ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai, ya ce dai duk yadda zan yi nayi na fitar da mijin aure in ba haka ba zai bani wanda ya ga dama. Daman na san bazan taSa mallakar abinda nake so ba Salma, shiyasa ni zan bawa Abiy ha™uri ya zaSa min duk wanda ya ga dama. To Mama ce take bani bani ™arfin guiwar zai iya amincewa da Omar."""

"Salma ta ce, ""Gaskiya Abiy bazai amince da Omar ba, gwara ma ki daina yaudarar kanki. Duk dani shaida ce"

"Omar ba kamar da ba yake ba yanzu ya canja, harkar sana'arsa yake yi kuma Allah ya saka masa albarka. Ke in kika ga takalman da Omar yake yi sai abin ya baki mamaki, sai kin ce daman yana da wannan talend Win ya zauna yana Sata rayuwarsa a banza da wofi.....huhh amma duk da haka rayuwarsa ta baya zata saka a ™i bashi aure Nayla. Musamman auren irin ki, mai ilimi, nasaba, kyau da sauran su."""

"Nayla ido ya kawo ruwa ta zubawa Salma ido ta ce, ""da gaske kike yanzu Omaar ya koma yin sana'a sosai?."""

"""Da gaske nake wallahi, bara na nuna miki handles Win su da suke posting kayan. Naga didi ta saka a status, shine naje na gani ke baki ga abu ba baza ki Wauka Omar yana da wayewar yin abubuwa haka ba"" Tana faWa tana danna waya tana duba page Win."

"Nuna mata wayar tayi ta ce, ""kin gani.. wannan shine irin takalman da Omar yake yi yanzu. Shiyasa zaman"

"unguwar nan ma yanzu ba yi yake yi sosai ba, ko yaushe baya nan suna shago suna aiki."" Nayla kalla take yi zuciyarta na rawa sosai kafin ta sauke kai ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""wata™ila babu Omar a cikin ™addarata."" ""Calm down, ki cigaba da addu'a komai zai wuce. Kuma ba kince Mama na supporting Winki ba?."""

"""Ita kaWai ba, Yaya cewa ya yi a bashi ni mu tafi Lagos sai na dawo hankalina na dawo gida. Yaya J ma da yake aminina shima yana bayan Abiy. GabaWaya jina nake wani iri wallahi."""

"""Ki dai yi ha™uri. Yanzu ki tashi kiyi wanka, kiyi break sai mu je gidan Didi."" Nayla ta ce, ""Ina so naje gidan Twiny ma."""

"""To ki tashi mu shirya."" Nayla tayi ajiyar zuciya ta tashi ta shiga banWaki cikin damuwa mai yawa."

Su Abiy lokacin da suka shigo Kano umartar Jawad ya yi da su wuce gidan su na Kano. Kai tsaye nan

suka wuce kamar ko yaushe. Mai gadin gidan jin ana horn ya buWe ya ™araso ganin mai gidan ne da kansa ya saka ya buWe suka shiga cikin gidan. Falon gidan suka shiga bai yi dauWa ba sai dai ΄ar ™ura kaWan mara yawa.

"Abiy ya kalle su ya ce, ""ku huta zuwa sha biyu da rabi zamu fita."" Amsa masa suka yi ya shiga ciki. Ahmad ya"

"kalli Jawad ya ce, ""Wai me yake faruwa ne? Me muka zo yi Kano?."""

"""Wallahi ban sani ba Yaya, abinda na sani kawai jiya Nayla ta bar gida ta taho nan Kano. Da Fari na Wauka gidan Hajja Win zamuje sai naji ya ce mu zo nan."" Da mamaki Yaya ya ce, ""ta bar gida ta taho nan? To Akan me?."""

"Jawad ya ce, ""Akan wannan yaron mana, ran Abiy ya Saci matu™a a jiya da daddare."""

