ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tayi zai kawo mata sassaucin tsoron da take ji. Kuma tunda Allah ya yi sai ta ji wannan ciwon ko bata fita ba sai an shigo har gida an cutar da ita. Dole zaka WanWana irin abinda ka dinga WanWanawa mazajen wasu akan matansu a baya..."""

"Omar ya bita da kallo jin abinda take faWa, ta ce, ""Eh Omar. ba dai kaji zafi a ranka ba? Ka ji ciwo da raWaWin a zuciyarka saboda abinda ya same ta ba?. To Allah ne ya WanWana maka dan kaji abinda wasu suka ji a lokacin da ka yiwa nasu, kai kanka baka san iyaka adadin matan da aka yiwa irin abinda aka yiwa Nayla ba, ba dan komai ba sai dan saboda laifin mazajensu ya shafesu. Dan haka ka nutsu kawai, mu yi fatan Allah yasa ya tsaya a haka."""

"Ganin ya kasa magana ya tafi tunani sai ta ce, ""A firgice take Omar, tsoronka ya riga ya tsarata, ka taimaka ta"

"dawo nutsuwarta ta daina wannan firgicewar don Allah. Ka san a ina yarinyar nan ta taso, ba sabawa da wannan tashin hankalin tayi ba shiyasa ta tsorata. Bana tunanin allura in ba ta neman lafiya ba ta taSa sokarta, yau gashi hannunta a Waure yake saboda an sare ta da wu™a. Kuma ido da ido ta ganka da jini a jikinka dole ta ji tsoro, abinda bata taSa gani a zahiri ba sai a film, dole ta shiga wannan yanayin. Ka yi ha™uri, ka yi mata uzuri, duk fushin da ka ke yi da ita a kan ta fita ka ajjiye shi don Allah."""

Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba. Bashir ya saka suka raka su Didi dan a yanayin da ake ciki bazai yi sake da

lafiyarsu ba.KRB3P074 Nanahaleema.

"Lokacin da ya koma bata falo, Wakin ta ya shiga ya tarar da ita a kwance a kan gado layi luf a kan gado, ya kunna hasken Wakin suka haWa ido ya ce, ""kin ci abinci ne zaki kwanta?."" Yadda yayi maganar babu wasa ya saka ta ce, ""mun ci da Didi."" Ya girgiza kai ya ce, ""a nan kika saba kwana kenan?."""

"Ta mi™e zaune ta ce, ""ba a nan ba ne."""

"""Rainin ne ko?."" Ta sakko daga kan gadon bata ce komai ba ta wuce ta tafi Wakinsa. Ya sauke numfashi ya bita Wakin dan bazai iya barinta ita kaWai ba a kusa dashi zata kwanta. Sai da ya shiga Wakin ya ce, ""me yake damunki?."" Nayla ta ce, ""babu komai."" Ya taka inda take ya taSa wuyanta, ya ri™e kanta yaji babu alamun ciwo, ya duba hannunta yaga ciwon babu abinda ya same shi."

"Ya bita da kallo ganin tana rawar jiki ya ce, ""ke wai meye abin tsoro a jikina?."" Ta sunkuyar da kai ta ce, ""ka yi"

"ha™uri."" Yayi ™aramin tsaki ya bata waje ta kwanta cike da fargaba"

"Washe gari da kansa ya kai ta aka yi swapping sim card Win ta, bayan sun dawo suka biya asibiti aka duba ciwon, sannan ya siya mata sabuwar waya ya ajjiye mata. Jikin ta duk a sanyaye yake haka ta Wora komai na wayar saboda ta san ΄an gidansu suna nemanta."

"Kwana biyu suka kwashe a wannan yanayin, bata shiga harkarsa kuma a waje Waya suke kwana, daga ina kwana babu abinda take iya ce masa, shima daga ya amsa shikenan babu wata magana. In ya riga ta tashi zai yi abinci kuma su zauna a waje Waya su ci, in ta riga shi tashi zata yi abinci itama. Zuwa lokacin waWanda ake zargi hukuma ta shiga tsakani, komai ya wuce kamar bai faru ba amma ita dashi basu dawo daidai ba, dan ita tsoronsa take ji, sannan kuma tana jin haushin faWan da ya dinga yi mata ko ciwon hannunta bai duba ba."

