ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

™ as™anci ne ΄arsu ta so Omar. Yanzu zancen asiri suke yi, sun ce asiri ya yi mata take sonsa, ko nazo na karya asirin ko kuma bazan sake ganinsa ba har abada!& ..Kashe Omar suke son yi, kashe shi suke son yi kawai! Ta faWa da rauni tana hawaye mai taSa zuciya."

"Nayla kuka take yi sosai wanda ya bawa kowa mamaki, sun santa da tausayi sosai kuma tsaf labarin zai iya saka"

"ta kuka. Amma yadda take kuka da zuciyarta da gangar jikinta zaka tabbatar da ba iya kukan tausayi take yi ba akwai wani abun a cikin zuciyarta. Hajja a sanyaye ta ce,  Aisha na ce ki yi ha™uri komai zai zo ™arshe in sha Allah. Didi ta ce,  Hajja wallahi mahaifiyar Narma so take a kashe Omaar, yanayin kalamanta kashe shi suke son yi kawai. Sun san in sun kashe shi sun kashe banza tunda bashi da gata, bashi da wani gatan da za a neme shi shiyasa. "

"Hajja ta ce,  su Baba Adamu dasu Kawu duk babu wanda zai samu hanyar magana da Sanata?. Didi ta ce,"

" Tunda har Daddyn Salma bai samu ba bana tunanin zasu samu. Kuma ni ko faWa musu ma ban yi ba, ban saba kai damuwata gare su ba na saba ni da Omaar mu ke warware ko meye in ya tunkaro mu. Ban sani ba ko sun ji a gari amma ni ban sanar musu da komai ba. Hajja ta ce,  ai ya kamata ace sun sani Aisha, iyayen Omar ne fa, ya kamata a sanar dasu ko da addu a su taya mu. "

"Didi ta ce,  Hajja yanzu bana cikin wannan nutsuwar, hankalina baya jikina wallahi. "

"Nayla dai kuka take yi har sautin nata kukan yafi na Didi fita, Didi ta kalle ta cikin rauni tace,  ki bar Kuka Nayla,"

"ni ban faWa miki dan ki yi kuka ba. Ki share hawayenki. Nayla ta kalli Didi cikin muryar kuka ta ce,  Didi ki yi ha™uri in sha Allah zan yi ko meye ganin na dawo dashi, zan yi duk abinda zanyi dan ganin ya bar hannunsu. "

"Didi ta murmusa cikin tsokana da son kawar da damuwa ta ce,  na Wauka zaki barshi a can kawai, kin manta"

"tsorataki yake yi?. Nayla bata yi murmushi ba sai ma hawayen da ya sake sakkowa daga idonta ta ce,  Didi ba maganar wasa nake yi ba, zan yi ko meye ganin na dawo da shi. "

"Didi tayi murmushi ta ce, to Nayla. Na gode sosai Allah ya bar zumunci. Idanu Nayla ta goge ta kulle idanun"

"nata, ita kaWai ta san raWaWin da take ji akan rashin Omar, ita kaWai ta san azabar da zuciyarta take mata akan Omar. Dole ta san abinda zata yi ta fito da Omar, ko meye shi kuwa zata aikata in dai zai dawo. Zata iya sadaukar da komai dan Omar ya dawo, zata iya rasa komai indai Omar zai fito ta amince."

Ganin tayi shiru sai kowa ya yi shiru Salma da Jidda dai kallon Nayla kawai suke yi cikin tuhuma. Nayla sai ta mi

"™e ta shiga Waki tayi alwala tayi sallar azahar kafin ta dawo falon. Abinci ta tarar suna ci, Hajja ta kalle ta tace,  baza ki ci abincin ba?. Nayla ta ce,  bana jin yunwa, kaina ciwo yake yi. Jidda ta ce,  dole kan ki ya yi ciwo, kin zo daga Kaduna ko hutawa baki yi ba kina taho nan, ga kukan da ki ka yi gashi ko abinci baki ci ba, ai dole ki yi ciwon kai. Hajja ta ce,  Hauwa u me yasa haka?. "

"Kallon Jidda ta yi tace,  Twiny mu je gida ta faWa tana Waukar mayafinta da yake wajan. Jidda ta ce,  ki ka"

ce sai anjima zamu tafi.

" Na fasa, mu tafi yanzu. Salma zaki je bikin ko baza ki ba?. "

" Zan je mana. Nayla ta ce,  ku zo mu tafi, Hajja sai gobe abinda ta ce kenan ta fita da hanzari bayan ta"

Wauki key Win motar Jidda ta fita dashi.