"""Daman Nayla bata da hankali ban sani ba? Ana ganin ta mai kirki da hankali ashe itama ΄ar iska ce?. Ta taho na saboda ance bazata aure shi ba ko me?."" Jawad ya ce, ""nima ta bani mamaki wallahi, ban Wauka zata aikata haka ba. Ashe macijin sari ka no™e ce, a haka sumi-sumi da ita kamar bazata aikata ba."""

"Yaya ya girgiza kai ya ce, ""Lallai tana bu™atar duka, dan sai na zane mata jikinta sannan zata fahimci kuskurenta. Bara Abiy Win yazo, Wauketa zan yi wallahi mu tafi lagos na koya mata hankali a can tunda ita shashasha ce"" ya faWa yana fita zuwa Wakin da suke zama a cikin gidan."

"Ba su jima sosai ba Abiy ya yi musu waya ya ce su fito, suka fito suka tarar dashi a bakin mota suka shiga kai"

tsaye ya ce su wuce unguwar Kundila. Can suka nufa Abiy yana basu address yadda aka faWa masa suna tafiya sai gasu har ™ofar gidan Kawu.

"A ™ofar gidan suka faka motar Abiy ya kalli gidan da aka tabbatar masa nan ne gidan Kawu. Babban gida ne mai kyau kana gani ka san mai shi yana da abin hannu sosai. Abiy ya kalli Agogo ya ce, ""mu ™arasa masallaci muyi sallah in ya so sai mu dawo."" Da to suka amsa suka ™arasa masallacin da yake kusa suka yi sallar juma'a sannan suka dawo mota."

Abiy da kansa ya tambaya aka nuna masa Kawu da yake tahowa yana amsa waya zai shiga gidan ya dawo daga

"masallaci. Abiy ya ™arasa ya ce, ""Assalamu alaikum."" Ya dakata da wayar ya amsawa Abiy suka yi musabaha kafin Abiy ya ce, ""na san baka sanni ba, ba™o ne in babu damuwa Ina so zamu tattauna."" Kawu ya ce, ""to bismillah shigo."" Abiy ya yi musu magana alamun su shigo suka biyo bayan Abiy."

"A wani babban falo ya sauke su wanda maza biyu suke a zaune ya kalli Abiy ya ce, ""΄an uwana ne, Ina fatan babu damuwa."" Abiy ya ce, ""babu damuwa. Na ji daWin hakan sosai."" Kawu ya ce, ""Da yake yau muna Wan ™ aramin taro, an kawo kayan lefen ΄ar wajan ™anina gashi a zaune shiyasa muke gabaWaya"" ya faWa yana nuna masa Kawu Yusuf. Abiy ya ce, ""Allah ya sanya alkhairi."""

"""Amin ya Allah. sai dai ban sanka ba."" Abiy ya ce, ""Sunana Alhaji Abdullah Ahmad, ni mazaunin garin Kaduna"

"ne. Nazo wajanka ne akan Wan ™aninka Omar ™anin Aysha."" Kawu ya gyara zama ya ce, ""to Allah yasa ba laifi ya yi ba."" Abiy ya murmusa ya ce, ""ba laifi ya yi ba, na zo ne ina nemawa ΄ata aurensa a yanzu in hakan zai yu."""

"Duk mutane wajan mamaki ya kama su, suka bi Abiy da kallon mamaki ba tare da ya basu damar magana ba ya"

"ce, ""na san komai, kar ku tambaye ni dalili ko meyasa, ina sane duka abinda nake yi. Kawai in zai yu ina so zan bashi aurenta a yanzun nan a Waura auren. Tunda ku ne waliyansa ga nata waliyya a zaune"" ya faWa yana nuna su Jawad da suka yi mutuwar zaune."

"Kawu ya ce, ""To ai ka kulle mana baki ne, wai ka san wanne Omar ka ke magana akai kuwa?."""

"""Na sani, tunda kaji har nayi maka kwantacesa da Yayarsa ai ka san na sani. Ni sirikin Hajja ne ma™ociyarsu."""