"A haka ta je bank aka gyara mata account Winta da aka yi blocking har lokacin ba shiri suke yi ba. Ranar da aka kwana biyar da faruwar abun da daddare sun dawo daga asibiti an duba mata ciwon, ta gama shan tea ta"

"dawo Waki ta canja kaya zuwa na bacci ta Wauki wayarta zuwa Wakinsa. Tana shiga suka haWu a hanya, suka ha Wa ido ta Wauke kai ta yi gefe zata wuce ya tare mata hanya, ta sake juyawa Waya side Win ya sake tare ta, ya matso kusa da ita har yana jin saukar numfashinta. Ganin ya hanata wucewa gashi ya matso kusa da kusa ita sai ta tsaya cak tana sauke numfashi a hankali. Cikin nutsuwa ya saka hannu biyu ya Wago fuskarta yana kallon idonta da suka fara taruwa da hawaye."

"Kumatunta ya shafa, calmly ya ce, ""Jiddana, Ashiq!"" Ya furta a sanyaye yana kallonta. Fuska ta ™waSe zata yi kuka, ya Wan yi tsaki kaWan ya ce, ""Kar ki yi kuka mana..."" Nayla ta faWa jikinsa da hanzari ta rungume shi tightly tana kuka. Murmushi ya yi ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali cikin salo na ™auna."

"Nayla cikin kuka ta ce, ""Ka dana sona...ka daina sona...!."" Omar ya ce, ""Shiii! Ki daina magana"" ya haWa yana ri™ o ™ugunta ya sake haWe ta da jikinsa sosai. Sun jima a haka kafin ya sassauta ri™on da ya yi mata ya ri™e fuskarta ya fara kissing Winta slowly. Bai jima ba ya raba kansa da ita yana yamutsa gashinta yana kallon idanunta da suke zubar hawaye."

"""Ki yi ha™uri!"" Ya furta a hankali, ya sake kissing Win bakinta na ΄an sakanni kafin ya zare bakinsa yana shafa fuskarta. Ta sake komawa jikinsa ta kwanta tana jan numfashi. Sake ri™e ta ya yi yana jan numfashi kafin ya ri™e ta har kan gado ya zauna da ita ya zauna a gefenta ya ri™e hannunta baice komai ba."

"Ganin tana kallon sa sai ya ce, ""Ki yi ha™uri da ni, na faWa miki ban iya Sacin rai ba, daman kuma na faWa miki zan Sata miki rai wata rana, gashi ya faru"" ya faWa yana kallon ta."

"Nayla ta bishi da kallo ya Wan yi murmushi ya ce, ""ki daina jin tsorona Jidda, abinda ki ke tunani bai faru ba a ranar, jinin Waya daga cikin yaran da suke yi min aiki ne, lokacin da na fita sun ji masa ciwo shine na ri™e shi su Bashir suka kai shi asibiti. Amma bayan nan ko wu™ar da na fita da ita bata yi min amfani ba."""

"A raunane ta ce, ""Ka bani tsoro Rouhii, ka bani tsoro sosai. Kar ka sake koma min Tiger, ka cigaba da zama a"

"Rouhiina kuma YaMar Wina. Tiger zai iya sakawa zuciyata tayi bindiga, Tiger tsawa yake yi min, Tiger baya sona, Tiger tsorata ni yake yi. Rouhi ne yake sona, shine baya ™aunar ganin kukana, shine baya so na shiga damuwa ko kaWan. Ka cigaba da zama a haka, don Allah ka daina rikiWewa kana koma min wancan kaji!"" ta faWa tana W ora hannunta a gashin fuskarsa."

"Murmushi ya yi tare da pecking Winta a goshi yana kallon ta da murmushi ta ce, ""saura ™iris Tiger ya sa na gudu Kaduna, kuma in na gudu bazan dawo ba!"" Ta ™arasa faWa da shagwaSa tana kallonsa. Murmushi yake yi mata wanda yake kashe mata jiki kana ya ce, ""Tiger yana sonki Jidda, Omar ma yana sonki. Koda kin gudu Kaduna da kaina zan je na Wauko ki."""

"""A'a, Rouhii ne yake sona ba tiger ba. Shi fa tsawa yake yi min, kuma ya ce min Naylaaaa!. Rouhi kuma Jidda"

"yake ce min ko ya ce Ashiq. Tun a gidan Didi Tiger baya sona, amma YaMar yana matu™ar ji da ni"" ta faWa tana kallonsa."