"A mazaunin driver ta zauna ganin haka sai suka shiga motar ta ja motar da ™arfin gaske suka tafi. Gudu take yi sosai ga yanayin gari na juma a a cushe garin yake da mutane amma haka take gudu kamar zasu bar gari burinta kawai ta je gida. Jidda da take a zaune a gaba ta kalle ta ta ce,  Twiny wai lafiyar ki kuwa? Wannan gudun da ki ke yi na meye?. "

"Bata yi magana ba Salma da take baya ta ce,  malama magana ake miki ki rage gudu Ina zamu je? Sai gudu ki"

"ke yi kamar zaki tashi sama. Daidai nan suka ™araso gate Win gidan ta dinga danna horn dashi ™arfi, mai gadi ya buWe da gaggawa ta shiga da motar ganin motar Abiy tana nan ko parking daidai bata yi ba ta fita daga motar da sauri."

"Jidda ta kalli Salma ta ce,  lafiyar ta kuwa?. Salma tayi tsaki ta ce,  ™iris ya rage bata saka mun ba™unci lahira ba, ko aure ban yi ba zata kashe ni. Jidda tayi dariya suka shiga cikin gidan."

A zaune suka same ta a gaban Abiy da yake waya suma suka zauna saboda ya kammala. Kashe wayar ya yi ya

"kalli Nayla ya ce, ""Mamana lafiya ki ke kuwa? Meye ya same ki haka fuskarki tayi ja haka?."" Nayla ta ce, ""Abiy ai ka san Didi ko?."" Abiy ya ce, ""Wacece Didi kuma?."""

"""Ma™ociyar Hajja Yayar...."" Kafin ta ™arasa ya ce, ""Oh Yayar Wan daban nan ko? Na gane ta, da Aisha na santa ni ba wani Didi ba. Mutuwa tayi?."""

"Nayla gaban taya buga dum jin da sunan da Abiy ya kira Omar dashi, amma bata nuna ba ta ce, ""da ranta."""

"Abiy ya ce, ""to lafiya ki ka shigo a firgice haka?."" Jidda ta ce, ""Haka ta dinga gudu damu a titi Abiy, gari ya cushe mutane an dawo daga masallacin juma'a amma bata daina ba, ™iris ya rage bamu yi hatsari ba."" Abiy ya kalli Jidda ya ce, ""Wai daman ba Jawad ne ya shigo da mota a guje ba itace?."""

"""Wallahi itace"" ta bashi amsa tana kallon Nayla."

"Ya kalli Nayla a nutse ya ce, ""Me ya faru haka?."" Nayla ta ce, ""Tausayin Didi nake ji Abiy, an kama mata ™aninta sai kuka take yi har da zazzaSi. Don Allah Abiy ka taimaka a fito dashi don Allah."" Abiy ya bita da kallo cikim mamaki ya ce, ""akan wannan ne kika kusa kashe kanki da ΄an uwanki?."""

"""Na kasa sarrafa kaina ne kawai Abiy, bana jin daWi a zuciyata, Didi tana sona, nima ina son abinda take so."" Abiy ya kalle ta a nutse ya ce, ""mun yi maganar da Hajja jiya sai dai ba a bani labari duka ba aka kira ni a waya. Waye ya saka aka kama shi Win sannan me ya yi?."""

"Shiru tayi bata amsa ba ya ce, ""ke nake saurare, me ya yi aka kama shi har kike so na fito dashi?. Ko wani ya"

"kashe?."" Ta girgiza kai alamun a a ya ce, ""to faWi."" Nayla ta ce, ""Dama ya je gidan Sen Sagir Sani ne, shine ya saka aka kama shi."""

"""Me ya je yi gidan? Sata ko kuma kisan kai?."" Salma ce ta bawa Abiy labarin abinda ya faru kaf har zuwan Didi wajansa. Abiy ya girgiza kai cikin mamakin ™arfin halin Omar ya ce, ""Barr Narma ya je yace yana so? Kuma yana da hankali?."" Salma ta ce, ""gashi nan dai akwai Abiy."""