"Kawu ya ce, ""™warai na san Hajja, har gaisheta na taSa shiga nayi sau biyu, kuma Ina jin labarin alkhairinta sosai a wajan Aisha."" Abiy ya ce, ""na auri ΄ar Hajja kafin mutuwa ta raba mu, yarinyar da zan aura mata ΄ata ce ta cikina kuma jikar Hajja. Amma naga kamar kuna tantama, in kuna so ku tabbatar ku kira Aisha ku tambayata ku ce ta san Nayla."""

"""Assalamu alaikum, Kawu ashe ba™i ne da kai bara na koma"" aka faWa daga bakin ™ofa ana ™o™arin komawa. Kawu ganin Didi ce sai ya ce, ""Aisha shigo mana."" Didi ta juyo tana takowa a hankali har tazo tsakiyar falon. Kallon Abiy tayi cikin mamaki ta ce, ""Abiy! Ikon Allah kaine a nan?"" Ta faWa da fara'a tana kallon sa. Abiy ya murmusa ya ce, ""ni ne Aisha."""

"""Barka da rana."""

"""Barkan ki, ya gida?."""

"""Lafiya lau Abiy, ya su Nayla? Tana lafiya?."""

"""Lafiya lau."" Didi ta kalli Kawu ta ce, ""Kawu mahaifin jikar Hajja ne Nayla, kuma shine wanda ya karSo Omar daga hannun Senator kwanaki da abin nan ya faru."""

"Kawu ya sauke ajiyar zuciya ya ce, ""ya yi min bayanin komai Aisha. Wata magana yazo da ita mai girma, wai"

"yana so a yanzu a Waura auren ΄arsa da ™aninki Omar."" Wara idanu Didi tayi tare da dafe ™irji cikin mamaki ta ce, ""Aure Kawu!?."" Ya Waga mata ka ta juya ta kalli Abiy ta ce, ""Abiy auren Nayla da Omar?."""

"""Haka nake so, yanzu kuma babu Sata Lokaci."""

"Jawad da yake gefe ya ce, ""Amma Abiy...."" Dakatar dashi yayi ta hanyar Waga masa hannu ya ce, ""kar wanda ya yi min magana yanzu"" ya kalli Aisha ya ce, ""Auren zai yu?."" Didi ta kasa magana sai kallon Abiy da take yi dan ta rasa abinda zata ce. Abiy ya ce, ""in bazai yu ba ki faWa min kawai."" Didi cikin kiWima ta ce, ""Abiy ni wallahi ban san me zance ba, abin nake ji kamar a mafarki. Meyasa ka ke son aurawa Nayla Omar?. Abiy na san ka san Omar ba sai na faWa maka ba, meyasa haka kwatsam zaka yanke wannan hukuncin?."""

"""Haka nayi ra'ayi"" ya bata amsa a ta™aice."

"""Amma Abiy Nayla ba sa'ar auren Omaar ba ce, ka san halin sa ba sai na faWa ba, kowa ma a nan ya san halinsa ba sai an maimaita ba. Meyasa ka ke son aurawa ΄arka shi don Allah?"" Ta faWa a sanyaye tana kallon Abiy."

"Abiy yayi ajiyar zuciya cikin Sacin ran da yake ciki, danne Sacin ransa kawai yake yi yana magana amma Allah kaWai ya san irin yadda zuciyarsa take tafasa akan abinda Nayla tayi masa wanda bai yi tunani ba. Ya ce, ""Aisha ki amsa min tambayata kawai, in auren zai yu to in bazai yu ba ki faWa min."""

"Didi ta sunkuyar da kai dan bata san me zata ce ba, auren Nayla da Omar kuma...? to akan wanne dalili kenan?"

"Kuma ta tabbatar Omar Win ma bai san labarin ba, aka Waura auren sa bai sani ba ai an shiga tashin hankalin faWansa, dan tsaf zai saka yi ya™in duniya. To ita Nayla Win ta sani ko bata sani ba..? Meyasa lokaci Waya Abiy zai zo da wannan maganar?."