"Fuskarta yake shafawa a hankali kafin ya ri™e hannunta da aka ji mata ciwo ya ce, ""ke kika jawo Ashiq, ke kika Wauki tsoro ki ka saka a zuciyarki har in nazo kusa dake kike rawar jiki. Yanzu Ashiq kina ganin zan ji daWi in naga bakya so nazo kusa dake? Uhumm zan ji daWi?."""

"""Ni Damisa nake tsoro ba Rouhii ba, Damisa ne bana so yazo kusa dani ba Rouhi ba. Ga Rouhiina a kusa dani yana rarrashina"" ta faWa tana turo baki gaba."""

"Bakin nata ya ri™e yana murmushi yana kallonta ya ce, ""Jidda kin Sata min rai, ana cikin irin wannan yanayi kawai ki tafi gidan Didi? Kuma ba ma ki Wauki mota ba, ki ka hau keke napep kika tafi ke kaWai. Ga ruwa anyi a ranar, ga yamma, ga adadin abubuwan da suka faru. Why Jidda...!"" Ya faWa yana kallon ciwon hannunta. Ya sake kallon fuskar ta ya ce, ""kalli sakamakon fita babu izinina abinda ya jawo miki, da baki fita ba da jini bai"

"zuba a jikinki ba."""

"Ganin murmushin ya gushe daga kan fuskarsa sai ta rausayar da kai ta ce, ""ka yi ha™uri, wallahi tsoron gidan na dinga ji. Tunda na ganka da jini a jikinka shikenan na rasa nutsuwata, sai nake gani kamar wani abun zai same ni a gidan nan. Kuma wallahi na kira ka baka Wauka ba, sai na yi maka message na faWa maka. Kuma na san baza ka hana ni zuwa gidan Didi ba shiyasa na tafi."""

"""Da ki ka fita Win me ya faru? ˜o™arin kashe min ke aka yi Jidda, kai tsaye kashe ki suka yi niyar yi ba wannan ciwon ba. Har waya aka ™wace miki, kina tunanin wannan abinda ya faru dake Win zai saka naji daWi a zuciyata?."""

"""Ka yi ha™uri, bazan sake ba."""

"""Jidda kin san da cewa duk motsinki akan idanunsu yake? Ina da ma™iya masu son ganin bayana, ina da abokan gaba da muka cutar da juna a baya suna so su Wauki fansa a kaina ko a kan ahlina. Kina fita daga gidan nan aka bi bayanki, ba dan Allah ya taimaka Tk ya gani ba da me zai faru? Da bai je a lokacin da ake ™o™arin sukar ki a cikin ki fa?. Iya wannan ciwon da suka ji miki basu cuce ni ba Jidda?"" ya ™arasa faWa cikin rauni yana kallon ta."

"Nayla a sanyaye ta ce, ""ka yi ha™uri."" Ya sauke numfashi ya ce, ""Jidda hannunki aka yanka da wu™a fa, jini ya S ata jikin ki gabaWaya..."" ya yi shiru yana girgiza kai ya ce, ""na faWa miki wani abu..? Ni Omar na zubar da harkar daba saboda Didi, na watsar da makamaina saboda ita kawai. Duk wani wanda muke tare ya san Didi ce raunina, na yarda na cutu indai zata zauna lafiya. An kawowa Didi hari ana neman rayuwarta ko lafiyarta sau babu adadi, wannan dalilin ya saka na hana kowa shiga gidanmu, sannan duk wanda zai shiga za a sanar dani. Wannan shine dalilina na ko ina Didi zata je ana biye da ita, hatta lokacin da take zuwa makaranta ana yi min gadinta ba tare da ta sani ba. Saboda lafiyar Didi ban taSa zuwa wani waje na kwana ba, duk dare sai na dawo gida wajanta saboda kar wani abun ya same ta. Akwai masu jin haushina da zasu wuce akan Didi in basu samu dama a kaina ba. """

"Ya yi shiru yana kallon ta kafin ya Wauke ido daga kanta, ya sake kallon ta ya ce, ""Saboda kar a cutar da ita na daina cutarwa da kowa danginsa, na zubar da makamaina na dawo gida na zauna a tare da ita. Ba dan ina jin tsoro ba, ba dan na ja da baya ba, ba dan an fi ™arfina ba, ba dan anyi nasara a kaina ba, sai dan saboda kar wani abun ya same ta."""