"Abiy ya ce, ""gaskiya dai gashi nan dai kawai, dan in har yana da hankali to tabbas shaye-shayen su na Sata gari ya taSa masa ™wa™walwa. In ba haka ba ya Wauki ™afa ya je ya ce yana son ΄ar Sen Sagir? Ya san waye Sen Sagir kuwa?."" Suka yi shiru Abiy ya ce, ""To ai ko zauna gari banza wanda bashi da komai ya je ya ce masa yana son ΄arsa dole ya Wauki mataki balle Sen. Kuma dole ya ce asiri ya yiwa mata take sonsa. Meye abin so a tare dashi har da zata fita hankalinta haka?."" Nayla dai wani irin sanyi jikinta ya yi da jin kalaman Abiy, zuciyarta na bugawa, guiwarta kamar ana dukanta saboda sagewar da tayi."

"Abiy ya numfasa ya ce, ""well, ya taimaki Nayla a lokacin da take bu™atar taimako, ya kuSutar da ita daga masu sharrin fyaWe. Ya cancanci na taimaka masa a fito dashi tunda ba wani laifi ya aikata ba. Na san Sen Sagir sosai, abokina ne sosai tare muka yi ABU Zaria. Kuma ni ne class captain a lokacin, bara mu ga"" ya faWa yana Waukar waya yana dubawa."

"A speaker Abiy ya saka kiran daga can Sangaren Sen yana Wauka ya ce, ""Class Captain. !."" Abiy ya murmusa"

"ya ce,  ni Wauka baka da number ta ai. Sen yayi dariya ya ce,  Haba ni na isa nace bani da number ka?.  Ka isa mana Sem, ai ka kai matsayin da ba number kowa zaka ajiiye ba. "

" Ai kai kana cikin mutane na farko a wayata. Abiy yayi murmushi suka gaisa cikin wasa da dariya na ΄an makaranta kafin Abiy ya ce,  kwanaki nazo Abuja na karSi offer ta ΄ar wajena Nayla, naso nazo wajan ka sai kuma na sha afa wallahi. "

"Sanata ya ce,  gaskiya baka kyauta ba, duk da dai nima kwanaki na shiga Zaria naso na kira ka wallahi dare ya"

yi min. 

" Haka ne, komai sai Allah ya yi. "

 A wacce ma aikata ta samu aikin?.  FIRS.

" Haba Captain, me zata yi da wannan ™aramin aikin da salary sa bai wuce 400k per month ba? Ga aiki a nan Abuja da zata samu kuWi me zata yi da 400k kamar wata almajira?. Abiy ya yi dariya kafin ya yi magana Sen ya ce,  ka turo ta Abuja akwai aikin da zan bata, 900k ne per month banda allowances da suke shigowa. Shima dai tayi manage kawai. "

"Abiy ya yi dariya ya ce, Senator! Ai ba dan salary take aiki ba, hakan burinta ne shiyasa kawai na bari tana yi. "

"Sen ya ce,  Sai ta cika burinta da abu mai kyau ba wannan ba, ka rasa aikin da zaka bata sai wannan ™aramin aikin? Me zata yi da kuWin da bai wuce albashin house maids Win gidansu ba?& Ka turo min ita kawai, zan cika mata burinta da aiki mai kyau, in kana tunanin baka so ta zauna ita kaWai a guest house sai ta zauna a gidana wajan Narma da Najwa. "

"Abiy ya ce, A a, barta a Kaduna kusa dani ya fi. Nayla me zata yi da kuWi tana yarinya ™arama?. Tana da shop fa. Senator ya yi dariya ya ce,  Najwa ba ma Narma ko Nabil ba, itace take kula da Sangare guda na companyna, kuma tana aiki sannan itama tana da shops. Ai yaran yanzu sai da kuWi Captain, haka duniyar ta zama. "

"Abiy ya ce, kana Abuja ne?. Sen ya ce, A a ina Kano, nazo Waurin aure ΄ar sarkin Kano da za a yi gobe. Abiy ya ce,  nima Ina Kano Win, gobe zan kuma shiga Waurin auren in sha Allah. Sen ya ce,  to ya kamata mu haWu gabaWayan mu, dan yawancin ΄an class Winmu duk suna nan goben. Abiy ya ce,  Allah ya kaimu goben, sai mu haWu gabaWaya yi zumunci a samu lada. Sen ya amsa yana dariya kafin su yi sallama Abiy ya kashe wayar."