"Kawu ya katse shirun ya ce, ""zai yu mana tunda kana so, amma ka san waye Omar kuwa?."" Abiy ya ce, ""kaf"

"labarin Omar na sani, har wanda baku san dashi ba na sani, har wanda kuke tunanin ban sani ba shima na sani, yanayin alaqarku da duk abinda yake yi na sani. Kawai ina so ku amince min ne yanzu babu Sata Lokaci."""

"Kawu ya kalli Didi ya ce, ""Aisha ya ki ka ce? Kece uwar Omar, kina ganin kin amince?."" Didi tayi ajiyar zuciya"

"bata san abinda zata ce ba wallahi, in ta amince kamar ta cutar da Nayla ne duk da bata san dalilin Abiy na aura mata Omar rana tsaka ba, in bata amince ba kuma kamar bata kyautawa Abiy ba duk da tarin taimakon da ya yi mata bai cancanci haka ba. In ta amince ma aka Waura auren da wacce fuska Omar zai karSi auren?."

"Numfashi ta sauke a hankali ta ce, ""Ayi abinda Abiy yake so."" Abiy yayi murmushi ya ce, ""na gode. A yanzu"

"nake so a Waura auren nan babu Sata lokaci."""

"Kowa mamakin Abiy yake yi kawai kallon suke yi, a take aka kira mazan gidan cousins Win Omar kenan aka tara shaidu Kawu ya bada sadaki naira dubu Wari biyu. Abiy ya umarci Jawad da ya je mota ya Wauko goro da alewa ba jimawa ya kawo aka shaida saurin aure a wajan. Didi dai tana zaune tana kallon su kamar a mafarki take ganin abin, wai yanzu Nayla ta zama matar Omar, ko da wacce fuska zai karSi auren ma oho, ko meyasa Abiy ya yiwa Nayla haka oho."

"Bayan an Waura auren Abiy ya kalle su ya ce, ""Na gode sosai da karamcin ku a gare ni, duk da baku sanni ba amma ku ka amince ku ka ™ulla a™alar aure dani, naji WaWi sosai Allah ya saka da alkhairi ya ji™an mahaifa. Sannan zaku iya tambayar kowa a garin Kaduna waye Abdullah Ahmad, in sha Allah zaku samu magana mai kyau a kaina."""

"Kawu Mamman ya ce, ""Ni na sanka, mun taSa yin wani taro an gayyato ka matsayin babban ba™o. Na san labarinka kaf, suma baza su rasa sani ba ai kai ba Soyyayen mutum bane."" Murmushi Abiy ya yi ya ce, ""Na gode. Sai a fara shirin tarewar amaryar nan da kwana biyu masu zuwa in sha Allah."""

Kowa kallon Abiy yake yi dan gani suke kamar yana da taSin hankali ko kuma ba ΄arsa ba ce. A haka yayi musu sallama cikin mutunci tare da karSar number juna suka rako shi har harabar gidan yana kallon su.

"Jawad suna so su yi masa magana amma ya ™i bada fuska dole suka ri™e bakin su suka bari aje gida. Didi ce ta biyo bayan Abiy ta samu har sun fita zasu shiga mota ta ce, ""Abiy."" Ya jiyo yana kallonta ta ce, ""Don Allah meyasa ka yanke wannan hukuncin akan Nayla?."""

"Abiy ya murmusa cike da takaici da Sacin rai ya ce, ""ki kwantar da hankaliki babu komai, ki fara shirin karSar amarya ranar lahadi jibi kenan, ranar Nayla zata tare a gidan mijinta"" ya faWa yana shiga mota suka suma suka shiga suka bar unguwar."

