna mata ne ya jawo raini? Ko kuma dan ta ga yana bu™atarta a kai a kai shiyasa hakan? Jan aji ne ko wula™anci?. Juyowa ya yi ya kalle ta ya ga jikinta ya yi sanyi bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi.KRB3P082"

Nana haleemaa

"Ranar alhamis da daddare faWa suka yi da ita kaca-kaca, ya yi fushi ya ™yaleta dan yana ganin kawai raina masa hankali take yi da wannan sabon salon da ta Wauko, yana kuma ganin nuna mata da yake yi yana bu™atarta shiyasa take yi masa haka, wata™ila jan aji ne ko wani abun a wajanta. Dan bazai manta ba, a cikin mazan da suka zauna a China ya ji Waya daga cikinsu na maganar, yana cewa mata in suka ga ana nuna ana bu ™atarsu ana jin daWin tarayya dasu wasu suna rainawa mijin hankali, su dinga jan aji har wasu su ce sai an biya su."

"A lokacin bai Wauki abin da mahimmaci ba, kuma bai saka musu baki ba dan ba sabawa ya yi dasu ba, amma a yanzu ya ji a ransa tabbas dan yana sonta yana bu™atarta ya saka take yi masa haka. Ya san baza ta yi haka dan kuWi ba sai dai jan ajin, kuma zai nuna mata shi Wan halak ne, bazai sake sauraronta a wannan S angare ba."

"Nayla haka ta kwana duk ta damu, tayi kuka har ta gaji amma ta kasa gane abinda yake damunta. Tana ji a"

"ranta tana so ta samu na gaba da ita ta faWa masa ko taje asibiti, yanayin yana cutar da ita kuma yana cutar da mijinta."

"Da safe juma'a bai nuna mata yana fushi da ita ba, dan a wajansa komai Sangarensa daban, dan tana nuna masa wani hali a wancan Sangaren bazai shafi wani Sangaren na zamansu ba. Tare suka ci abinci har ya shirya ya tafi masallaci, bai jima baya dawo ya kalle ta ya ce, ""Zo ki zaSar min kayan da zan saka."""

"Tare suka je ta Wauko masa sabuwar suit Win da ya siyo, ya kalle ta ya ce, ""ta yi? ni da kayan hausawa zan saka."" Ta Waga amsa gira duk da nauyinsa take ji sosai, ta ce, ""tana yi maka kyau, ka saka ta"". Bai musa ba ya mi™a hannu zai karSa, ™in bashi tayi tana warwarewa alamun ita zata shirya shi."

"Bai hanata ba, ta shirya shi ta fesa masa turare, ya Wauki comb zai gyara gashin kansa ta karSa zata fara gyara masa ya zare shi daga hannunta ya ce, ""ki barshi, zan yi da kaina."" Sak Nayla tayi, jikinta ya sake yin sanyi dan ta san fushin jiya ne ya jawo haka, ta koma ta tsaya ya gama abinda yake yi ya kalle ta ya ce, ""na yi kyau?."" Murmushi ta yi ta ce, ""ka yi kyau sosai."" Murmushi ya yi kawai ta bi shi da kallo, in ba dan yana fushi da ita ba babu abinda zai hana bai rungumeta ba."

"Cikin rauni ta ce, ""Ka yi ha™uri Rouhii, wallahi....."" dakatar da ita ya yi ta hanyar Waga mata hannu, ya Wan daure fuska ya ce, ""na ce miki kin yi min laifi ne?."" Ta ce, ""A'a."""

"""To meye na bada ha™urin?."""

"Shiru ta yi bata ce komai ba. Share batun ya yi yana gyara maSallan rigarsa ya ce, ""da wanne yare zan yi magana? Ni ba turanci nake ji ba, ba kuma yaren China nake ji ba."" Sai ya bata dariya ta ce, ""ka yi magana da yaren ka, suma ai da yaren su suke magana. In ban da nigeria ma ai ko wacce ™asar da ta cigaba da yaren su suke amfani."" Murmushi ya yi ya ce, ""ki kasance active, kin san kece transilator Wina."""

"Murmushi ta yi ta ce, ""An gama."""