"Kallon Nayla ya yi da ta sunkuyar da kai ya ce,  Gobe zan yi masa maganar Omar Win, in sha Allah zai dawo. "

"Nayla farin ciki take ji a zuciyarta har hakan ya bayyana akan fuskarta, ta ce,  to Abiy na gode. Abiy ya kalle ta a nutse ya ce,  ga murmushi nan kina yi, da alama dai shima kina shiri dashi sosai ko? Ya tambaya da niyar bugun cikinta."

"Sunkuyar da kai tayi ta ce,  A a Abiy, ko magana bamu taSa yi ba, ni saboda Yayarsa kawai nake so ya fito. "

"Abiy ya girgiza kai ya ce, ko dan taimaka miki da ya yi a shekarun baya ai ya cancanci ki so ya fito. Kar ki damu komai ya ™are. Nayla ta yi dariya tana kallon Mama da ta zuba mata ido tana kallon ta."

"Da sauri ta tashi ta shiga Waki Salma da Jidda suka bita. Murmushi suka samu tana yi a bayyane tana cewa,  zan zama silar fitowar Omar in sha Allah, in sha Allah zai fito. Wayyo daWi, Allah na gode maka. Jidda ta kalli Salma da suke kallon Nayla da mamaki, Jidda ta girgiza kai tana gasgata abinda take zargi a zuciyarta. Jidda ta ce,  Twiny ko dai Omar shine wanda ki ke so?!. KRB2P006"

Arewabooks@nanahaleema11.

"Nayla gabanta ya faWi sosai, ta jiyo a firgice tana kallon su dan tambayar tazo mata babu zato babu tsammani. Duk sun tsare ta da ido suna jira su ji abinda zata ce. Kallon kallo ake a tsakanin ta su, suna jiran amsarta ita kuma duk ta firgice. Salma ta ce, ""tambayar ki mu ke yi Nayla, Omar ™anin Didi shine wanda ki ke so Win?."" Tayi ™o™arin dakewa da son Soye damuwarta ta ce, ""Wacce irin magana ce wannnan? Ni ba haka bane ba."""

"Jidda ta ce, ""to meyasa muryarki take cracking? Meyasa ki ka ji tsoron tambayar da muka yi miki?. Sannan"

"meyasa hankalinki ya tashi a kan ance yana cikin wahala?, gudu kika dinga yi da mota sai da kika zo ki ka samu Abiy sannan hankalinki ya kwanta. Ki faWa mana shine wanda ki ke so Win?. Duk alamomin soyayya ya bayyana a yanayin ki, yadda ki ka za™e a kansa ya saka muna zargin shine wanda soyayyarsa take wahalar dake, ki amsa"

"mana Nayla."""

"""Eh shine!"" Ta faWa a sanyaye tana zubewa a kan gado tana sake fashewa da kuka. A tare suka wara idanu Jidda ta ™arasa inda Nayla take dan Salma tayi suman tsaye. Jidda ta zauna kusa ta da ita ta ce, ""Twiny da gaske shi ki ke so?."" Kai ta Waga tana kuka ta ce, ""Shine Twiny. Ban san ya akayi hakan ta faru ba, na san dai tsoronsa nake ji amma ban ya akayi na fara sonsa ba. Nayi kuka, na yi addu'a amma na kasa cire shi daga zuciyata. Bai san ina yi ba, tunda shi Abuja ya je neman aure a gidan su wata bani ba, amma duk da haka bana jin haushinsa Twiny."""

"A kan kafaWar Jidda ta Wora kanta tana kuka sosai Jidda tana shafa kanta dan bata san ne zata ce mata ba. Salma da™yar ta iya motsawa tazo wajan da suke ta zauna a Waya gefen ya zama sun saka Nayla a tsakiya kenan. Salma ta ce, ""Nayla wai Omar Win Didi ki ke so?."""

"Bata iya bata amsa ba sai numfashi da take saukewa a jikin Jidda. Salma ta ce, ""Innalillahi! Mun shiga uku."""

"Nayla ta Wago daga jikin Jidda idanunta sun ji™e da hawaye ta ce, ""shiyasa na™i faWa muku saboda faWar babu amfani Salma. Babu ribar da zan samu da soyayyarsa, wahalar da ni kawai take yi wata™ila tayi ajalina. Wallahi duk samarin da Abiy yake basu damar ganina na kasa kallon kowa da fuskar so, shi kaWai nake so, shi kaWai zuciyata take da burin aure, shi kaWai nake ji a raina in ban aura ba kamar bazan iya zaman aure da kowa ba, na kuma san bazan taSa mallakarsa ba har abada."""