"Didi ko da ta koma su Kawu tsare ta suka yi da tambayar anya Abiy yana da hankali kuwa, Didi ta ce, ""wallahi"

"yana da shi, mutum ne na gari dattdijo ban san meyasa ya aikata hakan ba. Kuma baka ji Kawu ™arami ya sanshi ba? Babban mutum ne mai kuWin gaske a Kaduna, zan iya cewa kaf garin Kaduna an sanshi."""

"Kawu ya ce, ""Nima na san shi Aisha, yana da manya-manyan store a garurun dake cikin ™asar nan. Kawai tantama nake yi akan anya yana da hankali? In kuwa yana dashi anya ita Hauwa Win ΄arsa ce?."""

"""Wallahi ΄arsa ce wacce yake matu™ar ™auna, kaf yaransa ma babu kamarta."" ""Iko sai Allah, to yanzu shi Omar Win ya san labarin nan?."""

"""Wallahi bai sani ba Kawu, tashin hankalina bai wuce Omar ya sani ba. Ban san da wacce fuska zai karSi auren nan ba."""

"Kawu ya ce, ""kuma ke zaki faWa masa ba, Haka zaki same shi ki sanar dashi zai iya fahimtar ki. Sai a fara shiri tunda ya ce jibi zata tare."" Didi ta ce, ""to Kawu ina Omar yaga gidan ma da zai saka amarya?."""

"Kawu ya ce, ""wannan ba abin damuwa bane, ki san yadda zaki yi dashi, akwai gidan da na siyawa ™aninki mai sunan Omar Baba kenan, an gyara shi anyi komai babu abinda ba a saka ba, hatta solar an haWa 24/7. Da yake Allah bai nufa zai zauna a gidan ba kinga an fasa auren, ki lallaSa Omar ki san dabarar da zaki yi masa sai ya zauna a ciki. Kar sunana ko sunan wani ya fito a kyautar gidan nan, ki san yadda zaki yi dashi amma kar ki ce daga hannuna ya fito. Kuma wallahil azim na bar masa kyauta, yadda na siya da sunan Wana auren bai yu ba na barwa Wana na wajen marigayi ™anina Usman gidan halak malak."""

"Didi a sanyaye ta ce, ""To Kawu, an gode Allah "" Dakatar da ita ya yi ya ce, ""Aisha kar ki gode min, muje"

"magana ta gaba."" Didi ta ce, ""To Kawu. Ni yanzu so nake a san yadda za ayi a tunkare shi tukunna."" Kawu"

"Yusuf ya ce, ""Aisha wannan ai aikin ki ne, mu a cikin mu akwai wanda ya isa ya tari Omar da wannan"

"maganar ne?."""

"Sai taji jikinta ya yi sanyi a sanyaye ta ce, ""kun isa mana Kawu."""

"""Ba mu isa ba wallahi, kema kin san bamu isa a wajan Omar ba. Tunda hakan ta kasance naji daWi da kina nan, da bakya nan tsaf zai iya zuwa ™ofar gidan nan ya tara mana jama'a. Ki je ki san yadda zaki faWa masa."""

"Kawu Mamman ya ce, ""Aisha ni kuma in za a haWa lefen amarya kizo ki yi min lissafi zan siyi komai in sha Allah."" Didi tayi murmushin ya™e zata yi godiya ya dakatar da ita ya ce, ""kije ki tattauna da Omar kawai."""

"Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, ""To Kawu zan yi. Bara jama'a su Wan ragu a gari sai naje na same shi"" ta faWa a sanyaye tana kallon su. Suka amsa mata ta shiga ciki tana tunanin dalilin Abiy da aikata wannan Wanyen aiki."

"Su Abiy sai da suka tsaya a hanya suka siyi abinci sannan suka wuce gida. Suna shiga Abiy ya Wauki pack Waya na abincin yana ci ba dan yana jin daWinsa ba sai dan babu yadda zai yi ne. Jawad kam sun kasa ci kallon Abiy kawai suke yi suna jiran ™arin bayani, ™arfin hali Yaya Ahmad ya yi ya ce, ""Abiy meyasa ka yanke wannan hukuncin akan Nayla don Allah? Wannan ba yukunci bane, taya zaka Waura auren ta da wannan yaron?."""