"""Zan tafi"" ya faWa yana kallon ta. Tare suka fito harabar gidan, da yake motar tana ™ofar gida sai ya kalle ta ya ce, ""ki koma, ki ta yi min addu'a."""

"""In sha Allah Rouhii, sai ka dawo."" Fita ya yi ba tare da ya ri™e koda hannunta ba. Nayla ta fara hawaye dan ta san fushi yake yi da ita shiyasa tun daren jiya bai sake kai hannunsa jikinta ba."

"Jiri ne yake Waukarta ta koma falo ta zauna tana jin kanta na juyawa sosai. Ta yi shiru tana tunanin mafita, kunya take ji ta tambayi Mama Sa'adatu ko Mamanta ta Kaduna, dan maganar akwai nauyi sosai, ta ya ya zata iya ce musu da zarar mijinta ya fara taSata da niyar aikata wani abun sai ta ji kamar zata mutu? Ta ya zata iya faWa musu wannan maganar?. Ajiyar zuciya tayi dan bazata iya ba gwara ma ta je ta ga likita kawai."

"Bayan ta tafi da jimawa ya kirata a waya, tana Wauka ya ce, ""Jidda wa ki ka sani lawyer a nan Kano?."" Nayla ta ce, ""Yaya Muhammad, Wan Daddy ne."""

"""Tura min number sa yanzu, da gagggawa."" Da to ta amsa ta kashe wayar ta tura masa number ta yi shiru tana jiran tsammani."

Daga nan bai sake yi mata waya ba har bayan magriba kuma bai dawo ba. Duk ta damu tana kiransa

"amma bai Wauka ba, so take ya dawo kawai ta ji ya aka ™are. Tana wannan tunanin ya shigo gidan da sallama,"

"abin mamaki shida Yaya Mahmmad Win ne wanda take k1ira da Yaya Babba, kaf jikokin Hajja shine babba shiyasa suke ce masa Yaya Babba."

"Da mamaki ta ce, ""Yaya Babba! Yau kai ne a a nan?."" Yayi murmushi ya ce, ""dole ki ganni a nan, na zo na taya ki"

"murna."" Kallon sa tayi ta kalli Omar da yake tsaye ta ce, ""me ya faru?."""

"""Zaki ji daga bakin mijinki, Ni dai ina tayaki murna Allah ya sanya alkhairi."" Ya kalli Omar ya ce, ""Omar zan wuce."" Tare suka sake fita da Omar suka barta a wajan, duk ta ruWe tana jira ya dawo. Ba jimawa ya dawo, ta matso inda yake amma sai ya yi baya yana kallonta, bata damu ba ta ce, ""Rouhi me ya faru? Ka faWa min don Allah."""

"Takardar da take aljihunsa ya mi™a mata,"

"hannu yana rawa ta buWe tana karantawa. Baki ta rufe da hannunta tana sake wara ido a takardar kafin ya ga ta zube ta yi sujjada a wajan ta Wago zata shiga jikinsa ya Wan kauce ya ce, ""baki ce Alhamdu lillah ba!."""

"Jikinta ya yi sanyi ganin ko taSa shi ya™i bata damar yi. Abin ya yi mata yawa ga damuwa ga farin ciki, haka ta daure ta ce, ""Na faWa da na yi sujjadar godiya ga Allah. YaMar contract na aiki da company ka suka nema har na shekara Waya fa, ai dole na ce Alhamdu lillah."""

"Murmushi ya yi yana girgiza kai ya ce, ""Kamar wasa ba, wai Omar ne zai yi aiki da babban company na ™asar China. Sun ga products Win mu ya yi musu suna so a dinga fita dashi zuwa ™asar su. Ni ban san abinda zai faru ba kenan, kin san komai na su mai ™a'ida ne shiyasa na tambaye ki lawyer. Sai da Yayanki ya je aka saka hannu aka jima ana ta cike-cike sannan komai ya kammala."""

"Nayla hawayen farin ciki ya sakko mata ta ce, ""Allah mun gode maka, Allah ka cigaba da saka mana albarka a"

"duk abinda muka saka a gaba."""

"""Amin Ashiq!."" Wayarta ce ta fara ™ara ta duba ta ga sunan Salma ta Wauka Salma ta ce, ""Ke Nayla kinga yadda hotunan mijinki da ΄an China suke trending? Wai ashe contract ya samu da su shine ko labari?."" Nayla ta ce, ""Salma yanzu abin ya faru, dawowarsa gida kenan."""