"Jidda a sanyaye ta ce, ""Meyasa ki ka ce haka?."" Tayi murmushi ta ce, ""baki ji me Abiy ya ce bane? Ko zauna gari"

"banza yaje yace yana neman aure a gidansa baza a bashi ba balle gidan Sen. Dame Sen ya fi Abiy Twiny? Mulki kawai ya fi Abiy, amma duk abinda ya mallaka a duniya Abiy ma ya mallaka. Kinga kenan harda gidan mu a cikin gidajen da baza'a bashi aure ba, ni daman na san aurena dashi bazai yu ba shiyasa ban sakawa zuciyata zan aure shi ba. Kuma shi bai ma san ina sonsa ba."""

"Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, ""gaskiya ne zancen ki Nayla, auren Omar bana hango yuwarsa a rayuwarki."

"Gwara mu faWa miki gaskiya kar mu cuce ki mu yaudari zuciyarki da kalamai na ™arya dan mu kwantar miki da hankali. Omar ba irin wanda ya cancanci a bashi aure bane, sam ba tsarin auren ki bane."""

"""Na sani Salma. In ba dan Wabi'arsa ba ni zan iya zama dashi, ban damu da bashi da kuWi ko bashi da wani abu ba. To Wabi'a sa baza ta taSa sakawa Abiy ya amince ba, Inda Abiy zai amince ni zan iya zama dashi a haka, koda zai dinga bani tsoro kamar yadda yake yi ko yaushe na shirya Salma. "" ta sake faWa a sanyaye"

"hawaye na sakkowa. Jidda ta kalle ta da kulawa ta ce, ""kuma kin ce bai ma san kina sonsa ba ko?."""

"""Bai sani ba, kuma bana fatan ya sani Win. Domin Didi ta faWar min kalar wula™ancin da ya yiwa Narma a lokacin da ta je gidan su ta ce tana sonsa. Da™yar ta iya samun kansa har ya amince mata, jin kunnena naji yana waya yana yi mata faWa kamar ba wacce yake so ba. Wata™ila soyayyarsa kashe ni zata yi, dan wallahil azim ina matu™ar son Omar, Ina matu™ar ™aunarsa, ina yi masa ™aunar da ban taSa yiwa wata halitta a duniya ba sai shi. Matu™ar dauriya nake yi, juriya da ha™uri da jajircewa nake yi nake iya sarrafa zuciyata akansa. Amma ha™uri na ya fara ™arewa, gab nake da karaya..."" ta faWa tana kuka sosai."

"Salma ta rungume ta tana kuka itama cikin tausayin ΄ar uwarta. Jidda a bayan Nayla ta Wora hanunta cikin tausayin Nayla, dan yanda Naylan take yin maganar zai baka tabbacin daga zuciyarta maganar take fitowa. Sun jima a haka ko wacce na kuka kafin Nayla ta tsayar da kukan ta ce, ""Abiy ya bani lokaci na fitar da wanda nake so a cikin mutune huWu. Wallahi bana son su duka, bana tunanin zan iya zaman aure da Waya daga cikin su, ko na zauna zuciyata tana ga Omar ba ga wanda na aura ba. Ya zanyi? Ku faWa min abinda zan yi na daina sonsa don Allah!"" Ta faWa da rauni wanda ya saka su Jidda sake fashewa da kuka."

"Duka kuka suke yi da™yar Salma ta iya dakatawa ta ce, ""Addu'a zaki yi Nayla, addu'a zamu dage da yi Allah ya kawo mana mafita."" Nayla ta ce, ""Ina addu'a Salma, Ina yin addu'a babu dare babu rana. Wallahi zuwan mu"

"umra ban san adadin addu'ar da nayi akan lamarin nan ba, kuka na ke yiwa Allah Ina faWa masa ya cire min son Omar daga zuciyata amma soyayyar ta™i fita. In ina kuka a cikin sujjada ina faWawa Allah damuwata sai na yi awa Waya a haka ban san nayi ba. In aka cigaba da haka zan mutu ne kawai, dan na san bazan same shi a matsayin miji ba mutuwar itace hutu a gare ni."""