"Abiy bai yi magana ba Jawad ya ce, ""Abiy don Allah meyasa aka yi mata haka? Ko me ta aikata ai yarinya ce sai"

"ayi mata uzuri a tsawatar mata, amma Waura mata aure dashi ba hukunci bane ba Abiy."" Abiy bai ce musu komai ba ya ajjiye abincin ya tashi ya shiga ciki."

"Jawad ya kalli Yaya ya ce, ""wannan hukunci ne Yaya? Wannan ai lalata mata rayuwa aka yi ba aure aka yi mata"

"ba. Ko me tayi ai wannan ba hukunci bane, sai a zaunar da ita ayi mata faWa, in auren ya zama dole sai aura mata wani amma ba irin wannan yaron ba."" Yaya cike da damuwa ya ce, ""ni ban san ma abinda zan ce ba wallahi, ban san abinda ya saka Abiy ya aikata haka ba. Dan ta ce tana sonsa akwai sai a bata shi? Haba gaskiya Abiy bai kyauta mana ba wallahi."" Abincin da basu iya ci ba kenan Abiy ya fito ya kalle su ya ce, ""abinda ya kawo mu Kano mu yi, ku tashi mu wuce gida."""

"A sanyaye suka tashi suka bi bayan sa bayan sun Wauko abincin har wanda Abiy ya ajjiye. Yaya ne yanzu ya shiga gaba wajan mai tu™awa Jawad ya shiga kusa da shi Abiy ya shiga baya. Har zai kunna motar Abiy ya tuna ya yi mantuwa ya koma ciki. Jawad kasa ha™uri yayi ya Wauki waya ya kira Nayla yayi sa a ta shiga, tana Wauka kafin tayi magana ya ce, ""Malama duk abinda ki ke yi a Kano ki tabbatar kin wuce Kaduna yanzu, ko me ki ke yi ki ajjiye ki wuce gida."" Nayla ta ce, ""Yaya J rana ta yi yanzu, driver Hajja baya nan waye zai kai ni Kaduna yanzu?."""

"A tsawace ya ce, ""ki san yadda zaki yi ki dawo gida, in ba haka ba wallahi sai ranki ya Saci sosai"" ya faWa ya yanke wayar ganin Abiy ya taho. Yana shiga motar Jawad ya ce, ""Abiy mu biya gidan Hajja mu tafi da Nayla?."" Abiy ya ce, ""tare muka zo da ita?."" Jin abinda ya ce sai ya yi shiru amma zuciyarsa gabaWaya babu daWi akan abinda Abiy ya yi, to babu yadda zasu yi ne dole su yi shiru kamar yadda ya ce. Fita suka yi daga gidan bayan sun bawa mai gadi abincin suka Wauki hanyar Kaduna."

"Nayla kuwa da suka je gidan Didi bata nan sai kawai suka wuce gidan Jidda, suna zaune a Jawad yayi mata"

"waya duk sun ji abinda ya ce. Ta kalli Twiny ta ce, ""Yaya J ne yau yake yi min wannan faWan, yanzu waye zai kai ni Kaduna?."" Twiny ta ce, ""ke share shi, gobe sai ki tafi. Haka kawai sai yaja Abiy ya yi miki faWa daman gashi Abiy na fushi."""

"Nayla ta ce, ""yanayin maganar Ya J da Sacin rai ciki sosai Twiny, ko dai naje na hau motar haya na koma?."""