"Ya murza yatsun hannunta ya ce, ""Yanzu ba Didi ce kaWai dangina ba, har dake, kuma kece a kusa dani a yanzu ba ita ba, ke zasu fi kawowa hari fiye da kowa. Kina ganin abinda ya same ki dai, duk hakan ya faru ta dalilina. Anya zan yafewa kaina abinda ya faru Jidda!?."""

"Nayla ta girgiza kai tana kallon sa ya ce, ""baki san hawa ba, baki san sauka ba, bake kika aikata laifin ba,"

"lokacin da na aikata ban sanki ba, lokacin da na aikata baki sanni ba, lokacin da na aikata ban taSa kawo batun aure a zuciyata ba balle na san zan aure ki. Amma gashi hukunci ya sauka a kanki, ciwo ne a hannunki a matsayin sakamakon laifun da na aikata. Jidda ban kyautawa Abiy da ya bani amanarki ba, sannan zaman aurena dake bashi da wani amfani a gare ki sai cutarwa."""

"Ya dam™e hannunta gam ya ce, ""bana so na rasa ki Jidda, bana so wani abun ya same ki ta dalilina. Na gaza kula dake, na gaza baki kariya har aka ji miki ciwo aka zubar miki da jini. Ke ba kalar macen da zata shiga tashin hankali bace, sai yanzu nake sake tabbatar da baki dace da auren Omar ba! Baki dace ba Jidda!."" Nayla ta ce, ""YaMar babu wanda ya wuce ™addara."""

"""Ganganci ne wannan ba ™addara ba Jidda, ni na kai kaina tun farko, da ace ban aikata laifuka masu yawa a baya ba da hakan bai faru ba. Sau biyu kenan ana neman rayuwarki, sau biyu ana zuwa gidan nan dan a cutar dake, anya na zama miji na gari a wajanki kuwa Jidda!."""

"Ta ri™e hannunsa itama ta ce, ""Rouhii!"" Bai bari ta ™arasa ba ya ce, ""Ta silar laifukan mijinki ake neman rayuwarki, ana so a cutar dake dan a biya bashin da mijinki ya ci a shekarun baya. Ni ba miji na gari ne a gare ki ba Jidda, ban amsa wannan sunan ba"" ya faWa yana jan numfashi da™yar cikin ™unar abinda ya faru."

"Nayla ta ce, ""Wannan ba komai bane, ya riga ya wuce ai. Kuma Allah ya rubuta dole sai hakan ya faru, ko da"

"ban aureka ba wannan ciwon da naji yana cikin ™addarata."""

"""Bai wuce ba, lokacin da hakan ya faru a cikin azumi na Wauka ya wuce sai gashi ya sake faruwa.."" ya juyo ya kalle ta ya ce, ""akwai irinsu da yawa Jidda, ni kaina ban san adadinsu ba. Suna nan suna fakon rayuwata, in basu samu ba su nemi taki ko ta Didi. Ba iya Wal™iya ko Kb ne kaWai ba, akwai su da yawa Jidda, za a cutar min dake a wani wajan da bana nan, za a iya biyan bashin da na Wauka dake ko Didi Jidda. Shiyasa ban cancani na amsa sunan miji na gari a gare ki ba. Muryarsa tayi ™asa sosai cikin rauni da bugawar zuciya ya ce, Jidda na fara wani tunani akan zaman aurena dake, bana son cutar dake, bana so ki rasa rayuwarki ko lafiyarki ta dalilina"" ya ja numfashi ya ce, ""Jidda!"" Ya faWa yana jan sunan nata cikin wani yanayi tare da kallon idonta kamar yadda take kallonsa nasa gabanta ya faWuwa tana jin tsoron abinda zai fito daga bakinsa.KRB3P075 Nana haleema."

"Ganin ya shiru yana kallon idonta bai ce komai ba sai ta daure ta ce, ""me ka ke shirin faWa?"" Ta faWa tana zare ido waje. Ya Wauke ido daga kallon ta yana jin ™irjinsa yana bugawa sosai, idanunsa har tara ruwa yaji suna yi saboda tashin hankali. Ya sauke numfashi ya ce, ""Bazan iya rabuwa dake ba Jidda, rabuwa dake kamar rabuwa da numfashina ne."""