"Jidda ta ce, ""kar ki sare, ki cigaba da addu'a Allah zai miki magani Nayla. In kika ro™a yau Allah bai baki ba ki ™ ara ro™a gobe, yana ji kuma yana gani, shi ya ™addara miki kuma shi ya nufe ki da fara son Omar. Allah ya san damuwarki amma yace ki ro™e shi zai yaye miki, kar ki sare Nayla, kar guiwarki ta yi sanyi akan addu'a, ki cigaba kar ki tsaya. Ki yi ha™uri."" Basu hanata kuka ba dan ya cancanci tayi kukan, zuciyarta ta yaudare ta da ta fara son wanda auren ta dashi bazai taSa yuwa ba. Shiyasa suka barta tayi kukan son ranta ko dan taji daWi a zuciyarta. Ai kam ta kwashe sama da mintina ashirin tana kuka, zuwa lokacin kanta ya yi nauyi zazzaSi ya rufe ta ruf."

Salma ce ta kwantar da ita ta tashi ta samo towel a banWaki ta ji™a shi da ruwan sanyi tana goge mata fuska da wuyanta. Rarrashin ta suka dinga yi har ta daina kukan Salma ta takura mata ta sha magani suna zaune a gefenta. A hankali kuma sai tayi bacci su dai kallon ta suke yi cikin tausayi.

"Salma da Jidda fita suka yi zuwa harabar gidan dan su tattauna abinda ya kamata su yi. Salma ta ce, ""Zuciyar"

"Nayla bata yi mata adalci ba da ta fara son Omar Jidda, gashi bai ma san tana yi ba, sannan ko ni bazan goyi bayan ta aure shi ba duk da son da take masa."""

"Jidda ta ce, ""yanzu meye abin yi? Wanne abu ki ke ganin zamu yi da zai taimaka mata?. Tana cikin halin azabar"

"so da raWaWi mai ciwo, ya ki ke ganin zamu yi?."""

"""Addu'a kawai zamu taya ta Jidda, to in ba addu'ar ba me zamu yi mata?. Zamu je mu samu Omar in ya fito mu ce masa Nayla na sonsa ne?. Ko zamu je mu samu Didi mu faWa mata?."""

"Jidda ta ce, ""Amma tana bu™atar Wauki Salma."" Salma ta ce, ""shiyasa na ce addu'a itace mafita."" Jidda ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba Salma ta ce, ""ikon Allah, shi kuma farin jinin mata masu hankali da kyau Allah ya bashi. Ki dai duba Nayla da Narma, a cikin babu wacce tayi sa'ar aurensa, amma lokaci Waya duk sun birkice a kansa kamar wani mutumin kirki? Anya ma ba asirin ya yi musu ba kuwa?."" Jidda tayi dariya ta ce, ""Wanne asiri ana zaune lafiya?."""

"""Allah Jidda abin da mamaki, ΄an mata zu™a-zu™a kamar Nayla da Narma ace sun birkice akan sa? ³an mata masu asali, kyau, ga arzu™i amma su rasa wa zasu fara so sai wani Omar....Omar Win ma na gidan Didi Wan daba wanda ko sana'a bashi da ita?. Allah lamarin nan abin dubawa ne, dan ni zuciyata ta fara amincewa da batun sanata akan asirin nan wallahi. Kuma da alama wanda sunan su fara daga N ne suke faWawa tarkonsa, wata™ila wani malamin ne ya bashi sa a akan Nayla da Narma. Aniyarsa ta bishi, in sha Allah Nayla tafi ™ arfinsa."" Ita dai Jidda dariya kawai take yi jin kalaman Salma na asiri."

"Sai yamma Nayla ta farka a lokacin har sun shirya tafiya bikin Shayida, ta bisu da kallo ta ce, ""har kun shirya?."""

"Jidda ta ce, ""ya ciwon kan?."" ""Ya yi sau™i sosai."""

"""To ki tashi ki yi sallah da wanka mu tafi."""

"""Anya zan iya zuwa Twiny? Ku je kawai basai naje ba."" Salma ta ce, ""A'a tashi ki shirya sai kin je, ganin mutane zai iya rage miki damuwa."" Ta dole suka saka ta wanka ta shirya suka fita zuwa wajan bikin gabaWaya.KRB2007 Arewabooks@nanahaleema11"

"Washe gari bayan sallar azahar Abiy da Senator da wasu manyan mutane su shida gabaWaya suna zaune a wani babban falo na alfarma suna hira da nishaWi ana tuna rayuwar makaranta. Su huWu a ciki duk ΄an siyasa ne, Abiy da wani ne kawai ba sa harkar siyasa."

"Ana cikin hira Abiy ya kalli Senator

Please Login or Register in order to submit comment