"""Ki share shi, gobe da safe sai ki tafi."" Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, ""Allah ya sa Abiy bai yi fushi da tahowa ta Kano ba, Allah ya sa ya fahimce ni ya yafe min laifin da nayi masa."" Suka amsa mata da amin. Hira suke ta janta da ita amma ta kasa sakin jikin saboda bata da walwala ko kaWan, yamma nayi suka wuce gida a motar gidan"

Hajja da Salma ta kawo su.KRB2P021

Su Abiy da suka koma gida bai cewa kowa komai ba sama ya hau ya barsu a wajan a tsaye. Mama ta kalle su

"ganin fuskar su Wauke da damuwa ta ce, ""Wai ne ya faru ne? Me kuka je yi Kano?."" Jawad ya kalle ta ya ce, ""dangin wannan yaron Omar muka je, abin mamaki Abiy ya bada auren Nayla, dan yanzu haka Nayla matarsa ce."" Mama ta wara idanu waje a zahiri, a baWini kuma farin ciki ne ya mamaye mata zuciya ta ce, ""Aure kuma? Auren Nayla da Wan daban aka yi?."""

"Yaya ya ce, ""Wallahi shi aka yi Mama, Abiy ya™i faWa mana dalilinsa, sannan kuma ya hana mu tamabaya. Yanzu zancen da nake miki an Waura auren su ita dashi, kuma ko sani Omaar Win bai yi ba, haka Nayla Win ma bata sani ba."""

"""Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Meyasa mahaifinku ya yanke wannan hukunci? Me Nayla tayi masa haka?. Ko"

"dan ta tafi Kano ne ya saka ya yanke wannan hukuncin?."" Jawad ya ce, ""itama bata da mutunci ai Mama, ban da rashin hankali da shirme meye na barin gida a akan wannan maganar? Na rantse da Allah in ta dawo sai na zaSa mata kamanni."""

"Mama ta ce, ""bara naje na samu Abiy Win naku naji dalilin sa na aikata wannan Wanyen aiki."" Yaya ya ce, ""Yauwa Mama, in da hali a kira yaron kawai ya sake ta tunda daman bai san anyi auren ba. In yaso ni a bani Nayla mu koma Lagos ta koma zama a gidana, nayi alqawari zan kula da ita babu wata damuwa irin wannan da zata sake kunno kai."" Mama ta girgiza kai ta hau sama da sauri wajan Abiy. Sallar magriba ta samu yana yi sai ta zauna tana zaman jiran ya idar suyi magana."

"Koda ya idar lazimi ya fara ta san kuma baya gamawa sai za a yi i'sha gashi ita ta ™agu tayi magana dashi. Mama ta ce, ""Don Allah Abiy ka katse lazumin nan muyi magana. Ta ya za a aurawa Nayla wancan yaron?. Bai kamata a biye mata a aikata abinda take so ba."" Ko motsi bai yi ba balle ta saka ran zai bata amsa. Mama ta ce, ""Abiy don Allah kace wani abu, ka dakatar da lazumin nan muyi magana don Allah."""

Ban ma bai kula ta ba Mama ta zauna tayi tagumi tana kallonsa. Gajiya tayi da zaman ta tashi ta fita shi kam

bai ma kalle ta ba. Sai da ya kammala yaji ana kiran sallar i'sha sannan ya tashi ya fito dan zuwa masallaci.

"Koda ya dawo a falo ya tarar dasu gabaWaya da alama zaman jiran sa suke yi. Wucewa yayi ba tare da ya zauna ba suka bishi da kallo ganin ya shiga ciki. Jawad ya ce, ""Mama don Allah kije kuyi magana ya bar mu cikin tunani."" Mama ta ce, ""maganar ce baya so shiyasa ya wuce bai kula mu ba, amma bara na sake zuwa naji"" ta fa Wa tana hawa saman ta barsu a ™asa."

"Tana zuwa ta same shi ya zauna akan kujera yana kallon tv, ta zauna a kusa dashi ta ce, ""abinci fa?."" Ya girgiza"

"kai kawai alamun baya ci. Mama ta ce, ""maganar dai da baka so ita zanyi Abiy. Meya faru ka yanke wannan hukunci akan Nayla?. Naji bata kyauta ba amma da ka sani baka yi haka ba."" Bai ce mata komai ba itama sai tayi shiru bata sake

Please Login or Register in order to submit comment