"Ta yi murmushi tare da ajiyar zuciya ta ce, ""me ya kawo batun rabuwa kuma?."" Ya sake kallon idonta ya ce,"

"""Jidda bana so a cutar dake, bana so wani abun ya sake samun ki. Shiyasa. "" Ta katse shi ta ce, ""shiyasa ka ke"

"tunanin rabuwa dani?."""

"Ya girgiza kai alamun a'a bai ce komai ba. Ta ce, ""daman akwai damuwar da zamu shiga har ka yi tunanin"

"rabuwa dani YaMar?."" Ya matsa kusa da ita sosai ya ce, ""bana so naga kina yin koda ciwon kai Jidda, har din™i aka yi miki a hannunki. Jidda ciwo nake ji a zuciyata wallahi."""

"Ta haWe rai tana kallonsa ta ce, ""akan wannan ™aramin dalilin sai ka yi wannan tunanin? Ashe daman soyayyar da ka ke yi min iyakacinta kenan?."" Ganin ta haWe rai alamun bata ji daWi ba sai ya murmusa ya ri™e fuskarta ya fara kissing bakinta cikin salon soyayya da son kwantar mata da hankali. A hankali ya zare bakinsa da nata yana ri™e da fuskarta ya ce, ""ina sonki, ina ™aunar ki. Rabuwa da ke daidai yake da rabuwa da raina."" Cikin shagwaS a ta ce, ""to shine ka ke wancan tunanin?."""

"Ya sauke numfashi ya ce, ""tsoron nake ji, da ace wani abun ya same ki ta dalilina gwara na mayar dake wajan"

"Abiy kin cigaba da zama cikin kwanciyar hankali. Rashin ki zai yi min illa, rashin ki zai cutar dani, rashin ki zai zama ajalina Ashiq. Amma gwara na rasa raina da ace wani abun ya sake faruwa dake!."""

"Ta sauke numfashi cikin son kwantar masa da hankali ta ce, ""in sha Allah babu abinda zai faru, da izinin Allah"

"komai ya ™are, ka daina damuwa. Kuma don Allah ka daina yi min magana irin wannan, bana so."""

"Omar ya sauke ajiyar zuciya yana kallon ta cike da damuwa ya ce, ""Dole na damu Jidda, kalli hannunki fa,"

"ciwon yayi girman da sai da aka Winke shi. Har abada da wannan tabon zaki rayu har ki bar duniya, iya kallon wannan tabon na hannun ki ba ™aramin ciwo zai saka min a zuciyata ba, saboda na san ni ne sila. Baki da tabo ko kaWan a jikin ki, amma ta silata gashi kin samu tabo mai girma. Wallahi ban taSa jin na damu akan abinda na aikata a baya ba sai yanzu. Kuma nima haka nayi, matar mutum ko ΄ar uwarsa da bata ji ba bata gani ba a kanta zan mu Wauki fansa, duk da ban taSa kisa ba, amma na..."" sai ya kasa ™arasawa ya sake jan numfashi yana kallon ta ya ce, ""ina hasashen yanayin da zan kasance in wani ya yi irin abinda nayi a baya Jidda, ban san a"

"wanne yanayi zan kasance in aka sake cutar dake ba."""

"Nayla ta ri™e fuskarsa cike da damuwa ta ce, ""Rauni nake gani a fuskar mijina, mijina bai yi kama da namiji mai rauni ba."" Ya lumshe ido ya buWe ya ce, ""Nayi rauni Jidda, raunin zuciyata ne ya bayyana akan fuskata Jidda, wallahi zuciyata tayi rauni sosai. In na tuna ta silata kika kwana a asibiti da ciwo a hannun ki sai naji duniyar tayi min zafi. Wannan shine dalilin da na kasa sakewa dake, gani nake kamar za a cigaba da cutar dake in na cigaba da amsa suna mijinki"" ya faWa yana ri™e hannunta gam."

"Nayla ta ce, ""in sha Allah babu abinda zai faru, ka kwantar da hankalinka, Allah yana tare damu."" Ya bita da"

"kallo kafin ya Wauke ido daga kanta ya ce, ""Rayuwarki bata dace da rayuwa a nan ba Jidda, ina jin tsoron kar wani abun ya sake samun ki, ina jin wannan tsoron a zuciyata. Sai yanzu na sake gasgata maganar Didi da take cewa baki dace dani ba!."" Nayla a sanyaye ta ce, ""YaMar ka daina faWar haka, yana cutar dani."""