"Salma ta ce, ""Maza ki duba wayarki zaki ga abin mamaki."" Katse kiran Salma ta yi tana shiga instagram da"

"abinda ta fara karo kenan. Ta karanta caption Win a bayyane tana cewa, ""Mutum na farko Wan africa, Wan nigeria, bahaushe ya saka hannu a yarjejeniya tsakaninsa da ™asar China. Sun ™ulla yarjejiya akan zasu dinga karSar products Winsa suna kaiwa ™asar China."" Kallonsa ta yi ta ce, ""Rouhii kaine mutum na farko a kaf africa da aka taSa bawa wannan damar, kaine na farko fa Rouhii, kaine na farko."""

"Gangar jikinsa bu™atarta jinta a jikinsa take yi, rungumeta yake so ya yi tsam-tsam tayi kukan a ™irjinsa amma baya son aikata hakan dan ™arshe shine zai kwana a ciki. Ya dake bai nuna mata ba ya ce, ""Sun faWa Jidda, da ni suka fara signing wannan contract Win a kaf Africa. Fatana Allah yasa mu fita kunyarsu."""

"˜arar shigowar message ya ji, ya kalli wayar ya ga kuWin da aka turo masa a acc ya haskawa Nayla wayar ya ce, ""alert Winsu ya shigo."" Kalla ta yi ganin yawan kuWin ta wara idanu ta ce, ""Numbers Win sun rikice min, nawa ne?."" Dariya ya yi ya ce, ""ke da kike ΄ar boko ma kenan, balle ni."""

"""Didi ta sani?."""

"""Yanzu zan faWa mata."""

"""Mu je gidan tare kawai."" Zai yi magana sai ga kiran Didin yana shigowa, ya yi murmushi yana Wauka ta ce, ""Omar zo ka buWa mana ga mu mun zo."" Murmushi ya yi ya ajjiye wayar ya kalle ta ya ce, ""ki saka hijjab."" Ba musu ta tashi ta Wauko shi kuma ya fita. Didi tana shigowa ta rungume Nayla, itama kuka take yi sai ta saka Nayla kuka."

Omar gaisawa suke yi da AbdulHamid yana yi masa murna kafin ya karSi Marmerh da take hannunsa. Sun saba

"da yarinyar sosai, ta fara dariya shi kuma yana yi mata wasa cikin ™aunarta. Nayla daman kuka biyu take yi, ga na damuwa ga na farin ciki, Didi ta Wagota daga jikinta Nayla ta ce, ""Nayla ina ta ya ki murna, Allah ya taya ri™o ya tabbatar da alkhairi."" Nayla ta ce, ""Amin Didi, nima ina taya ki murna, Allah ya sa silar nasarar kenan."" Ta yi murmushi ta ce, ""Amin."""

"Ta kalli Omar ta ce, ""Ina ta jiran wayarka shiru, sai yanzu YallaSai yake nuna min hotunan ka da ΄an China a waya, ga takarda an saka hannu. Allah ya cigaba da dafa maka Omar, Allah ya cigaba da shiga lamarinka Omar."" Murmushi ya yi ya ce, ""Amin Didi, Duk kin ruWe, ki zauna don Allah."" Didi ta ce, ""ba dole na ruWe ba Omar"" ta faWa tana zama akan kujera shima ya zauna da Marmerh a hannunsa."

"Didi ta kalle shi ta ce, ""Yanzu sai me..."" kafin ta ™arasa aka kirata a waya, ta duba ta ga Mama Zainab ce ta yi murmushi ta ce, ""΄an uwa sai kira na suke yi a waya, iya wannan ma abin alfahari ne."" Šauka tayi tana amsawa, itama Nayla Abiy ne ya kira ta yana kashewa ya kira Omar. Omar da ya Wauka murna dai Abiy yake taya shi daga nan ya kashe sai ga Yayan Nayla ma ya kira shi."

"Zaman falon gabaWaya amsa waya yake yi shida Nayla, sai da akayi kiran sallah sannan suka fita

Please Login or Register in order to submit comment