"""Jidda har suma ki ka yi fa saboda tsoro, kika kwanta a asibiti saboda ciwon da aka ji miki. In aka sake cutar"

"dake da wanne ido zan kalli Abiy?."""

"""Babu abinda zai kuma samu na, ka daina damuwa don Allah."" Ya lumshe ido ya buWe ya kalle ta ya ce, ""Ki yi ha ™uri, na kasa kula da lafiyarki har aka ™wace miki waya, na kasa kula dake har aka yanke ki jini ya zuba daga jikin ki. Ki yafe min, aurena ne ya saka kika shiga yanayin da ki ka shiga, da baki aure ni ba da hakan bai faru ba."""

"Ta saka hannunta a tsakanin kafaWarsa ta ri™e shi tare da kwantar da kanta a jikinsa ta ce, ""Ka daina faWar haka, bana jin daWi ko kaWan. Kuma ciwon da naji ™addara ce."" Ya Wan lumshe ido ya buWe yana ji zuciyarsa na bugawa sosai."

"Nayla ta ce, ""Ya jikin wanda suka jiwa ciwo?."""

"""Ya ji sau™i, yana gida."" ""An kama su ko?."""

"""Uhum, amma bazai jima ba zai fito. Yana da manyan da suka tsaya masa, baza su bar shi ya jima a gidan yari ba."""

"""Ko ya fito bazai yi mana komai ba, ka daina damuwa."""

"Numfashi ya sauke baice komai ba, yana jin zuciyarsa babu daWi akan abinda ya faru, ya san duk ta silarsa ta shiga yanayin da ta shiga. Sai yanzu yake jin raWaWin da iyaye da ΄an uwan wasu suka ji a lokacin da yake cutar da yaransu. Sai da ya ga Nayla a kwance a gadon asibiti sannan ya tabbatar da ba ™aramin cutar da ΄an uwan wasu suka yi ba. Gashi Allah ya fara saka musu, ya cutar da matar wani an cutar da matarsa, ya zama silar zubar jinin wata shima an zubar da na matarsa, ya zama silar kwanciya a asibitin matar wani shima ga tasa ta kwanta. Addu'a yake yi da fatan Allah yasa abun ya tsaya iya haka, in kuma sakayyar zata cigaba da bibiyarsa Allah yasa ta tsaya a kansa ba sai ta tsallaka kan Nayla ko Didi ba."

"Nayla ta kalle shi ganin ya yi shiru yana tunani, ta zame ta zube guiwa a ™asa ta ce, ""zan iya ro™ar ka alfarma?."" Ya Waga mata kai alamun eh, ta ri™e hannunsa ta ce, ""Don Allah ko me zai faru kar ka ce zaka koma rayuwar da ka bari a baya, ko meye zai tunkaro mu ka karSi ™addara kar ka tunzura ka koma rayuwar baya Rouhi. Ko da zasu kashe ni, ka yi min al™awarin baza ka cutar da kowa ba."""

"Ya yi murmushin gefen baki yana kallon ta ya ce, ""ke kin san bana yin kara, bana faWar abu dan na burge wani ko wata. Wallahil azim duk wanda ya sake ™o™arin cutar dake sai dai a haifi wani ba shi ba, wannan da aka yi na ™yale tunda an kama wanda ya aikata, amma in aka maimaita wallahi bazan ™yale ba. Jidda ko ban kashe shi ba sai nayi masa abinda zai ji ina ma ya mutu. Daga ranar kundin laifukan Omar Tiger da aka rufe za a buWe sabo, domin kuwa laifukan da na yi a baya ba komai bane akan wanda zan yi. Hmmm kedai Allah ya kiyaye kawai, amma zancen alfarma indai wannan ce bazan yi miki ba Jidda!."""

"Bata ce komai ba dan ta san bazai yi Win ba, ta rausayar da kai ta ce, ""ni kuma hakan bazai yi min daWi ba."" Bai ce komai ba ya girgiza kai kawai, ta ce, ""sannan wannan wu™ar da ka ke kwana da ita ta meye?."" Ya kalli idonta ya ce, ""ko a addini dan na kwana da makami ba laifi bane, tunda na tare a gidan nan take kusa dani, duk

Please Login or Register in order to submit comment